Tarihin Jaruma Maryuda Yusuf ( Salma Kwana Casa'in)
Jaruma Maryuda Yusuf ( Salma Kwana Casa'in)
Jaruma Maryuda Yusuf wadda aka fi sani da Salma acikin Kayataccen shirinnan na arewa24 mai dogon zango "LABARINA SERIES". Maryuda Yusuf na daya daga cikin sabin Jaruman kannywood da shigo a masana'antar Kannywood a baya-bayannan amma a yanzu haka jarumar tasamu daukaka da kuma shahara a masana'antar Kannywood.
An haife Maryuda Yusuf a jihar Kano 5 ga wata satumba 1997 kuma ta girma a kano, Maryuda Yusuf ta kammala karatunta cikin nasara inda ta yi makarantar firamare da sakandare a ƙasarta najeriya.
Kuma tare da lura da kuma kulawar iyayenta da suka yi mata, ta idarda kammala ƙarshen makarantar sakandare a ƙasashen waje. Daga nan An ta je jamhuriyar benin inda ta halarci shirin matakin digiri.
Jaruma Maryuda Yusuf ta fito a shirin fina-finai kamar irinsu:- Waƙa Shekara, Rawar Nau'in, Kwana Casa'in, Haram, Namijin Kishi, Karki Manta Dani, Halimatu Sadiya, Nana Fiddausi , Ciwon Idanuwa
Duba wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Maryuda Yusuf
0 Response to "Tarihin Jaruma Maryuda Yusuf ( Salma Kwana Casa'in)"
Post a Comment