Asaukake: Yadda Mace Ko Namiji Zasu Nemi Rancen Cbn Daga Gida - Nirsal Household
Asaukake: Yadda Mace Ko Namiji Zasu Nemi Rancen Cbn Daga Gida - Nirsal Household
Babban bankin kasa wato CBN ya kara bude sabuwar kofa ga mata da maza mazauna gida da masu kananun masana’antu domin suma a dama da su a karkashin shirinnan na bada bashi wanda babu kudin ruwa a ciki (Non Interest Facilities). CBN ta fitar biliyan N50 (Non- Interest Targeted Credit Facility) domin wannan shiri.
Babban bankin na kasa ya bude wannan tsari ne ta karkashin bankin Nirsal Microfinance Bank wanda akaiwa taken Household da kuma SME (Small and Medium Rnterprises) domin ganin wadanda ke zaune a gida kuma suke yin kananun sana’oi sun amfana da irin wadannan damammaki.
YADDA ZAA CIKE WANNAN PROGRAM (HOUSEHOLD)
i. Za’a shiga wannan link: CLICK HERE sai a danna APPLY FOR NON-INTEREST FACILITY
ii Sai a danna NON-INTEREST TCF – APPLY. Za’aga wani fegi ya bude sai a danna APPLY FOR HOUSEHOLD FACILITY (NON-INTEREST)
iii. Bayan andanna za’aga inda za’a fara cikewa, sai a danna NEW. Idan mutum ya fara sai ya fita bai gama ba to sai ya danna RETURNING
iv. Za’aga wani fegi ya bude sai a karanta bayanan sannan a danna CONTINUE
v. Sai a danna NEXT sannan a saka BVN domin ayi Validating.
vi. Bayan an danna NEXT a inda za’aga bayanan da ke kan BVN
vii. Sai a danna NEXT a inda za’a cike bayanan mutum
viii. Bayan an danna NEXT sai cike bayanan sana’ar da mutun zai nemi wannan bashi. Yanada kyau a nema a bangaren noma da kiwo. Duk da ana iya cikewa da kowace sana’a.
ix. Sai a danna NEXT domin ayi cike ragowar bayanai da kuma submitting
0 Response to "Asaukake: Yadda Mace Ko Namiji Zasu Nemi Rancen Cbn Daga Gida - Nirsal Household"
Post a Comment