Tarihin Jaruma Jamila Umar Nagudu (Jamila Nagudu)
Jaruma Jamila Umar Nagudu (Jamila Nagudu)
Jamila Umar Nagudu wadda aka fi sani da Jamila Nagudu fitacciyar jaruma ce a masana'antar kannywood dake kano. Jaruma Jamila Nagudu an haifata ne a ranar 10 ga watan Agusta Jamila Umar Nagudu dunbin masoyanta na cewa ita ce Sarauniyar Kannywood, ma'ana ita ce fitacciyar 'yar fim a fagen fina-finan Hausa wadda ke da hedikwata a Kano, arewacin Najeriya. Tana da matukar girmamawa daga al'ummar da ke magana da Hausa, ta ci lambobin yabo na masana'antu har sau bakwai. Wasu daga cikin fitattun hotunan Jaruma Jamila Nagudu
Jamila ta kasance yar wasan hausa wacce akafi kiranta ko sani da sarauniya saboda ficewarta a harkar shirya fina finan hausa. Jamila ta shigo harkar film da yawa a shekarun baya to amman ta zama wacce tayi suna da daukaka bayan da babban darakta malam Aminu Saira ya sanya ta a wani film na shi mai suna 'Jamila da Jamilu'. Tun lokacin ne Jamila ta zama sananniya a bangaren film din hausa.
Jaruma Jamila Umar Nagudu ta fito a fina-fianai da dama kamar shirin:- 'Ya 'Ya Na, Alhaki Kwikwiyo, Aska Tara, Bashin Gaba,bCikar Burina, Farin Dare, Fataken Dare, Fitilar Dare, Ga Fili Mai Doki, Gamdakatar, Halisa, Haske, Ranka (Kasha Kallo), Jamila Mai Wasa Da Kura, Jamila da Jamilu, Jani Jani, Jarumta, Kama Da Wane, Kanin Miji, Kishiya Ta, Komai Daren Dadewa Wahidin, Laifin Dadi, Larai, Mai Dalilin Aure (Match Maker), Marayan Zaki, Masu Aji, Mijina Sani , Muradi, Murmushin Alkawari, Na Hauwa, Nijeriya Da Nijar, Rayuwa Bayan Mutuwa, Sai Na Dawo 1,2,3, Sai a Lahira, Salma Hayat, Sa ar Kiwo, Shu'uma (The Evil Woman), Wani Gari, Waye Isashshe, Ya Salam, Zatona , Ƙayar Ruwa da dai sauranzu
Jamila ta fito a fina finai da dama kamar su Haske, Hindu, Jani-Jani, Farin Dare, Subulli da Subulluwa, wani gari dama dai sauran su. Jamila ta sami lambobin yabo da dama daga wajen daraktoci har zuwa kamfanoni. Kuma jakada ce ta Globacom
Duba wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Jamila Umar Nagudu
0 Response to "Tarihin Jaruma Jamila Umar Nagudu (Jamila Nagudu)"
Post a Comment