Idan so hauka ne, kada Allah ya sa na taɓa samun lafiya: Ahmed Indimi ga Zahra
Idan so hauka ne, kada Allah ya sa na taɓa samun lafiya: Ahmed Indimi ga Zahra
Surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya nunawa mabiyansa a yanar gizo cewa shi gwanin iya soyayya ne
Dan hamshakin attajirin ya wallafa hotonsa tare da matarsa, Zahra Buhari, sannan ya bi shi da kalamai masu dadi wanda ya birge mabiyansa
Matashin ya kuma rubuta a cikin bayaninsa cewa idan so hauka ne, ba ya burin sake samun lafiya
Surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya birge mabiya a kafofin sada zumunta da irin rayuwar soyayyarsa bayan ya rubuta wa matarsa Zahra Buhari kalmomi masu dadi.
Da ya je shafinsa na Instagram, dan hamshakin dan kasuwa ya bayyana yadda yake haukan son matarsa.
Matashin ya wallafa hotonsa tare da Zahra inda ya raka shi da rubutu mai ratsa zuciya wanda ya kayatar da mabiya kafofin sada zumunta.
A cewar Ahmed, idan kasancewa cikin soyayya wani nau'in hauka ne, baya fatan ya sake samun hankali.
0 Response to "Idan so hauka ne, kada Allah ya sa na taɓa samun lafiya: Ahmed Indimi ga Zahra"
Post a Comment