-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayyar Zamani

Kalaman Soyayyar Zamani

Kalaman Soyayyar Zamani

  1. Babu mamaki yanda idanuwanki ke satar zuciya haka murmushinki yake kara saurin bugawar zuciyata.kamar yanda kinka san cewa amo na sautinki yana tasiri ko a kunnuwan yan uwanki haka nake jin canzawar yanayina duk lokacinda nake jin muryarki.ki kara godiyar Allah akan tarin baiwa da ya baki.
  2. Farkon rayuwarda nayo a baya dariya nake ga wadanda suke soyayya har nake ganin cewa shirme sukayi saboda ban yarda da siddabarun da ke acikinta ba.amma yau na samu damar gaya miki cewa kin canza kowane motsi na rayuwata.har nake jin kamar zan iya daukar nauyin kowane mai yin soyayya ya samu cikar dukan muradin shi.yanzu na yarda indai har akwai soyayya aduniya to sanadinki ne
  3. Kece gaskiyar rayuwa,kece asalin burin da nake fata,kece gaskiyar mafarkinda nake kowane dare,kece farko da karshen kowane tunani da nakeyi idan nayi zaune shiru ni kadai. Idan kin yarda kece kinka bayyanarda asalin ni wanene awannan duniyar..kiyi yanda kike so kowa ya amince numfashi da nake domin ki ne.kece kadai mafarkinda ke yawan zama gaskiya arayuwata.
  4. Watakila bazan samu damar sanar dake a kullum ba amma ki sani kalmomin da ke a baki ba zasu iya gabatarda shaukin da nake ji ba duk lokacinda nake sauraren dariyarki.hakika dariyarki magani ne na kowace irin cuta dake addabar zuciya.
  5. Kowa ya kasa yarda dani cewa ban ta6a ganin halitta mai kyau da kwarjininki ba,idanuwanki bansan dame zan misalta haskensu ba,kyawo kike ko ba kwalliya,kowa cewa yake aljana nake gani nace kece mutune biyu kacal suke yarda da zance na.mama da baba nima kaina na fara amincewa ke aljanarda ke hana idanuwana runtsawace idan dare yayi.ki daina zuwa a mafarkina indai ke ba aljanar bace da gaske
  6. Me yasa nake girmama sunanki?  Me yasa zuciya da idanuwa suke yawan yaba kyawonki? Me yasa rai da jiki suke jin kamar babu wata aduniya da ta kaiki? Me yasa nake yawan tuna sunanki? Me yasa nake da tsananin buri da bege akan soyayyark? Wadannan sune tambayoyi da kullum suke dakatar dukan motsina.
  7. DAKE NAKE
  8. Dukkanin abinda zakiji daga gareni babu Karya ko niyyar yaudara a cikinsu yanxu ko kuma a chan gaba,Gundarin abinda maganata zuwa gareki zata kunsa KALMAR SO che,amma fa idan zaayi mata gunduwa gunduwa bani tsammanin zan iya warware maki zare da abawa,RANKI YA DADE kamar da wasa kyakykyawar tarbiyyarki ta saKa min SONKI a cikin zuciyata a cikin Kankanin lokachi,idan da zan samu yanda nake so DAKE NAKE fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar da kuma wanda ke a Kiyama,koda ban samu yanda nake so ba ina fata zaki rubuta sunana a madaukakiyar fadar zuciyarki a matsayin masoyi mai daraja koda bata farko Dukkanin abinda zakiji daga gareni babu Karya ko niyyar yaudara a yanxu ko kuma a chan gaba,Gundarin abinda magana zuwa gareki zata kunsa KALMAR SO che,amma fa idan zaayi mata gunduwa gunduwa bani tsammanin zan iya warware maki zare da abawa,RANKI YA DADE kamar da wasa kyakykyawar tarbiyyarki ta saKa min SONKI a cikin zuciyata a cikin Kankanin lokachi,idan da zan samu yanda nake so DAKE NAKE fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar da kuma wanda ke a Kiyama,koda ban samu yanda nake so ba ina fata zaki rubuta sunana a madaukakiyar fadar zuciyarki a matsayin masoyi mai daraja koda bata farko bace.
  9. Sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina. kada ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin SAMANIYA. KALAMAN SACE ZUCIYA sukuma wadannan wasu dadadan kalamaine da akefurta su ga abar qauna a mabanbanta lokaci ko yananyi. Dandanon su yafi zuma dadi balle sukari ,sukan sanyaya zuciya ,sukan raunana zuciya ,sukan qarfafa zuciya ,sukan sa a sallamar da zuciya duka ,saboda shauqin su da saka masoyiya cikin
  10. Inama ace za'a maimaita shekarun da suka wuce baya domin na samu damar bayyana kalmar soyayyarda nake miki domin kuwa karni yaya kadan na iya bayyana miki matsayinki arayuwata.
  11. slm allah ka karemin mijina ^ allah kataimaki mijina ^ allah yafewa mijina ^ allah kaga tausan mijina ^ allah kadaukaki mijina ^ allah kabarni nida mijina amin.
  12. Hubby nah inasonkah sosai allah dai yabarmin kai har abdah kaxama nawah nikadai my inah kaunarkah matukah karekeni amanah mijinah bye
  13. tattausan kalami zazzakar murya hadadden murmushi kayataccen kallo kyau natsuwa kunya hakuri kamala tausayi aminci allah yakara tabbata gareka malami kamili salihi hafizi haziki sarki sarkin kyawawa gami da yardah da aminci su kara kasancewa ga amintacciyar zuciya wadda so da kaunar tah suka mamaye rayuwatah hakika kai nawane domin kai kadai ne nake burin kasancewa tare dakai abin alfaharina I LOVE YOU with all my heart bye.
  14. slm mijinah barkah da safe rabin rainah allah y karah mah tsawon kwanah mijinah sobodah inkasance tare dakai cikin farinciki my inama tukar kaunar kah mijinah
  15. allah sarki mijina rabin rainah farincikinah hasken idanuwanah inasonka mijina banidah kamarka arainah ina matukar jidah kai xuciyah allah yamallakah mini kai nikadai badah kowa bah da nayi farinciki marar misaltuwa mijinah plx don allah karikemin amanah har abada karka barni my ina matukar kanarka sosai a cikin raina
  16. matata Kin wadata zuciyata da farin ciki kin haskaka rayuwata da haskenki kulawarki a gare ni ta musamman ce hakan ya sa nake jin kaina tamkar sarkin wata masarauta mafi girma da karfin iko. Ina Son Ki. nakira baki dauka ba hope dai lapia
  17. A hankali  a hankali ina ta ba ki filayen zuciyata ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba da sannu sannu dai ina ta mika rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kinzama abar kaunata wannan duk saboda karamcin kine a gare ni a yayin da nake kara kusantuwa dake duk tunane tunane na suka fara bayyana ya masoyiyata kin zama abar kaunata kamar giza-gizai haka kika zamo inuwa a gare ni kamar ruwan sama haka kika jike ni da farin ciki kamar iska haka kika tafi da tunani na kin sabunta kaddarata ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwata Dake kawai nake son kare rayuwata
  18. da akwai wasu lokuta da nake zubr da hawaye saboda ke na san za ki ce saboda me Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin dana ji muryarki ko na tina da ke Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki maryam don Allah kitaimaka ki sabamin da naji muryanki Kafin na kwanta👏
  19. Matata Ina sonki ina kaunarki ba zan daina sonki ba har sai lokacin dana rufe idona wanda ba zan kara bude su ba har abada ballantana nayi tozali da kyakkyawar surar jikinki da tattausan murmushinki wanda da mutum yana halitta da za’a iya cewa ke kika tsarawa kanki komai ba tare da tawaya ba. Hausawa sunce dan Adam tara yake bai cika goma ba, to ke a wurina kin kai 100% hakika yin maganarki da godiyarki a gareni yafi bani duk wani abu da yake cikin duniya. Nasan a cikin masu neman zuciyarki nine makaskanci a wurin rubutu sannan nakasasshe a wurin kalamai, hmm! Ina ma ana iya rubuto zuciya a turo da ita da ananne za ki iya tantance masoyi na gaskiya sauran duk gwadawa suke amma ni aikatawa nake
  20. Yayin da kika iso bakin kofar zuciyata na sadaukar da rayuwata ga sunanki na koyi yadda zan rayu masoyiyata ada ban taba koyon yaya zan rayu ba ban taba koyon yadda zan rayu ba tare dake ba masoyiyata wadannan yabo ne na gaskiya nake miki da zuciyata yayin da na same ki sai duniyata ta kawatu matuka duniyata ta cika burinta duk kanmu ba a ciki muke ba yanzu ne da muka hadu muka zama daya. wlh matata inason Fiye da so idan da yanda zanyi  da zandaukaka martabanki dasai nakira taron duniya nasanar da kowane namiji cewa nafi kowa dacen mata
  21. Shi so wani linzami ne da ke jefa kansa a cikin zuciyar da ya ga dama domin sarrafata, wanda muddin ya sarkafe zuciyarka to hakika baka da wani yunkuri da za ka iya yi domin kubutar da kanaka face nemo wanda ka ke so din Ki sani cewa tuntuni wannan linzamin so da kaunar naki ya sagale zuciyata ta yadda bani da wani sauki da ya wuce na ga na mallakeki
  22. Matata  so tamkar rayuwane ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki a zukatan mu Rukayya duk sanda nace kituromn abbu, Rukayya ita Soyayya wata abace dake shiga cikin zuciya batara da kasaniba kuma itace jigon rayuwa Na tarasune waje daya
  23. Na rasa me zance acikin wannan dare amma zan gaya miki abinda ya hana barci zuwa idanu na..ba komi bane illa tsananin kewanki.sai da safe
  24. SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA. Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki! HMM!! KI YARDA DA NI. A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
  25. Labarin farin cikina yana farawa ne daga jin muryarki,asalin ma'anar soyayyata sunanki ne,.asalin kasancewata awanan duniyar sanadin ki ne..inason ne na bayyana ki da kalmomi amma zaki ce nayi son kai.kece asalin samun nutsuwa da kwanciyar hankalina
  26. ZAN SO KI JI. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki! KE CE MURMUSHI NA. Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
  27. SLM yake tauraruwar mata kece dai kika ciritutar kyau abirni da kauye masoyiyata inhar nasa meki nayi babban rabo aduniya, Kaunarki tayi mini katutu tayadda bana numfashi har saida amincewar bugawar xunxurutun ruhin rayuwarki agareni
  28. Na maza KIN ZARCE SAURAN MATA Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki. SINADARIN RAYUWA TA. SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
  29. Kin zame min komi arayuwata.kece kaddarata kuma kece manufa ta..nagoda Allah kuma nagode fadi tashin da nayo baya har zuwa yau da na sameki.

0 Response to "Kalaman Soyayyar Zamani"

Post a Comment