Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba – Adamar Kamaye
Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba – Adamar Kamaye
Daga: Ahmad Muhammad Inyass
Fitacciyar jaruman nan kuma wacce ta yi suna a cikin shirin nan mai dogon zango na “Dadin Kowa”, Hajiya Zaahra’u Sale wacce aka fi sani da Adamar Kamaye.
Jarumar ta bayyana burin da take dashi na yin aure, a kowanne lokaci matukar ta samu irin mijin da take mafarkin samu a rayuwa.
Fitacciyar jarumar ta sanar da haka ne a wata hira da tayi da jaridar Dimukaradiyya, inda suke tambayar ta ko tana da sha’awar yin aure kuwa, ganin yadda shekarunta suka ja.
Adama ta ce:
“Ba ni da aure a yanzu, sai dai ina da niyyar yin aure, idan Allah ya kawo mun miji nagari zan yi aure. To Amma ka san su maza har kullum ba sa yi wa matan adalci, wani lokacin kuma matan ne ba sa yi wa mazan adalci, to amma ina son, duk wani mai kauna ta da masoyana, su taya ni da addu’a Allah ya ba ni miji nagari wanda za mu zauna lafiya ni da shi” inji ta.
Source: Labarun Hausa
0 Response to "Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba – Adamar Kamaye"
Post a Comment