-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Maryam Booth

Tarihin Jaruma Maryam Booth

 Jaruma Maryam Booth

Maryam Ado Muhammad (an haife ta watan October ranar 28, shekarar 1993), jaruma ce a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood. An haife ta a garin Kano. Yawancin iyalan gidansu ƴan fim ne. Mahaifiyar ta Zainab Booth fitacciyar jaruma ce a masana'antar Kannywood. Haka nan ma yayan ta Ahmad Booth shi ma jarumi ne na fim ɗin Hausa. Maryam ta yi makarantar Ebony Nursery, a karatu na matakin farko. Sannan kuma ta yi karatun sakandare a Ahmadiyya secondary school wadda ke a unguwar Briget a birnin Kano. Tun Maryam tana ƴar shekara 8 ta fara harkar fim lokacin da mahaifiyarta ta gabatar da ita ga masana'antar Kannywood.

Baya ga harkar fim kuma, Maryam na da kamfanin kayan kwalliya na ta mai suna MBooth Beauty Parlour.

Masana'antar Kannywood ta shiga ruɗani bayan bayyanar wani faifan bidiyo na tsiraici na Maryam Booth a shafukan Sada Zumunta

Wasu daga cikin hotunan Jaruma Maryam Booth 













0 Response to "Tarihin Jaruma Maryam Booth"

Post a Comment