-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Nafisat Abdullahi

Tarihin Jaruma Nafisat Abdullahi

Jaruma Nafisat Abdullahi

Nafisat Abdullahi asalin sunan ta shine Nafisat Abdurrahman Abdullahi Amma anfi sanin ta da Nafisa Abdullahi ko Kuma Nafisa Sai Wata Rana.

An haifi jaruma Nafisat abdullahi a ranar 23 ga watan January a shekara ta dubu daya da dari Tara da casa'in da buyu 1992. Ta fara karatun ta na secondary a garin Jos Kuma ta karasa a Abuja. A shekarar 2013 an dakarada da ita daga shirin finan kannywood saboda ta karya doka

Ta karanci theater art a university of Jos, sannan ta karanci ilimin daukan hoto a landan a School Of Photography dake Birtaniya.


Shigar Jaruma Nafisa Abdullahi A kannywood

Nafisat abdullahi ta fara harkar film ne tun lokacin tana yar shekara sha takwas Kuma film din da ya fito da ita shine SAI WATA RANA a 2010 a karkashin FKD PRODUCTION Wanda Ali Nuhu ya bada umarni. Ta bayyana a cikin wani Nigerian film wato Nollywood Mai suna Blood and Heyna Wanda Kenneth Gyang ya bada umarni, tare da Ali Nuhu da Kuma Sadiq Sani Sadiq.

Sannan Jarumar tayi fim me suna Blood and heyna a shekarar 2012 mana‘antar nollywood tare da Sadiq Sani sadiq, da alinuhu. Tasamu nasarar shiga jerin kyaututtuka sama da shida da shirin. Kuma tasamu nasarar lashe kyautar karramawa ta kwararriyar jaruma daga 9th Africa Movie Academy Awards. 

Jarumar tayi shiri dadama a kannywood irinsu Abdulmalik, Ahalul kitab, Gaduhu ga haske daku lamiraj shirinda ya jamata nasarar lashe Gwarzuwar jaruma ashekarar 2013. 

Jarumar tasamu nasarori dadama kuma tana daya daga manyan jarumai Mata a masana‘antar ta kannywood wadda kawo yanzu tayi samada fina finai 50. Ashekarar 2020 taja ragamar wani shiri mai dogon zango wadda Aminu saira, tareda dan’uwansa Naziru Ahmad dakuma Nazifi Asnanic suka shirya mai suna “Labarina’Tare da jarumai da yawa kamarsu nuhu Abdullahi maryam waziri Da sauransu shirinda ake haskawa a tashar Arewa24. 

Ta fito a cikin fim din da Aminu saira ya bada umurni wato Ya daga Allah da kuma Kalamu wahid a shekarar 2014


Tayi finafinai da dama kamarsu: 

sai wata rana 2010, Blood and heyna 2012, 'ya daga Allah, madubin dubawa, toron giwa, ummi , yar agadez, ahalul kitab, alhini , baban sadiq, alhaki, kuikuyo, blood heyna, Dan marayam, zaki dare, cikin waye, guguwar so, zango laifin dadi, lamiraj 2013,  madubin, dubawa, cikin waye, , baiwar Allah, labarina 2020, labarina 2021 da sauransu.


Lamban girma Gyara

Ta samu kyautittikan girmamawa da dama irin su City People Entertainment Award 2013, sannan ta kasance jaruma ta daya a masana'antar Kanywood a shekara ta dubu biyu da sha hudu 2014.Jarumar ta karbi kautar girmamawa ta AMMA award a shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, MTN award a shekara ta dubu biyu da sha shida 2016, da Kuma Afro Hollywood award a shekara ta dubu biyu da sha bakwai 2017. Nafisa Abdullahi tayi soyyaya da Adam Zango har tayi burin aurenshi

Wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Nafisat Abdullahi























0 Response to "Tarihin Jaruma Nafisat Abdullahi"

Post a Comment