Cristiano ya tuna da abokin kwallon sa wanda yataimaka masa lokacin dashi ba kowa bane
Cristiano ya tuna da abokin kwallon sa wanda yataimaka masa lokacin dashi ba kowa bane
Cristiano Cristiano Ronaldo: “Dole ne in godewa tsohon abokina Albert Fantrau saboda nasarar da na samu. Mun yi wasa tare a kungiya daya a gasar U-18. Lokacin da wani dillalin yan wasa ya zo ziyara, ya ce duk wanda ya fi zura kwallaye a raga zai dauke shi ya shiga karamar kungiya. haskenews.com.ng ta rahoto.
Mun ci wannan wasan 3-0. Na zura kwallon farko sannan Albert ya ci ta biyu da bugun kai. Amma kwallo ta uku ta burge mu duka. Albert ya kasance daga shi sai mai tsaron raga, ya yaudare shi kuma ina gudu a bayan sa. Abin da kawai zai yi shi ne ya zira ƙwallon, amma ya bada kwallo zuwa ga ni kuma na ci ƙwallo ta uku, don haka na sami gurbin zuwa karamar kungiya.
Bayan wasan na je na gan shi na tambaye shi dalilin bani kwallon naci? Albert ya ce ‘Saboda kai (Cristiano Ronaldo) ka fi ni’.
Don haka ‘yan jarida sun je gidan Albert kuma sun tambaya ko wannan labarin gaskiya ne. Yace eh. Ya kuma ce wasansa na kwallon kafa ya kare bayan wannan wasan.
kuma yanzu ba shi da aikin yi. ‘Amma tambayar da yan jaridu suke masa shin ta yaya bakada aiki a kwallon kafa, kuma kake da wannan katafaren gidan mai ban mamaki, kana da mota? Zamu iya cewa kai mai kudi ne. Hakanan kana iya kula da dangin ku. Daga ina wadannan kudade da kadarori suka fito? ‘
Albert cikin alfahari ya amsa yace : ‘Daga Cristiano Ronaldo’! “
0 Response to "Cristiano ya tuna da abokin kwallon sa wanda yataimaka masa lokacin dashi ba kowa bane"
Post a Comment