-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

ADALILIN GATA Hausa Novel

ADALILIN GATA Hausa Novel

*SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕



         *(1)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




*GODIYA*

Ina godiya ga Allah mai kowa da komai, mahaliccin sammai da k'assai, mai kashewa mai rayawa, mai badawa a duk lokacin da yaso, maji6incin bawan shi.


Godiya ta tabbata a gare shi daya bani ikon rubuta wannan littafin, kuskuren da ke ciki Allah ya yafemin.


*JIN JINA CE A GARE KU*

Anty Ybk

Benaxir Omar

Umma ta Lubiee Mai tafseer

Bebeelo

Hauwa Jabo

Ummu Abdul

Feenat Ja'afar

Mmn Shakur

Mum Faty

Zarah B~B

Mamu

Autar Haj.


*KUNA RAINA*

Anty Innah

Anty Fatima

Anty Rukayya 

Sis Atiks

Sis Maryam Mela.


*BAN MANTA KUBA*

Jegal families

3stars

Hindatu Jegal

Nafeesa Jegal

Aisha Jegal


5stars

Assy Jegal

Sumee Jegal

Balkisu Jegal

Hauwa Jega

Asmee Jegal


*K'ANNE NA NA KAINA*

Yaha Saddik

Bizzy

Yagani

Ummy

Salma

Yasmeeny

Salmatun Innah

Habiba Yayaji

Maryam Idris katsina

Zainab Abdullahi

Naanah

Umamat

Mmn Sajjad

Khairat

Ummeen Alamein.


*K'AWAYEN ARZIKI*

Hindatu shehu

Shema'u Bello Bari

Shafaatu zakariyya

Y'ar gidan Ango

Khadija Manga

Fati Salihu

Balkisu Bilyamin

Jidda A.K.A

Mum Zee

Mmn Jamila

Mmn Hanan

Princess Meenat

Hauwa'u Ag

Mmn Haneef

Mrs Jawaheer

Deeja Abdul

Mrs Zannah

Maryama

Namcy Sadururah

Stylish 

Fatima.

Ban manta da sauran ba ku saurare ni a last page.


*YARA MANYAN GOBE*

Halima

Maryam

Khadija

Abduljalal.

Allah yaraya min ku akan sunnah.

Sai yayyen ku

Lawiza & Zainab.




*GORO NE*

Ga dukkan masoya na way'anda na sani da way'anda bansani ba da sannu za ku shigo list d'ina luv y'all.


*SOYAYYAR KU TA DABAN CE*

Nagarta writers association luv y'all, Allah yakara had'a kawunan mu.


*GAISUWA*

Ga kowace Mumcy na.


*SADAUKARWAR TAKI CE*

Anty na, Mai bani shawara had'e da kulawa *Jidda Musa Mmn twin's*.


*TSAKANINA DAKE SAI ALLAH*

Sanah Isma'il Suleiman Matazu.


*LITTATAFAN MARUBUCIYAR*

*FATEEMA*

*BAHIJJA*

*SANADIN K'UNCI*

*ADALILIN GATA*



Cikin shirin shi na alfarma ya fito falon ya durk'usa har k'asa yana gaida mahaifiyar shi. Kafad'ar shi ta rik'o ta mik'ar dashi ya zauna gab da ita.


"Sai ina yanzu son?".


"Mum zanje company ne saboda muna da meeting da za muyi da wasu bak'i ne".


"Sai ka shiga ku gaisa da Dad d'in ka duk da ina tunanin kamar barci yake yi".


"In hakan ne bara kawai in wuce don nasan Dad sai mu wuce 15mnt muna gaisawa, ga shi sauri nake yi".


"Kenan kasan halin abinka nan 6angaren, amma d'ayan 6angaren duk yanda nake lurar da kai ba ka gane wa".


Da saurin shi ya mik'e cikin murmushi ya doshi hanyar fita "inna dawo ma yi maganar".


"Kullum hakan kake ce wa, fatana d'aya Allah yaganar daku baki d'aya".


Yana gab da fita ya ji muryar ta tana furta "Brother ni ma ba za'a tsaya mu gaisa ba kenan"?.


Cikin saurin ta ta k'araso gab dashi, hugging d'in shi ta yi "Mrng Brother".

"Mrng Little Sister, inna dawo za muyi magana".


Da sauri ya fice saboda agogon hannun shi daya duba ya ga saura minti biyar, a k'a idar shi bai son African time yayi ko ayi mai.


Sai da ya hau kan titin ya k'ara gudu sosai saboda saurin da yake yi.


K'eeeeeee kake ji sanadiyyar mugun birkin da yaja wanda saura k'iris ya kad'e mutumen.


Cikin isa da k'asaita da kuma 6acin rai kwance a saman fuskar shi ya fito daga motar.


Mari biyu k'warara ya yiwa dattijuwar fuskar mutumen wanda baki sake ya bishi da kallo.


Hannun shi na dama ya saka ya cire glass d'in shi no respect, yasa d'ayan hannun ya fitar da handkerchief a gaban rigar shi ya goge fuskar shi.


Cikin azama ya koma cikin motar ya tada ta, ganin ce wa zai iya bi saman kan shi yawuce yasa cikin sauri yaja jikin shi gefen titi da mamaki fal a ran shi.


"Ohhh! duniya ho yanzu wannan yaron zai fito ya faffallamin mari hankalin shi kwance kuma yana k'ok'arin takani ya wuce, duniya ce ta ishi kowa riga da wando".


****


Yau kam tana ganin sun makara ga yanda suke fitowa mazaunin su na masu bara gefen wata ma'aikata. 

   Bayan sun iso gurin ne ta gayar da wa'anda ta tarar sannan suka ne mi guri suka zauna.


"Har ga Allah ba na son wannan zaman barar da muke yi, kawai abin ne ya riga yafi k'arfi na, don in mun daina bansan miye mafita a garemu ba".


Matar kusa da ita ne ta ta6o ta sanadiyyar wani da ya zo yana raba masu d'ari-d'ari wanda har ya zo kanta bata sani ba nan ta kar6a ta yi godiya.


*12:00pm* suka fara watsewa da kad'an-kad'an inda ita ma Zajla ta rik'a sandar mahaifin ta suka doshi hanyar gida. Asaman hanyar ne suka had'u da yaran da ke tallar zogale da 6ula had'e da k'uli mai magi da yaji.


"Baba ko mu siyi zogale da 6ula?".


"Nawa ne muka sa mu yau hala?". Kud'in ta fitar ta irga taga 350 ne, nan take gaya mai ko nawa ne.


"Siya mana 6ula na 100, zogale da k'uli na 50".


Hakan ta tsayar da yaran ta siya suka wuce gida. Da shigar su gidan ne ta yi masu kwad'o suka ci.


Bayan sun gama ne ta ebi ruwa ta je ta yi wanka ta yi shirin islamiya.


Wasu kod'add'un uniform kalar blue ta saka sannan ta yiwa Baban ta jagora ta fito dashi k'ofar gida cikin inwar icen mangoro gurin su Malam Inuwa.


"Y'ar Baba za'a je makarantar kenan?".


Ta bashi amsa ta re da durk'usa wa ta gaida su. "Sai ki biya ki kira Salmat in ta shirya ku wuce".


Gidan Malam inuwa ta dosa a k'ofar gida suka ci karo da Salmat, hakan suka sa kai sai makarantar su.


® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:26 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                *(2)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Suna shiga islamiyar suka tarar da mutane na alwala sanadiyyar kiraye-kirayen sallar azahar da ake yi ko ina, nan su ma suka yo alwala suka bi jam'i akayi sallah.


Bayan sun k'are ne suka wuce ajin su na d'aukar hadda, hakan suka biya da d'ai d'aya inda Ustaz Lukman ke sauraren su had'e da gyara ga duk wanda ya yi kuskure.


Da hakan suka k'are har la'asar ta yi suka fito akayi sallah.

    A k'a idar makarantar duk ranar larba za'a za 6i d'alibai uku cikin Maza uku cikin Mata domin gabatarda abubuwan da ake koya masu a cikin class.


Hakan ta kasance yau ga d'aliban da aka za6a sun fito sun gabatar da abubuwan gwanin sha'awa ga ma su saurare.


K'arfe shida na yamma aka tashi kowa ya ka ma hanyar zuwa gida. Asaman hanyar ne Salmat da Zajla suke tattaunawa.


"Gaskiya Salmat yau sai gaba na ke fad'uwa na zata Ustaz Lukman zai sanya ni a cikin masu karatun satin nan".


"Tabbb! Ai kima shirya kinsan satin sama dole za ki shigo a cikin wa'anda za su yi".


"Ni fa abinda naso su bar mu muji da karatun haddar mu tunda lokacin musabak'a na k'aratowa".


"Lallai ma Zajla kin kai, kawai kije kiyi ta bitar haddar ki sannan ki zauna da shirin fitowa larbar sama karatu gaban ko wa".


"Muguwa kawai tunda kin ga kin yi yau hankalin ki ya kwanta ai zaki rik'a kayar min da gaba", tana maganar had'e da kai mata dundu a bayan ta.


"Gaskiya kar ki tayar da hankalin ki abin baida wata fargaba kawai dakin fito dakewa za kiyi, kuma kar ki rik'a kallon mutane ki nok'e kan ki kawai".


"Shikenan Allah yakai muna rai yasa fargaba ta fice min kamin ranar".


"Ameen", ta amsa a gajarce.


Da hakan har suka k'araso gida, a tare suka shige gidan su Salmat d'in saboda wannan k'a idar ta ce in sun da wo daga islamiya gidan su Salmat take zama har sai Baban ta sun k'are hira sannan ta fito su shiga gida.


****


Cikin 6acin rai ya shiga d'akin meeting d'in wanda sanadiyyar hakan kowa ya sha jinin jikin sa.


Hakan akayi meeting d'in rayuwar sa 6ace wanda mataimakin shi ne Imran ya jagoranci komai har aka k'are.


Bayan bak'in sun wuce ne wani cikin ma'aikatan ke ba da shawara kan ce wa me zai hana ayi musaya da wa'ancan bak'in a basu fata suko su bada ire-iren takalma, jakunkuna da sauran dangin kayan da ake sarrafawa da fata d'in?.


Ya cigaba da ce wa "a tunani na hakan zai fi akan abada fatar su bada kud'i ko ya kuke gani?".

   Ya k'arashe maganar had'e da kallon mutane cikin nu na bajin ta kan shawarar da ya bayar.


Kallon da mutane suka bishi da shi ne na alamar ba kada hankali, wasu kuma na tausayawa gare shi ya sa ya sha jinin jikin shi ya yi tsit.


Ko wa ya yi zugum domin jiran me zai biyo bayan maganar da ya furta, saboda duk yanda aka zauna meeting ba bu mahaluk'in da ya isa yace tak ba tare da ya bashi dama ba, barrantana yau da ya shigo rai 6ace wanda ya hana yayi magana har akayi meeting d'in aka k'are.


"Duk da ce wa kai bak'o ne a wannan ma'aikatar bazai hana hukunci na yahau kanka ba".


Cikin damuwa Imran ya tari numfashin shi had'e da bashi hak'uri amma ina ya gama furta "na sallame ka daga yau".


Hakan ya ta shi tamkar guguwa yabar gurin cikin mintunan da basu wuce uku ba.


Durk'ushe ya yi gaban mataimakin A.K.A kuma babban aminin shi yana mai bada hak'uri had'e da furta


"In har kuka sallame ni bansan ina zan dosa ba, da wannan aikin nake kula da mahaifiya ta da sauran k'anne na marayu".


"Sai dai kayi hak'uri aikin gama ya gama duk nan ba wanda ya isa ya janye wannan hukuncin".


"An samu matsala ne tun farko ba'a gaya ma tsarin shi ba shiyasa, ko ni nan da nake mataimakin shi kuma babban aminin shi indai a office ne ban isa yayi magana inyi ba har sai ya bani dama".


Hakan sauran ma'aikatan suka rik'a bashi hak'uri had'e da fatan alkhairi saboda bakin alk'alami ya bushe, don shine mutum na bakwai da hakan ta kasance dashi tun lokacin da mahaifin shi ya yi ritaya ya bashi kula da company d'in, da hakan kowa ya Kama gaban shi.


Mutum biyu ne suke tattaunawa akan matsalolin da ke faruwa a ma'aikatar.


"Gaskiya wannan ma'aikatar ba ta nesa da rushewa, kaduba kaga yanda yaron nan ke shuka rashin mutunci son ranshi", cewar tsamurarren.


"Tabb to ai abin gado ne haka mahaifinshi yake tsula tsiya lokacin da yana manager, don ni na rasa gane tsakanin d'an da uban wa yafi rashin mutunci", a cewar bak'in mutumen kakkaura.


"To Allah yayi masu magani, kuma yaganar dasu".


"Ameen".



® *SDY JEGAL*


Www.sadijegal.blogspot.com



Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕










                  *(3)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


www.sadijegal.blogspot.com


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Hakan ya fad'o gidan ko sallama babu sanadiyyar wani huci da yake yi shi ala dole an 6ata mai rai fuska tur6une tamkar namijin zaki.


Da saurin shi ya ta shi ya taryo shi yana bubbuga bayan shi, sanadiyyar ya k'i jinin jure damuwar d'an shi komi k'ank'antar ta.


"Wa ya ta6a uba ga Dad kuma d'a ga Dad?, bazan juri ganin ka cikin 6acin rai ba komai k'ank'antar shi".


Ruwa ya tsiyaya a cup ya d'ora mashi a baki ya kauda kai yana huci, d'ayan gefen ya mayar da cup d'in sannan ya sha kad'an ya kauda kai tamkar wani jinjiri.


"Gayamin Babana meke faruwa, kuma wa ya 6ata ma rai?".

    Mum baki ta sake tana kallon sarautar ubangiji, abu gwanin haushi.


Cikin yanga tamkar wata mace ya kora mai abinda ke faruwa.


"Yo banda abinka Son miye laifin wanda ya baka shawara akan cigaban ka?, kuma wai har za ka iya ta da hannu ka fallawa dattijon mutane mari", Mum ce ke wannan maganar cikin 6acin rai da fad'a-fad'a.


"To shi dattijon titin uban sa ne da zai zo yana tafiyar yanga akai?", cewar Dad.


"Wallahi dai ku bi duniya a sannu daga kai har yaron ka, shin kud'i hauka ne? Su talakawan su sukaso ganin Kansu a hakan? Ku da kuke hakan siya kukayi aka baku gyara?, bai dace ka rik'a nunawa yaran nan gatan da yazarce misali ba".


"Mu shiga daga ciki Son, saboda ta fara wa'azin nan na ta da take zama alarammar kan ta taja kuma ta fassara", hannun shi ya rik'a suka haura sama sai bedroom d'in shi.


"Mum wannan abin fa ya kusa yawa, miye laifin wanda zai kawo cigaba akan lamurran ka da Brother zai yanke wannan d'anyen hukuncin".


"Rufamin baki ai duk halayyar ku iri d'aya ce ku ne masu uba mai kud'i to wallahi ina guje maku ranar nadama saboda wannan abin ba gata ne uban ku ke nuna maku ba", cikin fad'a sosai ta k'arashe maganar.


"Kin san dai Mum na d'ara Brother don bazan yi abinda ya aikata yau ba".


"Ku dai kuka sani, Allah ya ganarda ku daga ku har uban na ku don wallahi rayuwar ku kanta abar tausayi ce, don mutumen da baisan darajar d'an Adam ba yana cikin matsalar rayuwa, komai za kuyi ya kamata ku rik'a duba cancantar abin".


"Kullum game da tarbiyar ku tufka nake yi mahaifin ku na yiman warwara, a tunanin shi wannan gata ne".


"Mum tunda munsan girma da darajar ku ai ba muda laifi, dama ca akayi mu girmama iyayen mu".


"Sai akace ku taka duk wanda kuke so wannan shine dai-dai a cikin aya da hadisin Dad d'in ku?, wato mu ne mutane saura dabbobi ne a gurin ku".



"Mum ba kya ga newa ne, shi fa Dad raini da wulak'anci ne bai d'aukar mana ba shiyasa kike ganin tamkar wulak'anta mutane muke yi, amma ba hakan bane".

  "Mum fa su mutane ba ka iya masu idan kayi sake sai su ta ka ka son ransu".


Mugun kallon da ta bi ta dashi ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru.

D'aki Mum ta wuce tabar Saudat zaune a falon, ganin hakan ya sa ta bi sawun su Dad.


****


Sanadiyyar yau ta kama alhamis ba islamiya ya sa tun safe tana siyo masu koko suka sha ta hau wankin su ita da Baban ta.

   Bayan ta gama ne tayi shara ta tsaftace gidan, yau girki ta d'ora masu sanadiyyar tsakin masarar da Mama Inno ta ba su jiya wanda zai kai kwano uku.


Waje ta fita ta yi sa'a da yaran da ke tallan zogale dafaffe nan ta siyo ta had'o da d'an magi ta koma gidan.

     Faten tsakin masara ta yi wanda yaji zogale.


Sai da ta samu guri ta saka ma su Mama Inno faten ta kai masu sannan ta dawo gidan.


Ruwa ta ebo ta kaiwa Baban ta ya wanke hannun shi ita ma ta wanke sannan suka yi Bismillah suka fara ci.


Suna gama wa ruwa ta fara kai mai ya yi wanka sai da ya fito ta taimaka mai ya shirya yana ta sanya mata albarka sannan ta shiga wankan ta fito.


Sai bayan la'asar yau suka fita yawon su na bara, daka gansu tsaf dasu sai dai talauci dake barazana dasu.


Hakan ta gayar da mutanen gurin sannan suka nemi guri suka zauna, sai gab da magrib suka wuce gida inda ya tsaya gurin su Mal Inuwa itako ta shiga gidan su Salmat.


Sallah suka fara gabatarwa bayan sun k'are ne suka rik'awa juna bitar haddar su domin su k'ara daddak'awa.


"Salma zo ki lek'a daga waje ki kira Sagiru yakaiwa su Baban ku abincin su".


K'ur'anin ta ajiye ta fice bayan ta kira shi ne sannan ta dawo masu da nasu abinci d'akin, nan suka ci suka gama sannan suka gabatar da isha sai k'arfe tara sannan Zajla ta fita ta ja Baban ta suka wuce gida.






























® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕



                  *(4)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Zaune suke saman dinning table suna breakfast sai tattaunawa suke yi akan lamarin company.


Sai da aka yiwa wayar shi Kira biyu ana ukun sannan ya d'aga wayar ya nufi hanyar d'akin shi, gaisawa suka fara yi sannan ya fara magana fad'a-fad'a had'e da ya mutse fuska.


"Kana sane da ce wa duk inda ake taro in har akwai Mata ba na nufar gurin, saboda haka kuci gaba kawai idan kun gama ma had'u, ka isar da sak'on taya murna ta zuwa ga Salis, in ya natsu zan kira shi".


Yana kai k'arshen maganar ya dak'ile wayar shi ya bita da wani kallo tamkar ta yimai wani laifi, gado ya fad'a domin ya d'an huta saboda ba mutum ne maison fita ba.



****


Kwanci ta shi asarar mai rai, yau ta ka ma Larba wanda Zajla sai gaban ta ke fad'uwa sanadiyyar tunanin da wuya Ustaz Lukman bai fitar da ita cikin masu karatun k'arshen sati ba.


Kamar kullum yau ma hakan ce ta kasance, bayan gabatar da sallahr azahar suka shiga class domin bitar haddar su saboda k'aratowar lokacin musabak'ar su.


Bayan an gama sallar la'asar ne aka fitar da mimbari da kujeru domin zama tsakiyar makarantar a gabatar da ire-iren abubuwan da ake koya masu.


Mutum uku cikin maza suka gabatar da yadda ake taimama da kuma sallar gawa, sai matan biyu da suka gabatar da koyar da alwala a aikace.


Zajla ce za ta gabatar da bayanin wankan tsalki da kuma addu'o'i.


Bayan ta yi basmala ta gabatar da sunan ta da Zajla Abubakar Zubair sannan ta fara da ce wa'.


"Shi dai wankan tsalki ya kasu zuwa kashi-kashi, akwai wankan janaba, akwai wankan haila, akwai wankan d'aukewar jinin bik'i (jego) da sauran su.


"Kamar yanda kuka sani su dai wad'annan abubuwan wanka iri d'aya ake yi masu sai dai niyyar su ce data ban-ban ta".


"Da farko za'a so mutum ya sa mu ruwan shi tsaftatacce, wa'anda kalar su bata canja ba, d'an-d'anon su bai canja". 

  "Anan abinda ake nufi da kala ko d'an-d'ano shine kar mutum ya d'ebi ruwan Lipton ko ruwan wankin shinkafa ko ruwan da ke da gishiri yace wankan tsalki zai yi dasu".


"Da farko mutum zai fara wanke gaban shi, bayan ya wanke zai wanke hannun shi saboda najasar da ya ta6a, zai d'ebo ruwa har sau uku yazuba ma kansa, ya murza kansa har ruwan sukai k'asan kansa, daga nan zai yi alwala shud'i guda-guda sannan ya wanke 6angaren jikin shi na dama daga sama har zuwa k'asa, 6angaren hagu ma haka sannan ya game jikin sa da ruwa ya murza ko ina".


"An samu sa6anin wasu maluma da suka ce idan mutum ya wanke gaban shi zai fara gabatar da alwala, wasu kuma sukace sai bayan ya k'are wankan gaba d'aya sannan yayi alwalar. Allah masani".


"Addu'ar shiga kewaye

*(( Allahumma inni A'uzu bika minah khubithi wal khaba'ithi))*


"Addu'ar fitowa daga kewaye".

*((Gufranak))*


"Addu'ar mugun mafalki".

*((Allahumma inni A'udhu bika min sharri ma ra'aytu fii manaamee an yadurranee fii deeni wa dunyaay))*


"Addu'ar kariya daga azabar k'abari".

*((Allahumma innee As'alukar Jannah, wamaa k'arraba ilaiha min k'aulin wa amal, wa A'udhu bika minan naar wama k'arraba ilaiha min K'aulin wa amal, wa A'udhu bika min fitnatil mahya wal mamat wa min fitnatil k'abr wamin fitnatil masihid dajjal wamin Adhabin naari wasu'il maseer))*


"Addu'ar  neman ya fiyar sa6o.

*((Allahumma inni a'uzu bika an ushrika bika wa ana a'alam wa astagfiruka li maala a'alam))*


Gyaran muryar da akayi da speaker shi ya nu na mata alamar lokacin ta ya yi, speaker ta ajiye ta koma mazaunin ta. 

     Kabbara ce ta biyo baya had'e da jin-jina mata akan abubuwan da ta gabatar.


Nan akayi salati ko wa ya ka ma gaban shi sanadiyyar gabatowar magriba, kowa da maganar (ZAZ) ya fita a bakin shi sanadiyyar add'o'in da ta yi tamkar itama Malama ce ba d'aliba ba.




































® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                *(5)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


"Gaskiya (ZAZ) kin kawo wuta sosai yau, kinji yanda kike rero addu'o'i tamkar Ustaz Yusuf?".


"Banson sharri wallahi, kina ji yanda murya ta ke wani rawa-rawa alamar tsorace nake. Ni fa shiyasa kika ga ko wannan musabak'ar da za muyi gabana ke ta fad'uwa saboda na k'i jinin karatu a cikin bainar jama'a".


"Tabbb ai wannan shafin mai ne wallahi, kina ganin yanda ake taro sosai idan lokacin musabak'a yayi. Kuma hakan da ake yi duk Larba anaso abin yabi jikin mune har mu saba mu daina jin tsoro", cewar Salmat.


"Ranar da duk Ustaz Lukman ya ji kina furta wannan (ZAZ) d'in a bakin ki kya yi bayani, saboda kinsan ya ce adaina kira na da hakan".


"Yo ai ba sai kin gaya min kina da mai tare maki ba, duk kauce-kaucen ku za ku fito kuyi bayani ne".


"Shin tsaya me kike nufi ne, ban fahimce kiba?".


"Kinsan dai ko kin 6oyewa ko wa soyayyar ku da Ustaz Lukman bai dace ni ki 6oyemin ba".


Cikin gwalo ido da wani cin birki tamkar mai tuk'in mota ta ja ta tsaya, mamaki kwance fal a fuskar ta.


"In har kin yarda kalmar "So" bata ta6a ratsawa tsakanina dashi ba, sai dai mutunci".


"Ke ce baki fahimci hakan ba, amma duk wanda ya yi mai duba na natsuwa idan kina gaban shi to zai hango son ki kwance a k'wayar idon shi".


"Allah yashirye ki, ke kika san wani abu "So" ni kam da saura na".

   "Ke ma za ki sani idan lokacin kisani yazo, wa yaga ana soyewa tsakanin Malami da D'alibar shi".


"Allah ni ko guntun namiji bai cikin tsari na ko Aure zan yi, na fison dogon namiji wanda zai yi guda da rabi d'ina".


Dundu Salmat ta kai mata had'e da furta, "makira kika ce baki san So ba kuma amma ga shi kina wassafa mijin da kike son Aure".

    "Shi ne sai aka ce maki wassafa ra'ayin ka shi ne So d'in?".. Yanzu bara in tambaye ki akawo maki gabjejen namiji wanda yayi hud'u d'in ki ya kika ga abin?", tana maganar ne had'e da dariyar k'eta.


"Bakin ki yasari d'anyen kashi muguwa kawai, Allah ya kiyaye ni".

   Dariya Zajlah tayi sosai akan yanda Salmat ke maganar had'e da ya mutse fuska tamkar ga mijin nan gaban ta.


Da hakan suka k'araso gida sannan suka gabatar da duk wani abu daya dace kafin Zajla taja sandar Baban ta su wuce gida.



****


Har gida yau suka kawo mai ziyara shi da Salis, bayan sun gayar da Mum suka fita gardener, saboda a al'adar shi in har yana gida indai ba bacci yake yi ba to nan ne gurin hutawar shi.


"Gaskiya (A.K.A) baka kyauta min ba, yanzu ace ayi birthday d'ina ko wa ya hallara kai baka je ba, kuma kana sane da ce wa duk duniya banda friends d'in da suka wuce ku kai da Imran".


"To ku ne da jaye-jaye kuce duk abinda za kuyi sai kun saka Mata a ciki shi ne birgewa a gare ku, ni ko in har hakan za ta cigaba da kasancewa to ina mai tabbatar maku za kuyi lamurran ku ba dani ba".


"Ni wannan abin na ka na d'aure min kai, zanga ranar auren ka da kuma matar da za ka aura, saboda wannan abin na ka ya yi yawa", ce war Imran.


Murmushi ya rik'a yi sama-sama wanda har fararen hak'oran shi na bayyana had'e da dimple d'in shi.


"indai ku kuka ta shi auren Allah sanya alkhairi don kunsan ba dani ba a y'an dinner da sauran su, zan dai je d'aurin aure shi ne na mu".


Kallon da suka bi shi dashi ne ya sa ya yi saurin kauda kan shi yana dariya k'asa-k'asa.


"Ka ma mayar damu wasu sha ka wuce za ka gani ne. Na ma manta in gaya ma Lubnah ta ce in ba ta number d'in ka".


Mugun kallon da ya yimai ne ya sa ya fahimci amsar da yake nufi zuwa gare shi.


"Baiwa wata Mace number ta na nufin rabuwar mu ta har abada dakai, ka sanni kasan waye ni. Duk cikin contacts d'ina number Mace biyu nake da, Mum da Lil Sis".


Cikin 6acin rai ya mik'e ya tattara wayoyin shi ya nufi hanyar shiga gida, duk yanda ya so tsayar dashi don ya nuna mai wasa yake yi abin yaci tura.

   Bayan ya shige ne gidan Imran ya kai duban shi ga Salis had'e da hararar shi sannan ya furta.


"Sai ka ta shi mu fice tunda ka takaro zuciyar manya". Dariya sosai Salis ya yi had'e da furta.


"Ni fa suk'uwar shi dariya take ba ni, da abin 6acin rai da wanda bana 6acin rai ba za kaga ya had'e fuska ala dole shi fushi yake yi".


"Allah wataran da gayya nake tsokanar sa saboda inyi dariya".


"Don kasan duk rintsi yana tare damu ne, ko ya yi fushi dole yasauko shiyasa kake mai hakan", ce war Imran.


Hakan suka had'a nasu da nasu suka fice saboda sanin in kwana za suyi gurin bazai kuma kula su ba sai ranar da ya sauko daga zuciyar.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                 *(6)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Kamar kullum yau ma ta gama kimtsa komai na kula da gidan suka shirya suka fito sai mazaunin su na bara, wanda kullum suka fito wani irin mugun nauyi take ji a ranta.


Saboda a tunanin ta kamar ta ya ci ace ta wuce zama y'ar jagora, sai dai ba yanda za tayi sanadiyyar in har bata kula da mahaifinta ba wa ye ta ajiye da zai kula dashi yanda yadace.


Ga shi dai in har ta ce baza su fito yawon bara ba to batasan wa zai ciyar dasu da sauran lalurorin su ba, tunda mahaifinta ba yada idon da zai fita yane mo musu abinda za suyi lalura.


Don ma Malam Inuwa na k'ok'arin basu abincin dare, duk da shi kan shi ba wata wadata ce dashi ba saboda ba kullum za'a ci abinci sau uku a rana gidan shi ba.


Duk ita kad'ai ke wannan tunanin a ranta, wanda har kullum take tunanin ina za ta ne mo masu mafita akan wad'annan matsalolin.


Sanadiyyar bugawar da motocin biyu suka yi ya janyo hankalin tsirarrun mutanen da ke zaune gefen hanya.


Dattijuwar na fitowa daga motor ta ya tayarda hannu zai sharara mata mari.


Hannun da ya ji ya rik'e na shi hannu ne ya bi da kallo.


"Ka daraja mutum ko da baka san shi ba, wanda ya girme ka haka yake tamkar yaya a gurin ka, haka zalika wanda ya yi sa'ar mahaifin ka tamkar mahaifin kane".


"Bai kama ce kaba kuma hakan bai dace dakai ba, yanda ka daraja manyan ka haka Allah zai sa a daraja na ka iyayen ko bayan idon ka".


Cikin sanyin jiki ya bi dattijuwar matar da kallo, sai wata irin kunya ce ke ratsa ga66an jikin shi, hak'uri yafara bawa matar had'e da neman yafiyar abinda ya tashi aikatawa.


Su duka biyun suka bi gurin da kallo domin ganin ta ina za su ga yarinyar amma ina ta 6acewa ganin su.


*********


Sandar mahaifinta ta rika suka doshi hanyar gida. "Zajla ki daina saka kan ki a cikin rayuwar wa'annan mutanen, ba mutunci ne dasu ba".


"Baba ai Ba  komai na yi ba nasiha ce kawai na yimai saboda abinda naga ya kusa aikatawa bai dace ba".


"To Allah yamaki albarka yaba ki miji nagari inga auren ki da jikoki na".


"Baba ni fa na gaya ma bazan yi aure ba, saboda bansan wa zai kula dakai ba", tana maganar ne had'e da zum6uro baki tamkar yana ganin ta.


"Haba Zajla kidaina fad'ar hakan, Allah zai kula dani saboda shi ya so gani na hakan kuma zai ya yemin lokacin da ya so. Tunda abin ciwo ne bana halitta ba kuma daga baya ya same ni".


"Baba kayi ta addu'a Allah yaba ni hanyar samun kud'i insa a gyara ma idon ka".


****


Fitowa tayi da sunan kai ziyara company maigidan ta, amma sanadiyyar abinda yafaru ne ya sa duk ta ji ba za ta iya k'arasawa ba akalar motar ta taja takoma gida.


Da shigar ta falon Saudat tagani zaune tana waya, ganin shigowar Mum ne ya sa ta yi saurin tsinke wayar had'e da mik'ewa tsaye.


"Mum ba dai har kinje company kin dawo ba?".


"Ban k'arasa ba na dawo". Ta ba ta amsa a tak'aice, ganin 6acin rai kwance saman fuskar Mum ya sa bata k'ara magana ba.


"Me ya hana ki zuwa skul yau?".


"Mum fa har na shirya Hafsat takira ni ce wa lecturer d'in bai zo ba shiyasa nayi zama na saboda dama yau shi kad'ai muke da".


Bayan ta bawa y'an aiki umurnin abinda za'a dafa abincin rana, bedroom d'in ta ta wuce duk ranta jagule.


*02:30*

Talatu mai aiki ce ta gayawa Saudat ta fad'awa Mum an kammala komai.


Bedroom d'in ta wuce ta gaya mata sak'on k'are girkin, nan Mum ta bata umurnin kiran Brother su had'u falon Baban su.


Bayan sun kammalu anyi lunch an k'are ne ta kai duban ta ga Al'amein.


"Za ka iya tuna ranar da kashigowa Dad d'inku cikin 6acin rai har kana gaya mai ka mari wani dattijo?".


"Mum me ya kawo wannan maganar?, ai ina ga ta wuce, ko kuma wani fad'an za'a maimaita min?". Yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi.


"Kaba ni amsa kawai". Ta furta a tak'aice.


"ina ga za'a yi sati biyu ko kwana goma".


"Wannan dai-dai yake da maimaita abinda ka aikata akan fuskar mahaifiyar ka", tana kaiwa k'arshe ta fad'a bedroom d'in Dad.


Cikin razana su duka uku suke kallon junan su kowanne 6acin rai kwance a fuskar shi musamman Al'amein da har jiyojin kanshi sun fara bayyana.


(4 breakfast, luv y'all My fan's)



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                   *(7)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



"To wai Dad wa ye ya isa har ya d'aga hannu ya kai wa Mum mari kuma ya zauna lafiya a garin nan?".


"Son ni ma wannan shi ne abinda nake tambaya, amma nasan ba wanda zai bamu wannan amsar sai ita kanta, kuma nasan mu shekara muna tambaya ba za ta gaya mana ba".


"Dad mushiga daga ciki muji ko za ta gaya mana d'an gidan uban waye shi". Ce war Saudat.


Hakan suka d'unguma sai bedroom d'in Dad domin sa mun amsar  tambayoyin su.


"Mum Alamein ta shi kigaya min wane isasshe ne zai d'aga hannu duk garin nan yadakar min Mata?".


Wani guntun murmushi ne ta saki a fuskar ta had'e da girgiza kai alamar ina tausayin tsarin ku.


"Wannan shi zai tabbatar muku ce wa duk abinda kayi na alkhairi ko na sharri za ka had'u da makaman cin shi ko mai dad'ewa".


"Kuma kai da kake ta da jiyojin wuya me za kayi akai ko da na gayama wa ya mare ni? Ko ka manta shi wanda ka mara yana da y'ay'a kuma sun san darajar shi".


"Me kake tunani a wancan lokacin in har ace ko da ka mare shi wani d'an shi na gurin? Ko kana tunanin dukiyar ka za tasa in har suna gurin su k'yale ka?".


"Mum ni fa mutumen laifi ya yimin, har ta ya ya zai zo yana tafiyar ganin dama a saman titi".


"Haka zalika nima laifi nayi yaron ya mare ni".


Cikin damuwa Dad ya bi ta da kallon mamaki, ya rasa ga ne ita wace irin Mace ce da batasan y'ancin kanta ba.

  

Durk'usawa ya yi gabanta ya d'ora hannuwan shi saman k'afafun ta tamkar yayi kuka yake ji ya furta.


"Don Allah Mum ki gayamin ya akayi hakan ta faru? Kuma in kin san waye ki gayamin shi please and please Mum?".


Murmushi ta yi sosai har hak'oran ta suka bayyana, sannan ta kwashe ko mai ta gaya masu had'e da yaba halayyar yarinyar.


Sai lokacin suka saki fuskokin su har Al'amein na furta "wallahi ya kuru da ya aikata wannan d'anyen aikin da ya had'u dani".


"Inna san waye shi ko in ban sani ba? Ko kuma inna gaya maku waye shi za ku d'auki mataki?".


Da hakan dai ta k'ara janyo hankalin su had'e da k'ara lurar dasu kan muhimmancin girmama na gaba dasu, wanda Dad ke zaune yana sauraren su.



******


Duk abinda aka saka ma rana zai zo indai da rai da lafiya. Yau ne ake shirin gabatar da musabak'a ta gari wadda za'a gabatar a makarantar su Zajlah saboda kasancewar makarantar ta su ce babba kuma itace kan gaba a duk sauran makarantin nen garin su.


Daga kan y'an izifi biyu aka fara har zuwa kan izifi sittin wanda aka share sati d'aya ana gudanarwa tsakanin makarantu biyar dake garin.


Inda aka k'are kuma makarantar su Zajlah ta zamo gwarzuwa a musabak'ar wanda har da Zajlah da Salmat acikin gwarzayen, saboda Zajlah ta yi haddar izifi talatin inda Salmat ta yi izifi ashirin.


Bayan kwana ki bakwai ne aka gabatar da ta Jaha a garin Birnin kebbi, daga nan akayi ta k'asa gaba d'aya inda Zajlah ta zo ta d'aya a cikin y'an izifi talatin Salmat kuma ta biyu a cikin y'an izifi ashirin.


Sun sa mu kyaututtuka da dama wanda ya had'a da kud'i da keken d'unki Zajlah harda kujerar Makkah wanda sanadiyyar hakan har da guntun hawayen ta na farin ciki.


Ko Malaman su kaduba lokacin za kaga farin ciki kwance fal a fuskokin su musamman Ustaz Lukman dake kula da 6angaren masu haddar da kuma wani abu da yake ji kwance k'asan zuciyar shi akan Zajlah.


Mahaifin ta farin ciki fal a ran shi harda hawayen shi, ji yake yi ina ma ace yana gani da idon shi yaga wannan rana ta farin ciki da y'ar shi ta zamo gwarzuwar shekara.


Hakan suka tarkata suka dawo gida farin ciki fal ransu, sai mak'ota ke ta shigo masu murna da Allah sanya alkhairi.


Sun samu kud'i sosai musamman Zajlah da tazo ta d'aya, har gida Ustaz Lukman ya biyo su had'e da kyaututtukan da suka sa mu mota ta kawo masu har k'ofar gida.


"Za ku sa mu shigowa makaranta ranar assabar?", ce war Ustaz Lukman.


"Ustaz a bamu sati d'aya mana mud'an huta sannan mu shigo".


"Sati d'aya ya yi yawa gaskiya saboda bazan jure...... Sai kuma ya canja akalar maganar.


"Shikenan Zajlah ku shigo zuwa ranar Larba, tunda kunga yau ta kama Assabar".


"To Ustaz mun gode sosai". Da hakan suka shige gidan su Salmat d'in.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(8)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Kamin su shiga gidan ne Salmat ta kai duban ta zuwa ga Zajlah had'e da furta.


"Yau kin yarda da abinda nake cewa Ustaz Lukman son ki yake yi?".


"Ke dai ina ga aure kike so shiyasa kullum maganar ki ba ta wuce ta So ba".


"Kina ji fa yau har da furta cewa bazai juri rashin ganin ki ba, sai ya juya maganar saboda kar mu gane inda ya dosa".


Dundu ta sakar mata had'e da janyo gashin kanta sai da ta yi k'ara, da hakan suka shiga gidan.


Mama Inno ce ta tarye su dukan su ta rungume sai albarka take saka masu har da guntun hawayen ta.


"Zajlah yau burin ki zai cika da yardar ubangiji saboda ya yi maki hanyar samun kud'in da za ki kula da matsalar idon mahaifin ki".


"Wallahi Mama ina jin tsabar kud'in da nasamu tun a can matsalar Baba ce nafara kawo wa, sai kuma samun abin Sana'a da zai raba mu da yawon bara".


"Don ko babu kud'in zan soke matsalar bara tunda na samu keken d'unki zan tashi da koyo har in iya".


"Gaskiya kam kinyi tunani mai zurfi, yanzu sai abubuwa sunyi sauk'i ku had'u ke da Salmat kuje koyon d'inki".


Da hakan aka shigo da kayan da suka samu gidan su Salmat, inda kowannen su ke da keken d'inkin sai Salmat dake da kud'i dubu d'ari biyu Zajlah ko na da dubu d'ari biyar da kujerar Makkah da shugaban k'asa ya baiwa duk wanda ya yi na d'aya a matakin haddar su tun daga izifi biyu har zuwa izifi sittin.



****


Tun lokacin da yarinyar ta hana ma saurayin marin ta take kwana kuma ta tashi da ita aranta, saboda yarinyar ta burge ta sosai, sai tunani take yi ina ma ace y'ar tace ke da halayyar wannan yarinyar.


Hakan take gurin Fadeel wanda duk yanda ya so yafige yarinyar a cikin zuciyar shi abin ya faskara.


Duk inda zuciyoyin mutum biyu suke da tunanin ta suke kwana kuma suke tashi, duk inda suke farautar ta domin su ganta abu ya faskara.


*******


Falon ta shigo ta d'auki remote domin canja tashar, abinda ta ga an nuno ya hana mata canjawa sai gata zaune jagwaf saman kujera.


"Saudat! Saudat!! Saudat!!!".


Gigice ta fito daga d'akin ta ta fad'o falon saboda kiran da Mum ke ta k'wala mata. 


Plasma d'in ta bi da kallo saboda itace Mum ke nunawa da yatsan ta, ita dai bata ga komai ba bayan yarinya tana rero karatun Qur'an cikin baiwa kowane harafi hakk'in sa had'e da tajweed.


"Mum me ke faruwa halan? Ban fahimci me kike nuna min ba fa".


Nan Mum ta yi mata bayanin yarinyar. Hakan itama Saudat ta ji yarinyar ta burge ta sosai.


"Ina so kishirya zuwa anjima ki rakani makarantar su yarinyar nan, dama na yita neman ta duk inda nake sa ran ganin ta bangan taba".


"Yanzu Mum me za kije kiyi mata? Sai kita neman yarinya tamkar wacce ta k'ulla maki wani abin arzik'i".


Mugun kallon da Mum ta bita dashi ne ya sa taja bakinta ta tsuke.



*05:00pm*

Dai-dai wannan lokacin Mum ta faka motar ta k'ofar makarantar, da Ustaz Yusuf ta fara cin karo k'ofar makarantar.


Nan ta yimai bayanin abinda ke tafe da ita, mashin d'inshi yahau yayi mata jagora har k'ofar gidan su Salmat, godiya ta yita yimai har da fitarda kud'i taba shi saidai bai kar6a ba yajuya yakoma.


Mota ta hakimce tana wani yatsinar fuska saboda k'ofar gidan da taga sun tsaya wai nan Mum tazo kuma gurin k'aramar yarinya.


"Fito mushiga ciki mana".


"Shiga ki fito Mum zan jira ki a mota".


Fad'a ta dinga yi mata sannan ta fito har da wani handkerchief tana toshe hanci. Gidan suka shiga inda Mama Inno ta yi masu tarbar da ta dace duk da batasan su waye ba.


Bayan sun gaisa Mum ke yi mata bayanin gurin Zajlah tazo. Nan Mama ta kira su daga d'aki suka fito.


Durk'usawa sukayi har k'asa suka gayar da Mum, bayan ta amsa ne take ta yabon musabak'ar su data gani ana ta haskowa a cikin kowace tasha.


Nan ta d'ora da gaya mata itace ta hana wani saurayi ya mara. Har ga Allah ta manta da abinda ya faru sai yanzu data tuna mata.


"Laaah Haj wallahi ba komai, ai yiwa kaine don ni ma zanso a daraja nawa iyayen".


Da hakan Mum ta basu dubu goma-goma suna ta godiya, itako ta fice daga gidan.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                 *(9)*



*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Da sannu Fadeel ya binciko gidan su Zajlah wanda karo uku kenan yana zuwa k'ofar gidan su amma sai jikin shi yayi sanyi yaka sa tunkarar ta yakoma.


Yau dai da k'arfin gwiywar shi ya tashi na tunkarar ta yaga ya mata gaskiyar lamari ce wa yana son ta.


K'ofar gidan ya zo, amma a tunanin shi na zai iya tunkarar ta yau sai gashi abin ya gagara, ta gaban shi suka zo suka wuce ita da Salmat domin zuwa koyon d'inkin su gidan wata mata dake k'arshen layin su.


"Ni fa Zajlah abin nan ya fara d'aure min kai, in har kin lura kusan kwana uku kenan duk muka wuce zanga wannan motar".


"Kuma fa abin mamaki ba a ganin na cikin motar su waye saboda duhun glass d'in motar".


"Ke kika damu da wannan motar, ni fa zan iya ce maki ban ma ta6a lura da motar ba sai yau dakika yi maganar".


"Ai ke dama ba komai kike lura dashi ba, inaganin wataran sai halaka ta hau kan ki bakisan za ta zo ba".


"Au dama in abu zai same ka zaka san da zuwan shine?".


"Ba hakan nake nufi ba, amma dai ana so ka lura da yanda abubuwa ke tafiya saboda tsaro".


Dariya sosai Zajlah ta yi, da hakan suka isa gidan da suke koyon d'inki.



******


Yau ne aka aje kan za'a yiwa Baban Zajlah aiki a idon shi, Malam Inuwa, Zajlah da Salmat ne suka yi mai rakiya zuwa Birnin kebbi. Asibitin Sir Yahaya ce aka yi mai aiki kuma aka gama cikin nasara wanda sai da suka had'a shi da medical glass saboda rashin ganin abinda ke nesa dashi.


Je kaga murna fal a gurin Mal Abubakar inda yake alfahari da y'ar shi k'waya d'aya tak da Allah ya bashi, wacce ta zame mai y'a d'aya tamkar da dubu.


*****


*Wacece Zajlah?*


Mal Abubukar d'an asalin k'auyen giwa tazo ne shi da matar shi Basira, auren zumunci ne aka yi masu  domin mahaifiyar ta da mahaifin shi ne uwa d'aya uba d'aya.


Sun ta so tare da Mal inuwa ne tun shigowar shi garin Jega sanadiyyar Sana'ar kayan gwari wanda daga baya har ya samu matsakaicin gida ya saye a kusa dashi ya dawo nan da zama.


Allah ya had'a kan matan su wanda inka gansu zaka rantse da Allah y'an uwan juna ne. Basira ta rasu ne tun ranar da ta haifi Zajlah wanda bata ko saka yarinyar a idon ta ba.


Lokacin ita kuma Mama Inno ta haifi Salmat da sati biyu, nan ta kar6i Zajlah ta had'a da Salmat tana shayar dasu. 

      (Asalin sunan Zajlatu ne k'awaye ne suka tak'aita shi da Zajlah, abinda sunan ke nufi rayuwa kyakkyawa kuma mai sunan tana daga cikin tabi'ai, me neman k'arin bayani akan asalin sunan da tarihin mai sunan zai iya searching da *KISASUT TABI'AT*, amma da larabci).


Sun shiga tashin hankali sosai musamman Mama Inno da Mal Abubakar, dole suka dangana saboda wanda yafi su son ta ya kar6i abarsa.


Zajlah na da shekara takwas a duniya  Baban ta ya makance sanadiyyar ya jima yana gani bishi-bishi sai bai d'aukin abin wata matsala ba har abin ya ta6a idon duka ya daina gani, tun yana iya lalurar kan shi har abin ya gagare shi.


Lokacin ne sauran tsirarrin dangin shi suka guje shi sanadiyyar ganin ya zama wata lalura a gare su, wanda shi ba hakan yazauna dasu ba don mutum ne mai taimakon dangin shi duk da shi ma ba wani hali ne dashi ba.


Sanadiyyar makarantar shi ne Zajlah ta dawo gurin shi da zama domin taimaka mai da wasu abubuwan da ba za'a rasa ba.


Zajlah yarinya ce mai kimanin shekara goma sha shida zuwa sha bakwai, chocolate colour ce ba wata kyakkyawa ce ta azo a gani ba sai dai manyan idon ta da gashin girar ta shike fitar da kyawon ta, yarinya ce mai shape  sai dai batada k'iba irin sosai d'in nan.


Kamin abubuwa suyi tsanani ansaka su makarantar boko iya primary daga nan basu cigaba ba sai makarantar Arabic dasuka mayar da hankali akan ta.


Saboda kowaccen su ta yi sauka uku sai kuma hadda da suke yi har Ustaz Lukman ya saka su acikin musabak'a, wanda sanadiyyar ne har duniya tasan da zaman su inda iyayen su ke alfahari dasu.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:29 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(10)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


www.sadijegal.blogspot.com


®NWA


*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


Mamaki fal a ran Saudat na miye silar zuwan Mum gidan su wannan kucakar yarinyar, ga shi tana so ta tambaye ta sai dai kuma bata ga fuskar tambayar ba.


Bayan sun dawo ne direct bedroom d'in Dad ta wuce, zaune yake k'asa saman carpet ya jingina jikin shi da kujera yana karatun jarida.


"Daddyn Alamein hutawa kawai ake yi"?.


"Ba dole ba tunda yanzu kin rage So na da tattali na, ina ga aure zan zo in yi ko zan samu mai bani kulawa", yana maganar ne d'auke da murmushi a dattijuwar fuskar sa.


Murmushi Mum ta yi sosai had'e da tattara hankalin ta guri d'aya ta k'ara matsawa gab dashi.


"Shikenan fad'uwa tazo dai-dai da zama, ka ga inka nemo mata sai a had'a da naka auren dana son ad'aura rana guda".


"Yaushe Son ya nemi mata banda labari? Yaron da ko mata bai cika kulawa ba ina yaga macen da yake so?".


"Sanin hakan ne ya sa na nemo mai mata da kaina, yarinya y'ar asali y'ar gidan mutunci mai ilmi".


Wata irin zabura ya yi ya kai duban shi zuwa gare ta.

    "Kina nufin Son ne za ki yiwa auren dole? Ko ni da nake uban shi ba'a yimin auren dole ba barrantana shi da yake cikin k'urciyar shi", yana maganar ne cikin fad'a-fad'a.


"Dad'i na dakai duk yanda ake magana cikin kwanciyar hankali indai aka ta6o yaran ka cikin second d'aya za ka birkice".


"Duk duniya ba ni da farin cikin da ya wuce na yara na, babu takura ko matsi tsakanina dasu duk abinda suke so shi nake so saboda haka babu maganar ki za6ama son abokiyar rayuwa sai ranar da yaganta da kanshi yakawo ta".


Suna cikin maganar ne sai ga Alamein da Saudat sun shigo d'akin, bayan sun gaida mahaifan sune suka nemi guri suka zauna.


Sai da ta tattara hankalin ta a gare shi sannan ta fara magana cikin hikima da basira.


"Alamein matsayi na na mahaifiyar ka data shayarda kai kuma ta raine ka da gudun 6acin ranka in na nemi wata alfarma gurin ka za ka iya yimin ita?".


"Haba Mum miye duniya bazan iya yi maki ba? Duk duniya banda tamkar ku ke da Dad sai kuma Lil".


"Da kyau Son! Mata na nema ma mai hankali da nutsuwa ga ilmi wanda nake fatar inka amince aure nan da wata d'aya indai har iyayen yarinyar basu yi mata miji ba".


Yanda kasan ana kid'a ganguma haka zuciyar Alamein ke bugawa, cikin abinda bai wuce second biyar ba zufa ta wanke mai fuska duk da sanyin A.c da fanka da suka yalwata d'akin.


"Aure kuma? Mace? Ni da kaina? Bazai yuyu ba, miye abin so ga Mace d'in? Me zan yi da ita? Tauyewar rayuwa kawai".

   "Anya zan iya bijirewa buk'atar Mum? Duk k'ask'anci na nasan darajar mahaifa na, in na yi mata hakan banyi biyayya ba", duk a cikin zuciyar shi yake wannan tunanin.


Ka aure ta kawai in ya so daga baya ka mak'ala mata wani sharrin ka sake ta kawai.


"Bazan so in zamo mai rayuwar auri saki ba shiyasa tun farko Mace ba ta gabana".


Duk a zuciyar shi yake ta sak'a wad'annan maganganun da ya rasa samun mafita akai.


"Mum ina fatar ba wannan maganar ce silar zuwan mu gidan su wannan kucakar yarinyar ba? Me Brother zai yi da wannan mitsitsiyar yarinya, kuma ma y'ar talakawa haba Mum".


Maganar Saudat ta dawo dashi hayyacin shi daga tunanin da ya cunkushe mai zuciya.


"Y'ar talakawa fa? Duk yanda naci buri akan auren Son da bak'i daga k'asashen waje a hakan zan tozarta?".


"Alamein".


Kai ya d'ago ya kai duban shi zuwa ga Mum had'e da saka handkerchief yana sharce zufan da ke karyo mai ga jiki ta ko ina.


"Amsar ka nake jira in har ka amince shikenan, in ma baka amince ba ka gayamin bazan tilasta kaba, sai dai ina hango alkhairi tattare a zaman takewar ku".


"Mum na amince". Da hakan ya mik'e ya fita daga d'akin zuciyar shi tamkar ta fashe.


"Alhamdulillah! Allah na gode ma, yanzu sai ayi haramar zuwa neman aure".


"Ke kuma fitsararriya da kike maganar y'ar talakawa ce na gaishe ki y'ar k'aruna, a hakan dai ta fiki mutunta mutane, ta shi ki 6ace min dagani".


Cikin 6acin rai Saudat ta mik'e sai da ta kai k'ofar fita ta furta "Allah yasa anmata miji kuma har an saka rana", sannan ta fice da sauri.


Murmushi Dad ya yi had'e da ce wa "wannan auren kan ki za ki d'aurawa shi saboda babu mai son shi".


"Saboda son kai da rashin hango abinda nake hangawa ba, amma nan gaba za ku gane inda na dosa.


® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(11)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


www.sadijegal.blogspot.com


® NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


Cikin sauri suka gaggauta shiryawa suka hau hanyar makaranta. Suna fita suka ci karo da mutumen kamar kullum sai dai sa6anin kullum yau ya fito ya jingina da motar yana waya idon shi akan su tamkar maye.


Hakan suka gilma ta gaban shi suka wuce, sallamar da ya yi ce yasa Salmat ta ja birki ta tsaya had'e da rik'e hannun Zajlah dake neman fincikewa.


Amsa sallamar ta yi sannan ta nemi ci gaba da tafiya, ganin ce wa in ya k'yale damar shi ta k'arshe za ta wuce, nan ya furta.


"Don Allah ki taimakamin da number k'awar ki ina so zanyi magana da ita, na yi tunanin bai dace in tsayar daku saman hanya ba shiyasa nake neman lambar muyi magana a tsanake".


Tana ta yar da kanta karaf idon su suka had'e take hoton abinda ya faru ranar ya dawo mata tangaragan, da sauri ta kauda kanta had'e da furta.


"Malam kayi hak'uri banda waya kuma an yimin miji, sai an jima".


Hannun Salmat ta fincika da k'arfi suka fice wanda Salmat sai mamakin ta take yi fal a ranta.


"Haba (ZAZ) wannan abin dame yayi kama?, ke ce fa a kullum ke yi muna nasiha kan ce wa wulak'anta d'an Adam bai da kyau amma ga shi yanzu kin yi da kan ki".


Nan Zajlah ta ba ta hak'uri had'e da ba ta labarin abinda ya faru, sannan ta d'ora da ce was' "a ganin ki wannan ko mijin aure na rasa ya dace da rayuwa ta?".


"Duk da hakan ya kama ta ki yi masa uzuri don baki sani ba ko godiya zai yi maki, ko kuma yana tafe da wani abu mai muhimmanci".


"Ko ma miye yanzu shi ta sha fa don ba ya gaba na". Da hakan suna tattauna wa har suka kai makaranta.


****


"Daddyn Alamein banji kace komai ba har yanzu kan maganar yarinyar, wallahi ina hango alkhairi ne tattare cikin wannan auren in har ta yiyu".


"Me kike so ince? Ai magana na hannun ki saboda yanzu ke ce mijin ni ne matar, tun da har kika iya k'udurta neman auren ba da yawu na ba".


"Haba abin bai kai haka ba, yanzu ya kamata mukai k'arshen magana kan turawa gidan su yarinyar, in kuma har kana ganin abar maganar ne wallahi ba matsala sai abar ta".


"Tu da kin yi magana da Son har ya amince ni me zance? Yanzu ki fara bincika wa kiji in har ba'a yiwa yarinyar miji ba sai kiyi k'ok'arin samun wa'anda za ki tura ayi maganar don bazan sa kai na ba cikin abinda yaro na bai so ba".


"Shikenan ba matsala za'a yi yanda ya dace tunda Abban Yusrah na da rayuwar shi, kuma ko da ran ka shi ne waliyyin shi".


Da hakan ta fice daga d'akin ta shirya sai gidan su Zajlah. Bayan sun gaisa da Mama Inno ne ta sako mata buk'atar da ke tafe da ita kan tambaya in ba'a tsaidawa Zajlah miji ba kan za su turo manya domin ne mawa yaron su ita.


Nan Mama ke tabbatar mata ce wa Zajlah ba tada miji, har suka ajiye kan ce wa za'a turo manya, da hakan Mum ta fice daga gidan.


****


Yana batun fice wa ne suci abinci Mama inno ta tsayar da shi take gaya mai abinda ke faruwa.


"Kin ga abinda nake gudu, shiyasa nake matsawa Mal Abu kan ce wa yasamu mata yayi aure tunda ya samu lafiya kafin yaran nan su samu mazajen aure, ga shi har an fara zuwa neman su bai da mata, kuma bai dace ayi auren d'aya daga cikin su bai da iyali ba".


"Yo in haka ne abar min maganar zan tuntu6i k'awata Asabe in har ta amince sai ayi auren nan da sati d'aya tunda dukan su ba yara bane kuma tana da hankalin ta da nutsuwa, kasan ita ma mijin ta rasuwa yayi".


"To shikenan sai munji daga gare ki duk yanda kukayi".


Da hakan ya sa kai ya fice zuwa mazaunin su yana mai labarta wa Mal Abu maganar neman auren shi tunda ya k'i nemo wa da kanshi had'e da gaya mai za'a zo neman auren Zajlah.


"Ba komai Mal Inuwa Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi, na gode sosai da karamci Allah yabar zumunci".

   Amein ya furta a tak'aice. Saboda hakan yake jin Mal Abu tamkar d'an uwan shi na jini.


******


*BAYAN SATI BIYU*


Anyi auren Mal Abu da Asabe wanda ta tare gidan, suna zaman su na fahimta akan su duka ba yara bane, kuma Asabe Mace ce mai hak'uri da sanin ya kama ta don bata san inda take aza Zajlah ba kan kulawar da take ba ta.


Cikin hakan ne Zajlah da Salmat suke zama duk gidan da suke so tsakanin wurin Mama Inno da wurin Mama Asabe.


A 6angare d'aya kuwa k'anen Baban Alamein wato Alh Muttak'a Mum ta nema had'e da d'ora mai nauyin maganar auren Alamein, domin halayyar su ba d'aya ba shi da Dad, mutum ne mai karamci da iya zama da mutane.


Wanda karamcin shi da sanin halayyar shi ya sa yana tunkarar su Mal Inuwa da magana take nan aka ba shi Zajlah, saboda a tunanin su yaron gurin shi ne ke son ta.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda``` ```Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                *(12)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Ustaz Yusuf ne da Ustaz Lukman ke tsaye suna tattauna wa akan tafiyar da tsarin makantar su kan musabak'ar da za'ayi nan da next year. A tsayen da suke ne suna tattaunawar  d'alibai ke wuce wa ta gurin suna gaida su ciki kuwa har da su Zajlah.


"Wai har yanzu baka tunkari yarinyar nan da maganar cewa kana son ta ba?, kasan fa ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kar wani ya yima shigar sauri".


"Bazai ma kawo ba saboda ina nan da shirin tunkarar ta kwanan nan insha Allah, akwai abubuwan da nake jira ne da komai ya kammala zan tunkari mahaifin ta".


"To Allah yataimaka yasa kuma rabon kace, da na yima murna sosai saboda hankali da nutsuwar yarinyar".


A hakan dai suka k'are tattaunawar suka shiga cikin makarantar domin fara karantar da d'alibai kamar kullum.


******


Tun ranar da aka sanarda shi maganar tsayar da ranar auren shi da wacce bai sani ba ya shiga tashin hankali marar misaltuwa wanda daka kai dubanka zuwa gare  shi za kasan ya fice daga hayyacin shi.


A kullum tunanin shi da wanne ido zai kalli friends d'in shi da kullum yake cika bakin kan cewa Mace ba ta gaban shi, wanda a kullum maganar shi bata wuce shi aure baya gaban shi. K'arar rufe k'ofa ce ta dawo dashi hayyacin shi wanda kan tsabar tashin hankali idon shi har sunyi ja, guri ta nema ta zauna sannan ta fara magana.


"Yanzu Brother kana gani za ka zuba ido a d'aura ma aure da wannan yarinyar? Wallahi talakawa ne sosai kuma da ka ga yarinyar za ka shaida cewa ko boko batayi ba, ko kusa baku dace ba wallahi".


"Ya kama ta in ma aure ake so kayi to a baka dama ka zak'ulo yarinya mai class ba kamar waccan kucakar ba".


A kasalance ya tashi daga kwancen da yake ya saka filo a bayan shi ya jingina da gado, ido ya sako mata tamkar yayi kuka.


"Ni ba ma yarinyar ce ta dame ni ba kamar auren da za'a yimin a dai-dai wannan lokacin da ban shirya ma abin ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba bazan iya bijirewa buk'atar Mum ba a gare ni zanyi mata biyayya insha Allah".


"To Brother Allah yaba ka iko, kuma yasa auren ya zamo alkhairi a gare ka kamar yanda Mum ke furta wa".

    A tak'aice ya amsa da Ameen.


"Amma ya kama ta ka gayawa su brother Imran saboda fara shirye-shirye, kaga sati biyu ya rage har auren".


Wayar shi ya d'auko ya mik'a mata had'e da bata umurnin ta kira Imran da Salis ta gaya masu yana neman su yanzu.


Cikin mintunan da basu wuce goma ba suka iso gidan, Mum suka fara biyawa suka gaida sannan suka wuce part d'in shi saboda ba suda shamaki da gidan.


Bayan sun shiga d'akin ne suka tarar da Saudat na rarrashin shi kan ko tea ne yasha Wanda duk ya fara jemewa, dak'yar yasha tea d'in kad'an sannan suka gaisa.

      Nan Saudat ke labarta masu abinda ke faruwa, kowannen su mamaki fal a ran shi. Sai dai jin cewa za6en Mum ne suka ga cewa lallai gata ne aka yimai.


Nan dai suka tattauna yanda abubuwan za su kasance, amma ya jajirce kan ba za'a yi komai ba bayan d'aurin aure, a hakan suka biye mai saboda sanin hali.


*****


6angaren Zajlah kuwa mamaki ne fal a ranta kan ce wa an tsayar da maganar auren ta da wanda bata sani ba, kuma har yanzu bai zo gidan su ba, to wannan waye shi? Tasan dai ba wanda suka gani a mota bane.


Koda jiya ankawo kayan sa Lalle har da lefe duka, anan take jin ana fad'ar cewa mijin bai Nigeria sai ana saura kwana biyu aure zai dawo.


"ZAZ mu gayawa Mama ta fitarwa y'an ajin mu da ta su alawar da kuma malamai".


"Wannan aikin na kine, ni dai inkin shirya ki fito mu wuce kinga ko jiya mun kusa makara har Ustaz Yusuf na mana fad'an mun fara rashin mayar da hankali yanzu".


"Ke kam yanzu da mayar da hankali da rashin mayarwa duk uwar su d'aya ubansu d'aya, saboda dole ki jingine makaranta".


Muguwar harara Zajlah ta sakarwa Salmat wanda yasa cikin sauri ta fad'a d'akin Mama Asabe ta d'ebo iya adadin alawar da zasu baiwa y'an ajin su da malamai suka fice.


Ustaz Yusuf ne ke rarrashin Ustaz Lukman kan tashin hankalin da ya shiga sanadiyyar alawar da Salmat ta kawo masu had'e da bak'in labari a cewar shi.


"Tun ba yau ba nake lurar da kai kan ka gaya mata muradin ka a kanta amma ka tsaya sanya ga abinda ya faru yanzu".


Magana kan ta kasa yin ta yake yi saboda sai ya bud'a ba ki ya kasa furta komai. A hakan ya buga mashin d'in shi ya fice daga makarantar da ya ga ta koma mai tamkar bak'in hadari.


(Sorry 4 late posting kamar kullum, ina busy ne shiyasa)



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                *(13)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


Bai gasga ta maganar ta ba har sai da ya tura manyan shi da maganar aure aka tabbatar mai cewa auren ta saura sati biyu.

         Har ga Allah ya so yasa mu yarinyar a matsayin abokiyar rayuwar shi, har kullum yazo kwanciya muryar tace ke yimai amsa kuwar maganar da ta yi mai, a tunanin shi duk wanda ya sa me ta ba k'aramar sa'ar rayuwa yayi ba.


Fadeel kenan yaro ga Alh Ibrahim da Haj Fatima wanda yataso cikin gata da jin dad'in rayuwa har yake tunanin zai iya taka kowa ba tare da antakura shi ba.


Sai gashi yanzu ya yi sanyi sosai tamkar ba Fadeel ba sanadiyyar soyayyar da ya d'orawa Zajlah tun ranar da ta rik'e mai hannu had'e da yimai nasiha kan abinda ya kusa aikatawa, sai gashi kuma ashe ba rabon sa bace.


*******


Imran ne had'e da Salis suka zo k'ofar gidan su Zajlah, bayan sun gaisa dasu Mal Abu ne suka yi masu bayani kan cewa abokanen Ango ne ya turo su gurin Zajlah ne. Da hakan Mal Inuwa ya shiga gidan shi ya gaya masu su shirya suna da bak'i saboda suna gidan shi.


Shimfid'a aka yi masu a zaure ya fito ya gaya masu su shiga daga ciki. Zaman su bai wuce minti biyar ba Zajlah da Salmat suka fito nan suka gaisa duk da basu san su waye ba.


Sarkin tsokana ne Salis ya yi gyaran murya had'e da furta. "Amaryar mu ya kike?".


Nok'e kan da tayi ne ya bayyana cewa ita ce amaryar, a ranshi yake k'iyasta lallai Mum ba k'aramin gata tayi wa Alamein ba saboda Zajlah ba tada makusa ko kad'an, don ga alama inta sa mu guri za tafi haka fresh.


Gyaran murya Imran ya yi ya kai duban shi ga Salmat yana mai tambayar ta abubuwan da za suyi na aure.


"Gaskiya babu abinda muka shirya sai walima wacce za'a yi cikin makarantar mu ranar juma'a ana gobe d'aurin aure".


Wani dad'i ya ziyar ci zuciyar su Salis duka sanadiyyar jin ra'ayin su d'aya da Alamein. Yanzu sun sa mu hujjar da za su kare kansu ga friends d'in su koda sun dame su da tambayar ya akayi biki babu wasu events, za su basu amsar amaryar ustaziya ce.


"Ashe Ustaziya zamu aura bamu sani ba, to Allah sanya alkhairi ya had'a hankulan ku", cewar Imran.


Waya Salis ya fitar yana kira tak'i shiga yakai duban shi ga Imran yana mai cewa' "ka ga wayar mutumen ta k'i shiga yana yuyuwa network ne ba kyau, kuma gashi ya ce yana so yaji zazzak'ar muryar amaryar shi".


Ido d'aya ya kashewa Imran saboda ganin ce wa bai fahimci inda yadosa ba har yana batun magana ga shi yana gudun ya kwafsa mai.


"Tun da ba'a sa mu wayar shi ba sai ki ba da taki number a tura mai ku gaisa kamin yadawo".


"Wallahi banda waya, saboda su Baba sun hana mu rik'a waya". Ba k'aramin dad'i yaji ba da amsar da ta bashi, saboda ya san ko number ya kar6a ko kallo bata ishi Alamein ba, asali ma za ta iya zama silar samun sa6ani tsakanin su.


Dubu hamsin suka zube masu domin hidimar aure inji Ango a cewar su. Da hakan sukayi sallama dasu suka fice had'e da yaba hankali da nutsuwar yaran.


*******


Tabbas yau ya tabbatar da cewa a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, "gaskiya ba k'aramar asara nayi ba da ban sa mu Zajlah a matsayin mata ba, saboda ban zaci wannan risk'in ba ko kad'an".


"Ko da ance wani bai auren matar wani Allah bai k'addar to aure tsakanin mu ba dole inyi hak'uri in fawwala ma Allah lamari na, takan yuyu ba ita ce alkhairi a gare ni ba".


Duk a zuciyar shi yake wannan tunanin yana cikin tsananin tashin hankali, a hakan ya tashi ya yi nafila raka'a biyu had'e da addu'o'i ta ke yaji nutsuwa ta sauko mai.


******


Suna koma wa gidan ne Salis ya saka Alamein gaba da surutu har yana ce mai,

"Gaskiya friend ka gode ma Allah da wannan gatan da Mum tayi ma, wallahi ta za6o ma Mace mai hankali nutsuwa da ilmin islama, ko fa waya ba'a bari ta rik'a gidan su wallahi hakan ya burge ni sosai".


"Saboda waya ga budurwa ba k'aramar illah bace, itace jigo na farko dake fara taka rawa a lalacewar tarbiyyar yara".


"Duk wannan kai ta shafa kuma matsalar kace ba tawa ba, ina ruwan k'wai da aski, kuma in ka zo ne kacika min kunne da surutu sai in ta shi in ba ka guri, saboda na ga ka zo da sabon salo kiran sallah da usur".


"Wa ne ni in takura Ango, ai sai dai ni in d'aga in ba ka guri". Hakan ya gama zolayar shi suka fice daga gidan.


(Ina so inyi kira gare mu iyayen yara akan sake ma yaran mu domin amfani da waya, muna ganin tamkar burgewa ce ko wayewa to gaskiya wannan bai yi ba.


Ba'a ce kar ku bari yaran ku suyi amfani da waya ba, sai dai ya kama ta ku saka ido akan kowan ne tako na yaran ku saboda kaucewa fad'awa hatsari. Kar kice ai shiriya ba a hannu na take ba ga Allah take, kulawar ki zai sa Allah yadubi zuciyar ki ya tallafa maki gurin d'ora tarbiyyar yaran ki akan hanya madai-daiciya.


Gare ku y'an mata, ina mai kira zuwa gare ku daku tsalkake zuciyar ku akan mu'amala da waya domin sharrinta ya fi alkhairin ta yawa.


Ya Allah don darajar sunayen ka tsalkaka, don k'udurarka don iradarka don k'arfin mulkin ka ka shirya mana y'ay'an mu Maza da Mata.)



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


               *(14)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


     Sun baro part d'in shi ne suka had'u da Mum har za su fice daga gidan, bayan sun gaisa ne take tambayar su shirye-shiryen da suke yi a game da auren.


"Gaskiya Mum babu wani abu da za muyi, saboda yanzu haka daga gurin yarinyar muke ita ma babu wasu events a tsarin ta, walima kawai za su yi a islamiyar su".


"Ni ma ranar assabar zan had'a k'aramar liyafa insha Allah. Ku cigaba da lurar da mutumen ku had'e da shawarwarin da suka dace, Allah yak'ara had'a kan ku yabar zumunci".


"Ameen Mum, ai tsakanin mu da Alamein sai dai godiya don ya yi mana duk yanda ake yi", cewar Imran.


Nan Mum ta wuce bedroom d'in Dad, ta bi shi da ido hankalin shi kwance yana karatun jarida. Gefen shi ta samu ta zauna sannan ta fara magana.


"Ya kama ta a fara shirye-shirye, na ga ko I.V baka bugo ba gashi lokaci sai k'aratowa yake yi".


"Kisa a buga ko Abban Yusrah yasa a buga don ni na fad'a maku bazan saka baki na a wannan auren ba har sai na ga cewa Son ya sauko yana walwala kamar kowa".


"Yo ko yanzun ce ma akayi baya son maganar?, ni fa na rasa gane wane irin mutum ne kai, don Allah kayi hak'uri ka saka ma wannan auren albarka".


Dak'yar da lallami ta samu ta shawo kanshi ya sauko har suna tattaunawa kan abubuwan da suka dace ayi na auren.


*******


Akwana a tashi wataran jariri ango ne, yau dai ga shi har ansaka Zajlah a lalle duk wani abu da za'a yi na al'ada 6angaren amarya da ango duk anyi, inda a 6angare d'aya Amarya tasha gyara daga wata shuwa dasu Mama Asabe suka d'auko musamman domin wannan rana.


Yau ce ranar da za'a yi walimar Amarya a makarantar su, inda ba k'aramin jurewa Ustaz Lukman ya yi ba cikin Maluman da suka gabatarda walimar. Amarya tasha nasihohi sosai ga Malaman ta sai dai fatar d'orewar zaman lafiya ita da angon ta.


"Yanzu Yusrah duba kiga wai wannan yarinyar ce Brother zai aure, da ace auren da yake so ne da events da za'a sai mun ture".


"Ai ko hakan ba laifi, don ni dai abin ya burge ni sosai har ina tunanin in aure na ya tashi ni ma irin wannan walimar za'a yiman".


"Ni kam wallahi ranar aure na sai an gwangwaje bazan yi irin wannan ba, kinga har Mum ta biye wannan abin wai ita ma za tayi liyafa gobe".


"Ke inda Dad na son wannan auren ai wallahi da yanzu gari ya d'auka tun ana saura wata d'aya auren, amma duba yanzu wai gobe d'aurin aure amma abu shiru tamkar mutuwar sarkin gari".


Dariya sosai Yusrah ta yi tana mamakin wannan ak'idar ta Saudat na k'yamar talaka, ta san da ace Zajlah masu kud'i ne to da duk yanda suka tsara abin ba za ta kushe ba.


"Mu wuce gida Yusrah tun da an k'are". Maganar Saudat ce ta dawo da ita hayyacin ta.


"Kibari mutane su rage sai mu gaisa da amaryar sannan mu wuce, kin ga yanzu jama'a sun mata yawa".


"Don Allah ki wuce muje, ai dai tasan ba za'a rasa zuwa daga dangin Angon ba kuma munzo buk'ata ta biya ai shikenan".


"Miye amfanin kiran sallar kurma?", ce war Yusrah.

 

"Ban fa fahimce ki ba, ke sai ki rik'a je fawa mutum magana a dunk'ule".


"Ke kuma ga ki ba cikakkar bahausa ba, to ina nufin miye fa'idar mu zo bamu gaisa da Amarya ba mu fice".


"To ni dai ba don ta na zo ba, saboda yaya na nazo kuma babu lallai sai na tsaya".


"Yo ai duk d'aya an cewa shege marar uba".


Maganganun na Yusrah suka ishe ta ya sa taja bakin ta ta tsuke, ba don ta so ba ta tsaya har mutane suka rage sannan suka k'arasa gurin ta, cikin yatsinar fuska Saudat ke kallon su da d'ai d'aya sun sha manyan hijabayyen su har k'asa.


"Kyawon zaman takewa ka samu abinda yada ce dakai, amma wasu da ka gansu kasan abin sai maneji".


"D'an hakin da ka raina shi ke tsokane ma ido, kuma mutunci siyen shi ake yi ba shi ke kai tallan kanshi ba, mai hikima shi ke tauna magana kamin ya watso ta, wani ko maganar ke neman mak'alewa domin ya suturta ta shiko yana k'ok'arin hankad'o ta".


Cikin muzan ta Saudat ta bi Salmat da kallo had'e da mamakin kalaman da ta feso mata tamkar dafin maciji.


Yusrah ce ta tsaya suka yi gaisuwar mutunci har suna ta6a hira tsakanin su, daga nan suka fice su kuma suka shiga napep sai gida.


(Kuyi maneji da wannan, y'ar mutan Jega na mik'a gaisuwa ga fan's d'in ta, luv y'all)



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                   *(15)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

 *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



*WASHE GARI*


Yaune ranar Assabar misalin k'arfe *12:00* dubban jama'a suka shaida auren.


*AL'AMEIN KABEER AL'AMEIN (A.K.A)* 


                DA


*ZAJLAH ABUBAKAR ZUBAIR (ZAZ)*


Wanda ya samu halartar manyan bak'i daga gurare da dama duk da ba hakan Dad ya soba, musamman gidan su yarinyar da yake ganin k'ask'anci ne kamar shi yaje wannan k'azamar unguwar kuma ace auren d'an shi ake yi gurin.


Dak'yar da lallami k'anen shi Abban Yusrah wato Alh Muttak'a ya shawo kanshi kan zuwa gurin auren.


A 6angaren Alamein kuwa shi ma dak'yar da lallami Mum dasu Salis suka ciwo kan shi ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin dakakkiyar shaddar shi fara k'al wacce ta k'ara fito da kyawon shi na asali, sai dai daka dubi fuskar shi babu annuri sam a tattare dashi.


Bayan gama d'aurin auren ne Imran ke yimai tuni kan gaisuwar da Ango da abokanen shi ke shiga yi gidan su Amarya, tur6une fuska ya yi tamkar wanda aka yiwa wahayi da mutuwa.


"Kayi hak'uri A.K.A kakka bijirewa umurnin Mum in kayi hakan ba za taji dad'i ba kuma kasan da za mu fito sai da ta k'ara jaddada mana hakan".


Da hakan suka d'an shawo kanshi suka shiga gidan su Zajlah shi da tsirarrun abokanen shi suka gayar da iyayen, sai yak'e yake yi wanda ya fi kuka ciwo had'e da wani tur6une fuska tamkar yad'ora hannu Saman kai yafasa da kuka.


Muryar Salis ya ji had'e da wasu friends na su suna tambayar ina Amarya ta fito a gaisa. Zumbur yamik'e tamkar wanda ya zauna akan kunama, hanyar fita daga gidan ya dosa ganin hakan ya sa suka mara mai baya.


Can na tsinkayo maganar wata daga cikin dangin Zajlah na giwa tazo na furta. "Gaskiya wannan Angon na da kunya akan wasu mazajen da za kaga sun shigo gaida iyaye an saka Amarya gaba har da su d'aukar hoto".


"Gaskiya kam wannan na da sauran kunyar shi", inji wata mata.


Da hakan sauran k'awayen Zajlah suka shiga gidan su Salmat suna ta yabon kyawon angon, har wasu na zolayar ta da cewa' "shiyasa ake mana 6oyon Angon ashe ansan mai tsada ne hakan, gaskiya kin more Allah yabada zaman lafiya".


Salmat ce ta kar6e da Ameen had'e da cewa ai dole mu 6oye angon mu ga irin ku masu hangen kyawawan Maza.


Da hakan dai suka ta zolayar juna wanda Zajlah tayi shiru ita d'ai tasan me take tunani a ranta saboda tana hango abubuwa da dama.


*******


*10:00pm*

Aka kai Amarya d'akin ta had'e da y'an rakiyar ta iyaye da abokanai har da dangin ta y'an giwa tazo, a unguwar G.r.a aka kaita gida ne d'an matsakaici mai part uku wanda yasha shuke-shuke na flowers sai k'amshi ke tashi.


Nan dai dangi suka yi mata nasiha gwargwado had'e da lurar da ita muhimmancin hak'uri da biyayya, har wata na cewa duk da munsan abinda za mu fad'a duk malaman Ku sun riga mu. Da za su tafi ta ci kuka sosai har ta gode Allah inda take ta tunanin wace rayuwa za ta fad'a yanzu.


Har k'arfe goma sha biyu bataji d'uriyar kowa ba, da hakan ta rage kayan jikin ta ta zazzagaya d'akin wanda ta jinjina ma mahaifinta da k'ok'arin da yayi duk da cewa yawanci siyayyar da kud'in da ta samu a musabak'a ne, ta ji dad'in ganin cewa har da keken d'inkin ta aka had'o mata dashi.


Da hakan ta shiga ta watsa ruwa had'e da alwala ta yi karatun K'ur'an had'e da addu'o'in ta, ba ita ta kwanta ba sai wurin k'arfe d'ayan dare.


*****


6angaren Alamein kuwa ba yanda su Imran basuyi ba kan siyen wani abu da zai shiga dashi gida yak'i, Salis ya nuna zai siya kuma ya hana. Dai-dai da rakiyar da akewa Ango d'akin Amarya cewa yayi ya hutar dasu, hakan ya fice ya bar su nan da mamaki fal a ransu.


Da shigar shi gidan ko ta kan Amarya bai bi ba yayi part d'in shi, kayan jikin shi ya rage yayi wanka duk da bak'ar yunwar da yake ji hakan ya dunk'ula ya kwanta don rabon shi da abinci tun goma na safe.


*****


Kiran asubar farko ta tashi daga baccin,  sallah ta fara gabatar wa sannan ta zauna zaman lazimi wanda bata tashi daga gurin ba sai bakwai na safe. Carpet d'in sallar ta ninke sannan ta d'an kimtsa d'akin, k'ullewar da cikin ta yayi ne ta tuna rabon ta da abinci tun la'asar d'in jiya.


Bugun k'ofar da ta jine yasa ta saka hijab d'inta ta fito falon, kayan abinci ta gani jere a dinning table d'in. Gate ta nufa inda take jin k'arar ta bud'e k'ofa Sagiru k'anen Salmat ta gani da kula had'e da babban jug.


Gayar da ita ya fara yi sannan ya mik'a mata kayan had'e da juyawa zai koma. "Kashigo mana daga ciki".


"Aah zan ko ma islamiya ne ko yanzu break muka fito Mama ta aiko ni".


"To mu shiga in baka kud'in mashin ko?".


"Mama fa ta bani, ga ma mai mashin nan na tsaida waje zai ko ma dani".


"Duk dai salon kar ka shigo ne, to ya yi ka gaida su na gode, ka gaya wa Salmat ina dubin ta".


Da hakan ya wuce ta rufe k'ofar ta juya zuwan falon, abinda taci karo dashi ne ya saka ta razana wanda saura k'iris jug d'in yafad'i daga hannun ta.


(Maryama ga shi na cika alk'awari, tun da ba'a bani wani novel sai na turo nawa, _lolx_.


Masoya na masu kira na, masu kula ni private da kuma group nagode sosai Allah yabar zumunci.


Daga yau zaku rik'a samun wannan buk sau biyu kullum insha Allah, luv y'all My fan's.)



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                   *(16)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


www.sadijegal.blogspot.com


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Tana doso falon karaf idon su suka had'e yana mai aika mata da mugun sak'on harara tamkar fararen idon shi su fad'o k'asa. Gaban ta ne ya yi mugun fad'uwa had'e da razana, ba k'aramin k'ok'ari ta yiba gurin rik'e kayan da ke hannun ta har za ta ratsa shi ta wuce part d'in ta komai ta tuna ta durk'usa har k'asa ta gaida shi, ba tare da ta jira zai amsa ba ta wuce kawai.


Mamaki ne fal a ranshi sai kuma d'imbin haushi dake cunkushe da zuciyar shi na ganin ce wa ga abinci Mum ta aiko masu tun d'azu amma don rainin hankali ta kira gidan su akawo mata abinci. 


Wata zuciyar ke yimai tuni kan cewa ka gaya mata an kawo abinci? Ko kuma jiya da ka yi kwanciyar ka ka yi tunanin me za taci?.

    Hannu ya bud'a alamar ba ruwan shi ko a jikin shi. Abin sai damun shi yake k'ara yi yanda ya ga wannan mitsitsiyar yarinya wai itace matar shi, a tunanin shi ma ko sa'ar Saudat k'anwar shi bata yi ba aiko k'auye an rage wannan bala'in.


Hakan dai ya zauna saman dinning table ya d'an tsakuri abincin kad'an saboda tun ranar da maganar ta 6ullo bai k'ara saka wani abincin kirki a bakin shi ba, har wata rama ya yi sai tsawon da manyan ido.


******


6angaren Zajlah kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba na mugun kallon da ya bita dashi, tun jiya take ta nazari ko za ta kamo makamar auren amma kash data had'a zaren zai tsinke.


Saboda tun tashin ta ko a tarihi bata ta6a ganin angon da ya shigo gida daren amarcin sa bai waiwayi Amarya ba sai a kanta. Yanzun take d'ora abubuwa akan mizanin awo ko za ta samu wanne zai rinjayi wani, sai dai abin sai k'ok'arin gagarar ta yake yi. Ba komai bane wannan sai zuwan Mum gidan su da kuma zuwan su Imran, sai dai a tunanin ta mizanin awon ta zaifi rinjaye akan zuwan Mum.


Ba akan komai ta karkata can ba sai ganin babu tausayi ko kad'an a k'wayar idon angon barrantana shi So ya samu mazauni ko da kad'an ne, kenan hakan na nufin Mum ce mai auren sanadiyyar gajeren taimakon da tayi mata, inko hakan ne wani taimako ya kusa zama masifa domin dai ita wannan bai dad'a ta da komai ba sai tarin k'uncin rayuwa, in ko hakan ne sam babu adalci a cikin wannan lamarin da sake ashe ranar walima k'anwar shi tadinga so ka mata magana, wanda a wancan lokacin har laifin Salmat ta so hangowa na mayar da martani da ta yi.


Tabb lallai ko akwai aiki sabo wankan jego da ruwan fridge. K'arar da cikin ta ya yi ne ta dawo daga duniyar da ta lula, kular ta bud'e taga waina da miya ce sai kuma kunun tsamiya cikin jug.


Sanin cewa ba ta iya canye ta ya sa ta dake ta fito daga d'akin, kitchen ta nufa ta d'auko plate da cup har ta dawo d'aki bata ganshi ba.


Abinci ta ci sai da ta yi k'at sannan ta shiga ta yi wanka ta kimtsa had'e da k'ara kimtsa d'akin na ta.


******


*04:30pm*


Sai hada-hadar shiri ake yi domin y'ar liyafar da Mum ta shirya da za'ayi a gidan ta nan cikin G.r.a d'in wacce za'a yi Mata zalla. Yusrah ta kira ta aike ta takaiwa Zajlah kayan da za ta saka.


Duk k'awayen ta da dangi na kusa ko wa ya zo har da iyaye sun hallara gidan Mum. Wata dakakkiyar shadda kalar purple Mum ta aiko mata sai wani k'aton gyale mai kalar ash da takalman ta ash, Salmat ce mai take mata baya har zuwa masaukin da aka yi mata.


Mum Faty & Jegal fan's su ne na farko da isowa gurin liyafa, su Bizzy, Yagani, Zainab, Sharubutu, Maryam, Mmn Eman, Hindatu sune kan gaba-gaba, Musha karatu group su ma sun hallara inda Fatima, Aunty Baraka, Maryama, Ummietta wabi, Mrs Zannah ke ta rabon ido, Mumbarin Jabo ma sun iso Innah Habiba da Yasmeeny a sahun gaba.  Zauren karatu Serdeeyer, Meenah, Batul A. Go I sune a gaba, sai Zumunci group had'e da Greatest women inda khairat, ummen Alamein, fati salihu, Jamila sahabi suke jagorantar sauransu.  Zahra B~B fan's duk ba'a barsu baya ba, Ashnur, Hauwa jidda, Anee fan's Anee, Ayusha, Zayyenab sun hallara su ma, sai kuma y'an Taskar Lubiee.


Kallo ne ya ko ma k'ofar shigowa gurin sanadiyyar wasu Mata da suka doso gurin cikin ankon su na materials iri d'aya wato blue sai gwaggwaro da takalman su kalar sky, cikin nutsuwa suke tafiya har suka doso gurin, Stylish, Autar Hjy, Feedoh Deedoh, Munayshat, Miss Hafcy, Queen Miemie sai kuma Miemi Bee, Fulani ced'iya, Hauwa damary, Mrs Umar su ne suka fara ne mawa manyan su gurin zama sannan suka zauna, ba kowa bane wad'annan face Nagarta masu Nagartattar zuciya duk inda suka gilma kallon su ake yi tamkar wasu taurari.


Da hakan akaci liyafa cikin farin ciki da walwala abin sai son barka.


(Amma fa na hango masu wawason abinci da lemukka, ko in zayyano maku su?, *lolx*)



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                     *(17)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Bayan an watse daga liyafar ne Mum ta tsaida ta gidan ita da Salmat a ce war ta su bari mutane su watse lokacin an gama gaisawa tasa direba ya maida su, duk da ba wani nisa ne dasu ba.

   Ad'an zaman da ta yi na awanni ne ta fahimci tsantsar son da Mum ke yi mata da kuma Yusrah wacce ta fahimci d'iyar k'anen Baban shi ce, sa6anin Saudat dake bin su da muguwar harara.


Zuwa bayan isha'i ne Dad ya shigo gida, bayan Mum ta yi mai barka da dawowa ne take gaya mai cewa, "na fa tsayar da matar Son don ku gaisa".


"Ai da kin bar ta ta wuce ba sai mun gaisa ba, tunda ke da kika k'ulla abin kin ganta kuma ta gan ki. Wai ma kina hankalce da yanda kika lalatamin rayuwar yaro?".


"Haba Dadyn Alamein ban fahimce ka ba, me ya ka wo wannan maganar?, me yasa abu baya wuce wa a gurin ka?".


"Ba wai baya wuce wa bane, rai na ke 6aci in har na dubi yanda Son ya koma yanzu, walwala, farin ciki, nishad'i duk sun kau a rayuwar shi har wata uban rama ya yi duk ya zabge tamkar wanda ya kwanta ciwo".


Murmushi ta yi irin na su na manya had'e da furta "Adalilin gatan da nayiwa Son in har muna raye za kaji dad'in abin, kai dai ka rik'a d'ora shi akan turba ta k'warai had'e da lurar dashi wasu abubuwan".

   Tana kaiwa k'arshen maganar ta fito zuwa falo ta janyo Zajlah sai falon Dad.


Har k'asa ta durk'usa ta gaida shi cikin nutsuwa da girmama wa, har ga Allah yarinyar ta burge shi sosai, sai dai matsalar d'aya ce da Son baya son ta. Saboda shi fa duk abinda zai yi sanadiyyar farin cikin yaran shi yake yin shi, kuma in ba su son abu har ga Allah zai iya yafe abin nan duk son da yake yimai.


Mum ce ta ta6o shi alamar yayi magana ya sanya wa auren albarka, hakan ya yi gyaran murya suka k'ara gaisawa ya sanya mata albarka had'e da fatar zaman lafiya.

   Da za ta wuce dubu goma ya ba ta, sai dai k'in kar6a tayi sai da Mum ta kar6ar mata. Mum kuma turarukka had'e da humra y'ar asali ta Maiduguri ta had'a mata, har za su wuce take tambayar ta ina wayar ta halan?


Amsa ta ba ta kan ce wa wayar na cikin kayan lefen ta ko bud'a ta bata yi ba. 

   "In kinje gida ki had'a wayar mana tunda can su Maman Sagiru sun hana kiyi amfani da ita, ko ba kyaso ki gaisa da k'awaye da kuma ni Mum d'in ki?".


Murmushi ta yi ta soke kai, karaf Yusrah ta ce' "Mum ta bari gobe zan zo in had'a mata".

   "To anji sarkin iya yi", cewar Mum.


Da hakan direba ya kai ta gida inda ta so Salmat ta shigo ta nuna mata ce wa dare ya yi, kuma ta san unguwar ta su sai a slow, amma za tazo ranar Alhamis ita da k'awayen su na makaranta. Warmers d'in da Mum ta ba ta ta d'auka ta shiga gida had'e da sauran kayan ta ita ko Salmat direba ya wuce da ita gida.


******


Bayan Zajlah ta shiga gidan ne ta ajiye kayan abinci a falon, bedroom d'inta ta wuce, saboda tsabar gajiya tu6ewa tayi ta fad'a toilet ta yi wanka. Kayan ta na lefe ta bud'e wanda bata ma san ya suke ba, akwatin k'ana nan kaya ta bud'e ta samu wata night gown mai d'an girma ta saka, hijab k'arami ta d'ora sannan ta fice zuwa falon, plate ta d'auko kitchen ta d'ibi abincin ta koma d'akin ta.


Bayan ta gama ne ta je kitchen ta wanke abinda tayi amfani dasu sannan ta koma d'akin ta, alwala ta yo ta shimfid'a carpet ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi lazimi sannan ta kwanta.


Tabbas ta dad'e tana tsara ma kanta irin rayuwar da za tayi ta farin ciki a gidan auren ta, da kuma kyautata wa duk wanda ta aura saboda samun lada a k'ark'ashin shi, sai dai kash tana ganin da wuya hakan ta kasance a yanda take ganin wannan auren.


Gashi a tsarin ta tana son namiji mai tsayi kuma gashi ta samu sai dai a banza don bata gaban shi "ya Allah kakka d'ora min son wannan bawan Allah a zuciya ta".


*****


6angaren Alamein kuwa har akaci aka sud'e bai lek'a gidan su ba saboda dama ba mutum ne maison shiga gurin harakar mata ba.


Yana shigowa gidan ya ci abinci daya gani a dinning table sannan ya shiga part d'in shi, wanka ya yi ya nemi guri ya kwanta da tunane-tunane fal a ranshi har bacci ya yi awon gaba dashi.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                    *(18)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



® NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



*WASHE GARI*

Bayan ta gabatar da sallah ne da abubuwan da suka dace tayi wanka ta shirya cikin atamfar ta kalar lemon green fitted.

    Bakin gado ta zauna ta zabga uban tagumi komi ya cunkushe mata, sai tunani take yi dama haka rayuwar auren take ko kuma nata ne yazo a hakan? Duk iya nazarin ta ta rasa gane wane matsayi take dashi a gurin Angon.


Jin hayaniyar mutane a falon ne ya sa ta janyo gyalen ta ta yafa ta fita, saboda tana tunanin Yusrah ce kamar yanda ta yi alkawari za tazo jiya.

   Tana fita karaf idon ta cikin nashi yana dariya k'annen shi sun saka shi tsakiya. Gabanta ne ya yi mugun fad'uwa saboda annurin fuskar shi daya kau cikin second uku.


"Laah Brother kace Amarya bata ta shi ba, ga shi har ta tsantsara kwalliya", da saurin Yusrah ta taro ta had'e da zaunar da ita, d'an zamewa ta yi k'asa ta gayar dashi, ya amsa ba yabo ba fallasa saboda k'in amsawar zai sa Yusrah ta dame shi.


Breakfast ta had'a mata da kanta tana tarairayar ta sa6anin Saudat dake binta da mugun kallo.

   Zumbur ya mik'e ya wuce part d'in shi saboda bazai iya kallon kayan haushi ba.


Bayan ta gama karyawa ne suka shiga hirar duniya ita da Yusrah har tana tambayar ta matsayin karatun ta.

   "Gaskiya iya primary school kawai nayi saboda na fi son islamiya akan bokon".


"No wonder! Biri ya yi kama da mutum", cewar Saudat.

   Harara Yusrah ta dinga zabga mata had'e da yi mata alamar gamon ki da Mum, sanin za su iya komawa ta gayawa Mum ya sa ta yi shiru, wayar ta ta fitar tana latse-latse.


Hakan ya tuna ma Yusrah maganar had'a ma Zajlah wayar ta, nan ta gaya mata taje ta d'auko wayar ta kawo mata.

   "Ina fatar kin saka charge". "Eh na saka tun jiya", ta ba ta amsa.


Wayar ce ta had'a mata har da layi biyu cikin kwalin wayar da credit, Mtn da Etisalat.

   Ba number kowa a wayar hakan ya sa Yusrah ta saka mata ta ta number data Mum, ko kad'an batayi gigin saka mata ta Saudat ba sai kuma number Alamein da ta yi mata saving da (HUBBY), lambar ta shiga kira sau biyu tana tsinkewa sai ana ukun kamar bazai d'aga sai kuma ya d'aga.


"Brother number Madam kenan". Bata jira me zai ce ba ta tsinke wayar, wayar ya bi da kallo had'e da furta "lallai yarinyar nan ta samu sake, don ma ta samu shekaranjia Mum ta ce nakar6i lambar ta mu rik'a zumunci shi ne za ta wani zak'ewa da baiwa wata lamba ta", za mu had'u ne".


Bayan ta nu na mata duk abinda ya kama ta tasani take gaya mata su shiga kitchen suyi girki tunda an kawo komai na amfani a store.

     Suna cikin girkin ne Alamein ya fito daga part d'in shi ya yi waje sai ga shi ya dawo falon had'e da Imran da Salis, sai wani dake aiki company dayace zai zo taya shi murna.

   Falon suka zube dukan su inda Saudat ta gayar dasu ta cigaba da latsar wayar ta.


A tare suka fito daga kitchen d'in ita da Yusrah, gyalen ta ta k'ara janyowa ta rufe jikin ta saboda wannan shi ne karo na farko da Maza za su ganta ba hijab a jikin ta, har k'asa ta durk'usa ta gaida su had'e da yi masu sannu da zuwa,  nan suka amsa cikin sakin fuska da walwala.

   Part d'in shi Yusrah ta wuce ta kawo masu ruwa da lemu, itako Zajlah ta koma kitchen domin k'arashe aikin.


"Tabbb da sallamo wata k'anshin girki yadoki hanci na sannan a kawo min ruwa da lemu, kawai abari in na yi lunch na danne da ruwan", Salis kenan sarkin barkwanci.

    Hakan suka kwashi dariya duka falon sa6anin Alamein dake wani cin magani.


Abincin suka jera ma su Imran a falon bayan sun gama, suka wuce da na su part d'in Zajlah saboda ta gayawa Yusrah ba za ta iya cin abinci gaban Mazan ba saboda bata saba ba.


Ba k'aramin dad'i Alamein ya ji ba da suka wuce part d'in ta, saboda a tunanin shi in har zai cigaba da ganin ta falon zuciyar shi za ta iya tashi  ya kasa cin abincin, don ko yanzu zai ci ne saboda tabbacin ba ita tayi girkin ba Yusrah ce.


Bayan sun gama cin abinci ne har da santin su suka tashi za su wuce, su Zajlah ne suka fito domin suyi sai an jima nan sukayi godiya suka ba ta kud'i wanda ta kasa kar6a saida Yusrah ta kar6a suka yi masu fatan alkhairi da d'orewar zaman lafiya.


Saudat ce ta ce su sauke ta gida ita ta gaji da zaman gidan, shi ma Alamein makulin mota ya d'auko domin suje tare tunda sun ce za su biya su gaida Dad.

   "Ai kai mun yanke ma fita har company sai nan da wata d'aya", inji Imran.


"Saboda ga mai laifi an yanke mai hukuncin gidan yari ba", cewar Alamein.

    Dariya sukayi sosai sannan suka fice daga gidan har Saudat d'in, akabar Yusrah da tace sai marece za ta koma, wanda hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Zajlah ba.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                   *(19)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


® NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


(My fan's na gode sosai da kulawar ku agare ni, way'anda suka kira ni da way'anda suka yimin magana private da kuma group duk na gaishe ku, ji na shiru kwana uku waya ta ce ta samu matsala, amma yanzu insha Allah za ku jini kamar kullum, love y'all)



      Hira suka shiga yi sosai ita da Yusrah, saboda gaskiya yarinyar ta yi mata ba tada girman kai irin na masu kud'i, kuma ga alama za ta girme ta kad'an.

    Tunani take tayi a ranta kan ta tambayi Yusrah asalin ya auren su yake ko kuma ta k'yale ta, saboda gaskiya har ga Allah abin na damun ta sosai.


Bayan sun yi sallar La'asar ne suka shiga kitchen domin girkin dare, duk da tana tunanin mawuyacin abu ne yaci abincin ta don tana tunanin k'ila ko d'azun bai ci ba.


"Me ya kama ta mu girka abincin dare?".

      Maganar ce ta dawo da ita daga hayyacin ta, ta kai duban ta zuwa gare ta ta sauke ajiyar zuciya.


"Me kike ganin yayan ku ya fi ra'ayi da dare d'in?, duk da ban tunanin in ya shigo zai ci abincin".


"Ko da wasa kar kiyi tunanin tunda ba shi yagan ki yace yana So ba za ki rage shi da wani abu na kyautata wa, a tunani na ta hakan ne za ki janyo hankalin shi zuwa gare ki".

     "Nasan ce wa watarana Brother zai yi alfahari da auren ki *ADALILIN GATAN* da Mum tayi mai. Saboda har kullum in dai namiji zai jure ya auri Mace ma'abuciyar ilmin addini to tabbas babu shi babu dana sani, yanda tarbiyar yara ke ta6ar6arewa yanzu ka samu mai d'ora yaran ka akan hanya ma abin alfahari ne".


"Amma yanzu abinda mutane basu gane wa musamman Maza har kullum burin su shi ne su auri Mace wayayya kuma y'ar boko, basu san ce wa da wayewar  waje k'ara ta gida ba".

   "Nasan matsalar Brother mai sauk'i ce, saboda shi kwata-kwata matan ne basu burge shi, asali ma ko taro ake yi muddin akwai Mata gurin bazai halarci taron ba, ni kai na da nake k'anwar shi ta jini sai shekaranjia ne Mum ta matsa mai ya kar6i lamba ta, kin ga ko irin shi bazai yi wuyar shawo kai ba tun da idon shi basu bud'e da soyayyar kowace Mace ba".


"Saboda haka ki dage ki janyo hankalin mijin ki, in zama ya yi dad'i za ku dace sosai da Brother, kar ki biyewa zugar k'awaye".


Hakan dai ta yi ta tsara mata irin abubuwan da ya dace tayi da way'anda basu dace ba har suka k'are girkin.


Zajlah ta kai duban ta zuwa ga Yusrah had'e da furta.

"Ni yanzu abu d'aya nake so ki samo min customers na d'inki tunda kin ga ba karatu nake yi ba sai dai zaman gida".


"Ba yanzu ba kam sai an gama kula da yaya na sannan, kuma ai ni ban tabbatar kin iya d'inki ba, kar in kwaso atamfofin k'awaye na ki yanka ba dai-dai ba Brother ko ya biya su", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta.


"Ke dai ki samo za kiyi mamaki".


Da hakan suka kammala ayukkan had'e da kimtsa gida sannan Yusrah ta yi haramar wuce wa, leda ta cika mata da kayan sha fa cikin na lefen ta, kuma ta had'a mata da dubu biyu cikin kud'in da su Salis suka ba ta, dak'yar ta karb'i kayan tayi mata godiya.


***  ***  ***  *** 


Alamein na shigowa gidan ko takan abincin bai bi ya wuce part d'in shi, duk da kamin ya fito daga gidan Mum ta yi mai nasiha dai-dai gwargwado kan kula da hakk'in yarinyar mutane wanda ya nuna mata zai yi insha Allah.


Sa6anin yanzu yana doso gidan ya ji gaba d'aya ranshi duk ya 6aci shiyasa ya k'i kula abincin ya wuce kawai. Kuma dama bai saba da cin abincin kowa ba sai na Mum, don ko yanzu sai da ya sa Saudat ta d'ebo mai abinci ya ci sannan ya fito.


***  ***  ***


Tana jin shigowar shi tana part d'in ta wata zuciya ke ce mata ta fita tayi mai barka da dawo wa, wata na ce mata kar kije ya maki wulak'anci.

    Gaskiya ba k'aramin fad'uwa gaban ta ke yi ba akan irin muguwar hararar da yake zabga mata. Da hakan ta yanke shawarar zaman ta d'akin ta, wanka ta yo had'e da alwala ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi addu'o'in ta sannan ta kwanta duk da irin tsoron da take ji.

    Tunani kawai take yi anya za ta iya biyar shawarar Yusrah kuwa?, saboda a tunanin ta ko kyautata wa mutum na tafiya ne da samun fuska, kawai dai ta yanke ma kanta in har ta ga fuska za taci gaba da kyauta ta mai, da hakan 6arawo bacci ya yi awon gaba da ita.


(To Zajlah asuba ta gari.)



®  *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(20)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



® NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


Sadiyajegal.WordPress.com



      Yau ta kama Alhamis dai-dai da kwanan ta biyar kenan a gidan Alamein, wanda sai ta wuni ta kwana basu had'u dashi ba, kuma har ko yaushe ta yi girki za ta ajiye mai sai dai yanda ta ajiye hakan za ta zo ta d'auke shi sai dai ta bayar sadaka wa almajirai.


Tun safe take hada-hadar tarbon k'awayen ta da suka yi mata alk'awarin kawo mata ziyara yau d'in.

   Tana gama ayyukkan ne ta yi wanka ta shirya cikin wata shadda brown fitted gown, ko minti biyar bata yi da shirin ba sai ga su sun zo su hud'u Salmat ce cikon ta biyar d'in su.


Hakan suka baje sai hirar makarantar suke ta zubawa, wanda a ciki ne suke gaya mata Ummulkhairi ce matar Ustaz Yusuf ya yin da Safiya ake maganar ta da Ustaz Lukman.

     Da la'asar ne suka ta shi wuce wa ta rik'e Salmat kan ce wa sai zuwa marece za ta wuce, da hakan suka fice suka bar ta. Hira suka dasa tsakanin su inda Zajlah ta kwashe yanda maganar auren ta ta kasance ta gaya wa Salmat, hak'urin nan dai da Yusrah ta ba ta shi Salmat ta ba ta had'e da nuna mata muhimmancin biyayya.


"Ni yanzu ba ma wannan ke damu na ba irin yanda zan yi in tafiyar Baba saudiya ta yi, saboda ko ganin shi ban yi barranta na in gaya mai zan je gida".

     "Hakan za ki jure gaskiya, kuma ki rik'a kula da gyara mai part d'in shi in har ya fita tun da ya zama dodon ki, Allah ni wannan in ni ce cikin wata d'aya zan gama dashi". Murmushi kawai Zajlah ta yi, da hakan suka yi girkin dare suka k'are.


Ba yanda bata yi ba kan Salmat ta tsaya har a gama magrib sannan ta wuce tak'i, "in ma na tsaya wa kika ajiye da zai kai ni in nayi dare? Ga wannan unguwar ta ku kuwar ka banza, ko misk'ilin mijin ki za ki sa ya mayar dani?".


"Ina nagan shi ni kaina barranta na insa ya mayar dake, ke dai ayi ta sha'ani".


Suna cikin hakan ne sai ga Alamein ya shigo gidan, saboda falo suke tsaye suna maganar za ta wuce.

    Ba k'aramin mamaki ya yi ba yanda ya jiyo maganar mutane a falon, saboda yau kwanan shi biyu ko motsin ta bai jiba, abincin da yake gani saman dinning ne ke ba shi tabbacin tana gidan, ba don hakan ba da yace ba mutum a gidan.


Ba don suna gab da k'ofa ba da ko sallamar shi ba za su ji ba, saboda iya la66an shi sallamar ta tsaya, gaida shi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa, Direct hanyar part d'in shi yayi, "am ji mana Malam".


Muryar ta daki kunnen shi cak ya tsaya ya juyo yana yi mata kallon raini had'e da 6acin rai tattare a fuskar shi na jin haushin Malam data kira shi.

     "Baban mu zai wuce saudiya zuwa jibi in kai bai da darajar da ko gaisuwar surukai kaje yi mai to y'ar shi na da buk'atar zuwa ta gana da mahaifin ta", cikin isa da gadara Salmat ke gaya mai maganar, don ita ba ta hak'urin wulak'anci.


Ba k'aramin k'ok'arin ta Alamein ya gani ba na tsaya ta gaya mai magana a gadaran ce, saboda ita ce Mace ta farko da hakan ta ta6a had'a su har ta dubi k'wayar idon sa ta so ka mai magana.


"Kin san ce maki aka yi da aka ta shi d'aura auren a k'afa ta aka d'aure igiyoyin uku akace duk inda zan fita tana manne dani da za ki ce min za taje gida, in ta iya ta biki kuje tare kar ta dawo gidan ba damuwar Alamein bace".

     "Wannan sunan ga alama kuskure akayi gurin rad'a ma shi, ina ga wanda aka k'udurta daban wannan ya fito a fatar baki daban, saboda kwata-kwata sunan bai dace da mutane irin ku ba".


"Amma ina mai baka shawara daka canja takon zamantakewar aure saboda in kai ba'a ta6a ganin ka aka furta ana son ka ba, to Zajlah har masoya sai da ta ture, ba'a kawo ma ita saboda rashin mashin-shi ni ba, darajar iyaye ka ci".


Ba ki sake ta barshi ta fizgi hannun Zajlah wacce ta zamo mutum mutumi tana kallon Salmat ta kasa ta6uka komai, falon suka bari don ta taka mata.


Sai da suka kai gate sannan ta ja ta tsaya, "yanzu ke har wannan namiji ne za ki tsaya shakkar tunkara don kina son fita?, Allah in ni ce wannan sai dai mu gasa juna wanda ya gasu shi zai yi bayani, kin ji ance in masara ta ji wuta ita ke fad'i".


"Allah ran da duk kika jibgu hannun mutane ba ruwa na, kinga haka ranar kika so kawa k'anwar shi magana".

    "Tabbb su jibga manya, ke ni fa zan iya d'aukar rainin hankali daga talaka d'an uwa na ban d'auka ga mai kud'i ba wallahi, saboda abin sai yayi yawa in kayi sake, don mutum bai ga uba na yawon maula gurin shi ba barranta na ya wulak'anta ni".


"Kuma yanzu kin ji da kunnen ki abinda ya furta, saura kar ki shirya kije ma Baba ban kwana, ni wallahi da ni ce to ya bud'e shafin yawo sai inda mai ya k'are".

    Sosai Zajlah ke mamakin rayuwar Salmat don kwata-kwata bata yo halayyar Mama Inno ba, don tun suna yara ba ta d'aukar raini.


Hakan ta sa kai ta fice daga gidan had'e da jadda da mata ce wa sai sun gan ta kamin wu cewar Baba.


**** **** *****


Fadeel ya shiga damuwa sosai saboda tabbatar da ya rasa yarinyar har abada, domin akan idon shi aka d'aura auren ta da wani, ya san ba k'aramar asara yayi ba saboda samun nutsuwa irin ta ta ga y'an matan yanzu abu ne mai wuya, da hakan ya hak'ura sai dai har kullum yana fatar samun Mace natsattsiya tamkar ta, Fadeel kenan da Zajlah ta yiwa nasiha da zai mari Mum.


Ustaz Lukman ma hakan ya yakice Zajlah daga zuciyar shi har ya furta wa Safiya k'awar Zajlah yana son ta saboda gudun yakuma nauyin baki.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:32 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(21)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


® NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


    Yau dai abinda ta k'udurta data gama girkin breakfast gidan Mum za ta je tayi mata wuni, hakan ya sa ta gama girkin ta cikin lokaci ko ta kan Alamein bata bi ba ta fice saboda sanin cewa yana company.

   Da shigar ta gidan Mum ke ta tarairayar ta, bata san ina za ta d'ora taba kan murna ita dai yarinyar ta yi mata har ga Allah don tana ganin mutuncin ta sosai.


Ganin cewa Mum ta shiga kitchen ne ya sa ta bi ta domin taya ta girki, "ai da kin koma falo kawai, saboda ba girki ne zan yi ba Daddyn ku ne kawai zan yiwa ferfesun kifi".


"Ba komai Mum kawo in d'ora". Hakan ta ba ta girkin saboda matsa mata da tayi kan ta ba ta, suna hira da mai aikin Mum ita ko tana aikin har ta kammala.


"Ni fa har yawu na sun tsinke da wannan girkin naki, duk gida ya d'auki k'amshi haka", cewar Mama Talatu.


"Kai Mama ai ban ma iya girki sosai ba saboda ko da na tashi gidan mu ban san mahaifiya ta ba sai mahaifi na, Mama Inno kuma bata cika ba mu girki sosai ba duk da mu ma ba zama muke yi sosai ba kullum muna islamiya".


"Duk da hakan na san zai yi dad'i gaskiya, don kin fi waccan sangartacciya da ko ruwan Lipton bata iya dafa wa ba sai d'an banzar girman kai da raina mutane".

    A rayuwar ta ta k'i jinin cin naman musulmi d'an uwan ta, saboda sanin illar hakan, duk laifin ka gare ta ba za ta iya zaman zagin ka a bayan idon ka ba.


"Allah ya kyauta Mama, a yita hak'uri. Wai ma ina Saudat d'in tun shigowa ta banji motsin ta ba?".


"Yanzu za ki gan ta tun da azahar ta yi, dama tana zuwa health makaranta, auren nan ne ya sa ta kwana biyu bata je ba".


Da hakan har ta kammala girkin ta fito falo, har k'asa ta durk'usa ta yiwa Mum sannu da hutawa, hannun ta ta rik'o ta zaunar da ita gab da ita. "Haba Zajlah har yaushe wai za ki daina jin nauyi na? Na gaya maki ki saki jikin ki tamkar kina gaban Mama Inno, ko Mama Asabe zance ne?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta.


Da hakan dai ta samu tana jan ta da hira har ta d'an saki jikin ta, nan Zajlah ke gaya mata tana so gobe taje gida yiwa Baban ta bankwana zai wuce saudiya jibi.


"Ba matsala Zajlah zan shirya gobe muje tare in ya so in baro ki can ki wuni ko, ina fatar kin gaya wa Son batun tafiyar Baban na ki?".


Tunawa da cewa jiya Salmat ta furta mai maganar ya sa tace' "eh Mum yasan da maganar".

   Tana shigowa falon ta yi turus ta tsaya tana wani shan k'amshi, da murnar ta ta taryo ta duk da tsorace take saboda gudun hantara, hannu ta mik'a ta kar6i litattafan da ta rungume had'e da furta "sannu da zuwa, ya makarantar?".


Yauwa ta furta a tak'aice, duk da taso yi mata wulak'anci ganin Mum ya sa ta yi shiru, don ta san ko ta sha giyar wake ba za ta fara ba. Littafan ta kar6a ta wuce d'akin ta, (ni dai Jegal da ido na bi ta saboda mamakin ko mahaifiyar ta bata gaida ba).


"Wai Zajlah ki na da ra'ayin makarantar boko ne ko ya ya?", "a ah Mum an ce boko da wuya kuma ni iya primary kawai na tsaya, sai dai ba laifi ina gane k'ananun abubuwa".

     "Kuma Mum ni yanzu d'inki kawai na sa gaba, in dai ina sa mu ba laifi nasan zan rage kewar wasu abubuwan".


"Au kice da mad'inkiya nake zaune, da fatar kin iya kar ki 6ata kayan mutane a tarar da Mum ranko", tana dariya take wannan maganar. Yanzu ta fahimci Mum na da dad'in zama ga kuma raha da take da, tabbas albasa bata yi halin ruwa ba.



"Mum hala Dad bai shigo ba?, yau yunwa nake ji sosai wallahi, ko break ban yi ba a skul".

 

"Kira shi kiji in ba yanzu zai shigo ba sai kici na ki, kin san yau ko yayan ki nan zai ci abinci tunda ga matar shi nan gidan".

    Jin cewa Brother zai zo gidan ya sa ta hak'ura har sai da suka dawo. A tare suka shigo gidan wanda ya sa ya yi turus ya bi ta da kallon mamaki, sai kuma ya basar ya k'araso cikin falon, don dama ko ta kan gidan shi bai bi ba ya yo gidan saboda ya samu abinda ya ci.

   Durk'usawa ta yi ta gaida Dad sannan ta yiwa Alamein sannu da zuwa, Dad ya kar6a ba yabo ba fallasa sa6anin Alamein dake yak'e wanda ya fi kuka ciwo.


Falon Dad suka wuce saboda nan ne gurin cin abincin su, sa6anin Mum data tsaya suje tare da Zajlah aci abincin, inda ta nuna ma Mum ak'oshe take duk da yunwar da take ji tasan da nauyi taje cin abinci da surikin ta, duk da ta hango su a gurin su ba komai bane, kuma ita ma da tana gida tare da Baban ta take cin abinci.


Tsinkayo muryar Mum tayi tana ba Talatu umurnin ta had'a abinci ta kai mata falon ta. Hannun ta ta rik'a ta kaita falon ta, sai da Talatu ta kawo komai sannan ta ba ta umurnin taci abinci kamin ta dawo, da hakan ta fice zuwa falon Dad.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:32 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(22)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITER ASSOCIATION*



  Falon Dad ta koma ko da ta shiga har sun gaji da jiran ta sun fara cin abincin sai santi suke yi, guri ta samu ta zauna ta saka abincin ta fara ci.


"Mum baki ta6a ferfesun kifi da ya kai na yau dad'i ba, ga shi ya ji garlic sai k'amshi ke tashi".


"Kawai Son ka fito ka gayan cewa matar ka ta fini iya girki, shiyasa har gaba na kake kasa hak'uri sai ka yabi girkin ta". Cak su duka suka tsayar da cokulan su daga cin abincin, kallo ya koma gurin Mum, Dad ne ya kasa hak'uri ya furta.


"Yanzu kina nufin wannan mitsitsiyar yarinyar ce ta yi wannan girkin?, lallai Son kana kwasar ragwada, sai dai har yanzu banga ka fara kaurin wuya ba". Yana maganar yana Shafa wuyan shi alamar tsokana.


Shi dai kawai basar da abin ya yi yana dariya yana nok'e kai, sai tunani yake yi ashe kan shi yayi wa da baicin abincin ta.


"Gobe ma zanje gidan su yarinyar saboda mahaifin ta zai wuce saudiya, don haka kai ma Son ka shirya don kai za ka kaimu gobe d'in ni da ita".

   Ji yake yi tamkar yafasa ihu saboda yanda Mum ke son kusancin shi da yarinyar, shi ko har ga Allah ko ganin ta bai son yi, hakan dai ya kar6a ba don ran shi ya so ba.


**** **** ****


6angaren Zajlah kuwa abincin ta ci sai da ta k'oshi sannan ta kai kayan abinci kitchen, d'akin ta dawo ta hau gyaran shi duk da ba wani gyara ne a d'akin ba, har toilet ta wanke ta shimfid'a sabon blanket ta feshe d'akin da air fresheners sannan ta dawo falon ta zauna, don jin take yi ba ta da ra'ayin fita falon gidan saboda kar ta had'u da Alamein.


Tun daga k'ofar shigowa falon wani dadda d'an k'amshi ya tarye ta, ko da ta shigo falon ta gan ta kwance saman 3sitter barci ya yi awon gaba da ita. D'akin Mum ta za ga ko ina fes dashi sai k'amshi ke ta shi, a ranta take ta saka ma Zajlah albarka had'e da hango alkhairin da ke tattare a cikin auren.

   Sai la'asar Mum ta ta da ita ta gabatar da sallah ta kuma fad'awa kitchen suka yi girki ita da Mama Talatu, bata wani samu sakin fuska daga Saudat ba shiyasa take mak'ale da Mum ko Talatu.


Har k'arfe 09:00pm ba  labarin Alamein ba bu alamar shi, kuma wayar shi ma ta k'i shiga dole direba ne ya maida ta duk da ba nisa da gidan sai dai shirun unguwar.


Kulolin abincin da ta zo dasu ne ta ajiye a falon ta wuce part d'in ta, saboda ba yunwa take ji ba sai da ta ci gidan sannan ta fito.


*******


Alamein kuwa da gayya ya k'i ko ma wa gidan, saboda yasan da ya je dole shi zai dawo da ita gidan, sanin cewa Mum za ta iya ne man shi a waya ya sa ya kashe ta duka. Akan idon shi ta shigo gidan ta ajiye abincin sai da ya tabbatar ta shige sannan ya fito ya ci abincin ya ko ma d'akin shi.


Kwata-kwata bai son abinda zai janyo alak'ar had'uwar su ko da ta second biyu ce, kwance ya yi yana ta tunanin yanda wai kamar shi za'a yi mai auren dole, don bai ga abin so ga Mace ba.

   Wasu lokuta in har yana tuna lokacin degree d'in shi yanda friends d'in shi ke rud'ewa in suka ga Mace abin har haushi yake bashi over, don ganin yake yi rashin abinyi ke sa ka 6ata lokacin ka ga Mace.


In har bai manta ba akwai lokacin da wata Lubna ta mak'ale mai tana bibiyar shi wanda shi ba ta ko gaban shi, ranar ta tarar da shi zaune dasu Imran kawai ta rungumoshi wait gaisuwa ce, marin da ya kifa mata ne ya dawo da hankalin tsirarun mutane dake gurin nan take aka ta mata dariya tun ranar bata k'ara kula shi ba, da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba dashi.


(Alamein asuba ta gari inji Jegal, _lolx_.)


***  ****  ****


*WASHE GARI*


Misalin k'arfe *11:00am* Mum ta kira Alamein kan cewa ya d'auko Zajlah ya biyo ya d'auke ta su wuce, rasa ina zai saka ran shi ya yi ta yanda zai gaya wa Zajlah ta shirya su wuce d'in, wata dabara ta fad'o mai take ya lalabo lambar ta da Yusrah ta kira shi da ita.


Text message ya tura mata kamar haka ( *ki fito Mum na jiran mu*).


Ta dai ji wayar ta ta yi k'ara kuma ta d'auko taga alamar abu a sama amma bata gane miye ba, saboda bayan saving number da call ba abinda Yusrah ta ko ya mata, asali ma bayan Yusrah da Mum ba wanda ya ta6a kiran ta a waya. Ba sarwa tayi kawai ta fad'a wanka.


Bayan ta fito ne ta kimtsa tana zaune saman mirror tana taje kanta aka banko k'ofar d'akin da k'arfi wanda sai da ta razana da sauri ta zabura. Gashin kan ta ya kama da k'arfi ya fizgo cikin rinannun ido yake nuna ta da d'ayan yatsan.


"Ke wace irin dak'ik'iya ce da zaki banzatar da ni a mota fiye da minti ashirin?, waye bawan ki ko wa kika ajiye?, kinsan ba don darajar Mum ba wallahi baki yi darajar ko da takalmin Alamein su ta ka wannan k'azamiyar unguwa ta ku ba".


Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta ga shi har lokacin yana rik'e da gashin kanta. Wayar shi da Mum ta k'ara kira a karo na uku ya sa ya sake ta had'e da kai mata muguwar harara.


Nan ya d'aga kiran had'e da ce mata ga sunan zuwa, cikin tsawa ya ce mata "fice muje banza kawai dak'ik'iya".


Hijab d'in ta ta janyo daga saman gadon ta saka suka fice wanda har lokacin hawayen idon ta basu kafe ba.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:32 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(23)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



    Gaban motar ta je shiga saboda gudun ta zauna baya yace ta mayar dashi direban ta, ashe duk da hakan bata tsira ba harara ya bi ta da ita had'e da furta "baki yi matsayin da zan zauna gaban mota ni da ke ba sai dai ki koma baya, jahilar banza kawai".


Sum-sum ta ko ma bayan mota ta takure sai zuciyar ta ce ke mata wani tuk'uk'i. Da hakan har suka iso gidan, Mum ta fito sai dai ta ce dole Zajlah ce za ta shiga gaba ita ko ta zauna baya, akan ta matsa ne ya sa ta fito had'e da durk'usawa ta gaida ita.


Tallafo ta ta yi cikin sauri had'e da tallafo ha6ar ta sai ga hawaye shaaa, "me ya same ki Zajlah? Son ne ya 6ata ma ki rai?", duk cikin rud'u take tambayar ta.


Kai ta girgiza alamar ba komai, "haba Zajlah yau fa ranar murna ce gare ki za ki je gida kiga iyayen ki, ni da na zata ina fitowa inga bakin ki har kunne kan farin ciki" murmushi ne d'auke a fuskar ta alamar zolaya.


Hakan ya saka Zajlah ta d'an murmusa "Mum fa ba komai ina d'auko hijab ne zan saka naji abu ya fad'a man a ido, kuma na duba banga komai ba sai wani zafi da nake ji a cikin idon".


Sannu Mum ta mata had'e da saka bakin ta ta bushe mata idon sannan ta rik'a hannun ta ta saka ta gaban motar ta rufe sannan ta shiga baya ta zauna.


Unguwar su Zajlah ya nufa wato Birnin yari, ran shi 6ace sai wani cin magani yake yi, har suka isa ba wanda yace uffan har Mum d'in saboda kowa da abinda yake sak'awa a ranshi. Sai dai tunanin Mum har yau babu wani cigaba tsakanin zaman takewar su kawai Zajlah na 6oye mata ne, lallai tabbas yaro man kaza.


Da hakan suka iso gidan inda Zajlah bata ko jira su ba ta fad'a gidan su Salmat, Mama Inno ta tarar zaune tsakar gida tana gyaran wake, saman ta ta fad'a tana razgar kuka wanda ya sa ta kayar mata da gaba.


*********


A can 6angaren Alamein kuwa Mum na fitowa daga motar ya je zuwa juya akalar motar shi ya koma gida Mum ta bishi da harara.


"In ita gidan za ta wuni sai aka ce ma ni ma nan zan wuni?, wato ka fi k'arfin ka fito mu shiga ka gaisa da mahaifan yarinyar nan ko?, wai kai sai yaushe ne za kayi karatun ta nutsu a rayuwar ka?". Cikin 6acin rai ta kama hanyar shiga gidan ta bar shi, dole ba don yana so ba ya rufe motar ya mara mata baya da handkerchief saman hancin shi yana yatsinar fuska tamkar Wanda ya shigo cikin jeji.


*******


Mama Inno ta tallafo ta had'e da jera mata tambayoyin meke faruwa wanda amsa tak'i fitowa sai dai ambaliyar hawaye.


Suna hakan ne sai ga Mum ta shigo gidan da sallamar ta had'e da murmushi a fuskar ta, hakan ya sa Zajlah ta fad'a d'aki.


Shimfid'a Mama Inno ta yi masu had'e da yi masu kyakkywar tarba cikin fara'a da sakin fuska, Mum ta furta "kin ga y'ar tawa da sangarta muna kawowa k'ofar gida tana fasa kuka, ita da ya kama ta yau ta zamo cikin walwala baki har kunne", cikin zolaya Mum ke furta maganar.


"Yo ai kad'an kenan daga aikin Zajlah, ba dai shagwa6a ba har dai in tana gaban Baban ta".


D'agowar da Mum za tayi ta ganshi k'erere saman kan ta, muguwar hararar da ta zabga mai ya sa ya janye handkerchief d'in da ya toshe hanci dashi, sannan ya d'osa na gefen ta ya zauna tamkar mai tsoron zama saman allura.


"Mu shiga can wurin Mal Abu d'in?". Maganar tace ta dawo dasu hayyacin su su duka biyun. D'aki ta shiga ta d'auko hijab had'e da sako Zajlah gaba suka shiga gidan na su.

    Nan aka gaggaisa inda suka tarar Baban ta bainan yana gurin Sana'ar shi ta kayan gwari, Mama Inno ce ta fita ta samu yaro don yakiro su Mal Abu.


Cikin minti goma sai gashi sun iso, nan dai aka gaisa suka yi mai Allah sanya alkhairi da fatar zuwa lafiya adawo lafiya. Dubu ashirin Mum ta ajiye sannan ta yiwa Alamein alama da ido yaba da nashi, hannu ya saka gaban rigar shi ya kwaso kud'in da shi kanshi baisan nawa ne ba ya ajiye, saboda a matse yake da subar gidan.


Shi ya fara ficewa sannan Mum ta kai duban ta ga Mama Asabe tace' "ga y'ata nan ku kulamin da ita zuwa dare Son zai dawo yaje da ita", cikin jin dad'in irin kulawar da Mum ke bata Mama Inno ta furta "za ki samu y'arki lafiya in ma murnar ganin Baban ta baisa ta k'ara k'iba ba".


"Ai ko in hakan ta kasance zanfi kowa murna da farin ciki".


Da hakan dai suna ta walwala Zajlah ta raka Mum har gurin mota sannan ta dawo gidan.

    "Zo nan Zajlah inga me ke damun ki, na ga idon ki sun kumbura". Kusa dashi taje ta lafe tana wani zuba shagwa6a.


Mama Inno ce ta kar6e da cewa "wacce ta shigo da kuka gidan har ta kayar min da gaba, ashe duk tsabar shagwa6ar zuwa gida ce", nan dai suka ta tsokanar ta ita ko sauraren su kawai take yi.


***** ****


6angaren Alamein kuwa har suka kai gida fad'a Mum take mai kan abubuwan da yake yi marar dacewa musamman ga sirikan sa, tun tana fad'an har ta dawo rarrashi tana mai nuna mai irin yanda Zajlah ke mutun ta ta bai dace ya wulak'an ta na ta iyayen ba.


Zurum ya yi yana sauraren ta tamkar mai d'aukar darasi, (ni dai Jegal na ce Allah yasa maganar Mum ta shiga kunnen ka Alamein).



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:32 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                 *(24)*



*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


www.sadijegal.blogspot.com


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


*04:30pm*

Lokacin Salmat ta dawo daga islamiya saboda yanzu ta daina zuwa ta marece da safe zuwa la'asar take dawowa gida. Tana shiga gidan ta ci karo da Zajlah je kaga murna tsakanin su tamkar sun dad'e basu had'u ba, d'aki suka fad'a aka bud'e shafin hira.


Bayan sun gaisa ne Salmat ke ce mata "ina gadararren mijin ki?, ina fatar kin fara gyara mai zama yanzu?".


"Hmm! Bari ke dai Allah ya had'a ni da miji marar tausayi, ai ni wannan auren nan kallon auren k'addara nake yi mai", nan dai ta kwashe yanda zaman su yake da yanda ya yi mata d'azun ta gaya mata.


"Tabbb sai kika tsaya kallon shi gashin ki ya zamo linzami agare shi, wai ke wace irin Mace ce?, ni fa in mutum ya siyi mutunci wallahi zan nuna mai nice na raini mutuncin har ya girma, sa6anin ka nuna min rashin mutunci in nuna ma cikin shi nayi na haife shi".


"Salmat ya kike so na yi ne?, wallahi ko Mum ban iya gaya wa irin zaman da muke yi dashi, nasan komai yayi farko zaiyi k'arshe watarana sai labari".


"Lallai ko yarinya za ki zama goro ko abin saye, tunda kin za6i siyar da farin cikin ki ga wanda bai san darajar d'an Adam ba".


"Ko dai ba za ki rama abinda yake maki ba to kiyiwa kanki gatan rashin d'aukar raini, saboda in kince ba za ki motsa to kin zama shara kenan duk abinda ya d'auko zai sauke shi saman kan ki".


"Ni fa kinsan ko Mace y'ar uwa ta ban iya sa'insa da ita bare namiji, don haka kawai ki taya ni addu'a ita ce kawai mafita gare ni".


"To Allah ya kyauta kuma ya dasawa Alamein bala'in son ki a ranshi". Suna had'a ido ta yi mata gwalo tana dariyar k'eta.


Da hakan dai suka rik'a hira wanda Salmat ta so ta lurar da Zajlah muhimmancin k'watar y'ancin ta ga Alamein amma abin ya ci tura.


D'inkin da aka ba ta na ashobe ta kwaso kusan turmi goma sha biyu ta jibge ma Zajlah had'e da furta "ga d'inki nan kije dasu kiyi ko za ki rage nisan gadin gida, gobe nake so in ba Sagiru su ya kai maki ki ragen aiki".


"Zan dai d'auki goma inje dasu, sauran kuma kya k'arasa tun da ke kika yi had'ama kika kar6i kayan mutane".


"Yi hak'uri matar Alamein, uwargida kuma amarya daga ke babu k'ari".


Share ta kawai ta yi ta fad'a kitchen domin kama ma Mama Asabe girkin dare, ita ko ta fice gida tana mata dariyar shak'iyan ci.


*** *** *** ***


Babu abinda yake tunawa ran shi yayi mugun 6aci sai tunanin komawa d'auko waccan kucakar yarinyar da Mum ta mak'ala mai.

   Tabbas ba abinda Mum za ta sa shi ya kasa yi mata, kuma yaji fad'an da tayi mai d'azu sai dai ranshi ke 6aci ko yarinyar ya tuna da ita.


Murmushi yayi sosai saboda samun mafitar ba sai ya je d'aukar Zajlah ba kuma abinda zai yi Mum ba za ta ta6a sani ba.


***  ***  ***


Kud'i Zajlah ta fitar dubu goma ta bawa mahaifin ta inda dak'yar ta samu ya kar6i kud'in, a cewar shi na mijin ta da Mum sun isa, duk da hakan sai da ya tambaye ta inda ta samu kud'i.


"Baba abokanen shi suka bani dubu ashirin cikin su na ba ka goma na ajiye sauran saika dawo in yima dafuwa". Murmushi ya yi dajin dad'in yanda take kula dashi tun bata kai hakan ba.


********


*09:00pm*


Aka aiko daga waje wai anzo d'aukar Zajlah, kayan ta ta had'a hadda d'unkunan da Salmat ta jona mata, har da guntun hawayen ta na rabuwa da Baban ta.


Salmat ce ta d'auko mata kayan ta domin ta taka mata daga nan ta wuce gidan su, da biyu ta yi rakiyar saboda tana so Alamein ya yiwa y'ar uwarta ba dai-dai ba a gaban ta tayi mai tasss, sai dai sa6anin hakan suna fita suka ganshi jingine ga mota da fara'ar shi kamar kullum.


"Ustaziya barka da fitowa", Salis kenan yaro mai kamala da ganin mutuncin manya. Nan suka gaisa har yasa Zajlah ta kira mai Baban ta su gaisa, ko da ta dawo hira ta 6arke tsakanin shi da Salmat domin hali ya zo d'aya kowa akun kanshi ne gurin surutu.


Har k'asa ya durk'usa ya gaida Baba had'e da yimai fatar alkhairi, shi ma kan shi kud'i ya ba Baban suna ta yimai godiya. Mota ya bud'e mata ta shiga ya kai duban shi ga Salmat "to sai na ganki alhamis d'in banda karya alk'awari".


Cikin jin kunya Salmat ta shige gidan, shi ko ya shiga motar ya ja suka fice. Mamaki ne fal a ranta, lallai ta tabbatar da Alamein bai san darajar aure ba, wato ya fi k'arfin yazo d'aukar ta sai dai yaturo abokin shi, irin haka ne shaid'an ke samun kutsawa zuk'atan masu raunin imani sai daga baya azo ana fad'in wane da matar abokin shi yake mu'amala alhali abokin ne ya bashi wannan damar.


(Allah ka tsalkake mana zuk'atan mu ka k'ara mana k'arfin imani, kasa mufi k'arfin zuk'atan mu).



® *🇸DY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:33 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*


                  *(25)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


sadiyajegal.WordPress.com


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



       Har suka kai gida ba wanda yace da wani uffan, kowa da abinda yake sak'a wa a ranshi, fitowa tayi daga motar bayan maigadi ya bud'e masu gate sun shiga godiya ta yi mai sannan ta nufi hanyar shiga falon da kayan ta Salis ya rik'o mata wasu.

  A falon suka tarar da shi zaune yana kallo yana latsar waya, part d'in ta ta wuce ta kai kayan sannan ta dawo d'aukar na hannun Salis, abinda ta ji ne ya sa ta ja birki ta tsaya.


"Yanzu don Allah A.K.A abinda kake yi a tunanin ka ya dace?, don kawai kar kaje d'auko yarinyar nan sai ka kira ni kace inje in d'auko ta wani aiki kake yi kallon ne aiki ko kuma chart da kake yi?".


"Salis ya kake so inyi da rayuwa ta ne?, ka duba kaga yanda damuwa tayi min yawa, abubuwa duk sun ja baya, ko company sai ku ne ke kula dashi".


"Wallahi in na ga yarinyar nan har wani k'unci ke ziyartar zuciya ta, na rasa ina zan tsoma kaina inji sanyi".


"Hak'uri za kayi, muzgunawa yarinyar tamkar rashin bin umurnin Mum ne, kuma ni banga illar Zajlah ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa, don Allah ka sassauta mata dame za taji? Auren dole ko rashin bata kulawa da baka yi?".


"Ko ma miye ita taja wa kanta, da ace da Mum taje da buk'atar neman auren tace ba taso ai da ta hutar da kan ta, to nasan kwad'ayi ya kawo ta shiyasa".


"Ai ko da kaga iyayen ta kasan mutane ne masu wadatar zuci da neman na kansu, kwata-kwata wannan abin bai dace ba wallahi".


Ganin cewa baza ta iya jure sauraren maganganun ba yasa ta fad'a falon ta yiwa Salis sai da safe ta kwashi kayan ta ta koma part d'in ta.


"To yanzu duba don Allah alama ta nuna ta ji me kake fad'a, kasan dai ba dad'i".


"Kai ni fa ko a gaban ta zan furta abinda nayi niya don ba tsoron ta nake ji ba".


   Ganin in ya yi gabas yayi yamma ne yasa ya yimai sai da safe ya fice daga gidan rai 6ace da halayya irin ta A.K.A.


*** *** ***


6angaren Zajlah kuwa tana shiga d'akin gado ta fad'a tana ta razgar kuka cikin damuwa da tsananin 6acin rai. A rayuwar ta bata ta6a saka ma ranta auren mai kud'i don taci kud'in shi ba, asali ma tafi hangen auren rufin asiri ta samu talaka d'an uwan ta da zai san darajar ta da k'imar ta, saboda yawancin masu kud'i basu cika d'aukar talaka wata tsiya a doron k'asa ba.


Hakan ta ci kukan ta har ta gode Allah ba mai rarrashi. Alwala ta yo ta yi sallah had'e da kaiwa Allah kukan ta kan yakawo mafita acikin wannan aure na ta, bayan ta gama ne ta dunk'ula ta kwanta had'e da tunani iri-iri har bacci ya yi awon gaba da ita.


*** *** ***


*WASHE GARI*


Bayan ta gama sallah ne ta kimtsa d'akin ta, wanka ta yi ta shirya sannan ta nufi kitchen tea ta had'a iya cikin ta sai k'wai biyu data soya, bayan ta karya ne ta koma d'akin ta ta kwashi turamen da tazo dasu ta nufi d'ayan k'aramin d'akin da aka saka mata keken d'inkin ta da sauran komatsan ta, zaune ta yi ta fara yankan d'inkin sai da ta yanka turmi hud'u sannan ta hau keken ta fara.


*** *** ***


6angaren Alamein ko yana dosowa falon k'amshin wainar k'wai ta doki hancin shi, sai dai yaja ya yi turus da yaga dinning table d'in wayam sa6anin kullum da yake tarar da girki a gurin.

   Yau har ga Allah yaso yaci girkin ta kodon fad'an da Mum ta yimai ce wa kar yadawo gidan ta cin abinci in har ba matar shi ce taje mata wuni ba da tasan cewa babu mai bashi abinci ba. (Tabbb ni dai Jegal nace jin dad'in ferfesun kifi ne yasa Alamein zai la6a da fad'an Mum ya kwashi girki, sai ga shi ran Zajlah ya 6aci yau bata ajiye ba, lolx).


Zaune ya yi turus a falon yana tunanin mafita, ga shi yana so yaje office cikin lokaci saboda wani meeting da zasu yi da wasu dasu ke da share a company d'in. Ga shi shi ba gwanin girki ba don ko ruwan Lipton bai iya dafawa ba.


Kitchen ya fad'a ya yi sa'ar ruwan lipton har sun fara hucewa, hakan ya zuba madara da sugar kad'an ya sha ya fice daga gidan.


*** *** *** 


Zajlah ko na can na fama da d'inkin ta, har wani nishad'i take ji na ganin ta samu abinda zai rage mata damuwa, don har ga Allah ta manta wani 6acin rai data shiga jiya.


Jin cikin ta na k'ugi ne ya sa ta ajiye d'inkin ta shiga kitchen macaroni ta yi jallof d'inta da dama ta saka a kula ta d'auki plate da cokali ta koma d'akin.

   Bayan ta zuba ta ci ne ta tsinkayo kiran azahar, nan ta yi sallah sannan ta hau d'inkin ta.



® *🇸DY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:33 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(26)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*

 sadiyajegal.WordPress.com



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Kwanaki hud'u sun shud'e ba wani cigaba tsakanin zaman Alamein da Zajlah sai ma abinda ya k'arasa kwa6e wa, don yau kusan kwanan su biyu basu had'u da juna ba.

  Alamein ya fara shiga takura saboda ga shi ba gwanin yawon restaurant ba, asali ma yana iya cewa tun tashin shi bai ta6a cin abincin waje ko na wani aure ba sai dai na gidan su. A hakan yake buge-bugen shi in ya fita office yasha lemo da biskit, sai kuma maltina rabon shi da abincin kirki tun ranar da Zajlah ta wuni gidan Mum.


**** **** ****


Yau tun safe ta taya Mama Inno aikin gida saboda tana so taje gidan Zajlah, k'arfe *11:00* ta gama kimtsawa ta shiga gidan su Zajlah ta ja Naja'atu domin ta raka ta, saboda tun auren Zajlah ba ta jin dad'in fita ita kad'ai.

  Naja'atu y'ar k'anen Mama Asabe ce mai kimanin shekara tara a duniya, tun auren Zajlah Mama Asabe ta ji gidan ya yi mata shiru dayawa ta shawarci Mal Abu ta d'auko yarinyar ta dawo hannun ta da zama.


Keke napep suka samu suka shiga sai G.R.A, gidan su Alamein ta fara shiga ta gaida Mum saboda karamcin dattijuwar, da murna ta tarye ta kamar ta had'iye ta, nan suka had'u da Yusrah ita ma ta zo ma Mum hutu kwana biyu.


Tare suka rangad'a sai gidan Zajlah har Mum na mitar Yusrah ba ta gajiya da zuwa wurin Zajlah, basu had'u da Saudat ba akan tana makaranta.


*** *** ****


Zaune take saman tela ta duk'ufa d'inkin saboda yau take so ta k'arasa ta samu ko d'an mak'ociyar ta ne Shema'u ta aika yakai wa Salmat d'inkin, saboda Salmat ba ta da waya haka ma iyayen mata, su Mal Inuwa ne kawai suke da kuma Baban ta ya wuce saudiya kwana biyu da suka wuce.


Jin sun shigo falon ne tsit ya sa direct suka yi part d'in ta, ganin su ba k'aramin farin ciki ya saka ta ba, da gudun ta ta rungume Salmat ta saki ta rungume Yusrah sannan ta saki baki tana kallon su.


"Daga ina kuka had'u haka ba sanarwa sai dai ku diro ma mutum ba shiri?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta.


"Allah ne kawai ya had'a mu don mu d'ebe maki kewa yau, Mum na shiga gaidawa na tarar da ita a gidan".


"Ai ko gaskiya na ji dad'i sosai da ganin ku", hannun Naja'atu ta rik'o had'e da tambayar ta lafiyar gida, yarinya mai surutu ta yita zubawa har da bata labarin da Baba zai wuce su Mama da Anty Salmat har da kuka suka yi, dariya sosai yarinyar ta basu yanda ta zak'e tana bada labari da kwatan ta yanda su Salmat suka yi.


D'inkin Yusrah ta janyo tana dubawa had'e da furta "anya Sis ke kika yi wannan d'inkin?, ko wata ke zuwa tana taya ki?", cikin zolaya take maganar.


"Tabbb ka ma kan ki ai wannan oga ce a gurin d'inki, tare fa muka fara koyon d'inkin amma yanzu ko wacce ta koya mana ta wuce ta musamman breast cup tamkar ta auna su".


"Kai Salmat ki rage sharri fa, ni dai kawai d'inki ke birge ni shiyasa na mayar da hankali na iya".


"Kin manta ana gab da auren ki da muka je gidan Zainab mai d'inki muka tarar ta saka wani style gaba ta zuba tagumi akan ta kasa had'a shi sai da kika kar6a kika had'a?".


"Na tuna uwar k'wakk'wafi". Keken ta hau ta k'arasa had'a rigar sannan suka koma d'ayan d'akin a falon ta, lemo da ruwa ta kawo masu sannan aka zauna dasa wata sabuwar hira.


"To ku tsaida hirar hakanan kuje kitchen ku ne ma mana abinda za muci, saboda ni dai na gaji bazan iya girki ba".


Salmat ce ta bi ta kallo had'e da "furta matar nan dad'i ya maki yawa, mu da muke bak'i mu za mu ne mawa kan mu abinci, to tsaya ma da bamu zo ba waye zai dafa maki?".


"Manta kawai barta ta huta, nasan gajiya biyu ce saman kanta ga ta Brother na, ga ta keken d'inki", tana maganar had'e da kashewa Salmat ido d'aya.


"Ku dai kunga bone wallahi, tahowa zanyi in gayawa su Baba duk ayi maku aure, saboda na fahimci inda kuka dosa".


"Kai rufa mana asiri, mu fa yanzu ake renon mu komai bamu sani ba", cewar Yusrah.


"Shi ne naga da rarrafe kuka zo gidan nan k'arewar raino, ku dai yi sauri ku fitar da Maza musha shagalin biki".


Salmat ce ta furta "ni kam bazan yi aure ba sai kin haihu hud'u tukuna", 

  "Tunda haihuwar kashi ce, wallahi da kin shiga uku in na haihu hud'u kina gida, Allah sai dai mu bada ke sadaka koda a lima mai ne".


 Dariya suka yi sosai nan Yusrah ta kama hannun Salmat suka fice zuwa kitchen domin samun abinda suka girka. Ita ko Naja'atu ta janyo tana ta ba ta labari sai dariya take yi, ji take yi tamkar farin cikin ta yad'ore hakan.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:33 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(27)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


Suna tashi daga office ya ce ma Alamein suje yau gidan shi zai je duba ajiyar shi, jin hakan ya sa Imran yace shima baza'a barshi a baya ba.


Hakan ta sa suka d'unguma su duka suka biyo shi, wanda sai fargaba yake yi in ba abinci za suje ci ba, duk da babu abinda basu sani a zaman takewar su ba, sai dai yanzu yana jin nauyin suje gidan ba su da abinda zasu ci.


Dabara ce ta fad'o mai na kawai ya nuna masu zai biya gurin Mum yakai mata sak'o, saboda sanin in dai daga office suke direct suka yi gidan to abinci ne na farko da Mum za ta tarye su dashi.

     Sai dai kash ba yanda bai yi ba Salis ya kafe kan cewa shi fa sai ya je yaga ajiyar shi sannan in zasu wuce su biya su gaida Mum d'in.


*** *** ***


Abinci suka yi kusan kala uku suka saka a kuloli, saboda cikin su ba wanda yasan cewa ta daina yin girki da Alamein, asali ma Salmat ce ta sa ayi girkin haka a cewar ta gidan Amarya har kullum bai rasa bak'i.


Bayan sun k'are girkin ne suka kimtsa gurin sannan suka koma falon ta, abin dariya ko da suka shiga Naja'atu na ta zuba bata lura da Zajlah ma bacci take yi ba.

   Dariyar su ce ta tayar da ita daga baccin da ya d'auke ta, zama suka yi suna dariyar ta suna furta "neman kud'i da wuya yarinya".


"Ai ni ba kud'i ne nake nema ba, rage zango ne nake yi saboda ban aikin komi".


"Ashe in aka bada kud'in wannan d'inkin in d'auka kenan", cewar Salmat.


Yusrah ta ce' "Sis ni ma zan kawo customers kwanan nan tunda na ga ke expert ce a 6angaren d'inki". Hararar su kawai ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka.


Bayan ta fito ne ta kimtsa Yusrah ta saka ta gaba da cewa sai ta yi mata kwalliya don tasan yanzu Brother bai nesa da dawowa, hakan ta saka ta gaba ta yi mata make up had'e da wani nad'i tamkar an d'aura gwaggwaro. 


(Saura k'iris waya ta ta su6uce ta fad'i, sai dai na rik'e ta gam saboda gudun rasa wacce zan kawo maku rahoto, tabarakallah ahsanul khalik'een kawai nake na natawa, _lolx_).


Baki Salmat ta saki tana kallon Zajlah had'e da furta "lallai make up na fitar da 6oyayyen kyau, to ni ma ba za'a barni a baya ba azo a tsantsara min tawa".


*** *** ***


Da dosowar su gidan k'amshin abinci ne yatarye su, mamaki fal a fuskar Alamein sai dai kawai ya dake kuma ya basar.

   Falon suka shiga sai dai wayam ba kowa sai dariyar su ce ke tashi daga falon Zajlah. Masauki suka yiwa kansu suka zube a falon.


Hayaniyar da suka jiyo a falo ce ya sa Yusrah ta lek'o, da d'an sauri saurin ta ta iso falon tana mai fad'in "oyoyo Brother na", cikin sakin fuska ya amsa ta sannan ta gaida su Salis.


D'akin ta koma ta gaya masu wanda Zajlah kamar kar ta fito sai dai mutuncin su Imran gare ta sun wuce ta yi masu haka, gyale ta janyo ta yafa sannan ta tunkaro hanyar zuwa falon.


Duk zumud'i da zagwad'in ta na saka Salis a idon ta sai gashi wata kunya take ji tana dabai baye ta, jin batajin motsin Salmat bayan taba ya sa har za ta bud'e k'ofar kuma ta juya ta saka ta gaba suka fito falon.


Gaisawa suka yi wanda Salmat da Zajlah d'in ko ta kan shi basu bi Ba, shi ko kallo guda ya yi ma Zajlah ya ji wani abu ya tsirga mai take ya mayar da kanshi k'asa yana latsar waya ganin cewa tana tare da y'ar uwar ta mai tsiwa.


Kamar kullum falon ta suka koma suka ci na su abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon su dukan su.


"Ka d'auki ajiyar ka mu wuce, in kuma baka ta shi ba ni in fice", a fad'ar Imran.

   Salmat ya nuna da yatsa "kaga ajiya ta nan", kallo aka bita dashi wanda ya yi silar k'ara jin kunyar ta tamkar ta nitse.


Zajlah kanta ta yi mamakin faruwar hakan, inda Alamein ke dubin me Salis ya hango a wannan fitsararriyar.


Da hakan dai suka ke6e suka k'ara tattaunawa tsakanin su, inda soyayya mai k'arfi ta d'inke tsakanin su.


Sai da suka yi girkin dare suka ci sannan kowa ya kama gaban shi. Alamein ko anci darajar Yusrah don ita ke saka mai abinci wanda Zajlah bata nuna mata cewa ita kad'ai ke girkin taba, kuma tasan ganin mutane ya sa shi kan shi yaci abincin.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa ```.

[2/5, 12:33 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                    *(28)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Awanni sun shud'e, kwanaki ma haka, wanda yanzu auren Zajlah da Alamein ke cikin wata na biyu amma ba wani canji tsakanin su kowa sabgar gaban shi yake yi, inda Zajlah d'inkin ta kawai ta saka ma gaba don tana samun customers da dama ta gurin Salmat, Yusrah da kuma Shema'u.


*** ***


6angaren Salmat kuwa magana ta yi nisa tsakanin ta da Salis inda manya suka shiga gida har an saka ranar auren su.


Aikin ta ta gama cikin lokaci saboda za taje gida wurin ganin Baban ta daya dawo daga saudiya jiya. Ba tada niyyar gaya mai komi saboda dama yanzu kusan kwana biyu sai taje gidan Mum, wani lokaci ta shiga gidan mak'ociyar ta Shema'u, ko yanzu a waya ta kira Mum ta shaida mata za taje wuni gida, hakan ya sa tace taje kawai ita ma za tazo daga baya.


Bayan ta kimtsa ne ta fita sai da takai saman titi sannan ta samu keke napep ta shiga sai gidan su, da murna ta fad'a gidan ta gaisa da Mama Asabe, gurin Baban na ta taje ta lafe tamkar wata mage, bayan sun gaisa ne yake ta ba ta labarin Makkah yana saka mata albarka har da guntun hawayen shi.


"Haba Baba miye na kuka a ciki?, ai wannan abin farin ciki ne a gare mu duka".


"Dad'i ne yayi man yawa Zajlah yanda na tai Makkah ta sanadiyyar ki, lallai tabbas y'ay'a mata rahama ne, gashi Allah bai bani d'a namiji ba amma kin zame min tamkar d'a dubu".


"Ba komai Baba, adai yi ta saka mu a addu'a, Allah yasa anyi hajji kar6a66e", "Ameen" ya furta a tak'aice.


Ferfesun kifin da ta yi mai ne had'e da alalen dankalin turawa sai so6o da jinja data had'o mai ta zube gaban shi.


"Zajlah Duke ina zan kai way'annan kayan? ai sun yi yawa", yana maganar farin ciki fal ranshi.


"Baba ba komai kaci sai ka k'oshi, nasan ka yi kewar abincin Nigeria".


Naja'atu ce ta zo tana furta "Baba in baza ka iya canyewa ba ni zan taya ka, kaga ma yau komai banci ba". Dariya ta basu sosai. Kayan aka d'iba akace ta kaiwa Mama Inno ta dawo sannan ta fice.


Sai zuwa bayan la'asar ne Mum ta iso ita da sarkin jin kai wato Saudat, sai wani sha k'amshi take yi tana yatsinar fuska tamkar anyiwa zawo yayyafi, saura k'iris Zajlah ta kwashe da dariya ganin yanda take yiwa fuska.

   Kaji ne dak'wa-dak'wa Mum ta soyo ta zo ma Mal Abu dasu, ba k'aramin dad'i Zajlah ke ji ba ganin yanda Mum ke tarairaya da ita da kuma mahaifan ta, godiya suka zuba sosai wanda har suka sa Mum na jin nauyin hakan da suke yi mata.


Basu wani dad'e ba suka fice daga gidan. D'aki suka wuce bayan wuce war Mum suna hira, inda magana d'aya ga ta biyu Salmat ta ce Salis kaza.


"Ke tsaya! Wai ke nan nuna min za kiyi kinsan soyayya kenan?, sai wani zak'ewa kike yi ba kida hira sai ta Salis".


"Habawa yarinya sunan ki sorry, gaskiya har tausayi kike ban da baki san dad'in "So" ba, yarinya da kin more rayuwarki".


"Rashin sanin gard'in So wani lokaci ya fi sanin So d'in kwanciyar hankali, ni kinga yanzu hankali na kwance, ke ko kullum la66an ki basu huta da furta Salis kaza ba".


Dariya Salmat ta yi sosai, inda a 6angare d'aya take tausaya wa rayuwar auren Zajlah da take ganin an tauye ta dayawa, saboda wannan auren sunan shi farin cikin uwar miji k'uncin surukar ta.


**** **** ****


Bayan sati biyu ne dubban mutane suka shaida auren 

*SALIS YUSUF*

               *&*

*SALMAT INUWA*

Wanda aka gabatar da biki cikin farin ciki da walwala tsakanin ango da amarya duk da ita ma ba wasu events akayi ba.

   Kullum Zajlah na saman hanyar gida tun ranar da aka saka Salmat a lalle har yau da za'a kai ta gidan mijin ta unguwar ni'ima.


Mum, Yusrah da Saudat sun yiwa Zajlah kara sun zo auren, duk da auren ya zamo tamkar 6angare biyu a gurin su saboda amintakar Alamein, Imran da Salis d'in sun taso tare ne tun primary skul d'in su, inda abotar tasu har ga iyaye ta kai.


Hakan aka dunk'ula Amarya aka kai ta d'akin mijin ta, sai dai fatar Allah yabada zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba.


Sai da kowa ya watse ne daga ita sai Salmat d'in ta duk'ar da kanta dai-dai kunnen Salmat d'in ta furta "to uwar soyayya kamin nan da wata goma muna jiran muga d'an soyayya".


Kasa magana ta yi sai hawaye dake yi mata zuba na kewar gida da iyaye, suna hakan ne Imran ya rako ango nan suka yi raha  da zolayar juna sannan Zajlah ta bi Imran ya sauke ta gida.


*** ***


Bayan kwana biyu Mum na zaune suna hira da Dad take gaya mai tana ganin fa kamar har yanzu babu wani cigaba tsakanin Alamein da Zajlah.

   "Koma miye Haj Hasana laifin ki ne, saboda kin tauyewa yaron nan rayuwar jin dad'i sosai, don haka gobe zan kira shi yasauwak'e ma yarinyar wannan auren".


Bud'ar bakin ta ke da wuya za tayi magana ya yi mata alama da bai son jin komai daga gare ta, da hakan suka je suka kwanta kowa da abinda yake sak'awa a ran shi.


K'arfe *02:00am* wayar shi ta d'auki k'ara kamar kar yad'aga saboda baisan lambar ba kuma da fargabar waye zai kira shi da wannan tsakiyar daren.


D'agawar shi dai-dai take da furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un", wanda ya yi dai-dai da zaburar Mum daga baccin da take yi, wayar ce ta ku6uce mai inda ya tafi luuu ya fad'i k'asa a sume.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:33 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                     *(29)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


sadiyajegal.WordPress.com



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



       Jijjiga shi Mum ta yi had'e da salati a bakin ta inda ko motsi baya yi, waya ta janyo ta kira Alamein sannan ta fito harabar gidan da kukan ta domin kiran direba da maigadi, har part d'in Dad suka shiga a rud'e, duk iya dabarar da za suyi sun yi amma ko motsawa baiyi ba, kukan Mum dana Saudat kawai kake jiyowa wanda gida duk ya hargitse ya koma tamkar safiya.


*** *** ***


Gigice ya lalabo makullin motar shi ya sauko ya bud'e falon ya fice, inda ya tayar da maigadin shi don yabud'e mai k'ofa, hankali tashe yake yimai bayanin abinda Mum ta gaya mai.


Motsin da ta ji ya yi yawa ne har an bud'e falon an fice ya sa ta yaye labulen window d'in ta, cikin tashin hankali ta hango yana yiwa maigadi bayani.


Hijab d'inta ta zaro daga cikin wardrobe ta saka ta fito, tana kawowa gate d'in yana ficewa da motar. Baba maigadi ta tambaya abinda ke faruwa, nan ya yi mata bayani kamar yanda Alamein ya gaya mai.


"Baba don Allah ka kula da gidan bara in k'arasa a k'afa".


"Haba y'ar nan ki duba fa kiga dare ne, kuma ke Mace ce kiyi hak'uri ki koma zuwa safe muji yanda abin ya kasance".


"Baba wallahi bazan iya zama ba har sai na ga wanne yanayi Dad yake ciki, da ganin yanda Alamein ya fita kasan abin sai a hankali". Ganin da gaske ta kama hanyar zuwa gidan ne ya sa ya rufe gate d'in ya mara mata baya.


Suna kawowa motar direban Dad na kunno kai a guje, inda ta Alamein ke daga waje ko rufe ta bai yi ba.


Mum ce da Saudat suka fito a rud'e inda idon kowa cikin su har sun kumbura, maigadin su ta ba umurnin ya shiga motar Alamein yakai ta asibiti saboda ba za ta iya zama ba, don direban su da Alamein suka wuce da Dad.


Nan Zajlah da Saudat suka fad'a motar aka fice dasu sai asibitin Aisha Buhari, wanda ko da suka isa har an shiga A&E dashi sai direba ne da Alamein ke kai kawo a wurin, wanda duk iya nazarin shi ya kasa gano miye silar wannan abin.

   Juyawa ya yi zuwa ga direba had'e da je fo mai tambayar silar wannan abin.


"Wallahi Yalla6ai yanda ka ganshi hakan Haj ta kira mu muka tarar dashi, bamu San takamemen meke faruwa ba, sai dai ka jira k'arasowar Haj kaji, Allah dai yata shi kafad'ar Alh", yana maganar yana shartar majina.


Da hanzari Mum ta fito had'e da tambayar su abinda ake ciki, Alamein ya bata amsa cikin k'arfin hali cewa tun shiga dashi ba wanda yafito har yanzu.


"Mum wai miye silar wannan tashin hankalin?, saboda ni dai a sani na Dad ko hawan jini bashi da barranta na inyi tsammanin shi ne ya ta shi".

    Nan ta kwashe abinda tasani ta gaya mai. Wayar ce ya buk'aci gani inda aka yi sa'a Mum ta fito da ita, kar6a yayi ya binciko last call d'in wayar ya kira, kawai Mum ganin shi ta yi zaune da6as a k'asa sai hawaye ke biyar idon shi.


Mutum mutumi ya koma saboda magana kan ta bai iya ta sai dai kaga la66an shi na motsi sai ido da yake saki tamkar sabuwar gawa, hawayen da bakin dake motsawa kawai zai tabbatar ma yana raye ba don hakan ba sai dai kace a sume yake.


Cikin tashin hankali Mum ta dafa kafad'ar shi had'e da jero mai tambayoyi cikin rud'u da firgici, wanda shi ko bin ta kawai yake yi da ido.


Cikin tashin hankali Zajlah ta samo ruwa a cup gurin masu jinya ta zo gab dashi tana jijjiga kafad'ar shi, addu'a ta yi sosai a ruwan ta bashi ya sha kuma ta dinga Shafa mai su a fuska tana mai k'ara karanto wasu addu'o'i tana tofa mai, inda gaba d'aya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye kan tausaya wa yanayin da suke ciki.


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai Mum ke furta wa wanda ta fara jin nutsuwa na sauko mata. Sa6anin Saudat dake wata irin gunza tana fisgar gashin kanta tamkar wata sabuwar kamun hauka.


Ajiyar zuciya Alamein ke sauke wa kad'an kad'an saboda wani sanyi da yake ji yana sauko wa tun daga saman kanshi har zuwa yatsan shi.


Hannun ta ya janyo da take rik'e da kanshi tana tofa mai addu'a ya d'ora saman k'irjin shi dake dukan tara-tara, ruwan ta kuma d'ora mai a baki ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya ya zube a jikin ta tamkar gawa.


K'arar da ta saki ne ta janyo hankalin mutane da dama suka yo gurin, wasu nurse ne guda biyu suka tallafe shi aka shiga d'ayan d'akin dashi na kusa da Dad.


(Wayyo ni Jegal meke faruwa haka?, zuciya ta duk ta cunkushe saboda rashin sanin takame-men me ke faruwa da d'a da uba)



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:33 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                     *(30)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


Sadiyajegal.WordPress.com



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



( *Don Allah Fan's ina neman addu'ar ku*)


Bayan an shiga da Alamein ne Zajlah ta koma gurin Mum tana rarrashin ta wanda ita kanta sai hawaye take yi. Babban tashin hankalin su rashin sanin takamemen abinda ke faruwa, suna hakan ne Dr ya fito daga d'akin da aka shiga da Dad, cikin rud'ani suka tare shi kan cewa  ya ake ciki?


"Ina son ganin wani daga 6angaren marar lafiyar amma kuma namiji ba Mace ba", daga hakan ya shige office ya bar su tsaye tamkar gumaka a chochi.


"Mum me zai hana a kira Abban Yusrah a gaya mai abinda ke faruwa, tunda ga Alamein shi ma akwance".


Wayar Dad dake hannun ta ta mik'a mata alamar ta kira. Alh Muttak'a ta gani rubuce nan ta kira kusan sau uku sai ana hud'u aka d'aga, bayan ta gaida shi cikin nutsuwa ta kora mai bayanin abinda ke faruwa, nan yace gaya nan zuwa.


Suna hakan ne direba ya kawo wayar Alamein da ake kira dake cikin mota, Zajlah ce ta d'aga wayar suka gaisa take kora ma Salis abinda ke faruwa, nan ya ce mata shi ma gayanan zuwa .


Kusan tare suka iso asibitin, Imran, Salis da kuma Abban Yusrah, ga alama Imran da Salis sun san me ke faruwa amma ganin tsananin tashin hankalin da ake ciki ya hana masu furta komai.


Office d'in likitan suka shiga nan yake ce masu "sanadiyyar abinda ya samu Alh wanda ko mu bamu san miye ba ya yi silar mutuwar 6arin jikin shi had'e kuma da hawan jini na farat d'aya wanda ke barazana da rayuwar shi".


Su duka ukun "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" suke furtawa, cikin tsananin tashin hankali Abban Yusrah ke furta "wannan wane irin tashin hankali ne dake neman rayuwar d'an uwa na?, ya Allah ka tada kafad'ar Yaya".


Imran ne ya yi gyaran murya had'e da ce ma Abban Yusrah "Abba wannan abin yana da nasaba ne da k'onewar ma'aikatar Dad gaba d'aya wacce ba'a san miye silar hakan ba, yanzu hakan daga can muke wanda har yanzu wutar ke ci".


"Shi ne ma kiran da muka yiwa Alamein domin yasan yanda zai gayawa Dad maganar cikin kwanciyar hankali, ashe an samu wanda ya gaya mai har ya yi silar jefa wad'annan iyalai cikin tashin hankali".


"Innalillah" Abban Yusrah ke ta nanata wa wanda shi ma ga alama ita ce tayi tasirin samun nutsuwar shi da yanzu shi ma ya zube a sume.


"To yanzu likita me ake ciki akan ciwon na shi?".


"Za ku jira nan da awa hud'u domin samun farfad'owar shi sannan a hau mataki na gaba".


Hakan yasa suka fito jiki a mace tamkar wa'anda k'wai ya fashewa a ciki, cikin k'arfin hali Mum ta tunkare su domin jin me ke faruwa.


Ganin cewa 6oye mata bai da wata fa'ida ya sa cikin nutsuwa da lallami had'e da nasiha suka gaya mata me ke faruwa. Ba k'aramar bajin ta ta yi ba gurin aro juriya ta yafa ba, bayan "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai "Hasbunallah wa ni'imal wakeel" kawai take nanatawa.


Zajlah kanta ba k'aramar gigita ta shiga ba na jin k'addarar da ta sauko ma wa'annan iyalin ba, k'arfin hali ta yi sosai sannan ta tunkari Saudat domin rarrashin ta ganin irin yanayin da ta shiga.


Likita ne ya fito daga d'akin da aka shiga da Alamein, cikin sauri suka tunkare shi had'e da jero mai tambayoyi na jin wanne yanayi yake ciki.

   "Za ku iya shiga ku duba shi, amma plxxx banda hayaniya saboda yana buk'atar hutu".


Haka suka rik'a rigen-gen shiga d'akin. Kwance yake kanshi yana kallon ceiling wanda kallon ne kawai yake yi amma bai da takamemen abinda yake kallo, saboda tunane-tunane da suka dask'are zuciyar shi wanda yake jin tamkar ma ta dai na aiki.


Sannun da suke jero mai ya d'an dawo dashi hayyacin shi wanda ba bakin sai ido kawai da yake bin su dasu, sai kai da yake kad'awa alamar amsawa.


"Mum kinji me ya samu Dad? Mum Dad ya mutu ko? Shike nan yanzu ba mu da komai? Mum kisa a kashe wutar da takama a company". Sambatu yarik'a yi tamkar wani zautacce, hakan yasaka Mum ta fasa wani irin kuka mai cin rai.


Da saurin ta ta zo ta toshe mai baki had'e da girgiza mai kai alamar yayi shiru inda ita ma sai hawaye ke sauka akan budurwar fuskar ta, ruwa ta kuma bashi tana dafe da k'irjin shi tana tofa mai addu'a, Zajlah kenan yarinya mai zuciyar tausayi.


Wayar Imran aka kira had'e da gaya mai cewa an samu nasarar kashe wutar amma fa ta lashe komai na ma'aikatar wanda ko fallen takarda ba'a fita dashi ba, hakan ya yi dai-dai da kiran sallar asuba.


(Hakan ya sa ni ma dole na dakata domin gabatar da farali).



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                    *(31)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


(Sanadiyyar y'ar wata matsala data faru ya sa na canja blog d'ina, sadiyajegal.WordPress.com).



    Kiran sallar ne ya sa suka ta shi dukan su domin gana wa da ubangiji, matan kuwa gurin Mata y'an uwan su majinya ta suka nufa, nan aka ara masu kayan buk'ata suka sauke farali.


Zajlah ta dad'e tana kwarara ma mijin ta da kuma surukin ta addu'ar samun sauk'i da kuma cin wannan jarabawar daga ubangiji, saboda ba k'aramin tausayi suka ba ta ba, asara ta farat d'aya akwai tashin hankali ba k'arami ba.


Bayan mazan sun dawo ne Abban Yusrah ya umurce su dasu koma gida tunda su mazan suna nan, sai dai kash cikin su ba wanda ya ji zai iya d'aga wa nan da can ba tare da ya ga halin da Dad yake ciki ba.


Mum ce ta yi k'arfin halin furta' "Zajlah kuje gida ku d'an huta, in Dad d'in ku ya farfad'o za mu iso".


"Mum gaskiya bazan iya tafiya ba, kuyi hak'uri Abba har muga ya yanayin jikin Dad, amma yanzu zanje gida in samo mana abinda za'a ci".


Direba ya kai ta gidan, gaggauce ta dafa ruwan Lipton sannan ta soya k'wai da dankali sai ferfesun kifi da ta yiwa Dad. Wanka ta shiga ta yo wanda ko mai bata shafa ma jikin ta ba ta zura wata doguwar riga y'ar kanti ta d'auki wasu kayan buk'ata ta fice.


Ko da ta isa asibitin kowa ya yi jugum ana sauraren farfad'owar Dad, bayan ta gaida su ne ta zube kayan da ta zo dasu, kowa sai sannu yake mata sa6anin Alamein da bakin magana ya mutu sai dai binta da yake yi da ido had'e da jin tausayin ta can k'asan zuciyar shi.


Dak'yar ta samu Mum ta sha tea kad'an sannan ta had'a wa Saudat ta rarrashe ta ita ma tasha kad'an, sa6anin mazan da suka nuna ba za su ci komai ba, tana so ta had'awa Alamein yasha ko kad'an ne amma nauyin Abba take ji.


Fahimtar hakan ya sa ya furta' "su Mum ne ake rarrashi su karya ba za'a had'awa yaro na ba?". Cikin zolaya yake furta maganar.


Kai ta soke tana wasa da yatsun hannun ta, ganin cewa tabbas ita Abba ke jira ya sa ta had'a tea d'in ta kawo mai, zurum kawai ya yi yana kallon ta sannan ya kauda kai, hakan ya sa ta girgiza mai kai alamar kar yace bai sha, nan ya kar6a ya sha kad'an ya bata cup d'in.


**********


*09:00am* likita ya fito daga d'akin da aka kwantar da Dad, su duka suka tunkare shi domin jin ya jikin nashi, nan ya gaya masu cewa ya farfad'o za su iya shiga su ganshi amma kar su cika shi da hayaniya.


Cikin murna suka fad'a d'akin dukan su, sai lokacin Alamein ya san meke faruwa da Dad, saboda ko da Abba ya yi bayani yana nashi d'akin.


Kowan nen su sai da ya zubarwa Dad da hawaye akan yanda ya koma cikin awa bakwai abin gwanin ban tausayi, lallai tabbas rayuwa ba a bakin komai take ba, rayuwa da lafiya ciwo da mutuwa duk ga hannun ubangiji suke, lokacin da ya d'oro ma d'aya ba wanda ya isa ya yaye ma sai Allah, an dai samu ya farfad'o amma ba uhm ba uhm-uhm sai dai ido, ga kuma 6angaren jikin shi da bai motsawa ko kad'an.

    Kukan da ya zo ma Mum ne ya sa ta fita daga d'akin ta jingina ga k'ofa tana rasgar kuka tamkar wata k'aramar yarinya, saboda hango tarin matsaloli masu tsabagen yawa a rayuwar su.


Tunkarar Dad ya yi yana kuka zai fad'a saman jikin shi su Salis suka tare shi, Abba ne ya bada umurnin duk su fita daga d'akin, bayan sun fice ne ya je gab da d'an uwan shi yana magana ko zai kar6a mai sai dai babu nasarar ko da motsawar la66an shi, duk da k'arfin halin da yake yi sai da hawaye suka wanke dattijuwar fuskar sa.


Fitowa ya yi daga d'akin yana mai shawartar su kan a wuce da Dad f.m.c Bk. Kowa ya yi na'am da maganar shi hakan suka yita rarrashin Alamein har suka fice su duka domin duba yanayin wutar da ta ci ma'aikatar, iya bincike anyi amma ba'a gano musabbabin wutar ba.


*******


Su Mum kuwa gida suka fice domin yin shiri zuwa Bk.

   "Mum in shirya muje ko?", cewar Zajlah.


"A'ah kuyi zaman ku ke da Saudat har muga yanda abin zai kasance, ke Saudat kishirya kayan ki ki koma can gidan su har mu dawo".


"Mum kibari ni zan d'ebo kaya na in dawo nan har zuwa dawowar ku, Allah ya tashi kafad'ar Dad yasa ayi farar jinya".


Hakan yasa Mum ta yita saka mata albarka. Da hakan ta fice ta d'auko kayan da za ta buk'ata ta rufe gidan ta dawo, Baban ta ta kira ta gaya masu abinda ke faruwa da sauran y'an uwa daya dace su san da faruwar abin.


Bayan Mum ta kimtsa ne suka raka ta asibitin, acan ne suka had'u da Salmat, da Yusrah, sai kuma iyaye daga 6angarori da dama da suka cika asibitin tamkar ad'auke wa Dad ciwon da ke damun shi.


Ba abinda ni kai na yak'ara firgitani tamkar yanda aka d'auko Dad za'a saka a mota kai kace gawa ce, nan matan masu raunin zuciya suka rik'a kuka.


Bayan an wuce dashi ne da Abban Yusrah sai Imran, Alamein, Salis da wasu abokanen Dad biyu. Nan su Mama Asabe suka wuce jiki a sanyaye, Mamar Yusrah da Salmat da Yusrah duk gidan su Mum suka wuce.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                   *(32)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


(Don Allah ina masu baku hak'uri masoya na da cewa waya ta bata hak'urin ture-turen buk ga mutane da dama, ko group yanzu sai na saka wasu sun min posting, masu nema su tambaya a group ko suje blog d'ina, da fatar zaku fahimce ni, luv y'all)


( *INA MAI MIK'A SAK'ON TA'AZIYYA TA ZUWA GA ANTY NA JIDDA MUSA NA RASHIN Y'AR YAYAR TA* اللهم اغفر لها، وارحمها، واعف عنها، واغسلها بالماء والثلج والبرد يا الرحم الراحمين.



    Kwanci tashi yau Dad satin shi biyu a asibiti ana yi mai gashin jiki wanda ga alama sauk'i ke shiga kad'an-kad'an, wanda har yanzu bakin shi bai koma dai-dai ba abin ya zamo tamkar mai kariyar halshe.


**** **** ****


6angaren su Zajlah kuwa ita da Saudat da Yusrah suke kula gidan, saboda tun lokacin da ta biyo su daga asibitin take gidan, sun je ganin Dad kusan sau biyar, haka ma su Mal Inuwa sun je sau biyu duba jikin na shi sai dai fatar Allah yakawo sauk'i.


*** *** ***


Yau ne aka sallamo Dad daga asibiti ba wai don ya murmure duka ba sai don ganin irin tsabagen kud'in da ake ci na jinya kuma ciwon sai dai hamdala ya sa Mum ta yi shawara da Abban Yusrah kan su nemi sallama aje gida a had'a da addu'o'i.

   Ba hakan likitoci suka so ba, sai dai ba yanda za suyi hakan suka bashi sallama d'in tare da shawarwari na kula da yanayin jikin na shi.


Hakan suka d'ungumo suka dawo gida wanda da murnar su Zajlah suka fito taryar su, sai gashi sunyi turus saboda sun zata za su ga Dad ko da da sanda ne ko kuma yana d'ingishi sa6anin ganin da suka yi an tallafo shi daga mota, dukan su sai da suka zubar da hawaye.


Godiya Mum ta yiwa su Imran sosai na ganin irin yanda suke ba da kulawa ga ciwon Dad, kuma basu zauna ba tun faruwar abin kullum suna asibiti.


"Lallai kun zama abokanen arzik'i, samun irin ku a wannan zamanin sai an tona, Allah ya yi maku albarka yasa ka maku da khairan", tana maganar tana hawaye.


"Amen Mum, amma kakki damu wannan ba komai bane yi wa kaine, kuma Dad tamkar uba yake gare mu duk abinda muka yi mai ba fad'uwa ce a gare mu ba, fatar mu kawai a gare shi addu'ar samun sauk'i".


Da hakan suka fice daga gidan suna masu tausaya wa zuwa ga Dad.


Zajlah ta so ta kwana gidan amma Mum ta nuna mata tunda sun dawo ta tashi ta koma gidan ta had'e da yi mata godiyar d'awainiya da kuma kulawa da ta basuwa akan ciwon Dad, hakan dai ta had'a kayan ta ta wuce don ba hakan taso ba musamman da taga Yusrah ta dawo gidan da zama gaba d'ai.


Hakan dai ta kakka6e y'ar k'urar da gidan ya yi sannan ta yi wanka ta kwanta, wata zuciya ke ce mata biki kyauta ba Zajlah ke fa sai da kika gyara inda za ki kwanciya sannan kika kwanta ya kama ta ki gyara wa bawan Allah na shi gurin, wata ke ce mata sassaucin da fa kika samu rashin lafiyar Dad ce amma yanzu in kika shiga sabgar shi zai iya wulak'anta ki, wannan shawarar ta fi duba wa ya sa ta yi kwanciyar ta.


*** *** ***


"Son ka ga har *10:00pm* ta yi kuma Dad ya samu bacci ka tashi kaje gida ka kwanta".


"Mum kibar ni na kwana anan, ko na je gidan ba bacci zan samu yi ba".

   "Bazai yuyu ba Son ko matar ka d'azu na kora ta gida saboda haka kai ma ka fice gobe ka dawo".


Ba don ran shi ya so ba ya fice daga gidan wanda ko sai da safe bai yiwa Mum ba, shi ala dole an 6ata mai rai.


Ko da ya shiga gidan tsab komai ta gyara sa6anin d'akin shi dake fama da k'ura birjit, ganin cewa bazai iya kwana d'akin ba haka kuma bazai iya ta6a k'urar ba ya sa ya d'auko blanket ya dawo falo ya yi shimfid'a ya kwanta, da tunane-tunane fal a ranshi 6arawo ya yi gaba dashi.


**** ****


*Washe gari*


Kiran sallar farko ya tayar da ita daga baccin duk da bata cikin tsalki, wannan sabo ne duk baccin da take yi da ankira sallah za ta tashi, alwala ta yi ta d'auko littafin ta na azkar tana karanta wa, sai wurin k'arfe *07:00am* ta fito domin samun abinda za ta dafa taci.


Turus ta yi a falon ganin shimfid'ar shi alamar nan ya kwana, ji ta yi ba dad'i a ranta ko ba komai ya ci ta kyautata mai matsayin shi na mijin ta kodon gudun fad'awa fushin ubangiji, saboda tasan hakk'ok'in miji akan matar shi kuma tasan na mata akan mijin ta.


A fili ta furta "insha Allah Alamein daga yau zan kula da hakk'in ka a kaina ko da ba zaka kula da nawa ba".

    Kitchen ta fasa shiga ta yi d'akin shi duk da gaban ta dake dukan uku-uku, ga mamakin ta tana tura k'ofar ta ji ta a bud'e turus ta yi ganin yanda d'akin ya yi uwar k'ura.


Ita da na ta ta kasa kwana cikin shi ina ta ga na shi da tun auren su bai ga gyara ba, karfa ta mayar da mijin ta *KAZAMIN MIJI* (SIS JABO), duk tsaftar namiji ba kowa ne daga cikin maza zai iya gyaran d'akin shi ba saboda haka za ta tashi tsaye a wannan 6angaren.


Gyaran d'akin ta shiga yi sosai, sannan ta fad'a toilet kayan shi k'anana ta saka a wash machine ta wanke sannan ta wanke toilet d'in, kayan wanki ta had'a ta fito dasu ta kaiwa Baba maigadi akan cewa don Allah yasamu mai wanki da guga yaba shi ya wanke, "aiko yaro na sana'ar shi ce zan kai mai ya wanke".


Godiya ta yi mai sannan ta koma gidan ta d'auki turarukan d'aki ta je d'akin shi ta fesa, kitchen ta wuce ta yi masu girki ta saka mai a kuloli ta kai dinning table, Baba maigadi ta kaiwa sannan ta ci na ta ta fad'a wanka.


****** ******


6angaren Alamein kuwa daga masallaci ya rok'i liman a saka Baban shi a addu'a sannan ya fitar da kud'i ya bada a raba sadaka, daga nan gidan su ya wuce domin duba jikin Dad.


**** ****


K'arfe *11:00am* ta kammala duka ayukkan gidan sannan ta fice zuwa gidan su Alamein, a gate suka had'u tana rik'e da kula a hannu kamar ta wuce komai ta tuna ta tsaya ta gaida shi, nan ya amsa ba yabo ba fallasa ta shige gidan shi ko ya fice zuwa gida.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa``.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                    *(33)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


sadiyajegal.WordPress.com



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



    Yana komawa gidan ya nufi dining table ya ci abinci kad'an duk da yana ganin yau ya ci dayawa akan tun fara ciwon Dad bai ta6a cin abinci irin yau ba, d'akin shi ya nufa domin ya yi wanka ya koma gidan su, yana tunkarar hanya k'amshi na tarbon shi har ya sadu da k'ofar, yana turawa ya yi turus yana kallon d'akin saboda yanda komai ya fito tsaf sai k'amshi dake tashi d'akin, saman gadon ya je ya kwanta yana ta tunane-tunane har bacci ya yi awon gaba dashi.


**** ****


Tana shiga gidan ta gaisa dasu ta bawa Mum Kular abincin da ta zo wa Dad dashi, "dama kenan jira kike yi gari ya waye ki fito tamkar wacce ke zaune saman k'aya", cewar Mum.


Murmushi kawai ta yi saboda tana son zaman gidan musamman yanzu da Yusrah ke gidan saboda Allah ya had'a jinin su sosai.


"D'auko kular muje kiga Dad jiki ya yi sauk'i akan jiya", masha Allah Mum Allah yak'ara sauk'i".


Da hakan suka shiga d'akin ta ganshi ta yi mai ya jiki duk da ba iya kar6awa yake yi ba sai dai yayi alamar amsawa da kai.

   "Mum akwai zam-zam a gidan nan?".


"Eh akwai Zajlah har galan d'aya da rabi".


"Mum kawo rabin galan d'in muga". Bayan ta kawo ne Zajlah ta karanta (falak', Nas, Ikhlas) kowaccen su k'afa uku-uku sannan ta had'a da (Ayatul kursiyyu) had'e da wasu addu'o'i na yayewar lalura ta tofa.


"Mum gasu nan ki rik'a bashi yana sha kuma ki rik'a shafe mai jikin shi dasu, insha Allah zansa a gayawa Ustaz Yusuf ko Ustaz Lukman su rik'a zuwa suna yimai addu'a, ba abinda addu'a ba za ta yaye ba sai in ba'a kai kuka gurin ubangiji ba, ubangiji Allah ya tashi kafad'un shi ya yaye lalura".


Mum har da hawayen ta na jin dad'in kasancewar Zajlah a cikin zuri'ar ta, "tun farkon had'uwa ta dake jiki na ke bani ke alkhairi ce a gare mu".


"Mum ba komai mudai dage da addu'a", da hakan ta fice daga d'akin ta koma falo gurin su Yusrah.


*** *** *** ***


Sai kiran azzahar sannan Alamein ya tashi daga bacci wanka ya fad'a ya kimtsa ya yi masallaci saga can ya wuce gidan su.


Bayan an gaisa ne Mum take gaya mai abinda Zajlah ta yi da kuma shawarar da ta basuwa na kiran d'aya daga cikin Malaman su don yiwa Dad addu'a.

   Baiyi k'asa a gwuywa ba ya yi makarantar tasu Zajlah, da Ustaz Yusuf ya ci karo suka yi magana ya bashi tabbacin zai rik'a zuwa da safe Ustaz Lukman ko bayan isha'i.

     Godiya ya yi sosai had'e da d'auko kud'i ya bashi, nan ya nuna mai bazai kar6a ba sai dai gobe d'in in ya zo.


**** *****


Yau sati biyu kenan ana kula da yiwa Dad addu'a had'e da mayar da ruwan zam-zam da Zajlah ta yi mai addu'a ruwan sha da kuma shafe mai jiki, jiki kam Alhmdulillah don yana magana yanzu kuma har yana iya takowa da k'afa daga d'akin shi zuwa gate abin sai son barka.


*** *** ****


D'an zaman da suka yi da Yusrah ya sa ta k'ara sanin kan waya sosai don har whatsap ta bud'e mata kuma ta saka ta group na gyaran jiki dana kwalliya, sai kuma group d'in musha karatu saboda gwada karatun littattafan soyayya, inda take samun littafai har ta rasa na za6a ta karanta.


Tana bud'e data ta shiga whatsap ganin cewa ba'a turo *AL'ADUN WASU* (SIS BATUL) ba ya sa ta rufe data ta hau d'inkin ta da Yusrah ta kawo kusan turmi takwas.


*** *** ***


Soyayya mai tsafta da kulawar juna ake bugawa tsakanin Salmat da Salis tamkar su had'e juna saboda tarairaya.


*** ***


Inda kuma 6angaren Yusrah da Imran soyayya ta k'ullu sanadiyyar zaman da ta yi a gidan Mum shiko Imran yana saman hanyar duba jikin Dad kusan kullum.


*** *** ***


6angaren Zajlah kuwa kullum sai ta gyarawa Alamein d'akin shi sannan in ta yi girki za ta ajiye kowanne kuma yana ci, kamar yanda inta gaida shi yake amsa mata cikin sakin fuska sai dai bayan hakan babu wata alak'a tsakanin su.

   Kamar kullum yau ma ta gama had'a breakfast ta d'auko ta kawo dining ta tarar dashi zaune ya had'a kai da gwuywa, ga alama yana cikin damuwa, bayan ta ajiye ne ta koma kitchen ta d'auki na ta kayan abincin ta yi falon ta.


Kasa cin abincin ta yi sai juya cokali da take yi a plate duk jinta take yi ba dad'i, waya ta janyo ta kira Salmat suka gaisa sannan ta kora mata abinda ke damun ta.


"Yanzu ne ya dace ki nutsi ku ajiye duk wani shirme da kuka yi a baya saboda mijin ki na cikin tsananin neman taimako da mai bashi shawarwari, saboda haka don Allah ki rik'a bashi kulawa ki ajiye komai a gefe".


"Tabbbb Salmat yau ke da kan ki ke furta hakan?, ke fa kika ce in gyara mai zama amma yanzu ke ce mai yi mai yak'i".


"Alamein d'in ne ya zamo abin tausayi shi da ubanshi, har dai yanayin da suke fuskanta yanzu dole a tausaya masu, amma kar kiyi saurin bada gari daga shawarwari ki zurma, don nasan ki da raunin zuciya sai anja aji", cikin dariya da zolaya take maganar.


"Ke dai kika sani, Allah ya shirye ki", daga hakan ta kashe wayar ta bita da kallo tana nazarin kalaman Salmat.

   "Lallai ni shaida ce ciwon Dad ya sa Alamein ya sauya, saboda daga ranar da abin ya faru kawo yanzu babu hantara ko kallon raini, ko don yana ta lafiyar ubanshi ce bansani ba".


A fili take ta maganganun ta ita kad'ai inda dai ta d'an ci abincin kad'an ta tashi ta mayar da kayan kitchen, turus ta yi a falo ganin yanda ta barshi hakan ta dawo ta tarar da shi tamkar ko yatsan shi bai motsa ba, kayan ta je ta ajiye sannan ta dawo kanshi ta yi tsaye saboda rashin takamemen ta ina za ta fara, don gaskiya har yanzu tsorace take ga kutsa kanta cikin lamurran shi.


A duniya tak'i jinin ganin babban mutum cikin damuwa duk sai taji ta kasa nutsuwa a ranta abin yai ta damun ta, hannu ta kai za ta ta6o shi ko me ta tuna ta fasa oho, zaune ta yi nesa dashi kad'an saman kujerar da yake zaune, gyaran murya ta yi amma kuma a banza ko motsi bai yi ba.


Tsoro ta ji sosai na ko ya suma ne a hakan, cikin sauri ta kai hannun ta saman kafad'ar shi ta girgiza shi kad'an ya zabura cikin razana, yana tayar da kan shi idon su suka had'e guri d'aya nan take bugun zuciyar su ya halba lokaci d'aya.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *ADALILIN GATA*💗💕


                  *(34)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



      Ganin ya k'i d'auke idon shi akan tane ya sa ta yi saurin kauda na ta idon, saboda ba zata iya jurar kallon fararen idon shi da suka rine suka koma ja ba kan tsananin damuwa tamkar wanda ya ci kuka ya k'oshi, yatsun ta ta dinga wasa dasu kanta na nok'e k'asa. Hannu ya kai ya tallafo hab'ar ta had'e da yi mata alama da d'ayan hannun na me aka yi?.


"Na ga tun d'azu baka ci abinci bane shiyasa",  "Ayyah kar ki damu zanci yanzu, nagode da kulawa".

   Wata zuciya ke ce mai me zai hana ka gaya mata damuwar ka tunda ita ta kasa jure taka damuwar har tazo ta yi ma magana, d'ayar ke ce mai kakka tsaya gaya mata komai, me za ta iya yi akai? Salon ka ja ma kanka raini daga gurin ta tunda wuri haka.


Tamkar guguwa haka ya ta shi ya nufi d'akin shi ya barta nan zaune sake da baki, "tabbas mai hali ba ya canja halin shi, irin hakan nake gudu shiyasa ba nason sa kaina cikin lamurran shi, ko ma miye Allah ya yaye", a fili take maganar ta ita kad'ai, da hakan ta wuce na ta d'akin.


*** *** ***


Zuwa la'asar ne ta gama ayukkan ta ta ji tana ra'ayin shiga tak'ara duba jikin Dad, har ta kimtsa ta fito ko motsin Alamein bata ji ba hakan ya sa ta ficewar ta.

   Tana isa gidan ta gayar da Mum haka ma Dad don jiki ya yi kyau sosai yana magana kuma yana d'an fita sai dai tafiya ba mai nisa ba.


Abu d'aya ya yi mata tsaye a rai ganin yanda kwana ukun da bata zo gidan ba Mum ta kod'e ta jeme duk ta fita hayyacin ta tamkar wacce ta yi jinya.

    "Mum hala ciwo kika yi bansani ba?".

"Wallahi a'ah Zajlah jarabobin rayuwa ce kawai da suka yi yawa".


"Mum indai ciwon Dad ne ai Alhamdulillah don jiki ya yi dama sosai, sai dai a k'ara dagewa da Addu'a".


"Tabbas a rayuwa anason bawa ya yawaita addu'ar Allah ya kare shi da miyagun k'addarori, to su ne suka hau kan Daddyn ku".


"Tun lokacin da yafara wannan ciwon abubuwa ke ta kunno kai, wanda masu bashi da way'anda k'addara ta rutsa da dukiyar su suke ta kunnowa neman abar su".


"To amma wannan ta su mai sauk'i ce akan wacce ta kunno kwana biyun nan, a rayuwa ana so mutum komai dukiyar shi yarik'a sayen kadara yana ajiyewa saboda ranar da lalura ta taso zai iya fitarwa ya saida yayi lalurar shi ba tare da wani ya ji shi ba".

   Zajlah dai zurum ta yi tana sauraren Mum, saboda har yanzu bata fahimci ina ta saka ma gaba ba, a tunanin ta irin dukiya ta Dad bazai ma yuyu ba ace cikin kashi d'ari an ta6a ashirin ba, amma dai bari ta saurare ta har takai k'arshe.


*** *** ***


*ASALIN MU*

"Mu haifaffin garin Jega ne, ni da Dad d'in ku auren zumunci aka yi mana sanadiyyar mahaifin shi da mahaifi na uwa d'aya uba d'aya, inda tun muna yara iyayen su suka yi hatsarin mota suka rasu, hakan ya yi silar dawowar su gidan mu da zama shi da k'anen shi Muttak'a wato Abban Yusrah".


"Hakan Baba na ya rik'a su amana had'e da basu tarbiya gwargwado duk da ba wani hali ne dashi sosai ba, ko da suka dawo gidan da zama dama mahaifiya ta ta rasu tun gurin haihuwa ta sai wata mata da Baba ya auro".


"Daga baya soyayya ta k'ullu tsakani na da Kabiru wato Daddyn ku har muka yi aure, shekarar mu kusan bakwai da aure Allah bai bamu haihuwa ba sai daga baya aka samu cikin Son wanda haihuwar shi ta sa Kabiru ya d'auki son duniya ya d'ora mai kuma nan yaci sunan mahaifin shi wato Aminu. Haihuwar shi da wata bakwai ne Allah ya yiwa mahaifina Baba Sani rasuwa inda matar shi Aisha ta gama wanka ta k'ara gaba sanadiyyar bata haihu dashi ba, shi ko Muttak'a ya auro Balkisu mamar su Yusrah".


"Hakan zama ya kasance tsakanin mu iya mu saboda bamu da wasu dangi na kusa, Son na da shekara biyar na haifi Saudat lokacin ne Allah ya k'ara bud'awa Dad hanyar samu yana bawa yaran shi kulawa da kuma soyayya wacce ko ni kaina na ta6a su to zan had'u da fushin shi ranar".


Lokacin ne kuma arzik'in shi ya k'aru ta hanyar wani babban aminin shi mai kud'i wato Alh Ibrahim wanda yake shahararren mai kud'i sosai, kusan lokaci guda akayi auren mu da nashi, Allah cikin ikon shi matar shi ta samu ciki gurin haihuwa ta rasu ita da abinda ta haifa bak'in cikin hakan ya sa kaf ya had'a dukiyar shi ya ba Dad ajiya, saboda gaskiya babu wanda yasan dangin shi Sana'a ce kawai ta had'a su ko ga hira bai ta6a cewa ga dangin shi ba, don ko neman auren gidan mu aka shige mai gaba, wancan lokacin kurmi ya yi shirin tafiya da zai wuce ne Dad d'inku ke ce mai yaushe zai dawo? Gaya mai ya yi babu rana, sannan ya ce mai in Allah ya yi mai rasuwa ya bashi dukiyar shi kaf.


Daga hakan Mum ta yi shiru hawaye na mata zuba cikin k'unar rai.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                    *(35)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


sadiyajegal.WordPress.com



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



     Zajlah ce ta ni sa had'e da rarrashin Mum ta d'auko mata ruwa tasha sannan ta cigaba kamar haka.

     "Da hakan ya wuce kurmi wanda bayan kud'in abinci da suturar jikin shi bai fita da komai ba dai-dai da gidan shi sai da ya saida sannan ya bar garin nan.


Dad ya so ta6a kasuwanci da kud'in da Alh Ibrahim ya bashi ajiya na nuna mai hakan bai dace ba sannan yabar kud'in ma'ajiyar su ya cigaba da juya nashi gwargwado Allah ya bud'a mai hanyar samu ba laifi.


Bayan shekara hud'u da tafiyar shi ne mummunan sak'o ya risk'e mu cewa Allah ya yi mai rasuwa sanadiyyar gobara data tashi gidan da suke zaune, wanda wancan lokacin Dad yaso share maganar sai da na takura shi kan cewa yashiga mota yaje kurmi don tabbatar da zancen, hakan ya sa ya shirya ya je wanda bai dawo ba sai da tabbacin duk wanda ke gidan bai fita ba sanadiyyar wutar dare data tashi ba zato ba tsammani.


Bayan rasuwar shi da wata uku ne Dad ke maganar dukiyar margyayin wanda sai da aka nemi malamai had'e da takarda daya rubuta na tabbacin tunda baida kowa in ya rasu Dad ya d'auki kud'in, hakan ya sa kud'i suka zamo nashi. Da su ne ya bud'e company da sauran abubuwan shi na kasuwanci."


*** *** ***


"Dad ba mutum ne mai son siyen kadarori ba, wanda kullum ina mai bashi shawara kan siyen filaye da kuma shaguna ya bada haya, maganar shi bata wuce yana da dukiyar da ba yaran shi ba har jikokin shi zasu ci su raga wani abu daga ciki".


"To yanzu gashi karon farko k'addara ta sauka kan company, kud'in da aka aje account sune ake cirowa ana lalurorin yau da kullum, dai-dai da gida daga wannan da muke ciki sai naku babu ko da filin da za'ayi kiwon kaji a ciki, duk wannan ba shine tashin hankali ba sai tahowar labarin tabbacin Alh Ibrahim yana raye don Alh Taheer abokin Dad da akayi d'awainiyar asibiti dashi shi ya ganshi ra'ayul ayni a Abuja kuma ya bashi tabbacin yana nan tafe kwanan nan".


(Ba Zajlah da ake ba labari ba ni kaina Jegal mai d'aukar rahoto ba k'aramar razana nayi ba, don sai da na zaga toilet, _lolx_).


Cikin razana ta tayar da kai ta kalli Mum "yana raye fa? To ya akayi haka? Anya ko inda akace anyi gobarar nan yake?".


"Tabbas an ganshi kuma shine, don har lambar Dad ya kar6a don ya kira su gaisa, sai dai ko da yakira ni na d'auka muka gaisa saboda Dad na wanka lokacin, bayani nayi mai kan cewa Dad na asibiti bai da lafiya, ba akan komai ba sai don gudun kar yakira Dad yasan da maganar yayi silar tashin ciwon shi farat d'aya a koma sabuwar jinya, to kinji babbar damuwa ta da kuma tashin hankalin mu ni da Son wanda muke neman mafita kamin abin yazo ga kunnen Dad".


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hala Mum kud'in za su kai nawa?", cikin tsananin tashin hankali take maganar don jin take yi tamkar ita wannan musibar ta fad'awa.


" kud'in wannan lokacin zasu kai million hamsin, kuma Son yace abinda ke cikin account ba zasu biya kud'in mutumen ba, sannan ba muda masaniya akan komai yanzu Zajlah har sai ya shigo garin nan munji daga gare shi".


"Mum ina da shawara d'aya akai in har hakan zai yuyu, saboda a kammala kud'in mutumen kamin ya iso".


"Zajlah ba muda wata mafita ta kud'i kuma babu wata kadara da zamu saida mu cika mai kud'in shi, shi ne abin dubawa".


"Mum ko mu muke da kadara da zamu saka kasuwa a biya komai cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya ji mu ba".


"Ta wacce hanya Zajlah?.

   "Mum gidan mu za'a saka kasuwa a saida mu ko mu dawo nan gidan mu zauna d'ayan part d'in da ba kowa a ciki".


*** *** ***


Maganganun ta ne yasa yaja birki ya tsaya don jin me za ta furta, abinda ta fad'a ne ya sa yaja ya yi turus, "me yasa duk iya tunanin mu ni da Mum bamu kawo hakan a zuwan mafita ba?, garin ya ya ta fi mu nazari da hangen nesa? Lallai tabbas ba girma ne hankali ba, ba shekaru ne tunani ba, dame yarinyar nan ke aiki cikin kwanyar ta?".


Duk shi kad'ai ke yiwa kanshi wad'an nan tambayoyin sanadiyyar mafita da ya ji Zajlah ta samo wanda iya nazarin su basu kawo hakan ba.


Mum ce ta janyo Zajlah ta rungume kan jin dad'i tana hawaye, sai albarka take saka mata wanda take jin tamkar ta maida ta ciki kan irin son da take yi mata da kulawa da dukkan damuwar ta.


Suna hakan ne ya yi sallama ya fad'o falon, wanda daka kalleshi zaka hango walwala, farin ciki, annashuwa kwance saman fuskar shi, har k'asa ya durk'usa ya gaida Mum, cikin farin ciki ta amsa fuskar ta sake.


"Sannu da zuwa", cikin sanyin muryar ta ta furta hakan sannan ta wuce zuwa d'akin Saudat da Mum ta gaya mata tana fama da zazza6i, kuma tana so ta basu guri su gana da junan su.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                      *(36)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



      Bayan ficewar ta ne Mum ta kai duban ta zuwa ga Alamein had'e da furta "ka fara ganin irin alkhairin da nake hango ma a cikin zamantake warka da yarinyar nan? Wallahi na yi imani da Allah da wata ce ko siyar da gidan kace za kayi sai kunsha artabu da ita, in ma bata ce sai ka sake ta ba".


"Wannan zamanin da ake ciki mun kawo ga6ar da yawancin y'an Mata basu cika yin aure saboda Allah ba, farko kana zuwa neman yarinya za kaji ana fad'in da wacce mota yazo? Daga hakan sai kaji iyaye na fad'in ai ko ki auri abinki ance yana da hankali da nutsuwa, nan ko nutsuwar kud'i ce ba nutsuwar Allah da Annabi ba".


"Ina mai baka shawara daka rik'e yarinyar nan amana domin ta wuce k'ask'anci yanzu daga gare ka, ina sane da har yanzu babu wani cigaba a cikin rayuwar auren ku saboda bak'ar ak'idar da ka saka a zuciyar ka na k'yamatar talaka".


Cikin razana da mamakin ina tasan irin zaman da suke yi yasa ya tayar da kai ya dube ta. "Kar kayi mamaki kuma kar ka zargi Zajlah da abinda ba haka bane, don tun auren ku wata magana data shafe ka bata tab'a had'a ni da ita ba".


"Na dad'e da fahimtar hakan tun ranar da muka je gidan su yiwa mahaifin ta sallama, kuma ko kukan da take yi nasan da biyu take yin shi saboda akwai abinda kayi mata".

    "Yanzu dai dabara ta rage gare ka ta yanda zaka shawo kan matar ka ku zauna lafiya, don yanzu ka tabbatar da ita ba k'ashin yarwa bace".



****  *****


Ko da ta shiga d'akin Saudat bacci take yi, hakan ya sa ta nemi guri ta zauna ta bud'e datar wayar ta ta hau whatsap, yanda taji ana comments kan wani novel  ( *AL'ADUN WASU, BATUL MAMMAN*) ya sa ta yi ta tambayar farkon buk d'in, nan take aka tura mata saboda musha karatu akwai kula juna.


Datar ta rufe sannan ta hau karatun littafin, sosai buk d'in ke saka ta nishad'i da walwala, dariyar tace ta tayar da Saudat daga baccin da take yi, had'a ido da suka yi yasa tasha jinini jikin ta saboda jiran saukar rashin mutunci kwando-kwando.


Kafad'ar ta ta dafa had'e da furta "matar Brother me ya saka ki nishad'i haka kike ta dariya?".

    Cikin sanyin jiki ta gaya mata har da nuna mata buk d'in, "kai an baro ki baya ai ni yanzu kullum cikin zuba ido nake in matsu ba'a turo cigaban ba, saboda novel d'in yayi gaskiya ga dariya cikin shi sosai".


"Aiko da zan iya dana ajiye karatun har tagama duka, saboda banson jira gaskiya matsuwa nake yi".


"Ni ko nafi so ana yi ina biya kodon y'an comments dasu ke baka labari kuma ban iya karatu in yayi yawa".


"Tabbb ai ina ga babu group d'in da suka kai musha karatu comments, kuma gasu da kula juna gaskiya, oh! kinga na manta, ya jikin ki?".

  "Ai naji sauk'i sosai don kan ya daina ciwo", hakan suka zauna suna ta hira wanda ni kai na Jegal nake mamakin hakan.


***** ****


Zaune yake jugum yana sauraren maganganun Mum had'e da nazari kan su duk jikin shi ya yi sanyi.


"Abu na gaba shine ka dai ga yanda Allah ya sako mana jarabawa farat d'aya wanda bamu yi zato ba kuma bamu yi tsammani ba to ya kama ta ace ka natsu kasan me duniya take ciki, a wancan lokacin in har ina lurar da kai wasu abubuwan sai dai ka rik'a biyar zugar mahaifin ku na rud'in dukiya, yanzu gashi duk tak'amar ku da ji da kan ku da izzar ku ta rushe lokaci guda wanda baku da wata dabara sai yanda wanda ya baku ya yi daku".


"A zamantakewar rayuwa ana so mutum yasan k'ima da darajar d'an Adam, ba akan komai ba sai don gama wa da duniya lafiya, wanda ka gani talaka haka Allah ya so ganin shi, ba don ba ya son shi ya yi shi hakan ba, sai dai ban-ban cewa tsakanin rayuwa da kuma hankalta".


"Yanzu ka duba kagani yanda Allah ke baiwa kafiri kud'i ya hana wa musulmi, kuma fa ba don ya fi son kafiri d'in akan musulmin ba, a'ah don ya gwada k'arfin ikon shi ne da kuma tsara abubuwan shi yanda yaso. Da wuya kaga kafiri yana fama da talauci tamkar musulmi, ko yaushe za ka ganshi cikin jin dad'in rayuwa, to wannan jin dad'in na duniya shine ribar su gaba d'aya saboda lahira jahannama ce mazaunin su".


"Sannan kayi nazarin wacce Sana'a ta dace ka fara, saboda yanzu zama haka kawai ba naka bane, don kaga kaine Babba kuma kaga yanda mahaifinku yake, ko babu ciwo akwai yanayin girma daya kamata kad'auke wa mahaifinka wasu abubuwan".


"Ba matsala Mum bari zan binciki Imran da Salis gobe muyi shawara, daga nan asamu mai sayen gidan, in an kammala kud'in sai muga abinda yayi saura sannan asan Sana'ar da za'a kama".

    "To Allah yasa a fara a sa'a, Ameen ya furta a taka'aice had'e da dogon nazari na rayuwar shi.


Duk wad'annan abubuwan da Mum ke jerowa har ga Allah yasan hakane, amma me yasa a wancan lokaci bai yi duba zuwa gare su ba? "Giyar kud'i", hakan wata zuciya ta bashi amsa.

     Lallai tabbas ya yarda da hakan, saboda yasan in can inda aka fito ne bazai tsaya ya saurari Mum ba har maganar ta tayi tasiri akan shi ba kamar yanzu.


Bayan sun gama tattauna wa ne ya k'arasa gurin Dad suka gaisa ya yi mai ya jiki, sannan suka d'an ta6a hira, duk da ba magana mai tsawo yake iya yi ba sosai.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                        *(37)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


(Ina mai baku hak'uri da rashin ji na kwana biyu, wannan ya faru ne sanadiyyar nepar unguwar mu data samu matsala, saboda haka ba zaku rik'a ji na kullum ba har sai an samu gyarawa, nagode da kulawar Ku wad'anda suka kira ni, luv y'all).



*WASHE GARI*


        Wata shawara ce ta yanke a ranta bayan ta kira Salmat ta gaya mata abinda ke faruwa, inda ita ma ta tausaya masu sosai had'e da k'ara k'arfafa mata gwuywa kan abinda za tayi.

 

Bayan ta gama breakfast ne ta jera a dining table sannan ta fad'a wanka ta fito ta kimtsa, sanin cewa yanzu yana gurin Dad ya sa ta shiga ta kimtsa d'akin na shi kamar kullum sannan ta fito ta ci abinci.


*11:00am*

Ta fita zuwa gidan Shema'u mak'ociyar ta,  "yau wace rana Zajlah a gidan nan?", cewar Shema'u.

 

"Kai Anty shaidar da za kiyi min kenan, yanzu fa zuwa na na uku kenan gidan nan, ai gara ni kefa zuwan ki biyu".

    Da hakan dai suka gama zolayar juna sannan suka gaisa, jugum ta yi kamar kar ta furta abinda ya kawo ta, sai kuma take tunanin duk duniya bayan Salmat babu wanda za ta iya gayawa halin da take ciki bayan Shema'u d'in, saboda ta yaba da hankali da nutsuwa irin tata, kuma ba mace ce mai yawan surutu ba ga alama za tayi rik'on sirri kuma gashi za ta girme ta da kusan shekara shida ko bakwai, sai da ta gama nazarin ta Shema'u na gurin kawo mata ruwa da d'an lemo ta dawo kenan take furta mata abinda ke tafe da ita kan ta yi mata magana da masu sayen kayan d'aki.


"Ke ko Zajlah me zai kai ki siyar da kayan d'akin ki?, duka fa aure ko wata hud'u bai yi ba za ki siyar da kayan d'aki". Nan ta kora mata bayanin abubuwan da ke faruwa, sannan ta bata tabbacin za ta sa a nemo masu siya.


"Kinga ko banyi mutunci ba wallahi ban shiga yiwa Mum Allah ya tsare gaba ba da abinda ya faru, Baban su Taheer d'ai yaje dubiya sau biyu".


"Yanzu ko daga nan can zan shiga", "ina ga bara in d'auko hijab d'ina muje tare in dawo". Hakan suka fice zuwa gidan su Alamein, Shema'u ta yi jaje da Allah tsare gaba ta koma gida.


***********


Su Imran suka samo masu sayen gida aka yi ciniki suka sai da inda Alamein ya nemi su bashi kwana biyu ya kwashe kayan shi daga gidan, da hakan suka fice zuwa gidan su shi da su Salis.


Kamar yanda Shema'u ta yi alk'awari hakan ya sa ta nemo masu siyen kayan d'aki aka dace da masu siyen su cikin daraja Zajlah ta sai da, kayan kitchen sai kayan falo da keken d'inki kawai ta bari.


******


6angaren Alamein kuwa yaje gida gurin Mum sun tattauna yanda abubuwan suka kasance, sannan ya d'ora da gayawa Mum tasa a gyara masu d'ayan part d'in gobe da safe zai samu way'anda zasu kwaso masu kayan su, da hakan ya wuce gidan shi.


Motsi ya ji a kitchen alamar Zajlah na ciki, yana son yashiga ya gaya mata ta kimtsa kayan ta zuwa gobe za su koma gidan Mum kuma yana jin nauyin yanda zai yi mata magana, saboda tun zamantakewar su maganar arzik'i bata ta6a had'a su ba, hakan ya sa ya tunkari kitchen d'in gaban shi na dukan tara-tara.


Alamar mutum ta ji a bayan ta ta juyo ta ganshi tsaye ya jingina da k'ofa ya sako mata ido, "sannu da zuwa", cikin sark'ewar murya da in ina ta furta hakan.


Da sakewar fuska ya amsa mata sannan ya d'ora da cewa "kar kiyi girkin dare saboda yau za mu yi parking kayan mu gobe a kaisu can, don an sayar da gidan kamar yanda kika buk'ata".

   "Ba matsala Allah ya kai mu lokacin", da hakan ya wuce d'akin shi.


Bayan ta gama girkin ne ta ajiye mai nashi ta d'ibi nata ta ci, sai ta yi zugum tana so taje d'akin shi ta had'a mai kayan shi guri d'aya amma bata son abinda zai had'a ta dashi guri d'aya kuma tasan yanzu yana d'akin bai fita ba.

Hakan dai ta daure ta nufi d'akin shi, ta fi minti biyar bakin k'ofa tana sak'a yanda za ta Shiga d'akin, jin motsin zai fito yasa ta k'wank'wasa k'ofar.

   Mamaki ya hana shi bud'e k'ofar ya yi zurum, sai da ta buga a na ukun sannan ya murd'a k'ofar ya ra6e gefe d'aya. Tsaye ta yi tana wasa da yatsun hannun ta sannan ta furta, "kayan kane zan had'a ma".


Hanya ya bata alamar ta shiga d'akin, k'ofar ya rufe ya dawo ciki shi ma, ganin hakan ya sa gaban ta ya bada daram!, saboda ta zata fita zai yi don da shirin shi ta ganshi.


"Hala kin kammala na ki kayan guri d'aya?", tambayar ce ta doki dodon kunnen ta. "Eh" ta furta a gajarce.


"To bara in kama maki aikin saboda suna da yawa".


"Ah da ka wuce kawai ai zan iya tunda ba girkin dare zanyi ba", ta furta hakan ne saboda ta fi so ya fita ya bata guri tayi aikin ta za tafi Samun sakewa, amma tasan zaman shi zai takura ta.

    Shi ma 6angaren Alamein gidan su ya yi niyyar zuwa ya turo Saudat a zuwan za ta kama ma Zajlah had'a kayan, to yasan in har ta zo to Zajlah za ta kama suyi aikin tare ne, amma da ta nuna za tayi ne ya sa ya fasa fitar.


Nan dai suka zauna jigum ba mai magana, shi ya yi k'arfin halin bud'e wardrobe yana jido kayan shi yana d'orawa saman gado, sannan ya bata umurnin ta d'auko akwati na ta jera kayan a ciki, ba k'aramin mamaki ta yi ba ganin yawan suturar shi kama daga manyan kaya zuwa k'anana.


6angaren turarukan shi suka koma ana jibga su guri d'aya, ta d'auko wani turare za ta ba shi yasaka a wata jaka karaf hannun su ya had'u guri d'aya, wani shocked da suka ji ne ya sa cikin sauri dukan su suka janye hannun su kowane a tsammanin shi d'ayan ya rik'a, hakan yasa kwalbar ta sauka k'asan tiles ji kake yi tarassss, da sauri ta ja baya sai ga k'afar ta saman kwalbar da ta fashe ta watsu a gurin.


K'ara ta saki da k'arfi ta rik'e k'afar tana yarfe hannu, da saurin shi ya zo gurin ta ya bata umurnin ta zauna bakin gado, dak'yar ya samu ta tsaya ya cire mata guntun kwalbar inda jini ke ta zuba, nan ya samu ya yi mata dressing gurin had'e da duban ta irin yanda take ta zubar hawaye tana cije le6e had'e da runtse ido.


Nan ya barta ya je ya kwashe kwalbar ya k'arasa had'a kayan, sai murmushi yake yi shi kad'ai ganin yanda ta yi kuka had'e da shagwa6a tamkar wata k'aramar yarinya, hakan ya sa ya ji ta burge shi.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                      *(38)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



 *washe gari*


       Jakar ta ta hannu kawai ta d'auka ta fice daga gidan tunda ya gaya mata zai samu way'anda za su kwashe kayan duka akai gidan su, ko da ta fita ko ruwan Lipton bata sha ba saboda ya gaya mata kar ta kunna komai na amfanin girki, kuma Mum ta kira ta gaya mata cewa za ta yi girkin safe dasu.

     Karfe *10:00am* ta shiga gidan, bayan ta gaida Mum ta yi mata jagora ta k'ara duba jikin Dad had'e da gaida shi sannan suka dawo falo suka zauna. 

   "Meke damun ki naga kina Jan k'afa?", Cewar Mum.


Nan ta labarta mata abinda ya same ta da suna gyaran d'aki, jajanta mata tayi ganin abin da d'an sauk'i.


"Ina Saudat halan? Banji motsin ta ba".


"Ta ji sauk'i yau ta wuce skul, kinsan tun ciwon Dad bata koma skul ba, to suna ta shirye-shiryen exam ta k'arewa shiyasa yau ta je", "ok Allah ya taimaka".


"Amein", ta furta sannan ta had'awa Zajlah kayan kari ta kai mata falon ta saboda tasan ba za taci  tare da su ba.


*********"


6angaren Alamein kuwa ba k'aramin mamaki ne ya cika mai ciki ba da ya shiga d'akin ta da sunan fitar da na ta kayan ba, saboda wayam ya gani ba komai kuma ya san dai ko da aka kawo ta da kayan d'akin ta, asali ma gaban shi aka had'a su saboda ranar Mum ta takura shi dole sai ya tsaya gidan har a k'are aikin sannan in fita zai yi ya fita.

    D'akin ya gani da alamar an d'auke kaya a gurin, to ko ta kai kayan ta ne wani gurin? Ko kuma ta sa ankai mata can gidan? Ganin bai samu amsa bane ya sallami masu kwashe kayan daga d'akin ta, saboda akwatunan tufafin ta tun safe ta saka almajirai suka kai mata, kujeru kuma da sauran tarkace dama ya sa an fita dasu.


Ba'a gama ba sai kusan k'arfe d'aya na rana, saboda wasu na kwashe wa suna kai gidan su can kuma da masu had'awa. 

    Dama part d'in da aka basu babban falo ne mai d'auke da d'aki biyu da suke fuskantar juna kowannen su ciki da falo sai toilet a cikin su, kamin a Shiga falon akwai kitchen da store, sai kuma 6angare d'aya toilet d'in tsakar gida.


D'aki d'aya aka saka mata na ta kayan a falo sai katifa uwar d'aka, shi ma aka saka mai na shi kayan d'ayan d'akin.


Da hakan aka kammala komai na gyara gurin. Zajlah da Saudat suka taya Mum girkin dare sai da suka gama ne sannan ta shiga part d'in su ta yi wanka akan tsabar gajiyar da take ji, abinci ta ci sannan ta je ta kwanta saboda dama Mum ta sako masu nasu wanda dashi ta shigo ta d'ibi na ta ta ajiye mai sauran.


Bata fi minti goma da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da ya shigo bai ji motsin ta ba hakan ya sa ya ci abinci ya yi wanka, jin ya yi yana son yaduba ya yanayin k'afarta yake, da hakan ya doshi d'akin ko da ya shiga tana kwance uwar d'aka saman katifa daga ita sai wata night gown mai d'an sharara sai dogon wando gashin kan ta ya bazu saman filon da ta yi matashi dashi, kallo d'aya ya yi mata ya kauda kai saboda wani abu daya ji ya tsirga mai, kuma bai ta6a ganin mace a irin yanayin da ya ganta ba, bakin katifar ya dawo ya zauna ya kai duban shi ga k'afarta yaga gurin har ya soma haushi kad'an, hannu ya kai zai ta6a gurin kuma ya fasa daga hakan ya zabura ya fice daga d'akin tamkar wanda aka tsikara.


********* 


Tana tashi da asuba ta gabatar da sallah had'e da azkar d'inta sannan ta koma saman katifa ta zauna saboda ba aiki za tayi ba don Mum ta gaya mata da safe za'a kawo masu breakfast, tana so ta shiga part d'in su ta taya Mum aiki kuma tana ganin ta yi sauko dayawa, don tasan saurin karyawar su gidan k'arfe *10:00am*.

    Kud'in ta ta jawo ta irga ta koma maidawa ta ajiye a tunanin ta lokacin buk'atar su bata yi ba. Bugun k'ofa ta ji ya sa ta zabura ta fito ta bud'e, Mama talatu ce ta kawo masu kayan breakfast bayan ta kar6a ne ta gaida ta ta koma daga ciki, abinci ta ci sannan ta shiga wanka bayan ta kimtsa ne ta shiga gurin su Mum.


********


Bayan azzahar ne Salmat ta kawo mata ziyara, bayan ta gaisa da Mum ne take tambayar jikin Dad inda Mum ta gaya mata ya samu sauk'i sosai. Part d'in Zajlah suka koma aka baje sai hira ake ta zabgawa had'e da shawarwarin abubuwan da suka shafe su.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                         *(39)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



    Akwana a tashi yau satin su biyu kenan a gidan su Alamein, wanda har yanzu babu labarin Alh Ibrahim sai dai a ko yaushe suna masu sauraren zuwan shi, jikin Dad kuma ya yi sauk'i sosai sai dai bai iya doguwar tafiya haka kuma bai cika son doguwar magana ba don in ta yi tsawo ji yake yi tamkar numfashin shi ya d'auke.

   Kusancin su ya sa abubuwa sunyi sauk'i sosai a zamantakewar su, saboda Alamein na ba ta kulawa gwargwado, kuma wani lokaci sukan had'u part d'in su Mum a baje ana ta hira, amma fa baza su iya hira tsakanin su ba saboda kowa tsorace yake da wani.


*********


6angaren Zajlah an samu k'aruwar wayewa a gare ta ta hanyar Anty Shema'u da kuma group-group na whatsap musamman na kwalliya da ake turo videos na kalar kwalliya iri-iri, wasu ma in an turo bata gane ba to gidan Shema za taje tayi mata bayani in ma ta kama ta zauna tayi mata to za ta yi mata da kanta.


Tun lokacin da aka yi mata aure Mama Asabe da Mama Inno basu zo gidan taba sai kwana biyu da suka wuce, koshi don ta dame su ne kan basu tahowa kuma Mum tasa baki shiyasa suka zo, inda taji dad'in zuwan su sosai.


******


Yau saura kwana biyu auren Yusrah da Imran, su Zajlah babu zama musamman da Mum ta mayarda Yusrah gidan kacokan, a cewar ta ita za ta shirya abar ta, duk wani kayan had'in gyara na jiki ko na Mata a tare Mum ke had'a masu shi wato Yusrah da Zajlah, inda Zajlah ta fito real amarya sai wani k'amshi suke zabgawa ita da Yusrah.


Kamar yanda Yusrah ta k'udurta ma ranta tun auren Zajlah haka ta gaya wa Mum cewa makarantar su Zajlah za'a yi mata walima saboda bata son bidi'o'in nan na raya Al'adu, ba k'aramin dad'i suka ji ba na za su ziyarci makarantar su, ko banza sun San cewa tsarin Malaman su da d'aliban na burge mutane da dama. A gurin walimar ne suke jin labarin auren Ustaz Yusuf da kuma Ustaz Lukman sati biyu da suka wuce, inda matar Ustaz Yusuf ke basu tabbacin har mazan su sun zo auren kuma tare da gudummuwa, nan suka yi masu fatar alkhairi aka k'are walima kowa ya kama gaban shi.


Washe gari bayan d'aurin aure ba'a gabatar da komai ba sai dare amarya ta tare a gidan ta dake ni'ima inda basu da wani nisa sosai da Salmat, Zajlah ne da Saudat suka tashi za su fice ta dafa kan Yusrah had'e da furta "muna jiran baby nan da wata goma, saboda ke ga su wance anji hud'uba ta sai wani tartsin yawu ake mana", tana maganar ne had'e da kallon Salmat tana murmushi.


Sanin cewa tsokanar ta ne take yi ya sa ta yi shiru ta k'yale ta sanadiyyar yanzu baki ya mutu ko dogon surutu bata so. Da hakan suka watse suka bar Yusrah had'e da yi mata fatan alkhairi.


*******


Bayan kwana uku ne da auren Yusrah Alh Ibrahim ya diro garin Jega, direct wayar Dad ya kira kuma akayi sa'a da babu kowa a tare dashi, kuma gashi su Mum basu yi mai bayanin komai ba. Wayar ya d'aga suka gaisa ba tare da yasan waye ba, daga baya Dad ke tambayar shi waye halan saboda bai gane mai magana ba, amsa ya bashi da cewa wani tsohon aminin shi zai kawo mai ziyara, ba tare da tunanin komai ba ya gaya mai address d'in gidan shi.


Suna gama waya Mum na doso d'akin na shi, nan yake gaya mata zai yi bak'o duk da bai san waye ba, ya dai ce mai tsohon aminin shi, take nan gaban Mum ya bada rass, saboda jikin ta na bata Alh Ibrahim ne, ganin jikin ta ya yi sanyi ya sa yake tambayar ta ko lafiya, cikin yak'e take bashi amsa da ba komai, "bara inje ad'an tanadi d'an abin motsa baki wa bak'on", da hakan ta fice daga d'akin ba tare data jira me zai ce ba.


Wayar Alamein ta kira had'e da gaya mai duk inda yake yayi sauri yak'araso gida. Lokacin yana tare dasu Imran suna process d'in wane business ya kama ta su fara, nan ya yi masu bayani da sauri ya wuce gida.


A gate suka had'u da juna dai-dai yana waya da Dad yana gaya mai gashi ya iso gidan, nan Alamein ya tsaya suka gaisa Alh na ta mamakin girman shi, da hakan ya yi mai jagora cikin fargaba suka doshi hanyar shiga falon. Sai yanzu Mum ke nadamar rashin gaya mai da basu yi ba, ba akan komai ba sai akan matsalar ciwon da yakan iya tashi farat d'aya wata babbar matsala ta samu, saboda ko dawowar su Alamein gidan bata gaya mai ansayar da gidan su bane, kawai ta ce mai wani gyara ake yi gidan in an gama za su koma, wanda ga wancan lokacin take hango hakan a zuwan mafita sai yanzu take nadamar aikata hakan.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:34 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                      *(40)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



     Alamein gaba Alh yana biye dashi suka shigo falon, karaf idon su suka had'e guri d'aya inda Dad ya yi mutuwar zaune, idon shi ya fara murzawa domin tabbatar da ba mafalki yake yi ba, bud'ar bakin shi kenan zai kira sunan shi wani irin tari ya taso mai, yi yake yi ba k'akk'auta wa, da saurin Alamein ya taso ya dafe mai gaba had'e da jero mai sannu ba adadi, Mum ce ta mik'o kofin ruwa Alamein ya bashi.


"Dad ka kwantar da hankalin ka duk abinda ake ciki munsani kuma insha Allah komai zai zo normal", Alamein kenan dake son kwantar wa Dad da hankali, saboda tsorace yake kar ciwon shi ya tashi. Cikin ikon ubangiji ba wani abu na tashin hankali daya samu Dad, sai dai daka ganshi kasan juriyar da ke tare dashi ba tashi bace shi kad'ai sai da ya aro wata. Mum kanta hankalin ta tashe yake, hakan dai ta jure ta baje ma Alh Ibrahim kayan motsa baki da abinci, bayan gaishe-gaishe ne na yaushe rabo Dad ya kai duban shi ga Alh Ibrahim had'e da furta "muna zaune kawai sai ga sak'on rasuwar ka ta risk'e mu, wanda bamu yarda da hakan ba sai da na garzaya da kai na kurmi sannan aka tabbatar min da hakan, sai kuma yanzu gashi ka dawo, meke faruwa halan?".

   Gyaran murya ya yi sannan ya fara basu labari kamar haka, "lokacin da wutar ta tashi gidan gaskiya bana ciki na fita siyen tea bakin titi, saboda akwai wani da Allah ya had'a jinin mu dashi wato Alh D'anjimma wanda kusan tare muke lamurran mu dashi, duk wasu abubuwa tare muke yi".


"Daren da wannan abin ya faru kuwa, muna kwance ciwon ciki ya taso ma Alh D'anjimma inda ya tada ni yake gayamin, hakan ya yi silar fita ta domin in sawo mai tea, don na ga koda ya kwanta bai ci komai ba, bayan na siyo mai tea ne na nufo hanyar dawowa kawai naga gidan ya kama da wuta sosai, wanda tsabar rud'ewa tasa na koma titin ban shirya ba, banyi aune ba kawai mota tayi watsi dani gefen hanya, nan mutumen ya fito yana neman agaji kan a taimaka mai amma ina hankalin mutane ya yi gurin ceton rayukan mutane da wuta ke ci, hakan mutumen ya cicci6e ni ya saka a mota daga hakan bansan me ya faru ba saboda loosing memory na da nayi, ina tare da wannan mutumen daya zamo ubangida a gare ni a cikin garin Abuja wanda na yi nema tare dashi har Allah yasa na samu d'an abin hannu na".


"Bayan y'an shekaru ne ya aura min d'iyar shi Binta wacce miji ya rasu ya bari da d'iya biyu tagwaye har sun girma, bayan auren mune muka samu k'aruwar yara uku wanda har lokacin bana tuna komai a rayuwa ta ta baya".


Daga baya ne ubangida na kuma siriki na Alh Usman ya aike ni Lagos gurin wasu harakoki na shi a hanyar dawo wa tane na samu hatsari wanda bayan farfad'owa ta na dawo hayyaci na, lokacin Husain da siriki na na gefe na ina masu kallon rashin sani, bayan an sallamo ni ne yake min bayanin abinda ya same ni".


"Bayan sati d'aya da hatsari na ne nake yawan mugun mafalkai wanda na rasa gane masu, sai dai suna tsorata ni sosai kuma abin yana da nasaba da abinda ya faru sama da shekaru Arba'in da suka wuce, sai yanzu nake hango illar abinda na aikata wanda son kai da rud'in shaid'an ya kai ni da aika ta hakan, sanadiyyar hakan yasa tunanin komawa gida ya dawo kai na, da hakan na gayawa suriki na zan je gida in dawo, daga nan na zarce asalin garin mu sokoto na yita bincike har na gano dangi na na asali, inda na nemi yafiyar gagarumin laifin da na aika ta zuwa gare su had'e da alk'awarin gyara akan( *BABBAN KUSKUREN DA NA TAFKA*, SIS RASH KARDAM)".


"A gurin kasuwanci muka had'u da Alh Taheer inda naji Jega rad'am a bakin shi, nan hira ta 6arke tsakanin mu har nake tambayar shi ko yasan ka, yake gayamin kai abokin shi ne, da hakan na kar6i lambar ka wanda gashi Allah ya yi had'uwar mu yanzu".

   Kowa falon ya jinjina wannan labarin na Alh Ibrahim, sannan Mum ta bashi nasu labarin bayan tafiyar shi, da hakan ya jajanta masu k'addarar da ta hau kan su, wanda har ya fara zargin kan shi da yana da nasaba da abinda ya samu Dad.


Cikin nadama k'arara a fuskar shi yakai duba zuwa gare su yana mai cewa "ina mai baku hak'uri da abinda ya faru, saboda bazai rasa nasaba da abinda na aika tane ya shafe ku ba".

    Cikin rud'ani da tashin hankali suka sako mai ido caaaa, wanda ya kasa had'a ido dasu ya nok'e kan shi k'asa.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                       *(41)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


sadiyajegal.WordPress.com


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



     Cikin rawar murya da fargaba Alamein ke jero mai tambayoyi, wanda bayan ido da Dad ke saki bai da wani abu da zai iya furtawa akan mutuwar jiki, inda dama tun shigowar Alh Ibrahim kawo yanzu kalma guda bai samu furtawa ba.


Nan Alh ya cigaba da bada labari kamar haka, "kamar yanda na gaya maku ni d'an sokoto ne to haka abin yake, asalin zamana nan Jega da kuma dukiyar da na barma na k'ara gaba to ba tawa bace hakk'in marayu ce".


"Kamar yaya, bangane ba", wannan karon Dad ne ya yi k'arfin halin jero mai wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali.


"Mahaifin mu ya kasance mutum ne mai dukiya a wancan lokacin, matan shi uku da yaran shi goma sha biyu, na kasance ni kad'ai gurin mahaifiya ta kuma ita ce ta farko a gare shi, ta biyu keda yara bakwai ta k'arshe kuma yara hud'u. Allah ya yiwa mahaifiya ta rasuwa tun ina da shekara bakwai a duniya sanadiyyar hakan na tashi wulak'ance a gidan wanda dai-dai da abinci sai mak'wabta sun bani ko kuma gidan abokai, da hakan na tashi har na girma ba wani canji na zamantakewa ta a gidan, ana hakan ne ciwon ajali ya kama mahaifin mu sanadiyyar hakan yaga cewa nine babba a cikin yaran shi yasa ya damk'amin duka kaf dukiyar shi a zuwan in rai ya yi halin shi in nemi malamai a raba mana gado, lokacin haukar k'urciya yasa na gudo da kud'in kaf saboda tunani na ta hakan ne zan d'ebe takaicin k'iyayyar da matan mahaifi na da y'an uwa na ke nuna min".


"Haka kawai raina ya bani in gudo Jega da zama, da hakan na shigo garin ina y'an sana'o'i na har Allah ya rik'amin wanda daga baya ne muka had'u dakai har mutunci mai k'arfi ya k'ullu, lokacin da abubuwa suka faru har na d'auki dukiya ta duka na baka nabar gari, wani k'anen mahaifi na ne yaji inda nake har ya aiko sau biyu yana nema na, hakan yasa na had'a komai na baka na yanke hukuncin zuwa gari mai nisa don ma kar aji labarin inda nake".


"Daga bayan nan ne nake ta mafalkai kan mahaifin mu na takure cikin k'abari yana rok'o na kan in d'auke mai wani k'aton dutse dake saman kanshi, ko in ganshi yana cemin wannan ce amanar da na baka. Da hakan hankali na ya yi mugun tashi kuma naji ina so in je gida sannan in dawo nan in kar6i hakk'in marayi in kai masu".


"Abinda yasa na furta ina da sila da abinda ya shafe ku kuwa shine, hakk'in marayu bazai ciyu kuma a zauna lafiya ba, saboda dukiyar kaf banda ko kwabo cikin ta in ba an raba gado bane an bani hakk'i na, saboda haka ina mai baka hak'uri da abubuwan da suka faru".


Nan kowannen su ya nisa had'e da jimamin wannan tarihi na Alh Ibrahim, nan aka yi lisafi kan abinda ya bada sai gashi kaf har kud'in gidan Alamein sun shige ciki kuma ana neman k'ari, sanadiyyar kud'in can baya sun fi na yanzun daraja sosai, hak'uri suka bawa Alh Ibrahim kan cewa yabari gobe yadawo za'a had'a kud'in, da hakan ya fice daga gidan.


**********


Ba k'aramin tausaya masu yayi ba kan k'addarar da ta hau Kansu ba, har ga Allah yana so yataimaka masu, amma yafi so ya raba su da lalura in yaso daga baya ya taimaka masu, saboda tabbas dukiyar maraya cin ta lalura ce, shi kanshi baiji dad'in abinda ya aikata ba, don da ya mutu hakan baisan da wanne ido zai tsayu gaban ubangiji ba, da hakan ya yi alk'awari a ranshi cewa da an raba gado an bashi nashi kaso zai dawo yakawo ma Dad saboda sun yimai halacci a zaman takewa musamman Baban Maryam wato Mum inda ya zamo tamkar mahaifin shi sanadiyyar amintakar shi da Dad.


*********


6angaren su Mum kuwa sabon nazari aka shiga ta neman mafita, "gaskiya Dad mutumen nan bai yi halacci ba, yanzu duk zaman takewar da kuka yi bazai iya yafe sauran kud'in da babu ciko ba?". Alamein ke wannan maganar cikin kumfar baki.


Murmushi Dad ya yi had'e da girgiza kai sannan ya furta "Son ko da yace ya barmin bazan yarda naci ta ba, musamman yanzu dana san cewa hakk'in marayu ce, yanzu abinda nake so dakai gobe kaje kasa ka motoci na biyu kasuwa, nasan za suyi saurin shiga tunda sabon shiga ne, kabar min d'ayar ta ishe ni lalurar yau da gobe".


Baki ya bud'e da niyyar yin magana hannun Dad ya dakatar dashi, "kayi yanda nace kawai", yana maganar yana murmushi, da hakan ya tashi ya koma d'akin shi ya bar su jugum a falon.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                     *(42)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



Washe gari Alamein ya samo mai siyen motocin Dad saboda suna sabon yayi don kaf garin Jega su biyu ke da irin motocin, da hakan aka kammala ma Alh Ibrahim kud'in marayi aka bashi ya wuce da alk'awarin sai sun ganshi.


Iya damuwa Mum da Alamein sun shiga wanda ya zamo Dad Allah ya sako mai tawakkalin da basu yi tsammani ba don shi ya zamo mai rarrashi a gare su, (ohhh! Duniya juyi-juyi kwad'o ya fad'a ruwan zafi, abin da mamaki wai liman ya auri karuwa).


A cikin ran shi gaba d'aya ji yake yi ya tsani dukiyar shi duk da ya biya hakk'in marayi, sai yana ganin d'an abinda ya yi saura hannun shi tamkar wata k'addarar za ta iya fad'a mai nan gaba. Da hakan dai ya kwantar masu da hankali kowa ya kama gaban shi had'e da tunane-tunanen miye mafita.


***********


Bayan kwana uku ne da faruwar wannan lamarin Zajlah na d'aki tana wasu d'inkuna da Shema'u ta kawo mata Alamein ya shigo d'akin wanda ko sallamar shi bata ji ba ganin shi kawai ta yi gaban ta, d'an zabura ta yi alamar razana.


"Lallai na tabbatar in kina d'inki ba ki jin motsin mutum, sau uku ina sallama shiru".


Gaida shi ta fara yi sannan ta d'ora da cewa "wallahi banji bane", hakan ya samu gefen katifar ta ya zauna ya yi shiru, ganin hakan ita ko ta basar ta cigaba da d'inkin ta.

    Ido ya zuba mata yana kallon yanda take sarrafa keken d'inkin sannan ya furta "ah ashe k'afa ta yi sauk'i tinda har ana iya d'inki da ita", "eh ai tin ranar ta yi sauk'i".


Daga hakan kowannen su ya yi shiru saboda rasa takamemen me za'a fad'a, d'azu ne Salis ya kira yake gaya mai Salmat jiki ya yi tsanani kullum cikin amai da k'arin ruwa take, nan yake jajanta mai had'e da gaya mai za su shigo duba jikin na ta, to shine yanzu yake son gaya mata ta shirya suje amma ya rasa ta ina zai kamo zancen, shine yake ta kame-kame.


"In kin k'arasa aikin zuwa bayan azzahar kishirya muje duba jikin Salmat, d'azu Imran ke gayamin bata ji dad'i ba kwana biyu".


"To" ta amsa a gajarce ta cigaba da d'inkin ta, hakan ya sa ya ja jiki sum-sum ya fice daga d'akin kamar wani munafuki.

    Ranar da za suje yiwa Baban ta bankwana kawai ta yi mata sak a rai, "ai ko giyar wake nasha bazan k'ara siyo ma kaina wulak'anci ba, hanyar mota daban ta jirgi daban", hakan ta furta a fili sannan ta yi wani gajeren murmushi na tunawa da message d'in da ya yi mata bata San ya za ta bud'e ba har yaci zalin ta ranar, saboda in har bata manta ba ranar da Salmat da Yusrah suka zo gurin ta har soyayya ta k'ullu tsakanin Salis da Salmat to ranar ne Yusrah ta koya mata yanda ake text message, don ba wai wasik'ar ce bata iya ba a'ah kan wayar ce bata sani ba, wanda sai ranar ta bud'e message d'in da ya turo mata.


*********


Tana gama girkin tane ta d'iba ta kaiwa Mum, saboda dambun shinkafa tayi Wanda ya ji kayan had'i da zogale, dama in tayi girkin marmari tana kaiwa su Mum, nan take gaya mata za taje ganin Salmat bata jin dad'i hakan ya sa Saudat tace tana zuwa suka fice tare, saman titi suka samu napep suka wuce.


*********


6angaren Alamein kuwa har ya dawo daga masallaci ya yi wanka ya kimtsa bai ji motsin Zajlah ba, hakan ta sa ya je d'akin ta, amma ga mamakin shi yana murd'a k'ofar ya jita rufe. Part d'in Mum ya wuce bayan sun gaisa yake ce mata ina Saudat halan?, amsa ta bashi da cewa ta raka Zajlah gidan Salmat, hakan ya ja motar shi ya wuce mamaki fal ranshi, amma kuma yasan wani 6angare tana shakkar fita dashi ne saboda gudun wasu abubuwan, amma duk zille-zillen ta bazai bari ta dawo a napep ba.


**********


Shigar su gidan kenan ana cire mata k'arin ruwan da aka saka mata, nan suka mata sannu suka zube a falon, wanka ta shiga ta fito duk ta jeme kan laulayi, dambun da Zajlah ta zo mata dashi ne ta saka mata, kad'an ta ci taji zuciyar ta na tashi ta ajiye, duk tsiyar da Zajlah ta so yi mata ta rushe saboda ta tausaya mata ganin yanda ciki ya mayar da ita gwanin tausayi.


Suna zaune suka ji shigowar Salis da Alamein, a falon suka zube duka, "lahhhh Brother za ka ma zo baka gaya mana mu jira kaba?", fad'ar Saudat.

    Ido ya bi Zajlah dashi suna had'awa ta nok'e kai. Alamein ne ya yiwa Salmat ya jiki had'e da mamakin yanda bakin ta na tsiwa ya mutu. Sai bayan la'asar ne Imran ya kawo Yusrah, nan suka baje ana ta hira inda mazan suka fita.


Bayan isha'i ne suka shigo gidan su uku, abinci suka ci sannan kowa ya yi haramar zuwa gida, inda Alamein ya kasa ya tsare wanda ya sa dole Zajlah ta bishi ita da Saudat suka koma gida ba don taso hakan ba.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa ```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                       *(43)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


Awanni sun wuce kwanaki sun wuce wanda abubuwa da dama sun faru, su Mum  an fara shiga rayuwar k'unci komai sai manage, da hakan aka sallami duka y'an aikin gidan saboda zaman su na k'arin wasu abubuwa Mama Talatu kawai aka bari.


*********


Yanzu ne take ganin ya dace ta taimaka ma Alamein saboda ko mota babu hannun shi, abincin gidan kanshi ya sauya, saboda ga nasu yanayin kuma ga yanayin k'asa wanda ya shafi kowa, duk inda ka zaga za kaga gidan da aka saba tafiyar da abubuwa 80% yanzu sun dawo 40% saboda yanayin k'asa, abin kawai sai addu'a.


********


Bayan sun karya ne ta Shiga gyara d'akin Alamein kamar kullum, zaune ta isko shi saman kujera ya yi zugum ya saka takardu gaban shi ga alama yana cikin damuwa.


Nan ta gaida shi ta wuce ta fara gyara k'uryar d'akin, ko da ta fito falon yanda ta barshi hakan ta tarar dashi, guri ta samu ta zauna sannan ta tattara dukan nutsuwar ta guri d'aya sannan ta jefo mai magana kamar haka, "meke damun ka haka?, bai dace ka saka ma ranka damuwa ba, kar ka janyo wani ciwo na daban".


Hankalin shi ya maida zuwa gare ta had'e da cewa "ya zanyi da raina kusan sati d'aya ina yawon neman aiki ban samu ba, kuma gashi takardu na sun yi kyau amma abu ya gagara".


"A tunani na me zai hana a ajiye neman aiki gefe d'aya a kama kasuwanci?, kana ganin yanda k'asar ta zama yanzu, way'anda ke saman ma tsige su ake saboda bincike ina aka ga damar d'aukar wasu ma'aikatan?".


Zurum ya yi baice komai ba saboda tuna lokacin da ya kori wani daga ma'aikatar su akan bada shawara kan cigaban su, inda ya tuna lokacin da yake neman yafiya gare shi kan yabar shi ga aikin shi wanda ko sauraren shi bai yi ba ya wuce, hakan ya sa ya ji tausayin kanshi da kan shi kan yanayin da yake ciki sai ga hawaye  shaaaaa.


Ba k'aramin rud'ani ta Shiga ba ganin yanda hawaye ke ambaliya a fuskar shi, zumbur ta mik'e ta koma d'akin ta sai gashi ta dawo da wata leda bak'a a hannun ta har lokacin hawaye yake yi, gaban shi ta je ta durk'usa had'e da mik'a mai ledar, handkerchief dake hannun shi ta kar6a tana shafe mai hawayen dake ambaliya a fuskar shi, saboda Zajlah akwai raunin zuciya.

 

Ledar ya kar6a ya bud'e, abinda ya gani ne ya sa ya tayar da kanshi cikin mamaki yana mai kallon ta, bud'e baki yayi zai yi magana ta yi mai alamar yayi shiru, nan ta d'ora da cewa "kayi shawarar wace Sana'a ce ta dace dakai, na baka su halak malak".

   Sakin bakin da Alamein ya yi yana kallon Zajlah ne har ta 6ace ma ganin shi ya sa na lek'a ledar na hango kud'i, wanda duk iya biyar kwakkwafi na na d'aukar rahoto naso insan ko nawa ne don in feso maku amma abin ya gagara.


Ledar ya k'ara lek'awa had'e da murza idon shi don tabbatar da abinda yake gani cikin ta, hawayen idon shine suka k'aru sai kuka yake yi tamkar wani yaro.


Kud'in ya d'auko ya nufi part d'in Mum ya tarar tana d'akin Dad, nan ya shiga da sallamar shi suka amsa sannan ya shiga, kud'in ya ajiye gaban su had'e da yi masu bayanin inda kud'in suka fito, dukan su baki suka sake suna masu tarabbabin yanda matar shi ta zamo mai halarci a gare shi duk da irin cin fuskan da ya rik'a yi mata.


"Je ka kiramin matar taka", cewar Dad.


Mum ce ta mik'e tana mai cewa bara ta kira ta da kanta, da hakan ta fice har part d'insu ta sako Zajlah gaba, wanda har ga Allah bata so yagayawa iyayen shi wannan abin ba, ta so yabar shi tsakanin su. Cikin jin kunya ta shiga falon ta nemi guri ta zauna tana mai gayar da Dad had'e da yimai ya jikin kanta na nok'e k'asa.


Gyaran murya Dad ya yi bayan ya kar6a mata sannan ya furta "na ga alkhairin da kika yiwa Son, muna masu taya shi godiya, amma zan so ki gayamin ta wacce hanya kika samu wad'annan kud'in?".


Nan ta yimai bayani kan cewa kayan d'akin ta ta saida sai kuma na d'inkin da take yi ana biyan ta. "Ai ko bai dace ki sai da kayan d'akin ki ba, da ki bari ak'ara duba abinda ya dace don har ina shawarar saka mota ta kasuwa musan abinyi".


"Dad wallahi babu komai, a dai saka mana albarka a cikin abinda za'a fara dasu", daga hakan ta tashi sum-sum ta koma falon Mum. 


Kowan nen su ya yi jugum saboda gaba d'aya ta kashe masu jiki, don basu ta6a tunanin hakan daga yarinyar ba, nan dai suka tattauna abinda ya dace Alamein ya yi da kud'in.


(Ni dai Jegal na yita baza kunne inji ko za su fad'i adadin kud'in da Zajlah ta bawa Alamein amma shiru abin tamkar had'in baki, don na hango su Hindatu shehu da Fati Salihu ana baza kunne, _lolx_).



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                         *(44)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



    Sana'a ya fara gadan-gadan inda ya shawarci Dad kan yayi zaman shi ya huta shi zai tashi da nema yanzu.

   Duk inda yake yanzu da tunanin ta had'e da muradin sauraren muryar ta yake, wanda sai ya ganta hankalin shi ke kwanciya, amma ya lura da ita yanzu wani basarwa take yi, bata cika shiga sabgarshi ba, asali ma indai ba d'inki take yi ba to tana part d'in su Mum don wani lokaci daga can za'a saka masu abinci ko da zai shigo gidan har ta rufe d'akin ta ta yi kwanciyar ta, hakan ba k'aramin damun shi abin yake yi ba.


********* 


Yau gidan su ta shirya za taje saboda ta kwana biyu bata je ba, nan ta dad'e tana hira da mahaifinta har yana k'ara yi mata nasiha kan hak'uri da halin da suke ciki har yana yi mata nuni da kowane bawa bazai kaucewa k'addarar shi ba, kuma ta rik'a mijin ta hannu biyu ta girmama iyayen mijin ta.


Bayan magrib ne aka aiko yaro ana sallama da Malam Abu, ita ko lokacin za ta shiga gurin Mama Inno ta yi mata sallama don tana son wuce wa gida, abin mamaki motar Dad ta gani k'ofar gidan su wanda ta yi mamakin hakan a ranta, sai kawai ta dake ta fad'a gidan su Salmat saboda tunanin ba shi kad'ai ne mai irin motar ba.

     Tana zaune suna hira da Mama Inno sai ga Naja'atu ta shigo da gudun ta tana gaya mata Baba yace ta fito ga mijin ta ya zo d'aukar ta, sai da safe ta yiwa Mama ta fice daga gidan tana ta mamakin wai Alamein ne ya zo d'aukar ta yau, mamakin ta bai k'aru ba sai da ta ganshi da Baban ta suna hira cikin girmamawa da mutuntawa, hakan ta shiga gidan su ta yiwa Mama Asabe sallama ta d'auko jakarta ta fito, nan Baban ta ya shige gida.


Gudun ta shiga gaban ta janyo ma kanta ya sa ta je bud'e k'ofar baya amma ta ji ta rufe, gaban ya bud'e mata sannan ta shiga badan ta so ba. Yau ko gaisuwa bai samu daga gare ta ba sai wani cin magani da take yi, saboda bata ma son irin yanda yake bibiyar ta kaita unguwa ko d'auko ta, wayar ta ta fitar had'e da kunna data tana charting.


Warce wayar kawai ta ji ya yi sai ta bishi da kallo kuma ta sadda kanta k'asa, saboda bata iya jurar had'a ido dashi. Wayar ya rik'a bincike ya ga group uku, na make up, mu koma kitchen sai musha karatu, contacts kuma Salmat, Saudat, Yusrah sai Shema'u ya gani.


"Kasan dai bincike ba kyau, kabani waya ta", cikin zumb'uro baki take maganar had'e da mik'o mai hannu.

  Wayar ya mik'a mata tana mik'o hannu ya rik'e ya d'ora saman sitarin motar yana murza yatsun ta, abinda ya tsirga masu lokaci guda yasa ya yi saurin sakin hannun na ta sannan ya d'ora mata wayar saman cinyar ta, daga hakan ba wanda yak'ara magana har suka iso gidan.


K'ofar motar ta rik'a za ta bud'e ta ji ta gam, sai da ya fita ya zaga ya bud'e mata k'ofar ya rik'o wayar ta da jakar ta inda har ta ji nauyin Baba maigadi daya bud'e masu gate, (nidai Jegal hab'a na rik'e nace sabon salo kiran sallah da usur, ina ruwan neman gindin zama, _lolx_).


*********


Ya dad'e yana bibiyar ta tun lokacin da ya rasa Zajlah lokacin tana zuwa school of health. Ko da ya yi tafiya ya dawo ne yake tambayar wani friend d'in shi dake aiki B.L.B plaza kan cewa ya dai na ganin yarinyar, nan yake bashi tabbacin sun k'are makarantar, bincike ya yi har ya gano gidan su yarinyar, inda bai son a kuma samun matsala ya rasa yarinyar saboda ya yaba da hankalin ta had'e da nutsuwar ta, sai dai ga alama za ta d'anyi ji da kai irin na masu kud'i.


Hakan dai ya ji ta kwanta mai a rai, da hakan ya gayawa iyayen shi kan yana so aje mai tambayar neman iznin ganawa da yarinyar.

   Manyan shi basuyi k'asa a gwiywa ba suka je gidan su yarinyar inda kuma magabatan ta suka bashi damar shigowa ya gana da yarinyar.


************


Tun da aka gaya mata cewa za tayi bak'o ta shirya tsab sai zaman jiran ganin bak'on na ta. Ba'a fi minti goma da shirin ta ba sai gashi an aiko tazo bak'on ta ya iso. Sit room d'in Dad na bak'i aka saukar dashi shi da wani friend d'in shi, hakan ta je suka gaisa, nan ya Isar da sak'on k'ok'on baran shi zuwa gare ta kuma ba laifi ta yi na'am dashi, nan yake ba ta labarin tun lokacin da ya fara son ta da kuma shakkar tunkarar ta kamar bazai yi nasara ba, da hakan hira ta 6arke tsakanin su.


Lokacin da zai wuce ne ya nemi tayi mai iso ga iyayen ta domin ya gaisa dasu, gidan ta shiga ta yi masu bayani sannan ta fito ta yi masu iso, bayan sun shiga falon ne suka gaisa da mahaifin ta, inda ya yaba da hankali da nutsuwar yaran kuma yana ganin y'ar shi ta dace.

    D'akin ta doso sanadiyyar y'ar ta data matsa sai ta zo sun gaisa da sirikin nata, suna had'a ido take gaban su ya bada rasssss!.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                         *(45)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



     Cikin azama ya zabura da k'arfi tamkar wanda ya zauna dama saman allura, wannan dattijuwar fuskar ba za ta ta6a 6ace mai ba.


"Koma ka zauna, ina zaka je?".


Nan ya gagara bata amsa saboda irin tsabar rud'ewar da yayi, cikin murmushin ta dake k'arawa kamilallar fuskar ta fara'a ta nemi guri ta zauna, "a cikin Ku waye sirikin nawa?". Farouk ne ya nuna Fadeel da yatsa yana mai Sosa kai.

       Shi ko Fadeel ji yake yi tamkar k'asa ta bude yanitse a gurin, tsabar jin nauyi duk da a wancan lokacin ya bata hak'uri.


Kawai ganin shi suka yi durk'ushe gaban ta yana mai k'ara neman yafiyar kuskuren da yakusa tafkawa. Har ga Allah bata so hakan ba, kuma ba don hakan da ya yi ba to tayi alk'awari baza ta fad'awa kowa abinda yafaru ba, amma sai gashi yana batun bayyana kanshi.


Mamaki ne k'arara a fuskar sauran mutanen da ke falon, kowa alamar tambaya fal a fuskar shi, muryar Mum ce ta daki dodon kunnen su yayin da take furta, "wannan abin ya riga ya wuce a guri na, kuma na d'auki faruwar hakan silar abubuwa da dama, saboda ta nan ne na samu sirika data zamo alkhairi a cikin iyali na, kuma ta hakan ne Allah ya had'ani da siriki na", nan ta k'arashe maganar cikin murmushi.


Fadeel ne ya tayar da kai ya kalle ta, sannan ya kuma nok'e kai, alamar tambaya ta hango fal a fuskar shi. "Wannan yarinyar dai yanzu haka tana gidan nan matsayin matar yaro na".


Daram! Ya ji gaban shi ya buga saboda jin Zajlah na gidan, duk da ya dad'e da cire ta a ran shi saboda hango irin nisan da ta yimai na tabbatar da ta yi aure.

        "Ni fa bangane ba sai wata magana kuke yi a dunk'ule wacce mu bamu fahimci ina kuka dosa ba, dama kinsan sirikin na ki ko yaya?", Dad ne ke yiwa Mum wannan tambayar.


Hakan ne ya sa ta kwashe abinda ya faru tsakanin ta da Fadeel ta gaya masu, inda jikin kowa ya yi sanyi musamman Saudat da tasha jinin jikin ta tana jiran ko ta kwana, amma ita gaskiya tunda bai kai da marin mahaifiyar ta ba tana son shi a hakan don ta hango nadama k'arara a fuskar shi, amma dai za ta jira taji daga iyayen ta.


"Kar ka damu kanka akan wannan abin, saboda zan iya cewa wani wa'azi ne na daban ya sauka akan mu duka, don yaro na bai wuce sati da marin wani dattijo ba muka yi karo da kai, kaga ko naka mai sauk'i ne akan na shi".


"Yanzu muna lokacin da y'ay'an masu kud'i basu cika d'aukar talakan mutum da wata k'ima ba, ko kuma sun d'auki cewa dukiyar su za ta sa su taka mutum son ransu kuma su taka banza, suna ganin bashi da wani tsayayye ko kuma a'ah bai da k'imar da za su dube shi da gashi tunda yana talaka".


"Shin shi yayo kan shi talaka? Ko kuma shi ya rok'i Allah yabar shi hakan? Ko kuma wani laifi ya yiwa ubangiji shiyasa ya barshi hakan?, ko d'aya, iko ne da kuma banbancewar ubangiji tsakanin bayin shi".


"Ni dai ina mai shawartar Ku da girmama mutum ko da ko baku San inda ya fito ba ta hakan na Ku iyaye za su yi daraja ko a bayan idon Ku, kuma indai ni na haifi Saudat na baka ita halak malak", tana duban Dad ta furta hakan.

     Sannan ta d'ora da cewa "Dadyn Alamein Allah yasa ban yi kaud'i ba", tana maganar tana murmushi.


Jikin kowa sai da ya mutu a falon, saboda yanda Mum bata d'auki lamurran duniya a bakin komai ba, da wata ce tabbas da hakan za ta gilma Katanga tsakanin Saudat da Fadeel.


"Ba komai Mumyn Saudat, Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairin sa", fad'ar Dad kenan da shi ma yake magana cikin sanyi jiki had'e da jin dad'in yanda Allah ya bashi mata mai hankali da nutsuwa, lallai tabbas ya yarda da akace in Allah ya baka mata ta gari to ka samu rabin addinin ka sai dai ka cika rabin tsakanin ka da ubangijin ka, kuma sai yanzu yake hango illolin gatan da ya yi nuna wa yaran shi don yasan ba don ita ba da yanzu gidan shi ya rushe gaba d'aya.


"Ku tashi ku koma sit room ku k'arasa zancen ku, siriki na Fadeel a gaida gida". Nan dai suka fahimci Mum Mace ce mai son raha.


Da hakan suka koma sit room suka cigaba da hirar su sai yabon Mum Fadeel da Farouk ke yi, inda ita ko Saudat ke jin dad'in yabon da akewa mahaifiyar ta.


**********


Yana falo yana kallo Zajlah ta shigo ta zauna saman d'ayan kujera sannan ta yi mai sannu da hutawa, bai amsa ba kawai ya taso ya zo saman kujerar da take zaune ya zauna.


"Ba ni aron wayar ki zan d'an yi wani abu da ita". Jin ya matse ta har cinyoyin su na gugar juna ya sa ta mik'a mai wayar, a zaton ta ta shi zai yi sai ga shi ya k'ara gyara zama, xender d'in wayar ta ya bud'e ya kamo pix d'in ta da Saudat ta d'auke ta kwana biyu da suka wuce, saboda in bata manta ba ranar ta dame ta da zolayar cewa ta had'u shiyasa ta matsa ta yi mata pix d'in.


Tsam ta zabura daga gurin ta koma d'akin ta falo ta kwanta saman kujera, sai mamaki take yi yanda yake shisshige mata kwanan nan, da kuma son kusancin shi da ita, duk yanda take kauce mai sai ya sako ta a lamurran shi, wanda ita ko ko kad'an bata son hakan.


(Tau fa Alamein sunan ka sorry, ni dai Jegal na tausaya ma daka bari Zajlah ta gano lagon ka). 



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                      *(46)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



    Alamein sosai yana ganin cigaba a cikin kasuwancin shi, abin kawai sai dai hamdala don yanzu ne yake jin shi mutum kamar kowa kuma yake sanin ya lamurran duniya ke tafiya. Haka kawai ya ji yana sha'awar siyo ma Zajlah wani abu saboda kyautata wa tsakanin su, musamman yanzu da yake ganin cewa da bazar tace yake rawa, in ya tuna cewa tun auren su kawo yanzu bai ta6a siyen wani abu ya bata ba har kunya yake ji, dai-dai da cefanen gidan bai san ya yake tafiya ba, ita ke yi ko Mum bai sani ba, tabbas yanzu yasan cewa ba k'aramin gata Mum ta yi mai ba, gashi duk abinda suke tak'ama dashi sun rasa lokaci d'aya amma gashi ADALILIN GATAN da Mum ta yimai na aura mai nagartattar mata basu shiga k'unci sosai ba, ba abinda yake so irin ya tsokane ta ta dinga fad'a tana cuno baki, wai ita a dole an ta6a ta, yanayin ta da yanayin maganar ta na burge shi, a hakan ya wuce B.L.B plaza ya yi mata siyayya sannan ya hau hanyar gida.


Da sallamar shi ya shiga gidan lokacin tana kitchen tana girkin dare, direct ya risk'e ta kitchen d'in, nan ta yi mai sannu da zuwa sannan ta juya ta cigaba da aikin ta.


"Ga wannan na siyo maki Zajlah", yanda ya furta sunan na ta ne yasa tsigar jikin ta tashi, ji take yi duk duniya ba wanda ya kaishi iya furta sunan ta. Ta so ta share shi kuma zuciyar ta ta kasa juren hakan, wai me yasa kwanan nan kusancin da yake yi da ita yake janyo mata jin wasu abubuwa a tattare da ita?, ko fita ya yi yanzu har matsuwa take yi bai dawo ba, tana so ta gansu guri d'aya yana tsokanar ta hakan na mata dad'i duk da ba wata doguwar hira ke had'a su ba.


Hannun ta ya kama ya damk'a mata ledar da ya shigo da ita, daga hakan bai saurare ta ba ya yi part d'in su Mum. Acan ne Mum take bashi labarin ashe mai neman Saudat ne suka yi karo ranar, nan ta zube mai yanda suka yi daya zo gidan, jikin shi ne ya yi sanyi da hakan had'e da al'ajabin wannan lamari, lallai tabbas Allah mai juya lamurran shi ne yanda ya so, yana nan suna hira da Mum ta k'are girkin ta ta shigo part d'in rik'e da kula data sako ma Dad tuwon semovita da miyar agushi ta ji kifi.


"K'arasa ciki ki kai mai y'ar albarka", cewar Mum kenan, da hakan ta wuce d'akin Dad saboda inda sabo yanzu kam ta saba don har zama take yi su yita hira ita dashi, bayan ta kai mai ne ta dawo falon lokacin Saudat ma ta fito nan suka baje ana ta hirar yanda auren Saudat zai kasance.


Kiran magrib ne ya tada kowa daga gurin domin gabatar da farali, part d'in su suka wuce inda ya yi alwala ya wuce masallaci ita ko ta fad'a na ta d'akin domin sauke farali.


*********


Bai shigo gidan ba sai da ya yi sallar isha'i sannan ya wuce ya yiwa Mum sai da safe ya koma part d'in su, abinci ya tarar a dining table kamar kullum amma bai ji motsin taba, hakan ya sa ya fad'a d'akin ta.


Zaune take saman sallaya tana karatun K'ur'an cikin k'ira'ar ta mai sanyi da kuma dad'in saurare inda take karanta suratu Luk'man. Saman katifa ya je ya kwanta yana sauraren ta har ta kai matsaya ta ajiye K'ur'anin sannan ta yi addu'o'in ta ta shafa inda shi ma Alamein ya taya ta shafawa.


Sallayar ta ninke ta ajiye ta had'a K'ur'anin ta da littattafan ta na azkar ta ajiye, sannu da zuwa ta yi mai wanda bai ko samu damar amsawa ba sai fararen idon shi daya bi ta dasu.


Towel ta d'auka ba tare data cire kayan jikin ta ba ta fad'a toilet, jimawa ta yi gurin wankan saboda ba taso ta fito ta tarar dashi a d'akin.


D'aure da towel sanye da hijab d'in ta ta fad'o falon sai kuma ta ja ta yi turus sanadiyyar ganin inda ta barshi bai tashi ba, sai ma wayar ta daya janyo yana latse-latse, basarwa ta yi ta wuce saman kujerar ta da take d'inki ta janyo jakar kayan kwalliyar ta tana shafa mai.


Tausayin ta ya ji ya tsirga mai, ba akan komai ba sai don ganin kowace Mace mai ji da kanta in tayo wanka saman mirror take zama ta yi kwalliya sa6anin ita data zauna saman kujerar keken d'inki.


Jin shi kawai ta yi ya rik'o jakar yana mayar da kayan cikin jaka, sannan ya rik'o hannun ta ya ja ta sai d'akin shi, galala ta saki baki ta bishi tamkar rak'umi da akala, bai tsaya ba sai gaban mirror d'in shi, ita ko ya janyo kujerar ya zaunar da ita, "daga yau ga gurin kwalliyar ki kuma ga d'akin ki", daga hakan ya juya ya koma d'akin ta.


Akwati nan ta ya janyo yayo d'akin shi dasu, baki kawai ta saki tana kallon shi har ya gama kwaso kayan ta kaf ya kawo d'akin nashi, har lokacin bata samu motsawa daga yanda ya ajiye ta ba.


"Bara in maki kwalliyar in ba zaki iya ba", kayan ya fitar na kwalliyar ta ya jera saman mirror d'in, kiciniyar cire hijab d'in ta ya rik'a yi hakan ya sa ta daddafe jikin ta, tana rok'on shi yabari ta kimtsa da kanta.


D'akin ta ya koma domin ya bata guri ta samu sakewa, saman katifar ya kwanta yana kallon videos na d'aurin d'ankwali.


Mamaki ne ya ishe ta na Alamein, tamkar ba shi ne yake hantarar ta yana kira mata dak'ik'iya kuma jahila ba, da mamakin shi fal a ranta ta kimtsa ta saka riga da siket d'in ta na atamfa sannan ta fito domin taci abinci.


Motsin da ya ji falo ne ya tabbatar mai da fitowar ta, hakan ya fito daga d'akin ya ganta zaune falon su ta saka filet d'in abinci tsakiya tana ci. Hannu ya saka suka rik'a cin abincin tare, sai satar kallon ta yake yi yanda yake ganin take tsantsara kwalliya kamar wacce ta shiga makarantar make up, gano cewa neman magana yake so ya sa ta k'yale shi har suka cinye abincin, na shi dake saman dining table ya d'auko ya zuba suka koma ci, da hakan ta tashi ta wanko hannun ta sannan ta fad'a toilet ta yo brush, d'akin shi d'in ta zauna saman kujera bayan ta d'auko wayar ta ta kunna data ta hau whatsap.


Da hakan ya risk'e ta tana charting ya fad'a toilet ya yi wanka, d'aure da towel ya fito inda take satar kallon shi, mutum ne dogo ba sosai ba mai faffad'an k'irji sai dai ba za'a ce mai mai k'iba ba kuma baza'a ce mai siriri ba, fari ne ba sosai ba yana da hanci har baka, sajen fuskar shi ke k'ara fitar da kyawon shi had'e da fararen idon shi tamkar madara, sumar kan shi bak'a ce wulik ta kwanta tamkar ta Fulani, ya fi yanayi da larabawan Sudan.


Firgigit ta dawo hayyacin ta sanadiyyar ruwan kanshi daya sharto mata a fuska, cikin jin nauyi ta nok'e fuskar ta tana latsar wayar ta, "ko in zo ki taya ni Shafa mai ne, na ga hankalin ki ya tafi a kallo na, kinga sankacecen saurayi", yana maganar ne cikin zolaya da kashe mata ido d'aya, still kasa tayar da kan ta ta yi sanadiyyar kama ta da ya yi tana yi mai kallon k'urilla (Zajlah kar ki bada irin su Anty Sis, Hauwa Jidderh, Salmatun Innah, Namcy Sardeeyer, da Wamsyl, masu cewa sun matsu Alamein bai shigo hannun ki ba, toh fa ko reshe ne zai juye da mujiya ke ki shiga tarko?, _lolx_).


Turare kawai ya fesa ya saka jalabiyar shi mai ruwan anta, ya hau gado ya kwanta, ita ko ta jona wayar ta a charge ta kwanta saman three sitter.


"Wannan ne kuma baki isa ba, saboda haka ki taso ki dawo saman gadon ki kwanta, ba wani abu nace zan maki ba".

    Ji rainin hankali, to me tace zai mata, ina ga in na k'yale wannan mutumen rainin zai yi yawa, cikin zuciyar ta take wad'annan maganganun.


Gaban ta kawai ta ganshi yana batun sunkutar ta, da hannu ta yimai alama sannan ta kalle shi sama da k'asa "ina ga ka hutar da kanka da shiga mu'amalar kucaka kuma jahila, saboda gudun kar ta6on ta ya shafe ka".


Daga hakan ta juya ta bashi baya ta yi kwanciyar ta. Tamkar gunki haka ya dask'are a gurin, lallai tabbas magana zarar bunu ce, kuma yana da tabbacin watarana za ta maida mai amsa, wannan ba damuwar shi bace indai za ta hak'ura ta yafe mai laifin shi a gare shi, hakan dai ya ja jiki ya je ya kwanta.


********


Yau ne aka d'aura auren Saudat Kabeer Aminu da Fadeel Ibrahim mai dala, inda aka yiwa Saudat abubuwa cikin tsaka tsaki na masu rufin asiri, sai dai fatar d'orewar zaman lafiya.


Sai ranar da aka kai tane Zajlah tasan Fadeel ne da ya ce yana son ta, tuna abinda ya faru tsakanin shi da Mum ne yasa jikin ta ya k'ara sanyi da lamurran duniya had'e da ikon ubangiji.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                         *(47)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*



®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



       Yau ne mummunan labari ya risk'e su cewa Allah ya yiwa Alh Ibrahim rasuwa akan hanyar shi ta zuwa Abuja daga sokoto ya yi hatsari, inda suka jajanta abin had'e da yimai murnar sauke nauyin marayin Allah dake saman kanshi, addu'a suka yi mai inda Mum taso ko Alamein ne yaje, sai dai a labarin shi bai gaya masu takamemen address d'in gidan suba, Allah ya gama rai da gafara, Amein.


*******


6angaren Baban Zajlah yana ganin bud'i a kasuwancin shi saboda yanzu shine shugaban masu kayan gwari, don ya daina kasawa a table sai buhu-buhu da yake d'aukowa ana siya gare shi, amincin su sai k'ara k'arfi yake yi tsakanin shi da Malam Inuwa sun zamo tamkar y'an uwa na jini.


*********


Cikin Salmat yanzu ya kai wata bakwai, yanzu laulayi ya rage sai d'an banzar kwad'ayi dake taso mata inda Imran ke tarairaya da ita tamkar k'wai.

    Yusrah na mak'ale da na tacikin d'an wata biyu wanda ba kowa yasan da zaman cikin ba saboda ba wahala yake bata ba.


*********


Alamein ne zaune k'asa dirshan inda Zajlah ke zaune saman kujera tana fuskantar shi sai wani cin magani take yi, ta yi wanka ta ci ado tamkar wacce za ta je bikin aure sai cingum take tauna yana bada k'as-k'as.


"Bazan iya jure wannan garawar da kike min ba, Zajlah nasan ni mai laifi ne a gare ki, amma na yi ta baki hak'uri kin k'i ki hak'ura".

   "Tun farko wallahi bansan miye "So" ba ban ta6a tsayawa na yi magana da mace ta minti uku ba, a wancan lokacin na saka ma raina tsanar mace ne ba akan komai ba sai don ganin yanda suke taka rawa a ta6ar6arewar rayuwar d'a namiji cikin shu'uman cin su".


"Bazan manta ba muna farkon shiga university mu hud'u muke tare, Salis, Imran, Salim sai ni Alamein, duk wanda ya san mu tare yake ganin mu, bamu shiga sabgar kowa karatun mu kawai muka saka ma gaba.

    Akwana a tashi Salim ya had'u da wata yarinya da ake cema Hafsat inda soyayya ta shiga tsakanin su, ganin rayuwar shi ta fara sauyawa muka nemi raba shi da ita saboda ya kula da karatun shi gashi maraya amma abin ya gagara, saboda y'ar mai kud'i ce yarinyar kuma gwargwado tana sakar mai kud'i, daga hakan ta ja ra'ayin shi suka rik'a holewa har ya zamo tamkar miji a gare ta, hakan ya yi silar muka tsame kan mu daga lamurran shi, wallahi tun daga lokacin na k'ara tsanar Mace a rayuwa ta".


"Tabbas nasan ina da tak'ama da ji da kai, amma ba na saka Mace a tsarin rayuwa ta kwata-kwata, kuma kiyar da dacewa kece first love d'ita kuma last insha Allah, wannan horon da kike yimin ya yi tsanani don Allah ki sassauta min", hakan ya k'arashe maganar yana rik'e da hannun ta har da guntun hawayen shi.


Tabbas ta tausaya mai, amma ita miye na ta ciki na hantara da hwulak'antarwa, tunda ita ma ba ita tace tana son shi ba, kawai daga sama akace an mata miji, me zai hana yayi wa iyayen shi biyayya ko da bai son ta ya shafa mata lafiya kowa tashi ta fisshe shi.


Yatsun hannun tane da yake murza wa ya sa ta fincike hannun ta ta mik'e ta yi d'aki, key ta murd'a ta yi zaman ta d'akin.

    Har ga Allah tasan tana son Alamein kuma shine kalar namijin da take so tun bata san miye "So" ba tsayayyen namiji ke burge ta, sajen fuskar shi da dara-daran idon shi ke k'ara d'aukar hankalin ta zuwa gare shi, amma tabbas sai ta nuna mai darasi sannan za ta bada kai bori ya hau.


Tsam ya tashi ya yi part d'in Mum, saman kujera ya zube ya yi kwance hannun shi d'aya ya yi matashi dashi d'ayan kuma ya dafe kanshi inda har jiyojin kanshi sun tashi rad'o-rad'o.

     Mum ce ta fito daga d'akin Dad ta risk'e shi hakan, tafi minti uku saman kanshi bai ma san tana nan ba. Tabbas kwanan nan tana lura da takon shi tsakanin shi da Zajlah, tasan ba komai ne ke wahalar da shi ba sai "Son" Zajlah dake d'awainiya dashi, saboda yanda yarinyar ta k'ara fresh yanzu ga wayewa dake shigo mata kad'an-kad'an, inda ko Mace y'ar uwar ta ta ganta cikin kwalliya sai ta k'ara kallon ta barranta na namiji, da hakan ta yi alk'awari ba za ta ta6a nuna mai ta fahimci matsalar shi ba, sai Zajlah ta gama gara shi ta sauko don kanta.


Hannun shi da ya rufe fuskar sa dashi Mum ta janye had'e da furta "waini Son kwanan nan me ke damun ka?, duk sai in ganka tamkar kana cikin damuwa, ko gurin kasuwancin ne?".


Ji ya yi tamkar ya gaya mata me ke faruwa ko za ta taya shi shawo kan Zajlah, sai dai kuma yana tunanin ko ya gayawa Mum ba lallai ne ta bashi had'in kai ba, tana ma iya basarwa da tuna mai baya.


"Ba komai Mum yanayin rayuwa ne kawai, a dai taya mu da addu'a", "toh Allah yashige mana gaba, kaima ka dage da addu'a".


Bayan ya amsa ne ya ji kuma zaman ya gundire shi ya tashi ya yi part d'in su, wanda har lokacin Zajlah na d'aki bata fito ba. D'ayan d'akin ya fad'a ya shiga toilet ya sakarwa kanshi ruwa, sai da ya yi wanka ya fito ba kayan sakawa suna d'akin da Zajlah take, k'ofar yaje yana bugawa had'e da magiyar ta bud'e zai d'auki kayan shi, hakan ya sa ta fito ta bar mai d'akin ta dawo falo.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                      *(48)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



    Duk mahaluk'in da ya ga Alamein yasan cewa yana cikin damuwa, saboda har y'ar rama ya yi kuma ya tara wani uban saje a fuskar shi da ya maida shi tamkar wani Sabon shigar hauka.


Ba k'aramin tausaya mai Mum ke yi ba sai dai kuma tana ganin in har tace za ta saka baki a maganar su tamkar ta so kanta dayawa, kuma in za ta duba bata San iya muzguna warda ya yi yiwa ita Zajlan ba har aka kawo yanzu, kuma a 6angare d'aya ta fi so Zajlah ta garashi saboda yasan darajar ta.


Abincin rana ta gama ta kawo ta ajiye, amma ga mamakin ta yanda ta ajiye na safe hakan ta tarar da shi, mamaki ne fal a ranta saboda yanzu suna wasar y'ar 6uya tsakanin su in yana d'ayan d'akin to itako za ta koma d'ayan.

     D'akin da yake ta tunkara, har ta rik'a k'ofa za ta murd'a kuma ta fasa, saboda a tunanin ta in tayi hakan ta bada kanta, sai kawai ta dake ta koma d'ayan d'akin ta yi kwanciyar ta, whatsap ta hau amma duk da hakan zuciyar ta tak'i natsuwa guri d'aya, hankalin ta d'ayan na gurin me yasa yau bata ga Alamein ba.


*********


A daddafe ta kai la'asar bayan ta yi sallah ta fito domin d'ora girkin dare, still duka abincin ba abinda aka ta6a, cikin rawar jiki ta fad'a d'akin, can k'asa gurin gado ta ganshi zube male-male cikin amai yana dafe da cikin shi, da saurin ta ta kai gurin ta tallafo shi duk jikin shi ya saki.


Toilet ta nufa domin samo ruwa da towel ta gyara mai jikin shi amma ya rik'e ta gam ya hana mata tashi, "Zajlah ki yafe min laifi na zuwa gare ki, inason kisan cewa ko da ta Allah ta kasance a gare ni to na tafi da d'inbin K'aunar ki a zuciya ta, ina sonki kuma bazan daina son ki ba har k'arshen rayuwa ta".

     Wani tari ya rik'a yi mai had'e da majina da jini-jini daga hakan ya some a jikin ta. Wata k'ara ta saki ta fito a guje sai part d'in su Mum, koda ta shiga tana zaune falo da remote a hannun ta tana kallon tashar Manara T.V. jin kawai ta yi mutum ya fad'o mata, "wayyo Mum Alamein ya mutu, Mum ki tausayamin kar in rasa shi, Mum ki gaya mai wallahi ina son shi nima".


Sambatu kawai take saki wanda ta kasa yiwa Mum takamemen bayani kan abinda ke faruwa. Remote d'in ta ajiye ta ja hannun ta suka koma part d'in, ko Mum data ganshi a hakan ba k'aramar razana tayi ba, saboda har ga Allah ta zata bashi da rai.

    Da saurin ta ta doshi gurin ta tallafo shi, inda Zajlah ke ta shar6ar kuka tana gunza, "yi sauri bani ruwa a cup".


Fridge ta bud'e ta d'auko ruwa ta bawa Mum ta koma gefe ta raku6e sai gaban tane ke dukan uku-uku. Ruwan Mum ta watsa mai a fuska saboda tabbacin yana raye suma ne ya yi, firgigit ya motsa dafe da k'asan marar shi sai hawaye ne ke yi mai zuba.


"Mum kice wa Zajlah ta so ni kamar yanda nake son ta, Mum wallahi na gano kuskure na, zan iya rasa rayu.....".

    Mum ce ta rufe mai baki, sannan ta kai duban ta ga Zajlah da ta nok'e kan ta tamkar wata marar gaskiya, "ki kula da mijin ki", hakan kawai ta furta ta bar masu falon, saboda dama tasan duk "So" ne ke d'awainiya dasu amma kowan nen su na basarwa a dole bai son d'ayan ya fahimci hakan.


K'arasowa tayi gurin shi had'e da tattara kayan da ya yiwa amai ta kai toilet ta wanke sannan ta had'a mai ruwan wanka ta fito, taimaka mai ta yi ya shiga wankan, ko da ya fito ta kimtsa d'akin ta fesa turare, sannan ta had'a mai tea mai kauri.


"Sannu ya jikin?".

 "Da na mutu ai kin huta tunda ba damuwa kika yi dani ba", cup d'in da ta had'a mai tea ta mik'a mai ya kar6a ya ajiye gefe, gaban ta ya zo ya gurfana had'e da rok'on ta gafarar abinda ya aika ta mata a baya.


Bata San lokacin da ta rik'o hannuwan shi ba alamar ya tashi sai da ta ji ya fad'o mata ragwaf saman jiki, yunk'urin janyewa ta yi had'e da furta "wash! Hannu na", hakan ta sa ya yi saurin zabura, da saurin ta ta koma saman kujera tana dariya had'e da yi mai gwalo.


Cup d'in ya rik'a sannan ya dawo kusa gare ta ya zauna, baki ya bud'e zai yi magana ta yimai alamar yasha tea d'in sannan su yi magana.

   Hakan ya shanye tass ya ajiye sannan ya tattara dukan hankalin shi zuwa gare ta yana wasa da jelar gashin ta, "Zajlah plxxxx kice kina so na", cikin kasalalliyar murya ya furta hakan.


"Ai Kaine baka "So" na, amma ni tun farko ban ta6a jin k'iyayyar ka a rai na ba, sai dai kai da kake ji tamkar ka hasa wuta ka.......".

  Bai bari ta k'arasa ba ya dafe mata baki da hannun shi, "ki yarda ni kaina ban ta6a jin k'iyayyar ki ba, sai dai rashin son kula mata da baya gaba na".


"To yanzu gaya min wane irin kalar so kake yi min".


"Ni ba son ki nake yi ba K'aunar kice da ta dabai baye ni take batun mayar dani wani zautacce, saboda K'auna ba ta ta6a canja wa, So kuma wataran zai iya canjawa".


Hira suka shiga sosai kowan nen su na nunawa juna irin yanda yake jin shi a ranshi, wanda ta kai tun suna saman kujera har suka koma saman gado (ni dai Jegal k'ofa na ja masu na fita, su Aunty Sis sunan Ku sorry Zajlah ta lula a duniyar ma'aura ta, kunsan ance tsakanin mata da miji sai Allah, _lolx_).



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                       *(49)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



      Kiran sallar magrib ya dawo dasu hayyacin su, inda Zajlah sai wata shagwa6a take mata zuba mai, wanka Alamein ya fad'a sai da ya fito sannan ya had'a mata ruwa ya taimaka mata ta yi wanka, ganin lokacin sallah ya kusa shigewa ya sa ya jasu jam'i suka gabatar da farali suka d'ora da nafila sannan suka jero addu'o'i, basu tashi daga gurin ba sai da suka gabatar da isha sannan Zajlah ta ja jiki ta koma saman gado ta k'udun-dune, gadon shi ma ya hau yana tsokanar ta had'e da saka mata albarka.


Daka kalli fuskar shi za Kasan cewa yana cikin farin ciki, walwala had'e da nishad'i, "ya dace in fita in sawo maki kazar ki ta amarci amma kuma duk kin d'ibge min jiki".


Ido ta gwalo waje alamar mamakin maganar da ya furta, kashe mata ido d'aya ya yi sannan ya furta "ko k'arya nake yi?, ni da ke jinya ko k'arfin jiki bani da".


Kunya ce gaba d'aya ta lallu6e ta dole ta nok'e kan ta had'e da k'udun-dune wa cikin blanket, hakan ya sa ya zira jalabiyar shi ya zari key d'in mota ya fice daga gidan.


Fitar shi ya sa ta yaye bargon da ta lullu6a dashi ta ja jiki sai toilet, jikin ta ta k'ara gasawa sannan ta fad'a kitchen, indomie ce ta dafa masu da ta ji kifin gwangwani, tana juyewa a kula ta ji motsin shigowar shi, a falo suka had'u ta d'auko kular abincin za ta kai dining, shi ko yana rik'e da ledoji a hannun shi, da Sauri ya saki ledojin da ke hannun shi ya taryo ta, kular ya kar6a sannan ya rik'o hannun ta suka k'arasa falon, sai da ya ajiye ta saman kujera sannan ya ajiye kular abincin k'asa, ledojin ya koma ya d'auko ya wuce kitchen ya had'o da plates had'e da spoon.


Sai da ya ajiye kayan sannan ya kai duban shi zuwa gare ta "wa yace kiyi girki yanzu?, in je kawai in dawo ke ce makuku har kin fad'a kitchen", yana maganar ne da murmushi d'auke a fuskar shi tamkar gonar auduga.


"To in banyi girki ba me kake so muci?, ko mu kwana da yunwa kake so?, ni da ma ka maida ma ciki tamkar an yimin yaso".


Suna had'a ido ta nok'e kan ta tana murmushi, "yarinya za kiyi bayani ne".

   Daga hakan ya fitar da kaza biyu da fresh milk sai wani take away dake da ferfesun y'an ciki daya siyo B.L.B, baki ta saki tana kallon shi had'e da furta "da mu da wa way'annan kayan?, ka d'auki kaza d'aya ka kaiwa su Mum".


Ido ya gwalo waje yana kallon ta, "wato so kike in bayyana kaina gurin Mum", dariya ta yi sosai sannan ta ware d'ayar ta bashi ya saka a fridge gobe a d'imama akai masu, saboda ita ma tasan baza ta iya zuwa part d'in ba yanzu.


Da hakan suka ci suka k'oshi, sannan suka dasa baben hira da nunawa juna kula wa tamkar sa had'iye junan su, sai k'arfe *11:30pm*sannan suka kwanta.


************


Kwanaki sun shud'e watanni ma haka, inda yau ne Zajlah ke ta shirye-shirye tun safe kan zuwa sunan y'ar da Salmat ta haifa, akwati d'aya suka had'a ita da Alamein na kayan jinjiri da kayan amaryar k'arni, saboda yanzu gwargwado hanyar samu na k'ara bud'ewa Alamein a cikin kasuwancin shi, tun *08:00am* ta kammala aikin ta take ta tayar da Alamein kan ya tashi ya sauke ta gida ya k'i sai juyi yake yi saman gado, dabara ta fad'o mata ruwan sanyi ta d'ebo ta yayyafa mai a fuska, yana tashi ya janyo ta saman gadon sai da ta yi ta had'ashi da Allah sannan ya sake ta ya d'auko key suka fice.


Gidan su Salmat cike yake da y'an suna, Yusrah, Saudat, Zajlah sun kammalu gidan inda akayi taron suna aka watse kowa yaci ya k'oshi sai dai fatar Allah ya raya Mus'ab, sai dare sannan kowannen su mijin shi ya zo d'aukar shi suka wuce.


*************


Bayan sati biyu ne da sunan Salmat tana kitchen tana tafashen kayan ciki za ta d'ora girki ta fito aguje wurin toilet d'in su na tsakar gida tana lezaya amai tamkar za ta had'o da hanjin ta, k'arar aman ta ne ya ankarar dashi ya fito da sauri, taimaka mata ya yi ta wanke bakin ta sannan suka koma falon. K'amshin tafashen naman na bugun hancin ta ta k'ara fitowa tana wani aman.


"My Zaz me kika ci hakan yake ta sakaki amai?", a rud'e yake jero mata tambayar, gaya mai ta yi ya kashe risho d'in ya kawo mata gyalen ta za ta shiga gurin Mum, hakan ya kawo mata suka wuce part d'in Mum gaba d'ayan su.


Gaida Mum kawai suka yi ya jefo mata maganar "Mum kinga My Zaz sai amai take ta lezawa har ta kasa zama part d'in mu".

     Duban ta ta maida ga Zajlah sannan ta ce' "me ke damun ki halan?", duk da tana zargin shigar ciki ne da ita, amma tana so ta tabbatar da zargin ta.


"Mum tafasar nama ce ba naso shiyasa", murmushi kawai ta yi had'e da yi mata Allah ya sauk'ak'a sannan ta d'ora da cewa "sai ki ajiye girkin har zuwa lokacin da cikin zai yi k'wari, in yaso a rik'a baku anan".


Kunya ce ta kori Zajlah ta yi d'akin Mum ta bar su ita da Alamein, don dama tana zargin cikin saboda watan ta biyu bata ga al'adar ta ba.

    Bayan ta d'aga ne Alamein ke ta damun Mum da tambayar abinda ke faruwa, nan ta gaya mai ciki ne da Zajlah d'in. Kan murna bai tsaya ta k'arasa bayanin ta ba ya fad'a d'akin Mum d'in don nuna wa Zajlah tsabar murnar shi.


********


Akwana a tashi ba wuya a gurin ubangiji, saboda Yusrah ita ma ta sauka, sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba, sanadiyyar hakan yasa Imran ya hana ta zuwa gida wankan jego, dole cikin dangin mamar ta aka tura mata wata domin kulawa da ita yanda ya dace.


********


Dak'yar ya barta ta je barkar Ummulkhairi matar Ustaz Lukman, saboda a cewar shi yana kishin ganin ta tare da Ustaz d'in, "banda abinka *HUBBY* ni da zanje barka me zai had'i na da Ustaz?, wai ma tsaya wa ya gaya ma Ustaz Lukman ya yi "So" na?", da mamaki fal a ranta ta jefo mai tambayar.


Sai da ya k'ara had'e fuska sannan ya yi mata bayani kamar haka, "lokacin ciwon Dad kinsan su ke zuwa yiwa Dad addu'a, to nan ne Ustaz Yusuf ke yimin nasiha kan in rik'e ki da kyau, saboda ke Mace ce mai hankali da nutsuwa kuma nayi dace, inda har yake gaya min da yanzu Ustaz Lukman ne mijinki, ba don ma yana kula da mahaifi na ba gaskiya da na sallame shi wancan lokacin, saboda dana kalle shi wani k'unci nake ji".


"Su kishi manya, to ni dai tashi muje ba dad'ewa zan ba sai ka jira ni mu dawo tare", da hakan suka fice domin zuwa barkar.



® *SDY JEGAL*


Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

[2/5, 12:35 PM] *SDY JEGAL*💝: 💗💕 *🇦DALILIN GATA*💗💕


                       *(50)*


*DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA*


®NWA

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


*Last page*



      Zaune suke suna cin abinci da uban tutse-tsen cikin ta wanda haihuwa ko yau ko gobe. " *HUBBY* ya kama ta kabar ni naje gida wankan jego, kasan fa daga na farko shikenan ba komawa za'a k'ara yi ba".

   "Yanzu My Zaz za ki iya tafiya kibar ni cikin tarin kewar ki?, kinsan irin K'aunar da ke tsakanin mu bazan iya jure rashin ki a tare dani ba, ya kama ta ki tausaya min".


Zugum ta yi bata ce komai ba saboda ko ita tasan ba zata iya nisa dashi ba sai dole, ya koya mata k'aunar shi mai zafi yanda bata iya nisanta dashi, "My Zaz in kina ra'ayin zuwa bazan takura ki ba, ko yau zaki je sai ki had'a kayan ki, amma nasan zan takura fiye da tunanin ki".


"Ba komai Hubby na hak'ura, farin cikin ka shine muradi na har kullum, ni ma nafi so kullum ingan ni tare dakai. Yanzu yaushe ne za mu tare sabon gidan mu?".

    "Ina ga mubari sai Allah ya sauke ki lafiya kamin suna sai mu tare can ayi suna ko?".


"To Allah yanuna mana lokacin", da hakan suka cigaba da tsara yanda abubuwan zasu kasance.


*********


Baban Zajlah Allah ya bud'e hanyar samu har ya sayi wani fili bayan shi ya had'e da gidan shi ya yi gyara gwargwado, saboda a tunanin shi tilon y'ar shi za ta dawo gida wankan jego, baisan sun riga sun kitsa komai ita da mijin ta ba.


*******


K'arfe *01:00am* ta falka da nak'uda inda tun tana juriya har ta tayar da Alamein daga barci, gigice ya tashi ta gaya mai yakira mata Mum, hakan ya fice ya kira Mum suka zo tare ji yake yi tamkar yad'auke mata ciwon da ke tattare da ita.


Magana yake wa Mum kan suje asibiti, ganin haihuwar ta zo gadan-gadan ya sa tace yad'an tsaya suga yanda za'ayi. Duk addu'ar da tazo bakin Zajlah furtawa take yi saboda ta galabaita iya galabai ta, suna batun zuwa asibiti ta sunkuto y'ar ta sannan namijin ya biyo baya, je kaga murna gurin Alamein da Mum.


Nan dai Mum ta kimtsa yaran ta kaiwa Alamein sannan ta dawo ta kimtsa Zajlah, tea ta had'a mata mai kauri ta bata tasha.

   Ko da Mum ta fito falon ya saka yaran gaba yana kallo yana murmushi, "To baban twins aje a kwanta ko?, ba ni yaran inje dasu tunda yanzu *02:30am*, kuma nasan da wuya su nemi mamma cikin daren nan".


"Gaskiya Mum sai dai ki kwana nan ko kuma in biyo ki part d'in mu kwana can mu duka", baki ta saki galala tana kallon shi.


"Anya ko Alamein yanda nake murnar na samu jikoki za ka iya bani yaran nan?".


"Ba dai in baki duka ba ko Mum?, ai kyautar d'a sai Allah, zan dai rik'a baki aro koda na awa biyu ne", yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi da alamar zolaya.


Ita ma Mum murmushi ta yi ta d'ora da cewa "to mara kunya ai yara nawa ne saboda y'a ta ta yi nak'udar su ba kai ba, in yanzu tace ta bani sun zama nawa", ganin cewa tabbas baida niyyar bata yaran ya sa ta fice daga part d'in.


Duk abinda suke yi Zajlah na jiyo su daga d'akin tana murmushi, sai gashi yana k'wala mata kira, hakan ta janyo jiki ta fito falo d'in, "d'auki yaran mu shiga daga ciki, ni ban iya d'aukar jinjirai ba".


Kallon mamaki ta bishi dashi, "amma ko Hubby ka kai, yanzu ma ko yaran baka iya d'auka ba ka hana Mum taje dasu?, to kasan yanda za kayi dasu saboda ni bacci nake ji gaskiya", da hakan ta juya zuwa komawa d'akin.


Lalla6a ta ya yi sannan ta dawo ta d'auki namijin sannan ta runguma mai macen suka koma d'aki suka kwanta.

     Sallar asuba kawai ya yi ya dinga kiran mutane a waya yana gaya masu k'aruwar da suka samu, sai da safe aka kaiwa Dad yaran ya yi masu addu'a had'e da sanya masu albarka.


Kamin kace kwabo gida ya cika babu masak'ar tsinke y'an barka, inda Mum ta yi-ta yi dashi akai Zajlah gida ya k'iya, hakan tasa wata k'anwar Mama Inno da Naja'atu suka dawo gidan da zama domin taya ta rainon jinjirai.


********


Ana saura kwana biyu suna ne su Salmat, Yusrah, Saudat da Shema'u suka je kimtsa mata kayan ta a sabon gidan su nan cikin G.R.A d'in bayan gidan su Mum duk da Saudat da Yusrah na fama da nasu cikin.


Ranar suna yara sunci sunan Baban Zajlah da kuma Mum, inda ake ma Abubakar inkiya da Ikrama Maryam kuma Ikram.


Ranar gida ya cika mak'il da y'an suna, Zajlah, Saudat, Salmat, Yusrah Naja'atu da Shema'u suka saka kaya iri d'aya wata dakakkar shadda mai ruwan milk.


Fatima, Bahijja, Lateefa da Musirrah suma ba'a barsu a baya ba, don suma sun yima Zajlah kara har da yaran su.


Wata tawaga na hango tafe sunci ado, kowan nen su baki har kunne, sai da suka iso kusa ne sannan naga mai jagorantar tafiyar ba kowa bace sai Aunty Sis, Momma na Mariya girgir (snowhite), Badiyya, mmn Bakir, Ameena Bappa, Feenah umar, mmn Faruk, Humaira Ya'u, Mmn Khairullah, Sofys-closet, Aisha Bello, Maryam yusuf, Hauwa Jidderh, Aunty Baraka suma sun yiwa Zajlah kara, ashe da gaske soyayyar da suke yi mata ba a baki bace kawai.


Ranar twins sun sha d'auka ga mutane saboda pix d'in da ake ta d'auka, sai daga baya ne Alamein ya shige part d'inshi da yaran.

   Suna kam ya yi armashi abu gwanin ban sha'awa, kowan ne mutum sai da ya fita da jaka da agogo masu tambarin Ikram da Ikrama.


******


Bayan shekara biyar, yara na hango su uku suna kiciniyar bud'e mota zasu shiga yayin da Alamein ke tara-tara dasu kan su bari inya dawo zai kai su gidajen, yanzu yana sauri ne, rigima suka aza wanda ya rasa ya zaiyi dasu, suna hakan ne sai ga Zajlah ta fito da key d'in mota a hannun ta, nan ta fanshi Alamein ya fice sannan ta loda su a mota suka fita.


Shagunan ta na d'inki ne ta fara kai ziyara inda taga komai na tafiya yanda ya dace, daga nan ta wuce gidan Salmat, Mus'ab da Haydar ne suka shek'o taryar su, nan aka baje ana ta hira.


Sunje gidan Saudat da yaran ta biyu, Fa'iz da Muftah, Sai Yusrah ita ko y'ar ta d'aya  Zainab, daga nan gidan su ta wuce suka wuni can inda Ikrama yace tunda ba skul nan zai kwana, nan suka barshi suka wuce sai gidan Naja'atu, sai gidan Mum shi da yake kusa da gida.


Ikram ce da little Zajlah suka d'anewa Dad sai tumurmusar shi suke yi, Mum na fad'a kar su karya mata miji, nan dai Zajlah ta bar su ta fice gida, taso ta shiga gidan Shema'u aka ce ta wuce Abuja gurin yiwa oga hutu.


*******

Kwance suke yana bata labarin Visa d'inda ya je cuku-cuku an samu ta Mum da Dad sai Baban ta daya biyawa aikin hajji, saboda ita sunje bayan ta yaye su twins, cikin kud'in shagunan ta na d'inki daya bud'a mata ta biyawa Mal Inuwa inda suka yita sanya mata albarka.


"Ina alfahari dake a rayuwa ta domin kin zamo haske a lamurrana, yanzu gashi *🇦DALILIN GATA* da Mum ta yimin na zamo mai kamilallar zuciya da kuma alfaharin samun ki a matsayin uwar Y'ay'a na, ya kama ta yau asamu little Alamein tunda kin raba yara kina buk'atar hutawa da Hubbyn ki".


Ganin cewa abin zai fi k'arfin gani na yasa na jama su k'ofa na fice, Asuba ta gari.


TAMMAT BI HAMDILLAH



Duka-duka anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min, Allah yasa Ku amfana da abinda ke ciki.


*INA SONKU HAR CIKIN RAINA*

Momma Snowhite

Fatima Batul Mamman

Ummu Ahmad

Kareemat

S.B.R

Ayusha Iliyasu

Aneesa Abubakar

Sumayya Girei

Safiya Maikaji

Husna Yarbaiwa

Miemie lurv

Halima Bungudu

Mmn Twin's❣

Sa'adatu Abubakar

Ayshatu Adamu

Ummee

Mmn Ikram

Blacky Meenah

Ummi Adamu

Ummdilbar

Mmn Ansar

Muhibbat

Hajja ce

Mmn Walida

Abida Ahmad

Laurat (Mrs Zubair)

Mmn Muslihu

Nucee lurv novels

Aysha Ya'u Kurah novels

Khaleesat Hydar novels.




*BAN MANTA DAKU BA*


Duk wani group da nake ciki kuna raina, Allah yabar k'auna, musamman MUSHA KARATU group, da MUM FATY & JEGAL FANS taku soyayya ta daban ce saboda kun Nuna min k'auna.


Aunty Sis kina raina ina godiya da tarin kulawar ki a gare ni, Allah ya nuna min na cika alk'awari.


*MASOYA WANNAN LITTAFIN*


Ashnur

Zainab Dalhatu

Mmn khayree

Murjanatu

Murja Madelty

Mmn khalifa

Rukayya Ali

Rahmatullah

Sophy MD

Aishatu Aliyu

Maryam G

Sumee Luv

Princess Jamila

Matar soja

Mmn Nasir

Umm Haydar

Zee Zee

Mmn Mamee

Mrs Umar

Hajiya Babba

Mama na Mariya Jika

Fatyn Baba

Zarah nasir.


*KU MA GA TAKU GAISUWAR*


Aysha-Majid (Mmn Ameer)

Ikil-Bash (Mmn Meerat)

Bil-Bash (Mmn Abbalik)

Sister Juwaira.


Washhhh Allah na, kuyi min afuwa way'anda ban samu saka sunan su ba, kuna raina fiye da tunanin ku, a first page na saka sunayen wasu nan ma hakan, amma duk da hakan masoya basu shigo ba duka, nagode Allah yabar k'auna, na gaji da typing ne wallahi, duk da hakan kuna raina luv y'all.


Domin gyara ko k'orafi ko yabawa Ku ziyarce ni a blog d'ina sadiyajegal.WordPress.com


Sai kun jini a sabon buk d'ina mai zuwa *DAWA ZANYI KUKA???*  On 1/1/2017 insha Allah, luv y'all My fan's.



® *SDY JEGAL*



Dedicated to Anty ```Jidda Musa```.

0 Response to "ADALILIN GATA Hausa Novel"

Post a Comment