-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kafin Jiran Rancen Covid-19, Ga Alamu Bamu Fahimci Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Na Nirsal Microfinance Bank Ba, Karanta Cikakken Bayanin Rancen

Kafin Jiran Rancen Covid-19, Ga Alamu Bamu Fahimci Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Na Nirsal Microfinance Bank Ba, Karanta Cikakken Bayanin Rancen

Kafin Jiran Rancen Covid-19, Ga Alamu Bamu Fahimci Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Na Nirsal Microfinance Bank Ba, Karanta Cikakken Bayanin Rancen

Karin bayani akan bashi marar ruwa na NMFB.


Bashin da za a bayar marar ruwa through nirsal akwai benefit gasu wadanda zasu baka bashin wato suna da riba.

Andora tsarin bashin akan sharadi na 'Murabaha agreement' wato yarjejeniyar kasuwanci ta qe-qe da qe-qe  wato komai a bayyane. 

Misali ka nemi bashin 500K zaka sayi Generator 200K da Fridge150k da kuma wani abu shima na 150K.

To su nirsal zasu fada maka sunsayi wadannan abubuwan akan wacan farashin na 500K a gurin 'Vendor' (Kamfani ko kuma babban shago na siyayya) amma fa zaka sayi wannan kayan agurin nirsal ne kuma zaka basu riba ta 25% a jumulla kaga kenan zaka biya 625K total idan 500K akayi maka approving.

in kaya kake so shi zasu baka akan farashin da suke so su sayar wannan kaya wato tare da ribar su ta 25% na farashin da suka saya .

In kuma kudi kake so zasu iya baka amma fa har yanzu ribar su tana nan sabo da yarjejeniyar da kayi accepting ta murabaha agreement, kaga kenan misali kamar ka sayar masu da kayan ne akan farashin da suka sayo a wurin vendor, sai su baka kudin.

Most important part dai shine dole sai ka sayi kayan akan farashin nirsal na ribar 25% sannan in sun ga zasu iya baka kudin amatsayin sun saya a wurin ka on the same price da suka sayo sai su baka.



Note:

 An kirkiri wannan kalar bashin ne domin neman dachewa da Shari'ar addinin Musulunci na karbar bashi ba tare da ruwa ba, in kuma mun mashi duba na fahimta zamu ga su nirsal da suka baka suna da riba ne tunda sayar maka sukayi kuma kasan a nawa suka sayo sabo da haka in ka tashi mayarwa zaka mayar da kudin ne tare da ribarsu a jumlache.


Zamu iya Fuskantar wannan bayanin da nayi idan muka koma kan agreement offer da aka turawa wadan da suka samu.


Wallahu A'alam.

0 Response to "Kafin Jiran Rancen Covid-19, Ga Alamu Bamu Fahimci Sabon Tsarin Rance Marar Kuɗin Ruwa Na Nirsal Microfinance Bank Ba, Karanta Cikakken Bayanin Rancen"

Post a Comment