Abakin Aurenki HausHausa Novel
A BAK'IN AUREN KI...
漏Feenat Ja'afar.
1_Sauri take tamkar taci da k'a, kai daga ganinta
ka ga marar gaskiya, a d'ai d'ai layin da zai
sadata da gidanta ta t'saya tamkar munafuka ta
d'an leka, da sauri ta komar da kai tare da dafe
kirjinta mai barazanar fashe mata... "Na
shigesu.. Ja'afar? Ta fad'a tana mai sake
lekawa, sai karaf sukai ido hud'u dashi,tuni
buguwar zuciyar ta ya k'aru, bata ta6a ganin shi
a irin wannan yanayin ba.
"Mey yasa kika fita bayan yace ka'rki fita?...
Bak'in g'yalenta tasa tana t'sane gumin dake
t'sat'safo mata, cikin jihadi ta fito daga inda ta
boye harda d'aure fuskarta tamkar bata ganshi
ba.
Kanta na k'allon gefe tazo d'ai d'ai kofar gidan
zata shige ba tare da ta k'alli yanayin nashi ba..
Turus taja ta t'saya, ganin yadda ya d'aura wani
mukulli kan wanda ta rufe gidan dashi, cikin
k'arfin hali fuskarta na gefe tace "ya haka?
Wanda bai nan ma yafita,hakan yasa ta kara
fad'in "Ya Ja'afar ya haka?.. Tamkar kububuwa
yake cika, ji yake tamkar ya rufeta da duka dan
takaici, Ashe d'uk uban rat'suwar Salma ta mai
kan ta d'aina a fatar baki ya t'saya?..
Mota ya bud'e yana ko'k'arin shiga ta mot'so da
sauri, "Ja'afar magana nake fa... A tunzure ya
juyo da nufin kifa mata mari tai baya da sauri
gabanta na fad'uwa.
Lalle yau ta ta6o ran y'an maza, cikin bacin rai
yai mata k'allon banza, "kin za6i gidan suna
sama da sharad'i na koh? Toh mey kika dawo yi
min gida? Koh kin manta da sharad'in da na baki
na in kin fita toh kin fita "A BAK'IN AURENKI?...
Ido ta zaro tana dubenshi, kawai sai ta dake,
cikin k'arfin hali tace "A BAK'IN AURENA fa kace
Ja'afar? Daga gidan sunan shine har kake
wannan kumfar bak'in?.. Ta karasa tana y'atsine
mishi fuska,kawai sai ya k'ada kai ya shige mota.
Ganin da gaske tafiya zai yasa da sauri t ajiye
t'siwar ta fara kiranshi, ina,tuni ya juya a kalar
motarahi cikin zafin nama, da sauri ta mat'sa
ganin sai ya iya bi ta kanta..
Tana ganin da gaske yake hakan yasa tuni ta
t'sure, hannu ta aza bisa kanta cikin nadamar
fitar da tai sunan da ba'a ma gaiyace ta ba, "na
shiga uku ni Salma.. Na ja ma kaina wani bala'in..
"Yanzu igiyar Aure na biyu ta t'sinke kenan?..
Tuni zufa ta kara zubo mata dan tunawa da
kalaman Babanta, "d'uk randa zaki kara maimaita
haka Salma sai na 6alla kafarki in kin doso
gidana.... Fad'uwar gabanta ta t'sananta,t'saf
Baba zai aikata mata hakan,
ta k'alli gabar,da yamma, ta ma rasa ta ina zata
fara? Gefen dakalin gidan ta d'an dosana, da
d'ukkan hannunta biyu ta dafe kai,tuni kalaman
Ja'afar ya dawo mata, "in kin fita kin fita A
BAK'IN AURENKI....
Ku biyoni Bayan sallah dan jin yadda zata kaya...
By
Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 8:46 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *3*-
Kai ya k'ada mishi, _"aure ba shine mafita ba
Ja'afar,ka g'yara wacce ke hannunka tukun,bana
tunanin wannan shawara ce_. Murmushi yai tare
da k'ada mishi kai _("I know)_.. _"Amma ka gane
ba dan dad'i zanyi ba,nasan d'uk duniya ba
abinda Salma taki jini irin nace zan kara
aure,dole na d'andana mata mad'acin da ta
d'andana min nima_. Murmushi Garba yai yana
K'allonshi,wai yau Ja'afar ke maganar zai
d'andanawa Salman sa mad'aci?.. Kai ya girgiza,
lalle Salma tai wasa da damarta, dan yasan irin
dimbin son da Ja'afar ke mata, sai dai gashi za a
kaita a baro,dan ta fara sane ma abokinshi..
_"Bana tofa tawa ba nikam,nasan da kai da
Salma sai Allah,ni d'ai kai tunani abokina,kar ka
yanke hukunci cikin fushi azo daga baya ai
nadama_... Baki ya ta6e, kan ya ciro mukulli a
aljihunshi ya mika mishi, _"k'ar6i mukullin
motarka,dan aure kam nayi na ma gama,kuma
*Bintu* zan aura kasa ido_.. Ido waje Garba yake
k'allonshi,kan ya k'yalk'yale da dariya, _"lalle ka
d'ebo aiki..za kuma ka dasa ma Salma zargin ka
cikin ranta tunda kasan komai_... T'saki yai kan
yace _"zanso hakan ya kasance, dan zata fi jin
haushi sosai_.. Kai Garban ya k'ada yana kunshe
dariya, _"muje na sauke ka toh na Salma da
Bintu,kai (scene) din nan zai dad'in k'allo
wallahi_.. Ya karasa da dariyar keta. Murmushi
kawai yai suka shiga mota,har suka isa gida
Garba na mishi t'siya..da ya had'o shi da Salma
zai kicin-kicin. ************************ A wajen
Salma kuwa,sai da dare yai tana k'wance
d'akinsu na da sai juyi take,wanda ita kanta ta
rasa dalili,har yanzun haushin Ja'afar na kasan
ranta na ya mata wulakanci, sai dai da ta tuna
rabuwar igiyarta d'aya sai taji fad'uwar gaba. Yau
gata a katifa ba ta ita da Ja'afar d'inta ba?..yau
d'aya ta raba alakar matashin kanta(kafad'ar
Ja'afar) sai pillow... Hannu takai kuncinta,da
mamakinta hawaye take,kawai sai ta ida
karasawa ta fashe da kuka.. Wanda kai da gani
na k'ewar Jafaririn ta ne da t'sant'sar
nadama,amma ina,zuciya taki amsar hakan.. Ga
uban sauro da ya damu k'unnenta da ihu duk da
da Katanga a t'sakaninta dasu(net), ga uban zafi
ba wuta ba (Gen), d'uk t'siya tasan da a gidanta
ne da yanzu tana shan iskar injin da Ja'afar ke
k'unna mata d'uk dare ta k'wanta dan bata bidar
zafi.. Ga mama tace ba mai tada mata inji
Babanta baya gari, kuma bata kud'in mai... ***""*
Shima hakan take ga Ja'afar, kusan a hali d'aya
suke,sai dai shi kawai ya kura ma fankar d'akin
da ke kad'awa a saman d'akin ido. Tabbas har
yanzun baida sama da Salma koh a kasan
zuciyarshi.. Yana sonta, so marar misali,duba ga
yadda suka gina soyayyar tasu kamin aure.. Da
za'a ce mishi a da Salma zata sauya hali gaba
d'aya musamman akanshi da zai mu sa... Juyi
yai ya jawo filo,d'uk t'siya tanan yai k'ewar
Salma.. Dan karamin t'saki yai kamin ya tashi yai
waje dan kashe inji. *By* *Feenat Ja'afar*
9/29/16, 8:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 4-
Salma Umar Y'a ce ta biyu gun Mama(Haj Rabi'a)
da Baba(Malam Umar),y'an asalin Yobe
ne,kasuwanci ya kawo kakansu Kano da rabon su
Salma. Su biyu kawai ne a gun kakan su Malam
Bukar Mai buhu,baban su Salma ne karami, sai
yayanshi Baba Aji, yaranshi a kallah za suyi
(16),yayin da Baban Salma ke da uku,Aisha
(Aunty A'i)dan tafi Salma sosai,Salma,sai Ummi.
Kasuwanci ne gadon su Baba,dan koh bayan
rasuwar kakan su Salma sun cigaba da juya
abinda ya rage musu. Suna taimakon juna
sosai,hakan yasa kansu yake a had'e, duk da
rufin asiri ne kawai na Allah. Sannan d'ai-d'ai
iyawa sun bama yaran su karatu da tarbiya,suna
da t'sanani musamman Baban su Salma. Sai dai
fa ita Maman su gani take kakarsu ta yanke
saka,tunda Allah ya hore mata yara mata uku
setin samira ta zuba jari,shi yasa d'ukkan wani
abu akan A'i yake karewa dan ita tasa a lokacin.
Ba lefi,ak'wai dan k'yau irin na ainashin mutan
kanuri,sai kuma Maman dake asalin Shuwa,ba
farare bane,za dai mu iya kiransu da _"black
beauties"_sirrin su kuwa,diri ne da yalwar gashin
ka da _"beauty point"_ _(dimples)_.. Wanda
tamkar kowa diga mata ake. Hakan yasa kasuwar
Aunty A'i ta daga da sauri,tuni k'wa Mama abin
nema sai ya samu,hakan yasa ta kara sa ma
sauran Burin da yafi na Aunty A'in.. Barin Salma
dake doguwa ce cikin su. Ita kam Salma bata san
ma ana yi ba. Kasantuwar shagonsu Baba ya
zama biyu sai ya zamana aiki yai musu yawa,
har bai samun damar dawo wa gida cin abinci sai
d'ai Ummi koh Salma su kai mishi. Ranar kaiwar
Salma ne,tai shirin Islamiya ta doshi shagon su
Baba. Tunda ta ajiye abinci taki gaba taki
baya,kamar dai da alamun an mata abu daga
gida. Murmushi Baban yai kan yace tazo.. _"mey
aka miki uwata?_ Hawaye ta dan matso halamar
6aci. _"Mama ce ta hana ni kud'in tara_. Kai
Abban ya k'ada yana murmushi kan ya sa hannu
a aljihu ba chanji,gudar naira dari ya fitar kan ya
nuna mata shagon kusa dasu taje tai chanji. Da
sallamarta ta shiga,ta gaida shi,shago ne na
kayan k'yallin mata na sawa, attamfofi da
laces,ga materials kala kala,d'uk zuwanta bata
ta6a shiga shagon ba sai yau. _"Salamatu y'an
mata,ina su Ummi?_ Murmushi tai mishi,dan tana
ganin shi gun su Baba, dattijon na da kirki da
fara'a, banda yaron shagon shi da koh k'allo bai
mata ba, _"suna gida,Baba ne yace aban chanji_.
Kai ya k'ada, kan ya k'allo na zaune a acikin
shagon rike da littafi halamar yana dubawa.
_"amm *Ja'afar*_.. Kai ya dago karon farko,
_"Na'am Abba_,, sai lokacin ya kula da Salma,
_"Ba wa Salma naira ashirin ta tafi kar tai latti_.
Kai ya k'ada kan ya kara k'allo Salman wacce sai
hange take koh za taga wani dan islamiyar su
tana mika hannu. _"k'ar6i man_.. Juyo wa tai
taga yana miko mata kud'i fuska ba fara'a, da
sauri ta k'ar6a tana tafiya tana fad'in _"na gode
Abba_. Da k'allo Ja'afar ya bita,yana ganin Ummi
ce mai rawar kai ashe sauran ma haka suke.
_customers_ ne suka tada shi ya shiga shagon.
Washegari ma sai ga Salma,wannan karan koh
shagon su Baba bata je ba tai shagon su Ja'afar.
Da mutane da kusan d'uk y'an mata ne suna
siyayya, yana ganin Salma ya had'e rai, sam yaki
jinin a 6ata yaro da kud'i, ita kam Salma harda
mishi murmushi tana dago mishi hannu da kamar
abu aciki. T'saki yai,kan ya cigaba da abinda ya
ke,sai da ya sallami kowa kan ya ganta tana
gaida Abban shi da ya fita yana nuna mata cikin
shagon. Da dan gudinta ta shigo,a tunanin shi
kud'i Abban yace ta kara k'ar6a gun shi,dan da
zumudinta ta gaida shi. _"dama Abba ne yace
in_..... Cikin fad'a-fad'a ya katseta, _"bani da
chanji nima yau,jiya an baki kinji dad'i shin_....
Shiru yai sakamakon idonta da yaga ya cika da
k'walla tana k'allonshi. D'uk kuma sai jikinshi yai
sanyi.. A hankali ta ajiye masa gudar naira
ashirin akan benci ta juya tana goge hawaye. Ba
dai kud'in shi ta biya shi ba dan ya mata fad'a?
Da sauri ya d'auka da niyar k'wada mata kira ya
mayar mata sai dai tuni tai nisa sosai. D'uk
kuma sai yaji bai k'yauta ba. Yana nan zaune har
Abba ya dawo, _"kaga Salamatu wai kud'in ka na
jiya ya hau shine ta dawo ma dashi ba"_.. K'allon
Abban yai da sauri, _"Abba kud'i kuma?_
K'allonshi yai kan ya k'ada mishi kai, _"sai da
nace ta tafi wai A'a tana da wani,Salma ak'wai
hankali, ashe batai ma magana ba?_ Shi dai
Ja'afar yai shiru yana jin Abba,sai ya kara jin
wani iri. *By* *Feenat Ja'afar*.
9/29/16, 8:50 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *5*-
Washegari sai zuba ido yake yaga Salma
shiru,dan d'uk jiya ji yake bai k'yauta mata ba.
Sai d'ai Salma har k'wana biyu shiru ba koh kalar
ta sai Ummi ke zuwa kawo abinci. Ranar Ummi
ta kawo zata tafi ya t'sayar ta da tambayar ina
Salma k'wana biyu? "tana gida Yace "ya bata
kawo abinci sai ke?.. Tana zungura baki tace
"sai gobe ne nata kawowar. Dan koh ita Ummi
Ja'afar ke hanata zuwa gun Abba mai k'yautar
naira biyar goma.. Sam baida fuska,shi yasa taki
jinin shi. Washegari kuwa tun da ya ga lokacin
kawo abinci yayi yake k'allon shagon su
Baba,yau ga k'ananan shi a shagon baida
mat'sala. Kamar ance ya dago,sai gata kuwa
sanye da kayan islamiya,sai dai duk tai kicin
kicin fuska ba walwala. Yana k'allon yadda ta
t'suguna ta gaida su Abba kamar kullum, tana da
nut'suwa ba kamar Ummi uwar bankaura ba.
Tashi yai kamar mai tafiya wani gun,dai dai
k'wanar da take bi gida ya t'saya,sai gata
kuwa,har zata wuce ya kira ta,suna had'a ido ta
had'e rai,sai ta bashi ma dariya. Hannu yasa ya
ciro naira ashirin d'in ya mika mata yana
murmushi, a dan sace ta k'allo shi kan ta kawar
da kai tare da girgiza mishi kai. *"Salma*..K'all
onshi ta kara,ganin yana murmushi sai abin ya
bata mamaki,bata t'sinke da lamarin ba sai ji tai
yace tai hakuri, kai ta kawar kawai, kin huce?
tana wasa da hijab d'inta ta daga mishi kai, "toh
ki k'ar6a in kin huce,na bar miki.. Kai ta kara
girgiza mishi,kan tace "A'a ka barshi fa.. "baki
hakura ba kenan Salma?.. Kai ta k'ada mishi,
yace "toh ki k'alle ni ki amsa maza kar kiyi latti
kinji K'anwata.. Da lallami yasa ta sakko harda
dariya,har kusan makaranta ya rakata ya
dawo,yana mai mamakin fara'ar shi yau ga
yarinya Salma,sam shi baida sakin fuska
musamman ga mace d'uk k'ank'antar ta k'wa.
Tun daga ranar ya zamo in Salma ta kawo abinci
sai Ja'afar ya rakata ya kuma bata ashirin d'uk
bayan k'wana biyunta. Sosai sun saba,har in
batazo ba baya jin dad'i, har su Abba suka kula
da sabon kawancan Ja'afar da Salma,ana haka
Baba yasa ya dinga ma wa su Salma _lesson_
tare da kannenshi tunda ya gama _secondary_
_admission_ yake jira. Koh a gun _lesson_ misalin
Ja'afar a Salma yake t'sayawa, in k'wa duka ne
koh t'sawa Salma bata ciki,sai dai yai ma
k'annenshi, hakan yasa tun tana karama yaran
suke ce mata Salma budurwar Ya Ja'afar. A
lokacin takanyi bori kan bata so,har takai da ta
kai kara gunshi,sai dai mamakinta dariya ma yai
mata,yau da gobe har Salma ta saba da tsokanar
k'annen Ja'afar . Karatu ake sosai za ai _coming
interest_, sai dai ba Ja'afar dan ya tafi Zaria
sakamakon _admission nashi da ya fito. Sosai
Salma tai k'ewar shi,har hakan yasa ta d'aina kai
abinci shago sai almajiri,a hankali har k'ewar ta
sake ta suka gama jarabawa sai zaman jiran
sakamako... Sai dai Ya Jaafar na chan k'wance
kasan zuciyar ta. Yau ga Salma a _boarding_
babban burunta kenan makarntar k'wana.
************************** Lokaci ya shud'e,
kamar wasa yau ga nan Salma an zana
_J.S.C.E_, hutun mai dan nisa ne na yau. Mai
nut'suwa ce a d'uk y'an gidan su,a layin su,dama
unguwar gaba d'aya, Salma abar k'watance
ce,musamman rashin yawanta,kullum kaje in tana
hutu toh za ka samu Salma a gida. Batta
k'warafniya irin ta y'an mata masu tashen
tashi,asalima fitar ta in tai yawa toh islamiya ce
ta yamma, sa6anin su Ummi da tuni tun kar ta
far ta kone, dan wanka iya wanka Ummi ta
iya,hakan yasa Mama ta kara d'aure mata gun
siyan kayan k'arya. Dan a ganinta ta gama da
kason Aunty A'i tunda har an kawo sadaki, kuma
irin wanda mama ke da muradi. Ita kam Salma
zai wuya ka ga tama sanya g'yale bare har ta
zauna k'yali. Gata dai mama ita tafi sawa buri,
ga ta kuma y'ar _boarding_. *By* *Feenat
Ja'afar*.
9/29/16, 8:52 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 6-A
dai-dai k'wanar su Ja'afar take,dawo warta daga
islamiya kenan,sanye take da dogon hijab ruwan
kasa mai yashi har kusan kasa,rataye da jakar
littafai da Qur'ani a hannu,sai dan asirin _skirt_
nata na attamfa da ya fito _green_ da ruwan
kasa, duguwa ce,ba zangal ba,tana da kaurin
jiki,dan ta fita sahun ramammu,tafiyarta a
nut'sue tafi komai d'aukar hankali. Kamar kullum
ta daga kai dan k'allon gidan su Ya Ja'afar
kamar yadda ta saba k'ewar shi ta kawar da kai,
sai dai taku biyu taja ta t'saya tamkar an t'sayar
ta. Kanta duk'e dauke da murmushi,cikin
nut'suwa ta kara k'allon kofar gidan dan tabbatar
da wanda ta gani.. *"Ya Ja'afar*?...ta fad'a a
zuciyarta lokacin da ya taso yana mata
murmushi. Ikon Allah,wai kunyarshi kuma take
ji,cikin nut'suwa ta d'auke kanta daga gareshi
ganin ya karaso. "Assalam Alaikum Malama
Salma.... Wani irin buguwar zuciya taji ya ziyarce
ta,shekara uku da wani abin ba wasa ba,hatta
muryar Ya Ja'afar ta sauya mata. Cikin nut'suwa
ta dago da murmushi ta amsa mishi,kamin ta
gaida shi a kunya ce, shi dai kawai k'allonta yake
yana murmushi, kamar mai mamakin kara
girmanta,ga wata nut'suwa da ta kara shigarta.
D'uk sai ya kara yaba Salman nashi,ganin shirun
yai yawa yasa da hannu ya nuna mata hanya
halamar su wuce. Dan satar K'allonshi tai kan ta
sunne kai suka fara tafiya. "Salma koh murnar
gani baki yi,ba koh tambayar yaushe nazo? Kai
duk'e tace "yi hakuri,yaushe kazo?.. Kai ya k'ada
da murmushi,kan yace "jiya. Tambayar yaushe
gamo yake mata, yadda take kunyar tata gun
bashi amsa d'uk sai ya ji shi wani iri,mace mai
kunya itace muradinsa. Da haka har kofar gida
ya rakata yana mata tad'in makaranta da yadda
suka juma basu gamo ba. Ummi ya k'allo achan
dan nesa dasu tana tad'i, sai ya tuna mata yasha
zuwa ai. Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da
Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar
d'inta. Ganin haka yasa yai mata sallama tai
gida.. A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa
wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar
d'inta yau. Sai murmushi take saka cike da
kunya ita kad'ai kamar yana ganinta. A haka har
Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata
gami da had'a rai. "Yanzu Ummi kinyi dai dai
kenan? A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale,
"da nai miki mey? Iya jaraba.. Kai Salma ta k'ada
kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar
yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari
muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma
koda wasa baki fad'an ba? Allah kin ban haushi..
"Mtsww.. T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni
Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma
K'anwar ta. "Na zata wani abin kirkin ne wallahi,
toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken
shi?.. Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh.. A
tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji
Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan
koh? Yara kamar masu ganin hanjin junansu?
Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin
tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da
kunya sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare
ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan
uban d'acin ran kike wannan kumfar
bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama
abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son
fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki
ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki..
Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta
bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen
bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma
ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar*
Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 20
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 6-A
dai-dai k'wanar su Ja'afar take,dawo warta daga
islamiya kenan,sanye take da dogon hijab ruwan
kasa mai yashi har kusan kasa,rataye da jakar
littafai da Qur'ani a hannu,sai dan asirin _skirt_
nata na attamfa da ya fito _green_ da ruwan
kasa, duguwa ce,ba zangal ba,tana da kaurin
jiki,dan ta fita sahun ramammu,tafiyarta a
nut'sue tafi komai d'aukar hankali. Kamar kullum
ta daga kai dan k'allon gidan su Ya Ja'afar
kamar yadda ta saba k'ewar shi ta kawar da kai,
sai dai taku biyu taja ta t'saya tamkar an t'sayar
ta. Kanta duk'e dauke da murmushi,cikin
nut'suwa ta kara k'allon kofar gidan dan tabbatar
da wanda ta gani.. *"Ya Ja'afar*?...ta fad'a a
zuciyarta lokacin da ya taso yana mata
murmushi. Ikon Allah,wai kunyarshi kuma take
ji,cikin nut'suwa ta d'auke kanta daga gareshi
ganin ya karaso. "Assalam Alaikum Malama
Salma.... Wani irin buguwar zuciya taji ya ziyarce
ta,shekara uku da wani abin ba wasa ba,hatta
muryar Ya Ja'afar ta sauya mata. Cikin nut'suwa
ta dago da murmushi ta amsa mishi,kamin ta
gaida shi a kunya ce, shi dai kawai k'allonta yake
yana murmushi, kamar mai mamakin kara
girmanta,ga wata nut'suwa da ta kara shigarta.
D'uk sai ya kara yaba Salman nashi,ganin shirun
yai yawa yasa da hannu ya nuna mata hanya
halamar su wuce. Dan satar K'allonshi tai kan ta
sunne kai suka fara tafiya. "Salma koh murnar
gani baki yi,ba koh tambayar yaushe nazo? Kai
duk'e tace "yi hakuri,yaushe kazo?.. Kai ya k'ada
da murmushi,kan yace "jiya. Tambayar yaushe
gamo yake mata, yadda take kunyar tata gun
bashi amsa d'uk sai ya ji shi wani iri,mace mai
kunya itace muradinsa. Da haka har kofar gida
ya rakata yana mata tad'in makaranta da yadda
suka juma basu gamo ba. Ummi ya k'allo achan
dan nesa dasu tana tad'i, sai ya tuna mata yasha
zuwa ai. Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da
Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar
d'inta. Ganin haka yasa yai mata sallama tai
gida.. A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa
wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar
d'inta yau. Sai murmushi take saka cike da
kunya ita kad'ai kamar yana ganinta. A haka har
Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata
gami da had'a rai. "Yanzu Ummi kinyi dai dai
kenan? A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale,
"da nai miki mey? Iya jaraba.. Kai Salma ta k'ada
kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar
yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari
muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma
koda wasa baki fad'an ba? Allah kin ban haushi..
"Mtsww.. T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni
Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma
K'anwar ta. "Na zata wani abin kirkin ne wallahi,
toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken
shi?.. Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh.. A
tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji
Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan
koh? Yara kamar masu ganin hanjin junansu?
Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin
tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da
kunya sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare
ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan
uban d'acin ran kike wannan kumfar
bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama
abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son
fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki
ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki..
Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta
bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen
bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma
ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar*
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 20
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
7_Washegari ma ta fito zata makaranta sai gashi
shi da abokinshi Garba suna tafiya. Ido ya kura
mata ganin tai kasa da kai tana murmushi. Sai
ya k'ada kai suka karasa,cikin sanyin murya ta
gaida su,Garba kad'ai ya amsa,shikam Ja'afar
k'allonta kawai yake yana murmushi, kamar mai
son sai sun had'a ido. "Malama Salma fa kar tai
latti a mata bulala abokina.. Kasa ta kara da kai
tana dan dariya, shikam gogan sai binta yake
kawai da k'allo,kan ya nuna mata hanya kan wai
su rakata hanya. Ba musu ta wuce suka
jera,Garba sai shakiyanci yake zuba
musu,murmushi kad'ai ne nasu har suka zo bakin
_gate_ d'in islamiyar. Ka'ro na farko suka k'alli
juna cikin ido,da sauri ta K'awar da kanta tana
murmushi, shikam harda k'ada kai, tuni Garba ya
harbo jirgin nasu,sai ya hau shafa ha6a yana
k'allonsu,musamman abokinshi da yace bai san
so ba.. Hannu Ja'afar ya kai aljihu yana lalube,ita
kam sai ta hau satar k'allon shi ganin mey zai yi.
Da mamakinta k'wa sai gashi ya fito da naira
ashirin yana mika mata. K'alloshi tai tana kunshe
dariya,sai ta k'ada mishi kai, "Kud'in tara ne fa
Salma, ki k'ar6a ki sai hambididi... Dariya Garba
ya fara harda rike ciki,itama wacce take rikewa
ta fito fili, sai ta sa hannu a baki dan rufe sautin
ta.. Shikam Ja'afar kawai sai ya hard'e hannu
yana K'allonsu, musamman Garba yadda yake
k'yak'yata dariya. Shikam ba kasafai ya iya
dariyar keta ba irin ta Garba,shi yasa wataran
yakan kularshi a abu. "La Malam Ja'afar......
Gaba d'ayan su suka juya k'allon mey magana.
Ja'afar take k'allo tana murmushi halamar jin
dad'in ganin shi, shikam tuni ya had'e rai yana
k'allon ina ma ya santa. Kamar tasan mey yake
tunani tace *"Bintu*(Na Rufaida Omar) ce,dalibar
ka a day... Salma ya k'alla wacce itama ke kallon
Bintu,kan ya k'ada kai, "toh Bintu.. Salma Bintun
ta k'alla jiki a sanyaye ganin ko in kulan da
Ja'afar ya mata,"shiga za kiyi ne Salma? kai ta
kada mata, jiki a sanyaye tai gaba Salma ta daga
musu hannu halamar sai anjima tana murmushi.
Da k'allo ya bita cikin wani yanayi, da ko shi
kanshi bazai iya fassara wa ba. Kai ya k'ada kan
ya k'allo Garba wanda k'wachokam ya maida
K'allonshi kan abokin yana dariya kasa-kasa.
Harara ya maka mishi kan ya juya,sai k'wa
Garban ya kara sa dariya yabi bayanshi. "An
fad'a tarko makal ana hura mana hanci,sai anyi
magana kace wani "mey nene so? Ni ban sanshi
ba.. Karyan kawai,koh makaho ya laluba yaji ka
afka so ai yanzu kam. Chak! Ja'afar ya t'saya
tare da juyo wa gun Garba. "Mey kenan haka ke
nufi?.. Harara Garban ya k'wada mishi kan
yace"kar ka maida ni yaro fa malam,kana nufin
baka san kana son Salma ba ko mey?.. K'allonshi
kawai Ja'afar ke yi cike da mamaki,a hankali ya
furta *"SO"*?... Hararar shi Ja'afar ya kara,gani
yake kamar ya raina mishi hankali ne. "Kaga
Malam kawai kai saranda haka,tuni tun yadda ka
ke ta yawan fad'in Salma nasan a rina,ka bar
wani k'wane-k'wane. Shi dai Ja'afar ya
t'sunduma tunani maganar Garba,wai So? Salma
kuma?. *By* *Feenat Ja'afar* 庐NWA.
9/29/16, 8:56 AM - Queen Safiyyert馃憫: [7/21, 12:28 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
8-Har Ja'afar yazo k'wanciya yana tunanin
kalaman Garba,tabbas biri yaso kama da mutum,
dan yana jin sauyi tun ranar farko da ya dora
idonshi a Salma bayan dawowar shi.
"So"... Ya furta a hankali, murmushi yai kan ya
k'ada kai,dan yana da aiki a gaba,dan bai san
kom ba game da lamarin.
Tun daga ranar ya zamto kusan kullum da
yamma yakan raka Salma islamiya,koh da yana
shago zai zo ya ganta kawai,hakan na sashi
nishad'i, yau da gobe har ta fara sakin jiki dashi
a karo na biyu.
Sai ya zamana itama in bata ga Ya Ja'afar a
ranar ba batajin dad'i sam,haka zata k'wana
sukuku.
Shirye-shiryen bikin Aunty A'i suke,duk sun shiga
_busy_.
Da yamma sun fito bak'in shagunan su Abba
siyayyan kayan fitar biki, tasan kuma d'uk layin
ba inda ya kai shagon su Ya Ja'afar kawo kayan
k'yali, amma da tayi magana Ummi sai ta tanka.
Kai duk'e yana duba takaddu,kamar
_papers_,chak ya t'saya da abinda ya yake yana
murmushi kai duk'e, ajikinshi ya ji kamar Salma
na kusan shi,itama dai satar k'allon shi take,tana
ganin zai dago tai sauri ta juyar da kai tana
murmushi.
Fara'ar shi ta karu dan hango Salman.
A hankali ta dan kara K'alloshi,sai k'wa suka
had'a ido,da azama tai kasa da kai tana
murmushi har suka karaso.
Tuni Ummi ta had'e rai ganin Ja'afar a shagon,a
takaice ta dan harari Salman ganin sai wani
munafukin murmushi suke sakar ma juna,baki ta
ta6e kan a ciki ta gaidashi tai cikin shago ta
barsu nan.
_"My_ kanwa,.. Kai ta kara duk'ar wa tana
gaidashi,sai ya k'ada kai,ya rasa irin kunyar
Salma gare shi yanzu,abu kad'an duk'ar da kai.
"Biki ya karato ba? Kai ta daga mishi tana dan
k'allon _net_ d'in gefenshi da murmushi.
Tashi yai zuwa gun inda take k'alla ya fara
saukar mata dasu.
A hankali ta tako gun dan zabi,d'uk sun mata
k'yau.
Sai ta dan kallo shi, "malam Garba fa? Murmushi
yai yana k'allonta, "yaje inda aka tura shi
_service_ nashi yaga gun,gobe zaki ganshi.
Kai ta k'ada, d'uk sai taji ta kasa za6a ganinshi
kusa da ita.
Kamar ya sani ya kara s'akko mata da wasu.
"Bari na tayaki za6a.
Kai kawai ta k'ada mishi tana k'allon kayan,kan
wani _purple_ idonta ya kai,a hankali ta kai
hannu zata ja shima ya kai zai d'akko shi yana
fad'in
_"purple_ zai miki k'y... Shiru yai ganin itama shi
ta rike,ya rike rabi ta rike rabi.
D'uk sai suka k'alli juna ba koh kiftawa da wani
yanayi...
Tamkar wanda aka lika _poster_ a gun haka suka
kame da k'allon juna.
Ummi ce ta kat'se su da fad'in
"Ga nan wasu materials y'an leda Salma masu
kaman _lace_....
Shiru tai ganin wani ikon Allah,baki sake take
k'allon su,tuni Salman ta sakar mishi tai baya
tana sunke kai da murmushi tare da amsar kayan
hannun Ummin tana sunyi k'yau ba dan ta gani
ba.
Murmushi ya sakar mata shima,har yanzu yana
rike da _net_,ya rasa mey ke damun
K'wak'walwar shi akan Salma.
*By*
*Feenat Ja'afar*
[7/21, 8:05 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
9_Baki ta dan ta6e,kan a y'atsine tace ma Jafaar
d'in "mun zabi wannan, zamu nuna ma Baba sai
ya bada kud'in.
Murmushi yai yana k'allon gun Salma,itama
idonta na kusan hannunshi.
"Koh na tafi ne Salma? K'allo Ummin tai,kan ta
k'ada kan suka yi hanyar fita a shagon,a hankali
ta dago mishi hannu halamar _bye_.
Kai ya k'ada mata shima ya dago mata nashi.
Tai k'walli da Ja'afar ta ji dad'i,har aka je gida
bata umm ba um um,sai Ummi ke ta zuba kamar
kanya, yadda zata zuba wanka a bikin Aunty A'i
har ta kule.
Da dare sai ga yaro wai ana kiran Salma.
Rai had'e ta k'allo yaron, "je kace bana nan...
Shiru tai ganin yadda mama ke mako mata
harara, "anya yarinyar nan kalau kike kuwa? Wato
sai dai ai ta min asarar hoda da kazal a banza
ina tufka kina min warwara koh?
"Farin jini Allah ya bayar kina ma kanki bak'in
ciki? Haka zan ta barar miki ni baki ban bare na
maida g'urbin abinda na fitar Salma?..
Maman ta k'allo da mamaki,toh rokon samari
mama take so ta fara komai? Allah yaga ta t'sani
fita zance.
Amma ganin yadda mama ke wanke ta yasa ba
shiri tace ma yaron "yace ma waye?.. Kai ya
daga mata,"wai ince inji
"Ja'afar in kin tambaya... Ai koh karasa wa nai
ba ta mike,tuni murmushi ya maye g'urbin 6acin
rai, da k'allo mama ta bita, kamar ba ita ce
yanzu ba.
Yau kam ga su Salma harda mit'sika hoda da
_lips stick_ har ta d'au hijab ta kara k'allon
madubi,kawai sai ta janyi g'yalen Ummi tai waje.
Shine kuwa yana jingine da gidan,wani murmushi
ta saka na farin cikin kara ganinshi a daren.
Da sallama ta karasa d'uk da ba wani haske gun
sosai,amma sai dan sinke kai take kamar rana.
Bayan sun gaisa kowa yai shiru kamar basu abin
fad'a.
Chan dai ya nisa ya miko mata ledar hannunshi.
Kamar mai neman ba'asi ta t'saya bata k'ar6a
ba.
"Ajiya na kawo kimin zuwa gobe ne,ba wani abun
ba naga kina tsoro.
Murmushi tai kan ta amsa tana k'allon Ummi
zata wuce,koh ci kanku bata ce ba ta shige gida.
D'uk sai Salman taji wani iri,Ummi sam taki jinin
Ja'afar ta rasa dalili.
Ba jimawa yai mata sallama dan ya rasa abin
fad'i shima.
Dama da Garba ne yau kam da zai iya fad'in
komai ga Salma.
***
Tunda daga lokacin Ja'afar ke zuwa gun Salma
jefi-jefi,d'uk da har yanzun bai furta mata so
ba,amma ita a ganinta d'uk acikin so ne.
A k'wan a tashi gashi har ta kammala secondary,
wannan itace tafiya mafi tsawo da Salma tai bata
ga Ja'afar ba,kusan wata bakwai.
Tun tana damuwa har ta hakura ta rungumi
karatun ta na fita.
Gasu yau sune a gida,d'uk an rame anyi baki.
By
Feenat Ja'afar.
[7/21, 10:10 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
10_Babban tunaninta bai wuce d'uk t'sawan
lokacin nan da aka diba ba Ja'afar ba labarin shi
ba,tasan yakan je mata ziyara makaranta koh a
t'satt'saye ne,ga ita ba waya ba balle ta neme
shi koh lafiya?
K'wana biyu da dawo wa yau d'ai ta kudiri niyar
fita jin ba'asi,koh Garba in ta gani.
Hijab d'in _mss_ d'inta har kasa ta sa harda
nikaf.
Sai d'ai har ta gama zagayen layin ba wanda ta
gani ciki,kawai burinta ganin Ja'afar ne.
Iyanzu kam tasan tai nisa kan sonshi ba kad'an
ba,sai d'ai ita yanzu ta fara tantama.
Har zata juya ta tuna da shago,d'uk da tasan
yanzu ba kasafai yake zama ba tunda ya samu
g'urbin koyarwa.
Sai dai tai chan d'uk bata tunanin ganin nashi.
Daga d'an nesa ta t'saya kusa da wata bishiya ta
d'an kare ba mai ganinta, da sauri ta juya tare da
dafe kirji,zuciyar ta sai bugawa take da k'arfi.
Yanzu ta samo amsarta da kuma kokwantan ta
da ya zama gaskiya... Bata aune ba sai jin
hawaye tai na bin kuncinta cikin nikaf d'in.
A hankali ta fito daga bayan bishiyar tare da kara
k'allo shagon.
Murmushi yake harda darawa, ita kuma budurwar
sai washe mai baki take tana ta mai zuba,rike
yake da hannun wata y'ar k'yak'yawar yarinya
fara kamar yayarta.
Ji tai wani abu ya tokare mata kirji,da sauri tasa
hannu ta dafe gun,ga hawaye yaki ya d'aina
malala.
Lalle tai wautar kin kula kowa sai Ya Ja'afar da
bai furta mata so ba.
Ido ta rint'se ganin ya d'akko mata wani
had'adan net purple yana bata,wato har kalar da
yasha sanar mata yana so ya bata?
Tai imani mai irin wannan zankadediyar budurwar
fara ba abinda zai da ita Salma baka.
Hannu tasa ta cikin nikaf d'in tana goge hawayen
dake zuba mata.
K'allo sun da zatai taga Ja'afar ya zuba ma inda
take ido,har budurwar na k'allo itama,da sauri ta
juya gabanta na fad'uwa, kar dai ace ya gane ta?
Tab,da k'wa ta bada kanta wallahi.
Juyo wa ta kara,sai karaf suka kara had'a ido da
Ja'afar. Ba shiri ta tare mai adaidaita ta
shige,tana k'allo ya bi napep d'in da k'allo yana
girgiza ma budurwar kai.
Kawai sai ta sa kuka mara sauti tare da cire
nikaf d'in.
Lalle tai wautar zurmuwa ga soyayyar Ja'afar,
soyayyar da ba'a ma bayyana mata ita ba... Ya
Ilahii.
**************************
"Oh! Man Ja'afar, dama kana k'allon mata har
haka? Bafa koh kiftawa?
Murmushi yai mata tare da girgiza kai, "Hala tai
kama da Salma ne? Danma da hijab ga kuma
nikaf..
"Kusan hakan ne, jikina ya bani kamar Salman ce
kam..amma nasan ba ita ba ce ma.
Dariya ta danyi har hakorinta farare suka
baiyana,kan tace "sannu _Romeo_ toh, ni
sallameni kan Amal ta fara neman mamanta,
amma ina mamakin yadda ka iya zaben kaya da
color, halama kana son _purple_? Murmushi
kawai yai mata,kan ya k'ada mata kai halamar
eh.
Ita kam Salma tana zuwa gida ta taho da yaro a
kofa ya kaima mai Napep kud'in shi.
Allah yaso ba kowa t'sakar gidan mama na d'aki.
A katifa kawai ta zube ta sau kuka,sai da tai mai
isarta tai shiru tana maida numfashi.
Chan kuma kamar wacce aka t'sikara ta mike
zaune.
Tabbas Ja'afar bai ta6a nuna yana sonta ba
kam,d'uk zuciya ke yaudarar ta.
Asalima da "K'anwata" yake kiranta, kila hakan
ne tun da,ita kad'ai ke kidanta, gaba d'aya ta
gama kore masu sonta ita a dole ta riki Ja'afar.
Hawaye ne ya kara zubo mata tunawa da yadda
yake washe ma budurwar nan baki.
Tasan yadda Ja'afar yake a gaban mata baya
wargi,baya sake fuska ma bare har yai musu irin
wannan tad'in.
"Tabbas budurwar sa ce,nai wauta ni Salma...
"Lafiyar ki kuwa kike maganganu ke kad'ai ya
sabuwar kamu?
Kai ta dago jin batun Ummi tana wannan y'atsine
matan.
Sai dai ganin irin yadda idon salman yadda yai
ja,ga kuma hawaye yasa ta mat'so
"Mey ya faru kike kuka haka?.. Ai kamar mai jira
a ta6ota ta kara sa wani kukan mai sauti.
Tuni kuma sai Ummin ta zauna tana lallashi da
fad'in lafiya?
Ita de sai kukanta take baji ba gani.
Tashi Ummin tayi,"bari na fad'o ki da mama
toh,kila k'ya fad'a mata ita... Da sauri ta rike
mata riga, "ni ba komai.. Marata ke ciwo da
bayana kawai.
T'saki Ummin tayi, "Allah kina da aiki a gaban ki
Salma,kukan jinya sai kace wata yarinya.
Ita dai tana jinta ta karaci kardinta tai waje,a
hankali ta zame ta k'wanta,sai sauke ajiyar
zuciya take.
*By*
*Feenat Ja'afar*
庐*NWA*
[7/22, 12:02 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
11_Kan safiya har ta gama tunanin abin da zai
fisshe ta.
Hakan yasa t'saf ta tashi kamar ba ita taci kukan
nan ba. Aunty A'i yau za'a kaima wuni,tun (12)
suka fice ita da Ummi.
Chan suka yini har dare,a kafa ta ratso ita kad'ai
sakamakon Ummi da ta biya kar6an _style_.
Tunda tazo layin su Ja'afar d'in taji gabanta na
fad'uwa, duk da bata koh k'alli hanyar gidan ba.
"Abokina ina ka tafi ne daga lissafi kai shiru?
"Ba kaga kamar Salma ba waccan mey tafiyar?
Ido Garba ya k'wara, da mutum,amma a duhun
nan bazai tantance ba,kawai sai ya k'ada mishi
kai,
"A cikin duhun daren nan ne har zaka gane wake
tafi.... Shiru yai ganin Ja'afar d'in yai gaba,da
sauri yace "wai mey ke damunka ne? Ina za
ka?.. Binshi yake shi kuma yana bin mai tafiya a
duhun.
"Salma"... Chak! Ta t'saya dan jin kamar an kira
ta,a hankali ta juya,da dan tazara a tsakanin su
kad'an, amma hakan bazai sa ta kasa gane ya
Ja'afar ba koh a cikin dubu,hakan yasa cikin
sauri ta juya ta chigaba da tafiya,har dan gudu-
gudu sauri-sauri take.
"Mey zai fad'a min kuma? Ta fad'a cikin ranta.
Har kusan layinsu ya bita, tsammanin shi koh
tsorata tayi,amma tabbas wannan Salma
ce,kawai sai ya t'saya a dai-dai layin nasu yadda
bazata ganshi ba,da hasken inji a layin, yana gani
ta t'saya ta waiga,kan da sauri ta shige gida.
"Amma fa baka aiki sam Jaa, wai har nan ka
biyota kage ma koh aljana ce a daren nan?
Juyawa yai yana girgiza mishi kai,"Allah Salma
ce,toh yaushe ta dawo?.. Baki sake Garba yace
"hadda rantsuwa? In Aljana ce fa mai siffar ta?.
Harara ya sakar mishi kan ya juya suka tafi.
Ita kam tana zuwa gida Abba da Mama suna
t'sakar gida ta shigo sai haki,tuni k'wa Abba
fad'a ya karu, kan mey yasa sukai dare?
Tuni tai zuru zuru,fad'a sosai tasha,saura
Ummi,d'uk da laifin Ummin har sukai daren.
Washegari kusan yamma sai ga nan yaro kan ana
kiran Ummi da Salma inji su isma'il.
Harara Salman ta k'wada ma Ummi, kan tace
"yanzu sai da kika fad'i ma mutanan gidan mu
kika huta koh? Allah ban san yayi6e ni.
Hararar itama Ummin tai mata,"arziki na binki
kina guduwa,kowa yazo kice bai miki ba,ki mayi
karatun ta nut'su wallahi,dan aure zanyi ni ba
jira..
"Keai Kowanne dan chaburos ma yazo Ummi a
shirye kike, toh ba dani ba.
Yankan farcen Ummin ta bari tai hanyar d'aki
tana fad'in"sai kiyi ta zama kar kiyi aure,har
mahadi ya baiyana.
Cikin kuluwa zatai magana sai ga Mama ta fito a
d'aki, ashe d'uk tana jin su, "toh k'wa maza ki
wuce ki je tun kan na sa6a miki,daga yau na
d'aina zuba miki ido ba fus bare ass Salma...
Yarinya sai taurin kai,ace koh kishin yadda y'ar
uwarki take shiga take fita da y'an k'wabai ba
kiyi? Toh na gaji da gafara sa dan ban hangi
kaho ba... Maza ki shiga daga ciki ki g'yara ki
wuce...
Kai kasa Salma tace "toh.. Ita kam tana
mamakin halin Mama har kullum akan su,sai dai
tana tuna Ja'afar tuni taji tana da muradin
fita,tunda wanda take danshi bai ma san tana yi
ba.
G'walo Ummi tai mata,kan tai waje tana sai ta
fito.
Bata aune ba taji mama a d'akin nasu, bani waje
ki ga,da kaina sai na g'yara ki...
Baki sake take k'allon Maman,aikwa ta zage ta
hau cha6a ma Salma k'walliya irin wacce bata
ma san mama ta iya ba.
Fad'i take "na rasa gane wace iri ce ke
Salma,arziki na binmu kina zura da gudu,d'uk
wani buri da na sa kanki kin rushe shi, in banda
haka a jiya kad'ai kina ga irin bajintar da Ummi ta
shigo dashi daga gun isma'il yake ko wa?
"Haba k'alle ki a madubi man,san kowa kin
wanda ya rasa... Tana yi tana g'yara mata
d'aurin dank'wali.
"Maza ki fita kan Abban ku ya dawo ya hana
ruwa gudu..
Kai ta daga zata d'au hijabi,da sauri Mama ta
warce, "g'yale zaki sa matar Malam,koh a
Shari'ar a haka ake son a ganki,ta ina za'a yaba
in kin maka hijabin? Toh ba walima nace kije ba..
Kai ta k'ada, ta zama tamkar rakumi da akala,sai
yadda mama tace.
"A'a, ko ke fa,k'alli kanki a madubi ki ga man,ai
da banbanci, maza je ki... Kai ta kara k'ada
mata, har zatai waje da sauri Mama ta kara
kiranta.
Turare ta fesa mata,kamar tace ba k'yau
mama,sai dai taja tai shiru.
"Ki murmusa man Salma,haba..murmushi ma ado
ne ga fuskar Y'a mace...
A yadda maman take yi bata ma san sanda abin
ya bata dariya ba.
Allah ya gama su da uwa "LASHE MONEY", har
ta fita kuwa tana murmushi, mama sai barta.
Suna t'saye gaban wata jar _CRV_ tare da
Ummi,d'uk dinsu sun zubo mata ido.
Ita kanta tasan tayi ne, fari da manyan ido kawai
budurwar Ja'afar zata fad'a mata tasan.
Doguwa ce ita dai dai misali,farin jinin samarin
zamani,fatarta a goge take mai launin Wankan
Tarwada(black beauty), tana gashi ga gashin
ido,gata fuska doguwa,gata tana da diri dai dai
so,d'uk komai ya ji ba bau ba.
Ya dace kam tai amfani da lokacinta tun yanzun.
Cikin takun da ba irin na Salma ta da ba ta
karasa gun su Ummi,ga murmushin nan dan
_beauty point_ din nan sai lot'sa wa yake.
Tuni ta kara tafiya da imanin Muzammil,har yake
ji kamar ya taro ta kan ta iso.
By
Feenat Ja'afar.
[7/22, 4:57 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
12_Ita kanta Ummi tai mamakin Salma da
sakewar ta.
Sun gaisa da isma'il saurayin Ummin su kuma
suka zaga dayan bangaren motar,
Kusan kawai d'aurewa take tana mishi yake,
amma ita sam taki jinin saurayi mai shegen
surutun t'siya.
Hakan yasa d'uk taji ta gagu su k'auce, ga tasan
Abba gaf yake da zuwa da magriba tayi.
Kamar ance daga kanki, Ja'afar tagani kusan su
kad'an, tamkar gunki yaja ya t'saya, ga nan
wannan budurwar da ta ta6a ganin su itama tana
k'allo su,sai ta k'alli Ja'afar, kawai sai ta d'auke
kai kamar bata gansu ba.
Harda kara bawa Muzammil wani _attention_ na
daban tana murmushi.
Cikin sanyin jiki ya juya,tana dan satar k'allon
shi,a baya budurwar tabi shi tana waiwayen
Salman,ji tai kamar ta k'wada mai kira,So ba
k'arya bane Salma.
Da k'allo Ummi ta bisu lokacin da suka zago ita
da isma'il, sallama sukayi,suna kokarin jan mota
sai ga wata bakar mota ta _parker_.
Ganin su Garba yasa da sauri Salma ta daga ma
muzammil hannu tana mishi murmushi.
Ja'afar dake k'allonta ta glass din ya rint'se ido
da sauri.
Ganin zata juya yasa Garba fad'in "Salma" da
sauri.
Juyo wa tai lokacin da yake yafito Jafar da
hannu halamar ya fito.
Koh ta kansu Ummi bata bi ba tai gida.
Yake tai mishi lokacin da suke karasowa,sai dai
koh inda Ja'afar yake bata k'alla ba shi da
budurwar shi.
Cikin barkwanci Garba yace "duniya da alkawari
kuwa Malama Salma?.. Murmushi tai mishi iya
le6e, "ashe kin dawo amma koh mu sani..
Karon farko ta k'allo gun Ja'afar, idonshi k'wa a
kanta girrr...ba koh kiftawa.
Da sauri ta d'auke kai daga kanshi.
Gaidasu tayi,budurwar na mata an dawo. Lafiya?
A ciki ciki ta amsa,Garba yace "yaushe a gari?
An gama lafiya _hope_?
Da mamaki take k'allon shi,yanzu dama da
wanda zai ce bai san y'an makaranta sun dawo
ba?
Kawai dai sai ta maze, "yau kusan satin mu da
dawo wa.
K'allo Ja'afar d'in Garba yayi,kan ya dawo da
K'allonshi ga Salman.
Ba wannan dawowar ba,yau k'wana uku da
zuwan mu K'anwarki tace mana kinyi tafiya...
Da sauri ta dago kai da mamaki,tana k'allo gun
Ja'afar d'in ya d'auke kai.
Garba yaci gaba, "zuwan mutumin kenan daga
Zaria yace sai ya zo ya ganki ya miki murna,ashe
ke har kin ma fice a garin.
Batta bakin magana,dan bata san amsar basu
ba,amma Ummi tana mata daya a rayuwa..wai tai
tafiya?
"Ga nan mutumin jiya har sururu yake yaganki da
dare ina mishi t'siya, ashe ke ce.
Kai ta daga,kan ta kara k'allon Ja'afar, d'anna
wayarshi yake kamar bai wajen.
Cikin wasa Garba yace "toh ni zan gabatar mata
da ita ko mey da kai mikis?..kasan ba kunya zan
ba ni.
Murmushi budurwar tayi kai duk'e, dan sam bata
ga fuska gun Salman ba.
K'allon Ja'afar din take,yayin da yake k'allon
Garba yai shiru.
"Toh,mu bama sanya, sai ya juyo gun Salman,
"Salma ga nan budurwa,kuma matar... Da sauri
ta rint'se ido,kan ta karasa da "Ja'afar"... Na
sani Malam Garba...
D'uk ido suka zuba mata har Ja'afar baki sake,jin
shirun yasa ta bud'e ido akansu,yadda suke
k'allonta tasan tai su6ul da baka...
Cije le6e tai,amma ta bada kanta wallahi....
Dariyar keta Garba yasa harda k'yak'yatawa, sai
ta dago tana k'allonshi.
Sai da yai mai isarshi kan ya k'allo Billy,
"Haba,Yanzu na ji batu,ni fa naga kowa yana
sassahan kamshi,ashe-ashe...uhm uhm
_Jealousy_...
"Toh wannan Matar Garba ce bata Ja'afar
ba,sassauto madam.
Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta,har
batasan sanda murmushi ya su6uce mata ba.
A kunya ce ta k'allo Billy,sai ta mat'sa kusan da
ita kan tace "sannu da zuwa...
Dariya suka sa mata banda Ja'afar da ya dan
dara,idonshi kir a kanta,bazai iya fassara mey
hakan yake nufi ba, shin Salma na son sa da
kishin sa ne koh mey?
Ita dey sai dan satar K'allonshi take,amma
bazata iya fassara ina ya dosa ba.
Mota su Billy sukai suka barsu,ga nan magriba ta
gabato,gaidashi ta kara yi itama ciki
ciki,t'sayuwa ya g'yara kan ya amsa,tare da mata
murnar kammala karatu,shiru ba mai cewa
uffan,kowa miskilin kanshi,kawai sai sukai
sallama kan gobe zai zo.
Tana shiga gida dan takaici kasa ma Ummi
magana ta cikin fad'a."yanzu Ummi kina k'yauta
min kenan a rayuwa? Mey Ya Ja'afar ya t'sare
miki ne ki ka ki jinin shi?
Rai ta had'e, kan tace "oho,kawai bai min bane...
Ga nan sakon daga Muzammil,kinga in da ake
harka ai...
Kai ta k'ada dan takaici tai d'aki batabi koh ta
kayan ba.
Washegari dan kalata sai ga su sun dawo, ana
la'asar, mama ta fita unguwa.
Ado Ummi ta ciwo da tafi na jiya,sakare tai ganin
Salma koh mot'sawa batai ba.
"Koh ba zaki bane Salma?
A tunzure tace "ba zani ba..
Baki Ummin ta ta6e,kan ta daga kafada,
"mat'salar ki ce wannan kuma... Sai tai waje.
Aiko yaro sau biyu ana yi daga waje daga
Muzammil amma fur taki fita.
A ka'ro na uku ne yaron suka shigo da Mama da
ta dawo daga unguwa.
Dole ta tashi badan rai naso ba,sai dan ganin
Ummi ta shigo ta had'a ta da Mama kan taki
zuwa gun Muzammil.
Tana had'a rai ta fito,sai dai da mamakinta taga
Ya Ja'afar t'saye yana aiken yaro kan tazo. Da
sauri ta koma cikin zauren kan ya ganta.
Jim tai kad'an bayan fitar yaron kan ta fito,kanta
t'saye tai gun Ya Ja'afar, kan tace ya bata minti
biyu dan Allah.
Kai kawai ya k'ada mata,sai tai gun su Ummi,a
mutunce suka gaisa,kan tace da Muzammil
sakon shi sai gobe.. Bata jira amsa ba tai gaba.
Shi kam Ja'afar k'allonta kawai yake,amma tuni
har yazo wuya.
Tabbas dole ya bayyanawa Salma yau ranshi ba
sai an k'wana ba,dan wannan samarin tsaf sai su
iya kasa shi yana k'allo.
"Bissmillah, muje zaure... Bai yi musu ba yabi
bayanta.
Har ya dan saki fuska, dan sam ba kaunar zaman
ta a layi yake ba.
Bayan sun gaisa yake bata labarin abinda yasa
bai je mata ba.
"Kinsan Mamana tana a Zaria ne,sun rabu da
Abba tun ina dan shekara biyar,hakan ya zamana
Abba ya k'ar6e ni a dalilin tai aure,nakan kai
mata ziyara haka,sannan dan ita na zabi zuwa
Zaria karatu.
A _time_ d'in da za ai _visiting_ aka aiko bata
lafiya,chan naje har t'sawan wata uku.
"Taji sauki sosai,har tana ta fad'an na koma
bak'in aiki na,ana haka y'arta K'anwata ta dawo
sun gama makaranta,hakan yasa na tuna da
Salma.. Nan nai shiri na dawo,duk dan na
ganki,sai aka samu akasi, Ummi tace kinyi
tafiya... Shiru yai kai duk'e, itama tai tsam tana
sauraren shi.
"Salma"...kai ta dago ta dan k'alleshi, shima
idonshi a kanta. "Yanzu kam lokaci yayi da zan
sanar ki wani sirri,sai d'ai ina fatan wani bai
rigani yad'awa ba...
"Salma"... Cikin wata siga ya fad'i, kan yace "na
jima ina dakon son ki azuciyata,tun ma kan
Salman tasan itace...
K'allonshi take baki sake,shikam ya zage sai
tona sirrin ranshi yake a gare ta ido bud'e..
Dad'i, farin ciki har ya kasa misaltuwa a gun
Salma,So d'aya ne, tasan Ya Ja'afar tai ma.
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 8:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 13_Har
yai shiru ita kam idonta na kanshi,kan dafa bisani
tai kasa da kai cike da kunya,kawai shima sai ya
zuba mata na mujiya yana murmushi. Magana
suke jiyo wa kasa-kasa,duk sai suka zuba ma
kofar ido. "Ba mutunci ace kowa yana wuce wa
yana ganin ku a t'saye a titi, gaba na fad'a miki
ki nemi koh zaure ne koh cikin gid... Shiru Abban
yai dan ganin Ja'afar a zauren da Salma.
D'ukawa ya danyi kan yai ma Abban sannu da
zuwa. Cikin sakin fuska Abban ya amsa,Salma
ma ta mai kai duk'e. Sim-sim Ummi tazo ta
wuce,dan duk iskancin ta tana bala'in tsoron
Abban su sosai. Yana shiga gida shima yai mata
sallama da alkawarin gobe zai zo dan jin amsar
shi. Da t'sananin farin ciki ta shiga yau, haka
dashi ta tashi. Tun jiyan Ummi ke ci mata kunu,
tasan kuma d'uk akan Muzammil ne,shi yasa koh
bi takanta batai ba. Washegari tun kan Ummi ta
shiga wankan yamman ta na kullum Salma ke
gaban mudubi, sosai take k'yali, yau d'aya ta
bata lokaci dan Ja'afar d'inta. Ummi da tun dazu
ta fito tana jira ta ta6e baki, ''kiyi kare ni ki ban
waje na zauna Malama... Juyo wa tai da tana
yage mata baki, "dan Allah Ummi nayi k'yau?..
Bar zancen wasa. Baki ta ta6e kan ta juyar da
kai gefe, "oho miki ni kar ki daman. Murmushi tai
kan ta tashi ta bata gu. Bincike ta fara,a babu
babu Mama kala 5-5 ta musu kayan _candy_ na
ke ce sa'a, ciki masu ruwan _purple_ ne kusan
duk. Cikin nishad'i ta ciro attamfa wata mai
_purple_ da rat'sin _yellow_ riga da siket,
murmushi tai dan tuna wa da kalar da Ja'afar
yafi so kenan. Tunda ta zura kayan ta nad'a
d'auri take bin kanta da k'allo a mudubi ta gefen
Ummi. MashaAllah tai k'yau, gashin da ya fito ta
kasa take turawa cikin dank'wali,ta kai dubenta
ga Ummi wacce sai ko'k'arin fiddo nata take tabi
dank'wali ta kansu. Murmushi kawai ta
mata,tasan da tace ta mayar su ciki ma a iska.
Sai dai tana d'akko turare ta hau feeeee ba ko
kakkautawa. "Haba Ummi,turaren nan kinsan
haramun ne sashi ki fita koh?.. Ga gashi kullum
sai ance ki alkinta shi.. Allah kina *TABARRUJ*
da yawa.... Galala take k'allonta, kan ta ja t'saki
tai waje. Iya wuya Salma tazo, ta bala'in t'sanar
t'saki. Ba'a jima ba Ja'afar yazo.. Tabarma yau
ta d'aukar musu,shima yasha wankan farin kaya
da farin takalmi _half cover_ sosai yai mata
k'yau. Yadda yake fara'a da bin k'allonta tasan
itama ta wanke shi. Suna t'saka da gaisawa
cikin nishad'i yaro yazo,wai tazo a waje inji
Ummi. Tuni ya sauya,dan yaga zuwan su
Muzammil. "Minti biyu kawai.. Kai ya k'ada mata
da dan yake. Tana fita suka ware gefe,tsakani da
Allah ta fad'a mishi yai hakuri. Baki sake yake
binta dashi har ta kule cikin gida. Amma Ja'afar
ya bala'in k'wada shi da kasa,dan haushi koh
isma'il bai jira ba yai gaba. Ita kam tana zuwa ta
bashi amsa gamshasshiya, wanda tasa fara'ar
Jafaririn ta dad'u ba shiri. Tad'i suke kamar ba
gobe, mot'si kad'an yace "kinyi k'yau..... Itama
cikin kunya tace yayi shima. ***************
************** "Naga sai zarmewa kike fa akan
Ja'afar salma,sam kinfi k'arfin shi kima ji da
wai,gaba ake son ci ba baya ba wallahi,d'uk da
ban san wacce iriyar amsa kika bawa Muzammil
ba... Da harara Salma ta bita, kan tai k'wafa, "ina
ruwan ki da sha'anina? Ke har kin isa ki fad'a
min wanda ya dace dani Ummi? Baki Ummin ta
ta6e, "ke dai kika sani,dama ni meye nawa? Ni
koh ana saurayi mey zanyi da Ja'afar mai shegen
dacin ran t'siya... "Wai ku baku zama inuwa
d'aya ne da juna Salma? Mey yasa baki iya daga
ma Ummi K'afa sai kin tanka mata kullum kuna
sa makota na jin ina daga murya.. Kasa Salma
tai da kai kawai,tasan yanzu in mama taji ta
kad'e.. Kamar k'wa wacce Ummi ta karanci
zuciyarta ta amshe.. "Wai fa mama daga
shawara ta tsaya min masifa,yau akan wannan
dan gidan Malam Kabiru mai shago ta kori
Muzammil,daga fad'a mata gaskiya ta hau ni da
masifa.. Dan Mama daga ganin yadda Muzammil
ya tafi rai 6ace nasan cewa tai bata son shi...
"Eh bana son shi,koh ana son dole?.. Ja'afar d'in
da kika rena ni shi ya min ki ji da wai.... "Kunga
ku min a hankali,koh yanzun nan na sa6awa
mutum... Shiru sukai,yayinda Salma taci ka tai
dam. "Ke ummi wani dan wajen Malam Kabirun
kike fad'a? Da harara Ummin ta k'allo Salma kan
tai ma Mama bayani,"yanzu haka mama Malamin
makaranta ne wallahi yana chan yana kokawa da
alli.. Jim Maman tayi kamar mai tunani,chan ta
nisa tace "Ikon Allah..anya yarinyar nan Salma
ba'a min misanye dake ba a layin jarirai a
haihuwa ba?... Mutum arziki na binshi yana
ki?...Ina laifin yaran nan?har kasa suka gaida
ni,ga mota ga boko..amma in banda abinki mey
na sama yaci bare ya bawa na kasa? Da shagon
uban zaku dogara koh da kud'in malami?.....
Shiru Maman tayi ganin yadda Salman ke
hawaye... "Au,au,Salma kuka? Daga fad'an
gaskiyar? Kai ta k'ada ma Maman. "A ni tawa
mai sauki ne Salma,ina d'ai hanga miki gaba ne
kawai... Amma banga abin kuka.... "Wa ke
kuka?... Assalamu Alaikum. Shiru sukai salman
na goge ido,sai Mama da ta amsa mishi sallama.
"Sannu da zuwa Abba. Kai ya daga musu kan ya
amsa. D'uk suka tashi sim-sim sukai d'aki. Sai da
Abban ya gama komai yasa Mama ta kira su.
Kowa tai ladab kai kasa suna saurarar Abba. "Ni
ke Ummi na ma kasa gane alkiblar da ki ka kama
sam,kullum da wanda za'a ga yazo gunki,sai
aukin shegen zance a titi ba wanda ya iya yazo
ya samu iyayen ki.. "Ga nan yayarki yau d'in nan
yaron nan na wajen Alhaji Kabiru yasa Baban shi
yazo muka zanta kan yana son Salma da
aure,kuma har sun sasanta da ita.. "Koh ba ai
haka ba Salma?... Kai duk'e cike da kunya ta
daga kai halamar anyi. "Haka shine musulunci, ta
haka kuma ake gane da'ar yaron da zai auri
y'arka... Shiru kake ji Ummi anyi lakwas. Nan ya
kara ja ma Ummi k'unne kan tara samari da
zancen waje,ya kuma ja mata k'unne kan ta
fidda na aure koh ya fiddawa mutum. ***** ***
Zancen aure dai ya kank'ama tsakanin Ya Ja'afar
da Salma. Itama Ummi Isma'il yace da gaske
yake.. Mat'sala d'aya tafi damun Salma,yadda
komai Ja'afar ya bata na alheri a rene yake gun
su Mama, barin Ummi. Dan ita fachaka isma'il
yake mata kamar ba gobe. Tun abin bai damunta
yau da gobe har ta fara ganin kamar Ja'afar
mammako yake mata. Zuciya bata kashi. By
Feenat Ja'afar. 庐NWA.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 24
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
14_Anyi bikin su Garba. Ana haka saurayin Ummi
ya d'allo mata wata sabuwar waya,ita kam tun
wata Zain da ya bata,nan habaici ya karu gun
Ummi. Biki ya kusa sukai shirin zuwa Borno
dangin Abban su. Sunyi sallama da Ja'afar ta
shigo gida rike da farar ambalan,d'uk suna zaune
t'sakar gida har Aunty A'i da yaronta. Hannunta
Ummi ta k'alla, kan cike da shakiyanci tace "ta
Ja'afar mey aka samu ne haka har a farar
takadda?.. Harara ta dan mata kan ta mikawa
Mama. Kai Maman ta k'ada, kan tace "a rabani
da kayan haushi,rike abinki kawai ki kirga...
Dariya Ummi ta sa,wanda tuni ta kara kular da
Salma. "Mama ba ma sai ta kirga ba,dan wallahi
ba kaffara nasan kud'in nan bai fi dubu biyu ba...
Kanta Salma ta yiwo a tunzure mama tai musu
iyaka. "Meye na jin haushi?.. K'yautar tashi tana
wuce nan ne?... Ba dai d'an d'an kasuwa zaki
aura ba? K'wafa tai,kan tace "baki fara ganin
komai ba ma Salma. Aunty A'i ce ta k'ar6a ta
kirga,ai kam sabbin hamsin hamsin ne ta dubu
biyu. Mama tace "Ahab,na sani ai. D'aki Salman
tai tana hawaye,sam bata kaunar abinda ake ma
Ja'afar,amma shima da laifin shi,dubu biyu ina
zata kaita? ****************************** Biki
kam yazo,gashi yau har anje jere, k'warai sunyi
mamakin gidan Ja'afar da gina kuma da kanshi.
D'uk da ba wani babba bane,dan koh t'sakar
gidan karama ce,babban _parlour_ ne sai _bed
room_ da band'aki aciki,ga _kitchen_ a ciki
karami,sai d'aki d'aya daban a waje, d'ai d'ai
zaman mutum d'aya de,rufin asiri dai ak'wai
shi,Alli da shago sunyi rana. Sa6anin Ummi mai
tafkeken gida da mai gate yasha alatu. Yanzu
lefe ake wat'sa ido aga na Ja'afar, dan tuni na
Ummi yazo san barka,sai zuzutawa ake. Salma in
ta tuno gabanta har fad'uwa yake,fatan ta Ya
Ja'afar ya fitar ta a magana. Dan tun a kud'in
anko taga tasku,dan isma'il ankon k'yauta yai ma
k'awayen Ummi da dubu ashirin nata na fitar
biki. Shikam sai hakuri yake bata,kan shi bai
d'aura ma kanshi abinda bazai iya ba,bare daga
baya ya dame shi. Kawai sai ta toshe k'unnenta
gun su mama,komai ta samu ta samu,wanda ta
rasa tasan bai da hali. Mamaki kam Ja'afar ya
bama su mama, dan ak'wati shidan nan y'ar yayi
sai da aka bat'se ta da kaya, ga uban
_cosmetics_ har a jakar Ghana must go. Aciki da
swiss d'aya, holland biyu,engla biyu,sai su code
dav'ior,sauran kam duk kana na ne su dangin
material. Salma baki har k'unne jin ba wanda ya
kushe a dangin sai d'ai ace na Ummi yafi t'sada.
Anyi biki lafiya kowa ya wat'se an bar amare da
halin su a gidan su. Kauna ziryarta taga gun
Ja'afar mai t'sayawa a rai,sosai sukai amarcin su
cikin kula da tarairayar juna,musamman ga
Ja'afar d'in. _kitchen_ tare,wanki tare,shara
tare,duk aiki in dai ba ya fita bane yana a makale
da Salman sa, d'uk wata kulawa tana ganinta a
gun Ja'afar,shi yasa sai abinda yace take
aiwatarwa matukar bai sa6a Shari'a ba. Yadda ta
fuskanta ma kamar bai kaunar tai nesa dashi,koh
dan ganin har wata biyu kenan da bikinsu amma
ba inda taje sai barkar Aunty A'i da makotansu
da taje tun tana sati daya da zuwa. Sai dai tai ta
jiyo shewar su ta katangar gidan halamar ana ta
_chapter_. *Farin Bacin komai* Yau tun tashinta
sallar asuba ta kasa komawa bacci,sakamakon
tun dare da yace yau ta shirya da wuri zata gida.
Dan farin ciki ji take kamar a wani garin zata je
musu. Waya tai da Ummi kan zata fito yau gida.
Gaban madubi take tana yi tana k'allon agogo
har sha d'aya saura. Karar _machine_ d'in Ya
Ja'afar taji a kofar gidan,sai ta cigaba da
shiryawa. Sallamar shi taji,daga d'akin ta amsa
tana fara'a. Yana shiga ya jingina da kofar d'akin
yana mata murmushi,ta mudubin ta mishi tana
d'auri. Kan ya tako gaban madubin ya t'saya ta
bayanta. "Sannu da dawo wa.. Kai ya daga
mata,sai kare mata k'allo yake, kayan sun mata
k'yau, "Kinyi k'yau... Tashi tai da jin dad'in
kalaman shi,sai ta dan ja mishi kumatu kan tace
"na gode... Muje koh?.. Ta fara nad'a lifaya. Sai
ya rike mata daya gefen tana nad'a dayan da
murmushi. Da kanshi ya yafa mata akai ya rufe
ko'ina ruf. "Ba dan kin nace sa abar nan ba da
hijab d'inki za ki sa zai fi min k'wanciyar
hankali.. Murmushi tayi kan ta lang'wa6e kai, "ai
ba g'yale bane Ya Ja'afar, Allah ina son lifaya.
Kai ya k'ada mata yana d'aukar mata jaka. "Toh
naji,amma ni banga maraba ba. Murmushi kawai
tai tana d'aukan mukulli. Machine d'in ya karkata
mata kirar lifan,a hankali take ko'k'arin hawa sai
ya dan girgiza machine din,da sauri k'wa ta dafa
kafad'arshi suna dariya. In kagansu g'wanin k'yau
suna ta nishad'i har suka zo gida. Tana g'yara
lifaya tace "bazaka shiga ba?.. Kai ya girgiza
mata da murmushi,"ki gaida su Mama, anjima in
nazo d'aukan ki zan shiga, yanzun makaranta zan
koma. Kai ta k'ada mishi,kan ta bashi hannu,sai
ya bata suka gaisa suna dariya. "Abincin ka yana
a kitchen a bisa faranti,na had'a komai, a dawo
lafiya... Kai ya daga yana mata murmushi,jin yaki
tafiya tace "kaje man.. Kafad'a ya make yana
nuna mata gefen fuskanshi, kai ta k'ada mishi
cikin kunya. "A layi muke fa... Shima sai ya kada
kan tukun ya tada sukai sallama. Har ya kule
tana daga mishi hannu,kan tai cikin gida. Da dan
gudunta ta shiga tana kiran Mama. D'uk suna
d'aki, Ummi an hakimce a kujera ana d'anna
waya. "Har kun rigani ashe d'uk saurin nan
nawa?.. K'allonta Ummi take ganin tana since
lifaya,ga flasks da jaka an ajiye. "A ina zaki zo
da wuri,ke dad'i miji ce ai.. Banza tai da ita tana
gaida Mama, itama Maman a dan ciki ta amsa
mata. D'uk sai taji ba dad'i, jikinta yai sanyi,da
murnar ta tazo amma sun dakushe mata. "Sai ya
barki ki waiwayo mu?.. Maman ta k'alla, kan tai
kasa da kai, "ai na zata irin ta y'an da zai
miki,sai kin shekara koh kin fito yawan arba'in....
Baki Ummi ta ta6e,kan tace "d'uk mai irin halin
Ja'afar ai dole yai k'ulle Mama,in banda haka
wata biyu wai sai yau za kizo gidan ku,ni nazo
yafi a girga,wallahi tun wuri ki mawa tufkar
hanci.. Dan in kika sabar mishi da haka zai mike.
Dagowa tai da niyar yi wa Ummi magana Mama
ta tari numfashinta. "Y'ar uwar ki ce,dole ta fad'a
miki gaskiya, ke zaki nema mana mutunci a gun
miji ki ma ji da k'yau. Kasa tai da kai tana
murmushi, duk da a zuciyarta bataji dad'i ba
sam. "Mama baza'a a sake ba inshaAllah. Da
haka aka ware kuma zancen nawa ta tara a
banki. "Ni fa ba'a ban kud'in cefane Mama, komai
yana kawo min har katin waya,sai dai in ina da
bukata yana cewa na mai magana... Baki Ummin
ta ta6e,kan ta zuge jaka, sai ga nan kud'i tumi.
"Kinga kud'in cefane na,nima ai ba abinda na
rasa,ina ruwana da wani ni kud'in kati? Kawai naji
dumus ni... Gashi nan na banki ne dana sa Mama
ta sai min. Kai Maman ta k'ada, tabbas Ummi
tasan ta kan maza,shi yasa take burgeta sosai.
Itade Salma an sata duhu,dan sun raba
hankalinta biyu. T'saka mai wuya kenan. By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:00 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 15_Sai
dare yazo a dalilin yadda take fad'in bata gama
ba,har cikin gidan ya shiga,kawai kuma sai yake
ma Mama k'warjini, dan fuska sake ta amsa
mishi,kan suka tattara suka tafi. Koh da Salma
tazo k'wanciya maganganun su Ummi take ta
tunawa. Ita babban haushinta ma yadda aka fa
fad'in koh tsoron Ja'afar take. Washegari ma
haka ya yakaita gidan su Abban shi,nan ya wuni
suka biya gidan Garba. Yau tun (7:30) ya fita,
sakamakon an fara jarabawa a makarantu. Sha
d'aya ta gama aiki ta fara jiyo hayaniyar y'an
unguwa a makotanta,halamun sun hallara za'a
fara chapter. D'uk yau sai hankalinta yai
gidan,duk da ba sabawa tai dasu ba. Waya ta
d'auka,ta d'anna kiran Ja'afar _no answer_.. Ji
take kamar ta zaga in ya dawo ta fad'a mishi,sai
dai ta daure. Da yamma kam kamar kullum yazo
fita shago tace zata leka makota. Jim yai ba
amsa,sam tarbiyar matan unguwar bata mishi
ba,baya so Salma tai sabo dasu a samu
mishkila,amma kawai sai ya k'ada mata kai, "Sai
kin dawo. Cike da murna ta rakoshi har bak'in
kofa ta koma d'aki. Da sallamarta ta shiga,tun
daga bak'in kofar gidan zaka fara jiyo karad'in
matan. Da fara'ar su suka amsa,d'uk sun baje a
tabarma, wasu ba koh dank'wali. A dan kunyace
ta gaida su, dan ganin duk sun girme ta,sai wata
mai kamar shekarunta da D'a a goye. Chan hira
taci gaba, zabiyar ciki sai karanta musu makamin
kama wuyan maza take. Salma tai shiru tana jin
su,tabbas babban burinta shine Ja'afar ya so ta
har karshen rayuwa. "Su amarya yanzu ai farin
take gani kan a juya mata bak'in bayan.. K'allo
matar tai,bata gane nufinta ba,sai dai bazata iya
tambaya ba. Haka firar yau ta tashi kan makamin
rike miji har Salma ta fito. Tunda ta zauna a gida
take tariyo firar sun. Tabbas shawarar nan tayi ta
makamin rike miji, ta hakan kam ba yadda
Ja'afar zaiyi ya raina ta... Toh amma Ja'afar
yana sonta,batajin zai mata dabi'a irinta mazajen
sauran Matan da ke fad'i. Nan ta jefar da
dayawa a hudubar da taji a makota tai kitchen
dan k'unna ritio. Sai d'ai Washegari ma da
yamma Salma ta sake tambayar shiga makota.
Karan nan kam kir ya fito yace mata a'a, da ido
kawai take binshi, "Ya Ja'afar yafi zaman kad'aici
ne,ba jimawa zanyi ba ka ji... Ta langwa6e kai.
Ba dan yaso ba ya k'ada mata kai. Minti biyar
bata kara ba tai makota,gidan chapter. Yau kam
a sa'a taje,dan suna a kan firar rashin fitar matar
gidan,sai bata dabaru suke akan yadda zatai mijn
ya rika barinta fita. "Kar ki fara tambayar
unguwa kina fara'a, sosai zaki dake mishi,mud'in
yaga 6acin rai toh jiki na bari zai barki. Ni da
farko haka Salisu ya t'siro min da k'ulle,tun farko
nai ma tufkar hanci,da yace A'a yana fita zan
arce, gashi yanzu har ya saduda yana barina duk
inda na tambaya. T'sam Salma tai,tana tariyo
maganar Ummi da Mama ta ranar,ga nan ta
makotanta. Daga ganinsu sun san takan duniya.
Tabbas ta yarda itace tun yana d'anye ake
tank'wara shi. Tun yanzu ya dace ta takawa
Ja'afar birki koh dan ta t'sira daga zargin wai
tana tsoron shi. *Wasa farin Girki.* Daga ranar
Salma ta tsiri dan hali,fita makota,tambayar fita
gida,ga wani t'sarewa da take in tana tambayar.
Kamar kullum tazo rakiya taja ta t'saya a gefe,
"Ya Ja'afar... Jiyo wa yai shima rai ba dad'i,tare
da zuba mata ido,yasan abu daya zata tambaya.
"Zan leka gidan Maman Ummi gobe suna za ai
k'ulli... K'allonta kawai yake, yadda tasha mur
tamkar wanda take bashi umarni. "Anya Salma
wani abu bai shiga kanta ba kuwa?.. Gaba daya
ta sauya mishi hali k'wana biyu in dai akan fita
ne.. G'wara tun wuri ya taka mata burki dan yaki
jinin yawan fita sam shi. "Kiyi hakuri Salma,ki
bari ki leka goben tunda suna ne... Tuni ta
k'ank'ance ido, "gaskiya kar ka maidani saniyar
ware a unguwa ya Ja'afar, yau k'ulli kowa ya je
sai ni ce bazani ba?.. Ai sai a chake ni gobe
dama suna fad'in ni dad'i miji... "Kuma ma ba
wannan ba,nima sai ina zuwa za'a zo min in
nawa yazo ai.... Shiru tai ganin yadda ya zuba
mata ido yana kallo, chan ya nisa "amma Salma
kin fuskanci kin fara sauya hali kuwa?... Kin koyi
ja dani,kin koyi gantali k'arfi da yaji.. K'alloshi tai
a wani iri, "au gantali ma nake Ya Ja'afar?..
Fisabilillahi wace fita ce nake yi ba dalili? A satin
nan sau biyu koh uku ne fa na fita kuma dubiyar
Ummi ne ba wani waje ba, koh shi ka ke nufi da
gantalin? Kai ya k'ada,"kar mu rika ja in ja dake
Salma,kiyi hakuri kawai gobe ki je... Juyawa yai
ganin tana neman wata maganar yai waje, baki
ta ta6e,kan tai cikin d'aki. Tana jin tashin
machine d'inshi ta zaro hijabi ta k'ulle gida tai
cikin gidan k'ulli. "Ai na zata bazaki zo ba,da har
zanyi aike naga machine din maigidan. Hijab ta
cire ta jawo jarka, "bari ke dai Maman
Ummi,dak'yar na fito fa.. Murmushi tai kan ta
d'akko wani abu a bakar leda,"yanzu saratu ta
fita an kawo sabbin kaya dakakku wallahi,tai ta
jira baki zo ba zata tafi na dau miki wannan...
K'ar6a tai tana dubenshi kan ta kunce ledar,roba
ce karama da wani abu mai d'anko. "Takalmin
Kaza ake fad'a miki,nasan yafi haka,kawai ta
mana sauki ne.. Amma abin ba magana,sai an
g'wada akan san na k'warai... Dariya suka sa aka
tafa harda shewa. "Wannan ne kawai makamin
wulakancin D'a namiji,tunda kuka d'aurani kan
_network_ nake son raina Allah. "Dari biyu ai ma
yai araha... Bari yazo dari biyar zan tat'sa, dan
asusu nake kan zuwa watan haihuwar Ummi na
tara da yawa... Sai da aka gama k'ulli ana firar
duniya,a debo gulma har aka gama,ana kiran
magriba ta tuna Ja'afar, da sauri-sauri tai gida
dan yau abinci ta zarce tayi. Kamar kullum ya
dawo bayan magriba ana kiran isha'i, sai dai sam
ranshi ba dad'i,nan tasha jinin jikinta,koh ya
dawo bata gida ne? Har yaje masallaci akai isha'i
bai dawo ba har ta gaji da jiranshi ta k'unna inji.
Sai chan kusan tara ya shigo,har yanzu jiya
iyau,sam kuma sai taji ba dad'i, tun kan ya fad'i
lefin da tayi,amma de sai ta dake. Komai
yayi,dan har abinci ya ci,sai dai fur yaki sakar
mata. "Wai Ya Ja'afar mey nai ne ka ke ta shan
kanshi?.. K'allonta yake da mamakin anya
Salman shi ce wannan?.. Bai da amsa,sai a
gunta kawai,saboda haka ya tashi yai hanyar
d'aki. By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:03 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 16-Ya
fito a band'aki ya ganta zaune a gad'o,kai ya
dauke yana goge jiki da _towel_,d'uk sai jikinta
yai sanyi,tabbas tasan Ja'afar kila zuciya
yayi,har ya gama shirin bacci uffan bai ce mata
ba,tuni ta fara kuluwa ganin ya ja filo bai bi
takanta ba. "Wai mey in ma ina ta maka magana
tun dazun?.. Kai ya dago ya k'alleta da tuhuma,
"mey kika ce ban amsa miki ba?... Baki ta turo
gaba kad'an, kai ya kada,tukun yace "Salma!...
Salma!!.. Dagowa tai ta bashi hankalinta dan jin
kiran da yawa. "Na'am.. Ido ya tsura mata,sai tai
gefe da nata. "Ina kika fita dazu har magriba?..
Jin tambayar tai ta bazata,hakan yasa ta kasa
K'allonshi, sai da ya maimaita tukun ta amsa a
hankali da "gidan k'ulli... "Gidan k'ulli?.. Mey
mukai dake toh kan na fita?... Duk t'siya ta ki
jinin kuma taga ran Ja'afar ya 6aci, sai dai an
rinjayi zuciyarta. "Kai hakuri... Itace Kalmar da ta
fad'i. Tashi yai ya jingina da pillow,kan cikin
nut'suwa ya fara mata magana. "Ba wannan ne
ba karon farko da ki ke fita ba'a son raina ba
Salma,nasha aiko yaro da sako yace gida a k'ulle
yake,amma nai ta daga miki kafa. Duk gantalin
da take bada yardar shi ba sai da ya sanarta,ga
t'sinuwar mala'iku dake binta har ta dawo...
"Sam wannan ba Salman da nasani a wata 5 d'in
baya ba... Wannan cikin wata d'aya ta sauya,bata
jin magana ta,duk abinda tasa kanta take ganin
shine d'ai dai shi take... Sosai ya kasheta da
kalamai,har ta fara hawayen wai bata jin
magana. Murmushi yai kawai,kan ya dan taso ya
janyo ta ya hau kuma lallashi,da alkawarin
bazata kara ba,sosai ya ji dad'i,dan yana son
mutum mai gane kuskure in ya yi. Washegari
_week end_suna ma haka tai shiru,sai dai kasan
ranta ji take kamar tai filfilwa taje gidan. Tasan
iyanzu an kusa sauke abinci ana ta cin chapter
ba ita. Sai dai tai ko'k'arin ganin bata tambaya
ba. Shi kuma ganin haka yasa yaji dad'i,fatanshi
yasa Salma ta g'yara ne. Ce mata yai yana
zuwa,yana fita ta kasa zaune ta kasa t'saye.
Anya bazata leka ba kan ya dawo?.. Dan tasan
yanzu ana chan an kafa da ita uwar son miji. Sau
biyu tana k'wata fita tana dawo wa,a na ukun taji
dirin machine d'in Ja'afar ta koma. Sai gashi da
leda baka a hannu. Sannu da zuwa ta
mishi,burinta ya fita ta fice, amma fur yaki. A
jima kadan ta k'alli agogo,kafarta har kaikayi
take,da ya k'allota ta sai ta sau mai murmushin
dole. Kamar ya kula sai yace bari yai wanka,yau
sha biyu yake son yaje shago. Ita dai ta samu ya
fice,Allah koh satar hanya sai taje gidan sunan
Maman Abba. Toh sai ma ya barta harda mika
mata ledar riga ta barka. Abu kamar gaske
Salma kamar anyi hankali, sai hali ya dawo sabo.
Shiga makota kam Ja'afar har yai hakuri ya zuba
ma Salma ido, Gashi yanzu su Salma har ketare
ana t'sallakawa,kusan duk yanzu unguwar sun
san da Salma,ga surutu da t'sabar manyance da
ta koya zama cikin manya. Ranar Garba suka zo
gidan a 6ame da mukull,sai ya d'au waya ya kira
Ja'afar din. "Ba kowa fa a gidan nan Aboki,dan
da mukulli a 6ame.. Daga chan Ja'afar yai t'sam,
kan yace "oh,sorry pls,na manta tace zata je
dubiya, ga wayanta ba chargy... Kai Garban ya
kada "toh dai mun fita,dama ita ke mitar madam
shiru,yanzu kam ma had'u suna. Murmushin dole
ya k'akalo,yana cewa ace Billy tai hakuri. Bayan
sun gama ya ajiye waya,Salma tasa ya tafka
karya,dan da abin kunya ace yana mai gida
amma bai san matar gida bata nan ba... Toh mey
zai wa Salma ne?.. Ya mata d'ukkan nasiha,yayi
fad'a, yai lallami,amma tamkar a iska yake
zubawa. Sai tayi kamar ta d'aina, gobe ta fidda
sabon hali. "Assalam Alaikum... Kai ya
dago,ganin mey sallama yasa ya fad'ada
murmushin shi, cikin girmamawa yace "a
Abba,sannu, yana sunne kai, murmushi Abban
yayi,kan yace ''yauwa Ja'afar,ka ga na dawo,zan
dan zaga ne, baya,dayan shagon nan ba kowa ne,
nazo arar Sadi minti biyu.. Kai kasa yace "Bari
na zauna kan ka dawo nan bana komai. Yasan
zai samu ma damar yau amar da abin da ke
ranshi. Yana shagon Baban ya k'wance ya
d'aure, ya fad'a ya je gida ya shiga uku gun
Salma.. Shawara d'aya ya yanke, gun Mama, dan
yaga ita batta zafin Baban. Tun yamma ya
tashi,bayan sun gaisa da Maman faran faran
yake sanarta halin da Salma ta t'suro mishi.
Kamar abin kirki harda bashi hakuri,da fad'in zata
t'sawatar mata. Sai d'ai tana fita Ummi da tun
shigowarshi tai zamanta a d'aki ta fito. "Kai
amma mama mutumin dan rainin hankali ne,wai
kinji fitar Salma tai yawa? Matar da sai tai sati
biyu wataran ba tazo gidan nan bama bare har
fitar ta tai yawa.... K'wafa Maman tai,kan tace
"ke lefin shi ki ka ga?.. Ai lefi na gun Salma da
ta zauna yake juyata kamar waina... A zamanin
y'ancin kai ake yanzu, bana tsawalawa dana..
Kaza kaza,har Abba ya shigo zaure ya dan t'sinci
wani zancen,amma bai gane kanshi ba. Kullum
Ja'afar na sa ran yaga Salma ta sauya,sai dai
shiru,sai yai tunanin fad'an Maman ma bai shige
ta ba. Ranar Garba yace a gidanshi zai magriba
yace Salma tai musu irin gurasar nan tun tana
amarya. A gabanshi ya kirata, a lokacin an zube
ana ta firar kashe wando a makota bayan
layinsu, Koh da ta sauke waya ta cigaba hirarta.
Chan kusan magriba ta kusa ta tuna da zancen
Ja'afar,kusan ma d'uk y'an firar an wat'se amma
Salma matar gida ta riketa wai suna firar su zata
tafi? Yaron gidan tasa yai gudu bayan layinsu ya
siyo mata gurasa mai siga ta karbi kud'i gun
matar gidan. Cikin nishad'i suka zo sai dai gida a
6ame,ga yau ta bar mukullin shi a ciki. Ranshi in
yayi dubu ya 6aci,basu jima ba sai gata
tanan,duk tabi ta burkice, duk da koh k'allon inda
take Ja'afar bai ba. Sai da Garba take magana
tana ko'k'arin bude gida. By Feenat Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 17_Shi
dai Garba har suka shiga gida yana zungurar
abokinshi kan ya saki fuska. D'aki ta shiga tana
mai adu'ar Allah yasa a samu gurasar nan,in ba
haka ba yau ta kad'e har ganyenta a gun Ja'afar.
Suna t'sakar gida suna alwalar magriba sai ga
yaro yai sallama rike da k'wano,da sauri ta fito ta
amsa,har ta shiga Ja'afar na bin bayanta da
ido,k'wafa yai kamin yai ciki, shi dai Garba duk
ya gane da wata a kasa. Kitchen ta sameta tana
jera su a faranti. Tasan shine amma fur taki daga
ido ta k'alleshi. "Nagode Salma, kinji? Na
gode,amma ba zanci gurasar titi ba ki sani...
Kofar kitchen din ya rufo sukai waje. Ita kam koh
a jikinta,tunda de ta t'sallake fad'a ai shikenan.
Yau dai ya kasa d'aurewa, har sai da ya sanar da
Garba halin Salma ba ragi. Sosai yai mamaki,wai
Salma ce da halin nan? Sai dai kawai ya bawa
abokinshi hakuri, da kuma ya rage saurin fushi...
Haka ya wuce gida ba tare da shima yaci ba. Da
dare ya d'au pillown shi ya koma parlour,baki ta
ta6e tai k'wanciyar ta. Sai dai koh minti ashirin
ba ai ba ta hau juyi,ta ture pillow,dan Allah yaga
bata saba k'wanciya ba'a hakarkarin Ja'afar
ba,duk fad'a kuwa. Ba shiri tazo bada hakuri dan
tasan ya bala'in jin haushi. Shi kuma haushin shi
d'aya da hakurin Salma,tunda ba wai zata g'yara
bane. Kuka ta fara mishi harda shura kafa kan
wai ya juya mata baya yaki kulata. Juyo wa yai
yana k'allonta, duk da a kule yake da ita amma
har kusan dariya yaso saka. "Ba nace kai hakuri
ba,Allah kasan ban ta6a kin yi maka abinci ba da
gangan... Tashi yai ya zauna a kusa da ita. "Toh
naji na hakura,bar borin...ya sa hannu zai goge
mata hawaye sai dai kamas... "Au kukan ma na
karya ne ashe?... Dariya ta fara ta d'au mishi
pillow sukai d'aki. "Ina a gidan nan Allah ba kai
ba k'wanan parlour. Murmushi yai yana mai
tausayin kanshi, ina ma Salman shi ta da ta
dawo mishi... Ina ma zai yuwu ace kullum yaso
ganin Salma zai sameta a gida haka?... Ya sani
da yana son Salma,so ba na wasa ba,amma k'arfi
da yaji so take tafi k'arfin shi,ga ko kadan bai
kaunar yaga fushin ta. Ina ma itama haka take
nannan da nasa fushin... Yasani da *Mai Hali
Baya fasawa* **************************** Sauri
take tayi,dan yau gidan mai gumama suka
je,tasan kuma tabbas Ja'afar yana hanya. Aikwa
tana zuwa ga nan machine d'inshi a kofa
halamun yana ciki. Duk da tana jin dan shayin
shiga su ar'ba, haka ta d'aure ta shiga. Takaddu
yake nema, da sallama ta shiga, a chan ciki ya
amsa yana cigaba da abinda yake. "Sannu da
zuwa... "Uhmm.. Kawai yace, sai ta ta6e baki.
"Gidan fa mai gumamar nan da na fad'a ma jiya
ta aiko mana za'a kawo muka je..kaga zuwan
banza mukai ma wai sai gobe. A dirare ya
k'alleta lokacin da yake tashi, ganin yai banza
yasa tace "ni fa nan kad'ai naje,sai gidan Maman
Ummi dana biya mata muka tafi.. Kai ya k'ada,
kan yace "yayi k'yau... Maman Ummin ce mijin ki
koh mai gumamar?... Ido ta zaro,sai ya kada kai,
"no ba wannan ba ma, wai d'uk inda kike
azarbabin zuwan nan wa kike gani yana zuwa
gidan ki yafi minti goma aciki?... Koh d'uk suna
da aikin yi sai ke kad'ai ce bakki shi?.. Salma ki
nemi mutuncinki da hannunki,a ganina zai fi
mu.... "Ka ga malam,ba sai ka zage ni ba zan
san dama kana kule dani ba,daga fita nan da nan
din shine har zaka na cemin wata gantalalliya?...
Haka kawai,in ma kayan ne naga kai zan sawa
ba wani ba,toh meye abin zafi aciki?. Kai ya
k'ada kan yace "babu... Amma wallahi kar gobe
ki sake ki kara fita gun wata mai gumama,in ba
haka ba zan mugun sa6a miki... Waje yai rai
6ace, "Ja'afar?... Ni zaka sa6awa?... Chak! Ya
t'saya ya kasa gaba, a hankali ya juyo fuskarshi
d'auke da mamaki. "Salma... Yau ni kike kama
sunana garangatsai ba koh rufi?... K'ugu ta rike
tana girgiza, "ai sunan ka ne naga.. Kuma muna
kama sunan Allah ma bare wani chan... Na gaji
ne da hancini. Kai ya k'ada yana murmushi,
tabbas ba abinda yai saura da gantalin Salma bai
gur6ata ba,ciki kuwa harda iya fit'sara. Sai ya
k'ada kai ya fice,dan yasan komai zai iya faruwa
in ya tanka. ~~~~~~ Washegari haka aka tashi
kowa rai ba dad'i, yau ce ranar farko da har aka
waye gari ba'a shirya ba. Ga yau week end,yana
gida yaki fita shago. Har yamma ba bayani, sai
dai yai bacci,ya je masallaci ya dawo. A sama
take,dan gani take da gayya yaki fita dan ai ba
ita gidan gumama. Ya dawo daga masallacin
la'asar ya shiga wanka. Maman Ummi ta turo
tazo suje kan a za6e,yana jin lokacin da tace dan
aiken yace tana zuwa. Yazo fita ta biyo shi,dan
tambaya a ganinta ta wanke lefin jiya ya barta.
"Ya Ja'afar zamu gidan wannan mai kayan
Maman Ummi na jirana. Ja yai ya t'saya, kan ya
juyo ya koma parlour,ba musu ta bishi ai wacce
za ai. "Tun jiya ai mun gama magana dake,babu
fita... "A gaskiya sai na je, gashi nan ai kai ka ke
jawo komai, da lallami na tambaya ba zaka barni
ba,sai na fita cibi ya zama kari... Haka kurum
yanzu haka jirana ake ka ce wani bazani ba..ta
karasa tana kunkuni. "Sai kinje koh?.. Cikin
fusata tace "eh.. Murmushi yai ya k'ada kai,
"Bazan hanaki ba toh, sai dai wallahi ki sani,
mud'in kika sa kafa kika fita,toh *A BAK'IN
AURENKI*.... Bai jira komai ba yai waje,yana
jiyota tana ai wallahi bazaka sani kaffara ba,fita
kam nayi na gama. By Feenat Ja'afar. 庐NWA.
Like 路 6 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Ummu Maryam Tahir
Sannu da qoqari 6ter
Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Kareema Wakeeli
Tnx
Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 18
_Kitchen_ kawai ta leka,ta d'aura guntun ruwa a
tukunyar silver a _hot plate_ nata karama nepa
suka d'auke wuta. Kamar zata kashe,kawai ta
bari,a ganinta ba komai. Kan su kai gidan
gumama kuwa 5 tayi,fatansu Allah sa ba'a za6e
ba. Kaya kam gasu masu k'yau, tuni ta fara
daddagawa tana ware na wara. "NEPA"... Cewar
yaran gidan, sai dai da halamun su Salma hankali
yayi kan gumama. Suna nan a gidan har kusan
k'arfe 6,amma basu gama da mai kaya ba.
Kamar ance daga kai sama,sai ga nan dan
hayaki na yin sama halamar daga nesa ana
gobara a wani gu. "Ina ga wutar dazu tai ma
wasu aiki,hayakin nan gobara ce duk yadda
akayi.. Kai Salma ta k'ada, "koh taya ake konawa
ba... Sai dai kan su farga ihun gobara har kusan
layin da suke. Maman Ummi tace suzo su je,in
yaso daga baya sa dawo suyi bayanin. Da sauri
Salma ta tare, "A'a Manan Ummi,nasan yanzu Ya
Ja'afar na hanya 6 saura. "Muje dai koh gobe
tunda ta kirga wanda muka d'auka ma dawo ai
sabon lissa... "Umma!..Umma!!... Da gudu yaron
mai gumama ya shigo, matar tace "lafiya irin
wannan gudu? Ince dai ba daga gun gobarar ka
ke ba? Yana haki yace "a gidan Aunty Salma ne
fa Umma.. Ana ta neman inda za'a shiga a k'ulle,
yanzu aka kira Malam Jaaf... "Na shiga uku... Ni
Salman koh wa?.. Kai yaron ya daga,ai ina,da
gudu ta fice ta wat'sar da kayan a nan ta bar
Maman Ummi da kira. Kamar wata sabuwar
kamu haka ta iso wajen,kofar gidan cike da
jama'a wasu na kok'arin sanya t'sani su haura. A
ka ta d'aura hannayenta d'uk biyun,tama rasa ihu
zata kurma koh kuka. Baban Ummi ne yace ina
mukullin gidan?.. Nan ta fara tunanin mukulli?..
Innalillahi, ta barshi shima gidan gumama... Baya
ta fara yi ganin Ja'afar da Garba sun faka mota a
chan gefe, a gigice suka karaso, "Innalillahi
Wa'ina Ilaihirraji'un"... Itace kalmar da Jaafar ya
iya fad'i. Ina kan ta farga sai ga hawaye na zuba
tana girgiza mishi kai,mukulli Garba ya tambaya,
kan cikin azama ya lalubo a aljihu ya bashi.
Salman ya k'allo cikin tausayin kanshi, har yanzu
hannu na ka tana k'ada kai tana kuka. "Shikenan
kin zaunar mu Salma... Burin ki ya cika sai ki
zuba ruwa a kasa ki sha.... Tuni ta kara fashewa
da kuka. Fad'in "A kashe meter... Ne yasa yai
cikin gidan da sauri. Ba ka ganin koh ina sai
dusu-dusu dan hayaki. Da taimakon Maman
Ummi ta bar kofar suka shiga daga cikin gida.
Sai dai har yanzu kuka take baji ba gani. Yau
tasan ta kad'e har ganyenta. Motar kashe wuta
ce ta iso,da taimakon dak'yar wuta ta mutu.
Ilahirin kitchen da bedroom ya kone ya laso
parlour ta silin Allah ya t'sayarta. Fito wa tai
bayan taji komai ya dan lafa ta leka gidan,sai ga
nan Ja'afar din sun fito rike da barbadin
_documents_ nasa a hannu. Kamar munafuka ta
dan ra6a ta shigo kai duk'e tana jan hanci. Sai da
yazo dai dai ita ya t'saya. Kanta kasa tana
sharar hawaye,a hankali ya saki burbudin
takaddun ya fice jiki duk yayi sanyi.
**************************** Zaune suke a bak'in
masallaci shi da Garba bayan komai ya lafa yana
tausarshi,yan unguwa sai jajanta mishi suke suna
tafiya. "Dan Allah ka'r ka ce zaka d'au
mummunan mataki akan Salma, kai
hakuri,ubangiji ya mayar ma da alkairin da ka
rasa. Shiru Ja'afar d'in yai,zuciyar shi sai tafasa
take,dan ma yana ta kok'arin neman kariya daga
zugar shedan. Zuwa chan dai ya nesa, "Babban
ni takaici na Garba Takaddu na ne,tun jiya ake
_verification_ gobe ne namu,ni bana ta
Salma,dan a bakin aurenta ta fita... "Ni ga nan
d'akin waje zan iya maleji. Kafad'arshi Garban ya
dafa,lalle kowa da jarabawar shi a rayuwa,shi
kuma abokinshi ta mata Allah ya bashi. "Yanzu
toh ya za ai?... Murmushi Ja'afar d'in yai wanda
yafi kuka ciwo... "Ya k'wa zanyi Garba?.. Kana
sane da gamnatin nan tamu, wa zai k'ar6i uziri
na gobe?.. Shiru yai mishi,dan tabbas yasan bai
da abin fad'a ma abokin. Gida suka koma,tana
nan inda suka barta a durkushe ta tasa takaddun
a gaba tana shesshekar kuka. Ja yai ya t'saya
yana k'allonta, muryar ta har ta dashe. Abin
haushi wai kuma zuciyarshi ta fara tausayinta.
Da sauri ya d'auke kai daga k'allonta dan jin
zuciya na ingiza shi yaje ya lallaso ta, Salma ce
fa... Dake wa yai ya daure tukun yace "toh meye
ne na kuka kuma Salma?..ki tashi kawai kije gida
dan sharad'in dazu yana kan ki.... Da sauri ta
dago ta k'alleshi, tuni taji kukan ya kafe,sai ido
da ta kafe shi dashi, shaf ta manta wani sharad'i
ne ma? Tuni ta tafi duniyar tuna abinda ya afku
ka ta fita. Garba ne ya katse mata tunani da
fad'in "haba dai dan Allah? Wannan sharad'in bai
k'yautu a gun ka ba Ja'afar.. Aure ya fice wasa
fa.. Ka janye sharad'in nan tun kan kowa ya ji ku
koma auren ku.... Da sauri ta k'allo Garba,duk ta
kasa ta6uka komai, Mey Garba yake nufi da su
koma auren su? Yaushe Ja'afar ya sake ta?....
Bai furta ba sai dai in yanzu.. Cikin muryar kuka
tana ka'rkarwa tace "bai sake ni ba Garba, auren
mu na nan... Koh yanzu ya furta?.. Banji ba
Allah... Ni bai sake ni ba...bai sake ni ba.. Sai ta
karasa tare da fashewa da wani kukan mai ban
tausayi. Ido kawai suka zuba mata, tamkar
zararriya haka take magana. Duk sai ta karya
musu zuciya, barin gogan,har bai san ya je
gareta ba,da zummar dago ta yaje ya lallashi
abarshi,sai dai kamar wanda aka t'sayar ya
d'auke hannunshi, baya ya koma yana rint'se
ido... Tabbas yanzu saki ya gifta a tsakani,bai da
_right_ na ta6ata,tabbas bai dashi. A hankali ya
furta "Salma kin cuce mu... Kin fara dasa
katanga a tsakanin mu... Ban san da abinda na
rage ki ba Salma...ban sani ba, dazu a yadda
nake jin zuciya ta,wallahi dan banzan doka naso
na miki,Allah ya kareni da yin kuskure. Baya ya
juya mata,kan ya k'allo Garba. "Dan Allah ka
kaita gida gani nan zuwa... Waje yai ya barsu
nan,Shikenan ta tabbata,ba makawa Ya Ja'afar
ya sallama ta.. Ai tuni ta kara jiniyar
kuka,dak'yar ta tashi sukai waje da Garban. Sai
duba Yayan nata take koh zata ganshi. "Muje
Salma,InshaAllah komai zai daidaita,.. Juyowa tai
ta sadakar da yai nisa... Yana k'allon su har
suka kule kan ya fito a inda ya 6oye a bayan
bishiya. Harda goge y'ar k'walarshi... Salma kinyi
aiki. By Feenat Ja'afar
9/29/16, 9:06 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?...
Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan
Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima.
Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita
sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai
mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi
adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta
dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar,
kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba
cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na
bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya
sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da
yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da
ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta.
Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar,
"Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda
ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya
dago,mama in banda harara ba abinda take sakar
mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin
nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma
ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama,
kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki
Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da
wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare
da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma
kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada
kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba...
Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey
zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada.
"Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da
aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma...
Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN
AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma?
Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka,
"Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara
ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki
bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce...
Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai
kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da
haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya
lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole
kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min
ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya
kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk
laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take
aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au
mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi
hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya
gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi
hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na
rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa
banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba
nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake
bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa
ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai
yace bari yaje gida shima ya d'au machine
sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga
bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani
mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai
g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci
yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina
sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau
bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin
kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta
k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki
ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu
na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar
dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin
zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse
bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba
malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan
mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace
"sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?...
"Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje
yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya
babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin
samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai
ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki
saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min
ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki
Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita
haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na
6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi,
ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron
Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya
6alla tan. By Feenat Ja'afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Zeenat Yakubu
tnx 1st 2 cmmnt
Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?...
Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan
Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima.
Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita
sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai
mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi
adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta
dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar,
kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba
cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na
bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya
sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da
yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da
ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta.
Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar,
"Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda
ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya
dago,mama in banda harara ba abinda take sakar
mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin
nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma
ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama,
kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki
Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da
wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare
da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma
kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada
kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba...
Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey
zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada.
"Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da
aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma...
Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN
AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma?
Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka,
"Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara
ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki
bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce...
Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai
kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da
haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya
lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole
kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min
ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya
kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk
laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take
aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au
mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi
hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya
gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi
hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na
rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa
banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba
nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake
bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa
ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai
yace bari yaje gida shima ya d'au machine
sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga
bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani
mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai
g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci
yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina
sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau
bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin
kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta
k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki
ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu
na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar
dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin
zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse
bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba
malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan
mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace
"sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?...
"Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje
yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya
babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin
samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai
ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki
saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min
ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki
Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita
haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na
6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi,
ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron
Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya
6alla tan. By Feenat Ja'afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 20_Koh
da Ja'afar din yazo haka ya kara bashi hakuri kan
suka d'au hanya. Zaune take a d'akin da ya rage
musu,duk ta dawo kalar tausayi. Waya yake
amma yana k'allon yadda ya takure kanta tana
K'allonshi. D'anna wayar ya cigaba bayan ya
gama, cikin nut'suwa ta hau bashi hakuri, kan
Allah bazata kara ba. Sannan bazata kara fita ba
izinin shi ba. Shiru yayi,hakan yasa ta fara kuka
tana rantsuwa kan haka. Sauka yayi akan 1sittern
dake a d'akin ita kad'ai sai karamar katifa da filo
daya da ledar t'sakar d'aki. Yasan dan so yana
ma Salma,sannan yana matukar ganin darajar
Abba cikin idonshi, sannan yana mutunta
soyayyar da ta mishi a da chan baya. "Salma kin
d'aina so na yanzu sam,shi yasa ki ke ganin
damata a yanzu... Ki duba kiga abinda yawan ki
ya wanzar mana...nayi imani a garin saurin ki
fita ne har kika manta wani abu a k'unne a
kitchen... Ki duba irin kinjin magana ta abinda ya
jawo... Salma takadduna sun kone kaf...sai
guntu, sanin kanki gobe muna da _verification_
da za'a gunar mana. "Ba wanda zan je ma hannu
Rabbana ya k'alle ni... Kinga meyiwa na rasa
aiki,dan zan shiga _miss call_... Kinga kin zaunar
mu... Ba gida ba aiki.. Cikin kuka ta mat'so tana
bashi hakuri, "kai hakuri banzan kara ba Allah..
Murmushi yayi kamin ya janyota da sigar lallashi.
"Ina sonki Salma,kisa a ranki komai zanyi zanyi
ne _for your own good_... Bazan ta6a miki abu
dan tuzarci ba... _cos I love you_... Kank'ameshi
ta kara cikin jin dad'i... Tabbas tana son mijinta,
zata jure komai dan 6acin rana irin wannan. Koh
da yazo k'wanciya ita tana gefe yaga bata niyar
k'wanciyar tunda ta fito a bayan gidan waje.
Daga k'wancen ya mika mata hannu halamar
tazo. Har wata kunyarshi ce ta da tazo mata
yanzu. Da rarrafe ta isa gareshi,sai ya nuna
mata kafad'arshi kamar kullum,nufunshi ta sa
kanta. Da murmushi ta g'yara, kan cikin nut'suwa
ta zame ta k'wanta. Duk kusan tare suka sau
ajiyar zuciya, bata ta6a saba bacci a kafad'ar Ya
Ja'afar ba... Haka shima bai ta6a sa6a bacci,ba
tare da Salma na hakarkarinshi ba. A daren ta
tabbatar mishi da lalle har yanzu tana son
nashi,har ma tai kok'arin mantarshi wasu
abubuwan. *Hmmm..Allah sa da gaske ne
Salma*... *************************** "Haba dai?
Yaushe?.. T'salle ta doka lokacin da ta sauke
wayar a k'unnenta... "Ya Ja'afar.... Da sauri ya
katseta da "Ummi ta haihu... Yana murmushi.
Hannunshi ta kamo,sosai tana a farin ciki.
"Yaushe zamu ganin baby?.. Murmushi yayi,kan
ya k'alli agogo, shida da rabi,harda wasu y'an
mintuna. "Yanzu kam dare kinga ya gabato...
Gobe da safe kan ma an sallamota sai kije koh?..
Kai ta k'ada tana wani tunani... Jin ya kai hannu
cikinshi yasa ta dan murmusa.. Gira ya daga
mata,kamin yace "saura mu koh?... Murmushi tai
mishi ta k'ada kai. "Mun kusa ai...k'wantar da
hankalin ka sarkin son yara... Dariya sukai,kan
yace "sosai ina son su kam...in naje yaron Garba
kamar nace su bamu aro... Kai ta k'ada, "lalle a
gaishe ka.. Ni kam nafi son mu shekara kan na
haihu da... Murmushi yai yana kada kai kawai.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~ "MashaAllah, ganshi
kamar dan larabawa... Ta g'yara mishi hular
kanshi... Dagowa tai cikin wasa tana"um um,su
Ummi an iya haihuwa... Shiru tai ganin yadda
Ummin ta 6ata rai. "Mey akai kuma ki ke wani
6ata rai ina magana?.. Baki ta ta6e,kan ta ja
k'wanon namanta ta fara ci. A y'atsine tace "ya
bazan bata rai ba?... Saboda t'sabar wulakanci
tun jiya na haihu amma sai yau zaki wani zo kina
nad'e taburmar kunya?... K'allonta take ba
kiftawa, sam Ummi batta kunya.. Sai dai kawai
ta basar. "Dadina dake Ummi baki bada uziri a
koman ki.. Yanzu ina laifin kin haihu da magariba
nazo da sassafen nan?... Baki ta ta6e kan ta
had'iye naman bakinta. "Ki ce kinbi order mijinki
dai Malama, amma bare nawa ne suka zo tun a
jiyan?.. Karara tsoron mutumin yaci k'arfin ki
k'wana biyu na fuskanta... Shiru tai dan bakin
ciki, ba abinda ta t'sana irin a dinga cewa tana
tsoron Ja'afar...K'wafa tai cikin ranta. Zuwan
Aunty A'i ne yasa aka dawo mutunci kuma.
Kullum tana gidan Ummi,duk dan gudun magana.
Yau kam Ja'afar yace ta hakura gobe tunda aiki
jibi kuma suna,yau masu g'yaran gida zasu zo.
Ba tace toh ba,haka bata ce a'a ba. Sai dai duk
ta sauya,tunaninta muddin yau take zuwa gidan
Ummi,toh ba makawa sai sunce chaketa,hakan
ya tabbata kenan ita mai tsoron Ja'afar ce.
Tabbas lokaci yayi da zata nuna musu bata
tsoron Ja'afar. Hakan yasa da k'warin g'wiwarta
ta tashi ta bishi d'akin waje. Shiri yake yana son
fita wajen ciciku cikun neman takaddun shi da ya
kone. Yanayin da ya ganta ta dan kama kai
yasan yau abin ya mot'so. Kawai sai ya kau da
kai. Zama tai gefen gado tana k'allon shi ta gefe,
"Haba Ya Ja'afar dan Allah... Yau daya kar kamin
haka dan Allah, ka barni naje tunda an g'yara
kitchen ga kuma d'aki muna dashi a waje bayan
suna suyi aikin.... Ido kawai ya zuba mata,sai da
ta kai Aya tukun yai magana. "Ke mey yau din
zata miki in baki fita ba?.. Kullum fa tun
haihuwar nan kina fita Salma,dan yau kad'ai nace
ki hakura sai gobe shine ba zaki iya ba Salma?
Fuska ta y'atsine, kan tace ita dai kawai ya barta
ta fita toh. K'allonta yake,abu yai sauki yanzu
tana son dawo da hali? "Son ranki za'a bi yanzu
koh nawa Salma?... A gida na ban isa nace ga
abinda za ai ba sai ace a'a?.. Meye haka kike
son kawo wa kuma da ya wuce?.... Hawaye ta
fara mishi,tabbas yau in bata fita ba,toh gobe fa
sai dai ta toshe kunne. Haushi tai bala'in
bashi,akan wannan shine harda kuka?.. Sam bai
son abin da ya wuce a dawo dashi. Nan ta zaune
mishi tana mishi kukan gardamar sai ya batta.
Haka yanaji yana gani sai shi ya sauke ya barta
yace ta shirya su je. Da murnarta ta shirya suka
fita ya sauke ta. Sai dai shi sam baida walwala.
Haka tai ta fita har ran suyar nama,washegari
ma wai zata wanke gida,anan suka hau suka
fad'o.. Ya ja ta ja,harda fad'in dama ance
tsoronshi take ji. Ya rant'se da in har ta fita,toh
zai maimaita mata abin ranar,wato ta fita a bakin
aurenta. Tuni ta nut'su ta dawo hankalin ta. Tuni
ya kashe bakin t'sanya,har ya fice ya barta tana
kuka,harda dariyar mugunta... Ya k'wa gano lago
ai. By Feenat Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
21_Ranar ta fita a Napep ta layin su Ja'afar taga
wani kamar shi tare da wata, har zasu wuce ta
gane Bintu ce,da sauri tace mai Napep ya t'saya.
Sam a yadda suke ba kace ba masoya bane,dan
sai wani sunne kai take kasa halamar kunya.
Tuni zuciyarta ta hau tafasa,ba shiri tai wajen
gadan-gadan,dai dai suyi sallama harda dago
mishi hannu. Kan ta karasa har ya juyo itama ta
tafi... Ganin yanayinta shima ya dan
tsorata,amma sai ya maze. "A'a, har kin fito?..
Harara ta sakar mishi kan ta k'allo Bintun da har
tai mata nisa. "Ban sani ba... Ashe dama zance
ka fito shine kace na hau adaidata koh?.. Kuma
da Bintu?.. Har kana wani yage mata baki...
Hannu ya kai kan bakinshi halamar tai shiru yana
duba layin, "Haba Salma,a titi fa muke,kiyi hakuri
ba abinda ki ke zata bane ba... Harara ta kara
sakar mishi,kan ta farga har ido ya ciko da
hawaye. Tabbas yau ya tabo jaraba... Dan sarai
yasan Bintu kam sonshi take,kuma Salma ta
sani. Akan kishiya k'wa, yasan sai Salma taki ci
taki sha. Tuni ya hau lallami harda rantse rantse
kamin ta yarda bayan anje gida. Wataran yakan
yi tunanin koh Salma na da Aljanu,in ta tashi
sauya hali tafard daya ne,sai dai in ya bud'e
mata wuta su shirya. ~~~~~~~~~~ "Shiru ake
jinki makociya,koh dan ziyarar yamman nan an
daina zuwar mana sai jefi-jefi, koh mutumin har
yau yana nan da kullen?... Baki ta dan ta6e,kan
ta bawa maman Ummi amsa. "Ai sai abinda yai
gaba, yanzu tunda akai abinnan na farko abu
kadan sai ya kafan sharad'i kan in na t'sallaka a
bakin aurena, ina gudun rabuwar mu,yanzu ma
minti goma ya ban na dawo. Baki Maman Ummin
ta ta6e, "lalle kina da aiki in dai mazan nan ne,
saf zasu mayarka marar y'anci in bakai ma
tufkar hanci ba,harda lokaci? Tab aiki.. Ga gobe
sunan _nurse_ din layin chan (Maman
Nuwaira),ke koh barka baki je ba, ke kinsan za'a
watsa karya kiyi kok'ari ya barki muje. Kai ta
k'ada, "Ai dole,dan wallahi baza ai bani ba,ko bai
bari ba naje koh minti ashirin ne a wat'sa
warishan nan dani. Hannu Maman Ummi ta bata
suka tafa harda shewar su,ana haka Ummi tai
sallama,kan tunda ta shiga Jafar yace tana nan
ta fito,wai sai had'a rai yake,shi yasa ta bar
mishi gidan, nan ta daura kan na Maman Ummi,
Zuwa chan Maman ummin tace "Kiyi kok'ari hudu
ki biyo min zuwa 5 dawo. Da wannan suka baje
har ta wuce ka'idar Ja'afar. *Washegari*. "Wai
dan Allah Salma na tambaye ki zaki ban amsa?
Y'atsine fuska tai kan tace "ina ji.. "Shin dad'i ki
ke ji in kin t'saya muna musayarya magana
dake?.. "Mey yasa in na ce ki bar abu sai dai nai
son ranki,amma ni ban isa ba? "Ita maijegon ta
ta6a tako kafarta cikin gidan nan da sunan tazo
gunki?.. Ki ban amsa? Baki ta saka,kan tace
"oho,kana nufin gyaiyar sod'i zani kenan?.. Tunda
ga areni muje biki koh?.. Kai ya kada, "Ke ki ka
kira kanki haka,ba Ja'afar ba,abu daya na sani,ko
na fita ba jimawa zanyi ba, saboda in ma kin
fita,toh kisan inda dare ya miki... "Mey ka ke
nufi? Kana nufin yau ma zaka ce a bakin auren
nawa Ja'afar?.. Da sauri ya kada kai,
"K'warai,tunda abinki naga na yanzu har so yake
yafi na da, in har kam kin fitan,toh kisani,kin fita
*A BAKIN AURENKI*... Sai ki zabi wanda ya fi
miki, aure? Koh gidan suna?... Kofar ya bugo
mata yai waje tare da barinta baki sake. "Eh lalle
yau zan nuna ma tabbas ba tsoron ka nake ba
Ja'afar... Wannan kurin bakin wallahi bazai
hanani fita sunan ba,daga yau kalmar nan ta *A
BAKIN AURENKI* tabar bakinka. Daki tai tana
balbalin masifa ita kadai kamar yana k'allonta.
Kaya ta fito dasu tana duba wanda zata sa,
_lace_ din sunan Ummi ta dakko wani karamin
_swiss_ da aka sashi siyanshi dan dole. Sunan na
manya ne, dan haka sai da kure adaka. Ba koh
shakku ta fice, yau tun dazu taji gidan su Maman
Ummi t'sit kamar ruwa ya shanye su,halamar mai
gidan yana nan kenan,amma tunda ta fara jiyo
hayaniya tasan yai waje. Gidan suna kam ya
kayatu, sun samu abinda ake so tuni aka baje a
faranti ana ci ana kora wa gulmar wata. Kan ta
farga har 5 da yan mintina. Haka kawai taji
gabanta na fad'uwa hankalinta yayi gida. Tashi
tai ana fad'in ta t'saya k'ulli ya kare a k'ulla
mata tana a bawa Maman Ummi. Sauri take ta
zubawa, dan da y'ar tazara a t'sakanin su.
Adu'ar ta daya,Allah sa Ja'afar bai dawo ganin
koh ta fitan ba. Ta rasa dalilin da ya sa
hankalinta ya tashi,bayan ita ta zabi hakan.
Lekawar da zatai shine taci ka'ro da Ja'afar suka
had'a ido. *WAIWAYE*... ***************
************** Haka yai ta juyi har kusan k'arfe
biyu. Washegari haka ta tashi sukuku, ga
fargabar Abba yau zai dawo,ga wani mugun
mak'on Ja'afar da yake taso mata. Kai in ma ba
wai bata kula bane gani take zazzabi ne a jikinta.
"Salma... Dagowa tayi ganin mama a kofa,da
mamaki fal fuska ta karaso ciki. "Wai har yau
kukan nan ki ke Salma?.. Mey yaron nan yai miki
ne haka?.. Hannu ta kai kan fuskrta,sam ba
tasan tana kuka ba, da sauri ta goge tana
k'ak'alo murmushin dole. "Mama ina k'wana.. Kai
kawai ta kada mata. "Haba Salma,kar fa ki rako
mata duniyar nan...kar ki zamo mace mai
kulafucin D'a namiji duk k'wa wulakancin da ya
mata man... Ashe ni ina chan jiya nai baccin
farin ciki da aka rabu lafiya ba rabo bare ya kawo
cikas a zawarci ashe ke kina nan kina kukan an
rabu? Haba Salma, karan nan ne fa ki ke da
dama ta biyu,tunda har ya sallame ki. "Maza
goge hawayenki ki biyoni daki yanzu. Kai ta
kada,a gaskiya ta fara mamakin irin kiyayyar
dasu mama suke ma Ja'afar, wato har ma godiya
ake ta rabu da alakakai?... Allah yaga tafi jin
haushin kanta sama da haushin Ja'afar, in ma
taji haushin shi toh bai wuce yadda ya k'ulle
mata gida ya kuma tafi koh ajikinshi. By Feenat
Ja'afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
22_"Toh wa ya jawo?... T'sam tai yayin da zuciya
ta tambaye ta, "Ni ce... Tabbas ni najawo, amma
ba laifi na bane. Kuka ta fashe dashi,tabbas anci
k'arfinta,ta ko'ina an mata dabaibayi da huduba
gur6atacciya. "Gashi na jawo wa kaina saki biyu
ba tare da na samo kan ba(kan Ja'afar).. "Oh ni
Salma.. Ina tunani na yake da har na aikata
wannan wautar?.. Ina son da nake ikirarin ina ma
Ja'afar?.. Ina ya je... "Salma... Mama ce ta
kat'se mata tunanin gaskiya da kira. Hannu tasa
ta share hawayen ta,ta daga kai tare da fitar da
iska dan daidaita nut'suwar ta. "Na'am.. Ta amsa
kan ta tashi tai waje. "Gani mama, Kan gado ta
nuna mata kan tazo ta zauna. Ba musu ta
karaso. Kafad'arta ta dafa kan ta numfasa, "Kina
ji koh Salma? Kai ta daga mata. "Baban ki yau
nasan zai dawo,tabbas ya rit'saki nasan zai cid'a
ki ne a banza. "Yanzu abinda nake so kiyi
shine,ki je gidan A'i,dan mijinta baya gari ya tafi
sari,ki barni in na gama lalla6a shi sai ki
dawo,dan karan nan kam sai dai ai wacce za ayi,
amma aure kin gama... G'wara a chanja
hannu,tunda wannan d'in ba fus, bare ass,sai dan
banzan dacin rai ba koh gidan kai... Hawaye ne
ya zubo mata,ba da ban suna matukar kama da
Mama ba,da tayi shakkun akan haihuwar ta...
Mama na da kamasho a ta6ar6arewar aurenta
kashi 70 acikin dari... Tabbas uwa uwa ce,
amma su kam tasu uwar sai g'yaran Allah..
"Au,au,kuka ki ke? Dan nace baida gidan
kanshi?.. Koh shi ya siya ya gina da gumin ajin?..
Yarinya ki duba yadda ake harka,y'an uwanki na
shiga ta alfarma amma ke kin zama y'ar k'allo..
Ki farka a bacci Salma,dan rayuwar nan ta zo mu
fafata ce. Kai ta k'ada tana goge ido,sai ta mike
tai hanyar waje, "Bari na shirya zuwa gidan
Aunty A'in, naga 10 tayi. Kai Maman ta daga
harda washe baki, "Yauwa,ko ke fa.. Maza aje a
shirya,ga nan abincinki a kitchen. Kai ta k'ada
kan tai waje, da kallo Maman ta bita, ba abinda
y'arta ya gaza a gareta,wa ma zai ce ta ta6a
aure in ta fito da ita gari?.. Dole kud'in da ba taci
ba da yanzu taci gun Salma. ***************
************** A k'wance take kan _3sittern_
Aunty A'i,in banda ciwan kai ba abinda take,
"Tashi ga maganin kisha... Kai ta dago,Aunty A'i
rike da kofi da _paracetamol_. Bayan tasha ta
g'yara zama,d'uk gidan bata jin da wanda bai
ta6a kushe mata Ja'afar ba sai Abba da Aunty
A'i. Hawaye ne ya zubo mata,kan kai duk'e tace
"ban san mey Ya Ja'afar ya t'sarewa su Mama
ba da sam basa kaunarshi... Yanzu ki duba Aunty
A'i Mama yau tace murna take an sake ni..
Harda fad'in g'wara da bamu samu rabo ba...
Kuka ne yaci k'arfinta,tuni ta hau yi ba
kakkautawa. Taso wa Aunty A'in tayi zuwa kusa
da ita ta hau lallashi,chan ta numfasa itama
harda hawaye ta fara fad'in "Kinyi wauta Salma
matuka,samun irin Ja'afar a yanzu wallahi sai kin
tona,irin halin da kika dinga karta mishi duk na
samu gun Abba,kinsan nima ba wai Mama nayi
dani bane sosai,dan ban fiya shiga irin shirgin
nan ba. "A gantali har gida sukutum ki ka kona
mishi Salma.. Naji ance ya kuma shiga cikin y'an
_missed call_..Bana tunanin har yau ya gama
tattare takaddun da ya rasa kuma duk a dalilinki
fa,amma dai dai da rana daya bai ta6a hanaki ci
koh sha ba?.. Duk da baki san ta ina yake samu
ba. "Maimakon ki zama mace ta gari mai
k'wantar mishi da hankali har ya manta bakin
cikin da yake ciki na rasa aikinshi,a'a sai ma
kara hura mishi wutar masifa ki ke a gida.
"Salma kina da ilimi fa,kinsan d'ukkan hukunci a
game da matar da take sa6a umarnin mijinta,
bare ke da kusan kullum cikin shi kike?.. Ina ki
ka bar islamiyar taki Salma?.. Da har kika bari
rudin su Ummi da chan wasu jahilan makotan
suke hure miki k'unne,wanda in zaki titsiye su ba
mai iya rashin mutuncin da ki ke Salma.. "Nayi
imani zaman cikin gidan ki ya fiye miki alkairi
sama da zaga makota yawan gulma da ki ke..
"Ya sanar ni shi sai a shafe wata nawa,baiga
makotan naki na zirya gidan ki ba sai dai aiken
bani taliya bani mai, shin sun fiki sanin ciwan
kansu ne Salma? "K'wanaki haka har gida na
samu yana fad'a kina fad'a, amma dana shiga nai
miki fad'a, sai kika nunan wai maza sai da wuta..
"Kan kiyi aure Salma ni nayi da shekara hudu, ba
zaki fad'an halin maza ba,amma a lokacin na biki
da murmushi ne kawai. "Ki dube ni nan Salma...
Dago tai ido jajir hawaye na zuba. "Wallahi tunda
nake akan fita unguwa ban ta6a sa'inasa da
Abban Aslam ba,kar kara in naja,ya ja,hakura
nake na barshi,wani sa'in sai kiga har ya
fita,amma sai ya dawo yace in shirya ya sauke
ni,ina fara'a za'a gama komai ba bacin rai, duk
wanda zai fad'a miki ana tank'wasa namiji ta
fad'a da bala'i wallahi karya yake miki,sai dai ma
kullum yai ta baud'e ga uwa uba sane mishi da ki
ke. "Zuciya nason d'ukkan mai k'yautata mata
Salma,sannan a kullum tana kara nisa ga wanda
ke munana mata... Ki gane wannan, tunda dama
taki,shine ya koma miki ta hagu, ki fita a bakin
aurenki Salma, tun da kuruciyar ki wai har kin
zama bazawarar k'arfi da yaji? Ranar da kanshi
Ja'afar din yazo gidan nan,akan irin yadda ba
k'ya jin maganarshi,nai mishi alkawarin zanje har
gida na miki fad'a sai gashi Allah ya kawo
wannan. Sosai tai mamakin Aunty A'i,da yau ta
zauna fed'e mata biri har wut'siya.. Tai imani duk
maganganunta ba wanda ba ita ke da laifi ba
tabbas. Wata muguwar nadama ce ta sakko
mata,kuka kam ba kama hannun yaro, har sai da
taji ba dad'i. Bataki koh yanzu ta nemi gafarar
Ja'afar ba kan ya maidata aurenshi,tai alkawarin
d'auwama acikin dakinta har sai yace Salma fito.
Aiya Salma, Ja'afar baya tataki,yanzu ta Bintu
yake.. By Feenat Ja'afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
23_Zazzabi harda amai take,duk zatan Aunty A'i
akan kukan da taki dainawa ne. Washegari ba
zato ba t'sammani Aunty A'i ta t'sinkayi sallamar
Abba a t'sakar gida. Lokacin dawowarta daga
band'aki kenan ta gama zuba ma Salma ruwa a
amai na tun jiya da yaki t'sayawa,sai dai tana jin
Abba ne ta mike tare da yin waje da sauri.
Hannu Aunty A'i ta d'aura aka,ganin zabga-
zabgan bulalin da Abban ya shigo dasu gidan,
fad'i yake "Ina take Aisha?.. Tuni idonta ya raina
fata,fatan ta Salma taji ta buya. Cikin in'ina tace
"Abba wa d'in?.. Hannu daya marar bulala ya
nunota dashi, "Kinci gidan ku... "Bani hanya na
wuce,yau mai rabani da Salma sai Allah a gidan
nan.. Da k'arfi Aunty A'i tace ta gudu,hayaniyar
ce ta fiddota a band'aki ta had'a uban zufa dan
azabar amai, har bata danji sosai, lekawa tai ta
labule jin an ambaci sunanta... Ido waje ta koma
da baya tana neman ma6oya,tuni ta ware tai
bayan kujera tana rufe baki da duk hannunta biyu
jin Abba a parlourn. "Dan Allah Abba kai
hakuri,wallahi bata da l... "Aisha,koh ki fito min
da ita koh bulalinnan su kare a kanki... Ido Salma
ta rint'se da sauri,kirjinta sai d'ukan tara tara
yake. Sai dai mey? Kamshi turaren kayan Abba
ne ta busu hancinta,take taji amai ya taho tai
kokarin ta mat'se sai dai ta kasa,tuni k'ak'arin
aman ya taho sai dai ciki ba komai. Bata zata ba
sai jin magiyar Aunty A'i tai tana dan Allah yai
hakuri... K'wak'waran mot'si batai ba taji saukar
bulali tai ajiki ta ko'ina. Ihu take da iya guntun
k'arfin daya rage mata tana Abba zan mutu,
ina,kawai lafta mata yake,da Aunty A'i ta rike sai
ya cika ya hau zuba mata wata. Makogaro ba
ruwa,duk ya tafi a amai,tuni har muryarta ta
dashe,sai k'ak'arin amai da take. Kamar an hullo
mama sai ganinta sukai a kid'ime,ganin yadda
yake jibgar Salman ta bala'in tsorata, da sauri tai
waje dan kara kiran yayanshi Ganin Abba zai
kisa,yasa da sauri Aunty A'i tai ma Salman rumfa
tana yai hakuri cikin kuka,ganan Salma koh
k'wakkaran mot'si batai,bai bi takanta ba ya hau
zuba musu tare, "Abba ciki ne da ita,wallahi zai
zube.... Chak ya t'saya da bulala a hannu sai
zufa yake, yai dai dai da shigar Mama tai katari
da zancen Aunty A'in. Bulala ya yarda yana
haki,tamkar yasa kuka dan bakin ciki,tunda yake
basshi da fadanshi amma bai ta6a sa hannu ya
dakesu ba sai akan Salma,wannan shine karo na
biyu gareta. So take tafi k'arfin kowa a ganin
shi,toh shi bazata fi karfinshi ba. "Ba mai fin
karfina a gidana ban maganin shi ba... Yau kin
t'sira a dalilin zancen A'i,da na lahira ya fiki jin
dad'i.. Duk da laifin nafi daura ma uwarku data
zuba ido kuna abinda kuke so... "Mun shiga
uku... Da sauri Maman tai kan Aunty A'i mai
magana. Jijjiga salman take tana kira. "Salma!...
Salma!!.. Mama bata mot'si wallahi... Tuni suka
hau jijjigata Aunty A'i na kuka. "Shikenan Malam
ka kashe min Y'a ka huta... Babu yadda banyi da
kai ba akan kai hakuri kar kazo,kar kaje,ga nan
irinta ka... "Ki rufe mana baki, koma meye ke
kika jawo, ruwan k'anin Aslam ya gani a jarka da
sauri kuma ya dakko wai su mat'sa agun,ido duk
hawaye suka mat'sa. A hankali ya dagota tare da
yayyafa mata, a hankali ta kawo numfashi sai dai
ido a rufe. "K'unnen k'ashi gare ki ne Salma,shi
yasa baza mu shirya ba sam sai kin g'yara hali.
Kuka ta fara kad'an kadan lokacin da suke
dagata, sosai ta lillisu,duk jiki ciwo. Wayar Aunty
A'i,da Ja'afar suke magana wai yaji Abban su
yace Mama ta bugo kan Abba zai kashe Salma...
Cikin kuka tace "Kazo gidana suna nan. Duk ya
kuma kid'ime, tabbas ba d'ukkan wasa yasan
Abba yake ma Salma ba,tunda Aunty A'i take
kuka. Garba ya kalla,"dan Allah kaini gidan Aisha
yayar Salma. Da mamaki yake K'allonshi, "amma
dai kasan yanzu _chairman_ zai zo yama signing
koh?.. "In bazaka kaini ba na fita na hau abin
hawa. Kafad'a ya daga, "a muje, ni meye nawa.
Mijin Aunty A'in ya kira koh yana gidan,yace su
shiga kawai,Abba ya sanarshi komai tun dazun.
Abba ya fita lokacin da suka zo,mama ta tafi
nemo abin hawa. Aunty A'in ce ta shiga
dasu,ganin bulalin wajen duk sun kakkarye ji yai
kamar yasa kuka,yanzu duk bulalin nan a jikin
Salman sa ta kare? Jiki a sanyaye suka je
parlourn,duk ta kudindina tana rawar sanyi,da
sauri ya karasa gunta yana kira,tana jinshi ta
kara rushewa da wani kukan. Hijabin ya yaye
mata,yana ko'k'arin cicci6ota ya tuna da sakin
dake t'sakanin su,sai ya zame hannu tare da
zama. Bai san wani irin so yake ma Salma
ba,wanda har yake rawar jiki akanta duk da
abinda ta mishi, gashi har taja jiya ya bada kai
gun Bintu bori ya hau. "Mey yasa Salma?.. Mey
yasa ki ka zabar mana irin rayuwar nan?.. Gashi
yanzu kin dasa min son kara aure koh na samu
maslaha aciki... A zabure ta tashi,duk da yadda
take jin jiki tana cije le6e dan azaba. "Mey kace
Ya Ja'afar?.. Aure?.. Da sauri ya k'allo ta,sam bai
tunanin zancen ba a ciki yai ba. Ganin bai bata
amsa ba yasa ta yarda da abinda taji,hannu tasa
duka biyu ta dafa kan ta zamo kasa tana cije
baki,g'wiwa biyu ta durkusa duk tai kalar tausayi.
"Ka rufamin asiri Ya Ja'afar dan Allah,wallahi, na
rantse bazan kara ba..Dan Allah kar kamin
kishiya.. Dan Allah, wallahi bana sonta.. Allah
zan g'yara..nai alkawari,.. Ido ya rint'se, had'i da
cije le6e,ba yau Salma ta fara mai magiya da
rantsuwa kan ta d'aina ba,amma ba abinda ya
sauya zani.. Yanzu komai ya kare musu,aure
gareshi ya zama dole. By Feenat Ja'afar.
Juma'@ Mubarak.
9/29/16, 9:07 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24-Kai
ya kada tare da mikewa, "kiyi hakuri Salma.. A
baya na baki d'ukkan wata dama taki kinyi watsi
da ita.. K'arfi da yaji so ki ke ki mayarni wani
iri,dame zanji Salma?.. Na fita waje na samo
6acin rai,sannan na shigo gida nan ma wani
6acin ran ne,maimakon a lallashe ni..A'a ni
kullum ni nake lallashi. "Kiyi hakuri,Allah ya baki
lafiya.. Garba ya k'allo yai mishi halamar su tafi.
A hankali ta mike tana jin wata irin hajijiya na
debarta. "Nasan ni na ja ma kaina komai Ya
Jaafar... Ja yai ya t'saya, jin taci gaba yasa ya
juyo. "Tabbas na chanchanci d'ukkan wani
hukunci da zaka min in dai zaka yafe min.. Kasa
tai da kai,tai matukar zama abin tausayi a
gunshi,sai dai kawai ya kasa gane nadamar
Salma a yau,dan ta saba, ga kafa sai ka'rkarwa
take. "Amma dan Allah wa zaka aura?.. Ba dai
Bintu ba?. A yadda ta t'sareshi da ido yasa ya
kasa magana,sai ya kalli Garba,kafad'arshi ya
daga mishi halamar ba ruwan shi. Sai da ta
maimaita kan ya daga mata kai. Murmushi tai da
yafi kuka ciwo,a hankali take neman juyawa wani
kanta ya sara gami da ganin duhu. "Kar ki min
fassara Salma,ba abinda ya had'ani da Bin... Luu
ta fara halamun zata fad'i, cikin zafin nama yai
taku daya ya taro ta. Gaba d'aya jikinta ya
saki,ga wani irin zafi kamar garwashi. "Salma..
Jijjiga ta ya fara,da sauri Aunty A'i ta shigo,sai
ga Mama na fad'in ta taimaka su sa Salman a
Napep gashi ta nemo.. "Mey zan gani haka... Da
sauri suka juya ganin Mama da tai turus ganin
yadda ya mammakale Salman,ita k'wa k'allonshi
kawai take hawaye nabin gefen idonta. Garba ke
mishi da hannu kan ya saki Salman amma kamar
yana zigashi,sai kara naneta yake. Gaida Maman
sukai da girmamawa tai banza dasu. Sababi
Mama zata fara Aunty A'i ta jata sukai waje.
Garba ne ya tsayarshi ganin yana neman cicci6ar
Salman. "Kasan dai yanzu ba a mat'sayin
matarka Salma take ba,kar ka nemo mana
magana dan Allah.. Harara ya sakar mishi,kan
cikin fusata yace "na mayarta toh.. Koh da
magana? Kai ya k'ada mishi, kan ya bud'e mishi
labule, "Dan Allah kaimu asibiti... "Auntyn mu..
Aunty A'i ya k'wada ma kira, da sauri suka fito
ita da Mama dake huci. "Asibiti zamu kaita, dan
Allah Mama ki yi hakuri na kaita.. Harara ta
sakar musu kamin tabi bayansu ta sallami mai
Napep sai asibiti. Murna ta koma ciki,da d'ukkan
hannu biyu mama ta dafe kai,jin rahoton likita
kan tabbatar da cikin Salma,dan haushi ba tasan
tai waje ba. Shikenan an 6ata mata shiri, ciki?..
Kai amma an sha da ita, sam ta zata fad'in A'in
ne dan a bar Salma. "Mama kiyi hakuri zata
samu lafiya,bari naje na siyo allurori mu dawo.
Kala bata ce musu ba, asalima ji tai kamar ta
rufeshi da duka koh ta huce. A gun Garba ya
k'ar6i kud'i,basu juma da tafiya ba sai ga Ummi
da Aunty A'i sun zo,tuni k'wa ta ware tana
surfawa Ja'afar Ummi na tayata. Kai Aunty A'i ta
k'ada, fatan ta a kullum Allah ya ganar dasu
Mama alkairin Ja'afar, alkairin da batajin koh su
wanda suka auri masu halin suna musu. "Mama
Salma fa matar Ja'afar ce har yanzun,don
musulunci ya mallaka mishi,matukar batai idda
ba,bare da kunne na naji yace ya mayarta
wallahi, dan Allah Mama ki sassauta, in har da
mey lefi aciki toh fa Salma ce.. "Ke dama ina
kika ga kishin kai?.. Ai guntunki ta tsotsa, shi
yasa sam kusan halin ku daya... Aure kuwa in dai
ni nai nakudar Salma toh ya kare ya gama.. Ba
ruwana da wani ya mayarta,sakaryan yaro
kawai,sam bai da zuciya wallahi. Ummi ce ta
amshe tana k'wafa. "Ai wallahi dad'i yake ji dan
yaga Abba na jibgarta,dama garin d'ukan yaja ya
rasa cikin ai da shi ya jiyo... "Ummi mey yasa ke
sam baki da mutunci ne?.. Baki Ummin ta turo,
"Ja'afar fa ba sa'anki bane,in bazaki g'yara ba
toh kar ki 6ata... Salma ita ta chanchanci komai
ba Ja'afar ba,gashi taja yace aure zai kara... A
zabure Mama ta jiyo, "Aure?.. Shine ki ke kuma
fad'a min ya mayarta?.. Kai ta k'ada, "eh lalle
Ja'afar, toh k'wa zama da kishiya ba dai y'ata
ba, karan nan zamu banje da Malam wallahi akan
maganar komen nan,sam naki jinin yaron nan
wallahi.. "Ni kam Mama bana ganin aibun Ja'a..
"Kimin shiru,kar ki gani din,amma aure angama.
****************************** Yau k'wananta
biyu aka sallame ta,fur Mama taki bawa Ja'afar
fuska,daga ina wuni lafiya shikenan. Su Abban su
Ja'afar harda y'an cikin gida sunzo sun jajanta
abinda ya faru. Kowa ya bawa bangarenshi
rashin gaskiya, take Baba yace ya mayarta. Kai
duk'e yace ai tun ranar chan ya mayarta,nan ya
ja mishi kunne kan sarar ki fita A BAKIN
AURENKI. A gaban su Abba ya kara tasa zancen
zai kara aure,cikin fusata Abbanshi yace "Ba mun
gama maganar nan da kai tun jiya?.. Wane aure
kuma bayan wannan da aka mayar? Kai yai kasa
dashi yai shiru, murmushi Abban su Salma
yayi,kamin yace "Kamin dai dai Ja'afar, fatana
Allah yasa auren shi zai zaunar da Salma a
dakinta ta rungumi ibada. Ja in ja sukai tai
t'sakanin Abban Salma da Abban Ja'afar, dak'yar
Abban Ja'afar ya yardewa Ja'afar kara aure. Ana
watse wa koh gama jan mota basuyi ba Mama ta
fara sababi,ita a fafur ba inda Salma zata,bata
zauna da kishiya ba,saboda haka ba mai zama da
ita a yaranta. Itade Salma bata um bata um-
um,sai hawaye kadai ke zuba,ita kad'ai tasan ya
zuciyarta take hautsina mata,ta faru ta
kare,tunda har manya sun amshi magana.
"Ja'afar? kishiya? Kuma da Bintu kawarta?.. Tab
da matsala. By Feenat Ja'afar
9/29/16, 9:10 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
24_Daaga sosai akai da Mama akan komawar
Salma,sai da Abba ya bud'e mata uwata sosai
kamin harda Yayanshi ta saki aka ta koma din.
Ita kanta Salman yanzu ba kaunar komawar take
ba sai ta mot'so mata ga laulayi. Ga Ja'afar
tunda ya ji batun ciki ya kasa sukuni,kullum yana
zaryar dubiya da leda. Shi dai bai mat'sa da sai
ta dawo ba lokacin, dan g'yaran gida sosai yake
wanda Ummanshi ta bashi ya zauna aciki. Har
gida yau Abba yaje gun Abban sun kan lalle yau
Jafar yazo ya dau Salma. Da dare k'wa ta koma
dakinta. G'yaran nan gidan ya t'saya
chak,sakamakon aikinshi da aka mayarshi aka
bashi albashin da ya wuce shi,bai da mat'salar
kud'i yanzu,auren shi kawai yasa a gaba. "Ina
k'wana.. Cikin sanyin murya ta gaida shi kai
duk'e, kai ya daga kamin yace "ya jiki?.. Shiru tai
ba amsa. "Ki tashi ki zauna man.. Kai ta dago ta
k'alleshi kamin ta kada mishi, "A'a magana nake
son muyi da kai. Zama ya g'yara yana
sauraranta. "Mey yasa ka ke son auren Bintu?..
Da ido ta kafeshi tana jiran amsa. Murmushi yai
kan yai baya kad'an harda d'aura kafa daya kan
daya. "Saboda tana so na ne Salma.. Kai ta kada,
''kaima kana sonta?.. A bazata tambayar tazo
mishi,ga takafeshi da ido hawaye taro a idonta.
"Ki gane Salma, ba wai.. "Eh koh A'a?.. Amma
nake son ji kawai. Ba koh shakku yace mata "eh..
Amma.. Hannu ta daga mishi tana hawaye,
"Barni haka dan Allah,amma kasan Bintu k'awata
ce da koh?.. Ya zaka min haka? Kai ya kada
harda dariya, "A sani na banta6a ganin Bintu a
gidan ki ba,asalima... Sallamar Aunty A'i ce ta
kat'se mishi maganarshi,sai ya tashi dan dan
bud'e mata kofar,da kallo ta bishi tana mamakin
kalamanshi,sai kawai ta k'ada kai ta mike tana
goge ido. "Bissmillah mana Auntyn mu.. Yana
gaba ta biyoshi a baya, sosai suke dasawa da
Aisha,dan tasan abinda take sosai,shi yasa baya
6oye mata komai. Bayan sun gaisa ya mike yana
zai fita, kai kawai ta k'ada mishi,sai Aunty A'i ce
tai mishi a dawo lafiya. Zama Aunty A'i ta g'yara
tana ma Salman k'allon tuhuma. "Ashe Salma
baki fara g'yara ba har yanzun?.. Da rashin
fahimta ta k'allo ta tana hawaye, "Fita fa yayi
jiyan nan dawowarki amma har kin fara nuna
mishi baki sauya ba. "Aunty A'i ba abinda na
mishi fa Allah.. Katseta tai da fad'in "Amma zai
fita babu koh a dawo lafiya?.. Haba Salma,nan ki
ka dinga rantsuwar kin shiryu, koh har kin leka
makotar ne yau d'akko sabon darasi?.. Kuka ta
sa mata tana girgiza kai, "Haba Aunty
A'i,k'awata fa zai aura fa,taya bazanji zafinshi
ba?.. Da mamaki tace "wacce kawar taki? Cikin
kuka tace "Bintu,dalibar shi ce a Day school fa.
Ita dai ta hanga bata gano wace Bintu bace a
k'awayen,tasan sarai k'awayen Salma basu fi
biyu ba wanda tasan su. "Wace Bintu kuma cikin
k'awayen naki? Amma basan ta ba koh?.. Kai ta
daga mata, "islamiya mukai tare fa.. "Mtsww,
t'saki Aunty A'in tai tana k'auda kai, "har wata
kawar islamiya K'awa ce?, bana jin ko hanyar
gidan ku ta ta6a zuwa balle ta zama kawarki,
koh ta halarci bikin ki?.. Kai ta kada mata tana
goge hawaye. Cikin lallami ta fara lallashinta.
"Kar fa ki bari tun kamin ta shigo taci galaba
akanki Salma, yanzu ba lokacin t'sayawa kishi
bane a gunki, lokacin g'yaran kuranki na baya ne
Salma... Ki d'auka baki ma ta6a sanin wata Bintu
ba rayuwa,dan ba gaminki da ita sam. "Ki kuma
fidda zancen auren nan a ranki,dan koma meye
ke ce sila Salma. Nasiha tai ta mata tana kuka
har ta gamsu da bayaninta. Ta bata shawara
masu k'yau, ta kuma d'auka. Da ya dawo ya ga
chanji,sannan bata kara mishi maganar Bintu ba.
Yau satin ta daya da dawo wa,amma banda
Maman Abba ba wanda ya leko mata har Maman
Ummin, Ga sai wani kama mata kai Ja'afar din
yake bare tace zata leka,abu daya ta sani,shine
ta daina zuwa gidan kowa sai in ta kama.
Washegari har kofa ta rako shi zai fita tace zata
leka gidan Maman Ummi.. Yana fita yace mata
sai ta dawo kawai. Da k'allo ta bishi,sai ta ga
kamar gat'se ya mata,dan haka ta koma ciki tai
k'wanciyarta. Mukullin gidan da ake g'yara zai
fitar musu dashi sai ya dawo. A k'wance ya
sameta ido rufe a parlour,sai yai jim,ganin bata
fita ba har ya dawo. "Har kin dawo ne?.. Kai ta
girgiza mishi,sai yai d'aki yana tunaninta, haka ta
saba mishi kan gaba ta fand'are mishi,shi dai
yasan yai alkawarin mud'in ta tambaye shi fita
ya d'aina hana ta,yasan duniya makaranta,da
sannu zata gane abinda yake gujar mata. Koh da
zai fita sai ya kara nanata mata kan taje kawai.
Bai jima da fita ba ta fito,tana dan jin hayaniyar
su kasa-kasa. Har zatai Sallama sai ta ja ta
t'saya jin wata gulmar da suke. "Ai yanzu ya
zamarta mai gadinshi, tunda ta dawo ba inda taje
tana d'aka,koh duk sururin zai kara auren ne?..
Tana jin Maman Ummi tace "oho mata,ba ita
areni muje biki ba,mijina baya fad'a.. Muryar
Maman Abba tajiyo tana fad'in ''ni tausayi ma
take bani wallahi, ranar chan dana shiga duk ta
rame tai baki,kana yaronka da kai an ma saki
2.... Baya tai cikin sanda danjin wani na shirin
fitowa. Gida ta koma ta cire hijab tai dabar a
kujera, tun yaushe haka take faruwa da ita?..
Ashe ita k'allon mara wayo suke mata acikinsu?..
Kai ta daga sama, lalle ta gane mey Ja'afar yake
nufi da mutunci yake nemar mata.. Yau ta gane
ashe in an yi gulmar wani da kai yau gobe da kai
za'a kafa ai taka. "Allah na gode maka daka sa
na ji na kuma gani. Tabbas Ya Ja'afar babban
gata yai mata. Toh a ina ma suka samu labarin
za ai mata kishiya?..har dare tana neman amsa.
Ranar har kukan bakin ciki tai na taraiyarta dasu
Maman Ummi. Tuni ta tattare kowa ta wat'sar
shi,duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.
Ranar Maman Waleeda da suke kira uwar tsoron
miji ita ta zo mata harda nasiha har gida,matar
da koh gidanta sai tai fita ashirin bata leka
ba,kuma makociya ta kusa,har misali tai mata da
Maman Ummi. "A kaf unguwar nan bana tunanin
da matar da take cikin takura irin na Maman
Ummi Salma, ke shaida ce,in kinji gidan yai shiru
ba koh tarin yaro kasan uban na gida. Sannan in
zai shekara ba taje ko'ina ba shine dai dai a
wajenshi,duk fita in zatai satar hanya take tasan
in ya fita da yamma sai dare,amma a gun kuri
tafi kowa iya dadin magana,da ina cikin su,daga
baya na gane taraiyyata baza tai dasu ba,sai na
zabi zaman gidana ya fiye min alkairi sama da
yawan gulma. "Ka'rkara in abu ya faru in leka a
tsatssaye in dawo, dan Allah ki iya kafarki
Salma,dan zasu kai ki su baro ne kawai. Kai ta
k'ada mata, "Na gode Maman Waleeda,Allah bar
zumunci,kuma InshaAllah naji bayanin ki,duk da
mun kusa tashi a unguwar ma duka InshaAllah.
Anan ta sanarta za ai mata kishiya,k'warai ta
jajanta mata kan ta kara da y'an shawarwari,tun
daga ranar mutunci da Maman Waleeda
suke,kusan duk yamma tana turo mata su
Waleeda taya fira,har lokacin tashinsu yazo.
***************************** Cikinta yana da
wata biyar lokacin auren Ja'afar saura sati. Sam
bazaka zata Salma bace, dan tamkar bai dameta
ba haka tai a auren. Har ranar Ja'afar yana fad'in
wai ta daina sonshi gaba daya,koh kishi bata yi
zai kara aure,murmushi kawai ta masa,dan tsaf
ta kula da rawar kan da yake k'wana biyu. "Ba
k'ya shirye-shiyen komai gashi lokaci ya taho
fa... Tamkar ya choka mata abu makogwaro taji
wani iri,kawai sai ta sa mishi ido tana k'allo.
Tabbas rawar kan Ja'afar karuwa take akan
auran nan,banda haka wani irin tambaya ce
wannan?... Shikam tunani yake yadda Salman ta
g'yaru har kullum,a ganinahi halin ko'in kula da
yake nuna mata ne akan fita. "In da hali zan fita
kar6o wasu kayana unguwar Ummi. Kafad'a ya
daga mata,kan yace "sai kin dawo... Yai waje.
Baki sake ta bishi,tun bayan dawowarta ta kasa
gane inda Ja'afar ya dosa,abu yake mata tamkar
ya kosa da zaman ta a gidan. Gashi tun kamin
amarya ta tare har ya sallamata,wai ko'ina nan
gaba in zata kawai taje,dan yanzu bai son 6acin
rana irinta da. Toh mey yake nufi? By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 9:11 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana
murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi
an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci. Har
yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna
mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh
yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a
gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu. Kuka take
yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya
sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana
ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan
ba mai chazan hawan jini. Kai ta dago tana mishi
k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a
wa matarka baka so na?.. Ni nace ina son ka
koh?.. A haka za ai zaman lafiyan?.. "Ke kinga
bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?.. Da
sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato
harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan
kaina.. "Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki
ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata
fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita...
Waje yayi zuwa dakin Salman. Kai Bintu ta k'ada,
"ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a
da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada
mata mari tukuicin sharri. Ita kam tanajin bud'e
kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance
ido. "Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a
gidan nan?.. Yaushe nace miki Bintu ce tai min
tallar kanta na aura?.. Harara ta sakar mishi da
k'allon kar ka rainan hankali. "Ka nad'e taburmar
kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine
ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya
faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura
igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?.. Baki ya
saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi
na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla
mishi a gun y'ar uwarta ashe?.. Bai da tace wa,
kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka
fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba
kai ka fad'i ba... "Idan kuma habaici da iyayi
kake neman matarka ta dinga min dan ka huce
haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana
sa kafar wando daya da kowa a gidan nan
wallahi.. Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki
ta barshi t'saye baki sake. Titi ya fice ko ya
samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin
mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam
yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa. Tun
daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in
Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata
dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har
mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da
gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a
ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya
mata magana ita y'ar dika take,daga shi har
amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi.
Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata
kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu
suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe
kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai
ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar
keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi
da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune
kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai... Ta fada
tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk
abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su
aciki... Chak! Taja ta t'saya rike da labule a
hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar
su. "Sai yau Aunty Ladi zaki zo min? Har nayi
fushi ai.. Baki sake Salma take k'allonsu,tana
k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma
Bintun kuskus tai baya da sauri. Ido ta rint'se
tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu
ta gane inda Bintu ta samo duk wasu
_information_ na zaman aure nata ba agun
Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar,
har rantsuwa yai mata amma taki yadda. Karshe
har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai
da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya. Zama tai
tana jiyo shewarsu a dakin Bintun. Har kullum
bazata daina nadama akan taraiyarta dasu
Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da
t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta. Har hawayen
bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina
sa6awa mijinta ko da taji haushin shi. T'sakar
gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a
kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya. Ganinta a
t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a
t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai
tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau
inda-inda, "dama kina ciki?.. Sannun ku da gida..
Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar
waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku
hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita.
Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai
za tai rakiya waje ya bata izinin fita. Bokiti ta
zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai
waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja
t'saki ta shige band'aki. "A toh na zata koh rafka
mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan
wannan da gani zatai kishin hauka... Dariya suka
sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki
tafiya. Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e
band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin
saukar ruwa sukai akansu har Bintun. Bokitin ta
d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture
suka fita waje da gudu. Tana haki ta leko kofar
gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya
na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon
na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi,
InshaAllah kema dubinki ta kusa cika. "Ke kuma
yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai
Allah, yau zaki ga karyar iskanci. Gida ta koma
tana hakin daga ruwa bucket guda da tsohon
ciki. A t'sakar gidan ta zauna tana maida
numfashi a hankali, ta jima da zama kamin taji
tafiyar Bintu cikin sand'a, kofar ta zubawa ido
tana harara, kai ta leko dashi dan ganin koh
Salman bata nan sai suka had'a ido. "Wallahi
baki isa ki ce zaki hanani shiga ba, in gaske ne ki
bari na shigo na shirya in fad'an ki ke nema dani
ba hauka ba. Murmushi tai daga inda take, "Lalle
kinyi kuskure in kina zatan zan iya had'a jiki da
karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka
yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba
miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31
Feenat Ja'afar Novel's
"Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai
fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu
gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma
Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta
sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai
Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka
da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata
raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana
ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai
watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai
baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya
zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?..
Gidan ki ne da har zaki kafa dokar wa zai shiga
ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a
fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga
mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da
akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace
"eh wallahi, da da halin duka ma sai na
miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta
matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada,
kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code
wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi,
"Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka
dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar
g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan
Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana
lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita
harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan
wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin
dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in
ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki
kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin
yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun
ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai
murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta
fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita
Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in
zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga
shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk
inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye
kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya
take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai
waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta
shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta
samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure
yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata
cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira..
Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana
mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi
dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi
yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata
amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi
machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu
yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara..
Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu
sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan
har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta
hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:14 AM - Queen Safiyyert馃憫: *漏 Feenat Ja'afar*.
25_Yau amarya ta taro gidan Ja'afar,suna chan
d'aki yan d'anna kirjin Salma.
Tai kuka yau harta gode Allah,tukun daga baya
taje ta d'au wanka.
Tabbas ba'a iya dake wa kishi,koya sai ya tona
ka,dak'yar ta samu ta saita kanta kamin y'an
kawo amarya suzo kawo amana.
Kowa ya wat'se, daga ita sai amarya, kowa tana
dakinta.
Karadin Garba ta kiyo a parlourn ta,tuni taji
gabanta ya sara, tabbas tasan tare suke da
ango.
A hankali ta yaye labule tana k'allon su har suka
shiga dakin amarya had'i da parlour mai k'allon
nata.
Zama tai ido tuni ya ciko da k'walla, sai tai
ko'k'arin had'iye wa.
Tana jin Garba yana bazai shiga ba yaje tai
tanadin ta6aryar duka, tana suka sa dariya harda
tafawa.
Kwafa tayi,wato ga mahaukaciya sabon kamu.
Tana jin rufe kofar gidan tai sauri ta k'wanta ta
rufe ido.
Da sallama ya shigo parlourn, ba kowa sai
kamshin turaren uwar gida y'ar Borno jikar
Shuwa.
Ko'ina yaji sabon abu,kamar itace amaryar, labule
da kujeru purple da baki, su Mama anga ba sarki
sai Allah,kawai sai aka fito da tsohuwar
ajiya,baba ya cika aka sai mata kayan
parlour,ragowar nata na da suka siyar,gado k'wa
tace bazata siyawa wani gardi ba,harda kukan
Salma.
Sai ma kuma gashi ashe yana da niya,gado
barawan Italian da katifa yai mata a kud'in da
Ummanshi ta turo mai daga Zaria.
D'akin ya shiga,nan ma shiru ba amsa,tai
rigingine kamar mai bacci.
K'allonta ya t'saya yana yi kamin ya ajiye ledar
hannunshi,sosai cikin ya kara fito mishi da k'yan
Salma warai.
Tai k'yau cikin attamfa ruwan purple da
pink,tasha k'walliya sosai gun Ummi,idon nan
yasha (mascara/eyeliner).
Da komai Salman sa ta fi Bintu sau dubu
agunshi,sai dai ta nuna mata hasken fata.
Hannu ya kai kan cikin yana shafawa a hankali,
tana jinshi yana yan surutanshi ma cikin.
Ajiyar zuciya ta yi,sai ya k'allo ta,a tunaninshi
baccinta ne yai nisa.
A tashi yai yana k'allonta,kan a hankali ya duk'o
tare da nufin kai bak'inshi nata,tana jin hucinshi
sai ta juyar da kai da sauri.
Murmushi yayi kamin ya shafo kanta da suka sha
yiriyirin kitso.
"Asbha ta ga Salma.. Ki yafeni kinji...
Bargon kusa da kafarta yaja ya lilli6eta,kamin ya
kashe wutar dakin yai waje.
Ido ta bude tana nanata maganar shi a zuciyarta,
mey yake nufi da ki yafeni?..
Saboda ya tafka miki t'siya mana.. Cewar wata
zuciyar, le6e ta cije,yau gata a gidan Ya
Ja'afar,akan gadon su,amma ba shi ciki,yau zasu
fara raba matashin kafadar Ja'afar da wata
chan.. Tana son Ja'afar, sai ma yanzu ta gano
t'sant'sar son da take mishi,ji take kamar ta
had'iyi zuciya ta mutu dan kishin mijinta,
tuni tasau wani dan marayan kuka a
hankali,kamar tace Ja'afar dawo.
****
Ita k'wa amarya tuni ta mike ta fara zarya a
d'aki, dan a idonta ya shiga bangaren Salma,tuni
ta fara cika tana bat'sewa.
Tana ko'k'arin fito wa a parlourn ya shigo,da
sauri ta koma ciki har tana tuntu6e,duk ba tasan
ya ganta ba.
Ba laifi,tazo da tarikice dayawa,sam sai t'sarin
na Salma yafi burgeshi,dan shi bai son tarkace a
gida da sunan k'walliya,ga wani kala blue da pink
na kayan labule da kujeru,sam bai mishi ba.
"Ki fito da sallaya parlour.. Kawai sai yai waje
dan yin alwala a band'aki.
Assalatun farko ta farka,cike da mafarkin Ja'afar
wai yana ta mata fara'a.
Kasa tashi tai,tabbas da gaske yanzu tasan
bakinshi kamar gonar audiga dan fara'a, tunda
yai k'wanan d'akin amarya.
Hakan ne yasa ko da gari ya waye taje kitchen
ta d'aura abin kari,dan tun asuba taga text din
Aunty A'i kan ta k'auda kishi tai musu kalacin da
safe,dan Allah..
Wannan Kalmar ce tasa ta shiga dan dole.
T'saye take tana juye abincin a flaks,ba abinda
ta tsana irin hada kitchen da band'aki da
kishiya,harar bangaren kayan jeren amarya tai
tana gunguni ciki-ciki,bata nufa ba taji shafo
wuyanta ta baya.
A zabure ta juya dan ganin waye. Murmushi yake
mata kanar dai a mafarkinta,da sauri ta d'auke
kai daga K'allonshi zuwa gefe.
"Kamshi duk ya karad'e gidan nan K'anwata..
Hannunta yake neman kamowa ta mat'sa tana
"An tashi lafiya..
K'allonta yake daga sama har kasa,tana sanye
da rigar banci _sky blue_ nai filawa purple, sai ta
d'aura zani da dank'wali akai, tai mishi k'yau
sosai,ga dan kurcicin cikin ya fito yai d'as.
"Ya gajiyar jiya?.. Na shiga kinyi bacci ban son
tashinki.
Yawu ta had'iya tare da fad'in "ummm.
Fur taki k'allon fuskarshi balle ta fassara mata
bakin ciki.
Dan da ganin yadda ya fara mata zagwadin nan
ta faru ta kare.
"Ga abincin ku,zan wuce..
Hannu yakai zai karbi natan tayi saurin janye wa
ta wuce,kai ya k'ada bayan ya dawo daga
k'allonta.
Dakin amarya ya koma,tana kudindine cikin
bargo, sai baccinta take narka abinta.
Parlour ya dawo ya zauna,Salma nuna mishi halin
ko in kula take tun satin biki, sam bata koh
kishinshi,sabgar gabanta kawai take.
K'wafa yai ya kada kai,dan ba karamin haushi
hakan yake bashi ba.
Motsinta yaji a t'sakar gida,ta window ya dago
yana k'allonta zata wuce band'aki da bokiti da
kwandon wanka,watoh daga shi har amaryar shi
basu isheta ma kallo ba?.. Dan wai koh hanyar
d'akin bata kalla ba,k'wafa yai kan yai waje gun
band'akin ya t'saya kamar maigadinta.
Har ta gama wanka yana t'saye,tana bud'e kofa
sai ganin mutum tai a t'saye ya bake hanya,kai
ta k'auda da nufin ta wuce ya riko bokitin,yaja ta
taja,kawai sai ta sau mishi,k'wandon sabulun
yake neman k'ar6a tai baya dashi.
"Wanka zanyi man Salma.. Wani k'allon ta watsa
mishi kan ta had'e rai,
"Bana _sharing_ din soso.
Baki sake yake k'allonta, cikin fusata yace "da
da wanne muke yi?.. Kanta gefe tace "toh yanzu
na sake t'sari...
A tunzure yace
"Wai Salma meye haka?.. Bana..
"Kai Dear J,ga soso nan kai wankan.
Juyawa sukai gun mai magana, Bintu ce daga ita
sai y'ar yaloluwar rigar bacci ba koh zani balle
dank'wali.
T'saki Salma ta ja,kan tace ''Malam ban waje na
wuce,tuni ya kara kuluwa, shi take ma tsakin?..
Yai mata k'yau,kawai sai ya dungurar mata da
bokitinta ya shige band'aki,da sauri Bintu tai
kitchen ta d'akko mishi nata,koh ta kansu bata
kara bi ba ta zari bokitin ta kara mai,a ranta tana
"karamar y'ar iska kawai.
Sam Salma taki dad'i, dan fur taki bawa kowa
fuska a gidan,dan taga da mugun falli amaryar ta
shigo mata.
Har girkin amarya ya kare ya dawo ga Salma
amma ba sauki.
Zata gaidashi tai komai,amma ba magana
duguwa, sai ma haushin sa dake kara ziyartar ta.
Tuni ya kai kara gun Aunty A'i,wai Salma taki
sake masa fuska.
A ranar tai mata waya ta kare mata tass,tuni ta
hau kuka,wai ai dan ita bata kishiya ne,bazata
gane lamarin ba,ga kusan kullum Bintu na
chakalarta tana kaucewa.
Shiru Aunty A'in tayi,dole wannan ba zancen
waya bane,
"Ki bari zan zo koh zuwa gobe ne.
Ranar girkin Bintu ne,yau tun safe take fallin
fararo a t'sakar gida,sai ya6a mata haibaici take
ita kad'ai kamar sabon kamu.
Salman tana zaune kan taburma a kofar ta tana
yanke farce.
Harara ta sakar mata,kan taja t'saki,
"Wawiya kawai..
Shewa Bintun tayi harda guda.
"Kece babbar wawiya wacce zaman gidanta ke
mintsininta.. Ehee, naji komai ai,saki daya ya
rage miki duk a dalilin gantali gardi.
A masife ta tashi,sai dai nan da nan ta k'auda
bacin rai dan ya6a ma Bintu magana dai-dai ita.
"Ahaiyee,, naji,tunda banyi k'wantai a layi bare
ina bi ina tallan kaina agun d'a namiji ba ehee, ke
har kin isa ki ce kin san komai?. tunda dey ni ba
matar tushe bace ba... Dan tuni akasan da matar
tushe dai bata k'warjini... Karya uwar bin maza
kawai...
"Eh naji ki ce komai,igiya uku ce a kaina kinga na
fiki matsayi a...
"Ke... Bana son shashancin banza wallahi..
Juyawa sukai danjin mai gidan yai shigar bazata.
"Ihu har titi mutanan unguwa ana jinku sai kace
wasu karnika?...
Harara Salma ta sau mishi da t'sabar tuhuma a
k'allonta.
"A ni ba karya bace, dan har gidan mu ka samo
ni..chan ka nemi karya tun wuri..
Jiki ta kad'e tai dakinta ta barshi baki a sake.
Ita kam Bintu lukwas tayi,tabbas Ja'afar kadai
zai iya fad'a ma Salma cewa ita tace tana
sonshi,da kuka tai d'aki dan bakin ciki.
Itama haka take gun Salman,sosai taji zafin
maganar Bintu,tasan kuma babu mai fad'a mata
sai Ja'afar.
Toh fa Ja'afar, ka shiga t'sakiya.
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:16 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
26_Kowa bin kofar dakinta yai da kallo, yana
murna ba'a rikicin mata biyu a gidanshi yau gashi
an fara,dole ne tun wuri yai ma tufkar hanci. Har
yayi dakin Salman sai ya t'saya, dole ne ya nuna
mata kuranta, in da tai mishi fitsara ya k'yale toh
yanzu bazai d'auka ba,dan ba ita kadai bace a
gidan,kawai sai ya juya dakin Bintu. Kuka take
yana ta fadanshi taki kulashi, chan kuma sai ya
sassauto, "Ni tashin hankali ne bana so a gidana
ne,tun wuri ma in zaku had'a kai ku had'a, dan
ba mai chazan hawan jini. Kai ta dago tana mishi
k'allon tuhuma, "Au shine dalilin da yasa ka fad'a
wa matarka baka so na?.. Ni nace ina son ka
koh?.. A haka za ai zaman lafiyan?.. "Ke kinga
bana son iyayi,dawa nai wannan zancen?.. Da
sauri cikin kuka tace "da matarka man,wato
harda fad'a mata kwantai nayi nai ma tallan
kaina.. "Ban san anyi maganar nan ba Malama,ki
ma cire zargin ni na fad'a mata, bari na je zata
fad'a min yaushe muka fara y'ar sharri da ita...
Waje yayi zuwa dakin Salman. Kai Bintu ta k'ada,
"ashe munafuka karya take dan ta had'ani fad'a
da Miji,toh karyarki taci karya,Allah sa ya k'wada
mata mari tukuicin sharri. Ita kam tanajin bud'e
kofarshi ta mike tare kama k'ugu ta k'ank'ance
ido. "Salma yaushe muka fara y'ar sharri dake a
gidan nan?.. Yaushe nace miki Bintu ce tai min
tallar kanta na aura?.. Harara ta sakar mishi da
k'allon kar ka rainan hankali. "Ka nad'e taburmar
kunyar ka man ta haka,wato kayi amarya shine
ka zabi ka tuzartani agunta,karafkaf abinda ya
faru ta fad'a mini,toh da ka fad'a mata saura
igiya daya ta aurenka a kaina sai mey?.. Baki ya
saka cike da mamaki,lalle ya shiga tarkon kaidi
na mata, wato kowacce sharri take neman k'ulla
mishi a gun y'ar uwarta ashe?.. Bai da tace wa,
kawai sai ya juya zai fice, da sauri tace "a ka
fita man,dan nayi imani bazaka karyata cewar ba
kai ka fad'i ba... "Idan kuma habaici da iyayi
kake neman matarka ta dinga min dan ka huce
haushinka na da toh bissmillah,dai dai nake dana
sa kafar wando daya da kowa a gidan nan
wallahi.. Juyowa yai yana kallonta, sai tai d'aki
ta barshi t'saye baki sake. Titi ya fice ko ya
samu sa'ida, lalle yau ya jinjinawa sharrin
mata,amma kaf yafi jin haushin Salma,dan sam
yanzu ya fuskanci fitsararta tafi ta da yawa. Tun
daga ranar ba jituwa t'sakanin matan, daya in
Bintu ta fad'awa Salma sai ta fad'a mata
dubu,daga karshe ta bige da kukan bakin ciki, har
mai gidan yazo ta kit'sa mai karya da
gaskiya,wani sai dai ya bata hakuri, dan a
ganinshi yanzu Salma tafi karfinshi,dan da ya
mata magana ita y'ar dika take,daga shi har
amaryar zata chake tass, sai dai yai abinda zaiyi.
Shi yasa shi kuma ya t'siri mata t'siya,in dai zata
kona mishi rai,toh shi kuma zai ta biyewa Bintu
suna ta mata feleke a t'sakar gida, daga karshe
kam sai yaci nasara,dan haka zata shiga d'aki tai
ta kukan bakin ciki,a nan zai ta mata dariyar
keta. ***** Sallama taji kamar ta Maman Ummi
da Maman Abba,lekawa tai ta window, sune
kuwa, "munafukan Allah ta'ala kawai... Ta fada
tana kokarin ta fito rai 6ace,dan tai imani duk
abinda take fuskanta yanzu da sa hannun su
aciki... Chak! Taja ta t'saya rike da labule a
hannu ganin Bintu ta fito da gudu danjin sallamar
su. "Sai yau Aunty Ladi zaki zo min? Har nayi
fushi ai.. Baki sake Salma take k'allonsu,tana
k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma
Bintun kuskus tai baya da sauri. Ido ta rint'se
tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu
ta gane inda Bintu ta samo duk wasu
_information_ na zaman aure nata ba agun
Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar,
har rantsuwa yai mata amma taki yadda. Karshe
har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai
da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya. Zama tai
tana jiyo shewarsu a dakin Bintun. Har kullum
bazata daina nadama akan taraiyarta dasu
Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da
t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta. Har hawayen
bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina
sa6awa mijinta ko da taji haushin shi. T'sakar
gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a
kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya. Ganinta a
t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a
t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai
tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau
inda-inda, "dama kina ciki?.. Sannun ku da gida..
Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar
waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku
hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita.
Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai
za tai rakiya waje ya bata izinin fita. Bokiti ta
zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai
waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja
t'saki ta shige band'aki. "A toh na zata koh rafka
mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan
wannan da gani zatai kishin hauka... Dariya suka
sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki
tafiya. Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e
band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin
saukar ruwa sukai akansu har Bintun. Bokitin ta
d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture
suka fita waje da gudu. Tana haki ta leko kofar
gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya
na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon
na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi,
InshaAllah kema dubinki ta kusa cika. "Ke kuma
yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai
Allah, yau zaki ga karyar iskanci. Gida ta koma
tana hakin daga ruwa bucket guda da tsohon
ciki. A t'sakar gidan ta zauna tana maida
numfashi a hankali, ta jima da zama kamin taji
tafiyar Bintu cikin sand'a, kofar ta zubawa ido
tana harara, kai ta leko dashi dan ganin koh
Salman bata nan sai suka had'a ido. "Wallahi
baki isa ki ce zaki hanani shiga ba, in gaske ne ki
bari na shigo na shirya in fad'an ki ke nema dani
ba hauka ba. Murmushi tai daga inda take, "Lalle
kinyi kuskure in kina zatan zan iya had'a jiki da
karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka
yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba
miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31
Feenat Ja'afar Novel's
"Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai
fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu
gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma
Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta
sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai
Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka
da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata
raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana
ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai
watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai
baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya
zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?..
Gidan ki ne da har zaki kafa dokar wa zai shiga
ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a
fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga
mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da
akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace
"eh wallahi, da da halin duka ma sai na
miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta
matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada,
kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code
wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi,
"Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka
dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar
g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan
Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana
lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita
harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan
wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin
dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in
ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki
kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin
yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun
ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai
murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta
fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita
Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in
zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga
shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk
inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye
kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya
take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai
waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta
shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta
samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure
yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata
cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira..
Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana
mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi
dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi
yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata
amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi
machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu
yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara..
Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu
sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan
har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta
hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By
Feenat Ja'afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 27_Tun
kan Napep ta t'saya ta mika mishi kud'in, da
sauri ta shige gidan Aunty A'i fuska duk hawaye.
"Toh kiyi min bayani man ba kuka ba
Malama,mey aka mi... Wayan Aunty A'in ne ya
hau ruri Aslam ya miko mata. A takaice ta k'alli
Salman sai tai waje dan amsar wayar. Tana ji
tana waya da Abban Aslam kan zata shigo da
Ja'afar. "Dan Allah karki shigo dashi,wallahi ban
san ganinshi,gwara in na huce da kaina zan
koma. Baki sake take k'allonta hijab a hannu,
"Ok,kina nufin yaji kika yi kenan?.. Shiru tai mata
tana ci gaba da goge hawayenta. Bata kara bi ta
kanta ba tai waje. Ba'a jima suka shigo tare,kai
ta kautar gefe, tana jan hanci,ido yayi luhu-luhu
dan kuka. Abinda ya faru ya t'sarawa Aunty A'in,
tuni ganin duk ita ya d'aurawa lefi yasa ta hau
musu bori ba shiri. Ido kawai Aunty A'i ta sa
mata. "Auntyn mu kin gani koh? A gabanki ma
kenan,wallahi na rasa rikicin Salma sam
yanzu,abu kadan yanzu zata hau balbalin bala'i
sai dai ni na bar mata. "Yanzu da banzo ba Allah
kad'ai yasan mey zatai ma y'ar mutane,k'alli a
halin da take fa,amma Salma taki k'wantar da
hankalinta ai zaman lafiya.. "Ni fa kar ma ka
zata kishi nake da kai koh kuma waccan amaryar
taka,sam ba haka bane,ni mud'in za'a tada min
hankali toh lalle na kowa zai tashi... _period_.
Aunty A'i ya k'allo halamar tasa baki.
Tambayarta take mey ya had'a su?.. Amma fur
taki magana a gaban shi,har aka gama sulhu
yace ta taso su koma tace sai dare. Da kai Aunty
A'in tai mishi kawai kan ya k'yaleta. Ba musu ya
tashi kan sai ya zo,yana fita ta mike tai kitchen.
Tana cin abinci Aunty A'i na mata fad'a, kan ta
d'aina fada Ja'afar na fada,dan ta fuskanci Bintu
ta iya bariki. Nan ta fad'a mata ainashin abinda
ya faru,harda irin habaici da sharrin da Bintun ke
mata kullum. Baki ta ta6e. "Ni fa Aunty A'i Bintu
bata gabana, abu daya na sani na tsani a gabana
yana biye mata tana mishi abinda taga dama..
Yana konan rai ne,shi yasa yake rasa kaina.
Murmushi tai mata, "Lalle Salma kina so Bintu ta
kai ki ta baro, kin kuma yi saken da kika bari
kishiya har ta gano lagon ki,dole yai ta ganin
bakin ki ke kadai,dan ke kadai ki ke iya daga
jijiyoyin wuya agabanshi akanta,in sharri ma ta
miki ki barta da Allah kawai,shi zai isar miki,kar
ki manta igiya daya tai saura a t'sakanin ku da
Ja'afar, kuma kince ta sani,toh wallahi ki sani
ingiza mai kantu ruwa kawai zata miki,so take
tai ta tunzuro ki har ki tafka kuskuren da za ai
mai dika, kinga taci galaba kenan. "Gaba koh
abinsu suke kina d'auke kanki a kansu, sannan
abu in kinga zai ja ki fad'i wata magana
musamman kan Ja'afar kiyi shiru kar ki tanka
dan Allah Salma. "Ja'afar na sonki,kiyi amfani da
hakan sai ki ci galaba kan Bintu.. Har ta gama
mata fada tana ta nazarin abin,toh Allah yasa ta
iya k'auda kan. Ita kwa Bintu murna fal rai,dan
tana lekensu ta k'auran zauren, fatan ta Allah
yasa yadda ya figi machine din nan in yaje kawai
ya dankara mata saki. Shi yasa tun kan ya dawo
taje ta t'sant'sar wanka ta hau kananan kaya,
duk da ba ita ke dashi ba. Ita a ganinta an sau
Salma an gama,.. K'warai ta gode da shawarar
su Aunty Ladi ta waya da ta yau,tabbas da
BARIKI kadai zata mallaki Ja'afar ba boka ba
Malam. Sai dai har dare ba Ja'afar ba dalilin
sa,kawai sai ta zata bai gama hucewa
bane,tasan mutumin ak'wai saurin zuciya. Dirin
machine dinshi taji,da sauri ta kara fesa turare
ta haska touch light tai zauren da zummar taro
shi yasha Bariki. Turus taja ta t'saya gabanta na
fad'uwa, ganin ya mike yana fad'in ma Salma
"Dafani man toh,ban san ki fad'i ne garin sauka.
Da kamar kar ta kulashi,amma ganin hasken
fitilar Bintu yasa ta hau shagwaba. "Toh ni kam
tsoron sauka fa nake tunda cikin nan yai girma,in
zaka iya ka sauke ni toh... Ta karasa da kalar
tausayi. "Toh toh,amma ki kokarta,ki rikeni gam,
koh ki bari na fara sauka... Kofar Bintu ta saka
da sauri ta koma ciki dan bakin ciki. Tana jiyo su
a t'sakar gida Salman na fad'in "Wash.. Allah Ya
Ja'afar kafata rikewa take fa.. Tuni gogan ya hau
rikicewa abinda aka jima ba'a mishi ba yau yake
gani,bar zuciya da abinda take so. "T'saya na
d'auke ki toh ai kina ma kok'ari.. Tana jiyo
Salman na fad'in "kai Ya Ja'afar, anya zaka iya
kuwa?.. Nayi nauyi fa yanzu. A zabure ta mike ta
tana lekensu ta window ta cika tai ham. Dariya
suke k'yak'yatawa kan yace"bari ki ga,nawa ki
ke.. Da sauri ta sau labulen ganin ya k'wa daga
Salman ya dauke kamar y'ar tsana suna dariya.
Har d'aki ya dire ta suna nishad'i kamar ba su
bane dazu an bar Bintu da kukan d'aki. Sai yanzu
ya tuna ai koh sallama basuyi ba suka shigo.
Murmushi tai mishi lokacin da yace bari yaje ya
dawo. K'wafa tai tana kada kai, "kowa ya iya
BARIKIN ai,in na baje tawa sai kin ji jiki Bintu.
Yau da sauri-sauri yai ma Bintun sallama yana ta
zumudin sun dinke da ta k'arfen. Kuka wiwi tai
tayi bayan fitarshi. A gaban mudubi ya tarar ta
tana g'yara gashi,kowa farin ciki fal ranshi,ta
baya ya sakalo cikin yana shafawa harda sakar
ajiyar zuciya. Murmushi tai mishi,tare da shafo
siririn sajen shi ta bayan, sai ya k'wanto da
kanshi wuyanta suna ma juna murmushi ta jikin
mudubin. Yaushe rabon su kasance haka shi da
Salman sa?.. Ga y'ar shagwa6ar nan yau yana
shanta,duk sai ta mantarshi komai. A hankali ya
rad'a mata a kunne "I love you... Murmushi tai
kan ta juyo tana lumlumshe ido jin dad'in kalmar,
lafewa tai jikinshi tana fad'in ''Me too.. Sosai
yasha mamakin Salman shi yau,komai yi mishi
take cikin kauna da kulawa, kamar farkon
aurensu kamin komai ya wargaje. Hakan yasa
washegari kowa fuskar nan kamar gonar audiga
dan fara'a, amma banda Bintu Lol. By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 28_Tun
daga ranar aka dinke da Salma da Ja'afar d'inta,
sam ta d'aina sanya da abinta, shima abin nema
ya samu,wai ! Matar falke ta haifi jaki. Kan kace
k'wabo,tuni tsohuwar soyayya ta dawo d'anya,sai
ya zama kamar kamar yanzu ma tafi yawa. A
cikin wata guda duk sun sauya,takanas zaice su
fito aje siyayyar kayan baby,fur Bintu take kin
zuwa,sai suyi tafiyarsu a kafa suna tadin su,sai
jiran EDD. Kwana biyu Bintu an tsiri zaman
d'aki,sai ta kule ka rasa abinda take aciki ita
daya. Ranar tana bacci da safe wajen k'arfe
goma taji kwkwazon maigidan yana tayi ba
kakkautawa. Tashi tai ta fito parlour. "Na fita ban
karya ba,yanzu ma na dawo ashe baki tashi ba,
bayan tun asubar fari kika fara wannan charting
din danaki jini a rayuwa,na hana kin ki
hanuwa,toh ina gaf da fasa wayarnan a gidan
nan Allah. Baki ta ta6e tare da tashi a hankali
tayi d'aki dan fita wanka. Tana kallo ta fito wai
yai hakuri ta daura mishi indomie,koh ta kanta
bai bi ba yai waje yana huci. Kamar jira take,da
dan gudunta ta koma d'aki ta dane Facebook
cikin group din su na KI G'YARA DA KANKI.
Kusan duk anyi katari masu kishiya sun da yawa,
nan zatai ta samun shawarwari mey kyau da
marar k'yau,dak'yar ta tashi ta d'aura jalof ta
koma. "Wato sai yanzu nake hangen maganar ka
abokina, dan yanzu abinda Bintu take har yafi
mai na gantali ciwo,in ta hau wannan Facebook
din nata,sam bata ji bata gani,abinci a kone, in
ma ta samu d'aurawa kenan,sallah a kure,bacci
sai biyun dare,da asuba ta d'aura a inda ta
tsaya,ga in ka shigo kaji tana dariya ita kad'ai,
Allah zaka zata Bintu sabon kamu ce... Dariya ya
fara mishi harda k'yak'yatawa,har ya fara
k'uluwa,yasan haka zata biyo baya, amma shi
yanzu shawara yake nema ya zai da sabon halin
Bintu?. "In ka gama kai magana sai ka bani
shawarar abin da zanyi. Dak'yar Garba ya takaita
dariyar ya fara magana. "A lokacin chan baya ai
bakaji zance na ba,dake idon ka a rufe yake,na
sanarka baka san mey wani irin hali zaka jajubo
ba,kace kai fa gaji ka gani sai Bintu.. "Malam ni
shawara zaka bani,in babu zanyi gida. Dariya ya
cigaba dayi,kawai sai ya zuciya yai gaba. "Ma
had'u in ka gama,dan hankalina yai kan
Salmatee. "Wash Allah bayana,Bintu!...Bintu!!..
Tamkar ba kowa a gidan ka ke ji sai karar fankar
sama dake kadawa a parlourn wacce bata hana
gumi t'satsafo mata ba. Rarrafo wa tai zuwa
kofa,iya karfinta ta kwalawa Bintun kira,ji take
tamkar zata mutu dan azabar ciwo,tuni ta fara
kuka tana ambatan Allah,tasan koh zata mutu
Bintu bazata taimake ta ba,fatan ta Allah ya
hankad'o mata Ja'afar koh wani ya ceceta.
"Wayyo Ya Ja'afar, Innalillahi.. Bintu.. A razane
ya karaso cikin gidan dan jin ta ambaci Bintu
cikin kuka. "Subhanallah.. Salma.. Ina Bintun
toh?.. Da sauri ta dago,tana ganinshi ta kara
fashewa da kuka tana cije le6e. gaba daya ya
tallafota yana aikin sannu sannu. Waya ya ciro
dan neman Garba ya kaisu asibiti, tana ta ringing
shiru.. Da rigarshi ya goge mata gomin dake
tsatsafo mata, "Bari na ga koh bacci waccan
take na taso ta. Hannunshi ta rike gam tana
girgiza mai kai, Kanta ya shafa, "ki d'aure
Salma,bari na kirata kinji. Dak'yar ta cika shi yai
dakin Bintun, dan ji take yana tafiya zata mutu.
Bata parlourn, sai ya bankad'a daki,tana mike a
kan gado taja rabin bargo tana dariya kasa-kasa
tana charting hankalinta yai gaba. A sukwane yai
kanta,bai wata-wata ya sinketa da mari mai rai
da lafiya,a gigice ta mike tare da dafe
kunci,wayar ya warce, "Lalle haukar nan taki
karuwa take Bintu,yanzu dama kina cikin gidan
nan Salma take ta kakarin kiranki kamar zata
mutu?.. "Toh ki biyoni yanzun nan waje, tana turo
baki ta sakko kan gadon tana gunguni. Nishi take
ta dafe d'ukkan hannunta a kasa, sannu yake
mata da tausayawa,da harara Bintu ta bita da jin
haushin akanta an mare ta. "Ka kira min Iya
Shatu dan Allah Ya Ja'afar kar na mutu.. Bintu
ya kallo dake maka musu harara, "Kizo ki
kamamin ita na kira Iya Shatun, kamar bata so ta
matso kusa,yana fita ta mat'sa tana jan
tsuka,"aikin banza,dan kina wata shegiyar
nakudarki akan hakan kika ja aka mare ni, wallahi
za... "Eh dan Allah kazo yanzu mukaita asibiti..
Shiru tai jin Ja'afar na kokarin shigowa tare da
matsawa gun Salman da sauri zata ta6ata tana
sannu. A hankali ta janye daga hannun Bintun tai
dan ciki kad'an tana nishi, da sauri ya karaso
dakin yana mata sannu. Nishi take iya karfinta
sukaji sallamar Iya shatu,tana dubata tace ai
haihuwa ce tazo gadan-gadan, ya basu waje, ya
siyo reza da sauran abin bukata. Gam hannunta
na cikin nashi,ji yake tana cikawa in ya tafi zata
mutu. Kanta ya tallafo yana ta d'aure, iya shatu
sai k'allon ikon Allah take. "Kai hakuri
Jafaru,zata haihu lafiya dan ina jin kan D'a,
yanzu bazata ji komai naka ba sai adu'a. Kai ya
kada harda guntun hawayenshi yai waje,yana fita
Bintu ta d'aura a bayanshi. Iya shatu tsuhuwar
ingozoma ce mai ritaya, da guntun hand gulf din
zuwa awunta ta karbi haihuwar Salman. Allah ya
taimake tazo mata da sauki inji Iyan,sai shigowa
yai shi da Garba yaji ihun jariri,baki wangale zai
dakin iya shatu ta fito k'ar6ar reza. Ummanshi
ya fara mawa albishir sai Aunty A'i,tuni ya fesa
cikin gidan su,da ance mey ta samu? Sai yace
bai gani ba. Har aka kintsa komai basu kara
ganin keyar Bintu ba,sai da zasu asibiti ta fito,shi
kam baiya ma ta ita. Suna fita su Aunty A'i suka
zo da Ummi,lokacin Bintun na t'sakar gida tana
yankar farce,ita dey Iya sai mamakin karfin hali
irin na Bintu take. Sallama suke ta manna musu
bajon hauka,tuni Ummi taja dogon t'saki, taki
jinin Bintu a rayuwa. "Banza y'ar bakin ciki
kawai,toh sai ki had'iyi zuciya ki mutu ai.. Hannu
Aunty A'i ta daga mata halamar tai shiru,ita k'wa
da harara tabi su har suka shige. Sun dawo an
duba suna lafiya ita da babyn ta,Ja'afar baki har
kusan k'unne dan murna,yana makale da yarshi.
"Um,Baban baby ba koh dan karar nan ma ta
manyan yayu.. Kai ya sosa yana ma Aunty A'in
murmushi, ba dan yaso ba ya mika mata ita. Kan
kace mey gida har ya cike da dangi yan barka da
yan unguwa. Sai dare ta samu tasa hakarkarinta
dan hutu. K'allon babyn take mey kama da
Abbanta, gashi kadai da dan _beauty points_
(dimples) tai gadonta. Murmushi tayi tana kai
hannu kan kumatun babyn, Allah mai halitta.
Murmushi yake musu yayin da ya shigo d'akin,
sai ta daga kai ta k'alleshi, kai ta girgiza tana
dan murmushi. Sallama ta uku yana musu kenan
yana dawo wa,ta rasa wani irin kulafuci yake
musu musamman babyn. Zama yayi yana shafo
sumar babyn da farin ciki. "Oh ni kam,koh zaka je
da ita in tai kuka sai ka kawo ta. Murmushi yayi
yana kai baki kan dimple din babyn yana kissing.
"Ba kinki barina na k'wana anan ba?.. Da kalar
tausayi yace "yau dai daya naji dumin y'ata kinji?
Sai ya marairaice fuska. Dariya ta dan mishi,kan
tai magana ta jiyo Babah mai zamar mata tana
ya fito zata zo ta k'wanta,taga sallamar bata
karewa. Dariya suka sa kamin ya tashi yai waje.
"Maza ki rika biye mishi ki debo ma kanki
magana da kazamin goyo ai. Da rashin fahimta ta
k'allota tana neman karin bayani. ***** ***** Yau
suna,baby taci sunan Mama tun ran huduba
amma ya 6oye mata. Sosai yau daya Ja'afar ya
biya mama,harda mishi waya tana kwarara mishi
godiya ba iyaka. Maijego tai ras abinta da Baby
Miemien ta,sun fito sunyi k'yau sosai. By Feenat
Ja'afar. Ai hakuri da wannan dan zani gidan
Suna Salma.. Zuwa yamma in na dawo zakujini
Lol..
9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
29_Suna ya wat'se kalau,maijego tai
goshi,ak'wati guda Mama ta mata na suna sai na
baba,ga Umman Ja'afar nata daban da tazo
suna,chan gidan su Ja'afar su ma sun mata
karamci,sai son barka. Wankansu suke cikin
g'yara na musamman da Mama ta zage yi ma
y'arta, albarkacin Miemie mama ta sakko sosai.
Shirya Miemie take tare da taimakon Ja'afar din
suna ta nishad'in su yau za ai yawan arba'in. Ta
chakare sosai kamar yau ne sunan ita da Miemie.
Baya ta juya mishi yana goya mata ita, "D'aure
ta dakyau,dan kinga machine zamu hau.. Kai ta
kad'a tana murmushi, Sai da ya zaga ko'ina yaga
yayi kan ya bata majanyi tana mishi dariya, "A'a
toh in baki iya ba ni sai na goya abata kawai...
Dariya tai kan tace "Da kwa kabar abin fad'i
agari kuwa. Jakar ya d'au mata ta d'au mukulli
sukai waje,shima yasha sabuwar shadda abinshi.
Bintu na t'sakar gida tana d'anne-d'anne a wayar
da dak'yar ya bata. Da harara ta bisu harda dan
t'saki a hankali. "Toh mu zamu fita sarauniyar
charting.. Sai kisa mana mukulli a gida dan
gudun kar a dirko kina sana'ar taki koh.. Tuni ta
kara k'uluwa kuwa,ita dai an mayarta borar karfi
da yaji a cikin gida. Hannu Salman ta dago mata
halamar sai sun dawo,da harara ta bisu har sukai
waje. "Jishi kamar wani dan daudu rike da jakar
mata. K'wafa tai tana tashi t'saye, "Ba dai kin
fara fita ba?.. K'wanan nan zaki yabawa Aya
zakinta wallahi. ** K'wana biyu yau tayi tana fita
yawan arba'in, yau ne na uku,yau kuma aka tafka
t'siya da maigidan,dan fur yace ba inda zata je.
"Bazaki k'waso ma yarinya rana ba fa,kiyi hakuri
kawai. Iya wuya Salma ta kawo dan takaici, tayi
magiyar yaki kuma,kawai sai ta raya mata tunda
dama taki bari ta koma hagu. "Amma gaskiya
baka min daidai ba Abban Miemie in har ka
hanani fita yau. "A ka'ida sati ake fita yawan
arba'in fa,amma ni na yarda zanyi ukun shine har
na gama shiri amma kace bazani ba... Gaskiya
da sake. Gefe tai da kai tana kunkuni,tuni ta
kular dashi shi zuciya kusa. "Toh ban hanaki ba
kije d'in, amma ki ajiye min y'ata ki tafi ke kad'ai.
Baki sake take k'allonshi,ganin yadda ya fidda
waya yasha kunu ya barta. A zuciyarta tace "Eh
lalle,da gani abin Ya Ja'afar yazo da wulakanci...
"Kasan dai ba yadda za ai na tafi na bar Miemie
a gida,dan Allah in wasa ka ke ka bari,dan kam
nasa rai da fita yau.. A tunzure ya mike da niyar
magana cikin masifa,sai yai shiru yana k'allonta.
"Kiyi toh gaban kanki kawai.. Sai yai waje da
zummar barin gidan ma dan haushi. Sai dai
mey?.. T'saye yayi yana binta da k'allo galala,
ganin yadda ta fara kame-kame dan ya kamata
tana musu la6e ta window. "Ke kuma lafiya kike
abu kamar marar gaskiya?.. Dakewa tayi tai
ganin kamar bai ramfota ba. "Dama zuwa nayi
ina son na leka nan na dawo ne... "Ba mai fita
yau acikin gidan nan in dai ni ne mijin, wacce ban
isa ba ta fita nagani.. A fusace ya fice yabar
gidan,duk sai ta Salma tafi zafi. Ita kam Bintu
dariya tasa harda shewa, "Yau karya ta kare,sai
a za6a zaman gidan miji koh fita yawan gantali
gard'i... Tana jiyota tai banza da ita tana
hawayen bakin ciki. Waya ta d'auka ta kira Aunty
A'i kan abinda Ya Ja'afar ya mata. "Salma kiyi
biyayyar aurenki, dan Allah kiyi hakuri da fitar
kawai. "K'wana biyu ai yayi ma,tunda kin zaga
ko'ina ai har gidan su... "Aunty A'i ban fa wuni a
gida ba kullum a ziyara muke wuni. "Ai duk fita
kina zuwa,dan Allah kar ki dawo muku da hannun
k'yauta baya man,kuna cikin zamanku abin
sha'awa. Baki tai ta bata sai da ta tabbatar mata
da ta hakura kamin sukai sallama. Haka tanaji
tana gani ta hakura da fitar tai zamanta a d'aki.
Koh abincin rana kin zuwa yai yaci a gidan sai
gidan Garba yaje. Kawai zuciya ke raya mishi
Salma ta fita,bazai so yaje gida yaga tabbas ta
fitan ba,kawai sai yai zamanshi har yamma tukun
ya koma gida. Dakin Bintu ya nufa har yanzu
baida walwala sai ya tabbatar da Salma bata fita
ba,yasan Bintu kat ce,bata t'sallaka doka akan
fita,in yace A'a, toh ta hakura. Sannu da zuwa tai
mishi tana fara'a, a ranshi yana aiyana da Salma
ce yasan sai ta cika tai fa kan ta mishi sannu da
zuwa duk akan ya hanata unguwa,amma kullum
y'ar uwarta ko ajikinta. "Yau bayan fita ta Salma
ta fita?.. Kai zata girgiza, sai tai saurin kwa6ar
kanta, dole yadda tasa taga bakin ciki har yau
itama ta gani. "Eh,bata jima da dawo wa ba
ai,baka sani bane?.. Hannu ya daga mata,cike da
jin haushi yace "ya isa ni,tambaya na miki kawai.
Waje yayi tana binshi da g'walo, yana yin nisa ta
tuntsire da dariyar mugunta. Kamin cikin sand'a
tai waje jin ya zata kaya. Ba koh sallama ya
shiga parlourn, ganan takalmin a gefen kofa
wanda ta fitar zata sa dazu. Tana zaune tana
_feeding_ din Miemie ya shigo yana binta da
kallo,da fara'arta tai mishi sannu da zuwa.
Kekam yayi yana k'allonta ba koh kiftawa, tabbas
Salma ta fita,dan mud'in bata fita ba bazata tare
shi da wannan fara'ar ba haka,yasan kayarshi.
"Wato kin fita hankalinki ya kwanta koh?.. Ban
isa ba ashe har yau halinki yana nan baki sauya
ba koh Salma?.. Baki sake take K'allonshi da
tsananin mamaki,sai d'aure ta yake da jijiyoyinta.
Cikin nut'suwa tace "Ni fa ba inda naje tun fitar
ka,dan Allah ka d'aina tun.. Malama ki amshi laifi
kawai,kinsan nafi t'sanar musu sama da komai,
koh kina nufin Bintu karya zata miki?. K'allon
mamaki take mishi,a hankali ta maimaita
"Bintu".. Yaki ma bari tai mishi bayani sai
zazzaga mata yake kan bata maidashi abakin
komai ba. Kawai sai ta sau mishi kuka,tama rasa
abin fad'i,wai Bintu ce ta fad'a mishi,wato ita ba
abin yarda bace sai kishiyarta indai kan fita ne.
"Haka ki ke ai,da kukan rashin gaskiya
Salma..sam bana son ki dawo mana da hannun
agogo baya,ina ta murna komai ya wuce ashe
albarkar ciki ne yasa ki zaman dole. Ganin
kukanta na karuwa yasa ya fice ya koma d'akin
Bintu. Har da bawa kura ajiyar nama,wai duk
randa Salma ta fita dan Allah karta 6oye mishi.
Tun daga ranar ya sauya mata,sam in ya shigo
sai dai ya d'au ya'rshi ya fice,itama daga
gaisuwa shikenan ta gama,dan a ganinta
wulakanci ne wannan babba. Ga wani fi'ilin
mutunci da Bintu ta koya da kissa,kullum faram
faram take mata,harda gaisuwa in antashi. Ta
d'au Miemie ta goya a bayanta in Baban ya
d'akko ta. Ba karamin dad'i kwa Ja'afar din yake
ji ba,dan yana karrama mai son Miemien shi,ita
kam Salma nata ido,sai ta dukufa gun kai
kukanta ga Allah. Dan tabbas tasan tai saken da
har mijinta yai mata mummunan tambari. Bintu
kuwa kullum rokon ta Allah duk wani sharrin da
take nemanta dashi Allah ya mayar mata kanta.
By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/2, 2:29 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
30_Sai ya huce kamar sati ana mutunci da ta
tambayi fita unguwa zai kicin-kicin,yace tai son
ranta,haka zata hakura tanaji tana gani,in ya
dawo kuma tasha fad'an da batasan laifi ba.
Kawai Allah ya d'aura mata wani irin hakuri,daga
Ja'afar din har Bintun ido tasa musu kawai.
A haka har Miemie tai wata hudu Salma na
zaman hakuri, musamman ga saurin fushin
Ja'afar gareta,ga tai alkawarin daina kai kara gun
kowa sai gurin Allah.
Ana haka Maman Abba ta haihu.
Ganin yau y'an mutuncin na kanshi yana zaune
ya shagala da yiwa Miemie wasa tana wage
mishi baki tana dariya.
Da fara'arta ta zauna kusa dasu tana k'allonsu.
"Abban Miemie...
K'allota yayi tare fad'in yana jinta,cigaba yayi da
wasan su.
"Inda hali dan Allah zani barkar Maman Abba yau
kwananta hud'u da haihu banje ba.
Kai ya kad'a, "wace Maman Abba?..
Da zumudin zai batta ta sanarshi makociyarta ta
unguwar su ta da.
Abinda yake ya t'sagaita yana k'allonta ba koh
kiftawa.
Tuni ya zata an rufe babin y'an tsohowar
unguwar su a gidan,ashe har yanzu tana makale
dasu.
Bazai manta dasu ba,dan sune ummul aba'isin
wargaza gidanshi.
Kai ya girgiza mata,
"Kiyi hakuri ba halin zuwa..
Baki ta sake tana K'allonshi, a gaskiya bazata
zuba ido tai ta zaman gida na y'anci ba,da takura
gaskiya.
Amma sai ta bishi da lallami.
"Dan Allah ya Ja'afar ka barni naje,nima dana
haihu fa sau biyu tazo min har suna uku,kaga ba
dad'i ace ni koh sau d'aya banje ba barka ba sai
suna.
"Sunan ma ki fidda a ranki,dan inda mu'amular
dana fi tsana,toh mu'amular ki da y'an unguwar
chan ne,kin gane ai?.
Kasa tai da kai,sosai take d'aure irin halin da Ya
Ja'afar ya tsiro mata,yanzu da ta kara tambaya
zai ce tai gaban kanta,hakan yasa tai shiru.
Shi kuma yadda yaga batai gardama ba yasa yai
tunanin zancen bai shige ta ba ne.
Miemie ya ajiye kusa da ita ya bar mata d'akin.
A hankali ta zame ta kwanta,sai ga hawaye ya
zubo mata.
Zaman gidan nan ya fara isar ta,hakurinta ya
fara karewa.
Tana ji yai ma Bintu sallama ya fice,kawai sai ta
sau kuka a hankali marar sauti.
Wato a dake ka a hanaka kuka?.
****
Tun bayan fitarshi bayan ta gama kukanta
Miemie ta fara,kukan har ya wuce kima, komai
tayi taki shiru,kawai sai ta goyata tasa hijab akai
suka fita t'sakar gida dan sanyin magriba.
Bintun na t'sakar gida tana saita abin fad'i kan
Ja'afar ya dawo tambayar Salma koh ta fita,dan
komai a k'unnenta ya wakana.
Jijjiga ta take tana yawo daga t'sakar gida zuwa
zaure da ita,tasan Miemie ba mai rigima bace,
tabbas da abinda ke damunta yau,yawan kukan ji
take kamar itama tasa kukan koh taji sa'ida.
Dak'yar ta samu tai shiru,sai ajiyar zuciya take
halamar tai bacci.
Buta ta d'auka ta shiga band'aki kenan sai gashi
kamar an hulloshi gidan,fatanshi yau ya rit'sata
garin satar fita.
Bintu ya kalla wacce ke murmushin ganinshi,sai
taunar cingam take tana kas-kas,kai da ganinta
da yanayinta kaga na mai shirin kulla wani
sharrin.
"Sannu da zuwa..
Kai ya daga mata, kamar kullum zai tambayi
Salman sai yaji bud'e band'aki.
A fusace ya kallo Bintu, "bayan fita ta Salma ta
fita?.. Ki fad'an t'sakani da Allah.
Kwai tayi kan ta fasa tare da yin kas dashi,
"Eh ta fita,mey ya faru? Yanzun bud'e dakinta ta
shiga band'aki ka shigo.
Gadan-gadan Salma tayi kanta da butar data cika
zatai alwala anjima,kansu farga ta rot'sa mata
aka tana huci,bai isa ba ta rufeta da duka baji ba
gani,fad'i take
"Sharrin naki ya wuce bayan idona yanzu a
gaban idona ma yi..
Mari ya d'auketa dashi shima yana fad'in ta sake
ta.
A fusace tace bazata saka ba,ita kam tamkar
wawiya ta bari Salman na jibgarta,ganin da gaske
take yasa da sauri ya finciko Bintun tare da kara
mata wani marin.
Kunci ta rike tana K'allonshi, "ki sani na gaji da
halinki a gidan nan, karan nan zan d'au
mummunan mataki akanki wall...
"Ka sallame ni in ka gaji dani Ja'afar.. Dan ni tuni
na gaji da zaman gidan ka, ka sallame ni ka huta
toh..
"Haka ki ka ce?..
A fusace tace "eh haka nace..
Tuni shedan ya shiga cikin zuciyar
kowa,musamman Ja'afar da ya rufe ido tamkar
bashi ba.
"Ki je gida sai na neme ki toh...
Cikin kuka tace
''Ban isa zuwa musu ba sheda ba,dole ka bani
sheda..
Ba tare da jin komai ba mugu(shedan) yasa ya
rufe ido.
"Kije na sake ki toh..
Chak! Taji kukan ya t'saya sai na Miemie data
tashi dan hayaniya.
Baki sake take k'allonshi fuska wanke da
hawaye.
"Ja'afar ka sakeni kace fa?.. Muryarta na
ka'rkarwa ta tambaya.
Da sauri ya bud'e ido ya dawo hankalinshi kanta.
K'allon-k'allo suke ma juna cikin rashin sanin
abin fad'a, musamman Ja'afar dashi ya furta.
Ido ta rufe a hankali, sai ga hawayen da ya
makale sun zubo.
A hankali ta bud'e idon ta k'alli Bintu.
"Allah ya biya ki da dai-dai abinda ki kamin
Bintu.. Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai
dawo gun maishi..
Jiki a sanyaye ta juya gun Ja'afar.
"Shikenan abin nema ya same mu Ja'afar.. Aure
ya kare a t'sakanin mu..igiya uku ka rusheta
Ja'afar.. Ka rushe su..
Hannu tasa ta share idonta.
"Ba ka da bukatar na t'saya maka bayani yanzu
kam,dan ka zuba katanga a t'sakanin mu.
Cikin nut'suwa tai hanyar waje ba tare da ta koh
waiwayi d'aki ba.
Da k'allo ya bita, ilahirin jikinshi ka'rkarwa
yake,ya kasa tattara kalma daya da zai ambata,
har Salma ta 6ace wa ganinshi.
'By
Feenat Ja'afar.
[8/2, 10:40 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
31_"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un.. Allahumma
Ajurni fi Musibati,wakhluf li khayran minha...
"Salma ki ce min ba gaskiya ki ke fad'a ba
Salma?.. Dan Allah ki ce wasa ki ke..
Murmushi take,wanda da zatai kukan zai fi mata
alkairi, amma ta kasa,tun zuwanta gidan Aunty
A'i ido ya kafe,tunani ya t'saya.. Dabara ta ka
re,sai kallo da ido da murmushi da yafi kuka
ciwo.
Waya Aunty A'in ta d'auka dan kiran Ja'afar,
tayuwu koh shi ya mata bayanin da zata gamsu
tunda Salma ta zama kurma.
"Ja'afar..
"Bashi bane.. Tsam tayi dan tasan Bintu ce ta
d'auka.
Da karfin hali ta tambayi in yana kusa ta bashi
man, t'saki tai mata kamin ta kashewar.
Kasa tai da wayar tana mai tabbatar da kalaman
Salma na aure babu,ya ka re.
A hankali ta sakko ta t'suguna gaban Salman
tare da dafa kafafunta.
"Salma kimin magana ba shiru ba dan Allah.. A
dunkule kika bani, dan Allah kiyi magana, shin da
gaske ya sake ki cikon na ukun?..
K'allon Aunty A'in take cikin ido,tabbas wannan
kalmar ita ta 6acewa tunaninta.
Kan ta ankara ta sau mata wiwi,baji ba gani.
"Bintu ce... Wallahi itace.. Ban mishi komai
ba..ya raba aurenmu.. Allah banyi komai ba
karan nan Aunty A'i,ki yarda dani dan Allah, koh
su Abba baza su yarda ba...
Kamar karatun yara haka take had'a kalaman
cikin kuka.
Jiki a sanyaye Aunty A'in ta tashi tazo kusa da
ita,sosai ta gane sambatu take,cike da tausayin
y'ar uwartata ta rungumo ta, ta abu daya take
gane gaskiyar Salma tun a yarinta, shine fad'in
abin da batai ba cikin kuka.
"Na yarda Salma,na yarda dake karan nan.. Ki
bar kukan haka, Allahu yasa shi yafi zama muku
alkairi.
Ita dai kukanta take.
Ina Ja'afar ya gano abinda Aunty A'i ta sani
game da rayuwar Salma, da bai bawa CID na fitar
ta ba, da ya fuskanci ta sauya tun sa'ilin da in
yace ta fita take kuka,da ba ayi hakan ba.
*******************
"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'una... Ja'afar mai ya
kai ka wannan yanke d'anyen hukuncin kan ku?..
Mey ya kai ka?.. Abinda ya faru yake sanar
mishi,gaba daya ya rasa abin yi.
"Shin ka tambayi ta fitan koh bata fitan ba?.. Koh
har yanzu kai baka hango hankalin Salma ba ne..
Kai ya k'ada mishi
"Ba wannan ne karon farko ba,ni nasan Salma
fiye da zaton ka..
"Ka kuma yarda da Bintu fiye da yarda ka bawa
Salma yarda koh ka ke nufi?..
Murmushi yayi na takaici, "Ja'afar bakasan sharri
irin na mata bane.. Da baka ba Bintu amanar
aurenka sukutum ba Allah. Tayu ka tafka babban
kuskure na fahimtar Salma karan nan.. Amma ka
yi bincike, shine t'sarin Shari'a.. Ni na shiga gida.
Da kallo yabi bayan Garban, duk maganar shi
gaskiya ce,kuma ba daya daga ci da ya aiwatar
kamin komai.
Yau daya yaga fushin Garba karara kwance a
fuska,tabbas haushin shi yake ji shima,kamar
yadda shima yake jin haushin kanshi da kanshi.
Jiki ba kwari ya tada machine yai gida.
Dole ya tit'siye Bintu ta sanarshi gaskiya.
Bata d'aki,ga nan wayarshi da ya manta da tata
akan gado halamar tana sana'ar tata ta charting.
A garin ya d'auki tashi ya danno screen na
Bintun, haske ya baiyana halamar tana ma kan
charting din tai wani waje.
Kwanciya yayi da bayanshi jiki duk a
sanyaye,bazai iya bawa wannan ranar suna ba.
Ido ya kura ma wayar Bintun kirar _Techno_, zai
so yau yaga mey ke debe hankalin ta zuwa
Facebook.
*Bintu U*.
_"ke an saki shegiyar fa,ki tayani murna zan
sakata in wataya_..
*Shining star*:
_"Kai matar nan baki da dama,a bani satar amsa
dan yanzu na dawo makarantarki_..
Da azama ya mike zaune dan ganin charting din.
*Binta U*
_"Hhhhh,tuggu dai kamar kullum nayi,sai dai na
yau mai zafi ne,dan jiya an bani sa'a har gida,
take ina fad'in ta fita ya d'anna mata saki,baiwar
Allah harda dan guntun wa'azin ta ta min
hhhhh_..
*Shining star*
_"ina ma zan iya irin wannan sharrin naki dana
huta, sai dai tawa tasan takan duniya,ina mata
take dawo min da abu na_..
*BINTU U*
_"ba gari daya muke ba,da wallahi taci karya,ni
zan baki maganin y'ar banza_...
"Ya Allah... Kai shafo cikin ranar jiki hawaye na
zuba, da sauri ya d'anna _previous chat_
Sai gata kamar an jehota da buta a hannu tana
zare idano na munafukai.
Sam bataji koh dirin machine dinshi ba,sai
arbawa tai da takalmanshi.
Da d'ukkan hannu biyu ya dafe kanshi yana
hawaye,mey zai ma Bintu ya huce da bala'in da
ta jawo mishi?..
A hankali kalaman Salma ya dawo mishi,
_"Allah ya biyaki da dai-dai abinda ki kamin
Bintu..Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai
dawo gun maishi_...
Gashi tun kan a kwana ya dawo ma Bintu bata
shirya ba...
"Ka dawo..yaushe ka shigo..ban banji shigowar
ka ba..
Da in'ina take maganar, ganin yadda hawaye ke
diga a kafafunshi ga kuma wayarta a hannunshi
tasan yau karya ta kare.
Ido ya goge kamin cikin nut'suwa ya ajiye wayar
kan gado ya k'allota.
"Tabbas kinyi nasarar rabani da d'ukkan farin
cikina Bintu.. Kinyi nasara,tanan kam nasan kin
ma Salma fincinkau,dan ita bata sharri..
"Na baki d'ukkan wata amana,ki mayarni
shashasha.. Ki nunan yau abinda Salma take
gudu a kishiya,"makirci"..
"Amma ki sani,wallahi!,wallahi!!.wallahi!!!
Uku,yadda kikai sanadin 6allewar aurenmu da
Salma kinyi naki.
"Kamin nan zaki ji jiki kamar yadda ki ka sa taji
t'sawan zaman ku..
Kan tai kwakwaran mot'si ya hard'o ta, ta ko'ina
mari yake bata iya karfinshi tana ihun jama'a su
ceceta..
Sai da tabbatar ya taga wuta dan mari kamin
yana haki ya nuno ta.
"Kije kema,na yanke igiyar aurena dake kanki har
guda uku... "Tun kan ki kwana maganar Salma ta
kar6u gun Allah...
Ihu ta saka tana bashi hakuri kan ta daina, "dan
Allah karka sake ni...
Hanyar waje yayi yana sa waya a aljihunshi.
"Ki tabbatar baki kara awa d'aya cikin gidana
ba,dan saki uku na furta.
Waje yayi ya ja ya t'saya a zaure,tamkar wani
yaro ya rushe da kuka mai tsanin ciwo..
Yayi kuskuren da dak'yar ya g'yara shi cikin
rayuwarshi.. Yayi kuskuren da ya bari Salma tai
mishi nisa...
Yayi kuskuren kin kar6ar shiryiwar Salman sa..
Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwa.
"Allah ya isa t'sakani na dake Bintu... Ubangiji
yai ma Salma sakayya akanki daga yau har ranar
sakamako... Allah ya isar mata cikin sauri..
Ganin hakan ba mafita bace gareshi yasa ya
d'akko waya hannu na ka'rkarwa zai nemo Garba
yaga kiran Aunty A'i na dazu.
Garban ya kira,dole ayi wacce za ai,Aurenshi da
Salma mutuwa ce kadai zata raba.
Da Allah ya had'ashi cikin muryar kuka kan yazo
gidanshi yanzun nan..
"Isha'i ake kira fa Ja'afar..
"Dan Allah kazo,in bakazo ba komai zai iya
faruwa...
Ba'a fi minti goma ba yazo,fatattakar arziki yai
ma Bintu ta bar gidan ya rufe ya fad'a mota.
Da t'sananin mamaki yake k'allon abokin nashi, a
iya abotarsu bai ta6a ganin koh da hawaye na
Ja'afar ba bare kukanshi mai sauti irin haka.
Dan Ja'afar namijin duniya ne,Jarumi, kuma
jajirtacce, yasan komai ya sashi kuka ayau ba
karami bane.
"Gidan Aisha zaka kai ni yayar Salma..
Baki sake yake k'allonshi,
"Yayar Salma kuma?..
Ido jajir ya kalloshi ba halamar wasa,dole ya tada
mota suka d'au hanya.
Waya yai mata kan ta fito yana kofar gida.
"Malam mijina ya fita..kai hakuri.. Kit ta kashe
wayarta,yau Aunty A'i ta d'au zafi ya sani,tabbas
kuma Salma na gidan..
Murfin motar ya bud'e a fusace ya fice Garba na
kira.. Kofar a bud'e take,kawai ya tura ya shiga,
nufinshi a d'aureshi bayan yaga Salman.
"Salma!,, Salma!!.. A tunzure Aunty A'i ta fito a
parlourn dan tsayarahi shiga mata parlour.
Yadda taganshi bata isa hana shi ba ganin
Salman, dan g'wiwa biyu ya zube gabanta tamkar
yaga Salman.
Hanya ta bashi ba musu,da zafin nama ya mike
ya shiga parlourn, bata zata ba taga mutum a
kanta,da sauri ta zabura ta mike tana kwad'a
kiran Aunty A'i da sauri.
Bata nufa ba taga mutum zube a gabanta kanshi
a kasa.
Ido ta rint'se tare da kawar da kanta,koh kadan
bata son kara ganin Ja'afar a rayuwarta Abadan.
Juyo wa tai da niyar surfa mishi ruwan bala'in da
ba shiri zai bar gidan,sai dai mey?
Da t'sananin mamaki take kallonshi tana k'allon
Aunty A'i.
Hawaye ke malala a idonshi kamar wanda ya
rasa jin dad'in rayuwarshi,abin g'wanin ban
tausayi.
Ja'afar?.. Kuka ma?, a namey toh?.
"Salma gani gabanki, a matsayin wanda ya tafka
miki laifi cikin rashin sani,da kuma sharrin
Bintu..Salma kiyi hakuri,wallahi _am really really
sorry.. Kar ki barni dan Allah.. Zan tagaiyyara
Salma.. Zan zauce.. sharrin Bintu ne,kuma itama
ta amshi hukunci,dan na saketa kamar yadda ta
jawo mana,
_please_ Salma _forgive me_... Wallahi _I can't
live without you anymore_,ki tausaya ma mijinki
uban yaranki...
Baya taja da sauri ganin yana kara kusantota.
Da sauri Aunty A'i tai waje jin kuka zai kubce
mata.. Dole haka zata kasance dasu Salma,ranar
rabuwa, rabuwar da ba a da tabbacin za'a dawo
ta.. Tabbas tausaya wa rayuwar su,dan a irin
soyayyar nan ita ce ake kira *Mutu ka raba*..
Gashi yanzu K'ADDARA ta raba masoyan biyu.
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:24 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
32_Kuka take yanayi iya karfinsu, tabbas
K'ADDARA ta rigayi fata, duk kuma yadda ka
t'sara rayuwarka sai ka ga ba haka ya tafi
ba,tabbas ta Allah itace daidai. Baya tai ta zube
kan kujera da6ar.. Duk sunyi kuskure, kowa na da
laifi,meyasa ma tace ya saketa?.. Mey yasa?..
Le6e ta cije tana mai sa d'ukkan hannunta biyu
zuwa fuskarta, kuka kam yau har sunji ba dad'i.
A hankali ta dago tana K'allonshi ido yai luhu-
luhu,duk ya marairaice mata hawaye na zuba, tafi
tausayin kanta sama dashi, Kokarin magana take
su Aunty A'i sukai sallama ita da maigidan da
taima waya. Fuska Ja'afar yai saurin gogewa
ganin yadda Abban Aslam ya sau baki yana
kallonsu,bai tunanin abin ya kai haka ba, kuka a
gaban mace da zubewa g'wiwa biyu?.. Lalle
yasan abin babba ne. "Innalillahi Wa'ina
Ilaihirraji'un... Itace kalmar shima da ya fad'i
bayan yaji mai ke faruwa.. "Dole aje gida kowa
ya samu labari,dan wannan ba abin a 6oye bane
koh da za'a nemi sulhu,saki ya cike na uku abin
yafi karfin zama anan Ayush.. Zamu tafi da
Salman kai Ja'afar sai ku taho da abokin ka. Har
kusan goman dare ana abu daya akan zancen
saki. "Ka ce kayi saki,ita tace ya zama uku,
sannan kana zancen ai sulhu koh? Kai ya daga
da sauri, murmushi Abban yayi,abin yaso ma
bashi dariya, "Wato Ja'afar... "Malam Umar
wannan zancen ba zancen da za'ai wa sakwakwa
bane,kan Ja'afar ya dawo. "Kai kuma in dan baka
tashi mun wuce ba zan mugun sa6a maka
yanzun nan.. "Kana hauka ne?.. A wane garin ka
ta6a jin anyi saki d'ai daya har uku kuma ana
neman sulhu?.. "Ai baka fara ganin komai ba
Ja'afar, ba dai zuciya ba?.. Za ta sa ka dana
sani, "Malam Umar ai hakuri bisa wannan
K'ADDARAR da ta sakko mana,zamani ne yanzu
muke ciki da yara basu dauki saki a bakin komai
ba.. Tashi yayi yana bawa Abban Salman
hannu,kan ya kallo Ja'afar,har yanzu sautin
kukan su ke fita shi da Salman. "Muje koh?..
Salma ya dago ya kalla da sunkuyar da kai,
"Salma dan Allah ki basu hakuri kar su
rabamu,kin san bazan iya rayuwa ba ke
ba,Abadan Salma...Please. Kuka ta kara saka
mai karfi, t'saki Abba yayi ya karkade riga yana
nuno shi cikin fad'a. "Hauka kenan wannan, dan
koh a musulunce Salma ta haramta a gare ka..ta
haramta har abada,dan kai kam ka nuna mana
bazaka ta6a iya rike aure ba, saki tamkar wasan
yara? Itama waccan wai ka mata saki uku?.. Toh
koh aure Salma tayi na fad'a maka ta haramta a
gare ka har abada,kaje kaci zuciya. Da gudu
Salman ta tashi tai d'aki tana kuka.. "Haba
Alhaji, abin bai kai haka ba,kuskure ne kowa yana
iya tafkawa a rayuwa.. Anji bai k'yauta ba,amma
kar hakan yasa kai mishi baki,kai hakuri. "Hakuri
shine ya biyo ni yanzun nan.. Wace iriyar
haukace wannan kamar a jahiliya?.. Wani yai
mishi sakin?.. Haka Ja'afar naji na gani yai waje
yana waiwayen dakin da Salma ta shige yana
hawaye. Tun daga ranar duk suka zama sakwa-
sakwa, barin Ja'afar da baida kuzari,ga Abba ya
sako shi gaba ta ko'ina.. Dan har gida iyaye
Bintu suka zo sukai ma Abba rashin k'yauta wa
akan yadda bayan saki uku sai da aka
kumburawa ya'rsu fuska,harda ikirarin
koto,dak'yar aka basu hakuri kan suka debe
kayanta, ranar Abba yayi takaici har yaji ina ma
da ya barma Umman shi Ja'afar,kila da baici
karo da bacin ranshi ba. Sai dai yace kayan
Salma koh sama da kasa zasu had'e ba mai diba,
ashe ma in ya bari aka diba sun rabun kenan...
Ja'afar mat'sala. Anyi ban baki, Abba yayi fad'an
ya dawo lallashin amma Ja'afar ba sauki,kawai
sai Abban Salma yace a rabu dashi,dole in ta
tashi aure zai bari a diba da kanshi. Kullum ta
Allah yana kan jelar gidan su Salma,a wata guda
har kama ya sauya,ba aski,ba g'yaran fuska,ya
zama tamkar zararre. Sosai Abba yake tausaya
mishi,Mama kadai ke shafawa idonta toka ta
hana ya ga Salman,sai dai a bashi Miemie, haka
zai gaji har ya tafi,sai dai tai ta ganin text na ban
hakuri,gobe ma zuciya zai dawo. ***************
*************** Rayuwa irin ta kunci kam sun
ganta a wata hudu da ta gabata. Salma ta
saduda sosai akan Ja'afar,dan har yanzu shi
yana kan bakar shi. Sam in ka ga Salma ta
sauya,ta dawo shiru shiru sosai,kullum zaka
same ta a daki,koh ta dukufa tunani, koh tana
k'allon Miemie tana hawaye. "Salma... Gefe tayi
da sauri da kanta tana goge hawayen jin
maganar Mama akanta. Dole yau ta kawo
karshen matsalar nan. Zama tayi a gefen gadon
tana kare mata kallo. "Rayuwa fa kullum sauyi
take Salma,amma banda taku, ni dai ban ta6a cin
karo da kulafucin D'a namiji irin naki ba, wata
hudu ba kwana hudu bane Salma.. "Lokaci yayi
da za ki cigaba da rayuwarki ki manta da kashin
Ja'afar.. Ki d'auka Rabon Miemie kawai ya had'a
ku,ki manta da rayuwar da,dan ta wuce,ki
fuskanci zahiri a rayuwar gaba Salma.. Fad'a
Mama ke ta mata tana kuka, taya zata mance
Ja'afar?.. Taya zata mance zaman su?..Soyayyar
ta da Ja'afar had'i ne na Allah a ganinta ba wai
wani rabon Miemie ba... In har Ja'afar na bata
haushi bai wuce yadda ya dankara mata saki ba
ba ji ba gani,amma bacin hakan,tabbas bata da
sama da Ja'afar a zuciyarta kawo iyanzu..
"Nasan da kin gama iddar ki sarai... Da sauri ta
k'allo Mama da t'sananin mamaki, kai Maman ta
kad'a mata. "Tunda ki ka zo gidan nan ina
fuskance dake Salma,kin gama iddah tun wata
uku da suka wuce. Kasa tai da kai tana goge
hawaye,tasan Mama gaskiya ta fad'a, dan
shayarwa bai hanata period ba.. "Nasan ma
hakan ne Salma,yanzu abinda nake so dake
shine, "Dole ki fara fita,dan saki ba takaba bace,
bazai yu kiyi ta zama a gida ba kamar matar
kulle,tun yanzu zaki fara fuskantar cigaban
rayuwa,bana son musu koh taurin kai Salma a
zuwan nan daga gunki, dole komai nace kiyi kiyi,
kina jina koh?. Shikenan kuma,ta faru ta kare,wai
an ma mai dami daya sata.. Shikenan ta shiga
sahu,yanzu sai jiran bazawari.. Kuka ta sa mai
sauti,yi take ba kakkautawa,har ta kular da
Mama ta bar lallashi ta hau sababi. Dole kam in
dai ta yadda da K'ADDARA ta maida komai ba
komai bane.. Dole ta daina yaudarar
zuciyarta,tana biya zancen Ja'afar a kullum akan
tashi ce shi kad'ai.. Hannu tasa ta share
hawayenta,kan ta g'yara zama. "Na shirya bin
umarnin ki Mama matukar bai sa6a shari'a ba..
Baki Maman ta washe, "Koh ke fa,yanzu naji
batu,ko ke fa Salma. Kasa tai da kai tana
murmushi, sosai taga farin cikin Mama.
Washegari da dare bayan Abba ya dawo taje
gunshi suna zaune da Mama,yai mamakin
sauyawarta faradd daya,shima sai murmushi
yake mata. "Abba.. Zama ya g'yara da murmushi
ya amsa. "Abba makaranta nake son shiga
dama... Da sauri Mama ta kallota, ji zata kwafsa
musu kuma,wai makaranta? Baki ya washe dan
murna. "Toh Salma,kinyi tunani mai k'yau, Allah
yasa a shiga a sa'a. Kai kasa tace "Amin Abba...
"Anjima ina son zan k'waso akwatina na a gidan
Abban Miemie koh da y'ar makota ne.. Kai ya
kad'a mata "A'a,ki bari zan ma shi Ja'afar din
magana zai kawo miki har gida. Sosai sukai fira
Mama na jinsu bata ce kala ba,tana shiga d'aki
Maman ta bita. "Ya zaki min haka Salma?.. Wace
makaranta kuma ana zaune lafiya?.. Shiru tai sai
da ta gama kan tace ba abinda karatunta zai
tsare mata,tai hakuri tasan zai mantar ta wasu
abubuwan. Ba dan taso ba ta yarda. Ta gama da
Mama, saura Ja'afar. By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:25 AM - Queen Safiyyert馃憫: A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
33_Washegari Abba da kanshi ya samu Jafar din
a shago,duk da yai jim,daga baya ya tuna da
wannan ne damarshi na ganin Salma a yau dan
tuna mata da alkawarin shi. Da yamma k'wa
yasa Garba ya k'waso mata akwatinan ta da
sauran sabbin kayanta marar dinki. Da sallama
ya shigo gidan, ya k'wa taka babbar sa'a Mama
bata nan. T'saye yayi ganin Salman t'saye a
gaban famfo Miemie na mata kukan kunu tana
dauraye murfin feedern. "Sam baki da jimirin
yunwa Miemie,kimin hakuri yanzun zan... Itama
shirun tai dan jin sallamarshi. Da dan rarrafe da
tafiyar da batayi kwari ba ta nufi gun Abban da
murna. Ganin Miemien ne yasa shi dawo da
hankalinshi kanta,sama yai da ita kamar kullum
suna dariya. A hankali ta rufe idonta tanajin
zuciyarta na bugawa da sauri,kusan wata 2
rabonta da ta sashi a idonta,jin takunshi na
kusanto ta yasa ta juya da sauri tare da had'iye
hawayenta. Ya sauya mata,duk ba g'yara, har
wata kasumba ya had'a ta dole ta rashin g'yara
fuska. Da t'sananin murnar ganinta ya karaso sai
washe baki yake,da sauri tai baya ganin abinda
yake shirin yi tai gun taburma ta d'akko,sai ya
bita da kallo baki sake, tabbas Salma batai
kewarshi kamar yadda ya mato a kewarta ba..
Koh irin d'aukin nan na ganinshi t'sawan lokaci
haka bata yi. Dan dukan da Miemie take mishi ne
yasa ya kallo ta,da hannu take nuna mishi kan
feedern dake hannun Salman. Kan taburmar ya
nufa tare da zama,so yake sai ya fassara
yanayin Salman,shi yasa yake ta k'allonta.
Feedern ta mika wa Miemie tana dan satar
kallonshi kan ta kau da kai tace "Ina wuni.. Shiru
yai mata,sai ta dan kalloshi cikin ido,shima ita
yake kallo,bazata iya kallon kwayar idonshi
ba,zata chaza mata matsala,da sauri ta kara
dauke kai tana maimaita gaisuwar. "Mey yasa
kwana biyu ba k'ya d'aukan kira na Salma?.. Ba
k'ya ban amsa koh na miki text?.. Gefe ta kara yi
da kanta tana kallon wani waje, kan tace "Ban
gani ba ne.. Da mamaki yake kallon yadda tai
maganar cikin nuna ko'in kula. "Salma kin daina
so na yanzu koh?.. Yadda yai maganar yasa jin
wani iri da dan tausayinshi,da jihadi ta juyo ido
cike da kwalla. "Ya Ja'afar, ya dace mu fuskanci
zahiri fa yanzu,mu daina yaudarar kan mu dan
komai ya afku..Dole nai aure ka sani,ban maka
alkawarin zama ba aure ba,bazan maka alkawarin
kin kula wani ba.. Yanzu haka karatu zan
koma,ka d'auka rayuwar da ta shud'e a mafarki
muka yi ta, yanzu mun farka... Dole akwai cigaba
a rayuwa.. Kai hakuri, amma bani da alaka da
daukan kiran ka yanzu,ka manta Salma dan
Allah,mu fuskanci rayuwar gaba.. Kai ta kautar
tana goge hawaye, shi kam k'allonta kawai yake
ba koh kiftawa. "Ke nan kina nufin son da nake
miki karya ne?... Soyayyar mu hasashe ce
Salma?.. Zaman mu da rayuwar auren mu wasa
ne?.. Kina nufin Miemie ma mafarki ce?... Da
fusata yake tambayarta,kai kawai take girgiza
mishi tana hawaye. "Ba haka nake nufi ba.. "Toh
mey ki ke nufi?.. Shiru tai tana cigaba da kukan
ta,sai ya kada kai cikin takaici. "Salma kin d'aina
so na kam.. Girgiza mishi kai tai "Ina sonka Ya
Ja'afar, har karshen rayuwata.. Abu daya nake
son ka gane,yanzu komai ya sauya,alakar Mimi
ce kawai ta rike mu... Ka cire son zuciya aciki,
dan bazan iya haramtawa abinda Allah ya
halasta min ba.. "Assalam Alaikum, wannan
akwatunan fa a zau... Tsaye tai ba tare da
karasawa ba, kai kasa ta amsawa Mama
sallama,ciki Maman ta karaso,ya gaida ta kai
kasa,duk shiru sukai ba mai magana, sai muzurai
Mama take ma Salman kan ta shiga daga ciki.
Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga ciki,a hankali ta
sa kanta a kan katifa tana hawaye. Ba dan yaso
ba ya tashi yai fita,tare da shigo mata da
akwatunan ta. Har zauren Mama ta bishi ta sa
sakata tana sababi kan tai gun Salman. "Wai ke
baki da hankali ne Salma?.. Meye had'inki da
wannan da har zai shigo cikin gida ki bashi
taburma, har ki zauna a gabanshi kina wannan
shashancin cin?.. Mey fa rabawa(K'ADDARA) ta
raba ku har abada. Shiru tayi har Maman ta
gama tana ta kok'arin shanye kukanta, ta sani da
koh tayi bayani Mama bazata gane inda ta dosa
ba. "Kiyi hakuri bazan sake ba. Kai ta k'ada tuni
har tai laushi. "Ina kuje miki yaudara irin ta D'a
namiji ne Salma,gaba in kina mishi haka sai ai
abin kunya. Shiru tai tanajin wa'azin Maman
kawai. G'yale ne kusan kala 5 had'add'u,tana
washe baki ta fito dasu daga leda. "Ki zabi na
za6a ki darje,dan zawarcin ki sai yafi y'an
matanci a komai Salma, gobe kayan k'walliya
zasu zo dan na bawa Hajiya Jidda kud'in kayan
g'yaran jiki,ga wata yayi nisa da komai kin samu
akan lokaci.. InshaAllah sai mun cike gurbin da
muka rasa.. Ni da zakiji shawarata ma da an
yaye Miemie a satin nan a mikata ga gidan su
chan ya karata... Da sauri ta dago tana kallon
Mama, Kat'seta tai da fadin "Eh man,bashi yake
ikirarin yana kawo shi ba?.. Toh zamu mayar
mishi da abarshi kawai. Kai ta hau girgiza ma
Maman,Allah yaga ba mai rabata da Miemie sai
aure. "Mama Miemie fa karama ce,kawai tai
saurin tashi ne,koh fa wata tara bata cika ba..
Dan Allah kiyi hakuri,dan ba abinda zata t'sare
min koh a makaranta. Harara ta aika mata, "Kina
nufin da ita zakina fita?.. Kallonta take ta rasa
amsar ba Maman. "Toh da sake wallahi, ba
yadda za ai ina tufka kina bin bayana da
warwara.. Zawarci da goyo?.. Toh da sake,dan
ba mai gani ya kulaki alhalin kina sa6e da y'a.
"Aikina fitarshi ta naga dama ce,in ma kince
baza'a mayarta ba ni zan na miki renon,aje a
dawo lafiya. Shiru tai tana jinta kawai. Washegari
sai ga kayan k'walliya jibgi,su mascara, eye
shadows,su sabulun g'yaran fata harda su man
gashi,ga haddun man gyaran jiki,lalle Mama da
gaske take. Shi kam tunda ya koma da yazo
k'wanciya yake tuna dazu,lalle in Salma tasan
wata toh bata san wata ba. Tazo k'wanciya taji
karan wayanta,agogo ta duba, tasan ba mai mata
haka sai mutum daya. Badan taso ba ta d'auka,
sai dan jin dame yazo. "Naji kije makarantar,
amma bisa sharad'i uku.. Baki ta bud'e cike da
mamaki,wai koh ya manta bata karkashin ikon
shi ne yanzun? Dan dai taji sharad'in tace tana ji.
"Good. "Na daya kafarki toh kafar Miemie duk
inda zaki shiga. "Na biyu ba zancen yaye sai
Miemie ta cika shekara biyu kamin kiyi komai.
"Na uku,fitar ki sai da nikaf da hijab,sannan ni
zan sama miki mai kai ki a Napep ya d'akko ki in
kin gama, dan ba ko wanne kato zai na d.. "Ka
ga malam,ka bari ka fad'awa Miemie wannan
dokar taka ba wai ni da nake Salma ba... Dan ba
y'ar ka bace ni,ni nake da damar t'sara rayuwata
yanzu ba kai ba. "Abu daya nasan na yarda zan
iya shi,shima dan hakkin ka ne dole,shine yaye
Miemie,zanyi yadda kace, sauran kuwa ba
huruminka bane... Wayar yabi da kallo baki sake
jin ta kashe kit.. Lalle Salma ba ta so zaman
lafiya ba a garin nan, amma zata jidi mamakin
shi. Dan shi tai mishi daidai ma da zata tafi
makaranta. Tun daga ranar ya daina kiranta a
ganinshi zata damu ta bashi hakuri ayi yadda
yaso,sai dai ta daure ita. Ana haka ranar Abba
yace ya batun makarantar da yace zai koma?..
Kanshi t'saye yace ya ma Abban ai ya fasa. Nan
ya bud'e mishi wuta kan bai isa ba,duk haukar da
yake ranar ya samu labari gun Mama,dan har
gida tace ai mishi t'sakani da Salma,sai dai yazo
za'a bashi Miemie in dan ita ne. Sosai yaji
haushi,yasan aikin Salma ne..shi yasa ya d'auke
mata wuta,sai dai ya tura k'annenshi su dakko
mishi Mimi
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 4
Feenat Ja'afar Novel's
Su Salma an samu gurbi a school of hygiene,da
shawarar baba ta cike ba Polly ba. Ranar da ta
fara fita da personal zata kai takaddun ta. Ba
yadda zaka ga Salma ka gane itace da lokacin
tana budurwa, yanzu Salma ta daban ce,ta gaban
goshin Mama, dan ta dage dole sai tayi kara'i da
zawarci. Kwanar su Ja'afar ta shawo,tasan
yanzu haka yana makaranta dan sha d'aya na
safe. Sosai tai k'yau cikin doguwar riga ruwan
kwai mai duwatsu,da g'yale karami ta nad'a
fari,ta ritaya jaka karama mai (chain),ba wata
k'walliya tayi ba ta azo aga,dan wannan ma
Mama na t'saye tayi ta,ta kuma rantse ita da
hijabi sai a sallah. Zai wuya kace ta ta6a aure
har da rabon Miemie, dan yanzu ne take
shekarunta na (22) a duniya. Kanta kasa take
tafiyarta cikin nut'suwa, sai dai ji take duk ta
tsargu,tamkar Ja'afar na kofar gida yana
kallonta. Dak'yar ta kai kanta bakin kwalta tana
sauke numfashi, ashe feeling take... "Kin k'yauta
Salma kenan?... A razane ta juyo jin mai
maganar.. Rai had'e yake kallonta tamkar bai
ta6a dariya ba. Duk da ta tsorata da ganin
yanayin da yake amma ta cije itama ta ci kunu.
"Da nai mey fa? Rai 6ace yace "Ina Miemie?..
Kai ta k'autar gefe,kan tace "Gida".. A fad'a
fad'a yace "Wato bakiji abinda nace ba koh?..
Kalli shigar ki,kamar wacce zata party,sam baza
mu shirya dake ba in.. "Tafiya ne?.. Wani mai
keke napep ya tambaya, kallo irin na baka isa ba
tamai, kamin tace ma mey keken "Eh tafiya ne.
Tana kokarin shiga tace "ba ruwanka da shiga
ta,cos I know what i'm doing.. And ni ba y'arka
bace, na fad'a ma ka rabu dani. Sam taki k'allon
fuskarshi bare ta sare gun taka mishi burki. Baki
sake yake binta da k'allo har mai napep yaja
kamin ya samu k'warin ya tanka. By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 9:28 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/7, 11:03 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
34_Jingina tai a jikin Napep din tana sauke ajiyar
zuciya.
"Kai hakuri Ya Ja'afar, ya zama dole na koya ma
nisa dani,kai hakuri,ina sonka wallahi..
"Hajiya magana ne?..
Kai ta dago jin mai Napep na tambaya, ashe
maganarta ta fito fili.
Ta gama komai Monday zata fara zuwa,kwarai
taso ta yaye Miemie sai dai ba hali,dole tabi
yadda uban y'ar ya t'sara.
Shikam Ja'afar tun daga wannan ranar kullum
zata makaranta sai yai mata maganar wani
abu,koh yace k'walliya tayi yawa, koh yace
uniform ya d'ame ta.
Wani sa'in har ta wuce tana dariyar zariya irin ta
Ja'afar, tabbas gani take ya zare.
Shima kamar yadda Abba yace haka dole ya fara
_processing_ dan tafiya masters a B.U.K,sai dai
fur Abba yace garin zai bari,a Zaria zai yi,kar ya
damu an ma kusa shirya masa komai ba koh
kwandalar sa.
Tamkar ya aza hannu aka ya kwala ihu yake ji
ranar,yana nan ma ya ya k'are da Salma bare ya
mata nisa?..
Tafe suke ita da wata y'ar makarantar su da
tazo zata rakata bakin kwalta, ta gama shirinta
kenan zata gidan Aunty A'i sai fasawa tayi.
Tai kyau,fatar sai shining take taji mai da
sabulun Mama.
"Allah ba wanda zai ce kin haifi Miemie sis
Salma,kin ganki kuwa?..
Murmushi tai ma kawar tata lokacin da take
t'sayar mata da Napep.
"Haka dai kuke cewa kullum.. Murmushi tai mata
sukai sallama.
Tana kula da wani mai mota yana ta kallonta ya
t'saya siyan Apple.
Kokarin tsallakawa yake ganin zata wuce da
sauri,kai ta kada dan sarai tasan yau ma za'a
tafka dirama irinta ranar chan da Ja'afar, dan
tana kallon yadda yake maka mata harara a kofar
gidan su suna zaune shi da Garba da wani,tasan
darajar kawarta taci da yanzu ya taso bambami
dan tasa g'yale a kafad'a, kai ta girgiza dan
yanzu abin dariya yake bata ma...
"Assalam Alaikum.. Waiga wa tayi jin an mata
sallama.
Da dan sakin fuska ta amsa tana mai cigaba da
tafiya a nut'se.
"Gunki nazo fa y'an mata dan Allah.
Kai ta daga aikwa idon Ja'afar kyar kanta.
Da murmushi ta juya badan taso ba sai dan
yakice dan gudanta, duk da tasan baza a wanye
lafiya ba.
Tuni dad'i ya kama saurayin dan da har ya fara
d'ari-d'arin mata magana,sai ya ga kamar matar
manya ce.
"In bazaki damu ba dan Allah ki ban numbern
ki,wannan ne gani na biyu da na miki a layin nan
yanzu ina sauri zan kira ki...
Ta gefen ido ta sato k'allon Ja'afar ai kwa a
suk'wane yake zuwa gun nasu.
Da sauri ta karbi wayar mutumin da zummar sa
mishi ya iso.
Su dai su Garba ido ne nasu,dan abin Ja'afar ya
daina bashi dariya yanzu tsoro yake bashi.
"Bashi wayarshi ya kauce tun kan na
dagargazata a gun nan..
Banza tai dashi tana cigaba da latsa wayar
karya,bata aune ba taji ya warce da karfi.
"Karbi wayarka ka bar layin nan Malam, koh kaga
tayi sa'ar tsayuwar ka?..
Baki sake saurayi yake kallonshi,shi a tunanin shi
koh yayanta ne ma,dan shima haka yake ma
samarin k'annenshi baraza,dan haka bakin shi
alaikum ya kar6a yana kallon Salman.
Cike da tsiwa ta kallo Ja'afar din,
"Malam wai ina ruwanka da samari na ne
eyeee?..
"Kimin shiru tukunna, kema zan dawo kanki ne ai.
Da hannu ya nuna ma saurayin hanya halamar ya
ware,ba daban yaga Ja'afar din ba na wasa bane
ba da ba yadda za ai ya bar wannan
sankaceciyar budurwar.
Da sauri ganin zai tafi tace "Malam ina zaka
ne?.. Kai ya kad'a mata yana murmushi kan ya
kara gaba.
A fusace ta nuno shi da hannunta
"Wallahi Ya Ja'afar na gaji da wannan abin fa,dan
wallahi na kusa kai karar ka gun Abba ya mana
t'sakani,mey ruwanka dani wai?...
Shiru tai tare da matsawa da sauri ganin ya mika
hannu bayan gyalen ta.
"Wai kai lafiya ka ke?.. Harara ya sau mata kan
yace
"Tun muna sheda juna ki daina sarar nan ta
sauke g'yale a kafad'a Allah...
"Bazan daina ba din, na fad'a ma bani ba kai,
tunda kai har yanzu bakasan Annabi ya faku ba...
Shiru tai ganin Garba.
"Haba Salma,haba,a titi fa ku ke?.. Tunda kinsan
halin kayanki sai ki gaba ki barshi ya karata, dan
Allah ki daina biye mishi.
Harara ya sakar ma Garban, "ina ruwan ka toh
kai ma,kowa dai yasan da matata nake t'saye ba
kowa ba..
"Mtsww... T'saki taja rai 6ace, duk suka kallota..
"Wallahi you are sick..
"Ni matarka ce, amma fa a da, kai istigfari ma
tun wuri,dan wallahi za kayi sa6o...
"Kimin shiru fa Malama..dan kwanciyar hankalinki
wallahi kibi abinda na ce kiyi,period..
Shiru tai tana kallonshi,karfin hali sai gun
Jafar,tabbas sai tayi da gasken gaske,dan
abinshi gaba yske,shima Garban k'allonshin
yake,abu dai kamar wasa yake gani yanzu zai
zama babba.
By
Feenat Ja'afar.
[8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
35_Drama sosai sukai kan ta wuce gida rai 6ace
duk rai a dagule, dabarar ta ta kare kuma a akan
Ja'afar, duk hanyar da zai zuciya ya daina kulata
tabi ba nasara,tamkar ma zigi take mishi.
"Mtsww... Taja t'saki,Tabbas so so ne,amma na
Ja'afar son kai ne,dan shi yaja komai..
"Ke kuma ke da wa kike t'saki haka?..
Ba tare da ta dago ba tace "Ja'afar man.. Ya
hanani sakat a unguwar n...
Da sauri ta datse harshenta dan jin Mama fa ke
tambaya,
"Au har yau yana nan yana bibiyar taki koh?...
Kai ta girgiza da sauri, zarar bunu..
"A'a, ni nasan hanyar maganinshi,ki ban nan da
gobe.
Da sauri tace
"A'a Mama ba komai bane fa,kiyi hakuri zai
daina... Shiru tai ganin harar da take aiko mata.
Tun daga ranar Mama ta zama y'ar rakiyar
Salma hanya,sai ta tabbatar ta hau abin hawa
zuwa makaranta zata juyo tana aika mishi
harara,da tai na sati sai ya bar tare hanya kuma
ya dawo waya.
Ana haka shima admission nashi ya fito
shima,tuni ya shiga kunci,dan yasan ya kusa yin
nisa da Salma,hakan yana nufin komai zai iya
faruwa.
Ranar da yamma ana washegarin zai tafi yazo
mata sallama duk da sunyi fad'a.
Taimakonshi daya Mama bata nan ranar ma,dan
yana ga ita kad'ai zata iya tsaida shi a yima
Salma kashedi.
Shigarshi zauren kenan sukai kicibis zata
fito,harara ya sakar mata kan yaja ya t'saya.
Fita take shirin yi ya ruko gyalenta da sauri har
yana zamewa,don haka a fusace ta juyo da niyar
balbaleshi ya marairaice mata fuska.
"Saken g'yale toh.. Murmushi yake yaki saka, ''ka
saken gyale koh na fuce... Da sauri ya cika yana
tare kofar fitar.
"Maganar fahimta nake so muyi dake,dan Allah ki
t'saya..
Hannu ta hard'e a kirji ta k'alleshi,itama zata so
su fahimci juna.
"Ina wuni toh,tunda har gaisuwa kin soke dani.
Da kalar tausayi ya kara yana sukui da kai har
taso yin dariya kamin ta gaishe shi.
"Ina Miemie?.
"Da Mama suka fita,kayi kai maganarka kan su
dawo fa.
Tsayuwa ya gyara tukun ya kira sunanta, rai sake
ta amsa,fatan ta yasa zancen azziki zai mata ba
wai shirme ba.
"Salma".. A karo na biyu ya kara kiranta, bai jira
amsarta ba ya cigaba,
"Gobe zanje Zaria kan batun makaranta da zan
fara, kima Allah Salma ki yi kamar ina nan dan
Allah,banda kula tsagerun samarin nan wanda
har yau basu mallaki hankalin kansu ba dan
Allah.
"In ma aure naso kiyi ina ga ni ya dace na baki
mijin aura,bare a agendar mu bamuyi haka dake
ba...
T'sam tai tana kallonshi da halamun ya zare tana
murmushi, amma zata bishi a haka a wanye
lafiya.
"Toh naji,zan kuma kiyaye,happy?..
Kai ya kad'a da murmushi, "yauwa koh ke fa,dan
Allah Salma ki riken alkawari nan..
Kai ta kad'a tana taji ai.. Da haka suka rabu ya
bata kayan zakin Miemie, murna fal ranshi suka
rabu ranar.
K'warai ta samu sakewa sosai bayan tafiyar
shi,tuni ta kara bud'e shafin zawarci sabo,duk da
kasan ranta tausayinshi take ji sosai.
A wata daya tai samari biyu irin son Mama, barin
Alhaji Usman Dan chanji.
Kud'i sosai yake kar mata kamar ba gobe,
albarka kwa kullum samunta take gun
Mama,yace shi ba yaro bane,dan haka yana so ai
auren cikin k'ank'anin lokaci.
Ya sanar mata yana da mata daya da yara biyu
kachal,aurenshi uku,sun rabu da biyu sai Hajiya
ta k'arfen.
Tunda suka rabu tazo gida tana tuna abu uku,
tabbas a yanzu bata da ra'ayin auren mey
mata,dan taga aya akan Bintu.
Sannan bata son mutum mai irin kud'in Alhaji
Usman sam a rayuwarta.
Gwara ma Kamal dan shi matashi ne kamar su
Ja'afar, kuma yafi kwanta mata a rai,gashi da
saukin hali da saukin kud'i.
"Oh ni y'an nan,ashe arziki ke binki Salma a
rayuwa?..
K'allon Maman take yadda take daga abubuwan
da Alhaji ya bata,ita dey nata ido.
"Bana jin koh lokacin y'an matancinku kun ta6a
had'uwa da irin wannan, babbar harka ai tayi y'an
nan...
"Mama ni fa mutumin nan bai kwanta min ba
sam Allah,gashi har ya fara maganar aure tun
yanzu,ga yana da mata fa,ga ni sam irin kud'in
nan baya...
Baki sake Mama ke k'allonta,tuni ta tsayarta
cikin fad'a.
"Rufe baki ni sauraniyar y'an iya t'sari, ashe har
yau kina nan da halin nan Salma? Arziki na binki
kina zura da gudu?..
"Ina ruwanki da matarshi?.. Koh a kanta zaki
zauna?..
Kai ta girgiza zatai magana ta dakatar ta.
"Koh dai Salma hudubar yaron chan tai tasiri
akanki?..
Kai ta kad'a,
"Allah Mama ba haka bane,ni ina tsoron kishiya
ne,kinaji fa wai aurenshi uku suna rabuwa sai ita
ke zama...
"Sai mey toh?.. Kar ki bada mata mana Salma?..
Baki sake take k'allon Maman,kamar ba ita ke
fad'in ba mai zama da kishiya ba a yaranta tunda
itama bata zauna ba,wace daga ce ba'aci ba
lokacin auren Bintu da Ja'afar amma yanzu kud'i
ya warware Mama?... Kat'seta tai,
"Saboda haka komai yace ki ce toh, in ma ita ke
fidda su toh ke zama daram,dan wannan ba
gidan fita bane in an shiga...
Hawaye ke zubar mata yayin da tazo k'wanciya
tana tariyo zancen Mama, dole in dai tana son
faranta mata wai ta ba wa Alhaji dama.
Waya ta d'auka jin shigowar text message,tasan
na Ja'afar ne.
_"Salmatee,remember, a heart dat truly loves
never loses hope..but always believes in d
promise of love,no matter how long d time and
how far d distance,at d right time,love will fine a
way".._ ki rike alkawarin ki,love you..
*Ja'afar*
Kukanta ne ya karu sosai bayan ta gama
karantawa, tabbas in ta cigaba da sauraran
kalaman Ja'afar zasu sa ta karaya har ya ci
galaba akanta..
"Bani da kamar ka har kullum Ya Ja'afar, sonka
gareni ba mai misaltuwa bane,amma kai kaja
mana koma meye...
Fuska ta goge sakamakon jin tahowar Mama da
Miemie na kuka.
Washegari kanta t'saye ta bawa Alhaji damar ya
turo magabatanshi kawai koh ta huta da
dawainiya da son Ja'afar.
Sabon sim ta siya tasa a sabon wayar Alhaji da
ya bata,a haka suka raka wata kusan biyu, duk
da tai kewar text da kiran Ja'afar din.
Shikam yana chan hankali tashe na rashin samun
wayar Salma, ga Abba ya sanarshi kar ya sake
ya dawo sai an nemeshi a makaranta,
Duk da an sanarshi ana kawo Miemie gidansu ta
yini.
A jikinshi yaji abu na faruwa,duk sai yaji bai da
nut'suwa sai ya je gida dan tabbatar da
zarginshi.
***
Tunda daga d'anno kanshi layin su Salman ya ja
ya t'saya. T'saye take da dan murmushi a
fuskarta, sanye cikin favorite dinshi riga da skirt
na atamfa purple, tai kyau matuka gyalen nan a
kafada,daga inda yake zai iya gano bakin
gashinta a tufke ta chan kasan dankwalinta,
tasha ado tamkar zata party.
Wani abu ne yazo dai dai makogwaronshi ya
tsaya,kishi...
Bai san ya isa gun ba sai da yaji ana "lafiya?..
Kallo shi yayi, duk sai yaji yau baida ma k'warin
g'wiwar fad'a,Salman ya kalla,da sauri ta kawar
da fuskarta gefe ta had'e rai.
Sai ya dawo kan Alhajin,tsaf sai ya haifi
Salma,sai t'sabar kud'i da jindadi da suka 6oye
shekarunshi.
Kallonshi yake tun daga sama har zuwa kafa, so
yake ya gano ta inda ya fishi har Salma ke mishi
murmushi haka. A zuciya yace
"Babu... Sai dai kud'i kawai da sa kaya masu
t'sada.
"Kai fa,daga ina ba koh sallama?..
Cike da haushi ya kallota, "baki sanarshi ko ni
waye ba ne?.. Kan Alhaji ya dawo,ba shakku
yace "matata ce ita,zaifi mana k'yau in ka daina
zuwa gunta Alhaji.
Murmushi yayi Alhajin,kan ya kallo Salman, "sai
kinji ni kawai.. A takaice ya k'alli Ja'afar din,ba
sai an fada mishi waye ba,halamu ya nuna
tsohon mijinta ne,har zaga wa tai ta rufe mishi
tana daga mishi hannu d'auke da murmushi, har
ya kule tana daga mishi hannu kan ta d'au
kayanta koh ta kanshi bata tai hanyar gida,da
zafin nama.
"Wato abinda ki ke kenan tun bayan tafiya ta
shine yasa ki ka kashe waya? Salma mey yasa
kike son ki 6ata min rai wai?.. Jibi fa shigar ki,ji
gashi a waje,wace iriyar rayuwa ki ka za6a
mana?
Cike da fada tace
"Wace iriyar ka za6arwa kanka dai Ja'afar.. Ya
zaka zo kana fad'an wata iriyar magana mijin da
zan aura?.. Karan nan bazan dau abinnan naka
ba wallahi, aure zamuyi dashi nan da wata biyu...
Sai kayi abinda zaka yi.
By
Feenat Ja'afar.
[8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
36_Kan yai k'wak'waran mot'si ta shiga gida tare
taru kofa harda sa sakata.
Jiginna tai hawaye na neman zubo mata,daga
yar bular dake jikin kofar ta leka waje,kofar gidan
yake kallo jiki a sanyaye kamar yasa kuka,juyawa
tayi hawayen dake makale mata ya zubo,dak'yar
ta seta kanta ta shiga ciki rai cike da tausayin
Ja'afar.
Kusan kullum zai zo ba zuciya dan bata baki
akan Alhaji tana mishi wulakanci,shi kam Alhajin
har dariya yake bashi wani sa'in, dan baijin da
abinda zai iya rabashi da Salma a dai dai lokacin
nan,sai dai jin saki uku ne kawai sai ya bar jin
komai,iyaka ma yai ta tusa ma Ja'afar din bakin
ciki in ya gansu da kalamai ma Salman.
Biki ya karato ga makaranta,amma haka duk
week end daga Zaria zai zo kan batun Salma ta
janye zancen bikin nan.
Duk ya fita a hayyacinshi duk akan auren Salma.
Da halamu ya fara hankalin daina zuwa gun
Alhajin,sai dai in yazo ya tsaya chan gefe sai
tazo shiga ya tare ta da magiya.
Yau saura k'wana biyu biki, sai gashi shi da
Garba,dawowarsu daga gidan g'yaran jiki kenan
ita da Ummi.
Turus ta ja ta t'saya ganin Ummi ta wuce ita ya
tare mata hanya.
"Ka ga yau bani da lokacin jin wannan
mahaukatan zantukan naka,jibi iyanzu na d'aura
aure, ya kamata kasan inda dare ya maka,
sabuwar rayuwa zan fara,saboda haka kai yanzu
ya rage ma,danni yanzu baka gabana...
Kai ya kad'a mata,
"Karan nan bazan hanaki aure ba Salma,sai dai
ba da Alhaji ba.
Baki sake take kallonshi, Garba ya nuna,
"Garba zaki aura Salma,kimin wannan alfarmar.
Kai ta dauke daga kallonshi ta k'alli Garban
wanda shima ya cika da al'ajabin kan maganar
Ja'afar.
Sai ta girgiza kai da murmushin takaici.
"Tanan kuma ka bullo min?.. Auren kisan wuta
Ja'afar? Lalle kayi nisa ba zakaji kira ba.
Bayab hannunta tasa tana goge hawayen idonta.
"Wai ka zata ni din auren kisan wuta zanyi da
wanda zan aura?.. Kai ta kara kadawa,
"Kai kuskure toh,dan ni aure zanyi na tsakani da
Allah,ba wai nayi na fito ba Ja'afar..
"A'a Salma,ba haka ne nufi na ba.. Da muryar
kuka ta tareshi,
"Hakane man,haka kake nufi,wato ka kawo min
abokin ka na aura bayan wani lokaci ya sake ni
sai ka halartawa kanka ni koh?..
Baki sake duk suke k'allonta,ganin yadda hawaye
ke zubar mata.
"Jahilcina bai kai nan ba Ja'afar, a bazan ta6a
abinda ka ke so ba, a gareni yanzu k'allon Yaya
nake ma,da kuma uban yarinyar dana haifa,
bayan haka.. Kai ta girgiza, kan tace "you mean
nothing to me a yanzu kam..
Jin baice komai ba yasa taci gaba.
"Banzaci haka daga gare ka ba Garba,a ganina in
shi ya 6ata kai mey dawo dashi kan hanya ne,
wallahi auren t'sakani da Allah zanyi, ku sani
kuma auren so zanyi,wanda nake fatan mutu ka
raba ne,dan Allah,dan kaunar ka da Allah ka bar
bibiyata,dan Allah..
Shiru tai dan ganin shima idonshi ya taru da
hawaye,da sauri ta shige gida tana goge
hawaye..
Har ta shige yana binta da ido ba magana, sai
hawayen da ya zubo mishi shar, da sauri yasa
hannu ya share.
Kafad'arshi Garba ya dafa, "kaji zancenta, tai
mana fassara baibai,ya kamata kai hakuri ka bar
kulata in har kana wa Allahn data had'a ka dashi.
Kai ya daga, "InshaAllah..
~~~~
Taro ne iya taro,taron shedar auren Salma da
Alhaji Usman, daga inda yake t'saye a chan nesa
da kofar gidan yana k'allon komai har aka shafa.
Juyawa yai da jaka biyu hannunshi tare da sanya
bakin glass dan 6oye sirrin dake idonshi.
Yasan yanzu kam Salma ta mishi nisa.
"Mama taki ta bud'e dakin fa,daga ina jiyo sautin
kukanta Allah.
Ta window Ummi ta leka,gata k'wance ta tasa
tsohuwar wayarta a akan fuska tana razgar kuka,
So ba karya bane Salma.
By
Feenat Ja'afar.
[8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
37_Har aka kai amarya gidanta bata bar kuka
ba,dayawa sun zata kukan na Mama ta cire
Miemie ne, dan basa ji koh auren farkonta tayi
haka.
Kowa ya wat'se sai ita kad'ai, ko'ina take kallo a
dirare, gida ne iya gida,tun bata fita ba ta
zaga,yau gata a gidan da ba Ja'afar, ba kuma
Miemie,tuni ido ya cika da kwallar tuna baya.
Anya tai ma Ja'afar adalci kuwa?.. Anya bata ci
amanar so ba kuwa?.. Ta sani da takai Ja'afar
bango,hakan yasa bai kara waiwayarta ba,ta
yuwu yai zuciya... Ido ta goge da sauri jin motsin
za'a bud'e d'akin.
Ango ne yasha babbar bunjima da rike da leda,
bakin nan har kusan kunne,jan mayafinta ta kara
yi ta rufe fuska.
"Amarya! Amarya!!.. Ba k'ya laifi wai koh kin
kashe dan maigida koh?..
Murmushi ta k'akalo mishi, zama yayi a gefenta
tare da ajiye ledar a gefen bedside, bata aune ba
taji ya yaye mata g'yale yana kallon fuskarta.
Alwala yace ta d'auro suyi nafila,dan wai
agareshi babbar kyauta ce ita daga Rabba.
Sun gabatar da duk wani al'ada,sai dai har ango
ya d'ane gado amarya tana t'saye a gaban
madubi
sai sininiki take,gabanta sai mugun fad'uwa yake
tamkar wacce tai auren fari.
Murmushi yayi da kanshi ya taso ya karaso har
gaban madubin tare da kamo hannunta.
"Muje ki kwanta haka dare nayi sosai..
Kamar yarinya ya kwantar ta gefen shi yana kallo
da murmushi.
Salon ya sauya,tuni ta fara digar da hawaye,shi
kadai yake kid'anshi yana rawarshi,sai dan sautin
kukanta dake fita kad'an-kadan,wanda a gareshi
tamkar zigi take mishi.
Kai ta juya ta kallo Alhajin dake bacci
hankalinshi k'wance,abu uku sun hanata bacci,na
farko kukan zamanta ta wani ba Ja'afar ba,na
biyu tunawa da Miemie, na uku minsharin Alhaji..
Har gari ya waye bacci sai jefi-jefi-jefi ke
dibanta,sam taki jinin minshari kusa da ita,tsaf
yake hanata bacci.
Shikam da farin ciki ya tashi irin na sabbin
ango,ita kam da ido kawai take binshi.
Tara sai ga yaron uwargida ya kawo abinci,da
fara'a ya gaida ta,kanshi ta shafo kan tace ya
sunan shi?
"Sunana Ja'afar".... Kallonshi take da mamakin
jin sunanshi, koh dai bataji dakyau bane?...
Kat'seta yai da fad'in
"K'anwata kuma Nabila,Umman mu tace sai
anjima zamu shigo kar mu tashe ki a bacci.
Murmushi tai mishi yace ya tafi.. "Ja'afar...
Ido ta rint'se jin maigidan ya kira sunan,ba shiri
ta d'au abincin tai kitchen.
Bayan sun gama komai yace suje bangaren uwar
gida zai magana dasu.
Batai zatan da kishiyoyi masu kaunar kishiyar su
ta ra6e su sama da matar Alhaji ba,sosai tai
mata bazata,tun tana d'ari-d'ari har ta saki jiki da
ita da yaranta, musamman Ja'afar..
Yau Miemie ce tazo mata,sai murna take taga
Auntyn ta.
Duk babyn ta rame,yaye bai amsheta ba.
''Miemie, ga nan Abdul yazo ku tafi gun Mama
koh?...
Kafad'a ta make halamar taki tana neman kuka,
"Yi hakuri gobe zanje gida mu taho koh?..
Kuka ta saka mata baji ba gani, sai mak'e
kafad'a take tana ita "um-um.
Sai ta sallami Abdullahi kan gobe yazo ya d'auke
ta, har ya jima da tafiya Miemie bata bar kuka
ba.
Sai um-um kawai take fad'i, suna haka Alhaji ya
shigo,duk yai kicin-kicin da fuska, cikin fad'a-
fad'a yace ta lallasheta man,shi baison hayaniya
bare ta yaro...
Baki sake take kallonshi,kaya ya ajiye ya juya ya
fice harda dan tsakinshi,toh mey yake nufi?...
Y'arta ta d'auka ta sa6a a baya sukai kitchen
tana fad'in tai shiru ba inda zata toh,kan aje
ko'ina sai ga nan Miemie harda dariya tana bata
labarin Mama cikin gwaranci.
Har dare ba Alhaji ba duriyarshi,abinci ma sai
Ja'afar ya turo ya d'auka.
Suna k'wance Miemie sai k'allonta take,gani take
kamar guduwa zata yi ta barta.
Kanta ta shafo tana mata murmushi,
"Yi baccinki my Miemie, ina nan fa tare da ke
kinji?.
Kai ta daga mata tana k'allonta.
"Antee...
Kai ta dago kan tace
"Na'am Miemie nah...
"Abba...
Tsam tai tana k'allon Miemien,Abba? Ta nanata a
ranta.
Murmushin dole ta k'akalo tana fad'in Abba yana
nan Miemie,bata aune ba taji ta kara fad'in
Abba...
Hawayen da take makalewa ne suka zubo
mata,da halama yanzu Miemie ce matsalar
ta,dan zata dawo mata da hannun agogo baya.
Da dabara ta d'auke hankalinta daga tunanin
Abban ta hau lalla6ata har tai bacci.
Photocopyn Ja'afar ce Miemie,barin yanzu data
kara girma, tunani take koh dai Ja'afar har yanzu
baya zuwa gida, laifinta ya shafi Miemie?
Dan tasan sai Miemie ta kwana biyu bata ganshi
ba take nemanshi haka.
Tana nan har maigidan ya shigo,sai wani k'allo
yake aikama Miemie wanda ta kasa fassara shi.
Tun daga ranar ya zamana in dai Miemie zata
zo,toh fa zata rasa gane kan maigidan, ta rasa
dalili, musamman in tai la'akari da hadithn
hausawa na Duk mai son uwa toh yaso d'iyanta.
Ranar har ta kasa d'aurewa tai mishi magana,
amsar da ya bata ta jima tana sata hawaye.
Ga Miemie da kulafuci bare tace kar a sake kawo
ta,asalima duk randa tazo fara'arta karuwa take.
Sa6anin in tazo mata,data gane sai take d'akko
ta duk randa bata da girki su k'wana, ranar da
maigidan yake da ita su wuni ai rabuwar kuka
har uwar.
Allah yaga Miemie kadai take gani taji sanyi a
ranta.
Ranar suna fira a bangaren uwar gida take mata
korafi kan halin maigidan akan Miemie.
Murmushi tayi kamin tace
"Sai kinyi hakuri da halin Alhaji Salma,ba tone-
tone ba,a'a kawai dai ya kamata ki sani, Alhaji
sam baya son yara,musamman hayaniyar
su,hakan yasa ya d'aurawa kansa kin haihuwar
k'arfi da yaji, nayi ta zaman takaicin halin nan na
Alhaji har t'sawan shekara bakwai,a lokacin aka
tada kayar baya kan sai ya kara aure tunda ni
sun zuba ido shiru.
"Hanna ta shigo itama ta shekara biyu shiru, ni
dai nasan kusan kullum yakan tasa ni da Hanna
dan shan maganin daukan ciki.
Ana nan ranar wata kawar Hanna tazo suna
jajanta ko dai matsalar gun mijin ce,toh a ranar
dai asirin Alhaji ya tonu,dan kawar Hanna taga
magani tace na hana d'aukar ciki ne.
"Ranar muka mishi tawaye har Hanna,in takaice
miki yace shi bai shirya haihuwa ba yanzun,anan
sukai baram-baram da Hanna ya bata takardar
ta.
"Haka sauran mata biyun kowa tazo zai fad'a
mata ra'ayinshi, da taga bazata iya ba zata fice,
duk kuwa da tarin arzikin shi,a lokacin muna da
shekara kusan sha uku da aure,koh mai zaiyi na
daina shan magani, hakurina ya kare,nan na kai
kara gun Hajiyarshi.
"Ya saduda muka haifi Ja'afar, yace daga nan ta
isa haka,wai incigaba shan magani,a gabanshi
zanyi kamar nasha, daya kauce zan zubar.
Koh shekara Ja'afar bai ba na samu cikin
Nabila,cikin da a kullum sai naga tasku gun
Alhaji,gar da gar zai nuna bai kaunar su,barin in
Ja'afar na kuka,haka nai ta hakuri har na haifi
Nabila.
"Yanzu kam magani sai dai shi yai tasha,amma
banda ni,kinga Nabila har ta shiga shekara ta
biyar.
Tsam tai tana tunani bayan kammala bata labarin
waye Alhaji, ita ba kullen ne yafi damunta ba
sama da rashin son haihuwa..
A kalla yanzu ta doshi wata na biyar a gidan nan
amma ba bayani,sam bata kawo wani abin
ba,ashe wannan ne dalili?..
Bazata iya tuna ranar fitarta ta karshe a gidan
nan ba,tun kwa bayan aure sau daya taje gida sai
dai aukin waya koh azo mata, lalle duniya labari.
"Zaman hakuri kawai zamuyi Salma,sai adu'ar
shirya in da rabon zai gane, amma shawarata
gareki ki rike y'arki, dan kar kiyi sakiyar da babu
ruwa tun kina yarinyar ki dake,shi ba ruwanshi.
Kai ta kad'a mata,Allah sarki Ja'afar, ta tuno
lokacin data fara period tana kukan samun ciki
yana murna.
Ta tuno da abinda yace mata
"Allah sa Miemie ta samu k'ani a kusan nan...
Ta tuna data hau bori ya hau lallashinta,
harda alkawarin shi zai mata reno in bata shirya
ba...
"Ba kuka zakiyi ba Salma,muyi ta adu'a.
Hannu takai fuskarta, ashe kuka take bata sani
ba.
By
Feenat Ja'afar.
[8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
38_Ranar sakwa-sakwa ta yini tana tuna halin
Alhaji, bai da mugun hali koh daya sai na bakin
kulle da kin yara,bayan nan baza tace ga mugun
halinshi ba.
Zataso sanin wane hali Ja'afar yake ciki a
yanzu,dan tabbas tasan ya zuciya da ita,tunda
gashi ance koh wajen Miemie baya zuwa sai
aike?..
"Mey nai kenan?.. Mey nayi ni Salma?.. Mey yasa
ban iya jure zama ba aure ba a rayuwa kamar
yadda yaso muyi..mey yasa?..
Juyi tayi tana hawaye,
Kila rabon Miemie kadai take dashi a
duniya,tasan kuma aure dai ana yinshi ne dan
abu biyu,samun zuri'a na daga ciki, gashi ita
anan ana son a haramta mata.
Tabbas d'aukar y'arta shine babban mafita a
game da yadda take jin son ta haihuwa a yanzi..
Wayarta ce tai ruri, a hankali ta goge hawayenta
ta tashi,
"Billy" taga a rubuce.
Da sauri ta saita kanta kamin ta daga.
"Sarauniyar kirki kina gida ne?...
Dariya ta danyi kan tace tana nan..
"Toh ina kofar gidan ki yanzu haka.
Da sauri ta tashi dan g'yara fuska tana fadin gata
nan zuwa.
Sai da ta tabbatar da ba mai gane tai kuka kamin
ta fita kofa shigo da Billy.
"Matar nan kinganki kuwa?.. Kin zama big
madam da gaske fa.
Murmushi tayi tana kar6an Ilham.
"Kai Billy banda fa sharri..
Dariya tai tana "ba wani sharri, koh dai mun
karu?.. Miemie tayi k'ani?
Shiru tayi tana murmushin iya le6e.
Bayan sun gaisa take ce mata ai daga wajen
Miemie suke,tai ta kukan zata zo tana jin tace
gun Auntyn ta zata.
Murmushi tai tai kasa da kai,Allah sarki Mimi.
"Yau Miemie aka kaima ziyara kenan?.. Murmushi
Billy tai kan tace "ai duk sati sau biyu Abban
Ahmad (Garba) ke zuwa dan dubo ma Abban
Miemie lafiyarta.
"Shine yau muka je tare,Miemie akwai
wayo,kusan wata shida amma bata manta
Abbanta ba,tana jin muryarshi a waya ta fara
murna..
Shiru tai tana nazari,ba dai ace tun tafiyar
Ja'afar ya zuciya ya bar garin nan ba?..
"Ja'afar kanar wasa,kinga wata shida muke nema
yaki waiwayo mu,sai kulafucin a dubo mishi
gudan jininshi... "Rayuwa kenan fa,kana naka
Allah na nashi,in kai hakuri sai ka ga na Allahn
ne dai dai a gare ka.
"Amma Abban Miemie namijin duniya ne,mai
ra'ayin kanshi,tunda ya jima haka nasan alhinin
aurenki ne bai sake shi ba.
Shiru tai tana jinta,a hankali ta fara jin nadamar
wulakancin data kartawa Ja'afar, Abban y'arta.
Yau Billy ta kawo fitina,dan har ta tafi bata da
sukuni,har sai da ta tiki kuka son ranta taji
dad'i,yanzu burinta Miemien ta dawo gare ta.
Koh da maigidan yazo yaga yanayinta yasan
tasha kuka,da ya tambaye ta sai tace Miemie
take son gani ta d'akko ta.
Anan ya tada mata bori,har sai da tai da na sanin
maganar Miemie.
Ba abinda yafi kona mata rai sama da yadda
tanaji tana gani yai mata haramiyar
makaranta,sannan Mama ta goya mishi baya,abu
goma da ashirin sun had'e mata.
Adaddafe akai shekara, lokacin tuni ta jima da
d'akko y'arta,dan bazata iya da rashinta ba a irin
yanayin da take na son yaran nan.
Sai sai wani abu,fur Miemie taki jinin Alhaji, ko
abu take in zai kwan dubu yana ta bari bazata
koh k'alleshi ba,asalima har wani kumbura baki
take in ta ganshi,Salma tai magana tasa mata
kuka,ga bala'in Alhaji na wai yarinya tun kan ta
girma ta rainashi shi da gidanshi, har harara wai
take mishi...
A tunaninta kamar Miemie wane harara ta sani
bare wai kumbura mishi baki?.. Amma dan a
zauna lafiya yasa kullum take kwa6ar ta.
A gaban kowa har su Nabila zatai wasa harda
k'yak'yatawa, amma fa koh a nan bangaren taci
ka'ro da Alhaji zata d'unkume,tamkar ba ita
ba,shima kwa da harara zai bita, wani sa'in harda
t'saki..
By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:33 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
39_"Aunty A'i na rasa yadda zanyi ne,yadda yake
nuna t'sanar Miemie karara yafi damuna,abu
kadan tayi sai ya hantara,t'sawa, ga kullum yai
ta surutun wai tana hararar shi,koh fa wai turo
mishi baki,nawa take fisabilillahi?... "Allah bansan
haka agolanci yake sai gun Miemie. Murmushi
tayi "bari muga,ke dai sa ido... ta kallo Miemie
dake chan gefe tana mota da motar wasa. Da
k'arfi Aunty A'in tace "ke Miemie... Rai had'e,
itama ta dago tare da 6ata rai tana kumbura ma
Aunty A'in baki. Sai Aunty A'in tai mata
murmushi tare da mika mata hannu, "zo Miemie
naga kitso, waya miki?.. Kafad'a ta make
halamar bazata zo ba kenan. Cikin wasa Aunty
A'in tace "haba Miemie ta,zo zan baki sweet fa..
Da sauri ta taso har tana dariya ta d'are ta tana
kiran sweet. Baki sake Salma take k'allonta,Allah
yaga banda yau ta gani da idonta bazata yarda
Miemie zatai haka ba. Gira ta daga ma Salman
halamar ta gani ai. Miemien na fita tace "Ikon
Allah Aunty A'i, ashe dai gaske ne Miemie na
mishi hakan. Kai ta kad'a, ''amma in ya mata irin
yadda na mata,kila koh wasa take yana mata
ne,yaro kamar Miemie dan lallabi ne,shi yasa tun
farko banso kin karbi yarinyar nan ba
Salma,gudun irin matsalar nan.. Ba magiyar da
Abbanta bai min ba shima a waya kan baison
ya'rshi ta zama agola, Gashi in bakiyi wasa ba
shi kenan ta gama raina miki miji. Cike da
damuwa tace "Nikam ta rufan asiri karta kashen
aure Allah.. Dariya Aunty A'i tayi,lalle ma
Salma,wai karta kashe mata aure? "Haba dai ke
kuma,sai kace wata babba,kawai dai ita tata
salon fad'an ne haka,amma zata daina. Ajiyar
zuciya ta sau,kan tace "Bazaki gane ba Aunty
A'i,wallahi in Abban su Nabila zai kwana yana
cewa Miemie bari koh kallonshi bata yi,wannan
nasan tana dashi,shi kuma sai ya kule,baya duba
yarintarta,sai ma ki ga ya hauni da sababi. "Toh
ki dinga sata misali kai mishi abu haka,kina kuma
kula d yanayinta in yana mata magana,sai kina
sata a hanya. Har magriba suna abu
daya,matsalar gida Alhaji har ta tafi. Washegari a
ita ke da shi,tun wuri ta shirya Miemie ta d'auke
duk kayan 6arna duk dan a zauna lafiya.
Chankula chankoto take mata tana dariya,ta
sunkuya tana mata "aci ladan gabe" tana dan
mata duka yai sallama. Kallo daya ya musu ya
d'auke kai, dagowa Miemie tayi,in ba idonta ke
mata gezau ba kamar harara ma ta mishi,tuni ta
gintse fuska ta daina dariya. Ya salam, Miemie
tai nisa a tsanar Abban su Nabila. Yake tai kan
ta tashi dan binshi d'aki, "Miemie tashi muje gun
Abba koh?... Kafad'a ta mak'e tana turo baki, sai
tai kamar bata gani ba ta kinkime ta,a ranta tana
fad'in "sai nayi da gaske a kanki Miemie. Ihu ta
fara tana zazzamewa,a dole ita bazata je ba,jin
suna iyowa dakin yasa da sauri yace "Kar ki
shigo min kina min wannan kukan dama.. Chak
ta tsaya tare sauke ta,kafadar ta kara makewa
tana kallon Salman,sai ma ta fita tayi bangaren
su Ja'afar. Kai ta dafe tana mai mamaki ita
kam,Miemie,toh mey take so da ita?. *DAN
KUKA...* ************************** Dube yake
zai k'alli news amma baiga d'ayan remote ba, ga
Salman ta shiga wanka, Kamar ance diba hannun
Miemie dake chan gefen corridor tana wasa sai
ga shi kuwa,yau shine motar ta ma. Da zafin
nama ya tashi ya nufi gunta.. "Jiyinnnn" take
dashi cikin tsawa yace "Wannan ne abin yin
motar?.. Dagowa tai tana t'sareshi da ido cikin
had'e rai, "Bani nan ni labarai zai wuce ni
sarauniyar 6arna. Kafad'a ta mak'e mishi tare da
yi da remote din bayanta tana zunguro mishi da
baki. Cikin zafin nama ya dagota, dai-dai fitowar
Salma dan jin fad'anshi, binta yake daga zaunen
tana matsawa taki bashi,kawai sai ya fizgota da
niyar kwata ta tun karfi, kai cikin fushi ta kwada
remote din a kasa tana kuma mishi ihun kukan ya
hanata wasa.. Dagashi har Salman suka bi
remote din da kallo wanda kowanne part yai
nashi gun battery ya cire. Da sauri Salman ta
karaso ta kwada mata mari,sauke ta yai kasa
yana sababin ai wai ita tasa ta raina mutane yai
waje,k'allon da baiyi ba kenan ya fice. Harara ta
kwada mata kan ta kamo kunnenta ta murde
tana kuka, "Baki isa ki chazan matsala ba ja'irar
nan,wato bakin hali ki ke son kowa koh?. Kashen
aure zakiyi ne?.. Kullum baza'a aji kanmu da
mijina ba sai akanki?.. Cikata tai tare da dan
rangwashenta, "Toh baki isa ba,dole kizo ki koma
gurin Mama koh dangin Abbanki da zama... Bata
karasa ba Miemie ta fad'i tana burburwar fad'in
taki,ita bazata ba. Ido kawai ta sa mata,kan tai
kwafa tai d'aki,da gudu itama ta bita tana kukan
bazata ba Salman ta rufe kofarta ta batta da
bugun "Antee,Antee bata cho. Anan tai ta
mitarta tanaji daga dakin tana "Ai sai kinje...
Tuni ta kara jiniya, kuka harda shudewa amma
tai burus da ita tana kwalliyarta. Zuwa chan taji
shiru,sai tai murmushi, Miemie matsala. Fito wa
tai dan ganin koh fita tayi,sai ta ganta kwance
bakin kofa sai sauke ajiyar zuciya take tai bacci.
Sunkuyawa tai ta leka,ido har ya kumbura, duk
sai ta bata tausayi,batasan lokacin da ta d'akko
abarta ba,batajin tunda Miemie take ta ta6a
dukanta haka tai kuka. Kwantar ta tai a gado
tana goge mata fuska da tissue,baki ta kai
fuskarta, "am sorry kinji... kamar ta sa kukan
itama,Miemie taurin kai toh,Alhaji hancini,ya
suke so tayi da ranta ne? By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:34 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
40_Washegari bayan la'asar tace mishi zata
maida Miemie gidan Mama dan Allah ya batta
taje daga nan sai tai barkar Ummi data haihu
cikin dare. Da har zai hana,ganin kayan Miemie a
akwati yasa bai gardama ba ya batta,kwarai
tasha mamaki,dan rabonta da fita har ta
manta,amma dake wacce bai kauna za'a mayar
ya batta. "Ga driver in kin gama ya kaiku,kar
kuma ki dad'e.. Kai ta daga tace ta gode.
Rayuwa kenan,da ya batta ma taji dad'i,koh ba
komai zata leka gida yau. Gidan Ummi suka fara
zuwa,sai ta6e baki take tana korafin yadda ta
zama matar k'ulle. "Aure sama da shekara
wannan ne zuwanki na biyu gidana,wannan wace
iriyar rayuwa ce,mutum sai shegen kullen t'siya..
Tana jinta tai shiru,tana tunanin hali irin na dan
Adam,mai wuyar gane hali,lokacin Ja'afar mai
barinta fita haka ta gurza,yanzu kuma ta had'u
da dai dai kowa,ga kud'i ga cima, amma ba fita
ba haihuwa.. Zaman lafiya wai yafi zama Dan
Sarki. Ita kanta Miemie murna take sun fita
yau,sai dai suna zuwa gidan Mama taji Salman
na maganar zamanta ta d'ane cinyarta ta riketa
tam. Ban6are ta Mama take ajikinta tana ihun
kiran Aunty,ita kuka Salma kuka, ga magriba ta
sawo kai. Suna haka Abba ya shigo, duk ta rike
gyalen Salma kam tana ihu. Dak'yar ta fizge tai
hanyar fita da gudu tana kuka. "Subhanallah... Ta
shid'e fa wannan... Chak ta tsaya jin daina kuka
Miemien,da sauri ta juyo taga Abba na jijjiga ta.
Ba shiri tai gun dai dai Miemien ta kawo wuta ta
kar6e ta. Kuka na fitar hankali take tana bata
hakuri, ''Ni bansan mey yarinyar nan zata tsare
miki ba in ta zauna achan gunki ba,kullum sai da
kuka koh jinya za'a rabu?.. Ki bar y'arki a kusa
dake man tunda ita mai kulafuci ce... Kai ta
daga tana share ma Miemien hawaye tana tai
shiru toh.. Dole tana ji tana gani ta koma da
Miemie, dan yau fir taki yadda tunda ta d'andana
zama da ita. Kanta take shafawa,ita kam ta
tasata gaba tana ta kallo ba koh kiftawa. A
hankali tace "Miemie.. Idonta a kan Salman tace
"Uhmm. Kwanto wa tai a gefenta tana g'yara
mata kwanciya, kamar wata babba ta fara mata
fad'an ta zama mai ji dan Allah. "Ban san
matsala Miemie, ki rufan asiri ki daina halin nan
naki na kumbura ma mijina baki,kinji?.. Kai ta
daga mata kamar gaske. Sai tai murmushi tai
kan tace ta taso suje suyi girki a kitchen. Shikam
Alhaji da murnar yau Miemie ta tafi ya shigo
gida,shi kanshi ya rasa mey yarinyar ta tsare
mishi a gidan,duba ga su Ja'afar na gidan. Sai
dai tun daga bud'e kofar parlourn farin cikin ya
kau. Dariyar Miemie ya fara cin karo yana
shigowa ta kitchen,dan haka da sababi ya isa.
"Mey ya zaunarki har bayan magriba baki dawo
ba?... Mey kuma ya dawo da wannan? Duk ido
suka zuba mishi,mai hali kuwa Miemie tuni ta
chunno baki gaba tana mishi wani irin kallo jin ya
fara sababin nashi. "Wallahi har kusan suma tayi
dan kuka yau,tausayi ta bani shine na dawo da
ita,kai hakuri duk ita tasa muka kai magriba.
K'allon Miemien yayi da kamar harara kamin ya
kad'a kai dan takaici ya fice. Ajiyar zuciya ta
saka,ta tsalake rijiya da baya da k'yar,kan ta
dawo kan Miemie ita tuni har ta cigaba da
sabgarta. Sai dai ana zuwa kwanciya yace daga
yau Miemie zata bar kwana dakin su,koh ta koma
kasa. Ya ta iya,dan a zauna lafiya ta sauke
Miemie kasan,dan ba yadda za ai ta luluka
yarinya chan wani waje ita tana wata jahar,a
ganintq Miemie nawa take. ******* Fur yanzu ta
daina ganin fuska gun Alhaji, in ya shigo ba
wanda ya isheshi kallo,asalima ya daina zama
bangarenta sai cin abinci koh bacci. Yau dai ta
d'au damarar fara koyawa Miemie sabo da Alhaji.
"Abba ki ne kinji Miemie nah?.. Ki dinga mishi
oyoyo kina mishi dariya kinji?, banda
harara,banda turo baki,kina ji na? Shiru tai tana
binta da kallo kawai,chan sai ta yak'e mata
hakori. Cikin farin ciki Salman tace "yauwa,koh
ke fa,be a good girl ba? kai ta daga mata tana
dariya. Alhaji yai wanka ya shirya yaje parlour
yana duba abu a system nashi su kuma suna
daki gun shirya Miemie. Daga parlourn ya kwada
ma Salma kira wai ta fito mishi da agogon shi na
kan mirrior. Murmushi tai ta k'alli Miemie,tasha
parking da ribbon sanye da gown ja da baka iya
g'wiwa, dake fara ce sai tai mata k'yau sosai.
Agogon ta d'akko ta kamo hannun Miemie, "Kai
ma Abba a maza yana parlour,ki nutsu dan Allah
kinji Miemie nah.. Kai ta daga tana dariya ta
karbi agogo tai parlour. Bayanta ta biyo dan
ganin ya zata kaya, daga yau ne zata fara koya
musu kusanci da juna shi da Miemie. A dunkume
ta isa gunshi yana duba abu a laptop, mika mishi
tayi ba koh magana, sai ya dago ganin itace,tai
mishi kyau sosai,ga sai kamshi take,ba abinda ta
bari na babanta a ganin shi har dacin ran,in baxai
manta ba yanzu ne zata shiga shekara uku,amma
duk ta tara dacin rai wai da fitsara. Kai ya
d'auke ya cigaba da abinda yake, Salma har ta
fara murna ganin bai mata dan halin ba yau. Ita
kwa Miemie sai ta ajiye agogo kan hannun kujera
ta juya tsautsayi agogo ya fad'o kasan tiles sai
glass din ya fashe. Da azama ya juya,ganin
agogon akasa a fashe Miemie ta juya ta mike ya
fara sababi. "Duk wani mugun hali irin na ubanta
yarinyar nan ta iya,agogon nawa zaki saka da
gangan ki fasa min?.. Waje Salma ta fito ganin
ya yo kan Miemien a sukwane, duk tana k'allon
abinda ya faru. Kumatun Miemien ya ja tare da
kai mata rangwashi akai yana sababi,tuni ta hau
kuka jin zafin abin,da sauri Salman ta karaso dan
bashi hakuri. "Shegiyar yarinya kawai,kin san
kud'in agogon da kika fasa kuwa?.. Ja Salman tai
ta tsaya tare da rintse ido. Ga ihun Miemie tana
kiran Aunty,ga sai zagin y'arta yake harda
sheganta mata ita? "Alhaji.. Cikin fusata ta kira
shi tare da bud'e, Rai 6ace shima ya dago da
niyar huce haushin shi kanta ta rigashi. "A
gaskiya ka daina sheganta min yarinya, dan da
ubanta gaskiya,haka kawai, ina fa kallo tana mika
maka ka d'auke kai,ta ajiye ya fad'o kasa,toh
meye lefinta aciki har irin wannan zagi?.. A'a toh
gaskiya... Kai ta kawar ranta 6ace. Cika Miemien
yayi yana kallonta, wannan ne karo na farko da
ya fara ganin fitsarar Salma,shi zatai wa tsawa
akan Miemie? By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:37 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 41_Da
gudu ta karasa tana kama hannun
Salman,d'aukarta tayi a ta sa6a a baya, "Yi shiru
kinji.. Muje daki... "Kar ki kuskura ki shigar min
d'aki da wannan yarinyar.. Chak taja ta tsaya
tare da juyowa tana kallonshi. "Kema kar ki
shigar min d'aki,ni zakiyi wa rashin mutunci kan
y'arki?.. Toh baki isa ba,dan ba ayi macen da ta
isa daga min murya ba ki sani. Cikin karfin hali
tace "Toh mey ka ke nufi da hakan?.. Daga fad'in
gaskiya?.. Haba Alhaji,Kullum ina fuskantar
yadda ka ke tsagwamar yarinyar nan,shi yasa
sam bata shiri da kai ai... "Ba wani nan,bakin
halin yarki dai irin na tsohon mijinki dai,da kuma
shegen taurin kanta irin nashi,koh kin zata na
manta da waye shi zamanin neman aurenki? Da
sauri ta tare mai numfashi harda sauke Miemie
kasa da sauri, "Ba ruwan Ja'afar cikin maganar
nan tamu,zai fi kyau in ka daina sakoshi
ciki..kuma na fad'a maka y'ata bata da wani
mugun hali,sai dai naka mugun halin rashin son
yara, da kuma.. Shiru tai tare da ja da baya ganin
ya zaburo kanta, "wallahi kar ma ka soma,dan ba
yadda za ai in zuba ido kullum kana aibanta min
yarinya wallahi, nawa Miemie take? Amma k'arfi
da yaji so ake ta iya dan hali.. "Salma ni nake
fad'a kina fad'a?.. Ashe baki da mutunci?.. Kai
ta kad'a tare da juyar da kai, "Nikwa nake da
mutunci tunda a cikin gidan ubana ka auro ni
kuma... "Subhanallah,haba ku k'wa.. Juyawa tayi
taga Maman su Nabila na shigowa dakin. "Tun
ina shanya nake jiyo ihun Miemie da naku,bai
dace ba Allah,kuna abu a gaban yarinya.. "Ba
ruwanki cikin zancen nan,in ba so ki ke ya taso
da kwantaccen naki ba ke ma.. Shiru taja
bakinta tayi tuni idonta ya fara zubar da kwalla,
ya cigaba "Yara nawa ma basa gabana bare ta
wani, saboda haka akan yaro ba mai sani ciwan
hawan jini,dole yau ki mayarta gun ubanta,koh ki
san nayi da ita. Cikin kuka tace "Bazan iya
rabuwa da y'ata ba,kai hakuri raina ne ya 6aci..
Malalacin murmushi yayi,kan yace "Daga baya
kenan,amma dole ki za6a zaman dani koh da
yarinyar ki... Maman Ja'afar ta kallo da itama ke
hawaye tana kallonta,sai ta cije le6e da takaici.
Juyawa tayi ta d'au Miemie, kan ta kalloshi ido
na fidda kwalla. "Ni kam na kasance daga masu
taya annabinmu kishin Al'ummar shi,dan haka ina
son haihuwa,bi ma'ana zan iya rayuwa da Miemie
kad'ai mud'in Annabin mu zai alfahari dani...
Cikin zafin rai yace "Kimin hausar da zan gane
Malama ni.. "Annabinmu yace kuyi aure dan ku
hayaiyafa,domin go6e kiyama nai alfahari daku..
Kayi aure,amma baka fatan tara zuri'a, hakan
yana nufin kana tarjiya a bisa umarnin manzon
Allah.. A tunzure yai yo kanta, "Kimin shiru
fitsararriyar kawai,koh yayarki bata isa ja ina ja
ba wallahi, dole ne yau ki za6i d'aya.. Cigaba tai
da batun ta ido rufe, "Nai ma biyayya ta t'sawan
shekara guda ina bin yadda kaso,toh ka sani ni
Sunnah na dauki aurena,kuma zan cikashi ne ta
hanyar tara zuri'a, dan zanyi alfarhari idan na
kasance a daya daga wanda Annabi zai alfari da
ita... Mari ya de6eta dashi jiki na 6ari,da sauri ta
dafe gun tare da bud'e ido,kuka Miemie tasa
ganin an daki Auntyn ta, "Mutuniyar banza
kawai,ni zaki mayar jahili?.. Murmushi tayi kan ta
kad'a kai. "A'a,dan kuwa kafi jahili,danshi dama
bai sani ba bare take,kai kuwa ka sani amma
kana taya shedan rawa,dan baka kaunar.. Shiru
tayi ganin zai kara mata wani,da sauri ta rintse
ido tana hawaye,jin shiru bataji saukar mari ba
yasa ta bud'e ido. Hannunshi rike a hannun
Maman su Ja'afar, "Lalle lokaci yayi da ya
kamata in tanka maka Alhaji,lokaci yayi da zan
daina bin umarnin ka ina 6ata.. Ashe har alfahari
ka ke cewar yaranka ma basa gabanka?.. Jiran
amsa take tana kallonshi, da borin kunya yace
"Cika min hannu... Ba musu ta cika, Salma ya
nuno "Ke kuma ki tafi gidan ku,na sake ki saki
daya,na koyan hankali,in kin koyo kofa a bud'e
take ki dawo.. Ido ta rintse gabanta na fad'uwa,
wai ya saketa?.. Daga fad'in gaskiya. Kan
Maman su Ja'afar ya dawo, "Wato zuwan
fitsararriyar yarinyar nan ta sa kin fara sauya hali
Halima koh.. Kai ta daga da sauri.. "Kwarai
kwa,dan yanzu na gane kuskuren dana tafka a
zaman baya da nayi da kai, nima ina son zuri'a,
ina son su Ja'afar sama da komai yanzu,kuma
zanso wanda duk yake son su,zan kuma yi fad'a
da duk mai kinsu, aciki kuwa harda kai usman...
Baki ya saka yana mata k'allon mamaki
"Usman?.. Babbar magana.. Halima yau ke kike
kama sunana ba ma Abban Ja'afar bare Alhaji?..
Shiru tayi tana kallonshi,sai sababi yake daga
karshe itama yace taje sai ya nemeta. T'saki
sukai mai lokaci daya ita da Salma,duk da kallo
ya bisu Salma tai d'aki. "Ai nima ka sallame ni
kawai,dan bazan zauna da mutumin dake
kyankyamin zuri'a ba,dole yau na barka,Allah ya
yafen baya,amma yanzu kam ta kau,ka sake ni
nima kawai... "Bazan saki ba,amma dole ki fuce
min a gida,dan ba mai sa min hawan jini... Kuka
Salman take tana jiyo sababin da Alhajin ke yi..
Hannu Miemie ta kai tana girgiza mata kai itama
tana kukan,gaba daya ta rungumo y'arta tana
kuka mai cin rai,ita kuma haka Allah yayi ta
marar sa'a a zaman aure,gashi yau a dalilinta
auren shekara sama da ashirin na neman
tsinkewa bayan ta t'sinke nata. By Feenat
Ja'afar.
9/29/16, 9:39 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
42_Jugum Abba yai bayan jin bayanin Aunty
A'i,ita dai Salma sai kuka take,dan tasan yau
kam sai ta Allah,fad'a kam sai dai ta toshe
kunnenta. Amma da mamakinta sai ji tai ya
sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Allah ya
kyauta toh,dama tun farko ni mutumin nan ba
wai ya mun ba ne. "Yadda naga kowa na yinshi a
gidan musamman Babar taku yasa nabi yarima
nasha kid'a, sai fatan Allah yasa haka shi yafi
alkairi.. Mama ce ta riga kowa saurin fad'in
"Amin,ni nasan naso shi,amma daga baya sam
mutumin ya fice min akai,dan daga gani ba wai
zaiyi wani mutunci bane,ga dankaran kulle,yanzu
kuma an kara da rashin son haihuwa.. Dame
yarinya zata ji?.. Kallon mamaki suke ma Maman
musamman Salma, yau mama ke fad'in aibun
Alhaji da bakinta?... Lalle abu ya 6aci. Da dare
suna kwance ta tasa Miemie a gaba tana
kallo,itama ido ta sa mata, tunaninta zancenta ya
tabbata. A dalilin Miemie aure ya 6alle..
Murmushi tai kan ta gyara kwanciya. "Miemie..
Kai ta daga tare da fad'in "Uhmm.. Sai ta
mirgino kusanta tai rub da ciki "Kina murna
kuwa?.. Baki ta yage mata ba dan ta fahimci
nufin Auntyn ba. Sai ta kad'a kai,ta rasa wane
irin nishad'i ke shigarta da yamman nan zuwa
daren yanzu.. "A k'ya kam yi murna,wato kin
rabu da alakakai koh? Kai ta daga mata tana
dariya.. Itama tana dariya ta fara mata chakulkuli
su na k'yak'yata dariya har su Abba dake waje
suna jiyo su. Mama ya kallo,itama shi take kallo,
"kina jin mutananki koh?.. Kamar yau take
Sallah.. Murmushi tai tana sadda kai kasa, sai ya
girgiza kai yana tuna wani abu. ****** Tun daga
wannan lokacin hankalinta ya koma kan
makaranta, babban bakin cikinta bai wuce yadda
Alhaji yai burus da maganarta ba,a ganinta in har
da mutunci koh Abbanta ya samu da zancen..
Gashi a kalla yanzu ta kusa cinye kwanakin iddar
ta. Duk suna waya da Maman su Nabila tace
yana zuwar musu,sai dai ita baya samun ganinta.
"Aunty!.. Aunty!!.. Da dan gudunta ta shigo gidan
tana k'wada mata kira rike da leda tana ja,bakin
nan har kusan kunnen Miemie. Kamar a mafarki
taji kira ana ta6ata,a hankali ta bud'e ido dan
bata jima ba da bacci ya debeta sakamakon
ciwan period da take. "Uhmm Miemie.. Ya akai?..
Ledar hannunta ta hau bud'e mata tana mata
magana duk a hard'e dan murna. Riguna ne y'an
kanti masu kyau da tsada da takalma, sai teddy
guda biyu da y'ar tsana mai feeder a baki. A
zabure ta mike tana duben Miemien,tasan ba mai
irin ma wa y'arta tsarabar nan sai Abbanta,yawu
ta had'iye kamin tace "Miemie,ina kika samo
kaya haka?.. Dagowa tayi kamin tace "Abba ne...
Tsam tai tana kallon irin farin cikin da Miemien
take,wato in zai shekara bata ganshi ba tasan
Abbanta. K'allota tayi tana mata yake ganin
yadda take cire feedern a bakin y'ar t'sanar tana
fad'in Inya.. Inya. Da sauri ta tashi tare da zarar
gyale tai waje. A kalla zataso ganinshi koh dan
ganin yadda yake a t'sawan shekara guda da
d'auri. Sai dai har ta gama leke bata koh hango
mai kamar Ja'afar fa sai sawun mota. Zaure ta
koma tana lumshe ido tare da dafe kirjinta. Babu
makawa Ja'afar ya shigo zauren nan.. Dan ga
nan kamshin turarenshi ciki tana iya shakarshi.
Jiki a sanyaye ta juya ta koma cikin gida, a chan
d'akin Mama ta jiyo karad'in Miemie na ba ma
maman labari tana dariya. Da murmushi ta samu
ta dan dosana tana kallonsu kamar ta sa kuka.
"Na fuskanci yarinyar nan in dai tai arangma da
Abbanta tana kwanan murna, haka kwanaki
dak'yar na ban6areta jikinshi ashe bata manta shi
ba tana kuka,shima harda y'ar kwalarshi yana
daga mata hannu... Ido ta kurawa Maman ba koh
kiftawa.. Ba dai Mama na nufin Ja'afar yana
zuwa garin nan ba kuma har gidan nan?... Mama
ce ta kat'se mata tunani da fad'in "Ban tunanin
yaron nan koh a hanya ya ganni zai gaidani ba
sam bayan aurenki, duba ga yadda na rika mishi
fatattakar arziki.. Zuwan shi biyu gidan nan ashe
makaranta ya koma kinji.. Murmushi tai Maman
da iyakar shi le6e tare da daga kai. Tuni ta
zurfafa tunani,har bata jin mey Mama da Miemie
ke fad'a,kan ta farga har idonta ya cika da
kwalla,da sauri ta juyar da kai tare da goge wa
kamin su gani. Sakkowa tai tana taya Miemie
rad'awa teddy suna suna dariya. Kallonsu kawai
Mama take tana wani tunani, kai ta kad'a kamin
ta tashi ta basu gu dan tasan Abba yana gaf da
zuwa. Washegari da yamma tana kokarin shiga
wanka akai mata sallama. Hijab ta zira harda
shafa powder da zumudin Ja'afar ne ma,kila ya
samu labarin tana gida. Turus tayi tare da
chunno baki kamar Miemie ganin Alhaji da
abokinshi. Baki ya washe mata yana fad'in ta
karaso man kusa... Murmushin mugunta tai kan
ta kalloshi "Dan bani minti biyar na fito a gida...
Kai ya daga yana mata murmushi, ashe bazai yi
wahalar shawo kan Salma ba kamar Halima.
Ruwan da ta zuba na wanka ta d'auka da wani a
buta dan tsarkake kai in tai wankan t'sarki. Tana
yi tana murmushi har ta gama. D'aki ta shiga ta
tsane kanta da towel kan ta dan shirya a
gaggauce ta fita. Yadda take murmushi ne yasa
Mama tambayar waye yazo, a tunaninta koh
Ja'afar ne,tana cewa Alhaji ne ta 6ata rai. "Ki dai
kama kanki ki saiwa kanki mutunci,dan sam
mutumin ba nagari bane,kinjini ai? Kai ta kad'a
tana murmushi, lalle Mama, yau Alhajin guda?..
Sai ta kad'a kai, "adu'a bata fad'uwa kasa banza.
Bayan sun gaisa yake zungurar abokin nashi
sarkin iya t'sari, duk tana jinsu tana murmushi
dan feleke harda tambayar Miemie,sai da suka
gama tass tana jinsu tana kad'a kai. "Ai yanzu na
fita sahun matarka Alhaji,sai dai kabi sahun
zawarawa na..dan nayi iddah ni... Fuska ya
g'imtse yana kallonta, "haba kar muyi haka dake
man,ina fa lissafi,yau watanki biyu da kwana uku
rabonki da gida na, kinga ai bakiyi wata uku bare
ace kinyi iddah koh ba haka ba abokina? Kai ya
jijjiga yana fad'in "kwarai kuwa,dan haka muka
sani a al'adan ce. Kai ta kad'a tana murmushin
takaici, wato ga babyn roba,a hular a lokacin da
akaso a d'auka a randa aka ga dama.. 6aro-6aro
tai mishi dalla-dalla kan ita ai duk bayan sati uku
take period, kuma ya sani sai dai ya take. A fafur
yace shi baisan zance ba,kawai ya maida ta
dakinta. Juyawa tai ta koma gida,tana ji sai
kwad'a mata kira yake tai mishi banza. Da farin
ciki ta shiga har baya misaltuwa, dan da yanzu
dabarar yin wanka ba tazo mata ba da tuni
ansha da ita an gama. "Ba dai ya maidaki ba
naga kina murna tun yanzu Salma?.. Yanzu ke
bazakiyi kishin kanki ba har kin bada kai daga
fita bori ya hau?.. Ina laifin ya samo Abbanki da
maganar in dai da mutunci aciki... "Au dariya ma
na baki koh Salma?.. Ga shash.. "Mama ni fa ba
aure a t'sakanin mu da Alhaji yanzu,dan tau nai
iddah ta.... Baki sake take kallonta,dariya tasa ta
bata labari,sai ga Mama na tikar dariya. "Lalle
yarinyar nan da wayo ki ke,kwarai kinyi dabara,
dan sam mutumin ya sane min, dan ban fad'a
miki bane,ba'a fi sati da dawowarki gida ba muka
had'u da dan talikinnan,d'auke kai yai kamar bai
ganni ba fa,bayan sarai mun had'a ido.. "Shi yasa
yaron nan Ja'afar nake ganin kimarshi har
kullum,dan koh bayan rabuwarku yana daraja
mu,musamman zai sa azo har gida abokinshi yai
mana goma ta arziki in sun d'au Miemie... Shiru
tayi tana sauraran maganar Mama, wai Ja'afar
take ma ya6o haka da kirari?.. Farin cikinta a yau
bai misaltuwa,ina Miemie na nan ta rad'a mata
itama suyi tare,tasan dai duk inda take yanzu
tana neman gida,dan tun dazu tai mata kwalliya
da kayan Abbanta kaninshi yazo ya d'auke ta.
Murmushi tai tana jijjiga kai. Lalle ne *Duniya
Labari ce* By Feenat Ja'afar. feenat-jafar.my
wapblog.com
Feenat Jaafar's Mobile Blog
feenat-jafar.mywapblog.com
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 9
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
43_Waya yake d'annawa a nitse yana duba sakon
waya kamar bayaso,kamili ne,da hasken
shi,sajenshi a yanzu shine sirrin 6oye kyanshi na
ainashi, sanye cikin kananan kaya da glass
manne a idonshi,da gani yana ji da ajinshi a dai-
dai lokacin nan,dan miskili ne yanzu na karfi da
yaji. A yanzu ne yake tsone idon y'an mata
musamman na jami'a, dan ya iya t'sare kai da
tsare gida. Rayuwarshi ta sauya,dan ya dawo
ainashin halaiyar shi ta da,koma yafi da din,
Ja'afar kenan,namijin duniya. Dago kai yayi yana
duba yanayin garin da yadda kowanne shago
suke hadahadarsu,sai ya sauke kai kan Abdull
mai tahowa dauke da baby a kafad'a tana ta
washe baki tun kan ta karaso. Tuni fara'a ta
maye g'urbin rashin walwalar shi,kashe wayar
yayi tare da ajiye ta gefe dan tarar gudan
jininshi,duk Abba dake gefe kad'an yana kallo.
"Abbaaa... Miemien ta fad'a lokacin da yake
k'ar6ar ta,murmushi yayi mata tare da shafo
fuskarta "Na'am Miemien Abba.. Sai ta washe
baki. Ciro changi ya mika ma Abdull, "Kan
magriba kazo ka maidata kaji?... Kai ya kad'a
tare da amsa yayi godiya. Zama yayi tare da
d'aura ta cinyarshi, Tasha kwalliya da rigar da ya
yo mata tsaraba cotton ja da pink,kan nan kamar
an mata shampoo sai kyalli yake yasha ribbons..
Hannu yakai kan dan beauty point nata ya latsa
sai ta sa mishi dariya. A hankali shima yayi har
hakorinshi suka baiyana. Tashi yayi zuwa gun
Abba dan mishi sallama,kai ya kad'a Miemie na
mishi bye-bye tana dariya. Kamar kullum nai yai
ta yawo da ita suka sai ice cream suka nufi
gidan Garba nan suka yada zangon su. Miemien
Garban ya kallo yadda take tsalle kan Abban nata
shikam sai murmushi yake mata. "Abokina ina so
yau dai daya ka saurare batu na,sama da wata
hud'u dana fara ma magana zaka ce a'a kai baka
so.. Kallonshi yake jin inda yake neman dosa,tuni
ya fara sauya kama. Ba tare da yabi ta kanshi ba
Garban yaci gaba "Salma fa au... Cikin t'sananin
fushi ya rufe ido tare da daga mishi hannu. "Dan
Allah ka d'aina dawo min da hannun agogo
baya,ina a cikin farina yanzu,banson jin sunan
wata Salma chan.. Gefe yayi da kai yana
chunkune fuska,kai Garban ya kad'a kan yai y'ar
dariya, "Karyar banza kenan,yanzu da zance
Salma tana gida an sakota da nasan ba wanda
zai farin ciki a yau,kaine fa.. Baki sake yake
kallonshi, "kana sanin abinda zaka fad'a man
malam.. Matar mutanace fa yanzun. Murmushi
yayi yana mishi k'allon bakasan komai. "Toh
auren Salma ya rabu tun wata hud'u da ya
wuce,sai ka kurbi ruwan sanyi ka huce.. Baki
sake yake kallonshi ba koh kiftawa. Baya Garban
yayi da kai yana shafa ha6a tare da daga mishi
gira,ya dan jima a kame kamin ya d'auke tare da
wayance wa. "Wannan bazai sauya komai ba
kama ji da wai,dan ban manta abinda ta dirka
min ba a baya.. Kama d'aina wata dariya..
Kafad'a Garban ya make,kan yace "Daga baya
kenan kuma,chan ta matse ma,dan nasan yau sai
kafi kowa farin ciki a garin nan,karyar kawai.
Tashi yayi yana daukan Miemie tare da hararar
shi, "Kanka ake ji,ni nayi kaga tafiya ta.. Dariya
yai kan ya mike dan sauke su, "Kaima an kusa
jin naka soon. Harara ya sakar mishi kan suka
fice yana ta mishi t'siya. ***** "Mama zan tafi,a
min adu'a Allah yasa kar na samu mat'sala
kamar yadda principal yace.. "Amin kam, in Allah
ya taimaka zasu karbi uzirin.. Kai ta kad'a, ''Amin
toh, na tafi kan wannan ta farka. Da sauri ta fice
ganin zatai latti. Allah yasota tana zuwa wata
Napep zata tashi ta d'au wani da dan sauri ta
t'sayar ta shiga ba tare da ta dubi na ciki ba.
"Dan Allah ka taimaka school of... Shiru tai jin
wani kamshi da ya bigeta,turaren da koh ajikin
wani taji,toh mutum daya ke zuwa ranta. A
hankali ta waiwaya dan ganin waye masanyin
turaren. K'yam tayi tana kallonshi da murmushi
ba koh kiftawa, shima hakan take,kan da sauri ya
d'auke kai kamar ma bai ganeta ba yake nufi..
Dad'i ne..koh farin ciki a ranta a safiyar yau..
*Ja'afar* Wannan shine yaushe gamo. Kokarin
mishi magana take yace da mai Napep ya t'saya.
Ba musu yaja ya t'saya, da mamakinta taga yana
kokarin sauka a Napep d'in, da sauri mai napep
yace "Kazo gaba toh. Ba tare da ya kalle yace
"Kai hakuri,bana shiga keke da mata... Gaba yai
ya batta baki sake.. Kuturu,wa ya ga turnuku...
Ji tai tamkar ta d'aura hannu a ka ta kurma
ihu,wai ita Ja'afar zai haka?. By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:44 AM - Queen Safiyyert馃憫: Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
45_Washegari kowa da farin ciki ya tashi kamar
ma ance an shirya. Yau tana son ta koma
Salmanta ta da ne. Yau shima yana son komawa
Ja'afar d'inshi na Salmateen shi,dan haka tun
wuri yaje yai g'yaran fuska,ya rage sumar kai,tuni
ya hasko kamar zamanin angoncinshi da Salma.
Gun Garba yaje yasha kwalliya kamar wani sabon
ango. "Ya mutumina nayi kyau kuwa?鈥� banda
shakiyanci pls. Daga sama har kasa yake
kallonshi,yai kokakarin 6oye dariyar shi. "Kayi
man,ina zuwa haka da sanyin yammacin nan
haka?.. Da zumudi yace "gun Salmatee hayatee
man. Da rashin fahimta yace mishi "wace haka?..
Harara ya sau mishi tare da fad'in "Ban sani ba,
kaima ramawa zaka yin?.. Dan Allah ni taso
muje.. Kai Garban ya juyar yana fad'in "ba inda
zani bansan mace ba, haka kawai, Da zumudi
yace "Salma ta fa,kar kace baka gane ba mana
mun dinke.. Kunu yasha yace "ban gane
ba,yaushe aka dinke?.. Koh ka manta
kalamanka?.. Lallami ya fara yana kasa da
kai,tuni Garban ya ware yana dillika mishi dariyar
mugunta. Shi dai yau bata tashi yake ba,burinshi
kawai su isa ga Salman shi. Yau d'aya ta zauna
zaman kwalliya duk da bata da tabbas din
ganinshi,har Mama na mata t'siyar ina zuwa?.
Murmushi kawai tayi ta ciro wani arnan purple
swiss tana kallo, shafashi tai tana tunano colorn
da Ja'afar yafi kauna ya gani ajikinta. Riga da
zani ne single, dinkin yai mata kyau tsam ya
kama jikinta, da gaske yau ta fito a Salmanta.
Tana daga d'aki ta jiyo yaro yazo wai Salma
tazo,tana jin Mama na fad'in inji wa?.. Bataji
amsar yaron ba taji Mama tace kace tana zuwa.
G'yale ta rufa fari da ratsin flower purple tana
k'allon kanta a mudubi,ina ma Ya Ja'afar ne
man... "Ki fito ana kiranki a waje Ja'afar yanzu...
6ata rai tayi tana gunguni, "Ja'afar kuma
Mama?.. Ni fa ba danshi zan fita ba fa.. Harara
ta sakar mata,kan ta juya tana fad'in
"magulmaciyar kawai,ni zakiyiwa alaye?.. Da gani
shigar Ja'afar daban take gunki ai... Dariya ta
kunshe kan ta kara k'allon kanta a madubi ta
fita. Suna tsaye sun rike hannun Miemie da suka
dakko chan gidan su jaafar suna mata y'ar dage
tana dariya. Murmushi ta tsaya yi musu da
sallamarta. Ido ya zira mata,yayinda itama take
kallon sauyawarshi a yau kadai kamar sabon
ango. Murmushi ya sakar mata yana daga mata
hannu halamun tayi k'yau, da sauri ta d'auke kai
a kallonshi tana cinkune fuska. Kai ya kad'a yana
murmushi, karya kuma ai ta kare, tunda har
shigarshi an mishi. Ha6a Garba yake shafawa
yana kallon wani fulakon karya gun Salma da
Ja'afar. "Kaganta ni dai ya kamata nayi fushi
bisa abinda ta dibga min,amma kaga an dakeni
an hanani kuka... Harara ta sau mishi,kan ta kau
da kai, "lefinka ai dayawa,bar tunatune kawai.
Kai Garba ya kad'a,kan ya kallo Salman. "Salma..
Kalloshi tai,bata tunani ta ta6a ganin Garba ya
zama serious haka, hakan yasa ta bashi
hankalinta gaba daya. "Nasan nima har yanzu
kina ganin baki na sakamakon zuwanmu na
karshe gunki. Rantsuwa ya mata,kan yace
"Ja'afar baizo ranar gunki da neman auren kisa
wuta ba sam,asalima yazo ne danya sadaukar
miki da farin cikinshi gare ki sakamakon sanin
waye Alhaji Usman.. Kai ta dago tana kallonshi.
Sai ya kad'a mata kai, Ja'afar din ta kalla,shima
itan yake kallo. Yacigaba, "yana son ki samu
farin ciki ne Salma,wanda yasan a gidan Alhaji
dak'yar ki sameshi,dan kaf halin Alhaji ba wanda
ba'a karanto mana ba,hakan yasa ya gwammaci
ya baki ni,duk nai imani sai ya fi mishi ciwo
sama da auranki a waje.. Ya kallo Ja'afar da
murmushi, "nasan abuna. Murmushi sukai ma
juna,tabbas hakane,dan da Garba ya auri
Salma,da yana gani bashi ba sake ganinshi bare
hulda da gidanshi. "Dan haka banajin da wanda
ya kai Ja'afar son farin cikin ki,ki d'aure ki bawa
abokina second chance a zamanku kamar yadda
bukaci haka. Nan yai ta musu fad'an rayuwa sai
y'ar hakuri ce,da sanya tsoron Allah a
lamari,gashi sunji dad'in tawakallin tunda suna
fatan in Allah yaso su maida aurensu. Kan Garba
ya tafi sai da ya tabbatar kowa ya yafe. Zaure
suka koma ta sa musu taburma. Kallonta yake
suna ma juna murmishin so cikin kauna. Sai wani
dan sinke kai take halamar kunya. Hatta Miemie
ta gane iyayen sun dinke, sai kallonsu take tana
murmushi. "Assalam Alaikum.. Kai suka
dago,Ja'afar ya amsa. "Aunty Salma wai ana
kiranki a waje.. Kallon Ja'afar d'in tayi, Shima ita
yake kallo,sai yai mata murmushi. "Tashi muje
naga wane tsageren ne wannan... Miemie ya
d'auka itama ta tashi tana murmushi suka fita.
Alhaji ne yasha gayu da babar riga da wata
katuwar mota yana murmushin ganinta. Fuska ya
tsuke ganin fitowar Miemie da Abbanta suna
wasan su. Tana ganin Alhaji Miemie ta g'imtse
fuska,murmushi Ja'afar ya mata tare da shafo
fuskarta suka karasa. Hannu ya bashi dan su
gaisa Alhaji ya juyar da fuska gefe. "Gunki nazo
fa. Kallonshi tayi tana murmushi, "toh
Alhaji,gamu ai.. Da halamar tambaya ya k'alleta.
"Ban gane ga ku ba?.. Kina nufin dashi zan
ganki?.. Ja'afar d'in ta kallo tare da Miemie dake
kallon Alhajin duk rai had'e daga shi har y'ar.
Murmushi tayi tare da matsawa kusansu suka
jeru mishi a gaba. "Alhaji, kai hakuri, kai
hakuri,ka daina zuwa,InshaAllah aurenmu zamu
mayar da Abban Miemie.. Ka d'auka zaman mu
yazo karsh.. ka d'auka rabuwar aure na da kai da
auran duk had'i ne na Allah... Ja'afar ta kalla tai
mai murmushi tare da shafo fuskar Miemie. "Kai
hakuri na na zauna da iyalina, ka yarda sune
farin cikina, ni ce tasu,kai hakuri pls... Kai ya
kad'a,tare da kallonsu,duk daga gani suna a farin
ciki.. Tabbas yasan yai sake,gashi ya tashi a
tutar babu,ba Halima ba Salma,ba su Nabila ba
Miemie... Wa zai gane a jiya yayi nadama?.. Ya
zasu gane yasan dad'in jin motsin D'a kusanshi a
yanzu?.. Wa zai gane ya hakura yanzu kam yana
son zuri'a?.. Murmushi yayi yana d'auke kai,kila
haduwarshi da Salma sanadin shiryuwarshi
ne,koh yanzu ya gode Allah. Kai ya kad'a tare da
masu fatan alkairi, k'warai tai mamakin jin harda
mata godiya a bisa gaskiya da take tsage mata.
Hannu ya mikawa Miemie fuska d'auke da
murmushi. Kafad'a ta mak'e tare da lafewa a
kafad'ar Abbanta. Mota ya shiga tare da fitowa
da leda cike da shopping na chocolate da ice
cream.. Alawa daya ya fito dashi tare da fad'in
"Zan baki sweet fa,zo mu gaisa mana Miemie..
Salma ta kalla kamar mai jiran umarninta.
Murmushi tai mata tare da daga mata kai,abin
kai sai taje ba musu,yau sai ga Miemie harda ma
Alhaji dariya. Da zai tafi hannu ta daga mishi
tana mishi bye-bye tana dariya. Duk sai Alhajin
ya bata tausayi Alhajin,har Ja'afar na daga mata
gira halamar tambaya. Marairaicewa tayi tare da
shagwa6e fuska. "Y'arka ta rabani da Alhajina
shikenan kunji dad'i.. Harara ya sakar mata
kamin yace "toh bishi, Allah yai ma y'ata albarka
yarinya mai kishin Abbanta koh? Kai ta daga
mishi tana dariya,da murna ya shillata sama ya
chafe suna dariya. Gwalo yai ma Salman,sai
Miemie ma ta hau mata,tuni ta fara chunno
musu baki suna cikin shagwa6a. By Feenat
Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 11
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 46_Ba
sauran jira,dan karara suke nuna ma fitsara a
gidan Mama, su Ja'afar abin nema ya samu,ba
guntun fulako,ba shiri ta bama Abba shawarar ayi
a mayar da auren nan. Wata daya aka sa suka
sha biki kamar ba gobe.. Nan take jin labarin
auren Bintu a gidan mai mata uku,tana chan ta
zama bora. Su Maman Abba duk sun halarci bikin
nata,nan take tsurkuta mata labarin Maman
Ummi kan ranar ta fita gantali miji ya
dawo,bayan ta dawo yace ta nemi inda dare ya
mata,karshe dai akai saki. Murmushi tayi,tasan
Allah ba azzalumin sarki bane,dole yadda taga
tasku Maman Ummi tagani itama. Jingina yayi a
jikin bango yana kare mata kallo,fuska rufe ruf da
g'yale,murmushi yayi dan tunawa da daren
farkonsu a wanchan gidan. Karasawa yayi tare
da g'yaran murya kad'an yana leka fuskarta.
Zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya. A hankali
ya kai hannunshi tare da daga mayafin da ta rufe
fuskar. Tsam yayi yana kallonta ido cikin ido,tuni
ya marairaice mata fuska,kuka fa?.. Hannu yasa
yana share mata wani na zubowa,duka ya hayo
gadon tare da janyota yana shafo bayanta
halamun tai shiru. Sai da tai shiru kan ya dago
kanta. Ido suka zuba ma juna ba koh kiftawa.
Chan ya nisa cikin murya kamar mai jin bacci
yace "Kin tuna kalaman da na ta6a turo miki na
karshe cikin text message dina kuwa?.. Tunowa
ta fara,sai yai murmushi tare da zamewa kan
katifa da ita a kafad'arshi. Ajiyar zuciya suka
sauke tare da kamo y'atsunta. "Na ce miki _" a
heart dat truly loves never loses hope..but
always believes in d promise of love,no matter
how long d time and how far d distance,at d right
time,love will fine a way".._ "Hope kin yarda da
maganar ba wai soki burutsu Masoyinki bane?.
Kai ta daga mishi halamar ta yadda,tunda ga nan
K'ADDARAR wani zama ya kara had'a su waje
daya. Yau kam ya gama gasa mata jiki da
d'anyun kalaman da ya tanadesu kawai da
Salmanshi,fatanshi Allah ya kare sa6ani a
tsakani. Washegari da t'sant'sar farin ciki suka
tashi,suna kitchen had'a break fast sai nannan
yake da ita. Tashin Miemie suka ji tana kiran
Aunty cikin kuka taga sabon waje. Ganin iyayen
waje daya ita kanta sai binsu take da kallo,
mot'si kad'an ta kallesu,kamar wacce bata so su
rabu da juna suyi rayuwarsu tare. ********** Yau
ziyara aka fito ta sallah ita dasu Ummi, Sun zaga
duk inda ta tambaya saura gida 1 taga sun
karkata zasu shiga gidan kawunsu wanda jiya
sunje. Ja tai ta tsaya tare da ce musu su shiga
su fito dan yau bata tambayi nan ba. Murmushi
Aunty A'i tai tare da kad'a kai,a lalle kullum
Salma hankali na kara zuwar mata. Tuni Ummi
kam tai gaba tana t'saki. Tana nan tsaye
kawunsu ya fito a gidan,bayan sun gaisa yace
mata ya bata shiga ba ga y'an uwanta suna ciki?
Kai a kasa tace "Abba ban tambayi nan ba
ne,dan jiya munzo yini. Murmushi yayi na jin
dad'i, "hakane kinyi tunani mai kyau,Allah ya miki
albarka. Kai ta kara kasa kamin ta amsa. Kud'i
ya ciro daga aljihu ya kirga dubu ya bata,dan
sosai Salma tana wa mutane bazata,yana
matukar son mutum mai gyara kuranshi. "Sannu
da jira uwar y'an ka'ida... Juyawa tayi daga
kallon wani a mota sun tsaya da Kawunsu da ya
wuce yanzu,sai dai kan ta tantance su Ummi sun
fito. Murmushi ta mata tare da basar da zancen
suna tafiya. "Wannan ai wahala ce,ace duk inda
zan shiga sai miji ya ban izinin shiga?.. Kai ta
girgiza, "gaskiya da sake.. Hararar da Aunty A'i
ta mata ne yasa tai shiru. Kallo Ummin tayi da
murmushi, a irin hudubar nan a baya suka
dilmiyarta,ita kwa yanzu a shirye take da yima
Ja'afar biyayya matukar bazata sa6a Allah ba.
Har akaje gida nan ma Ummin ta hau zaiyyanawa
Mama halin da Salma ta tsiro, tuni Mama tai
mata kacha-kacha,Ummi harda kukan takaici
ranar. Da dare yazo ya dauke su,sai taga a motar
Garba da kamar ta ganshi dazun. Taga anje gida
yana kokarin rufe mota da abin rufa sai ta kasa
d'aurewa ta tambayi nan zata kwana? Murmushi
ya mata tare da bud'e gida. Sai da akazo
kwanciya yake sanarta ai shine albishir din dazun
da yace sai sun zo gida. "Ya sai sabuwa ne,sai
mukai cinikin wannan dashi tawan, munyi abin
hawa. Murna tai ba kadan ba tana k'allon
mukullin motar. Ido ya zuba mata yana kallo ba
koh kiftawa. Baki ta kai kan idon tare da hurewa.
"Salma.. Hankalinta ta bashi tana murza
yatsunshi cikin nata. "Daga yau na yard'e miki
koh ba idona ki taka ko'ina u r free... "Dazun
naga komai Salma,ina horn bakiji bane,kin sani
farin ciki dazun kinsa naji ni din na isa gun
matata.. Duk inda ta tambaya nan zata jefa
kafarta. "Sai ganan kuma kawu shima ya labarta
min yadda kuka yi sai murnar wai kin san ya
kamata yake.. "Nagode sosai,yau har kawu
yasan ni mai fad'a aji ne a gidanshi.. Murmushi
tayi tana kara ruk'unk'umo shi. Ta gode Allah da
yasa ta gyara dabi'ar ta maras kyau ta maye mai
kyau. Fatanta duk wata mace mai irin halinta ta
daina,dan ita taga misali akanta. Dan a yanzu
rayuwarta ta fi mata dad'i da kwanciyar hankali,
ta gane yanzu kulle ma wasu matan ke ja ma
kansu, tana fatan kowacce mace ta guji fita a
bisa sharad'in *A BAKIN AURENKI* da suke
yi,dan gudun haifar da saki irin nata mai
gabadaya. Alhamdulillah.. Nan na kawo karshen
littafin A BAKIN AURENKI.. Ina rokon Allah
kuskuren da nayi ya gafarta min. Da fatan
darasin ciki ya isar masu halin Salma za kuma su
gyara,Allahu ya datarmu aikin kwarai a
gidajenmu. Gareku dubin masoyan Feenat
Novel's, na gode kwarai da kaunar ku
gareni,Feenat na son duk mai sonta, dama wanda
bai yinta.. Luv you all. Sai kun sake jina a sabon
littafi mai sunan... *RABO IN YA RAT'SE*...
Nafisa Bashir Tanko, (Feenat Ja'afar) ke muku
fatan saduwa da alkairi.
0 Response to "Abakin Aurenki HausHausa Novel"
Post a Comment