-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

ZUMUNTAR KENAN Hausa novel

ZUMUNTAR KENAN Hausa novel

[6/3, 4:12 pm] Takori: ZUMUNTAR KENAN Hausa novel



Da ka doso garin Giwa gidan za ka fara hanga daga gabas masu kudu na garin, tangamemen gida da aka yiwa jan rufi na zamani mai zagaye da girgijejen gate na bakin karfe da aka fi kira da Mahdi-ka-ture. Dauke yake da (estate) guda wanda ya hadiye gidaje na zamani (flat) guda goma sha biyar.

Idan ka daga kanka sama, rubutu ne da aka yi da ruwan gwal mai sheki an rubuta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ESTATE. Gidaje ne reras (dispersed) masu sanyin gani a ido da fenti ruwan gwaiduwar kwai. Gida daya ne ya bambanta da wadannan gidaje guda goma sha hudu wato gida na farko.

Gida na farko ya fi duka gidajen girma, kuma shi kadai ne mai hawan bene. Mamallakiyar wannan babban gida tsohuwa ce ‘yar kimanin shekaru saba’in da biyar mai amsa sunan HAJIYA HADIZA GIWA, wadda ‘ya’ya da jikokinta ke kira da HAJJAH.

Za ka yi mamaki idan ka ji cewa, duk girman gidan nan ita kadai ta yi rayuwa a cikinsa a matsayin matar gida, haka duka ‘ya’yayen nan goma sha biyar ita ta haife abinta daya bayan daya, babu dan miji babu dan kishiya a ciki.

Wannan ya faru ne a cewar al’ummar garin Giwa a sabili da kaunar da marigayin mijinta Abubakar Bamalli Giwa ke mata, da kuma kyawawan halayenta da kyakkyawar mu’amala da kowa.

Don haka ne bayan rasuwar A.B Giwa ‘ya’yansa ba suyi maraici mai yawa ba. Hajja ta zamo bango abar jinginarsu, wannan kuma baya nufin cewa sakar musu take yi, a’a, akwai tarbiyyar sannan akwai (discipline) ga duk wani da ko jikan Hajjah.

Babu wanda za ta sakawa kara ya tsallake, babu wanda za ta cewa eh, ya ce mata a’ah. Babu wanda zai zartar da wani hukunci a kan gaban kansa ko iyalinsa ba tare da izininta ba.

Mace ce mai kyakkyawan tunani tare da kaifin basira, ta yadda duk wani motsi da ‘ya’yanta ko jikokinta suka yi ta san me suke nufi. Mutum ce kaifi daya ba ta zance ta canza.

Haka duk kaunar da take gwadawa ‘yan jikokinta ba za ta taba yarda karami ya kawowa babba raini ba. Jikokinta suna kaunarta sosai fiye da iyayen da suka haife su. Yawanci da daya da daya suka zame kayansu suka dawo nan (Babban gida kamar yadda suke cewa) wurin Hajja. Don a cewarsu, sun fi jin dadi gidan Hajja, abinci kala-kala kala-kala sai wanda suka zaba, tana kuma basu labaran hikaya da tatsuniyoyi na dabarun zaman duniya, tana rungume su komai girmansu ta rarrashe su ta ji abin da ya dame su idan iyayensu sun bata musu rai. Amma hakan ba ya nufin idan ka yi laifi ta sanya Baban Giwa ya hukunta ka, don dai ita dai ba ta iya dukan jikokinta in ba da mahuci ko rankwashi ba.

Haka nan bayan ran A.B Hajiya Hadiza ta tsaya tsayin daka wajen tarbiyyar zuriyarsa, tare da kiyaye auratayya tsakanin jininshi. Har yau, har gobe Haj. Hadiza na bisa kudurin mijinta A.B Giwa na gama auratayya tsakanin jininshi, suna so ko basa so, in yaso daga baya su suke sanin yadda suke yi su shirya su so juna a bisa dole har su zo suna gode mata.

Hakan ne ya haifar da yaduwa da fadada hadi da watsuwar zuri’ar A.B Giwa cikin garin Giwa da wajenta, inda kuma duk suka shiga dole a gane su, saboda kamanninsu da tsagin Mallancinsu dake gefe da gefen fuskar kowannensu, wanda wanzamin gidansu ke yiwa kowane yaro da kowacce yarinya ranar radin sunansa. Duk da cewa sun kebe kansu cikin Estate dinsu, sana’ar neman abinci ko aikin gwamnati na fiddasu cikin garin Kaduna ko Zaria

A cikin gidan A.B Giwa, bayan jikokinta akwai dangin mijinta mai rasuwa, ‘ya’yan ‘yan’uwanta Kaltume da Kubra, dukkansu zawara ne. Kuma da yake sun manyanta sai suka zamo masu jibantar ayyukan gyaran gidan da harkar dahuwar abinci, duk da akwai wadatar masu aiki a gidan.

Bangaren ‘ya’ya maza (Boys quaters) shi Hajja ta ware daga farkon gidan wadanda ga gidajen iyayensu amma sun gudo sun tare mata har girmansu. Sauran jikokinta ‘yammata da suka tasa duk ta aurar dasu a nan cikin Giwa ko Zaria da jininsu, mafi yawa na cikin Zaria, ‘ya’yan Hajja goma sha hudu ne, maza goma mata hudu.

Abubakar Bamalli Giwa hamshakin mai arziki ne na da can-can shekaru aru-aru da suka wuce. Asalinshi Bamalle ne na garin Giwa, iyaye da kakanni, sana’arshi noma ne na kayan abinci (crops production) su masara, gero, achcha, dawa, alkama, shinkafa, dankali, doya da kayan miya, su yake nomawa duk shekara a loda a Daf-Daf zuwa kasuwannin garuruwa masu bukata.

Ya mallaki tafka-tafkan gonaki sama da goma a cikin garin Giwa, wadanda shima gadarsu ya yi. Gidajen haya bila adadin a cikin Giwa da Kaduna, har ma da Zaria.

A duk shekara ya kan nome amfanin gona mai yawan gaske, a nan ake loda su a buhunhuna zuwa kasuwannin garuruwa daban-daban.

Zai yi tsayi in fayyace ko in lissafo sunayen zuri’ar Abubakar Giwa daya bayan daya, amma babban su shine Alh. Mukhtar Abubakar Bamalli wanda ke jagorantar reshen BAMALLI FOOD CROPS AND CASH CROPS PRODUCTION na Kaduna, wato wakilin kasuwancin kayan gonarsu na reshen jihar Kaduna baki daya, don haka zaman shi da iyalinshi ya fi yawa cikin kaduna, duk da gidansa na nan cikin A.B Bamalli Estate, in sun zo sallah ko biki budewa kawai suke yi su share su shiga.

Sai Ahmadu A.B Proffesor ne a jami’ar Ahmadu Bello a tsangayar harkokin noma da kiwo, gidansa na nan cikin jerin gidajen malamai na A.B.U Zaria, kamar Baban Kaduna (Alh. Mukhtar) shima gidansa ne na biyu a A.B Bamalli Estate. Yadda Alh. Mukhtar ke zuwa da iyalinshi suyi kwanaki ko sha’ani, haka yake zuwa da nashi.

Alh. Na’ibi Abubakar Bamalli ke bi mashi, gidanshi na nan cikin Estate shi ke kula da gonakinsu. Sai Ibrahim A.B, mai kula da gidajen hayarsu na cikin Kaduna. Barau A.B shine ke kula da Distribution (rarraba) amfanin gonakinsu zuwa garuruwa, shima cikin Estate yake shi da iyalinsa. Sani A.B, Sadi A.B da Salisu A.B, kowanne da bangaren da yake jagoranta cikin hanyar neman abincinsu.

Sai Aunty Hauwa wadda ke auren dan aminin marigayi A.B wai shi Alh. Sabi’u Kwangila da ‘ya’yanta biyar, suna nan cikin Kaduna a unguwar Malali. Yaya Ladidi ke bi mata, ita kuma Zaria take aure unguwar Tudun Wada. Sai Yaya Hafsatu dake aure nan cikin Giwa. Aunty Rabi (autar Hajjah) ita ce kadai mai karancin shekaru a cikinsu. ‘Yar kimanin shekaru ashirin da bakwai, shekarar baya ne aka yi auren ta da Yaya Muftahu dan kanin A.B wanda aiki ya hulla shi Kano, yana aiki da gidan wayar Zain.

Kwari irin na Hajiya Hadiza wannan ba zai rasa nasaba da jin dadin da take samu wurin ‘ya’yanta ba, domin a kulli yaumin kamar ana kara mata kwari da kuruciya ne, ba za ka yarda da tarin shekarun da take dasu ba a fuska da yanayin jiki. Ita kanta ba dukiya kadan ta mallaka wurin marigayin mijinta ba, iyayenta da kakanninta ‘yan asalin Zaria ne tushen unguwar Tukur-Tukur.

Marigayin mijinta Alh. A.B Giwa shine dan garin Giwa ba ita ba, ita aure ya kawo ta. Haka bayan ranshi ba ta tsallake ta bar wannan muhallin da suke ciki ba ita da ‘ya’yanta. Tana kokarin hada kansu ba tare da sun yiwa mahaifinsu nisa ba, don kara killace zumuncin su. Basu aure mace ko namiji sai cikin zuri’ar su (jinin su).

Wannan ne ya sanya suke kama da juna, inda duk ka gansu in ka san daya daga cikinsu za ka gane su. Farare tas-tas masu dogon hanci da yalwar idanu da garin jiki (girma da tsayi). Da an gansu an san su, in ba ta tsagin ba ta kamannin, in ba ta kamannin ba ta jin kai da yanga, daga matansu har mazansu.

Mutane da yawa kan ce zuri’ar A.B sun fiya girman kai da dagawa, amma a zahiri nutsuwa ce kawai da Allah ya haliccesu da ita da tsabar sanin ciwon kansu, domin dukkaninsu ilimi na Muhammadiyya da na zamani ya wadaci kwanyar su. Har kullum arzikin A.B karuwa yake, domin basa wasa da hakkin Allah cikin dukiyoyinsu (Zakkah).

Har zuwa inda yau ke motsi tun bayan ran marigayi A.B, ba a ko taba kwatanta auren bare cikin zuriyar sa ba, don a ganinsu auren bare zai bata musu family, zai jawo rarrabuwar kamanni, ya rarraba musu kan ‘ya’ya, kuma ya haifar da sauyin kamanni cikinsu.

Hajjah duk da kasancewar mace ce mai fada a yawancin lokuta, amma fa in ka iyawa halinta ka fahimci likes and dislikes dinta, to ta fi ruwan sha saukin sha. To haka gaba daya ‘ya’yanta suke lallaba ta, suke faranta mata, ba ta da  ciwuwwukan da tsofaffi ke fama da shi ko daya irin su sukari, ciwon kafa, hawan jini ko rikicewar girma. Musamman babban danta Alh. Mukhtar ya fi kowa iya zama da ita da tattalinta da yi mata biyayya a bisa dukkan umarninta.

A cikin Estate din akwai babban masallacin da suke haduwa suyi dukkan salloli biyar a kan lokaci, bangaren maza daban, an sanya labule tsakaninsa da bangaren mata. Yaransu da manyansu da wuya ka ga suna sallah a cikin gida in ba da wata babbar lalura ba.

An hore su da sallah da kula da lokacin yin ta. Da zarar Baba Barau (Limamin A.B Mosque) ya yi kiran sallah kowa zai aje abin da yake yi ya je ya daura alwala ya tafi masallaci ya bi jam’i, maza da mata, yara da manya, ‘yammata da samari.

A gefen masallacin karamin clinic dinsu ne (dakin shan magani ne wanda suke biyan likita guda duk wata da Nurse suke kula da lafiyarsu da ta yaransu akai-akai). Haka main market Giwa bangaren kayan abinci duka rabi shagunan Bamalli ne, suna hada-hadar tafiyar da harkokin kasuwancinsu rai kwance, hankali kwance.

Dukkan mazan fannin aikin noma suke karanta (Agricultural Engineering ko Agriculture Science) a jami’ar Ahmadu Bello. Matan ne kowacce da bangaren da ta karanta, Aunty Hawwa  ta karanci Quantity Surveying ne, Ladidi Education, malamar makaranta ce. Yaya Hafsatu Home Economician ce, Aunty Rabi kuma aikin jarida ta karanta. Da yake Musbahu mijinta a Kano yake aiki ya samar mata aiki a Kano da gidan rediyon Freedom, ko haihuwar fari ba ta yi ba.

Allah ya albarkaci wannan family da nutsuwa da biyayya ga mahaifiyar su Hajjah, babu mai zartar da hukunci a gidansa ko a kan iyalinsa face da sanin ta, da amincewarta. Haka igiyoyin auren da take kukkullawa a tsakaninsu basa ganin bekenta, domin duk wanda ya bi ko ba da son ransa ba, daga baya sai ya ga amfaninsa. Don haka duk cikin samarin da ‘yammatan da suka tasa babu mai tunanin yin budurwa ko nuna ga wanda yake so, sai wanda Hajjah ta ga ya yi mata dai-dai ta hada su.

A halin yanzu dai yara uku ne mata a gabanta da basu haura shekaru bakwai zuwa takwas ba, duka jikoki ne, Ummi, Zanirah da Fa’iza. Samarin maza ‘yan sakandire da na jami’a sune Allah ya yi yawa dasu a gidan. Duk sun baro gidajen iyayensu sun tare a baskwata din Hajjah.

Ba ta nuna damuwa sam, kamar yadda ba ta takura da zaman su, ita dadi ma take ji duk inda ta juya ta gansu, tana bari-bari ko suna hirarsu ta jika da kaka cike da kauna da fahimtar juna.

Dadi take ji ta ga jikokin nan nata sun zagayeta, wannan ya tsokani wannan, wancan ya tsokani wancan, ta yi ta shari’a, ta yi ta bari-bari ko ta kai musu duka da mafici.

Sai dai Hajjah ta raini jikokinta da kyakkyawar tarbiyya ta yadda babu yadda za ayi ka ga karami ya kawowa babba raini, ko ka ga da wuya macen da ta tasa ta zauna kusa da mazan ko kokaye-kokaye, haka nan duk motsin da dayansu zai yi, to a kan idonta ne.

Yanzu kam hankalinta duka yana kan ‘yan matasan jikokin nan nata mata guda uku da suka saura a gabanta ta dage wurin tarbiyyar damu. Wato ni, Ummi (Khadija) da Zanirah.

FA’IZ, Da ne ga babban dan Hajja Alh. Mukhtar, kuma rayuwarshi ta dawo gidan Hajja ne tun daga shekarun yaye ba kamar mu ba. Kaunar Hajjah da Fa’iz daban ce da duk sauran jikokinta, saboda shi kadai ne me sunan marigayi A.B wato (Abubakar), kuma a cewar ta kullum Yaya Fa’iz shine photocopy na A.B Giwa, daga kamanni har halayya.

Fa’iz ya shiga ran Hajja fiye da duk ‘ya’ya da jikokinta. A cewar Hajjah, Fa’iz yaro ne mai shiga rai, kuma mai nuna mata kulawa fiye da kowa a zuri’ar. Komi Fa’iz ya samu na Hajjah ne, baya kyashin kadar da komai nasa wajen faranta mata, musamman kasancewarta ma’abociyar cin farin goro da mu’amala da man zaitun, habbatus-sauda da turaren miski a jiki da tufafinta.

Tun yana karami ya san yadda yake samar dasu gare ta baya bari ta neme su bayan sun kare sai dai wani ya tadda wani, daga Abubakar-Fa’iz da take kira (Hafizi), kasancewar shi mahaddacin Alkur’ani a shekaru na goma sha biyar. Zai kuma iya karya harshe ya karanta shi tiryan-tiryan da dukkan kira’ar Hafizan da muke dasu a Saudiyyah, irin su Abdur-Rahaman Sudaith, Jabir da Abdur-Rahaman Bn Marwan Al-Juhainy da Khusairi.

Fa’iz ne kadai ya yi karatun sakandire a birnin Madinah Al-Munawwarah, daga aljihun Gwamnati. Yana da shekara goma ya yi musabakar izfi talatin daga jihar Kaduna ya samu sponsorship zuwa wata sakandire a Madinah.

Ya dawo gida yana da shekaru goma sha bakwai, ya kuma zabi gidan Hajjah a matsayin gidan zamansa maimakon gidan mahaifinsa Alh. Mukhtar a cikin Kaduna. Daki guda Hajjah ta ware ma mijinta Fa’iz a Boys Quaters da duk abin da zai bukata, sannan in ta ji shi shiru kullum kafarta na hanyar dakinsa don ganin “ko lafiya Hafizi baka shigo ba?”

Sai ya ce, “Akwai abin da nake yi ne Hajja, zan shigo anjima kadan”. Haka suke a kullum.

Zanirah kanwa ce ga Fa’iz, wato ita ma diyar Baba Mukhtari ce, zamanta gidan Hajjah ya samo asali ne tun wata tafiya da mahaifiyarta Mama ta yi aikin Hajji tana shekara hudu ta kawowa Hajja ita. Bayan dawowar Mama kiri-kiri Zanirah ta ki gidansu. Ita da Jabi Road sai hutu, shi din ma ba kowanne ba, sai wanda ta ga dama.

Babban Yayansu shine Bashir wanda ke karatu a matakin farko na jami’ar Ahmadu Bello, sai Fa’iz wanda a bana ne ya kammala sakandire, Abdulhakim ke bin Fa’iz, sannan Shu’aib, Yahaya, sai Zanirah da autansu Abbas da muke kira (Junior).

Khadija (Ummi) ita kadai ta fara cin sunan Hajja a cikin mu. Diya ce ga Aunty Hauwa dake Kaduna. Ummi tun tana shekara biyar Aunty Hauwa ke kawo ta hutu wajen Hajja su hadu ita da Zanirah suyi ta wasa, zuwan ta ya zama akai-akai duk hutun makarantar boko. Da dai Ummie ta gane irin dabdalar da yara sa’o’inta ke yi a gidan Hajja sai ta yiwa uwarta tawaye ta shiga ihu da tirjiya duk lokacin da aka zo tafiya da ita gidansu.

In kuma aka takura mata tafiyar, to a ranar duk gidansu ba mai barci da shesshekar kakanta har da shidewa. Dole iyayenta suka hakura da kulafucinta suka bar ma Hajja.

Ni FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA, ina daya daga cikin jikokin A.B Family, kamar yadda na fada a baya, mahaifina shine da na biyu a ‘ya’yan Hajjah wato Professor Ahmadu Bamalli na jami’ar Ahmadu Bello. Auren zumuncin Bamalli shi ke tsakaninshi da Mamana Maimunatu da muke kira Momin ABU, shi kuma Baban ABU. Nice ta fari, sai Abdallah, Walida ke bin Abdallah. Yayin da Kausar ta kasance autarmu.

Momi ma’aikaciyar jinya ce ita a asibitin koyarwa na Zaria (ABUTH). Tsananin rashin kulawarta gareni wai don nice diyar fari, kunya da kawaici mai sawa a hantari yaro ya sanya Babanmu ya dauke ni daga gabanta tun ina shekaru biyar ya bai ma Hajjah.

Nima dama na fi son gidan Hajja, ko don su Zanirah. Sai muka dunkule mu ukun nan muka bude rayuwar da ta caza kwakwalen iyayenmu a gaba da kakarmu Hajjah. Ta yadda babu ranar Allah da za ta fito ta fadi bamu bar abin fadi ba, domin dukkaninmun nan kowacce da halinta, muka kuma hadu da maganinmu Ya Fa’iz ta yadda babu ranar Allah da ba zamu barta ba tare da Hajjah ta yi shari’a ko rabon fada a cikin ta ba.

Ba zan manta ba, a ranar da zan koma Giwa ban iya na yi barci ba saboda doki da murna, da asubar fari kuwa na shiga bubbugawa Babanmu kofa ya fito mu tafi Giwa kafin su Zanirah su tafi makaranta.

Don haushi Momi fitowa ta yi ta mammake ni ta kuma ce ba za a tafin ba sai sha biyun rana. Haka na wuni ina duba agogo ina zumburar baki, domin dai har sai da Baban ABU ya shiga cikin makaranta ya fito sannan muka taho Giwa (makyankyasarmu).

Muna zuwa kuwa na gayawa Hajja abin da Momi ta yi min, ta ce (ya yin da ta rungume ni) “Ki barta daga yau ganinki ma sai ta cike form, tunda ba ta sonki ni ina sonki. Da kafarta za ta zo neman ki, ki zuba ido”. Ni kam na san abin da ba zai taba yiwuwa bane Momin ABU ta wanko kafa ta zo Giwa domin ni, sai in tata ce ta kawo ta.

Na ce, “Hajja ina su Zanirah ne? Tunda na zo ban ji duriyarsu ba”. Ta ce, “Suna Islamiyya yanzu za ki gansu, kema in Allah ya kaimu gobe Babanku na Giwa (Baba Barau) zai amso miki form daga boko har Islamiyyar ku dinga tafiyar ku tare”. Na shiga tsalle ina murna.

Daga nan na shiga kitchen din Hajja na soma bude kuloli da kwanuka ina tsame namomin dake kan abincin ina cinyewa, Hajjah na falo ba ta sani ba. Ni Allah ya halicce ni da shegen son nama kamar mage, Momin ABU kan ce kamar mayya. Don haka ko da nake Zaria Hajja kan sa ayi mani dambun nama mai yawa ta aike mani cikin samira duk sadda Babanmu ya zo gaishe ta.

Dai-dai sanda na bude wani madaidaicin (food flask) ruwan kasa Hajja ta shigo. Na kai hannu zan dauke cinyar kazar dake kai Hajjah ta rike hannuna tana murmushi, ta ce, “A’a, an cinye na kowa to ban da na Hafizina, haba Fa’iza? Don ya ga naman nan tun kafin a dafa shi ba zai zama haramiyarsa ba, dole ne ya ci cinyar kazar nan”.

Na dube ta rike da murfin flask a hannu daya, daya rike da cinyar kaza cikin mamaki na ce, “Hajja waye kuma Hafizi da ya fi kowa da za a sawa kowa abinci a kwanon samira shi a zuba mishi food flask?”

Hajja ta ce, “Fa’izu mana, dole ne a girmama Hafizin Qur’ani. Balle Fa’iz da duk ya fiku sona, ku baku yi min sai dai in muku, Fa’iz fa? Naman nan ko idan kika sake kika ci in dai Fa’iz ne sai kin amayo shi”.

Na soma yagar cinya ina ci abuna, na ce, “Hajjah ai dama ke kike daure masa yake cin zalin mutane, don bakya ganin laifinsa, kina fifita shi a kan kowa”.

Hajja ta ce, “Ba na gani din, na fifita din”.

Na cinye nama na bi lafiyar gado, ba jimawa barci ya kwashe ni, Hajja ta shiga harkokinta.

Hayaniyar su Ummi da Zanirah ce ta tada ni.... “Ehu! Fa’iza? Don Allah Hajja da gaske? Da gaske kike Hajjah ta dawo nan da zama?”

Ban ji amsar da Hajja ta basu ba, Zanirah ta fyallo a guje ta daka min duka a baya, na tashi wurgigi a firgice, sai kuma muka dafe juna muna kyalkyatar dariya.

Bayan sallar isha kowacce ta bude kwanonta za ta ci abinci, Ummi ta ce, “Shegiya Fa’izah dama tunda na ga kwanukan nan lami na san kin zo garin”.

Zanirah ta ce, “To meye don ta ci namanmu bayan kin samu ma ta zo? Da kafin ta zo ba cewa kike dama Fa’iza ta zo hutun nan muje muyi shi gidan Baban Kaduna ba? Wai inda ita tafiyar tafi daxi? Amma yanzu daga zuwan ta kin fara yi mata korafin cin nama?”

Ummi ta harare ta, ta ce, “Ka ji ta kamar gaske sai wani kakkare ta kike, dama ban san halin bane, gobe ne zuwa jibi za a fara rabon dambe tsakaninku”.

Dai-dai lokacin Fa’iz ya shigo yana sanye da ruwan madarar jallabiya da carbi a hannunsa, farin yaro tas kamar haifaffen Da’ifah, matashi mai garin jiki irin na zuri’ar A.B Giwa. Hancin nan mikakke har baka, kanshi akwai tarin suma. Gefe da gefen fuskarshi tsagin mallancinshi ya fito radau, dogo mai tsayi da kafadu tun a wancan kananan shekarun.

Da gani daga masallaci yake rike da tasbaha a hannunshi na dama. Shigowar shi ta katse Ummi da Zanira daga musun su, ya wuce ko kallon mu bai yi ba kai tsaye zuwa kitchen ya dauki filas dinshi ya fita.

[6/3, 4:12 pm] Takori: Jim kadan sai ga shi ya dawo a fusace, ya dangwara min ma’adanar abincin a cinya yana zazzare fararen idanusan wadanda tun a wancan lokacin suke da wata irin baiwa ta kwantaccen ruwa kamar hawayen da bai kai ga zubowa ba a cikinsu, da babbar murya ya ce, “Ke kwalamammiya amayo naman da kika ci ko billahillazee in yi kuli-kulin kubra dake yanzu a gidan nan, in lallasa ki dukan da uwarki ba ta taba yi miki ba”.

Na ma rasa me zan ce don mamaki da takaicin ambaton uwata da ya yi, haka Ummi da Zanira sunyi wuri-wuri. Ya ci gaba da magana cikin bala’i.

“Kazamar banza mai kashi a wando, wa ya ce ki sa min kazamin hannunki cikin abincina? Tunda ma kika saka wannan kazamin hannun naki wanda ya saba yin dama-dama da kashi cikin fo ba zan ci abincin ba....”

Ya daga kwanon shinkafa da taliya da miya ya zazzage min a tsakar kaina, ya ja dogon tsaki ya wuce yana cewa, “Dama dai kwalamammiyar nan ba ta zo gidan nan bane za a tadda kwayar nama cikin abinci. Ni kam shekarar bakin ciki ta zo min in dai da wannan mai kashi a wandon zan zauna cikin gidan nan. Mtsw!”

Ya yi ficewarsa yana ci gaba da bambamin fada da muryarshi mai karyayyen harshen larabawan Hijaz, Hausar shi ba ta fiye fita sosai ba.

Na fashe da kuka nan take, don ni babu abin da na tsana a rayuwata irin a ce min mai kashin wando (da gaske mai kashin wandon ce a baya, har na kai shekara biyar ban san idan na ji poo-poo in dauko fo in hau ba, sai dai in saki abuna a wando. Hajja da Momi sunyi fadan har sun gaji, kuma a wancan lokacin babu pampers sai napkin, haka su Inna Kubra dake gidan za suyi ta aikin kashi da yi min wanka a famfon wajen wanke-wanke).

Tun a wancan lokacin ne bama ga maciji da Fa’iz, kasancewarshi mai masifaffiyar tsaftar gaske da kyankyami. Ya dauki tsana da hantarar duniya ya dora a kaina, duk inda ya ganni sai tsawa da raraka yana toshe hanci. Ban samu sa’ida a zaman gidan Hajja ba sai da Fa’iz ya wuce babbar sakandire a Saudiyaya.

Su kam su Zanira dariya ce ta kama su suna makewa bayan wucewar Fa’iz, don sun san halina in ina cikin fushi kayi min dariya a kanka zan huce.

Da na kai karar abin da Fa’iz ya yi min wurin Hajja a uwar dakinta tana lazimi cewa ta yi Allah ya kara, ai na gaya miki amma da yake kunnen kashi ne dake sai da kika ci. In gaya miki wannan dabi’ar banza ce, ki daina ta. Kada ki kuma cin rabon wani bayan rabonki haramun ne. Ni bai burgeni ba ma da bai shake ki kin amayo shi ba.

Washegari Baban Giwa ya amso min transfer daga makarantarmu (ABU Staff School Primary School) zuwa ta su Ummi wato GIWA SOUTH PRIMARY SCHOOL. A rana ta farko da na fara zuwa Giwa South Primary na dawo da damuwa mai yawa, basu yin Arabiyya ko kadan, babu Arabic a darassanmu sabanin Staff School da muke zuwa ni da Abdallah a Zaria.

Shigowarmu gida ke da wuya na watsar da littafan a falon Hajja na zauna shirim ina ta zumbura baki. Hajja dake rike da littafin Bulugul-Maram da Medicated glass a idanunta tana karantawa ta dago ta dube ni ta ce, “Lafiya?”

Na yi tsaki na ce, “Bari ke dai Hajja....” Kafin in karasa sai ga Yaya Aliyu, Yaya Bashir da Yaya Fa’iz sun yaye labulen falon sun shigo, kowannensu dauke da sallama a bakinsa. Sun sha anko na farar shaddah (Hilton) sai salki take.

Hajjah ce ta amsa musu, kana ta ce, “Har an daura auren?”

Suka zazzauna cikin duma-duman kujerun falon, Basheer ya ce, “Eh, alhamdulillah an daura Hajja. Sadaki naira dubu dari Baban ABU ya biyawa Usman (Dan Baba Barau da ‘yar Baba Ibrahim Maryam aka daurawa aure). Sai fatan Allah ya basu zuri’a dayyaba da zaman lafiya da yalwar arziki mai albarka”. Duka suka ce, “Ameen”.

Yaya Aliyu da yake duk mun fi shiri da shi ya dube ni a nutse ya ce, “Hajja lafiya Fa’iza ke fushi?”

Hajja ta ce, “Gaka gata nan tambaye ta mana, nima haka ta shigo min”.

Ya dawo da idonshi kaina alamar sauraro ya ce, “Wa ya tabo min Fa’iza ta?”

Na tura baki sosai na ce, “Bayan makarantar su Ummi ba a yin Larabci sai Turanci”.

Duka suka sa min dariya ban da Fa’iz da ya ce, “Ji ta don Allah baka kirin da ita, duk gidan nan ita ce mummuna, ko meye gamin ta da Larabawa oho?”

Bashir dariya yake shi da su Ummi, Yaya Aliyu ya ce, “Rabu dasu Fa’iza, ai black is beauty. Na rantse dukkan su babu wanda zai samu mata mai kyan ki. Na yi alkawarin canza muku Islamiyya wadda ake koyar da Larabci sosai kin ji Fa’iza na?”

Kuka nasa sosai, ba abin da Fa’iz ya fadi bane ya sani kuka, a’a, na tsani ayi min gwasale cikin mutane. Shi kuma Ya Fa’iz na lura baya shakkar a gaban kowa ya ci mutuncina.

Halinshi sam ba irin na Yayan shi Bashir da Yaya Aliyu Haydar bane, in ya raina ka kawai ya raina ka, in ya tsane ka sai ka gwammace ko hanya ba ta gama ku ba balle jini.

Zama na a gidan Hajjah tare da Fa’iz daga farkon sa har zuwa inda yau ke motsi ba mai dadi bane, kai ka ce babu digon jinin juna a jikinmu.

Fa’iz ya tsaneni on the ground of kazanta, ni kuma na tsane shi on the ground of mugunta. Shi Yaya ne ba mai dadi ba ga kannensa, akasin Yaya Aliyu mai son mu, mai janmu a jikinsa da nuna mana kauna ta ‘yan’uwantaka.

A sannu nake fahimtar kazantar da Fa’iz yake yawan ambatawa a gareni da na soma tasawa. Na farko ban damu da sanya wankakkiyar suttura ba balle gogaggiya, ban san wani abu wai shi kintsi ko gyaran jiki ba. Uwata ba ta ja ni a jiki ta koya min wadannan abubuwan ba, ban san in gari ya waye in tatsa maclean jikin burushi in goge baki ba, sai dai in afa ruwan shayi da burodina in ci.

Ga Hajja tsohuwa ce ba ta mai da hankali kan irin wadannan abubuwan ba, wanka su Ummi kullum sai sun yi amma ni sai in kwana hudu fatar jikina ba ta ga ruwa ba. Balle sabulu da soso, gani kuma daman bani da hasken fata irin na Bamalli, kalar jikina irin na mahaifiyata ne.

Idan na cire kaya ban san wanne ne mai datti ba wanne ne mai tsabta ba, haka zan hada duka in danna su a wardrove dina babu ninki balle kintsi sabanin Zanirah da Ummi su da suke ma goyon Kaka.

Dalili kenan da in Fa’iz na wujijjigani da wulakanci da kaskanci bani da bakin kare kaina sai dai in yi ta kuka da tunanin na yi gudun gara na tadda zago, ko in komawa zagon ne (Momin ABU), amma in na daga ido na dubi Ummi da Zanirah na tuna irin kewarsu da zan yi idan na bar Giwa, sai in manta da al’amarin Fa’iz in shigar harkokina, in kuma yi kokarin kaucewa duk wata hanya da za ta sada ni da shi a gidan don in zauna lafiya.

Lokacin da muka gama makarantar firamare muna da shekaru goma sha biyu, muka samu gurbi a FGGC Gusau aji daya. Da yammacin ranar Yaya Aliyu ya shigo falon Hajja muna kallon shirin Risalah (The message) daga tauraron dan Adam ba tare da mun juyo ba duka suka amsa sallamar shi amma ban da ni, domin a lokacin ina gefen Ummi ina kuka sosai ni ba zan je makarantar kwana ba, Hajja da su Zanirah sun yi rarrashin duniya na ki yin shiru.

Hajja ta ce da Yaya Aliyu a sanda ya zauna, “Yanzu nake cewa Ummi ta kira ka ku je kanti su hado duk abin da za su bukata nima nan na yi musu duk nawa tana din  na su yaji da soyayyar miya, dambun nama na Fa’iza da su garin rogo ko za su bukace shi, to mutuniyar taka gata nan ta ja ta kafe ba ta zuwa makarantar kwana, ba ta kuma fada ba sai yanzu da aka gama musu komai gobe tafiya”.

Yaya Aliyu ya matso gefena ya zauna a hankali yana dubana ina ta share hawaye da majina da habar zanina, jikina na tashin tsamin tashen balaga da rashin wanka.

Ya ce, “Princess Fa’iza Bamalli, gaya mani matsalarki ta kin son makarantar kwana a yau, bayan a da baki ce hakan ba....”

Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu Ummi ta ce ana saka yara yin kitso duk sati, yanke farce duk sati, wanka kullum, kuma dole kullum sai ka yi brush safe da dare, ni gaskiya za a takura min, wallahi ba zan iya ba.....”

Su Ummi suka bushe da dariya har shi Yaya Aliyun. Daga bayanmu muka ji an saki wani dogon tsaki, dukkanmu muka juya, Yaya Fa’iz ne.

A hasale ya ce, “Yaya Aliyu don girman Allah ka fita hanyar yarinyar nan mahaukaciya ce. Raina yana matukar baci idan na ga kana shiga sha’aninta. Ni wallahi ba don kamanninta da Baban ABU ba sai in ce canza ma uwarta ita aka yi a asibiti can inda take aiki suka hada baki aka bamu”.

Fuskar Yaya Aliyu ta rine da bacin rai, ya dubi Fa’iz a hankali amma ya kasa cewa komai. Hajja ce ta ce, “Hafizi! Wacce irin magana ce wannan? Kada in kara jin makamanciyarta”.

Ya sadda kai ya ce, “Allah ya huci zuciyarku Hajja, amma yarinyar nan na bukatar makarantar kwanan da ba ta so, don kwata-kwata ba ta san ciwon kanta ba, uwarta ta jawo mana baragurbi cikin zuri’a. Kaico! Auren bare bai yi ba wallahi.....” Ya juya ya yi ficewar sa.

A fusace Yaya Aliyu ya mara masa baya, ya suka karke ya suka kare oho! Ya dawo fuskarshi babu annuri, ya ce (ba tare da ya dubi kowaccen mu ba) “Ku tashi maza mu tafi sayayyar”.

Yanayin yadda na bude motar cikin matsanancin fushi ya sanya Yaya Aliyu juyowa sannu a hankali ya dube ni na ‘yan dakikai, sannan ya sanya ma motar giya muka harba kan titi.

Babban Super Market din wanda ke kan hanyar fita garin Giwa kusan duk garin babu kantin da ya yi girma da habakar ta. Babu abin da babu na bukatun yau da kullum. A nan Ali ya yi parkin duk suka fita, ban ko yi motsin dake nuna inada niyyar fitan ba, zuciyata da tunanina duk da karancin shekaruna sun sanya min ayar tambaya a yau a kan Yaya Fa’iz da kiyayyar da yake yi mun da kuma dangantakar kiyayyar da raini ga mahaifiyata wadda baya jin kunya ko haufin jan sunanta a gaban kowa ya aibata ko ya zage ta.

Mintuna biyu Yaya Ali ya yi yana nazarina kamin ya rankwafo tagar da nake a tausashe ya ce, “Fa’izah ba a fitowa?”

Sai na ji ya yi min wani kwarjini mai yawa yadda ya yi maganar. A hankali na bude murfin motar na fito. Ya yi dariya ya ce, “Yau dai da alama mulki kike ji Fa’iza, ko duk fushin Fa’iz ne har yanzun?”

Ummi ta kulu da bata lokacin da nake yi musu da tarairayar da Yaya Aliyu ke min na yi banza da su, ta ce, “Don Allah Yaya Ali ka rabu da ita sai wani lallashinta kake tana basarwa sai ka ce mu muka kar zomon, ita wace ce?”

Ya yi murmushi ya ce, “Ita Princess Fa’izah Bamalli ya ya ranki?”

Zanirah ta ce, “Me kenan Pincess?”

Ya ce, “Princess yana nufin Gimbiya”.

Ta tabe baki ta ce, “Sunan da Ya Fa’iz ya ba ta ya fi dacewa da ita ba naka ba”.

A kaikaice da baki ya ce, “Wanne suna ne Fa’iz ya ba ta?”

Zanirah ta ce, “Impertinence Fa’izah watau Fa’izah mai tsiwa”.

Ya dubi Zanirah sannan Ummi, ya ce, “Wadda ta sake kiran Fa’izah da wannan sunan ban yafe ba, kun ji ko?” Suka daga mishi kai muka shiga cikin kantin.

Ko da muka shiga cikin kantin kujera na ja na zauna ina kallon su, dauki banza dauki wofi, wani zubin su juyo su kalle ni suyi kus-kus su ci gaba da dauke-dauken su. Shi ko Yaya Aliyu sayayyarsa daban ce da tasu, kwando uku suka cika da kayan zaki masu tsada, hatta biron da zamu yi rubutu basu bari ba.

Muna shiga mota kafin Yaya Ali ya tada motar Zanirah ta ce, “Ummi baki daukarwa impertinence rice pudding ba”.

Na yi kan Zanirah da duka, yakushi da cizo, dama kiris nake jira. Yaya Aliyu ya dakan tsawa ya ce, “Meye haka ne Fa’iza? Don kinga ina lallaminki shine kika koma hauka?”

Idona cike da kuka na ce, “Amma ita ba ka yi mata fadan sake kirana da sunan Yaya Fa’iz ba don kaima ka tsane ni kamar shi, shi kenan....!” Sai a lokacin ne na samu hawaye suka zubo.

A tausashe Yaya Aliyu yana ta da motar ya ce, “Lallai Fa’iza har yanzu shagwabar tana nan? Haka za a kwalejin ana musu?”

Ummi ta ce, “Ta yi mana in siniyoyi basu lallasata ba?”

Muguwar harara na rafka mata ta toshe bakinta da hannun damanta tana “Allah ya huci ran princess”.

Mun kusa shigowa unguwarmu ya ce, “Fa’izah don Allah don Annabi ki dinga hakuri da ‘yan’uwanki kin ji ko? Ko harshe da hakori dole a saba wata rana, ki rage zafin zuciya, kina da zuciya mai zafi”.

Na ce, “Amma shi Ya Fa’iz ba mai yi masa fada kan tsana da tsangwamar da yake yi min a duk lokacin da abu ya shafe ni? Laifina ma kake gani Yaya Aliyu?”

Yana girgiza kai ya ce, “Ba maganar Yayanki Fa’iz nake ba, bana so in ga kina halin yara, you are no more a child now, dambe da kokawa na su Walida da su Badar ne”.

Na zumbura baki ban ce komi ba. Ya ce, “Kin hakura Princess ko kina so na kasa barci saboda fushinki?”

Sai na bude dukkan idanuwana na dube shi. “Yanzu Yaya Aliyu in ina fushi sai ka kasa barci?”

Ya yi murmushi ya lumshe ido tare da daga kai sama. Cikin mamaki na ce, “To saboda mene?” Ya ce, “Saboda me? Saboda abin da kwakwalwarki ba za ta fahimta ba a yawan shekarun ki”.

“Mene shi wannan abun?”

“Wannan abun muhimmi ne mai girma da yaro baya jin shi sai ya girma”.

“To ai Zanirah ta girma in ji Hajjah, tun ranar da jini ya ziraro ta kafarta Hajja ta ce ta girma, to ita ka gaya mata mana?”

Ya yi dan dummm! Zanirah ta soma kumbura hanci da hurashi ta ce, “Yaya Aliyu wallahi karya take Ummi ce?” Ummi ta ce, “Wallahi ita ce”.

A dai-dai lokacin da Yaya Aliyu ya shigar da hancin motar A.B Bamalli Estate, ya yi kyakkyawan horn yaran dake kusa a kofar flat din Baba Barau suka rugo suka fidda kayan a boot suka shigar mana dasu gida.

Yaya Aliyu Boys Qtrs dinsu ya wuce bai kara kula mu ba. Su Abba na jidon kaya suna ihu wai za su ci cornflakes din ‘yan bording school. Na ce, “Wallahi duk wanda ya bude mana kaya sai na kabari ya fishi jin dadi”.

Ina kwance gadon Hajja na ji shigowar su Ummi, suka shigo da kaya niki-niki, Ummi cike da tsegumi take ce da Hajjah, “Wai Hajja ki duba ki ga duk yawan kayan nan da muka shigo sai da Yaya Aliyu ya sake sayen kwatankwacinsu wa Fa’iza ita kadai ranta”.

Zanirah ma ta ce, “Kuma Hajja baki gani ba, wai don dan fadan nan da Ya Fa’iz ya yi mata dazu kafin mu fita ya yi ta lallaminta tana masa wulakanci da kada ido, ita ba ta yarda ba babba”.

Hajjah ta yi kamar ba ta ji su ba ta shiga duba kaya, ta ce, “Ya ban ga kwaki ba bayan kun ce bakwa son wanda na sayo fari kuke so?”

Ummi ta ce, “Tab! Waye zai sha miki kwakin? Ki jimu da tsohuwa da neman ta da zaune tsaye”.

Hajjah ta dauki mafici ta yi kanta ta runtuma da gudu. Hajjah ta ce, “Ja’ira, gobe dai kun barni da ‘yan jikokina mu huta bakinmu alaykum. Haba! Yara uku duk kun bi kun isheni kamar ina zaune da zaratan ‘yammata”.

Ummi ta zo ta kwanta a gefena ina kwance rigingine na yi nisa cikin tunanin irin kulawar da Yaya Aliyu ke yi mani. Hakika shi dan’uwa ne mai matukar kirki da dabi’un kyakkyawar mu’amalar zumunci.

A lokuta da dama ina kwatanta kirkin Aliyu da wani cikin yayyenmu, amma ban ga kwatankwacin shi ba. Halinsa daban, simplicity dinsa daban da dukkan mazan zuri’armu.

To amma kulawarsa gareni ta zarta wadda yake yiwa kowa, babban misali su Zanirah da tare muke rayuwa yana fifitani a kansu. Sai a hankali nake jin Yaya Aliyu na kwanta min a zuciya saboda kyawawan halayensa da kulawar da yake yi mun.

Tunani na ya gangara ga abin da ya fadi dazu na cewa, wai ba zai iya barci idan ina fushi da shi ba, saboda abin da yaro baya ganewa sai ya girma. Shin mene ne wannan abun? I’m quite curious....

Kamar Ummi ta san abin da nake tunani, ta yi murmushi sai cewa ta yi, “Princess har an soma tunanin Yaya Aliyu? Ayi hakuri dai muje kwalejin mu gama, in kuma auren za ayi sai a fada mana mu fara shiri”.

Na mike a fusace na soma dukanta ina yakushinta ta sa ihu, nan da nan Hajja ta shigo za ni na zamewa kamar ta fadi. Ta ce, “Wai ke wacce irin masifaffiyar yarinya ce ne Fa’iza? Ke daya duk kin buwayi gidan nan, daga ki yi da wannan sai ki koma ki yi da wancan?”

Na sa kuka na ce, “Hajjah cewa fa ta yi wai ina tunanin aure, ‘yar iska ta dauke ni ko me? Bayan ni tunanin su Walida nake yi”.

Hajjah ta ce, “To yi hakuri wasa take miki, ke kuma Ummi kada na kara jin makamanciyar wannan maganar ta fito daga bakinki zan saba miki fiye da zaton ki”. Ta juya ta fita. Zanirah ta bimu da kallo kurum, sai dai na lura tun shigowar ta dakin akwai abin da ke damun ta.


****

[6/3, 4:12 pm] Takori: Ranar da zamu tafi FGGC Gusau ta kama litinin ashirin ga watan Nuwamba, don haka sanyi ya yi tsanani ainun. Tun asuba muke ta shiri, murna kamar kanmu aka fara zuwa makarantar kwana. Mun yi tsaf cikin uniform abin sha’awa.

Na hade gashina cikin (hair-bound) kalar tsanwa cikin sayayyar Yaya Aliyu ne. Hajja dake azkar din safiya a gefe bisa shimfidar sallarta ta shafa addu’a ta juyo ta dube mu.

“Yanzu duk wannan azarbabin da kuke wa kuke zaton cikin yayyunku zai mike cikin wannan azababben sanyin ya kai ku makarantar?”

Na ce, “Wallahi babu kam Hajjah, ai Isa direba ba zai ki ba. Ko ya kika ce Ummie?”

Ummi ta ce, “Kwarai”.

Zanirah ma ta shirya cikin uniform na GGSS Giwa, kasancewar ita makarantar ta daban ta gwamnatin jiha mune a gwamnatin tarayyah.

Riga da zani da hijabi shudi da fari, ta yi kyau abinta. Na tuna da banki na da nake tara kudi a ciki da na baiwa Yaya Aliyu amanarsa tun wancan satin. Na ce, “Hajjah ko Yaya Aliyu ya tashi yanzu? Bankina”.

Hajjah ta ce, “Tabdi! Aliyu makiyin sanyi ko na ruwan sha shine zai mike miki yanzun? Karfe shidda?”

Na janyo farin cambas na daurawa kafata na yo tsakar gida da niyyar daukar suwaita ta a kan igiya da na shanya tun jiya. Cikin muku-mukun sanyin nan ma’abocin hazo da ya lullube sararin samaniya, sanye da bakar shirt da shudin wando jeans ya daura ‘thick-coat’ doguwa har gwiwarsa, hannayensa duka zube cikin aljihun coat din domin kare sanyi, yana jingine jikin tagar dakin Hajjah. A hankali na ambaci sunansa cikin mamaki.... “Yaya Aliyu?”

Ya lumshe idanunsa da suka kumbura suntum saboda rashin isasshen barci.

“In kun kammala Fa’iza ku fito in kai ku, ku nake jira tun bayan fitowata masallaci sallar asubahi”.

Ban ce komi ba na karasa na dauki suwaita ta na koma ciki. Da na gayawa su Ummi Yaya Aliyu ne zai kaimu duk sun yi mamaki suma, Hajjah ba ta ce komi ba.

Zanirah muka fara rakawa kasancewar nan wajen gari ne, bayan an kammala mata (registration) an ba ta hostel an hadata da wata prefect muka juyo zamu tafi, idon Zanirah ya cicciko da hawaye.

Ta ce, “Yanzu Yaya Aliyu don Allah kwana nawa zan yi a nan?”

Muka yi dariya duka ganin yadda hawayen ya soma malalowa a kundukinta. Yaya Aliyu don ya kwantar mata da hankali ya ce, “Haba Zanirah? Ga ki ga gida meye abin damuwa ne? Bayan haka ma na yi miki alkawarin duk sati biyu zan rinka zuwa in ganki, zamu ke zuwa miki visiting duk wata har da Hajjah”.

Ta soma sharar kwalla muka rungume juna, sannan prefect din da aka hadata da ita ta ja hannunta suka shige ciki. Bamu tafi ba sai da muka ga kulewarsu.

A kan hanyar Gusau Yaya Aliyu ke ta tsokanarmu ni da Ummi, sai dai jiki da bakin kowaccenmu ya yi sanyi, kai baka ce ‘yan karadin nan na Hajjah bane masu kama da jiniya don kwakwazo a falon Hajjah ba.

Wala’allah hakan na da nasaba da rabuwarmu da Zanirah da tunanin sabuwar rayuwar da zamu je mu taras, ta doka da oda ba irin ta gida gaban kakarmu abin son mu Hajjah ba.

Ya tsaida motar a wani masallaci muka yi sallah, ya ce, “Ku dan jirani ko?” Ya tsallaka daya titin ya dawo mana da gasasshen nama da gorar ruwa da ta pepsi, muka ci muka ci gaba da tafiya.

Ummi na ta yi min hira na ki kula ta saboda kewar Zanirah. Ta yi tsaki ta ce, “Aikin banza ana ta yi miki magana kin yiwa mutane shiru ke wace ce?”

Na ce, “Nice Pirincess Fa’iza Bamalli”. A hankali yadda Yaya Aliyu bai jimu ba.

Ummi ta ce, “Umh! Ya Aliyu ka ji yau Fa’izah ta fadi sunan da ka rada mata?”

Idonshi a titi ya ce, “Ki bari don Allah?”

Ta ce, “Wallahi”.

Ya ce, “Kara fadi in ji Fa’iza”.

Na sanya fuskata cikin tafukana ina dariya. Ni yadda Yaya Aliyu ke nuna mana kauna da kulawa irin haka sai nake jin zuciyata na kara kaunarsa a kowacce dakika. Ina ma a ce Yaya Aliyu ya ce yana sona? Ina ma ya zamo miji a gare ni? Da wace irin sa’a zan yi a rayuwata?

Kamar ya san kallon shi da tunaninshi nake, sai kawai ya juyo muka hada ido, na yi saurin juyar da kaina ga titi.

Ya yi murmushin da ya motsa kyakkyawan sajen da ke gefe da gefen fuskarsa, ya ce, “Kallon na mene ne?”

“A kan me zan kalle ka Yaya Aliyu?”

“Nima abin da nake son sani kenan Fa’iza, dalilin kallon?’

Na zumbura baki na hura hanci. Ya yi dariya ya kara speed din motar, bamu kara tsayawa ba sai a FGGC Gusau.

Bayan ya gama mana duk shige da fice da ake yi daga ofishin vice zuwa na principal, aka bamu hostel daki daya ni da Ummi, amma ba aji daya ba. Ina A tana B.

Sai da Yaya Aliyu zai tafi Ummi ta ce, “Yaya Aliyu mai yasa aka raba mana aji?”

Ya yi murmushi ya ce, “Saboda ku yi karatu sosai in bakwa ganin juna akai-akai, amma idan an hada ku za ku shagalta da hirar gida ku ki yin karatu”.

Ummi ta ce, “Wa ya ce dasu gidanmu daya? Ga sunanmu ba iri daya ba, ni Khadija Sabi’u Giwa, ita Fa’izah Ahmad A.B Giwa?”

Ya nuna mata tsagin mallancinta, ya kuma ja dogon karan hancinmu da hannayenshi hagu da dama, ya ce, “Kowa ya ganku ya ga wadannan to ya san tushenku daya, kuma in har bazazzage ne to ya san zuri’ar A.B ne”. Jinjina kai na yi cikin gasmuwa da kalamansa.

Bayan Yaya Aliyu ya mana sallama, har ya juya zai tafi sai kuma ya juyo, idanuwanshi sun sauya launi daga farare sol zuwa na damuwa,  “FA’IZAH!” Da wata murya tamkar ba tashi ba.

A hankali na juyo na ce, “Na’am Yaya Aliyu!”

Ya ce, “Zo”. Tare da yafito ni da hannun daman shi. Na saki hannun Ummi na je gare shi muka tsaya muna kallon juna kamin in sadda kaina kasa a dalilin nauyin da kwayar idanunshi yai min.

‘Yan dakika kamin ya ce, “Ki daina kazanta, ki aje wasan da ke kanki ki tsaya ki yi karatu, ki zama mai kokari irin Zanirah kin ji ko?”

Idona taf da hawaye na ce, “Yaya Aliyu kazantar me nake yi? Mene ne KAZANTA?”

Bai bata lokaci ba ya dora da cewa, “Kula da tsaftar jikinki, kamar yadda zuciyarki take da tsabta. Ubangiji yana son tsabta ta yadda har ya mai da ita cikon addini. Tsafta ta hada da tsaftar jiki, da ta suttura, da zuciya baki daya.

Tsaftar jiki ita ce, kula da baki (yin brush a kalla sau biyu a rana, wato safe da dare). Tsaftar fatar jiki (yin wanka da sabulu mai kamshi shima a kalla sau biyu a rana, da yawan amfani da sinadaran dake kashe warin jiki na halitta (body odour), wadannan sinadarai duk na sanya su cikin sayayyar da na yi miki (mouth wash, deodorant spray da roll-on) da turaren fesawa a tufafi. Tsefe kai da wanke shi da yin kitso duk sati, kina jina Fa’iza ta?”

Na daga mishi kai ba tare da na iya duban shi ba sakamakon wata matsananciyar kunya da ta taso ta Yaya Aliyu ta lullube ni a dalilin kalaman shi.

Ba tare da ya saurari cewa ta ba ya ci gaba da cewa, “Don Allah Fa’za ki tsaya ki yi karatu sosai kin ji? Wallahi bana son na ashirin din nan da na talatin da kike dauka a jarrabawar firamare ko na goma sha kaza.....”

Na dago na dube shi idanuna fal da hawaye, na ce, “Insha Allah Yaya Aliyu zan dage ko don ka ji dadi ka daina jin haushi in Ya Fa’iz ya kirani Jaka! Insha Allahu ba zan kara kaiwa na ashirin ba ma har in kare makaranta..... insha Allahu ba zan baka kunya ba.... insha Allah sai ka yi alfahari dani fiye da yadda Ya Fa’iz ke alfahari da Zanirah!”

Ya yi murmushi ya ce, “Alkawari....?”

Na ce, “Eh, alwakari, kawo ma mu kulla”.

Na bashi dariya sosai kafin ya miko min yatsarshi ta karshe ta hannun dama, na mika masa nawa muka sarke. Sannan muka kyalkyale da dariya ba tare da Ummi ta san abin da ya bamu dariya ba, ta janyo ni ta baya. Yana daga mana hannu muna daga masa har sai da muka kule cikin hostel.

Rayuwarmu a makarantar Gwamnatin tarayyah ta ‘yammata dake Gusau ta ci gaba da tafiya yadda ake so, mun dukufa, ba ma tamkar ni da bani wasa da alkawari ko ya ya yake, fatana Allah ya fidda ni kunyar idanun Yaya Aliyu in kai mishi sakamako mai kyau.

Duk da ba class daya muke da Ummi ba amma a hostel ko da yaushe muna tare, tare muke tafiya school arena, class, prep da hostel, dining da sauran extra-carricular activities da makaranta kan shirya bayan working time. Bamu yarda mun yi kawa ko guda daya ba, tsakaninmu da kowa sallamar musulunci da abin da ya hadamu. Mun samu exposure na zama da mutane kala-kala ‘yan garuruwa da yare daban-daban, masu halaye da dabi’u daban-daban.


****

Gabatowar karshen zangon karatu na farko muka fara gwaji wato (test), inda na kara zage damtse iyakar iyawata na yi dan abin a zo a gani. Wannan ne dalilin da yasa kafin zuwan jarabawa na dan rike wasu abubuwa da yawa, don haka da muka fara sai ta zo min da sauki, na cinye darasin Arabic da English tsaf, sauran subject din dai gasu nan dai la ba’asa ya fi la shai’in in ji Larabawa. Su Hajjah sun zo mana visiting (ziyarar dalibai) har da su Inna Kubra.

Ranar hutu da murnar mu muka nufi bakin gate a zaton mu Yayanmu Aliyu ya zo daukar mu, don baki ganni ba fuska kamar gonar auduga don murmushi. Ina rike da (report card) dina wanda nake kyautata zaton na yi abin kirkin da zai faranta ran Yaya Aliyu, na sauke nauyin alkawari na yi abin a zo a gani.

Amma murnata ta daka tsalle ta burma ciki sakamakon ganin mutumin da na tsana da gani a rayuwata, mutumin da na tsani jin muryarshi da ganin fuskarshi mara alheri a gare ni, dan uwan da da za a bani wuka a ce in caka mishi ba komai da na yi gaggawar aikatawa. FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA.

Sanye da makubar shadda ‘getzner’ dinkin samarin garin Kaduna masu ji da tashen samartaka, bakar dara mai gezar bakin gashi ya kara haske sosai ya yi fresh ta yadda ko ni da bani son shi a duniya na san Fa’ezz namiji ne abin so ga kowa, ba ga mata kadai ba har maza jinsinsa ba za su bar yiwa kansu fatan zama ko dakacen komawa kamar shi ba.

Jingine jikin motar Yaya Aliyu kirar ‘Picanto’ (Kia), fuskar nan dinke babu alamun rahama kamar kullum, na damko hannun Ummi kam, kirjina na dukan tara-tara ba ma uku-uku ba. Fuskar Ummi kamar an aiko mata da Manzon rahama ta saki hannuna ta sheka da gudu aguje wai za ta rungume shi.

Ya kuwa doka mata tsawar da ta sa ta tsugunnewa a kasa cikin gigicewa. Ganin yadda ya tsoratata ya gigitata ya yankwanata a gaban sauran daliban da ke gefe, ko me ya tuna? Ya yi dan murmushi gajere wanda ya fidda lotsawar gefen kuncinsa na dama.

Ya ce, “To ai ke ce abin naki babu kan gado tsohuwa (sunan da suke tsokanarta don ita ce mai sunan Hajjah, shi kuma su Yaya Aliyu su ce mishi tsoho kasantuwar shi mai sunan marigayi Abubakar Giwa (A.B Bamalli Giwa). Ya ce, “Kai! Ummi ba a girma”.

Sannan ne ta iya mikewa a darare. Ni dai ina daga gefe hannuwana sarke a kirji ina kallonsu, a zuciyata in ban da Allah ya kara ba abin da nake yiwa Ummi.

Ya budewa Ummi kofa ta zauna a gidan gaba ya rufe, yana sanya kayanmu a boot din mota ya juyo inda nake tsaye ya dube ni, ina tsaye jikin bishiya kawai ina kallon su. Ya rufe boot din motar ya shiga mazaunin shi zai ja motar.

Ummi ta ce, “Ya Fa’iz, Fa’iza fa ba ka ganta bane?”

Wata muguwar harara ya yi mata, ya ce, “In na ganta sai me? Sai me zan yi? Ita ba ta ganin mutane? Ba ta san ta gaishe su ba ko don UWARTA! Ta koya mata rashin tarbiyya irin tasu ta kabilu”.

Sai kawai ya ja motar ya badeni da kura. Ummi kira take “Fa’iza! Fa’iza!! Fa’iza!!!” Amma ko sauraron ta bai yi ba.

Na durkushe a nan na soma kuka, na yi kuka har muryata ta dashe. Na daga kai na dubi dai-daikun daliban da suka rage kwata-kwata babu ‘yan Kaduna, Zaria balle garinmu. Daga ‘yan Kano sai ‘yan Jigawa, sai ko dai-daiku daga jihar Gombe da Adamawa.

Na dora hannuna aka na rafsa kuka. Duk dokina na son ganin Hajjah, Zanirah da Yaya Aliyu ya gushe, sai wani irin tukuki da zuciyata ke yi.

Wannan wace irin kiyayya ce Ya Fa’iz ke min? Wace irin kiyayya yake yiwa mahaifiyata da ta shafe ni? Wannan ma ai rashin imani ne ba kiyayya ba. Duk irin kin da nake wa Fa’iz babu yadda za ayi in baro shi a jejin da na san ba shi da kowa, a gari mai nisa da babu kowa nashi.

Na rasa inda zan sa kaina don bakin ciki, kawai sai na samu gefen bishiyar darbejiya na share na kwanta a wurin ina kuka. Ina addu’ar Allah ya kashe Fa’iz in huta.

“Ke me kike a nan a kwance a kasa? Ko ba a zo daukar ki bane?”

Muryar wata malama ta doki dodon kunnena. Na dube ta idona jage-jage da hawaye na ce, “Eh”.

“Yar wane State ce ke?”

“Na zo ne daga Giwa”.

“Giwa? Giwa ta jihar Kaduna? Oh! Ke Bamalliya ce ko?”

“Eh”. Na amsa a gajarce.

“Amma kin yi nisa sosai, yanzu ya za ayi kenan?”

Na ce, “Zan kara jira a nan zuwa yamma na san za a zo min”.

Ta ce, “Ba zai yiwu ki yi ta zama ke kadai a nan ba, ki tashi ki shiga daga Library tare da yaran can ‘yan Niger State, kinga za ki fi hango duk mai shigowa ki fidda naki”.

A sanyaye na ce, “To”. Na mike na kade jikina na dauki jakar littattafaina na rataya, da yake duk sauran kayan sawarmu suna cikin kayan da Ummi ta tafi dasu.

Ban dade da zama ba barci ya dauke ni a kan daya daga cikin kujerun labiraren, na farka ne karfe biyar na yamma sakamakon tashin da wata yarinya ta yi min wai in tashi in yi sallar la’asar.

Sai kawai na fashe da kuka ganin yadda duhun yamma ya lullube sararin samaniyar subhana. Na bita toilet din dake jikin labiraren muka dauro alwala muka yi sallah, ni azahar ma sai a lokacin na yi ta. Har na idar da sallah kuka nake.

Ta ce, “Ki daina kuka, ai tabbas za a zo daukar mu ne, kema da baki da nisa kamarmu? Ai iyayenki babu yadda za ayi su manta dake”.

Cikin kuka na ce, “An zo an dauki Ummi, ni tafiya ya yi ya barni, in Allah ya yarda ba zan dawo makarantar nan ba....”

Shigowar daya daga cikin masu gadin makaranta yasa muka yi shiru muka zuba mishi mayunwatan idanuwanmu da yunwa da damuwa suka hadu suka jeme su, ya kira yarinyar nan wadda da alama ta girmeni cewar ta zo an zo daukar ta daga Adamawa. Ta fita tana daga min hannu har ta kule.

Na kifa kaina cikin cinyoyina na ci gaba da kuka a hankali, ban san sanda sarkin barayin ya zo ya sake sace ni ba.

Karfe bakwai na magariba na farka sakamakon azababbiyar yunwar da ta sake murda min ‘ya’yan hanjina, don saboda dokin zuwa gida ko karyawa (break fast) bamu tsaya mun yi ba saboda tunanin tuni Hajjah ta gama shirin karbarmu da hadadden girkinta.

Na dafa cikina da hannuna daya na runtse idona da karfi, ganin yadda duhun dare ya mamaye sararin sama, hawaye suka ci gaba da yi min lugude a fuska.

Hannun mutum na ji ya cira ni tsaye, na bude ido firgigit na mike a razane cikin fadin “Wayyo Allah..... wayyo Hajjah....” Abinki da cikin da ba komai, sai hajijiya ta kwashe ni yuuuu! Gaba daya na fada ga mutumin da ke tsugune a gabana, na daddage na kara sakin ihu....

“Wayyo Hajjah na shiga uku na lalace.... na mutu!”

Ya rungumeni sosai a jikinsa yana fadi cikin tattausar murya irin ta marasa koshin lafiya, “Relax, relax Fa’iza, relax”.

Na dauki lokaci ina tunanin mai muryar, kwakwalwata ta shiga tariyo min inda na san mai murya mai taushi da rashin amo. In ban yi kuskure ba zan iya cewa ta YAYA ALIYU CE.... YA YA ALIYU HAIDAR NA’IBI A.B GIWA.

Na lumshe idona na dan lokaci, bugun zuciyata na saisaita da zazzafan jikin Aliyu, zuciyata da ta yi zafi na yi min sanyi kadan-kadan.

Tsayin minti biyar Yaya Aliyu na rike dani, ya ce cikin kankanuwar murya, “Fa’izah are you ok?”

Na gyada kai, ya sake ni muka mike a tare yana rike da hannuna. Ya dauki jakar litattafaina da daya hannun nasa na hagu muka fita daga dakin karatun, ya bude gidan baya na shiga,  ya fiddo cooler din abinci ya bude, kamshin girkin Hajjah ne ya doki hancina, ba girkin cikin gida ba, wannan girki ne da take yi lokaci zuwa lokaci da hannunta, da na dade da sani ya baibaye ni, ya tado min tsohuwar yunwar da na wuni da ita.

Yawun bakina ya wani irin tsinke tun kamin in kai lomar farko sanda Yaya Aliyu ke zuba min a farantin cin abinci (plate), dafadukar shinkafa ce da aka yi rabinta da zallar tsokar kaza da ganyen alayyahu da kabeji.

Ya bude wata foil paper din ya fiddo gasasshen naman nan na kan hanyar Gusau da ya saya mana a hanya a zuwanmu, duk ya ajiye min ya rufe kofar ya shiga mazauninshi ya ta da motar muka soma tafiya.

Bayan ya miko min robar ruwan swan mai sanyi ya ce, “Kina iya kwanciya idan kina jin barci in kin gama”. Da gudu ya fizgi motar bayan ya daga ma masu gadi hannu ya kuma yi signing shaidar cewa an dauke ni.

Amma fa ya sha fada daga malamin da ke kula da shige da ficen dalibai, har ya bawa uku lada. Magana daya yake fadi masu su yi hakuri ba laifinsa bane.

A yayin da wata danja ta tsai damu kusa da wata fitila mai hasken gaske, garin kalle-kallena mai nuna ciki ya dauka na fara dawowa hayyacina, na dubi hannun Yaya Aliyu wanda ke bisa giyar motar, allurar karin ruwa na gani soke jikin jijiyar hannunsa jini na diga amma bai kula ba, tukin shi kawai yake.

Da na kura ido sai na ga hanyar karin jini da wata siririyar allurar ita ma soke duka a hannunsa ya bi fatar jikinsa ya kwanta. Na dube shi a razane domin tun zuwan shi ban ga fuskarshi ba, ya rame sosai ya yi duhu ainun.

Na daga murya da karfi cikin tashin hankali na ce, “Yaya Aliyu ka tsaya”. Ba tare da ya juyo ba, haka nan ban ga annuri a kyakkyawar fuskarshi ba ya ce, “A kan me zan tsaya? Bakya ganin tafiyar dare zamu yi?”

[6/3, 4:12 pm] Takori: Na ce, “Ni dai na ce ka tsaya ko? Baka ganin hannunka yana jini ne?”

Ya ce, “Babu komi wannan, kina so mu yi kwanan hanya ne?”

Na ce, “Eh, mu yi ba komai”.

Maimakon ya tsaya sai ma ya kara ware speed zuwa (200), kada ki ga yadda ‘yan idanuwana suka yo waje, suka yi kwala-kwala. Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu baka da lafiya.... you are bleeding....”

Ya ce, “Don Allah don Annabi Fa’iza ki saurara min, da me zan ji ne? Insha Allahu lafiya zamu je gida babu abin da zai faru sai wanda Ubangiji ya riga ya kaddara”.

“To ka tsaya in cire maka allurar...”

“Na ce ki barshi ko dole ne?”

Yadda ya yi min maganar cikin tsawar da bai taba yi min ba ya sanya hantar cikina kadawa, ban kara tankawa ba don na lura yana cikin wani irin yanayi (tension) mai wuyar fassaruwa. Bai tsaya ba sai a Giwa, harabar adana motocin A.B Bamalli Estate.

Tsakar dare muka iso gida, yadda na ga mazan Estate din duka a tsaye cirko-cirko manyansu da samarinsu a kofar gidan hajjah ya tabbatar min babu lafiya.

Baba Barau ya hau shi da fada, cewa yake, “Baka da hankali ne iye Aliyu? Halaka kanka kake so ka yi? Wannan wace irin wauta ce ka cizge karin jini da na ruwa ka bar gadon asibiti, ce maka aka yi duk cikinmu an rasa mai zuwa dauko Fa’iza daga makaranta?”

Aliyu zai wuce su kwayar idonshi na neman rufewa, ya yi kokarin yin magana amma ya kasa. Ganin yana neman shan kasa Baban Giwa ya kama shi, shi da Baba Salisu suka mai da shi cikin motar da ya fito bai samu ya rufe ta ba. Baba Salisu ya ja motar aguje suka fice da shi asibiti.

Ni dai na shige cikin gida sai kuka nake saboda halin da na ga Yaya Aliyu a ciki a dalilina. Hajjah ta taso ta rungumeni ta ce, “Baki kyauta ba Fa’iza, don me za ki tafi yawo a neme ki a rasa? Ga shi kin ta da hankalin dan’uwanki yana kwance asibiti amma daga jin labarin nan ya tsinke karin ruwan da ake masa ya dauki mota kamin kowa ya farga ya fice ya biki”.

Na dubi Ummi dake zaune da mamakin sabon sharrin Ya Fa’iz, ta sunkuyar da kanta. Na ce, “Ni Fa’izar ce na tafi yawo Hajjah?” Muryata kamar na aro, kamar ba tawa ba.

“Kyale ta kawai Hajjah, babu inda ni da malaminsu bamu duba ba cikin makarantar nan amma yarinyar nan kamar aljana sama ko kasa an rasa ta”.

Hajjah ta ce, “To ai shi kenan zancen ya wuce tunda dai an zo lafiya alhamdulillahi, sai a kiyaye gaba. Ke Fa’iza jeki ki watsa ruwa ki ci abinci kafin asubahi ta karasa”.

Na juyo da idanuna a hankali na dubi Fa’eez dake tsaye jikin bangon falon sai murmushi yake yi mai taushi, da idanuna da suka jawur na ce, “Kwarai, baka ganni ba Yaya Fa’iz, amma rabbil samawati wal’arshi shi yana ganinmu, kuma shi ya san abin da ke boye da wanda yake a sarari. Wata rana na zuwa da zai bayyana shi fili kowa ya gani”.

Na wuce toilet abina yana fadin “Me kike nufi? Karya nake miki kenan?” Ko juyowa ban yi ba na shige toilet na rufo kofar da karfi.

A zuciyata tausaya mashi nake kan halin da ya jefa kanshi a ciki, shin meye amfanin wannan kiyayya da yake nuna mini? Ya san girman ZUMUNCI a cikin addinin Islma kuwa? Me kiyayyar da yake yi min da hakan da yake yi min za su amfane shi da shi? A ce mutum sam-sam baya tsoron Allah a al’amarinsa sai Hajjah mutum ‘yar adam?

Ni kam gani nake in an boye ma Hajjah da sauran mutane abu ko gaskiyar abu ba za a boyewa Allah ba, Allah ka shirye shi, ka ganar da shi illar karya da cin zarafin dan’uwa musulmi ba ma dan’uwa na jini ba.

Na kwanta barci a wannan daren amma sam na kasa, tunanin shin wane halin Yaya Aliyu ke ciki a asibiti shi ya addabe ni? Me ya same shi? Me yasa ya boye min cewar ba shi da lafiya? Me ya tunzura shi ya yi fushi haka irin wanda ban taba gani daga gare shi ba?

Na san dai ba zai wuce abin da Fa’iz ya yi mani a yau ba. A zahirin gaskiya ina tausayawa Fa’iz idan Yaya Aliyu ya fahimci cewa da gangan ya gudo ya barni.

A wasu lokutan Yaya Aliyu na (acting according to) sunansa (mafadaci ne kamar kowanne mai suna Aliyu zakin Manzo). A duk lokacin da ya shiga irin wannan tension din babu mai iya tausasa shi sai Baban ABU wato (mahaifina).

Tsorona Allah tsorona kada na zama silar wargaza zumuncin dake tsakanin Yaya Aliyu da Yaya Fa’iz (Mai sona da mai ki na). Don haka ya zama dole in kare Fa’iz albarkacin ZUMUNCI. In boye abin da ya yin wanda ba Aliyu kadai zai batawa rai ba har Hajjah dake matukar girmama shi da iyayenmu maza.

Dan’uwa kowanne iri dan’uwa ne wanda na sani na kuma tabbata cikin family dinmu babu irin wannan hatsaniyar, ba zan so kuma in zamo silar ta ba.

Na juya ga Zanirah dake gefena tana barci, sai na ga ashe ba barcin take ba sharar hawaye take yi. Na ce, “Ba ki yi barci ba Zanirah?” Ta ce, “Eh”. Na leka fuskarta sosai na ce, “To shin Zanirah me kike wa kuka?”

Cikin dasasshiyar murya ta ce, “Yaya Aliyu? Shin ko a wane hali yake yanzun?”

Na ce, “Wai me ke damun shi ne Zanirah? Wane irin ciwo ne ya cucemu haka ya kwantar mana da Yayanmu Aliyu?”

Ta share hawaye da bayan hannunta ta ce, “Yana da (ulcer) ne ba tun yanzu ba, ba ta tashi kada shi ba sai a ‘yan kwanakin nan muna makaranta, nima da Hajjah ta je mun (visit) take gaya mani. Ya dade a kwance, domin ta ci karfinshi sosai. Ana i gobe zamu dawo Hajjah ta ce numfashi ma sama-sama yake yinsa da taimakon oxygen a asibiti.

Sun samu sun fara shawo kan matsalar aka daura mishi ruwa da jinin da kika gani, lokacin ni Yaya Sani ya dawo dani gida kowa da kowa yana asibitin, wurin azahar Fa’iz da Ummi suka shigo, mu duka muna waje suka shige ciki wurin Hajjah. Babu abin da Yaya Aliyu ya soma tambaya sai ina ka baro Fa’iza? Ya ce, “Wai bai ganki ba....!”

Wallahi sai ya tsinke jinin da ruwan ya dauki flask din abincin da Hajjah ta kawo mishi a lokacin ya fizgi mukullin motarshi hannun Ya Fa’iz, bai hana shi ba, shima sai ya yi ficewarsa. Abinki da taron mata babu wadda ta yi tunanin hana shi (tsai da shi), musamman a cikin yanayin fusatar da yake.

Ya yi waje, Hajjah na kira da su Inna Kaltume amma bai ko waiwaye su ba, kuma babu mai ilimin kiran likita ko nurses a cikinsu balle kiran security na bakin gate. Ya tashi motar suka bude mai ya fita ya tafi dauko ki, shima Ya Fa’iz tafiyar sa ya yi......” Ta ci gaba da kuka, nima haka.

Cikin kuka na ce, “Yanzu Zanirah a ganinki abin da yayanki ke yi a kaina, ko in ce nau’in zumuncinsa gareni yana kyautawa? Zan rantse miki da sarkin sarakuna Fa’iz da niyya ya taho ya barni a Gusau”.

Zanirah ta zaro ido, ta ce, “Shi Yaya Fa’iz din?’

Na yi mata alamar ta yi a hankali kada Hajjah ta ji. Na ce, “Kin san Allah ina tsaye gabansa ya ja motar suka tafi, wannan meye in ba kiyayya ba? Me na yiwa Yaya Fa’iz ya tsane ni a dangi Zanirah? Fa’iz ya nuna bai damu da rayuwata ba, ko da na bi wasu can sun sace ni ba asarar shi ba ce, ko da na fito daga cikin makaranta na bata bai dame shi ba, ko da yunwa za ta kashe ni ba ruwansa bane.

Amma don Allah don Annabi Zanirah kada ki fadawa kowa tunda na kudurta zan rufa masa asiri wurin Hajjah da Yaya Aliyu to zan yi, bana so a samu kuskure daga gare ni kan kiyayyar da Yaya Fa’iz ke mani, na tabbata wata rana Allah zai bayyanawa duk dangi cewa, Ya Fa’iz bai dauke ni ‘ya a cikin gidan nan ba a kan dalilin da ban sani ba”.

Sai na ga Zanirah na hawaye, muka yi ta kukan tare. Daga bisani da muka ga kukan ba zai amfanemu da komai ba, Zanirah ta ce, “Mu tashi mu yi sallar nafila mu rokawa Yaya Aliyu sauki”.

Washe gari su Hajjah za su tafi asibiti da safe na marairaice na ce, “Hajja don Allah?” Ta ce, “Mene ne?”

“Don Allah zan biku”.

“Ki bimu ina?”

“Asibiti wurin Yaya Aliyu”.

“Ki yi me? Kai Fa’iza da rigima kike, to shige mu je”.

Ba abin da na dauka illa hijabi da report-sheet dina muka tafi.

Mun samu Yaya Aliyu yana shan tea da kaninshi mai binshi Mus’ab, ya hada mishi yana mika mishi bired da yankakken dafaffen kwai da (mayonnaise) yana ci.

Hajjah ta washe baki ta ce, “A’a, Aliyu lallai jiki ya yi kyau lafiya ta samu. Mus’abu an iya jinya, sai a dage da cin abinci a kan lokaci kuma yadda ya kamata yanzu ko? Tunda an ji kamshin kofar lahira”.

Shi da Mus’ab suka yi dariya, ya sauko daga gadon da yake an cire mishi karin ruwan, ya gai da Hajjah. Abin da na fahimta duka hankalinshi kaina yake, na tsuguna na ce, “Yaya Aliyu ina wuni?”

Ya ce, “Ko dai ina kwana Fa’izah?”

Hajja ta ce, “Jiya ai Fa’iza da Zanirah basu yi barci ba ina jiyo shesshekar kukansu. Kai, tsakanin Fa’izah da Zanirah ban san wa ya fi son Yaya Aliyun nan ba, ko mi.... Hajja Yaya Aliyu, Hajja Yaya Aliyu ne ya bamu, Hajja Yaya Aliyu ya ce yana gaishe ki.....”

Na rufe fuska da tafukana cikin jin kunya na ce, “Hajjah ai shima yana son mu ne, yana mana kirki, kuma ya damu damu shi yasa muke son shi”.

Hajjah ta ce, “To Allah ya bar zumunci, yasa a daidaita da Hafizina tamkar hakan”.

A zuciyata na ce, “HAR ABADA Hajjah!” Amma a fili murmushi kawai na yi, zuciyata kamar ta fito ta bakin don haushin kalaman Hajjah.

Yaya Aliyu ya ce, “Fa’iza ina alkawarinmu?”

Na zaro (report card) dina cikin hijabina na mika mishi, ya duba ya yi murmushi. Hajjah ta ce, “Ai kamar an san za ka tambaya har an fito aka zura da gudu aka koma aka dauko shi, in ce ko dai an yi abin kirki ba irin na baya ba?”

Ya dago kai yana dariya ya ce, “Anyi da kyau Hajjah, na tara cikin dalibai sittin kinga ko an ka da hamsin da daya”.

Hajjah ta ce, “Lallai Asma’u za ta yi tsalle (Maman su Zanirah) har ta gode Allah, ita ce mai damuwa da sakamakon Fa’izah a kullum baya kai wa rabin na ‘yan’uwanta. To takwara fa (tana nufin Ummi)”.

Na kyalkyale da dariya na ce, “Ta yi na ashirin da daya cikin mutum sittin, ai ta yi kokari domin a primary ana yin magana ko koyarwa da Hausa, a  can ko ba a yi kuma an kaita ajin kasuwanci, ni kuma ajin Arabiyya ne tuntuni na iya Larabci tun a gida Zaria, shi yasa nake fahimta sosai cikin ajinmu. Amma ka ga sauran subjects din ai duk ban ci da yawa ba”.

Hajjah ta ce, “Koh? Allah ya taimaka, gata nan ta kara habewa ta suntuma kamar yis, sai fada da karfi kamar diyar zaki amma babu karatun a zo a gani”.

Na ce, “A’a, Hajjah tana kokari”.

Duka suka yi dariya ganin yadda na bata rai, don cikin mu ukun nan babu mai son a soki ‘yar’uwarta ko a gabanta balle a bayan idonta.

Yaya Aliyu ya bar dariya ya ce, “Gaya min Fa’izah ya aka yi suka taho suka barki?”

Na ce, “Wallahi Yaya Aliyu ba yawo na je ba, na shiga teachers area ne gidan su wata ‘yar ajinmu in kai mata littafinta da na ara, shine da basu ganni ba suka taho suka barni”.

Ya ce, “Next time kada ki kara yin irin haka, kin ji na gaya miki, kina wasa da ranki ne da lafiyarki masu muhimmanci ga wadanda ke da bukatar su. Shi kuma da yake babban sakarai ne ba zai iya jiranki ba? Allah Hajjah Fa’iz zai gamu dani da kyar ma in.....”

“Na kashe zancen nan tun jiya Aliyu, kada wanda ya sake tado shi”.

Ya ce, “An barshi Hajjah”.

Har yamma muna wajen Yaya Aliyu, wannan ya shiga wannan ya fita. Sai biyar da rabi Aunty Zainabu Maman su Aliyu da Baba Na’ibi mahaifinsu suka zo, sannan muka bisu muka tafi.

Aunty Zainabu ke tsokana ta, “Fa’izah hutu bai zo da dadi ba, Babban Yaya babu lafiya ina kwanciyar hankali?”

Baba Na’ibi ya ce, “Ai laifin su ne tunda basa matsawa Yayan yana cin abincin cikin gida sai dai ya basu kwai da Indomie su soya masa, kowa ya gaya musu wannan taliyar abinci ce oho!”

Na ce, “Wallahi Baba daga yau ba zamu kuma dafawa Yaya Aliyu Indomie ba, durar tuwo kawai zamu dinga yi masa, ko kuwa Hajjah?”

Hajjah ta ce, “Ni ina ruwana ne?”

Satin Yaya Aliyu guda a asibiti aka sallame shi. Hutunmu ya ci gaba da tafiya cikin dadi tare da Yayanmu mai son mu Aliyu, wanda shiga goma fita goma in zai yi cikin gida sai ya neme ni, ko ya riko min wani abu. Na ci ne ko na amfani, ko wanda zai amfane ni wajen karatu.

Babban farin cikinmu Fa’iz an yi balaguro zuwa Kaduna. Duk gidan ‘yan’uwa mun zaga ba inda bamu je ba sai Kaduna da Zaria.

Hutunmu ya rage saura sati daya mu koma makaranta Baban ABU ya zo suna hira da Hajjah a falonta muka shigo daga Islamiyya ni da su Zanirah, baki daya muka tsugunna muka gaishe shi, muka wuce dakinmu.

Ya daga murya yana fadin “Lallai Fa’iza baki da kirki, kika yi tafiyarki Gusau ba sallama, kika dawo shima kina shirin komawa ba tare da an waiwaye mu ba ko? Ga su Walida kullum basu da zance sai na yaushe za ki dawo, kin kyauta kenan?”

Na ce, “To Baba ai matarka ce ba ta nemana shi ya sa”.

Ya ce, (cikin dariya) “Tana neman ki mana, jiya ma ta ce ka ga Fa’izah yau saura sati daya a koma makaranta amma shiru”.

Na buga tsalle na makalkale shi ina cewa, “Zan bika, zan bika to Baba”.

Zanirah ma ta ce, “Nima zan biku Baba ka sauke ni gidan Maman Ya Fa’iz (mahaifiyarta)”.

Ya ce, “Ke fa tsohuwa (Ummi)?”

Ta ce, “Ni  area one za ni”.

Ya dubi Hajjah ya ce, “Wai me yasa uwata ba ta son gidansu ne?”

Haka dai muka debi ‘yan kayanmu muka bi Baba. Sai da aka fara kai Zanirah Kaduna (Jabi Road), ko shiga gidan ban yi ba don sanin cewa Fa’iz na nan. Amma Baba na karya kan mota zai fita a get din gidan sai ga shi ya shigo da litattafai a hannu, Baba ya dan rage gudu suka gaisa.

Wai don ganin idon Babana Fa’iz ko kunya babu ya ce, “A’a, Fa’iza ba za a shigo a gai da Mama ba?”

Ban ba shi amsa ba na dauke kai. Ummi ta ce, “Ka dai ce muna gaida ta”.

Baban ABU ya ce, “Kun ci gidanku”. Ya auno mana umbola. “Ku zo har kofar gidan nan ba za ku shiga ku gai da Asma’u ba balle kannenku in Yaya Muntari baya nan?”

Kafin ya rufe baki muka bubbude kofa muka fita, ni kuwa muna dan yin nisa da motar na zura da gudu na je na gai da Maman, sanda suka shigo falon shi da Ummi na sake kwasa da gudu na yi cikin mota kada wata kalma ta hadamu ko ya yi min zalincin nasa.

Baba bai tsaya shawartar Ummi ba ya ja mota sai unguwarsu gidan Yaya Hauwa, wato gidansu. Ta ce, “Baba me zamu yi a gidan Maman Maryam?”

Ya ce, “Haba Ummi, kowa na marmarin ganin uwarshi wata da watanni bai ganta ba, in ke bakya marmarin ganinta to ita tana bukatar ganin ki ko?”

Ta zumbura baki irin na ‘yar fari, “Baba ‘ya’yanta fa fitsarin kwance suke yi, su bi duk su jike ni in na yi zarni a ce nice”.

Ya ce, “To ai ba sai kin kwana ba, ku je zan jiraku ku gaida su ku fito mu tafi (Area One) din (gidanmu)”. Nan muka kama murna muka fice.

Aunty Hauwa na tsaye jikin famfo tana wanke (under wears) din yaranta muka yi sallama da babbar murya. Ta saki wankin ta bude hannuwa ta rungumemu duka, fadi take, “Ka ga ‘yan Gusau an cakare har an cake! Irin wannan gayu haka kamar ba goyon tsohuwa ba”.

Muka kyalkyale da dariya. Na dubi jikinmu ni da Ummi, ni kaina na san mun yi kyau. Wani riga da wando ne da mayafi ‘yan (Lahore-Pakistan a jikinmu, na jikina yellow na Ummi green, gashin kowaccenmu babu kitso kalmashe cikin tafkeken ribbon kalar kayan kowacce, wanda dama mahadin kayan ne tare ake sai dasu.

Ashe Baba wayo ya yiwa Ummi, sai ga Yusuf da kayanmu ya shigo dasu wai Baba ya ce sai gobe zai zo ko ya turo direban makaranta ya tafi damu.

Da daddare bayan cin abincin dare muka shiga bai wa Yaya Hauwa labarin rayuwar bording school daga A-Z, sam ban yi zancen Fa’iz ko halayen da yake nuna min da wani jininmu ba, ko da wasa ban taba yi ba. Haka abin da ya yi min ranar hutu, balle wanda yake yi min a Giwa.

Haka Ummi ba ta tada zancen ba, ko da Yaya Hauwa ta sako sunan Ya Fa’iz cikin hirarmu bana tankawa (wannan shine babban kuskuren da na yi at the first place), ko kuma na kare shi idan Ummi ta so fadin rashin kirki da rashin alherinsa.

Sai lokacin Baban Ummi Alh. Sabi’u ya shigo gidan, Sabi’u Kwangila shi ke rike da (Bamalli Farm) gidan gonar A.B Family dake cikin garin Kaduna, inda ake kiwon poultry da noman kayan marmari. Shi din kuma babban dan kwangila ne na karan kansa.

Daidai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah, ba abin da suka nema suka rasa, don ita ma Yaya Hauwa babbar ma’aikaciya ce, principal ce a makarantar Sarauniya Amina.

Mahaifin Alh. Sabi’u shine babban aminin marigayi Abubakar Giwa, idan da wanda za a ce ya yi auren bare, ko ko auren da ba na jini ba to Aunty Hauwa ce, sai dai zumuncin dake tsakani irin tun na kuruciyar nan ne wanda aka zama tamkar jini daya. Ba shi kuma da niyyar yi mata wani abu wai shi KISHIYA, kamar yadda ya fahimci ba a yi sam a zuri’ar A.B Giwa, one-man-one-wife-one-life!

Baba Sabi’u ya zauna gefen Aunty Hauwa ya ce, “Ummi ai mun yi fushi, tafiya ba sallama, dawowar ma sai da muka ci arzikin Zanirah, na tabbata da ba ta zo Kaduna ba ke da Fa’iza ba za mu ganku ba”.

Ummi ta ce, “Don Allah Baba ka yi hakuri, wallahi ziyarce-ziyarcen ne ya yi mana yawa”.

Ya ce, “Ai dole duk inda hakuri take in je in sayo ta in hadiya. Ya ya jarrabawa? Ta nawa-nawa aka yi?”

Ummi cikin doki tace, “Wallahi Baba ta ashirin da daya na yi”.

Ya yi salati ya ce, “Allah ya yaye miki wautar da ke kanki Ummi, wallahi ki kama kanki, ki nutsu ki shiga cikin taitayinki, lokacin abu ayi shi in ya wuce ya wuce kenan”.

Ummi ta bata rai ta ce, “Baba na fa yi kokari na dauka za ka yaba min ne, a primary 40 fa nake yi”.

Ya ce, “To da dan dama-dama sai a kara dagewa”.

Washe gari da yamma Baban ABU bayan ya taho office gidan ya biyo har da kanwata Walida da Abdallah a bayan motar.

Baba Sabi’u ya yi mana provision sosai, har da Zanirah da ba ta nan bai ware ta ba. Sayayyar da ya yi mana ko da Yaya Aliyu zai kara sai dai ya kara kadan.

Muka nufi Zaria cike da farin ciki. Ita kanta Ummi sai na ga tana wani nishadi da annashuwa na musamman, na ce, “Yar banza ashe kina son su Yaya Hauwan?’

Ta ce, “To Fa’izah akwai wanda bai son mahaifan shi ne?”

Na ce, “Ba gaki nan ba, sai an miki dabara za ki gun iyayenki”.

Ta ce, “To ke kuma fa?”

Na ce, “Ai ni dole ce tasa na barsu kema kin sani”.

A gidanmu Momi na kicin tana girki muka yi mata sallama, ta washe baki tana yiwa Ummi sannu da zuwa ban da ni. Na ruga na rungume kugunta na ce, “Momi ni bakya nemana ko?” Muryata kamar zan yi kuka

Ta yi ‘yar dariya dauke da wata irin matsananciyar kauna cikin kwayar idanunta, ta ce, “In neme ki in miki me? Su Walida basu ishe ni ba kenan?”

Sai a lokacin na ga cikin Momi ya zama kato ya turo zani har baya kulluwa, na ce, “Momi haihuwa za ki yi?”

Ta ce, “Me kika gani?”

Na ce, “Cikinki na gani ya kumbura suntum”.

Ta yi tsaki ta fice ta bar min kitchen din tana cewa da Ummi ta kashe mata heater din ruwan zafi mu fito mu rufo kofar kicin din.

Walida ta zo kunnena ta rada min cewa, “Baba ya ce kanwa ko kani Momi za ta haifowa Kausar”.

Muka kyalkyale da dariya. Dariyarmu ce ta sata juyowa ta dube mu, ta girgiza kai tana murmushi, na san sha’awa muka ba ta. A kullum ni da Walida kamar ‘yan biyu muke, domin Walida akwai manyan barage, sai dai ita fara ce tas ni kuma ina da duhu.

Da ganin Walida ka san za ayi babbar mace mai babban jiki nan da ‘yan shekaru, ba mai cewa Abdallah ya girme mata da shekaru dai-dai har uku, don ni kaina ta dara ni jiki da tsaho. Haka yadda muke kaunar junanmu duka abin sha’awa ne wurin Mominmu da ta haife mu ma balle ga sauran al’umma.

Duk kawaici irin na Momi a wannan hutun na fuskanci ta ji dadin zuwana, domin ban taba kai wa irin tsahon wannan lokaci ban je ba. Kwananmu biyar muka juyo Giwa da tarin tsarabarmu na tafiya makarantar kwana.

A can muka tarar da Zanirah ta riga mu dawowa tuntuni. Washe gari Yaya Aliyu ya mai damu makaranta, amma duk da kayan da muka samo bai rage komai ba a sayayyar da ya saba yi mana, bai fasa komi ba.

To haka rayuwa ta ci mana gaba tsakanin gida da makaranta. Duk burin iyayenmu ya ta’allaka ne a kanmu mu ukun nan da burin gina mana ingantacciyar rayuwa, kasancewar mu ‘yammata matasa kadai dake gabansu.

Kauna ce muke gani daga kowanne bangare na iyayenmu, gata na duniya babu irin wanda bana gani daga iyayenmu, da kakarmu Hajjah da babban Yayanmu Aliyu Haidar.

[6/3, 4:12 pm] Takori: Wannan ne dalilin da yasa muka kara zage damtse don mu fita kunyarsu mu ba mara da kunya, mu nuna musu ba a banza suke wahalar da suke yi damu ba, we will insha Allah make them to be proud of it ta hanyar kara zafafawa kawunanmu da karatu.

Sai dai gatan da ake nuna mana baya shafar tarbiyyar da muka taso a ciki, muka gada iyaye da kakanni, muka kuma tashi muka ga ana yi cikin gidanmu tuntuni.

Ta fannin Yaya Aliyu, ya kara zage damtse da kokarin ganin na kara hazaka sosai da hikima da basira irin nasa. Ba zan manta ba a second term (zango na biyu) da na kai masa sakamakona na yi na shida, ya nuna min bacin rai sosai, ya daina kula ni, ya daina shiga sabgata, ko kallon inda nake ya daina. Ya daina sayo min gasasshen naman da ya zame min kamar taba.

Maimakon hakan duk ya koma yiwa Zanirah wadannan abubuwan a madadina, ita da ta kawo (second position), duk na bi na damu, na shiga cikin kunci da takura na babu gaira babu dalili.

Wannan ne ya zaburar dani na takurawa kaina da karatu a zango na gaba, iyakar iyawata na kawowa Yaya Aliyu (3rd position out of 60). Yaya Aliyu ya daga ni ya yi sama yana juyi dani a falon Hajjah, kayan dadi da nama kuwa sai da Hajjah ta yi ta fada tana zai sangarta ni, in na auri wanda ba shi da halin ciyar dani nama kullum fa? In shiga raina abin da ya kawo mani?”

A zangon farkonmu na sabon aji JSS 2, su Momin ABU, Maman Kaduna da Yaya Hauwa, Aunty Zainabu da matar Baba Barau Aunty Marwa, da matan su Baba Sadi duk suka yo Bus guda suka kawo mana ziyara.

Momin ABU rungume da sabon baby dinta kyakkyawa kamar Baban ABU, na rungume shi na rasa inda zan sa kaina don farin ciki. Bakina kamar ya yage don fara’a ina rungume da babyn, na ce, “Wai ya ya sunansa Momi?”

Ta ce, “Ban sani ba, ni fa ba wurinki na zo ba Aku sarkin magana”.

Na yi narai-narai da ido kamar zan yi kuka. Yaya Hauwa ta ce, “Rabu da ita Fa’iza, sunan shi Baban Kaduna (Mukhtar) shi kenan?” Na ce, “To, Ya Hauwa ya zamu ke kiran shi?” Ta ce, “Kowa a gida yana ce mishi ‘WALID”. Dadi ya rufe ni, na ce, “Yeh! Mun samu Waleed da Waleeda”.

Ta fannin Fa’iz karatun Diploma a Kaduna Poly ya sha masa kai, a kokarinsa na hattama (ND) wato National Diploma. Fa’iz wani irin mutum ne da baya son karatun boko sam. Diplomar ma sai da suka takura masa su Baban ABU suka bude mishi wuta, don bayan kammala sakandire dinshi a Madina kin ci gaba ya yi, kai dai barshi da tukin mota.

Duk wanda ke son zuwa unguwa Fa’iz ne direbansa, ba sai ka roka ba shi zai roke ka ka ba shi key din mota ya kai ka. Babu yadda bai yi ba Baba Muntari ya ba shi mota ya ki, don ya ce tukin mota ne yake hana shi karatu don haka duka bus-bus din A.B Estate mukullan su yana hannun Fa’iz.

Kowa da (nature) dinsa, kowa da kaddararsa, to “tukin mota shine kaddarar Fa’eez Mukhtar Abubakar Giwa”.

Yana kwanan makaranta ne a Kad Poly don haka yawancin hutun da muke zuwa muna samun sa’ida. Week end kawai yake zuwa Giwa ya koma lahadi, don haka marorinmu sun sarara cikin shekarun nan.

Wannan hutun da muke zangonmu na karshe na aji uku na karamar sakandire (JSS.) mun dukufa karatun jarrabawar (placement). A wani dare a hostel na dubi Ummi wada ke nazarin wani littafin Islamic Studies na B. Aisha Lemu (For Juniors) na ce, “Ummi kin san tunanin da ya zo min kuwa?”

Ta ce, “A’a, sai kin fada”. Tare da rufe littafin da ke hannunta.

Na ce, “Wallahi tunani na yi, gara mu hada baki mu ki makarantar nan haka. Babu mai tunawa damu, babu mai zuwa mana a kan kari ko akai-akai, komai mune karshe. In ba don ma Yaya Aliyu da ke zuwa duk wata ba, ai da mun kade.

Kina da masaniyar cewa Zanirah duk sati sai an je mata an kai mata girkin Hajjah da dambun nama, gaskiya ni ba zan dawo ba”.

Ummi ta ce, “Ni babu ma abin da ya fi ban haushi irin ranar hutu, kullum mune karshen dauka bayan yunwa ta gama kwakwale mu”.

Na ce, “Abin da nake so ki gane kenan, kawai mu bude wuta mu ce mu sai Sarauniya Amina (Queen Amina College Kaduna) inda Yaya Hauwa ke aiki. Makaranta ce ta hazikai kwarai, Aunty Hauwa ta taba gaya min dan JSS 2 a Queen Amina zai iya rubuta Formal Letter ba tare da kuskure ba, duk da ba ta federal govt. ba ce”.

Ummi ta ja numfashi ta ce, “To shi kenan, sai mu bi ta kan Yaya Aliyu shi kadai zai yi mana wannan kokarin, kuma shi kadai ne zai mara mana baya, amma cewa za’a yi don muna son kusa da gida ne kawai”.

Na ce, “Ai Allah ya ga zuciyata, ni dai abin tarihi da alfahari ne a gare ni a ce na zamo daya daga cikin daliban makarantar nan mai tsohon tarihi”.

Ranar hutu muka shiga sallama da kowa kamar har mun tabbatar ba zamu dawo din ba. Bamu bar ko tsinkenmu ba, mune har da amsar address din wasu daga cikin ‘yan dakinmu da ‘yan ajinmu wadanda aka saba da juna tsayin shekaru uku.

Yaya Aliyu ya ga kaya cancarakas! Har da su loka da katifu da filallika, ya ce, “Ku lafiya? Ina za ku da wannan kayan?’

Muka kyalkyale da dariya ganin yadda ya razana, muka shiga danna kaya a but muna fadin “Mun yi graduation ne Yaya Aliyu”.

Ya ce, “Aure za ku yi?”

Muka hada baki wajen cewa, “Eh! Yaya makaranta ta ishemu aure muke sooooo!”

Ya zuba hannaye a bannet din motarsa yana fadin, “La’ilaha illallahu......”

Na ce, “Muhammadur rasulillahi.....”

Ummi ta ce, “Sallallahu alayhi wasallam”.

A kan hanya muke yi masa bayanin shawarar da muka yanke. Ya ce, “Ke dai Fa’iza ko dai don ki dinga cin abincin Aunty Hauwa ne?”

Na ce, “Wallahi a’a Yaya Aliyu, kawai ina so na zamo daya daga shahararrun daliban Sarauniya Amina wadanda tarihin Najeriya  ba ya mancewa dasu (Old Student of Queen Amina College Kaduna)”.

Ya ce, “I trust you my dear sissy”.

A falon Hajjah Yaya Aliyu ya ta da zancen,ranar da muka kwana uku da komawa. Bashir da ya zo daga Kaduna ya ce, “Gaskiyar Fa’izah, don ko wannan jelen daga Giwa zuwa Gusau-Gusau zuwa Giwa ba karamin wahala bane”.

Fa’iz ya ce, “Wane irin wahala Yaya Bash? Tunda Allah ya hore abin da za a sayi man fetir din da lafiyar da za a tuka motar ba shi kenan ba? Kawai dai Fa’izah jakar yarinyar nan ka san ba son karatu take ba shine ta zuge Ummi don ita ma ta maida ta jaka kamar ta, amma ta ya ya za a ce wai Govt. School ta fi ta federal Govt. Na san don su dinga ganin Aunty Hauwa ne kurum..”

Aliyu ya yi saurin katse shi da cewa, “Ban tari hanzarinka ba Fa’eez, ban kuma ce Fa’eezah mutum ce ba jaka ba ce tunda uwarta ba A.B ba ce, don haka Fa’eezah ba mutum ba ce. Amma da ka ce wai don su dinga ganin Aunty Hauwa ne a kan me? Shin watanni nawa suke sharewa ma a nan garin ba tare da sun ziyarce ta ba ma sun taba damuwa? Ko ka taba jin tsakanin Ummi da Fa’iza wata ta taba tambayata yaushe zamu je wajen yaya Hauwa? In da ka ce Maman Kaduna to wannan sai in yarda”

Fa’iz ya kyabe baki ya ce, “Kai ai Yaya Aliyu ai dama kullum kana bayan Fa’izah, ba ta taba yin ba dai-dai ba ka kwabe ta, komi ta yi, duk hukuncin da ta yi dai-dai ne a wurinka, alhali she’s (empty-mindend)”.

Ya ce, “Yes! Fadi da babbar murya ina bayan Fa’ia a kullum, domin da ka ki da ka so FA’IZAH yarinya ce mai tunanin kanta, hikima da kaifin basira, da wuya tunanin ta in an auna shi za a ga rashin hikima a cikinsa. Kuma da kake cewa wani wai Allah ya hore kudin man fetir, to don Allah in tambaye ka, shin ka taba kashe kwandala ka sayi man ka zuba a mota ka kai ko ka dauko Fa’iza daga Gusau ko da sau daya ne? Ka taba kashe lokacinka ko da minti talatin ne ka je ka gano Fa’iza da Ummi a Gusau?

Amma Zanirah! Ka gaya mani don Allah, sau nawa kake zuwa mata visit per-term? Ko ko ka taba kawo kwandala ka basu ka ce su sayi sabulun wanka a makaranta? Amma Zanirah sau nawa kake sayen kaya ka kai mata Fa’iz! A wane dalili don Sun nemi sauyin makaranta za ka sanya baki, don haka ba damuwar ka ba ce bai shafe ka ba ina fatan ka gane?’

Fuskar Fa’eez ta yi jawur da wannan wankin babban bargo da Yaya Aliyu yai masa, ya ce, “Amma ka san ni ba wani aiki nake ba baya ga karatu, ina zan nemo kudin da zan ke musu provision har su uku, kuma su suna da nisa?”

Yaya Bashir ya ce, “Line perfect, wannan karatun naka ne kake kiran shi karatu? Wai National Diploma, amma a hakan ina kake nemo wanda kake yiwa Zanirah? Ina kake nemo wanda kake dinka sabuwar shadda duk sati? Tukunna ma, ina kake kai rabonka da ake baka na A.B family duk wata? Ban ga amfanin mutum ya tsaya yana faman cacar baki da mutumin da bai san ciwon kansa ba irin Fa’iz Bamalli....”

Hajjah ta zaburo ta ce, “Ku kun san Allah ku kiyaye ni, haka kawai kun sa min miji a gaba kuna tsiga kuna tsattsaga kamar ku kuka haifi Fa’izar da Ummin? Sai ku bari in ya zo ya ce muku yana son daya daga cikinsu sannan ku yi masa wannan gore-goren naku”.

Yaya Aliyu ya ce, “Ai shima baya fara ba, baya soma ba Hajjah, Ina! Ai alamar karfi yana ga mai kiba, kuma abin da ka yi shi za a yi maka. Makaranta ce ni Ali zan canza musu, zan ci gaba da kula da hidimarsu duka ba zan bambanta ba, ba zan fasa ba, don ni irin nawa ZUMUNCIN KENAN duka daya ake, A.B abu guda ne bana jikin-jikina kawai ba, in har ina da iko sai in ko bana numfashi Hajjah”.

Ta ce, “To Allah ya ba da sa’a, ga fili nan ga mai doki”.

Fa’iz ya ce, “Sai sukuwa Hajjah”.

Yaya Aliyu ya danna mai harara ya yi ficewarsa yana murmushin tura haushi.


****

Ina toilet ina wanka na ji landline din Hajjah na ta faman (ringing) babu wanda ya dauka ta yi ta ruri har ta katse, ta sake kama wani sabon kukan har tana neman ta sake katsewa. Cikin hanzari na ja tawul na daura duk jikina kumfa na fito falon aguje na dauki wayar na amsa da sallama.

Sai ga Ya Fa’iz ya sanyo kai falon, cikin  captan na makubar shadda Hilton, ya yi shar kamar ango sabon aure. Shigowar tashi da tunanin yanayin sutturar da nake ciki ya sanya ni rawar kafafu tare da sarkewar harshe wajen amsa sallamar.

Muryar Maman Kaduna ce ta ce, “Fa’izah ga direba nan na turo yanzu ku biyo shi dukkanku tafiya zamu yi Kano gidan Rabi”.

Na yi tsalle na dire na saki ihun murna, na ce, “To Mama”. Na ajiye wayar amma saboda rawar da hannuna ke yi na ajiye shi ba dai-dai ba.

Dagowar nan da zan yi muka yi ido hudu da Fa’iz yana yi min wani irin asirtaccen kallo da shi kadai ya san ma’anarsa, sai dai na nemi kibiyar kiyayyar dake cikin idanun na rasa. Kallo ne na kurulla wanda ya wuce gejin kallon addini. Na tuna a yanayin da nake na saki wani dogon tsaki na juya na shige dakinmu, na shige toilet na rufe na ci gaba da wankana.

Bayan na kammala na fito ina muttsika mai a fatar jikina (Norwegian Formula). Su Ummi suka shigo suna ta hira da kwasar dariya, na ce, “Ku don Allah mu shirya ga direba nan Mama ta turo zai debe mu zuwa Kaduna, daga nan mu tafi Kano wajen Ya Rabin Yaya Muftahu”.

Nan su Ummi har da tsalle aka fada wanka, Zanirah na hada mana kaya cikin (luggage).

Hajjah ta shigo daki ta ce, “Ku kuma shirin me kuke haka kamar za ku tashi sama?”

Na ce, “Hajja Kano zamu”.

Ta ce, “Kano? Wajen autata amma shine baku gaya min da wuri na tanadi tsaraba ba?”

Na ce, “Hajjah muma yanzu-yanzun nan Mama ta yo waya ta gaya min na gaya musu, amma na san ita Maman za ta yi tsaraba ai”.

Muka sha doguwar riga mai rubi biyu ‘yar Oman (tsarabar Baba Sadi ne ta Hajjin Bara), nawa baki da ratsin maroon, na Ummi baki da bula-bula mai hasken sararin samaniya, na Zaneerah ja da baki, muka debi ‘yan kayan da zamu butaka cikin travelling bag.

Kamar jira yake mu kammala, malam Garba direban Maman kaduna sai ga shi ya aiko su Abba ya zo mu fito.

Mun shiga mota Hajjah na daga mana hannu, nice a gaba su Ummi a baya, sai ga Yaya Aliyu ya fito daga gidansu ya ce, “Sai ina kuma ‘yammatan Hajjah?’

Na ce, “Sai Kano”.

Ya ce, “Kano? Gaskiya Fa’iza ban yarda ba, na ji an ce samarin Kano kwarraru ne wajen fashin mata”.

Cikin mamaki na ce, “Matar wa to za su kwace?”

Ya yi hanzarin gyara zancensa da cewa, “Ke dai kada ki kula maza a Kanon, Idan Baban ABU ya ji kin yi saurayi zai gayawa Hajjah ne ayi gaggawar yi miki aure ke da su Ummi, ba zai bari ki yi Sarauniya Amina ba”.

Su Ummi suka kyalkyale da dariya (ban da Zanirah). Na ce, “To na ji ba zan yi ba, amma su Ummi su yi?”

Ya kada kafada ya ce, “Eh, ba komai su suyi, ai kinga su sun girme ki. Baki ga Ummi ta yi biyunki ba”.

Malam Garba ya ja mota muka wuce muna mishi dariya ban da Zanirah da ta yi fuskar shanu tana ta sakin tsaki, to wa take yiwa? Allah masani.

Da muka isa Kaduna already Mama ta shirya ita da Junior, bamu bata lokaci ba sauran yara suka yo mana rakiya bakin mota da kayan Mama Kano ta diba.

Kusan karfe biyar na yamma muka iso Kano, unguwar da su Anti Rabi suke wai ita Gadon Kaya. Unguwa ce da ta tara duka masu karfi, masu karamin karfi, ‘yan kasuwa kawo ‘yan boko babu irin rukunin mutanen da ba za ka taras a unguwar ba.

Duk da babu inda ban sani ba a Kaduna, ban ga kyakkyawan gari mai albarkar al’umma irin Kano ba. Gidan su Aunty Rabi yana ‘Yarda Avanue.’ Mama ke yiwa Malam Garba kwatance har kofar gidan.

Abdul-Rahim dan Aunty Rabi muka fara gani suna wasan kwallo shi da wani yaro dan makotansu, duk da bamu san shi ba, amma tsagin mallancinmu da karan hancin sun tona shi, muka kama shi muka rungume.

Aunty Rabi ta fito da gudu ta makalkale Mama kamar wata karamar yarinya, tana lale Maman Kaduna, lale da ‘yan Giwa, lale da ‘yammatan Hajjah.

Ta yi mana jagora zuwa falonta, Yaya Muftahu ya fito daga nashi dakin shima yana mana marhaban, nan muka ga yadda ake karrama bako, ko da jini ne ba bako ba.

Kwananmu daya washe gari suka kwashe mu don nuna mana Kano ciki da bai dinta, duka kofofin nan, Kansakali, da Kabuga, Gadon Kaya, Kofar Ruwa, Duka Wuya, Dan Agundi, Kofar Famfo da Na’isa babu wadda bamu ratsa ta cikinta ba mun daga kai mun karanta sunan ta ba. Kofar Nassarawa, Kofar Mata.

Manyan wuraren tarihin Kanon Dabo irin su Gidan Makama (Museum), gidan Dan Hausa, Dutsen Dala da Gwauron Dutse, Gidan Zoo, Gidan Sarkin Kano da Fadar Masarautar Kano, har gidan Tsumburbura dake kan Dutsen Goron Dutse.

Haka manyan shopping malls din Kano babu wanda Yaya Muftahu da Aunty Rabi basu kai mu mun ciko ledoji ba, tun daga Sahad, Country Mall, Well Care, Grand Square, Jifatu da Ado Bayero Mall.

Lallai na yarda Kano ta amsa sunanta ta Dabo-ci-gari, yaro ko da me ka zo an fika. Mune har gidan Zoo da gidan Makama Museum. Sannan ranar juma’a mika ya da zango a fadar Sarkin Kano Alh. Ado Bayero muka yi gaisuwa ga Dabon Kano, duk da bai sanmu ba, ranar juma’a ya ware ta yana amsar gaisuwar talakawansa Allah ya yi masa rahma (amin).

Gaskiya mun ji dadin ziyararmu Kano fiye da duk wani gari da muka taba zuwa. Ko da yake mu dama duk yawon namu iyakacinshi Kaduna da Zariya, don haka zuwan mu Kano da kwanaki uku kacal da muka yi tare da Aunty Rabi da iyalinta ba karamin dadinsa muka ji ba.

Bayan mun dawo Yaya Aliyu ne ya tsaya ya sama mana gurbi a Queen Amina, duk da Yaya Hauwa ta so hanawa Hajjah ta ce ta kyale mu. Muka tattara muka koma muka fara karatu babu kama hannun yaro.

A hutun karshen zangon karatu na karshe na aji hudu da muka zo, Fa’iz yana makaranta ya kama daki a cikin makaranta. Don haka na saki jiki nake rayuwata cikin walwala da nishadi.

Ranar wata asabar Baban Kaduna ya zo gidan da maraice, ina uwar dakin Hajjah ina shirya mata kaya cikin (wardrove), ita kuma tana falo tana sallar walha na ji sallamar Baba Muntari.

Hajjah ba ta amsa mishi ba, nima ban amsa ba kamar wadda aka dinkewa baki. Ina jin shi yana waya da Baba Barau, Sadi, Sadisu, Na’ibi, Ibrahim yana fadin duk su hallara falon Hajjah tunda Asabar ce kowa yana gida.

Na ci gaba da abin da nake yi amma daga inda nake ina iya juyo hucin Baban Kaduna da ajiyar zuciyar da yake yi akai-akai. Ba a jima ba suka shiga shigowa daya bayan daya da sallama yana amsawa a wahale.

Zuwa lokacin Hajja ta idar suna ta gaggaishe ta tana amsawa. Sannan ta dubi Baba Muntari da kulawa da kauna ta manyantaka, ta ce, “Wa ya tabo Muntari ne? Wannan sammako da taron gaggawa haka?”

Baban Kaduna bai tanka ba ya ciro takarda cikin breif case dinsa ya mikawa Baba Na’ibi, Baba Na’ibi ya karanta ya mikawa Ibrahim, Ibrahim ya mikawa Barau, Barau ya mikawa Sadi, Sadi ya mikawa Sani, Sani ya mikawa Salisu, dukkansu suka hada baki suka ce da Hajjah.

“Takardar withdrawal ce (kora daga makarantar Fa’iz Abubakar Mukhtar) daga Polytechnic a bisa hujjar rashin zuwa aji kwata-kwata, rashin contineous assessment (CA), sai za ayi jarabawa kawai yake zuwa. Idan kuma ya je yadda aka ba shi answer sheet haka yake ajiye ta baya iya rubuta komi a ciki, sai sunansa da registration number. An dora shi a kan (probation) tun shekarar baya bai gyara komai ba”.

Duk suka yi shiru suna sauraron cewar Hajjah. Ta jima ba ta yi magana ba, sai daga bisani ta ce, “Ba zan ce komai ba sai na yi magana da Hafizin”.

Baba Muntari ya zo iya wuya, ya ce, “Ki gafarceni Hajja, duk lalatar da Fa’iz ke yi don ya samu faragarki ne. Na yi na yi a daina bai wa Fa’iz mota kin ki. Ba shi da aiki sai tukin mota da gyaranta in ta lalace, duk kanikawan garin nan sun san Fa’iz, in ya ce miki yana makaranta to yana tashar mota.

Jiya-jiyan nan (C.I.D) din da nasa ya dinga bibiyar min shi tun lokacin da ya ce miki ya kama daki a makaranta jikina ya bani ba haka kawai ba, don mutumin da karatun boko bai dame shi ba me ya kai shi tarewa a makaranta? To rahoto ya zo min cewa, Fa’iz ba a makaranta ya tare ba yana Kaduna Express (tashar motar Kaduna) ya zama direban peageout da express masu zuwa gari-gari ba ya makaranta.....”

Gaba daya suka dauki salati har ita Hajjah. Ban san sanda dariya ta kubuce min ba, na yi hanzarin shigewa toilet na sheka abata na more. Ban dai ji karshen tattaunawar tasu ba sai fitar su bayan sunyi mata sallama. A raina na ce, hakki ba karya bane. Ina zaace hakkina ba zai lalata Hafizin Hajjah ba.

Washe gari ina wanka Fa’iz ya shigo falon Hajjah, jikina duk kumfa amma haka na kwara ruwan na fito kar labari ya wuce ni, ina ji Hajjah na cewa, “Ubanka gata yake maka, kyakkyawar rayuwa yake so maka ba wani abu ba.....”

Ina jin sanda yake ce mata, “Hajjah ina da matsala ne, hannuna kyarma yake duk lokacin da na rike biro. Hajjah bana iya rubutu”.

Abin da ban taba ji ba a duniya, wato shesshekar kukan Fa’iz. Ya ci gaba da cewa, “Hajjah ko wacce makaranta ce na yarda a kaini, amma kada a rabani dake. Ba zan iya rayuwa bakya kusa dani ba Hajjah. Akwai wata makarantar irin ta ai a nan Zariya a kai ni mana. Wallahi na yarda zan je, amma ni bana son in yi nisa daku ko kadan, don Allah ki taimake ni Hajja, ke kadai ce za ki iya lankwasa shi”.

Hajjah ta dauki carbinta tana kokarin ficewa daga dakin kada ya karasa karya mata zuciya. Hajjah Hadija da Hafizinta Fa’iz (Abubakar) sai Allah.

Cikin dauriya ta ce, “Na gama maganar nan dasu tuntuni Fa’iza za ka Rasha (Russia) kana so ko baka so. In kuma ka isa, je ka ce dasu baka so ba za ka ba. Sun ce kasashen da suka ci gaba ba a yin rubutu da biro ya yin duk wani abu da ya shafi karatu, tafawa ake a computer (typing). Tunda dai ba ni na kawo maganar nan ba Ubanninka ne, to don Allah ka shafa min lafiya”.

Shiru Fa’iz ya yi yana tsane hawayen idonsa da hankici. Abun duniya duk ya bi ya dame shi. Ya san yau an canza masa Hajjansa, ‘ya’yanta sun gama yi mata famfo, kuma ya santa kaifi daya ce, tunda ta ce haka ba za ta taba canzawa ‘ya’yan nata ra’ayi ba.

Shi kam bai son ya tafi ne ba don komi ba sai don yarinyar nan Fa’izah ‘yar Maimuna za ta yi farin ciki ta sakata ta wala a gidan, don ya tabbata shine kadai matsalarta a zaman gidan. Shi kuma a duniya mai adawa ne da farin cikin Fa’izah, in da abin da ya ki jini a duniya to ya ga Fa’iza cikin walwala a gidan nan.

To wai shin meye dalili? Me yasa ya tsane ta kamar ba jininsa ba? Me ta yi masa ya tsane tan? Meye laifin ta? Meye aibunta? Me take yi wanda bai so? BAI SANI BA! Tabbas akwai katuwar (?) alamar tambaya cikin kwakwalwa da zuciyarshi game da yarinya FA’IZAH A.A. GIWA.

Watanni uku da suka biyo baya, Fa’iz ba shi da sukuni duk da yana cikin gidan kullum yana baskwata. Haka kuma a lokacin muna cikin zangon farko aji biyar. Damuwar har ta sabbaba masa ciwo, tun yana yi a tsaitsaye har ya kwantar da shi hajaran-majaran.

[6/3, 4:12 pm] Takori: Wannan ya ta da hankalin Hajjah ba kadan ba, ta yiwa Baban Kaduna maganar a kyale Fa’iz da tafiya karatun nan tunda abin ya kai ga taba lafiya.

Baban Kaduna ya ce, “Don Allah don Annabi Hajjah ki fita daga maganar nan kada kema ya kwantar mana dake, amma sai dai ya mutu na huta ganin dana yana direban tasha in dai ba zai yi yadda nake so ba”. Sai Hajjah ta yi shiru.

Cikin wani hutu da muka zo Fa’iz na shirya kayan shi cikin troller (akwatin tafiye-tafiyen bature) da muke kira (tura ni a tiles). Ummi ta yi sallama ta ba shi kaya cikin leda da Baba Na’ibi ya aiko masa ya yi guzurin tafiya.

Ganin yana loda kaya a jaka ta samu kujera ta zauna a gefensa a darare, ga mamakinta bai mata tsawa ba, bai hantare ta ba balle ya kore ta.

A hankali ta ce, “Yaya Fa’iz tafiyar kenan?”

Ya dago ya dube ta ya yi dan murmushi, “Eh, Ummi ya zan yi? Baban Kaduna ya dage. Daga nan Kaduna na nufa, daga nan mu wuce Kano inda zamu tashi ta filin jirgin Malam Aminu Kano ni da shi”.

Ummi hawaye ya cicciko idonta dai-dai sanda idonta ya kai ga wani karamin album saman kayanshi da yake hadawa. Ta dauka ta bude shafin farko ta shiga dubawa.

Shafin farko hoton Fa’iza ne ta yi tagumi jikin varanda ‘terrace’ na gidan Hajja.  Shafi na biyu kyakkyawan hoton Fa’izah ne ta yi tagumi a falon Hajjah. Haka shafi na uku Fa’iza sanye da koriyar suwaita mai kauri da jan siket kanta ba dankwali, wanda hakan ya sakko da jelunan kitson (shuku) dake kanta har bisa dogon wuyanta, tana rungume da (teddy bear) a gidansu dake Zaria. Sai kusan karshe ne ta ga hotunansu da sauran kannensa duka na Giwa da na Kaduna, har da su Walida amma 80% ba album din hotunan Fa’izah ne.

A matukar mamakance Ummi ta daga ido ta dubi Ya Fa’iz hankalinshi baya kanta yana ta shirya kaya haikan. Ta zari mai rungume da Teddyn ta ce, “Hoton nan ya yi kyau Ya Fa’iz in dauka? Fa’izah ba ta san da shi ba ma sam, don Allah ina ka same shi?”

A lokacin ne ya dago ya dube ta, ya zaro ido ya ce, “Ke! Wa ya ce ki taba mani album? Ina ruwanki da kayana?” Ya fauce album din ya danna a jaka ya ja zif. Ya shiga zuba mata bala’i ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Ummi dariya kamar ta kashe ta san (borin kunya ne yake nannade shi da hauka). Ta ce, “Ka yi hakuri Ya Fa’iz ban san baka so a taba ba”. Ta dauki wasu daga cikin hotunansa ta ce, “In dauki wadannan Ya Fa’iz?” Ya dube su daya bayan daya ya ce, “Me kika ce?”

Ta mike da hotunan a hannunta za ta fita, har ta kai bakin kofa ya ce, “Tsohuwa!” A kufule ta juyo don ya kirata da sunan da ta tsana a rayuwarta, amma ga mamakin Ummi sai ta ga ya yi murmushi.

“Don mi kike son hotona bayan duk kun tsane ni don kawai ina gaya muku gasiya?”

Ummi ta girgiza kai tana dariya, ta ce, “Allah Ya Fa’iz bamu tsaneka ba, daman can kai ne ka tsanemu, kuma mu har mun manta ma wallahi. Mun san kuruciya ne ga shi yanzu tunda ka shiga Poly ai baka cika shiga lamarinmu ba balle ka takura mana. Wani abin ma in aka ce ka yi ai ba za ka yi ba”.

Ya ce, “Ko? In ku kun manta ai Hussainar taku ba za ta taba mantawa ba. Domin na zalunceta na wulakanta ta na ci mata mutunci da yawa, wanda nima wallahi ban san dalili ba. Yanzu har nauyinta nake ji saboda halin RAI da muhimmancin ZUMUNCI, kunyarta nake ji wallahi-wallahi Ummi.....”

Ummi ta yi sakatoto! Tana duban sa cike da shakkar ba da Fa’izu (Abubakar) take magana ba, wani ne dai mai matukar kama da shi. Ko kuma mafarki take yi.

Ta ce, “Yaya Fa’iz wai kana nufin Fa’izah?”

Ya girgiza kai ya ce, “It may be itan, it may also be kuma ba itan ba.....”

......”Ban gane ba?” Ummi ta tambaya her voice is trembling (muryarta tana rawa).

Ya ce, “Ba za ki gane ba Ummi, kowa ma ba zai taba ganewar ba, amma Allah ya ga zuciyata na yi nadama da dana sanin abin da na yiwa Fa’izah”.

Ummi ta dan yi zuruu! Tana dubansa, ta ce, “Na tabbata na kuma hakkake cewar Fa’iza ba ta rike ka ba sam a zuci Ya Fa’iz, kullum addu’arta Allah ya shiryi Ya Fa’iz ya ganar da shi illar ‘KARYA, MUGUNTA, ZALUNCI da muhimmancin zumunci”.

Fa’iz ya dafe kai ya dubi Ummi duk idanuwansa sun sauya launi, ya ce, “Yanzu Ummi duk da wadannan sunayen Fa’izah ke kallo na? Kuma haka Ummi?” Tune din muryarshi wannan karon (in subdued) a karye.

Ita ma Ummin ta karaya a wannan gabar, ban da girgiza kai alamar, “A’a”. Ba abin da ta ce. Ya yi mata alamar ta tafi kawai ta kyale shi.

Washe gari kowa ya shirya za a tafi rakiyar Fa’iz, sai na zari mayafi na yi wuf na shige gidan Baba Barau na buya a kitchen. Neman duniya Ummi ta yi ba ta ganni ba, dole suka hakura suka shiga mota.

Daga tagar kitchen din ina hango shigar Ya Fa’iz mota, yana dan waiwaye kowacce kusurwa ta A.B Bamalli Estate kamar mai neman wani abu. Daga bisani ya shiga motar Ya Aliyu ya ja suka fita a get din.

Na yi wata irin doguwar ajiyar zuciya kamar an zare min kaya a kafa, kamar kuma an sauke dutsen Dala da Gwauron Dutse daga kaina. Na yi wata irin kakkarfar ajiyar zuciya.

                            ****


BAYAN SHEKARA DAYA

Shekarar ta zo ne da tarin sauyuka masu yawa cikin A.B Bamalli Family. Tafiyar Fa’iz da tafiyar Yaya Aliyu bada jimawa ba jami’ar Lagos yin digiri na biyu.

Don haka a hutu na gaba da muka zo mun yi kewar Yaya Ali ba kadan ba. Na yi kiba na yi bul-bul na dan yi haske dai-dai misali, sai sheki da kyalli nake yi, ke kuwa babu fargabar Fa’iz ko kadan wanda shine kadai matsalata a rayuwa.

A wannan hutun da muka zo ranar wata asabar ina dakin Hajjah ina sallah na jiyo sassanyar muryar Yaya Aliyu a tsakar gida yana gayas da Hajjah. Bai tambayi kowa ba, bai tambayi komai ba daga gaisuwa sai “Hajjah ina Fa’izah ne? Ban ji motsinta cikin gidan nan ba”.

Hajjah ta ce, “Tana ciki, nake jin sallah take. Ka san in aka soma doka nafilfilin nan sai Allah. Ai ma hushi ake da kai tunda ka tafi Lagso ba sako ba aike balle waya”.

Ya kama kai abin ban dariya, ya ce, “Oh! Ni Aliyu Bamalli na shiga uku!!” Ya yo cikin dakin da gudu-gudunsa. Hajjah ta yi dariya ta ci gaba da abin da take yi.

Zaneerah ta ya da tawul din da take tsane jikakken gashin kanta, ta zaro ido ta wara hannuwa tare da daka tsalle ta dire gabana ta ce, “Yaya Aliyuuu! Muryarshi a tsakar gida Fa’izah!!” Ta yi wuf ta yi bakin kofa zata fita.

Na ce, “Ke Zanirah baki da hankali ne? Haka za ki fita daure da tawul?” Zanirah ta dubi kanta ta ce, “Oh! Na gode Fa’izah, kin san Allah duk na rude sabida murna”.

Na bita da kallo a lokacin da take zurma doguwar riga a jikinta, jikinta har rawa yake yi. Ni yadda take rawar jiki a kan Yaya Aliyu da al’amarin sa, ko ni da ya fi nuna kulawarsa a kaina bana yin hakan balle irin wannan zumudin,  ni haushinsa ma nake ji wallahi tunda ya tafi bai neme mu ba, ba waya ba sako.

Tana kokarin fita yana kokarin shigowa, sai suka yi karo garam! Ya yi hanzarin ja da baya tare da ware ido.

“Zanirah kin makance ne?”

Da gudu ta nufe shi ya yi hanzarin kaucewa a hankali ya ce, “Zanirah kin girma, shekaru goma sha biyar, kada ki sake ki kara yi min irin wannan oyoyon kin ji ko?”

Ko ni kaina ba don na nutsu ba da ba zan ji shi ba, domin cikin kwantaccen sauti ya fada.

“Wannan sai su Hanifa sune yara (diyar Baba Sadi)”.

A raina na ce, “Ai ko Hanifa ba za ta yi haka ba, ita ma Zanirar ban san yau ina ta samo wannan bakuwar al’adar ba wadda sam bamu tashi da ita ba. Amma da na yi la’akari da dadewar da muka yi bamu ga Yaya Aliyu ba, sai ban ga laifinta ba, at the same time, na yi mata uzuri da ajizanci wanda dan Adam baya rabo da shi.

Zanirah na dariya ta ce, “Yaya Aliyu ka rage min fa, da watanni biyar cur!” Ya ce, “Yar gari, ashe kina sane?”

Bai koma ta kanta ba ya shigo ya russuna har inda nake, kamshin daddadan turarenshi ya doki masunsunata.

“A roka damu Alasabbinaki”.

Na zumbura baki na gyara zaman carbina cikin hannuna na kau da kai. Cikin dariya ya sassauta murya ya ce, “Na yi laifi ne Princess? I’m so sorry. Wallahi ban yi da niyya ba....”

Na kara turo baki na kau da kai. Yaya Aliyu ya yi dariya ya sa hannu cikin bakar leda ya bude, kamshin wani irin lafiyayyen balangu ya doki hancina.

Na hadiye wani tsinkakken miyau ji kake mukut! Dariya ta kashe Yaya Aliyu. Ya sa hannu ya zare carbin ya tura min kunshin balangun gabana. Ai ban bata lokaci ba tuni na ja kunshin leda cinyata na juya mai baya, na manta da fushin na soma dauka ina dannawa wani na bin wani.

Zanirah ta zo ta zauna za ta ci na doke hannun ta, ta ce, “Yaya Aliyu Fa’izah kadai ka sayo wa?” Muryarta abin tausayi.

Ya ce, “Eh, domin shine favourite dinta, kowa ma na sayo mai abin da ya fi so a rayuwarshi”. Ya sa hannu a aljihu ya fiddo alawar cakulet mai kwakwa (Bounty) ya mika mata. Zanirah ta yi tsalle ta cafke ta yi waje, na tattara ledar namana na mike zan bita amma Yaya Aliyu ya rike gefen hijabina, gaba daya na juyo.

“Wai me na yi ne don Allah Fa’iza? Na taho gari ya gari tun daga Lagos domin ki amma kike zumbura min baki?”

Na bude baki cikin mamaki na ce, “DOMIN NI?”

Ya yi saurin girgiza kai, ya ce, “A’a, DOMIN KU”.

Na ce, “To sakar min hijabin na gaya maka kada Hajjah ta shigo”.

Ya yi saurin saki. Na koma na zauna na ce, “To don me tunda ka tafi makaranta ba sako ba waya Yaya Aliyu? Don me za ka koma makaranta Yaya Aliyu?”

Ya yi murmushi ya ce, “Fa’iza ke yanzu ba makaranta kike ba?”

Na ce, “To in anyi degree ba shi kenan karatun ya kare ba? Da dadewa na taba jin an ce ka yi digiri”.

Ya girgiza kai “Is just the beginning Fa’izah digiri na farko shine tushen duk wani ilimi. Ilimi ba shi da iyaka, ba shi da karshe sai dai ka yi iya wanda za ka iya ka bari. Ina so na yi ilimi mai yawa ba digiri kadai ba, ko baki son wata rana in zamo Farfesa kamar Baban A.B.U? In yi gida nawa na kaina a duk inda nake so a outside ba a A.B Bamalli Estate ba cikin kauyen Giwa? In yi family mai tsari irin na Baban A.B.U? In yi rayuwa mai tsari irin ta Baban A.B.U? Ba irin ta su Baba Barau ba Fa’izah”.

Ban san sanda na tuntsire da dariya ba. Na ce, “Ai ni na yi zaton don ka gaji da kai mu makaranta da dauko mu ne da zuwa mana visiting shi ya sa ka koma karatun don ka gaji da saya min nama, Zanirah (Bounty) Ummi (Kit-kat), ka gaji da kai mu shopping da koya mana karatu, shine ka tafi”.

Dariya mai suna dariya kam Yaya Aliyu ya yi ta har ya gaji, ya ce, “Fa’iza yaushe za ki daina wauta ne don Allah? Shin in tambaye ki, da can waye ya sani yi muku hidimar makaranta? Waye ya sani sai muku balangun da alawa? Waye yake sani in kula daku in ba don ina son ku ba?

Na rantse da sarkin sarakuna ba zan taba gajiyawa da hidimta miki ba muddin rayuwata! Ko da bani da shi, zan yi aikin karfi da lafiyata in nemo in yi miki in har za ki yi farin ciki. Balle kuma alhamdulillahi Allah ya hore mana arziki na duniya dai-dai gwargwado, ta yadda har nake raina ‘yar hidimar da nake muku wanda har ke kike kallon ta kike kiranta hidima.

Ko da duk abin da na mallaka zai kare wurin sai miki nama ba zan damu ba, saboda dalilin da har yanzu kika kasa ganewa. Kada ki kara saka wannan a ranki (wai ina yi muku hidima), kada ki kara tunanin hakan, sa a ranki wannan Dutyn Aliyu ne”.

Ina wani irin murmushi mai fitowa tun daga karkashin zuciyar dan adam na ce, “Ba zan kara ba Yaya Aliyu”.


                        *****

Washe gari muna gidan Baba Na’ibi (gidan su Yaya Aliyu) muna kallon wani wasan kwaikwayo na ANTAR-BN-SHADDAD da ABLAH, domin mu zuri’armu kaf daga shekara kasa da sha takwas, ba a kallon finafinan Turawa, na Hausa ko na India, ko na ‘yan kudu (Nigerian Film), sai hikayoyi na Larabci da Risalah, ko tarihin Sahabbai da ake yi a matsayin film kamar na Khulafa’ur-Rashidun.

Domin wannan finafinai da na zayyano a sama a ganin Hajjah duk nau’i ne na illata tarbiyyar yara da hana su mai da hankali ga karatu. Daga na yake-yaken Larabci (Adventure) sai zaluncin da Isra’el ke yiwa ‘yan’uwa musulmi na yankin Gaza, sai Islamic Channel wadanda suke nuna halin da kasashe marasa karfi ke ciki, irin su Somalia da irin tallafin da NGO’s suke yi musu, irin su ‘Human Appeal Organization’ masu daukar nauyin irin wadannan kasashe ta hanyar abinci, ilimi, asibiti da tufafi.

Wadannan al’umma masu ban tausayi abubuwa ne dake karawa yara imani da wadatar zuci. Sai ko labaran Larabci na Al-jazeera, CNN, BBC. Saboda yawan kallon al’amuran Larabawa da nake, da sauran labaran Larabci da kallon rayuwarsu a talabijin, dadin-dadawa ana yin Larabci as (Subject) a ajinmu, sai ya kasance na iya Larabci sosai, kuma shine harshe mafi soyuwa a gare ni tun ina (Area One). Tun ina karama Allah ya dora min kaunar Alifun-Ba’un, Alifun-Arnabun, Ba’un-Baqaratun.

Maryam ta dube ni muna cikin kallon ta ce, “Wai me Antaru ya ce kenan Fa’izah?’ Na fassara mata, ban ida rufe bakina ba Yaya Aliyu ya shigo.

Ya samu gefen mahaifiyarshi ya zauna, ta ce, “Ya ya dai Yayansu? Na ganka rather moody? In ce ko ka dauki abincinka ka ci?”

Ya dan yi tsaki ya ce, “Mama na sha kunun alkama fa a wurin Hajjah yanzun nan”.

Ta dube shi tsaf, cikin babbar murya ta ce, “Aliyu!” Da hanzari ya dago ya dube ta.

“Na gaji kullum magana daya ta ki ci ta ki cinyewa. Yanzu kamar kai Aliyu sai an rarrasheka ka ci abinci za ka ci, sai ka ce wani karamin yaro, da gangan kake wasa da lafiyarka, to na daina, sai dai ka kashe kanka kai kadai, wallahi ka kwanta ciwo ko hanyar asibiti ba za ka ganni ba. Ko da yake in ka kashe kanka ai kai ka jiyo, wa ka yiwa asara?”

Na juyo daga kallon T.V na ce, “Mama mu mana? Mu aka yiwa asara”.

Zanirah ma ta ce, “Tabbas mu ya yiwa asara,  we cannot, never found a caring brother like him, Yaya Aliyo don Allah daure ka dinga cin abinci in ka mutu mun shiga uku”.

Na ce, “Mun shiga uku ko mun shiga tara?”

Ummi ta ce, “Har mun lalace”.

Zanirah ce ta mike ta yi kitchen da zafin namanta, ta shako plate da dankali soyayye da murtukekn kwai, ta zo ta zauna tsakanin Mama da Yaya Aliyu kasancewar suna zaune kujera daya ne mai cin mutum uku.

Cike da kulawa ta mika mishi, kana cikin muryar lallashi da kulawa ga karamin yaro in ya ki cin abinci ta ce, “Yaya Aliyu don Allah ka ci”.

Gaba daya aka kwashe da dariya har Maman dake bambamin fada, babu shakka yadda muke kula da Yaya Aliyu da hidimarsa, da yadda shima yake kula damu da al’amuranmu, yana yi mata dadi, don ko Maryam da suke ciki daya ba ta kulawa da al’amarinsa kamar yadda muke masa, haka shima.

Ga shi tana masifar son Yaya Aliyu kamar ba dan fari ba. Ita cikakkiyar lauya ce mai zaman kanta, sam ba ta irin kawaicin Momina, mu’amalarta da Yaya Aliyu kamar ta Yaya da kaninta mai binta da suka fito ciki daya. Hakan ba karamin bani sha’awa yake ba, in yi ta dakacen ina-ma a ce nice.

Na taso tsam daga inda nake zaune zuwa garesu na ce, “Mama tashi ki bamu fili in bai ci ba dura zamu yi masa”.

Ita da Yaya Aliyu suka sa dariya, ta ce, “Lallai kam ‘yammatan Hajjah kadan daga aikin ku, kuma aikinku yana kyau, Allah ka bani tsawon ran da zan ga da wacce za ayi tsakanin ke, Ummi da Zanirah.....”

A hargitse Yaya Aliyu ya yi ma Mama gyaran murya ga alama bai ji dadin abin da ta fada a gabanmu ba. Ta mike ta bar mana falon tana dariya tana fadin “Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba”. Sai da muka tilastawa Yaya Aliyu ya cinye abincin nan tas, sannan muka kyale shi.

Ya ce, “Ummi ban ji yadda aka riski Queen Amina ba?” Ta ce, “Tambayi gimbiyar taka mana ni ai baka yi dani Yaya Aliyu, ka kawo mata nama, Zanirah pack din Bounty, amma ni ko sannu don ni lukuta ce tun ranar da ka fada Zanirah ke tsokanata ba a yayin lokutayen mata”.

Ya murmusa a hankali, ya fiddo pack din kit-kat a aljihunsa ya cillawa Ummi. Ta dauke tana dariya tana godiya, ya ce, “Saboda Allah Zanira ina ruwan ki cikin wannan maganar har da kike tada ta bana nan?”

[6/3, 4:12 pm] Takori: Ta ce, “Rabu da ita Yaya Aliyu, ita ta fara ce min mai wuya uwa marikin lema, an fada din, ba a yayin lukataye sai ‘slim’ din ki yi duk abin da za ki yi”.

Ya fiddo mata ido ya ce, “Kada na kara jin irin wannan maganar, babu kyau gorin halitta Zanirah, kada na kara ji”.

Ummi ta ce, “Rabu da ita Yaya Aliyi, so take jikinta ya gaya mata ta ga ranar lukutin jiki, sai shegen cika bakin tsiya babu kwanji, don ta ji Hajjah na cewa ta girmemu to ba shekaru biyu ba ko goma kika bani in kika kara ce min lukuta lallasaki zan yi”.

Yaya Aliyu ya rasa inda zai sa kansa don dariya, ya ce, “Ana girma ana cin kasa Ummi da Zanirah! Inda Fa’izah ke burgeni kenan, tunda kuka shiga aji hudu ta watsar da shirme ta bar muku”.

Ummi ta ce, “Eh, ai daman a wajenka Yaya Aliyu Fa’iza ba ta laifi, ita ce ta iya komai, bayan ita din a bayan idonka tantiriyar kanta ce”.

Yana dariya ya ce, “Bakya son a fadi gaskiya, amma Fa’izah ta fiku hankali, nutsuwa da kamewa. Ko zaman wuni guda mutum ya yi daku zai fuskanci haka”.

Ummi ta sake kuluwa, ta tashi faram-faram ta fice. Yana kiranta yana ba ta hakuri amma ba ta juyo ba. Zanirah ko a jikinta, daman ita yarinya ce mai matukar sanyi cikin al’amuranta ba ta da fushi, ba ta da daukar zafi ko kadan a kan duk abin da za ka yi mata, da wuya ka ga bacin ranta. Kullum fuskarta cikin annuri take, ita dai barta a cika baki da kokarin karatu kamar Alhuda-Huda.

Ya maido duban shi gare ni ya ce, “Fa’izah ba a bani labarin Sarauniya Amina ba”. Na ce, “To Yaya Aliyu me zan ce maka ga yara duk sun zubo min ido?”

Maryam ta ce, “Lallai ma, su waye yaran naki?” Na ce, “Gaku nan mana juniors ‘yan JSS”. Ta ce, “Mts! Ke har yaushe kika fara SS din da za ki raina mutane?”

Yaya Aliyu ya ce, “Ke rufe mana baki ko na hambareki, wa ya sako ki cikin zancen nan? Ko sa’arki ce?” Na faki idonsa na yi mata gwalo, ta dalla min harara.

“Maza dauko biro da takarda ta rubuta min labarin Queen Amina”.

Zanirah ta ce, “Ba za ta iya ba Yaya Aliyu, ba ta iya Turanci sosai ba”.

Ya ce, “Da kowacce luggah Fa’izah rubuta min labarin Queen Amina, be it Hausa, Arabic, English, Fulfulde, Kanuri, Yoruba or Igbo, in har kika rubuta am sure zan iya karantawa in fahimta”.

Da karsashi na karbi takardar da biro, na matsa nesa dasu na soma yarfawa Yaya Aliyu kyawawan rubutu da harshen Larabci tsaftatacce. Na mika masa ya shiga karanta musu a fili, ga fassarar abin da na rubuta.


“Yaya Aliyu mun je Queen Amina lafiya, makarantar Sarauniya Amina babbar makaranta ce mai kyawun tsari, tsohuwa mai tsohon tarihi. Malamansu da dalibai duka masu kwazo ne. Bamu da kawaye, amma muna gaisuwar musulunci da duk wanda wata mu’amala ta hadamu da shi. An kai ni ajin Arabic, an kai Ummi ajin zane-zane (Art) saboda shi ta fi iyawa.

Akwai club-club a Queen Amina, irin su Maths Club, English Club, Jet Club, Arabic Club, Hausa Club, Science da sauran su. Na raba kafa na shiga Clubs har guda biyu, wato Arabiyya da English Clubs, Ummi ta shiga Jet don Allah bai halicce ta da kwakwalwar rike karatu ba, Jet kuma ana koyar da sana’o’in gida ga dalibai ne.

Aunty Hauwa ba ta kulamu ba ta neman mu, ta ce don ita muka dawo Queen Amina, don haka ba ruwanta damu mu manta mun santa, ba abin da take kawo mana daga gidanta ta ce mu karata”.

Nice Kanwarka.

Fa’izah A.A Giwa.


Yaya Aliyu ya ajiye takardar ya ce, “Good, very good, a tafawa Fa’iza, na ce a tafa mata!” Raf! Raf!! Raf!!! Suka hau tafi. Ya yin da Yaya Aliyu ya shiga manna min sababbin wa-zo-bia a goshina har guda shida.


****

To haka rayuwarmu ta ci gaba da mikawa, tafiya ta yi tafiya. Shigarmu ajin karshe a sakandire na dauke da wasu muhimman al’amura da ba zan taba mantawa dasu ba cikin tarihin rayuwata. Don haka ya zama dole in farka shekarar baki dayanta.

Alal hakika a lokacin na fara wadatuwa da abin da ake kira “Hankali” wanda yawan shekaru ke samar da shi. A lokacin ne kuma na fahimci mu’amalata da Yayana Aliyu ba komi ba ce illa SOYAYYAH! Soyayya ce muraran yake nuna min cikin ‘yan’uwana baki daya ba tare da shi kansa ya sani ba, a gaban kowa baya iya boye kulawarsa gare ni. Duk dangi babu wanda bai kwana da sanin matsanancin son da Yaya Aliyu yake min ba ko ba a furta ba.

Sai dai da bakinsa bai taba ko da kuskuren gaya min da fatar bakinsa ba, sai dai actions and emotions dinsa su nuna. Ko da cikin hira ya yi subul da baka sai ya yi kokarin gyarawa ya mai da zancen ko subutar bakin sa (otherwise).

Shekaru na goma sha takwas kenan, duk wani budurci ya tabbata gare ni. Hankali da nutsuwa sun wadace ni. A zahiri, tunda na soma hankalin nima nake so da kaunar Yaya Aliyu, so ba na wasa ba. Cikin kannena da tsararrakina da danginmu duka zancena daya ne (Yaya Aliyu). Shin don mene ne ba zan so Aliyu ba.

Mutumin da ya kwashe shekaru goma sha daya yana kula dani, kulawar da iyayen da suka tsuguna suka haifeni basu yi min ita ba. Yana bauta mini, yana dadada mini, yana faranta mini. In har ban so Aliyu Na’ibi ba, wallahi ni butulu ce cikin butullun ababen halitta wanda zuciya ba ta aiki a jikinsu.

Tun daga aji biyar na sakandire na dauki wasa na aje gefe, na bude file na sanya shi na adana a cikin akwatun karfe. Na yi “facing” karatuna yadda duk wani dalibi na kwarai ke yi da taimako da shawarwari da kulawa tattare da kwarin gwiwa irin na Yaya Aliyu.

Allah ya hore min baiwar kirkira (fiction) na labarai masu ma’ana da fadakarwa ko kuma articles, ina ba da wa ana sanyawa a magazine din makaranta, fili guda aka ware min a mujallar makaranta mai suna ‘KNOWLEDGE IS LIGHT’ tare da Fa’izah Ahmad Abubakar (English Club). Nice kan gaba a fita muhawara (Quizz and Debate) din duk da za ayi da harsunan nan uku, Hausa, Turanci da Larabci.

Da farko in na yi rubutun ‘yan ajinmu nake bai wa su karanta in ajiye, daga bawa shugaban clud dinmu ya karba ya duba sai ya mika shi ga hukumar makaranta. A lokacin an canza Yaya Hauwa daga principal an kawo Haj. Amina Atiku. Ita ta fara dubawa ta ce “Akwai ‘sense’ da ‘exceptional talent’ a ciki”. Rubutuna ya burge principal dinmu sosai, ya kuma bawa malamanmu da yawa mamaki da sha’awa.

Wani novel ne na rubuta labarin wata Bafillatanar yarinya da wani dan makarantarsu da yake taimaka mata a fannin karatu, kasancewarta dakikiya har ta zamo zakakura sahun gaba a masu kokarin makarantar.

Jin dadin hakan ne ya sa ta yi masa alkawarin za ta aure shi da zarar sun gama karatun sun samu aikin yi. Tsawon shekaru takwas tana dakon alkawarin. Bayan nan suka rabu kowanne ya koma wata duniya daban. Ga shi ta yi alkawarin ne a shekarun odolscence (goma sha uku ba ta gama mallakar hankalin kanta ba, ba ta san mene ne alkawari ba da muhimmancinsa balle SO, kauna da auren kansa).

Rayuwa ta mika, bayan rabuwarsu ta ci gaba da jiransa. Katsam Barister Haseen Danbatta ya fado cikin rayuwarta, wanda ya fassara mata hakikanin mene ne so, ya karantar da ita fannoninsa from every angle, dadinsa, dacinsa, zakinsa da rashin dadinsa, bambancin so, kauna, kusanci, shakuwa da halacci.

A zahiri wannan shine mutumin da zuciya da ruhinta ke so, suka kuma aminta da shi. Gangar jikinta da tsokar zuciyarta baki daya ke buri tun kafin bayyanarsa. Ga shi iyayenta sun takura mata da ta fidda mijin aure haka nan, shekaru takwas tana jiran wanda ta yiwa alkawari ya kuma yi mata halaccin da ba ta taba jin an yiwa diya mace ba.

Abin da mai karanta labarin zai tambayi kansa shine, shin za ta ci gaba da jiran wanda ta yiwa alkawarin ko kuwa za ta watsar da halarcin da alkawarin ta auri wanda zuciyarta da rayuwarta ke so? Labari ne tsakanin soyayya da alkawari da na sanyawa suna ARE VOWS MEANT TO BE BROKEN?

Ga shi na yi shine cikin sassaukan Turanci dai-dai karantawar dan sakandire, kuma dai-dai iyawata. Gyare-gyaren da malamar English Language dinmu ta yi min a ciki ba mai yawa bane, grammertical correction ne ta yi. Sai ka rantse da Allah Abubakar Gimba ne ya rubuta.

Principal dinmu ta kirani ta ce za a kaddamar da littafin ranar da zamu gama makarantar, kuma za a buga shi a dinga saidawa a makarantun da ake yin Literature da kasuwanni don sauran al’umma masu karatun Novels don nishadi. In yaso sai makaranta ta rike ribar, amma duk abin da aka samu wajen kaddamarwar nawa ne.

Da wannan daddadan labarin na tarbi Yaya Aliyu a wani visiting da ya zo mana. Na zaci zai yi farin ciki, amma sabani ga tunanina ya yi shiru bai ce komai ba. Na ce, “Baka ji dadi bane Yaya Aliyu? Na dauka abin kirki na yi? Na yi zaton wannan abin farin cikin mu ne duka?”

Ya ce, “Ba wai ban ji dadi bane da hikimarki ba Fa’izah, amma ina son ki san wani abu guda daya, taura biyu ba ta tauno, tunda karatu kika zo yi ba rubutu ba ki mai da hankali ki yi karatun nan. In kin kammala kin san dai hajjah ba barinku zuwa jami’a za ta yi ba AURE  za ta yi muku. Sai ki yi ta rubutun da za ki yi a gidan aurenki, ni kuma na dauki nauyin wallafawa”.

Na ce, “Yaya Aliyu na san wannan, amma komai da lokacin da na ware mishi cikin al’amuran rayuwata. Wallahi bana rubutun da malami cikin ajinmu, ko ana karatu sai a karshen sati (week end)  da (prefs), a sa’ilin da bani da ‘test’ ko ‘exams’ a kusa. Wato lokacin da ya kasance farko-farkon ‘term’. Inda bana karatu da ban kawo maka positions masu kyau ba ai”.

Ya ce, “Shi kenan Fa’izah, ai ko lauya nan ya ganki ya barki wurin dadin baki da kawo hujja da persuation. Allah ya taimaka. All the best my sister. Cross word!”


****

A shekarar aka nada wakilan malamai bayan tafiyar ‘yan aji shida, na yi mamaki matuka da aka kira ni Fa’izah Ahmad Bamalli Giwa a matsayin AMIRA! Aka kuma nada Ummi Gate Prefect. A hostel su Naja’atu Room-mates din mu ke yiwa Ummi dariya, domin ita Naja ta amshi dankwalin Head-Girl ne, ya yin da Haulatu Sani ta karbi Labour Prefect..

Ummi ta ce, “Aikin kawai, a rasa dankwalin da za a baiwa mutum sai na bakin kofa? Wani ya ce ina son mukami da za a hadani da gate?”

Muka tuntsire mata da dariya. Haulatu ta ce, “Khadija Sabi’u ke ce baki sani ba, cika idonki ya sanya (Vice-Principal) baki wannan dankwalin, don kin san an ce alamar karfi na ga mai kiba, ta san za ki yi fada (Ummi na da jiki sosai) ga masu yin latti da ‘yan komawa hostel during school hours. Zaki cikawa dalibai masu latti ido da kwarjini. Yawancin mata masu jiki fada gare su”.

Ummi ta yi tsaki ta ce, “A kan me za a bawa Fa’iza Ameerah? Wa ta fi tsoron Allah? Yarinya mai shegiyar tsiwar tsiya”. Naja ta ce, “Ai kuwa Fa’izah ta cancanci dankwalinta. Dalili;

-Duk da ta fimu nutsuwa da kula da addini.

-Zuwa jam’i a kan lokaci.

-Tun zuwanta Sarauniya Amina kullum sai ta share masallaci.

-Ita take riga kowa zuwa masallaci da asubah.

-Ta fi kowa iya Larabci, ta fi kowa iya karatun Alkur’ani, ta fi kowa iya kira’a da Tajweed. In ba a baiwa Fa’iza Ahmad ‘Amira” a makarantar nan ba ki gaya min wa za a bawa?”

Bakin Ummi ya mutu. Naja’atu ta ci gaba da cewa.

“Duk fadin Sarauniya Amina babu mai tsantseni da addini irin Fa’izah”.

Ummi ta ce, “Tana takurawa kanta ne kawai. Duk sanyi ba ta jin sa sai ta je masallaci da asuba. Da rana baka huta ba, da yamma baka huta ba haka dare. Ai ba zuwa masallaci yin sallah ne ke sanyawa Allah ya karbi sallarka ba”.

Haulatu ta ce, “Kin yi kuskure Khadija, duk taku daya zuwa masallaci lada ne da babu wanda ya san adadinsa sai sarkin sarakunan dake ba da shi. Sannan sallar jam’i ladanta ya ninka ta mutum daya, ko taka ba ta yi kyau ba Ubangiji zai duba ta na kusa da kai ya baka ladan, ai ba ma za a kwatanta ba. Kiwa ce kawai take damunmu Allah ya yaye mana”.

Ni dai ban tanka musu ba har suka gaji suka watse.

Washe gari Yaya Hauwa ta zo har ajinmu ta shigo da kaya a leda da wasika, ta ce, “In bai wa Ummi daga Fa’iz, jiya su Hajjah suka dawo Ukrain, sauran kayan bai yiwuwa a kawo su makaranta, in mun koma gida ta gani”.

Na ce, “Ayya! Yaya Hauwa da kin mika mata ajinsu don ni za ta bari da daukar kayan zuwa hostel”.

Yaya Hauwa ta yi dariya ta ce, “Ahaf! Na manta fa kayan da suka fito hannun Fa’iz-Abubakar ne, abokin fadan Fa’izah. Ya kamata ki yafi dan ‘uwanki haka girma ya hau ku ku manta kuruciyar baya, haka nan ‘yan’uwa kuke”.

Na yi dariyar yake kawai. A raina na ce, “Meye zai kankare kiyayyar Fa’iz a zuciyata? Wallahi babu shi Yaya Hauwa! Fa’iz bai so na, bai son mahaifiya ta, bai ganin girmanta balle darajarta, ya ya kuwa za ayi in taba shiri da shi a rayuwata??? Mu dai irin tamu ZUMUNTAR KENAN!

Na shigo dakinmu a gajiye tikis na ajiye (school bag) na zauna gefen gadona ina sabule socks (safar) kafa ta, na fada bayi na dan watsa ruwan sanyi a jikina, kasancewar ana tsakiyar yanayin zafi karshen watan Yuli.

Na fito na sanya riga da wando na yadin (house wear) dinmu na dan kishingida ina hutawa. Ummi ta shigo da gudu-gudu da kaya da takarda ta fado min a jiki tana shesshekar wata irin dariyar farin ciki, ta kara min takarda a fuska bayan ta zube kayan a gadona.

Sassanyan kamshin da takardar ke yi na turaren ‘Philips Lumea’ na daxe ban ji kwantaccen kamshi irisa ba, tun can wani lokaci mai tsayi da ya shude. Na lumshe gajiyayyun idanuwana a hankali na janye hannunta da takardar daga fuskata na dube ta cikin mutuwar jiki da ta zuciya gaba daya.

Ta kwanta kusa dani fuskarta dauke da annurin farin ciki da zumudi bayyanan ne, irin dai wanda kika sani a duk lokacin da wata zuciya ma’abociyar bege ta samu sakon masoyinta bayan lokaci mai tsaho.

Haulatu da Naja suka shigo suka zazzauna a gadon Ummi dake fuskantar nawa, daidai lokacin da Ummi ke fitar da kayan ledar da ta shigo da ita da Yaya Hauwa ta bani in ba ta na ki karbowa.

Littafin zane ne irin wanda su Ummi ke amfani dasu, alkaluman zane, penti kala-kala ‘yan waje da agogon hannu (hand-wrist watch) samfurin (L’OREAL) ruwan silver da zobe shima na silver dandasheshe mai kyau. Ummi ta sanya a yatsanta babban ya yi mata cif duk yadda ta juya hannunta sai ‘dot’ din zoben ya yi walainiya.

Ta rungume su Haulatu tana dariyar dadi gani kashe ni. Haulatu ta ce, “Hala sakon Yaya Fa’izu ne da kullum ake bamu labari mai cin zalin Fa’izah?” Ummi murna take, bakin ya gaza rufo, ta zaro hotuna cikiin ambulan din wasikar jikinta na rawa da karkarwa ta bude suka fara gani.

Kyakkyawa Fa’iz Giwa ne sanye cikin jibgegiyar rigar leda mai kare sanyi wadda ta sauko har gkwiwarsa, yana tsaye cikin dusar kankara baka ganin komai jikinsa sai fuskarsa, domin hatta hannayensa cikin bakaken safar hannu suke.

Hoto na biyu sanye yake cikin uniform na masu koyon tukin jirgin sama cikin karamin jirgi (jet) da wasu abokan karatunshi farare da bakake. Fuskarshi ta fi fitowa a wannan din sosai. ‘Yammatan uku suka ci gaba da kallon hotunan guda biyu suna kada kai kamar kadangaru, da kyar Naja’atu ta iya bude baki ta ce, “Khadija Yaya Fa’iz din ne?”

Ummi ta rungume hotuna cikin lumshe ido ta ce, “Yes, Fa’iz Bamalli kenan Naja’atu. Yau kinga yayanmu Fa’iz, tabbas Ya Fa’iz ne. Ni kaina ya canza min sosai fiye da yadda na san shi. Ya Fa’iz ya kara kyau kwarai, ya yi kiba da haske, ya kuma kara girma cikin shekaru uku kacal, kai abin da mamaki”.

Haulatu ta ce, “Amman yana da kyau fiye da ku duka, ko in ce fiye da dukkan zuri’ar A.B da na sani. Na so a ce yadda yake da kyau yana da mahadin sa wato kirki, amma kyau ba hali kyawun dan maciji ne Khadija”. (Can da jimawa Ummi ta sha basu labari na da Fa’iz tun daga kuruciya da rashin kirkinsa garemu).

Ummi ta yi murmushi kawai, ta ce, “Haule yadda kika ji labarin Yaya Fa’iz da Fa’izah ne kurum ya sanya kika fassara shi da haka, amma yana da kirki in his own unique way! Da za ki ganshi a zahiri rantsewa za ki yi ba zai ko kusa da taba iya aikata abin da yake aikatawa ba. Ni kadai na fahimci Fa’iz ciki da waje, zan iya rantsewa babu wanda ya kai ni sanin Ya Fa’iz a gidanmu, akwai dalilin da yasa Fa’iz yake kyarar Fa’iza wanda babu wanda ya sani sai shi daya sai Allah da ya halicce mu.

Amma wallahi ba gundarin halinshi kenan ba, koma da halinshi ne ni Ummi Khadija INA SON SHI HAKA! Zan iya jure kowane irin halinshi idan na yi sa’ar samun shi a matsayin miji. Ina son sa da yawa Haulatu, kamar yadda na fahimci shima yana sona kawai ba zai furta bane ko ya nuna kamar yadda Yaya Aliyu ke nuna ma Fa’izah. Ban san ina son shi ba Haule sai ranar da zai tafi”.

Ta yi shiru tana kallon yatsar kafarta kafin ta yi murmushi a hankali ta ce, “Wannan ya faru ne a dalilin babu auren na-gani-ina so cikin zuri’armu da family dinmu duka, sama da komai Fa’iz daban ne wajen halayya da dabi’a. Wanda zai ce miki ya san dukkan halinshi wallah ya fadi karya, saboda kullum sabon hali yake sakewa tamkar wahainiya mai canza launi daga wannan zuwa wannan. Irin wadannan mutanen ma’abota kaskantar da kansu ga abin da zuciyarsu ke matukar so tsiraru ne a cikin al’umma!”

Ta girgiza kai. Su kuma kamar masu daukar darasin tarihi, sai gyada kai suke, don haushi kamar na hada kawunan nasu su duka ukun na gwara, da suka tsaya suna sauraren shirmen Ummi da ba ta san inda ke mata ciwo ba.

Ta ci gaba da cewa, “Ni dai ku tayani addu’a Allah yasa Hajjah ta hadamu ni da Fa’iz, don in ba Yaya Fa’iz ta bani ba? Bana jin zan iya aure a rayuwata. Na gwammace in mutu haka nan ban yi aure ba. Zan jirayi Fa’iz ko da shekaru nawa zai yi bai dawo daga Ukrain ba in dai har Hajjah ba ta yi tunanin aurar dani ga wanin shi ba”.

A hankali na juyo da kaina sashen da su Ummi ke zaune, na dube ta tsaf. Shin mafarki nake ko ko a farke (idona biyu)? UMMI NA SON FA’IZ, FA’EEZ NA SON UMMI?

[6/3, 4:12 pm] Takori: “Wannan haka yake”. Daga can cikin wani sako na kwakwalwata aka bani amsar. Tabbas biri ya yi kama da mutum. Yawan zancen Fa’iz da Ummi ke yi har ya so ya baci. Bana jin akwai ranar Allah da za ta fito ta fadi, bakin Ummi bai ambaci kalmar ‘YA FA’IZ’ ba. Na kuma sha jin an ce ‘adadin  soyayyarka da abu adadin yawan ambatonsa a bakinka.....!;

“Amman Ummi kin cika banza, shashasha, dabba, mahaukaciya wadda ba ta san ciwon kanta ba.......!”

Ban san sanda kalaman suka yo ambaliya daga bakina ba. Kafin hawaye su shimfido a kundukukina. Na soma shesshekar kuka sosai. Su duka suka dube ni a razane. Na mike tsaye na shiga nuna Ummi da babban yatsana, idona a rufe bana ko ganin abin da yake gabana, na surfeta tas da zagin da ba ta taba tsammani daga gare ni ba.

A karshe na kare zancena da cewa, ......”Ummi in har kin yarda ki auri Fa’iz, ki sani karshen zumuncina dake ya zo, ko a hanya muka gamu babu gaisuwa tsakaninmu. Fa’iz kike so Ummi? Kyawun fuska ne zai rude ki ki manta da waye Fa’iz? Fa’iz Bamalli? Fa’izun gidan Babllan Kaduna ne fa, kyawun fuska zai rude ki? Mugu azzalumi, makaryaci, masharranci, mugun da bai san girman zumunci da girman iyaye ba. Mutumin da ya nuna mana kyara da tsangwama irin wanda wani dan’uwa bai taba nunawa wani dan’uwansa ba, Fa’iz HAFIZIN HAJJAH shi kike so Ummi?’

Muryata har dakushewa ta yi a wannan lokacin. Na dube ta da dukkan idanuna na ce, “Ummi kin manta baya? Kin manta duk abubuwan mugunta da tsanar da Ya Fa’iz yai mana? Shin farar fata koko zuwa Rasha ya rudeki ga son Fa’iz Ummi? Ko kuwa tukin jirgi da yake koyo.....?”

A nan ne ran Ummi ya yi mugun baci, domin da kallona kawai take kamar ta ga mahaukaciya. Ta ce, “Ke Fa’izah dakata, cin mutuncin naki ya isa haka, ya ishe ki kin ji ko? Kada ki kara don kuwa ni ba ‘yar cikinki ba ce da za ki sani gaba kina min wannan hayagagar ba tsoronki nake ba.

Da kin ki da kin so Fa’iz dan’uwanmu ne jininmu ne, ko me Fa’iz ya yi miki ya ci a ce kin manta haka nan as time goes on.... Haka kike da riko da gaba wanda ya wuce na musulunci? Wai ke baki san kuruciya bane? Ke abu baya taba zuwa ya wuce a wurinki?

Fa’izah ina son Fa’iz fisabilillahi na fada a yau na kara da babbar murya I LOVE FA’EEZ! Kuma insha Allahu shine mijina, ki yi duk abin da za ki yi, kada Allah yasa ki kulanin, kada Allah yasa mu yi zumuncin. In na auri Fa’iz don Allah kada ki zo gidana, in na haihu da Ya Fa’iz don Allah kada ki zo barka, kada kuma ki kawo riga ki ce a sawa dan ko atamfa in yi zanin goyo! In ce dai shine zumuncin?

Ni babu abin da Fa’iz ya yi min baya ga yanke gashi wanda daga baya ya zo ya zame min alkairi, domin ya zamo silar da na yi gashi irin wanda ban taba zaton zan yi ba (Fa’iz ya taba yankewa Ummi duka jelunan kitsonta da ya kamata a dakinsa ta dauki hotonsa ta boye cikin hijabi za ta fita).

Wata mugunta ko cin mutunci ko wulakanci kika ce ke ya shafa, matsalarku ne. Tsakanina da Fa’iz daban, tsakaninki da Fa’iz daban, ban ga dalilin da zai hada ki yi mana jimilla cikin al’amarin ba. Don haka ni a wajena komai ya wuce lafiya-lafiya, lafiyar Allah muka rabu ni da Ya Fa’iz cike da begen juna da fahimtar juna. Insha Allah sai kin goya ‘ya’yana da Fa’iz, kin ji ko Fa’izah?”

Ta fada cikin karaji da zazzaro idanuwa, duka a lokaci daya tamkar zararriya, ta daga hoton Fa’iz ta kai bakinta ta sumbata, ta kuma rungume a kirjinta ta ce, “Fa’izah, kin ce farar fata da kyawun Fa’iz ya rude ni ga son shi? Shin kin manta nima fara ce ba baka kamar ki ba? Kyawu na Bamalli duk ina da shi? Kina kuma tsammanin zuwan Ya Fa’iz Ukrain da tukin jirgi ne ya karkato zuciyata ga kaunarshi? Kin  yi kuskure da wannan tunanin naki mara tushe Fa’izah. Bari in gaya miki sirrina da ko uwata da shi kansa Ya Fa’iz basu sani ba. Na fara son Fa’iz ne daga ranar da ya dauko ni a Gusau ya taho ya barki......”

Wata irin sarawa kaina ya yi na rasa me zan cewa Ummi don bakin ciki. Da dai a gida ne ba makaranta ba daura hannuwa zan yi a ka in fasa mata kururuwa ko in rufe ta da duka. Tunda babu damar yin ko daya daga ciki sai na ce, “Kaico! Kin cuci kanki Ummi tunda kika sanyawa zuciyarki soyayyar wanda bai cancanta ba, bai san mutuncin dan Adam ba balle dan’uwansa na jini. Na tausaya miki Ummi, muddin kika yarda kika auri wannan mugun mutumin na rantse sunanki sorry....”

Ta katse ni da cewa, “Ki ce ma sunana sarai asarar duniya ba sorry ba, ‘to be frank’ yanzu na saka danba a son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA.....!”

Na ce, “Kin bata wayonki Ummi, wallahi kika aure shi za ki kwashi kashinki a hannu. Na rantse mai hali.......”

“Baya fasa halinsa fa Fa’izah!”

Ta karasa tana min dariyar tura haushi. Ta kuwa tura din. Ta ci gaba da cewa, “A ganina wannan ba damuwar ki ba ce tunda dai ba ke za ki zauna min dashi ba, bai shafe ki ba kowacce irin rayuwa zamu yi ni da Ya Fa’iz, tunda abin sa-kai-ne. Ina SON SHI HAKA!

Shine kadai ya tara dukkan abubuwan da nake so ga Da namiji, har ma ya zarta. Kafin a samu namijin da ya tara sura da ‘attributes’ din duk da ‘ya mace ke so irin Fa’iz za a jima Fa’izah. Don haka Fa’izah a yau ina mai farin cikin shaida miki cewa, ina son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!”

Sai na ce, “Allah ya ganar dake Ummi. Kin riga kin yi nisa ba za ki ji kiran ba. Allah ya shirye ki, ya ganar dake makiyinka baya taba rikidewa ya dawo masoyinka, ‘no matter what.... sai in ya ga kiyayyar tasa ba mai ci ba ce.....”

“wai ke sai kira kike FA’IZ MAKIYI! To makiyin wa? Ke ko mu? A lokuta da dama Yaya Aliyu kan ce bakya magana sai mai ma’ana da hikima a ciki, amma ga shi ni yanzu duk kin cika ni da rubbish (shirme). Wallahi duk kin isheni da surutu mara ma’ana. To wannan shirmen da kike shi zai sanya in tsani Fa’izun nima?”

Ta yi dariya ta shiga tattare kayan ta cikin ledar da aka kawo su. Tabbas da da ne ba yanzu ba da GIRMA da HANKALI suka zo ba, babu abin da zai hanani rufe Ummi da dan iskan duka, yakushi da cizo irin wanda muka saba da zarar mun samu sabanin ra’ayi ko don in huce bakin ciki da takaicin da ta kunsa mini, amma ina! Girma ya zo!! In ma mun yi ba zai mana kyau ba!!!

Sai na kyale ta na kwanta a gado na kama kuka mara sauti. Ni babban bakin cikina da muka yi a gaban su Haulatu muka farke sirrin gidanmu a gabansu, shin da me za su fassaramu ba dabbobi ba?

Wasikar da Fa’iz ya aiko abin da ya rubuta a ciki kawai “Ga Hankicina ki bawa Fa’izah, sauran kayan naku ne ke da Zanirah”.

Wannan wasika ta bai wa su Ummi da su Naja dariya. Wato su tsaraba wadda za ta amfane su, Fa’izah da ba a so ‘HANKICI! Suka kyalkyale da dariya.

Haule ta ce, “Kai zan so in ga Fa’iz dinnan face to face, am sure he will be vey funny”.

Ummi ta harareta ta ce, “Me kika ce? Ki ganshi ki yi mai uwar me?”

Suka kara kyalkyalewa da dariya. Naja ta ce, “Sorry Khadijan Fa’iz, ai mu Fa’iz ya wuce da ajinmu ba cewa zamu yi muna so ba. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa!”


****

Tun daga ranar na fita harkar Ummi, na ma tattara kayana na koma hostel din su Naja da muka fi dasawa. Ummi ba ta gaya min Fa’iz ya ba ta hankici ta bani ba, kawai na tsinci kyakkyawan farin hankici cikin kayana mai dauke da kalmomin Larabci guda (7) ‘AHUBBIK’.

Na kai hankicin karan hancina na sunsuna, sassanyan kamshin turare dan gidan (Philips Lumea) da hakincin ke yi ya haifar da wani takaitaccen nishadi a zuciyata, ya gusar da duk wani bacin rai na Ummi da nake fama da shi a cikin ranakun da bama ga maciji. Haka nan Allah ya sanya mani kaunar dan kyakkyawan hankicin a raina.

Sai dai kamshin Philips Lumea da hankicin ke yi na kan so in san inda na san shi amma Allah bai bani ikon tunawa ba. Na tura shi cikin jakar littattafaina ko cigiya ban yi ba. A raina na ce “Ina zaune ai ya zo ya tadda ni. In mai shi ta yi cigiya na ba ta”.

Kullum bana iya barci ba tare da na shaki kamshin daddadan hankicin nan ba, haka in na fito aji ana rana, na kan rufa shi ne a fuskata zuwa hostel, bana ko tsoron mai shi ta gani. Kuma abin mamaki har kwanaki suka ja, aka debi wata kamshin da hankicin nan ke yi bai gushe ba.

Wannan ya tabbatar min da ba karamin turare ne a jikinsa ba. Duk sanda zan wanke uniform sai na wanke shi, amma babu abin da ya ragu na daga kamshinsa kullum kamar ina kara fesa masa turare dan gidan (Philips Lumea) ne.

A karshen watan Yaya Hauwa ta zo ganinmu, ta bani letter daga Yaya Aliyu, kuma wai lallai-lallai in rubuta amsa in ba ta a take. Don a satin ya zo gidanta ya fi a kirga yana tambayar amsar wasikar tana cewa ba ta zo ba, yana ta yi mata mita.

Na yi dariya na ce, “Yaya Hauwa kyale Yaya Aliyu kawai, rigimar shi yawa gare ta. Yanzu haka duk zancen in bar rubutu in yi karatu ne bai san tuntuni na ajiye shi a gefe ba”.

Ta ce, “Ah toh! Sako-makoko na  dai isar don haka ragowar can ta matse muku kun fi kusa, wai harshe da hakori. Ban tambaye ki me ke cikin wasikarku ba”. Na rufe fuska da tafukana ina dariya cike da jin kunya.

Ban bude wasikar Yaya Aliyu ba sai a washegarin talata da daddare bayan na gama komi da ya zamo min al’ada kafin kwanciyar barci. Na saka (nighties) na saki net (gidan sauro) na shige ciki. Sannan na bude wasikar Aliyu;


“A gida, Giwa-

Fa’izah, ko kin san mene ne abin da na dade ina cewa ba ki yi girman da za ki fahimta ba? To ba wani abu bane strange. Abu ne da ya zamo (known) ga kowa a Giwa, Zaria, Kano da Kaduna. Idan har zuwa yanzu shekaru goma sha bakwai baki yi kwakwalwar da za ki fahimtar ba sai in ce zan yi  A BARI YA HUCE.....

Yayan is in love! Fa’izah Aliyu is in love!! Please save a soul..... ki taimaki “tuzurun” yayan ki ki zama zabin Hajjah gare shi nan da watanni uku wato bayan kammala jarrabawarku ta karshe. Hajjah ta yi rantsuwa nan da watanni uku ko na shirya ko ban shirya ba za a daura min aure, ta gaji da karatun da ba shi da karshe. Don haka ne na ga tunda wuri gara mu fito fili mu bayyana kanmu maimakon hannunka mai sanda. Babu zancen fahimtar juna sai cika burin zuciyoyin da suka dade suna ragaita.

-Aliyu-Na’ibi.


Wata irin murna marar misali na shiga yi tare da dariya-dariya da ni kaina ban san irinta ba. Abin da kunnuwana suka dade suna jiran ji daga bakin Yaya Aliyu. Gaskiyar Mama Asma’u ne da ta ce, “Sannu-sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba”.

Sai na kwanta a rigingine zuciyata da ruhi cike taf da begen Aliyu-Haidar. Kwakwalwata ta shiga wassafo min irin kyakkyawar rayuwar da zamu shimfida ni da Yayana Aliyu, irin kyawawan yaran da zamu haifa kasancewar Aliyu fari tas Fa’izah choculate colour. Na tabbata za suyi kyau, kyau mai suna kyau da babu irinsa cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa.

Watanni uku kenan da kammala masters din Yaya Aliyu a jami’ar Legas a kan (Agricultural Engineering), cikin lokacin kuma ya samu aiki da ma’aikatar gonaki ta kasa. Sun aje shi reshen jihar Legas matsayin mataimakin M.D. Gida cikin lekki da motar shiga ta zamani da matasa masu matakin rayuwa dai-dai da tashi suke hawa.


****

Shin wace irin amsa zan rubutawa Yaya Aliyu ne? Wallahi ban sani ba. Na shafa ko ina ban ji amsar da ta dace cikin kwakwalwata ba saboda kunya. Kuma wadda zan saka ta yi min gayyar ta watse (Khadija-Ummi) anyi ta ba dadi. Ina kuma ganin faduwa ce babba gareni in je ni neman sulhu. Sai dai in mu koma gida a haka amma ba zan ba da kaina ba ta kara kular dani a banza, don da alama babu sauran mutunci cikin al’amarinta in dai a kan wannan dan’uwan nata ne Musa a fuska, Fir’auna a zuci.

A kullum sai na karanta wasikar Yaya Aliyu a kalla sau cikin carbi. Aike na duniya Yayan ya yi in ba da amsa na ki, don tsakanina da Allah da gasken ban san me zan rubuta mishi ba. Don haka ne wai na bari ayi hutu tunda ya matso in yaso sai mu rubuta ni da Zanirah.

Yau saura sati biyu hutu Yaya Hauwa ta shigo makarantar wajen kawayenta malaman makarantar. Bayan ta gama abin da ya kawo ta, ta yi kirana staff office ta ce, “Fa’izah na gaji! Zaryar Aliyu gidana ta ishe ni, wai amsar me za ki ba shi ne? Ki yiwa Allah ki bani takardar nan in ba shi in huta ya sarara mini”.

Na ce, “Yaya Hawwa ki kyale Yaya Aliyu don Allah sai mun zo gida. Saura kwana goma sha hudu ya rage”.

Ta ce, “Ai shi kenan, ni tausayin shi nake ji wallahi. Ya damu fiye da zaton ki, wayar safe daban ta dare daban, ga ayyuka masu tsauri a gabanshi. Yarinya karama sai tamaula kike da ‘yan maza, ki ji tsoron gamuwarki da Allah Fa’izah ki tausayawa Da na”.

Na kyalkyale da dariya na ce, “Yaya ni ba ‘yarki ba ce sai Yaya Aliyu kadai?” Ta ce, “A’a, ni na fara cewa haka? Duka daya kuke”.

A ranar ne kuma hukumar makaranta ta sanar cewa, babu ‘yan set dinmu a masu zuwa hutu saboda karatun bita na jarrabawar karshe. Sai dai wadanda ke cikin Kaduna ne kawai za su fita su dawo sati daya jal.

Muka debi kayan sawa uku cikin jaka muka yi gidan Yaya Hauwa. Tsakanina da Ummi sai harara. Kwanana daya gidan yaya Hauwa gidansu Ummi kenan, duk na kasa sakewa sakamakon rashin sabo da gabar da muka tsira a junanmu.

Sai dai duk iyaka kokarina na yi Yaya Hauwa ba ta gane ba, don ko da za ta ji din na tabbata ni za a daurawa rashin gaskiya duk da nice mai gaskiyar, da rashin dadin zuciya ya isheni na dau wanka na sha atamfa super da mayafi, na yiwa Yaya Hauwa sallama da niyyar za ni gidan Baban Kaduna Jabi Road.

Ta ce, “To dai kada ki sake ki je Giwa, kin san dai dokar makarantar nan, iyakacinku cikin gari. Ga ummi ta shiga wanka ki tsaya ta fito ku tafi tare mana”.

Na ce, “Ai kwana zan yi, kin san kuma Ummi ba za ta yarda ta kwana gidan Baban Kaduna ba saboda abokin fadanta (Junior)”.

Ta yi dariya ta ce, “Yiwa Idi direba magana ya kai ki yana nan cikin lambu wajen tsintsaye yana basu abinci”.

Shigarmu harabar gidan ke da wuya idona ya kyallo mani motar Yaya Aliyu fake a harabar adana motoci. Gabana ya fadi, tabbas na yiwa Yaya Aliyu laifi babba kuwa, na yiwa Aliyu Haidar babban laifin da ban san (punishment) din da zan fuskanta ba, bani kuma da uzuri ko hujjar kare kaina.

Na gyara murya zan ce da Malam Idi mu koma na hango fitowarsu shi da Baban Kaduna yana rike da brief case din shi. Dole na fito, duk gwiwoyina sunyi sanyi kalau.

A dai-dai motocin Baba dake jere a cikin rumfar adana motoci na tsugunna har kasa na gaida Baba. Kallon da Yaya Aliyu ke min a yau ya kara sanya min mutuwar jiki da sanyin gwiwa har muryata karkarwa take ina gai da Baban.

Ya ce, “Faduwa ta zo daidai da zama, yanzu Mamanku ke cikiyarku game da shirin da za ku soma na bikin da za ku sha nan da watanni uku. Ina kika baro Ummin?”

Na ce, “Ummi na gidan Yaya Hauwa. Biki kuma Baba? Na wa?”

Ya yi dariya ya ce, “Na Hassanar ku”.

Ido warwaje na ce, “Zanirah?”

Dariya ya yi, “It sounds like a film  ko (kamar a shirin fim), to ya za a yi? Hajjah ta tada hankalinta aure za ta yiwa Zanirah, kinga kuwa babu mai ta cewa. Ko akwai?”

Da sauri na shiga girgiza kai, na ce, “Babu kam, babu Baba”. Na mike da sassarfa zan shige Baba ya ce, “Baki ga Yayanki bane babu gaisuwa?”

Yaya Aliyu ya ce, “Kyale ta Baba ai ta je kwaleji ta waye ne, kada ki sake ki bar gidan nan sai mun dawo Giwa yanzun nan”.

A hankali na cira kai na dubi Yaya Aliyu, sanye yake da shadda (Hilton) ruwan toka mai gautsi. Sai sheki take cikin hantsin na safiyar Asabar. Ya rame sosai ya dan yi duhu, in ban yi kuskure ba sai in ce ko (ulcer) ce ta tashi ta kwantar da shi muna makaranta. Dara-daran idanunshi sun fada sun yi ciki sun yi ja ainun. Muka yiwa juna wani irin kallo na sakan biyu a hankali na ce, “Ina yini?”

Ban damu da ya amsa ko bai amsa ba na wuce da sauri, har ina tuntube da kofar shigewar.

Gaba daya yara suka diba ga Fa’iza, ga Yaya Fa’izah. Daya bayan daya nake daga su tika-tika dasu ina direwa. Na tambayi Junior Mama ita da waye? Ya ce ita da Yaya Zanirah ne sun zo su tare da Yaya Aliyu tana ta kuka wai za a yi mata aure.

Na yi sallama a falon, Mama ce ta amsa. Zanirah na hango ta hade kai da gwiwa can a kusurwar falon tana rusar kuka. Na ce, “Wai Mama da gaske?”

Ta ce, “Ni gara da kika zo, na kasa ma Zanirah, ni yanzu da ta zo ta sani a gaba tana rusa min kuka me zan yi a kai don Allah? Sanin kanku ne in Hajjah ta yi hukunci Babanninku basa musu. Wannan kukan duk aikin banza ne Zanirah kike yi ba zai sa ba, ba kuma zai hana ba”.

Cikin kuka Zanirah ta ce, “To waye Mama? Waye mijin? An ce wa Hajjah yanzu ma irin zamaninku ne da ake irin wannan auren a kwashe lafiya? Ni ba aure nake ki ba, karewa ma ina da wanda nake so. Ta yi hakuri mana mu kammala makaranta zan kawo mata mijin”.

Ni sai Zanirah ma ta bani dariya, don ni dai tun tasowar mu ban santa da wani saurayi ba. Na samu wuri gefen Mama na zauna na ce, “Wallahi Mama ni dama na san dole ne tsayin Zanirah ya dami Hajjah, duba ki ga duk ta fimu cika ido ga tsayi, Hajjah na yawan cewa “doguwa hankalinki a gwiwa, ni kar ki fado min a ka”.

Mama ta yi dariya Zanirah ta zabga min harara. Mama ta ce, “Daman Zanirah ai ta girmeku, shekaru biyu ta baki kwarara, ke kuma kika bawa Ummi watanni biyar. Ni kam ban ga laifin Hajjah ba don an yiwa Zanirah aure yanzu, shekarunta goma sha tara ris, sai dai tunanin wanda ta baiwa auren.

Na yi iyaka tunanina amma hankalina bai bani ba. Baban ku ma ya yi tambayar duniyar nan amma ta kafe sai ana saura kwana uku daurin auren sannan kowa zai ji”.

Na ce, “Kai wannan tsohuwa da rigima take, ke Zanirah to mene ne abin kuka? Muma muna tafe, kin sani dai ko ba yanzu ba mawuyaci ne Hajjah ta kyale ki zuwa jami’a da shekaru kusa da ashirin, kai Hajjah ta yi dai-dai....”

Zanirah ta taso kamar za ta make ni, ko me ta tuna? Sai ta juya ta yi bed room din Mama tana sharbar kuka wiwi kamar ranta zai fita.

Ni dai Allah-Allah nake karfe uku ta yi na bar gidan zuwa Zaria kafin Yaya Aliyu ya dawo ya taddani, duk da Aunty Hauwa ta ce in bi umarnin makaranta duka gidajen biyu ba zan iya zama ba, can Ummi mun yi fada, nan Yaya Aliyu zai tirke ni. Ya kasa ganewa cewa nauyinsa da girmansa da nake gani ba zai barni in ba shi amsar wasikarsa ba. Na yi kokarin hakan amma na kasa.

Karfe ukun na yi na dauki jakata na yafa mayafi, na yiwa Mama sallama na roke ta tasa Malam Garba ya kai ni Zaria. Zanirah ma ta dauko kayanta ta ce, ba za ta kwana a gidan ba ta fasa tunda Mama ta goyi bayan ayi mata aure da mijin da ba ta sani ba.

Malam Garba ya ja mota, bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidanmu, yana aje mu ya juyo Kaduna.

‘Yan kannena kam sun yi farin ciki da ganina, suka shiga gyara mana daki. Daga momi har Baba babu wanda ya dawo aiki, Abdallah mai bi mani ya girma, yanzu yana aji uku na sakandire. Yayin da Walida ke aji shidan firamare ‘yar shekaru goma, Kausar na aji hudu, sai auta Walid yana Nursery.

Yaran gidanmu akwai nutsuwa da kyakkyawar tarbiyya, suna masifar son junansu, ko ina suna tare. Idan Momi da Baba sun tafi aiki su kulle kansu a gida suyi ta karatu, in sun gaji suyi game suyi kallo, ga son baki, kula da sallah da son zuwa Islamiyya nan cikin (Area One).

Walida ke fiddo ire-iren aiken da Yaya Fa’iz ke musu na kayan wasa masu aiki da batir da jirage masu tashi sama sosai na Abdallah masu aiki da (remote control). Zanirah ce kawai ta nuna sha’awarta ni ido kawai na bisu da shi.

Momi kan yi abinci ne mai yawa ta cika musu cooler, don haka mun samu abinci mai rai da motsi, mun ci mun yi kat! Mun yi wanka ina shafa a gaban madubi daure da faffadan tawul, ya yin da Zanirah ke gefe ta mike kafafunta cikin ‘sofa’ sanye da doguwar riga a jikinta, ta zuba min ido kurum.

Walida ta kyalkyale da dariya ta ce, “Aunty Fa’izah Yaya Zanirah fa kallon ki fa take yi”.

Na dan juyo muka yi ido hudu da Zanirah, na ce, “Ya dai amarsu? Ko ta samu ne?”

Ta tabe baki kamar taliya ta ce, “Amma kuwa wannan ango ya debo da zafi. Imagine Fa’izah yadda za ki yi zaman aure da wani alhalin zuciyarki, ruhi da gangar jikinki duka suna ga waninsa”.

Na dube ta na ‘yan sakanni, na ce, “Hakuri da juriya ya zama dole gareki Zanirah, rashin so daga mace na dan lokaci ne, na namiji shine ke lasting”.

Ta ce, “Ta ya ya zan yarda cewa mutumin da Hajjah ta bada ni gare shi yana sona?”

Na ce, “Zanirah cewa nake Maman Kaduna da Baban Kaduna, Baba Na’ibi da Maman Yaya Aliyu, Yaya Hauwa da mijinta, su Baba Barau da Yaya Ibrahim, Sadi, Salisu, Sani, Aunty Rabi da Yaya Muftahu kadai sun ishe ki ishara. Zanirah babu yadda za ayi HAJJAH HADIZA GIWA  ta hada aure ayi dana saninsa ko ayi dakacen wanzuwarsa, ko kuma ya zama mara dadi tsakanin ma’auratan. Sai dai ma daga baya a zo ana gode mata.

Saboda haka ki kwantar da hankalinki ( a ganina fa) Hajjah ba za ta kai ki inda za ki wulakanta ko ki tozarta ba. Insha Allahu babu komi cikin wannan auren face alkhairi. Ko ni da nake ganin zamu yi auren “So” da Yaya Aliyu ina gudun kada in zo auren bai mani dadi ba kamar na sauran zuri’ar A.B ba. Don haka har yanzu na kasa bawa Yaya Aliyu amsa”.

Ban juyo ba ina kallon ceiling ne dalili kenan da ban ga halin da kalamaina suka jefa ‘yar’uwata Zanirah ba. Ashe Zanirah fiddo ido ta yi warwaje, dafe kirji tare da bude baki duka a lokaci daya. Idanuwanta suka jirkice cikin dan lokaci tare da wuntsilowa daga cikin ‘sofa’.

Sai dai ‘yar’uwa ta gaskiya wadda ZUMUNCHIN har cikin zuciyarta yake ta yi kokarin controlling kanta ta hanyar komawa cikin sofa ta kalmashe ta runtse ido, tare da dafe kanta dake neman rabewa gida biyu saboda sarawa da juyawar bazata da ya yi mata.

Cikin sassanyar murya mai dauke da yankewar buri na rayuwa ta ce, “Wane Aliyu Fa’izah?”

Na mai da hannuwana baya na sarkesu na doshi taga a hankali na tsaya ina kallon waje ta tagar ina murmushi, na ce, “Aliyu nawa muke da shi cikin A.B. Zanirah? Baya ga Aliyu Haydar Na’ibi A.B Giwa?”

Na juyo gaba daya na fuskanceta ba tare da na gane rikicewa da gigicewar da Zanirah ta yi ba na isa ga jakata na zuge na fiddo wasikar Aliyu na mika mata ina fadin “Ban iya soyayya ba Zanirah balle kalamanta masu sanyi. Ban san soyayya ba Zanirah, ban san kalamanta ba. Na shafa duka duniyar kwakwalwata in nemo kalaman da suka fi kowanne dadi ga masoyi a duniya in rubutawa Yaya Aliyu na rasa baya ga (I love you too). Taimake ni ‘yar’uwa ki rubutawa Yaya Aliyu kalaman soyayyar da suka fi kowanne dadi da gardi a duniya ko da layi biyu ne kacal, ya san cewa ‘I do care for him too much’ ya san cewa ruhi, kalbi da gangar jikin Fa’izah gaba daya yana kaunar Yayanta Aliyu!”

Hawaye wani na bin wani sharaf-sharaf a fuskar Zanirah, a ya yin da take karanta wasikar Aliyu ga Fa’izah, tasa gefen rigarta ta share da sauri ta yagi wani gefe a karshen takardar ta ce, “Bari in rubuta maki amsa Fa’izah, ko dama can wauta ta hana ki gane Yaya Aliyu na mutuwar son ki, amma kowa ya sani. Ki rike Aliyu da kyau, ki yi mai rikon magnet.

Yaya Aliyu ba irin mazan da ake yiwa rikon sakaka bane. He has all the qualities and all the attribute to be love upon. Ina da kyakkyawan zaton cewa, muddin Yaya Aliyu ya zamo miji a gare ki babu ke babu ganin wulakancin namiji da ‘yan’uwa mata ke suffering, saboda Yaya Aliyu na daban ne. Babu ke babu kalmar nan da mata suke kira kamar ayar Alkur’ani wai “Duk wadda ta ce namiji uba ne.....” Domin Aliyu uba ne, uwa ne, aboki ne, dan’uwa ne, miji ne abin so da duk wata diya mace za ta yiwa kanta burin samu”.

Sakin baki na yi da kunne duka ina sauraron Zanirah. Me ya kawo duka wannan dogon sharhin? Ya ya aka yi muryarta ta canza haka kamar ba muryar Zanirar dana kwana na tashi da sani ba, tana magana cikin fidda rai da yankewar buri?

Na ce, “Za ki rubuta min amsar ne ko dauko diro zan yi in aje miki ki hau ki ci gaba da fadin how lucky I’m for having Aliyu as a husband?”

Ta yi murmushi ta ce, “Zan rubuta mana sister nah”.

Ta kammala cikin sakan biyu. Ta taso har inda nake tsaye jikin taga ta bani, ta juya ta shige toilet.

“If all my body is full of mouth, it’s not enough to expess the kind of love I had on you Yaya Aliyu”.

Na yi murmushi na rungume takardar ina fadi a cikin daga murya, “Na gode Zanirah.....”

“Da ta yi miki me?”

Gaba daya muka duba kofa ni da Walida, Yaya Aliyu ne!

Walida ta bude baki tana dariya, ni kuma na yi wuf! Na shige uwar daki cike da takaicin a yanayin sutturar da ya same ni na sanyo riga da zani da dankwali. Ina kokarin sanya dan kunne ya tsaya a bakin kofar sai na samu kaina da kasa hada ido da Yaya Aliyu a yau, sai sunkuyar da kai nake. Ya yi dariya ya juya yana fadin ina jiranki main falo.

Da ya fito dai-dai toilet sai na jiyo shesshekar kuka. La shakka Zanira ce take kukan da ba ta so a ji, ko a gani, shi yasa ta shige toilet take yin sa. Na tabbata ba zai wuce a kan aurenta bane. Ban yi mata magana ba, domin Zanirah mutum ce da ba ta son fadin damuwarta ga kowa, ba kuma ta son shisshigi cikin al’amuranta. Sai na fita falon a hankali duk jikina ya yi sanyi.

Yaya Aliyu ya dubi Kausar da Walid da suka yiwa cinyoyinsa dabaibayi ya ce, “Oya!” Ya fiddo alawar Zanirah a da (Bounty) ya mikawa kowannensu, ya ce, “A tafi wajen Yaya Abdallah ga shi can yana exercise kuma ku yi, ko kwa rage wannan kumburin naku”. Duk suka ware da gudu.

Abu ne da Hajjah ta raine mu da shi wato muddin bako ya zo kowanne iri ne abu na farko da zamu yi mishi shine, ba shi ruwa da lemo. Ban yarda mun hada ido ba har yanzu na yi kitchen na dauko lemon ‘Chivita’ da gorar ruwan ‘Faro’ masu sanyi da kofi na ja karamin center table gabanshi na aje mishi. Baya komi sai bina da ido, kamar yau ya fara ganina.

Na daga gorar ruwan da har raba take don sanyi ina budewa na soma tsiyayawa cikin tambulan, amma kallon da Yaya Aliyu ke bina da shi ya haifar min da karkarwar jiki, na tsula mai ruwan a cinya. Ya mike da sauri ni kuma na saki kofin bisa tayal ji kake taratsatsatsa.....

Muka yi tsaye cirko-cirko kamar zakaru, cikin murya mai sanyi ya ce, “Yaushe Fa’izah ta koma mara imani ne?”

Ban san sanda na saki dariya ba. Duk yadda Yaya Aliyu ya kular da kai sai ya san yadda ya yi ya baka dariya. Na ce, “Ni da imanina bai je ko ina ba. Bari in baka wani”.

Ya ce a harzuke, “Ke look! Bana bukatar ruwanki ba shi ya kawo ni ba. In shi ya kawo ni ai na san hanyar kicin din, kawai Malama ki bani amsar takardata. Da kuma dalilin wulakancin da kike min tsahon wata uku? Tun daga Legas na tako na kawo takarda a baki. An tabbatar min an bakin, to mene ne dalilin kin bani amsa just a single yes or no?

Duka cikin kwanakin aikina nake jele daga Legas zuwa Giwa don kawai na karbi amsar ki amma Fa’izah babu. Anya akwai sauran imani cikin ranki? Na ce kar ki bar Jabi Road sai na dawo daga Giwa, na je na tarar kin gudo nan. Nan din ma ban yi fushi ba na biyo ki kin jike ni sharkaf da ruwan sanyi, anya Fa’iza ke ce?”

Yadda yake maganar cikin sanyi, sai ya yi bala’in bani tausayi.

“Fa’izah magana nake fa?”

“To Yaya Aliyu ba ka zama?”

“Ba a zaman, kawai ki bani amsata, kin amince ayi aurenmu da zarar kin yi graduating?”

Na langanar da kai na ce, “Haba Yaya Aliyu”.

Ya yi murmushi ya zauna, nima na zauna, muka dubi juna, sai muka sa dariya a tare.

“Ke fa shu’uma ce Fa’izah, in mun yi aure zan sha wahalarki”.

Na kau da zancen cikin jin kunya da cewa, “Zanirah fa tana ciki Yaya Aliyu in kirawo ta?”

Ya ce, “In mata me? Ke, ina fa da abin yi, za ki bani amsata ne ko kuwa?”

Na yi rau-rau da ido kamar mai shirin kuka na ce, “Haka ake ba da amsar Yaya Aliyu kamar a fagen fama? Don Allah ka yi hakuri na amsa duka laifuffukana”.

Ya saki rai ya ce, “Ok!”

Na koma kicin na kawo mishi wani ruwan, har da cake da dambun naman kaza ya soma ci yana hararata ina share fasasshen kofin tangaram ina murmushi. Na kammala na koma daki na dauko takarda na dunkule a hannuna na fito.

Zuwa lokacin Yaya ya gama, na ce, “To Yaya Aliyu rufe idonka”. Ya mai da manyan idanunshi ya lumshe zara-zaran gassun girarsa. Ya bude su duka a kaina ya ce, “An ki a rufe, in rufe ki caka min wuka, tunda ba kya SO NA?”

Ido waje na ce, “Lalala! Sharrin da za ka yi min kenan Yaya Aliyu?” Na jefe shi da takardar na yi daki a guje tare da kullo kofar har da murza key.

Zanirah na tarar zaune bakin gado tana rubutu cikin karamin ‘DIARY’ din ta. Tana ganina ta boye shi cikin filo ta mike tana fadin “Fa’izah har yanzu Momi ba ta dawo bane?”

Na ce, “Nima na rasa abin da ya tsare su, amma lokacin dawowarsu har ya wuce tuni”. Ta ce, “Ke da wa kuke ta magana ne haka a falo?”

“Yaya Aliyu ne Zanirah, amma na ji tashin motarshi yanzun nan ya tafi, kina toilet sanda ya zo”.

Jikinta a sanyaye ta koma gadon ta kwanta tana fadin “Zan dan kwanta in samu bacci kafin kiran sallah, in sun dawo don Allah ki tashe ni”.

Wai Zanirah ta dauka kwanciyar nan da ta yi ban san cikin damuwa take ba. Damuwar ce ta yi mata yawa ba ta so na gane shine dalilin da yasa ta zabi ta kwanta din a dalilin dauriya da juriyarta sun kare. Umh! Na fa soma tunanin akwai wani abu tsakanin Yaya Aliyu da Zanirah, kai to mene ne.... kai babu komi.... to mene ne ma zai shiga tsakanin nasu? Oh! Ni Fa’izah! Anya ba son Yaya Aliyu Zanirah take ba??????

“..... Ina kammala makaranta zan kawo mata mijin..... Ki rike Yaya Aliyu da kyau, ki yi mai rikon magnet..... Yaya Aliyu ba irin mazan da ake yiwa rikon sakaka bane..... He has all the qualities and all the attributes to be loved upon.... ina da kyakkyawan zaton cewa, muddin Yaya Aliyu ya zamo miji a gare ki babu ke babu ganin wulakancin namiji da ‘yan’uwa mata ke suffering.... Saboda Yaya Aliyu na daban ne.... domin Aliyu uwa ne, uba ne, aboki ne, dan’uwa ne.... miji ne abin so da duk wata diya amce za ta yiwa kanta burin samu...... Imagine Fa’izah, yadda za ka zauna da wani alhajin zuciyarka da tunaninka, ruhi da gangar jikinka duka suna ga kaunar wani can daban....  Na tuno kalaman Zanirah!

Na tallabi kaina da hannayena biyu sakamakon wata irin kwankwatsa da yake yi min tamkar zai dare gida biyu. Ko da yake an ce az-zannu zambun, wato zato zunubi ne bai kamata in yi saurin gaskata hasashena ba, har sai na ga diary din Zanirah da take boyewa, sai na ga abin da ta rubuta dazu, sai na ga damuwarta ta shekara da shekaru wadda a kullum ke zane a fuskarta. Ko mene ne ni zan yi kokari in magance mata damuwarta in har ba soyayyar Yaya Aliyu bane, zan taimake ta insha Allah ta fita daga halin damuwar da take ciki.

...... Shigowar Walida ya katse tunanina. Ta ce, “Yaya Fa’izah, Yaya Aliyu ke kiranki yana cikin mota zai tafi”.

Duk da ina jin nauyin Aliyu ba zan iya kasa yi mishi sallama ba. Na rufe kaina da mayafi na bishi. Yana zaune cikin mota duka kafafunshi suna waje, ya jingina da makarin kujerar idonshi a runtse.

Har na karaso bai bude idon ba, sai da na kwankwasa gilashin kofar motar ya bude dukkan manyan idanunshi a kaina, sun kada sun yi jajir har sai da na ji gabana ya yanke ya fadi, ko amsar da na ba shi ne ya tayar da hankalinsa maimakon ya yi farin ciki?

Kallon juna muka yi cikin ido na ‘yan sakanni, kafin mu saki ajiyar zuciya a tare. Cikin sassanyar murya ya ce, “Abin da kika fada cikin takarda Fa’izah haka yake ‘heart and soul!”

Kunya ta rufe ni, na rufe ido da yatsuna goma ina dariya......

Ya ce, “Na gode, na gode kin ji Fa’izah. Ina fatan lokacin da na yanke ayi aurenmu bai zamo takura a gareki ba, wato watanni uku masu zuwa bayan kammala jarrabawar ku ta karshe?” na yi shiru.

“Akwai babban dalilin da yasa na yanke wannan lokacin duk da bana so na takura ki, akwai dalilin da yasa na yi hakan”.

Na kara yin shiru idona a kan kananan duwarwatsun da suka rufe harabar gidan, da gaske ne har zuciyata ban shirya aure yanzu ba. A ranar na cika shekara goma sha takwas. A ra’ayina in samu ko karamar Diploma ne in yi kafin aure. To amma bana iya yiwa Yaya Aliyu musu saboda matukar so da kaunar da nake masa, ina son shi fiye da tunanina, fiye da tunanin duk wani dan adam.

Bana iya musa mishi duk abin da ya umarce ni, don ina da tabbacin ba zai yi umarnin da zai zama cutuwa a gare ni ba sai wanda zai amfane ni. Har sau tari na kan ga kamar son da nake wa Yaya Aliyu ya ninka, ya dame ya shanye wanda shi yake mini.

Wani lokacin na kan yi tunanin muddin muka yi aure ba zan iya batawa Yaya Aliyu rai ba ko inyi masa ba dai-dai ba daidai da kwayar zarrah, ko da shi ya bata min abu kadan zai yi ya shafe laifin daga idanuna da zuciya, komin GIRMAN sa.

To amma dole in ji dalilin gaggawar tunda an ce ba a son garaje cikin aure, don gaggawar daga shaidan ce. Kamar wadda za ta gudu? Na ce, “Shin Yaya Aliyu to saurin na mene ne haka?”

Ya saita kwayar idanunshi cikin nawa cike da damuwa ya ce, “Saboda SONKI Fa’izah! Na kai na kawo a sonki da kaunarki da son ganin mun zamo abu guda, na mannu da fatar jikinki which is always hunting my dreams.....”

Na rufe fuska cikin jin kunya. Na ce, “Yaya Aliyu ai ba inda za ni, kullum muna tare. Ina laifin bayan candy da shekara daya? Bani da tunanin kowanne da namiji a duniya sai kai Aliyu Haydar......”

Sai bayan na fada na san abin da na fada. Juyawa na yi zan tafi, Aliyu ya riko gefen mayafina.

Ban juyo ba don haka ban san halin da yanayinsa ke ciki ba, ya ce, “Idan haka ne barshi a yadda na ce Fa’izah, watanni uku masu zuwa”.

“Saboda me Yaya Aliyu? Gaggawa daga shaidan ce”.

“What target do you have for making it longer haka Fa’izah? Wata babbar matsala ke neman fatali da farin cikinmu”.

Ban san sanda na juyo gaba daya ba, na ce, “Matsala? Wacce irin matsala ce Yaya Aliyu?”

Idonshi cikin nawa sun kada sunyi jajir, muryarsa a dushe ya ce, “Kina nufin baki sani ba? To Hajjah ke son in auri ZANEERAH!”

Ji nayi wani abu ya kwashe ni yuuuu! Zai maka da kasa, na yi kokarin kama hannun Yaya Aliyu dake jikin motar gam-gam na rike. Muryata na rawa harshena na sarkewa na ce, “ZA-ZA-ZANIRAH Yaya Aliyu? Haba! Biri ya yi kama da mutum....”

Na durkushe a gabansa kaina cikin cinyoyina, kamar in yi yekuwa a zo a tallafi rayuwata. Shi kansa Yaya Aliyu ya yi nisa a tunani, bai tanka min ba. Kowanne sakar da yake yi cikin zuciyarshi daban da na dan uwanshi. Kafin wata juriya da imani su shigeni ciki da bai dina.

Na dago a hankali idanuna taf da kwalla na ce, “Ka je Yaya Aliyu Allah ya kai ka lafiya”.

Ya dago ni daga durkushen da nake muka fuskanci juna. Don karfin hali irin na Aliyu murmushi ya yi min, nima ban san sanda na mayar mai da lallausar murmushi ba.

“Kada ki sa abin a ranki fa. Everything will be alright. Don Baban Giwa (Barau), Baba Sadi da Baba Ibrahim da Yaya Hauwa basa goyon bayan zancen sam”.

Na yi shiru ban yi magana ba, a zuciyata cewa nake, “Ni da kai kuma Yaya Aliyu ai sai wani babban ikon Allah, wanda in haka ta faru na tabbata na yi asara wadda ba mayarwa”.

Zuwa can na ce, “Wallahi ka je kawai Yaya Aliyu, ni ba zan damu ba”.

“How sure are you ba zaki damu ba.....”

Na ba shi amsa muryata na gab da barkewa da kuka.

“I am sure!”

 Ya gyada kai. Ya sanya hannu cikin aljihun motarshi ya dauko daurin kudi ‘yan naira dari biyu sardauna sabbi kar ya miko min. Na bata fuska gab nake da rushewa da kuka, don ji nake kamar sallamar karshe muke yi ni da Yaya Aliyu, kamar babban shinge na shirin shiga tsakaninmu, kamar wata sabuwar rayuwa zamu bude wadda dukkaninmu bamu taba tsammaninta ba.

“Kada ki min musu, ki karba kawai. Ban da yau na taba dauko naira tsurarta na baki?”

Na mika hannu biyu na karba.

“Yaya Aliyu na gode, Allah ya kara budi”.

Ya yi murmushi a cikin kallona ya yi min alama da hannunsa in tafi. Har na juya na soma tafiya ya ce, “Au! Fa’izah!”

Na juyo hawaye shimfide a fuskata wasu na korar wasu.

“Kika ce ba za ki damu ba, to meye na kuka?”

“Ni ba kuka nake ba hawaye ne”.

Ya yi murmushi, “Hawaye?”

Nima sai na yi dariya, ga hawayen fal a fuskata.

“Su zuba kawai suke, kuka kuwa zuciya ke yin sa”.

“Na yarda dake”.

Ya miko hannu.

“Wannan kyakkyawan hankicin na hannunki za ki bani mana?”

Na girgiza kai na ce, “A’a!”

Da mamaki Aliyu ya ce, “Dalili?”

Na ce, “Wallahi haka nan kawai nake son hankicin bana son rabuwa da shi, ina son kamshin sa”.

“Wa ya baki?”

“A dakin su kawata Naja na ganshi a hostel dinsu cikin kayana, wallahi ban san na waye ba”.

“Mu gani?”

Na mika masa ya karanta rubutun (AHUBBIK (I love you!”)

‘WA ANA AIDHAN (me too)” Na mayar masa muryata na karkarwa.

Ya miko min hankicin na juya da gudu na karasa cikin gida, ban san tsawon lokacin da ya diba kafin ya bar gidan ba.

****

Ban tashi sanin fitinar so ba sai a wannan ranar. Ban yarda it is injurious ba sai a wannan ranar. Ban san cewa its unbearable pain ba sai a wannan ranar da na tabbatar zuciyata ba za ta samu abin da ta dade tana SON ba, wato Ali Na’ibi.

A gaskiya so abu ne mai dadi in ya zo da matsala marar dadi. Kamar yadda Ya IM ya ce na (GIRMA YA FADI) “It’s so sweet, yet so painful”.

Wai sai na kama jin haushin ‘yar’uwata Zanirah (kishi), a ganina duk ita ta yi saurin girman da ya gundiri Hajjah har ta yi tunanin aurar da ita, kuma ta rasa wanda za ta likawa duk gidan sai Aliyuna, Yaya Aliyu, Aliyu Haydar Na’ibi A.B Giwa.

Daga ni har Zanirah, kowacce ta kasa barci sai juyi a kan gado. Da abin ya isheni kawai sai nasa kuka wiwi. Tunanin in na rasa Yaya Aliyu, idan ba Aliyu ne ya zamo mijina abokin rayuwata ba shin ya ya rayuwata za ta ci gaba da kasancewa? Ya Allah kada ka baiwa Hajjah ikon karfafa zumuncin akan wannan, ya Allah ka fidda Aliyu zuciyar Zanirah. Don na laluba na duba na hanga ko ina ban ga ta hanyar da zan iya cin kankanta in bar mata ba in ita ba ta ci girma ta bar min ba, sai dai duk mu rasa, ko duk mu samu.

Zanirah ta mike ba zato ta kunna fitila dakin ya gauraye da haske. Ta shiga kallona tsaf, ba ta ce komai ba sai ta shiga toilet ta dauro alwala ta zo ta burma hijab ta hau doka nafilfili.

Hankalina ya kara dugunzuma ya tashi, don a ganina Zanirah na rokon Allah ne a kan ya mallaka mata Yaya Aliyu ni ya hanani. Sai na kara rikicewa da kukan tun karfin gunjin da zan iya a hankali yadda sauran jama’ar gidan ba mai ji na.

Ba shiri Zanirah ta sallame sallarta ta ce, “Fa’izah wai lafiya ne?”

Na dan saurara da kukan na ce, “Na fara kukan rabuwar mu ne Zanirah....”

Da alama ba ta yarda ba har zuci, sai ta yi murmushi ta ce, “Allah yasa hakan ne har zuciyarki. Da sai in ce rabuwa ta zama dole ai, tunda babu yadda za ayi mu dauwama tare a matsayin mu na ‘ya’ya mata. In babu aure akwai mutuwa, akwai kuma kaddarorin Ubangiji iri-iri”.

Mu karasa a littafi na 2

Tare suke,Takori

[6/3, 4:12 pm] Takori: Hawayen da suka shimfido min su suka sanya na mike na yi daki aguje ina kuka wiwi. Yaya Hauwa ta taso za ta biyo ni ta rarrashe ni amma Hajjah ta ce ta kyale ni kawai in yi kukan zuciyata za ta yi min sanyi, kukan sabo ne da fitar SO.

Na ci kuka na a gado na share hawaye, na jiyo zubar ruwa a (toilet) wanda ya tabbatar min Zanirah wanka take yi. Idona ya kai ga abin da na jima ina fakon Zanirah don in dauka sai yau na hange shi cikin kwabar kayanta wato ‘DIARY’ dinta. Na yi hamzarin daukowa ban yi nawa ba wajen bude shafin farko. Kwanan watan ya nuna Zanirah ta yi rubutun nan ne tun muna JSS (karamar sakandire).


“Ban san abin da ke damuna ba, amma kamar son Yaya Aliyu nake in na yi la’akari da yawan tunaninsa da nake da mafarkinsa cikin barcina, da kwadaituwa da son ganinsa akai-akai. Me kenen hakan ke nufi?


Sai na shiga bude sauran shafukan a gurguje. Duk yawanci abin da ya shafi kuruciyarmu ne. Sai wani da ya dauki hankalina wanda kwanan watan ya tabbatar min Zanirah ta yi rubutun ne ranar 10/10 wato ranar da muka je Area One ni da ita (Zaria).


“Dole ne in yi jihadin fitar da Yaya Aliyu a raina, domin ina son shi ne a yayin da na fahimci zuciyarsa, rayuwarsa, ruhinsa da gangar jikinsa sunyi nisa a soyayyar ‘yar’uwata (Fa’izah.) Fa’izah da zumunci basu cancanci in yi tarayya dasu a son komai a duniya ba. Yadda nake son Fa’izah bana son abin da zai sosa ranta. Na tabbatar da Fa’izah ta san ina begen Yaya Aliyu, babu abin da zai hana ta bar mini.... zan ci gaba da lallamin zuciyata har sai ta mance da Yaya Aliyu.... in har Fa’izah za ta iya yi min wannan halacci ni me zai hana na kasa? In anyi duniya don Rasulillahi daga yau na cire son Aliyu a raina domin Fa’izah.......”


Da na kawo nan sai na rushe da kuka sosai, hawaye na zuba a kan littafin. Dai-dai lokacin da Zanirah ta bude kofar toilet ta fito, kukan da ta tarar dani ina yi ya kara tsuma raunanniyar zuciyarta.

Ta tsuguna nan a bakin kofar ta shiga rera kuka ita ma, muka taru muka yi ta yi kamar akuyoyi. Cikin gunjin kuka Zanirah ta ce, “Fa’izah ki yafe ni...... wallahi ban ci amanarki ba.... Ban taba sanin Yaya Aliyu ne mijin da za a daura mana aure ba..... da na san shine wallahi da na bar garin da in zauna in ga wannan rana.... wallahi ban san cewa Yaya Aliyu bane ban sani ba Fa’izah....  ban san za a daura ba.....”

Na mike da azama da sassarfa na isa ga Zaniraha muka rungume juna muka ci gaba da rusa kuka tare ba mai jin na wani.

Na ce, “Zanirah kada ki ce haka, (waman qaddarralahu haqqan qadrihi.) Kada ki kara fadin haka Zanira, ban taba zargin ki da wannan ba, mune muka yi kuskure, kuskurenmu ne ni da Yaya Aliyu da muka yarjewa zuciyoyinmu muka basu fili a kan abin da suke so, alhalin muna da masaniyar ko in ce mun kwana da sanin cewa babu auren soyayya a zuri’ar A.B muka bi ta kai muka take. So we are to be liable for the outcome, ban zarge ki ba ko kadan Zanirah. Baki da wani laifi, babu wata amanata da kika ci. Addu’ata da fatana Allah ya karkato da son da Yaya Aliyu ke mini da wanda nake masa kanki, ya baku zuri’a dayyaba... Ya bani miji kamar naki Zaneerah...!”


****

Yaya Aliyu bai tashi zuwa Giwa ba sai karshen wata kamar yadda ya saba, wanda ya yi dai-dai da sati biyu kenan daurin auren shi.

Tun daga gidan mahaifinsa, mahaifinshi Baba Na’ibi ya kira shi ya yi masa gamsasshen bayani. Ya kara zancensa da cewa, “Aliyu ka bi Hajjah da duk yadda take so in har kana so ka taimakemu mu rabu da ita lafiya. Hajjah mahaifiyarmu ce da ta tsuguna ta haife mu daya bayan daya. Bamu da ikon bijirewa tsarinta da mahaifinmu Allah ya ji kan rai ya dorata a kai, ka sanyawa zuciyarka hakuri da dangana tamkar kowane Da cikin gidan nan da ka budi ido ka gani.

Domin a yadda Hajjah ta dage a kan auren nan naka da Zanirah, ta kuma kawo hujjojinta masu ma’ana mu kanmu mun ga gaskiyarta mun mika mata goyon bayanmu wanda a baya bamu bayar ba.

Ta sanya tariya sati biyu masu zuwa, na biya sadaki dubu sittin, ga lefe kuma da Babanka Ibrahim ya yi maka, su Hauwa ya tura Kano suka hado komai, gobe in Allah ya kaimu za su Zaria (gidanmu kenan). Don Babana ne alwalin Zaneerah.”

Aliyu Na’ibi a zaune yake bisa kilishi dai-dai kafafun mahaifinsa, amma sai ga shi tsaye gaban Baba Na’ibi ba tare da ya san lokacin da ya yunkura ya mike tsayen ba.

Wani kakkauran gumi ya wanke shi daga kwanyar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Ya bude baki zai yi magana yawu ya kafe kat, a bakinshi. Bakin ya bushe fayau! Iyaka kokari Ali ya yi wurin tattaro kalma daga can kasan makoshinsa......

“Don me kuka yi min haka Baba?”

Da karsashi da tausayin da ake son boyewa karfi da yaji ya ce, “Don mun isa daku dukkanku”.

Aliyu ya ce, “Bana son Zanirah da irin soyayyar da kuke nufinmu da ita, ban taba sonta da aure ba Baba”.

Baba Na’ibi ya mike tsaye idanunshi tinjim da kwallah ya ce, “Aliyu babu bambanci tsakanin Zanirah da Fa’izah, abin da ya yi Fa’izah shi ya yi Zanirah. Uwar da ta haifi uban Fa’izah ita ta haifi uban Zanirah. Tare suka taso tun suna kanana, komai nasu iri daya ne sai a halayya da suka bambanta. Ka yi hakuri ka jure sauyin da Allah ya yi maka ka yi koyi da mai sunanka”.

Ya ce, “Matsalata Baba ba zan iya daina son Fa’izah ba.....”

Sai a wannan lokacin hawaye suka sakko bisa kundukukinsa.

Baba Na’ibi cikin dimuwar wai yau Aliyu ke kuka a gabansa, kukan ma a kan mace. Sai ya ce a harkuze, 

“To Aliyu ka yi yadda kake so, ka yi duk abin da kake ganin shine dai-dai, tunda mu bamu san dai-dai ba. Sai dai ina tabbatar maka da abu uku, na daya muddin ka wulakanta Zanirah sai Allah ya saka mata, domin ita ma yadda ka tsinci al’amarin haka ta tsince shi bakin iyayenta.

Na biyu muddin ka tsinka igiyoyin nan guda uku da muka damka maka sai dai ka nemi wasu iyayen amma ba cikin zuri’ar A.B ba. Na uku muddin ka dagawa gyatumar mu hankali tsakanina da kai sai Allah ya bi min kadina na haifar ka da na yi na raine ka har ka yi girman da za ka soka wa uwata tsinke cikin idanu”.

Hawayen Aliyu na zuba ya ce, “Ta ya ya Baba za a daki mutum sannan a hana shi kuka?”

Baba Na’ibi ya ce, “Har karya shi za ayi a ce in ya yi nishi Allah ya isa! Na dai gaya maka daga yau babu sauran wata hulda tsakaninka da Fa’izah sai ta ‘yan’uwantaka. Zanirah kuma idan ka wulakanta ta don kanka, sai dai a kullum kake tunawa ita ma ba ta taba cewa tana sonka ba dole a kai mata. Amma da yake ita mai biyayya ce ba ta dagawa ubanta hakarkari kamar yadda ka daga min ba”.

Haka ya fice daga dakin Baban cikin mummunan yanayi da ba zai misaltu ba. A take ya zari mota ya bar garin kwata-kwata ya koma inda ya fito (Ikko), fadi yake kamar zararre, “Ku rike amaryarku can bana so...... Ta ya ma za ayi na auri Zanirah?”

Gidan babban amininshi Isa Kaita ya aje motarshi. Isa ya kai shi filin jirgi ya bi jirgi zuwa Lagos.

Mu muna can dakinmu na ‘yammatan gidan muna jiran ango ya shigo ya bamu kudin alibidi da lancin din da zamu yi a Zaria da Walima a gidan Baban A.B.U. Labari ya iske mu ai Yaya Aliyun ya zo ya kuma koma Lagos ba tare da ya kwana ba ma.

Ban da salati ba abin da Hajjah ke yi tana fadin “Zai zo ya same ta”. Amarya Zanirah ta yi kamar ba ta san ma me ake cewa ba, ta yi bakam. Ta dauki remote ta karo sautin wakokin yaran Larabawa na (Ad-difl - wal-bahr).

A take na gano matsalar Yayan namu, wato ya ji labarin wannan rikitaccen al’amari na Hajjah. Ni kam da na mai da al’amurana ga Allah da addu’a, nafilfili dare da rana da addu’o’i na musamman cewa, in soyayyar Aliyu ba alkairi ba ce a gareni Allah ya sanya min hakuri da dangana, ya yi min zabin alkhairi mafi kyau, domin zabinsa shine zabi. Abin da nake maimaitawa kenan cikin sujjada ta a ko da yaushe.

Tuni nake da tabbacin Ubangijin nan maji rokon bayinsa ya amsa mini, zuciyata sarai, duk wani duhu da kunci sun gushe. Babu abin da zuciyata ke kwadayi kamar ganin daidaituwar auren Zanirah da Aliyu. Na kudurtawa zuciyata zan yi amfani da mahaukacin son da yake min in ciyo galabarshi a kan Zanirah.

Na dauki wayar Hajjah na yi kofar gida can inda babu kowa tsakanin motoci, na danna lambobin Yaya Aliyu wadanda tuni na haddace su. A washegari kenan da tafiyar shi.

Ta yi ringing har bakwai bai daga ba. Kafin ya daga a fusace a na takwas, “Wai wane ne? Mene ne?”

Wani sanyi da ya ratsa zuciyata ya tabbatar min har yanzu ina son Aliyuna, na kasa magana. So shu’umi ya rugurguza duk wata kalma ta bakina.

Aliyu ya sake cewa, “Hello! In ba wani abu ba  kuma sako bane zan ajiye ina sauri zan tafi Ibadan ne”.

Cikin jarumta na ce, “Yaya Aliyu, kana da ikon zuwa Ilorin, Abeakuta, Benue da Akwa-Ibom ma amma bayan ka zo ka dauki Zanirah kun tafi tare. Ni wannan wane irin so ne da kake neman lika min kashin kaji cikin ‘yan’uwa? Yanzu kowa ya bude baki cewa yake, “Aliyu ya ki Zanirah ne domin Fa’izah”.

To muddin son da kake ikirarin kana yi min na gaskiya ne ba kuma ka kaunar tashin hankali na da kasancewata cikin zargin jama’a, to ka dawo ka tafi da matarka yau ko gobe. Ko da baka son Zanirah ba haka ne hanyar da za ka nuna ba Yaya Aliyu. Wannan hanyar da ka bi ka nuna cewa ka ki bin abin da iyayenmu ke son ka da shi ne. Ka yi butulci ga alkhairin da suke hango mana ta hakan.

In kuma don ka batawa Zanirah rai ne ka yi hakan, wallahi Zanirah baka gabanta, harkokin gabanta take. Dakacen auren take yi, sai don ba yadda za ta yi ne. Ni din dai nice cikin damuwa..... tunda ni dangi za su tsana, ni zan shiga bakin duniya...!”

Da fadin hakan na kashe wayar baki daya ba tare da na tsaya sauraron amsar da zai bani ba, wadda na tabbatar ba shi da ita din.


****

To Ali kam ya nuna ya haifu cikin uwarshi Zainabu, da ubanshi Na’ibi, kuma mai son farin cikin Fa’izah. A washegari ya dawo Giwa, inda ya saki kudi aka yi shagulgulan al’adarmu namu na Mallawa. Ya nuna tamkar komi bai faru ba, kamar Zanirah zabin shi ce ba zabin iyaye ba.

Amma zuciyar ta fi duhun dare duhu. Babu yadda ya iya fadan da ya fi karfin ka aka ce sai ka mai da shi wasa. Iyayen nan bashi da saman su, Hajjar nan ta fi karfin komi a garemu in har muna da iko, in har bamu da shi, zamu yi iya kokarinmu mu nemo masu shi suyi mata.

Sai dai abu ne da har illa masha Allahu ba zai taba kankaruwa daga zuciyarsa ba wato SON FA’IZAH! In ka ga ramar da Yaya Aliyu ya yi kamar wanda ya taso daga gadon asibiti bayan doguwar jinya. Jirgin karfe taran dare aka ajiye za su bi zuwa Lagos.

Aliyu ya dubi Hajjah ya ce, “Tunda har anyi mai wuyar Hajjah, ba a bari in koma ni kadai in shirya in dawo in dauke ta? In gyara muhallina daga na saurayi zuwa na mai iyali. Saurin da gaggawar na mene ne? Cikin abokan aikina duka babu wanda na sanar mawa na yi aure kawai sai a ganni da mata kamar na sato ta? Yanzu haka a tsakiyar aiki nake zuwa Ibadan a bani lokaci ko da sati daya ne in je in dawo don Allah.....”

Hajjah goyon Mahillah diyar Baba Barau take a bayanta ba ta ko dube shi ba. Ta sunkuci fidarta dake shake da cereal ta yi daki tana bambamin fada har da kumfar baki. Ta ce, “Karewar gyaran gida mai da gidan fadar shugaban kasa. Karewar rashin so Aliyu sayar da kan Zanirah garin Yarabawa. Amma kafarka-kafar Zannura”.

Aliyu ya yi tsit! Na fashe da dariya, Zanirah ko tsabar takaicin  yadda Hajja ke mai da ta matar cushe kamar jakar da ta rasa miji na san shi yasa ta zub da kwalla.

Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Ni dai gaskiya Hajjah ki daina ce mun Zannura.....”

Hajjah ta ce, “Zannuraini an fada, ainahin sunanki kenan (ma’abociyar haske biyu)”.

Zanirah ta zumburi baki ta ce, “Hajjah Zunnuraini sunan namiji ne (Usman kenan)”.

Hajjah ta ce, “Allah ya bamu albarkacinsa. Abin da yasa na saka miki suna Zannura saboda an haife ki Ranar Arfah, kuma kwanan watan ya yi daidai da ranar da Najeriya ta karbi ‘yancin kanta daga hannun Turawa, ga ki fara kal kamar auduga, ga kyau ga kyan hali. In baka so Zanirah ba ina jin babu zuciya da mazantaka a tare da kai”.

Kalaman Hajjah sun girmi kunnuwan dukkanninmu daya bayan daya muka zame kowa ya bi hanya daban mai billar da shi wani sashe na gidan. Yaya Aliyu kuwa tunda ta dauko bayanin asalin sunan Zanirah ya bar dakin don haushi.

Ta fannina nima na nuna ni ‘yar halas ce, nayi ma Zanirah gudunmmuwar  (kayan amfanin kitchen) masu karko da tsada ‘yan Japan. Turare mai tsada ‘versace’ da ‘hugo boss’ na ango Yaya Aliyu, na ce, “A sha kamshin amarci lafiya Aliyu da Zanirah”.

Sai a wannan lokacin ne Yaya Aliyu ya dago ido ya dube ni da wata muguwar harara da ban tsammana ba. Zanirah dake gefen shi cikin farin (swiss lace) mara nauyi mai yarfin (silver) dinkin buba da zani, kunshi baki sidik ya kama tafukan hannaye da kafafunta. Gashin nan ya sha relaxing ya kara baki ya kwanta a dogon wuyanta, amarya dai sak!

Ta dago kanta a hankali daga kan yatsun kafarta ‘yan sirara itama ta harare ni. Ga mamakinmu duka sai cewa ta yi, “Wanea irin amarci kike fade Fa’izah? A ya yin da zuciyoyi biyu basu dai-daita da juna ba? Auren da ake lallashi da takurawa mijin ya so ka, shi kike ambatawa amarci Fa’izah? Kaico da auren da ake roko da lallashin mijin ya dauki amaryar yana gudu.

ZAMANI YA CHANZA, ya kamata iyaye da kakanni irin Hajjah su gane hakan, su ajiye traditionality su bi modernity in dai ba fadar Allah da manzo bane. Domin maimakon a gyara zumuncin sai a bata, ko a zalinci daya a kasa kwatar masa hakkinsa don a dorar da zumunci”.

Ta mike ta yi waje tana mai fidda zafafan hawaye. Na kasa cewa komi sabanin Yaya Aliyu da ya kyabe baki ya gyara kwanciyar sa cikin kujera. Tsam! Nima na mike na bar wurin. Ummi ta bimu da kallon tausayi baki dayanmu.

Karfe shida saura minti talatin, iyakar rakiyar mu dasu Zanirah filin jirgin saman Kaduna, inda suka hau jirgi mai zuwa Legas.

Sai a wannan lokacin ne zuciyata ta soma turiri, tana kurma ihun yarda da zancen Zanirah ZAMANI YA CHANZA.... ya kamata Hajjah da ire-irenta su ajiye traditional false beliefs su yarda love is a natural nature that cannot be totally eradicated. Yanzu ne na tabbatar na rasa Aliyu har abada! A lokacin da tayoyin jirginsu suka rabu da kasa. Sai na fashe da kuka a lokacin da wani bakon tunani ya bakunce ni, wato yanayin idanun Zanirah (oily eyes).

Sau da dama Yaya Aliyu kan ce “Fa’izah ina ma kema irin kwayar idon Zanirah gare ki? Wallahi da na ji dadi na.....”

Hawayena suka sake ninka na da.... Ga Zanirah nan complete din ta ka samu Aliyu. Hawaye na ya sake ninka na da, na kifa kaina a kafadar Ummi muka ci gaba da kukan tare. Inda wanda ya san sirrin son da nake wa Yaya Aliyu, to Ummi ce, don tare muka rayuwa a makaranta fiye da Zanirah dake Giwa a lokacin da muka mallaki hankalin kanmu.

Babu irin tsarin da ban yiwa rayuwar aure na da Yaya Aliyu ba. Yadda za ta kasance, yadda zamu yi ta, yadda zamu gudanar da ita da yadda zamu tafiyar da ita, amma a yau Hajjah and her false beliefs (a ganina) sun rushe komai.

Lokaci guda wata irin sabuwar zuciya ta shige ni mai dauke da sabon perception. Na san dadin ‘So”, haka na san dacin rasa shi. In Allah ya yarda ba zan yarda in auri wanda bana so ba! Ba zan yi auren zumuncin ba, ba zan yi auren A.B Family ba. Zan zamo mutum ta farko da za ta canza A.B Family, zan zamo mutum ta farko da za ta yi auren soyayya a cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa.

Bare zan aura wanda zuciya da ruhina ke so da kauna, wanda zai jiyar dani dadin soyayya da zakin dake cikinta. Ko duk duniyar nan za ta taru a kaina ba zan yi auren A.B House ba sai wanda zuciyata ta aminta da shi. Nake so, yake sona da irin soyayyar da muka yiwa juna ni da Yaya Aliyu.


****

Yau wata guda kenan da tafiyar su Zanirah in har na lissafa dai-dai, amma babu ko duriyarsu. Aliyu dai ya yi waya wa Hajjah cewa yana bakin aiki a Ibadan, don haka ba zai samu zuwa gida karshen watan nan ba sai na sama, suna tare da amaryar a Ibadan. Uhm! Namiji kenan. In ji Umma Sulaiman Shu’aibu ‘Yan Awaki. Kudan zuma, indararon roba ta ko ina zuba kake. Allah ya gyara.

Takurawar da Mansur Modibbo ke min a gida Giwa da Zaria yasa duk garuruwan suka fice min a rai. Domin dai ni tunda na rasa Yaya Aliyu bana jin zan iya wata aba wai ita soyayya nan kusa. So dai guda daya ne, na sha shi na warke, bana fatan Allah ya kara maimaita mini. Ko ina fatan hakan ba cikin garuruwan nan uku ba, Zaria, Giwa da Kaduna. He must be a stranger! Very far away!!!

Ban gama jinyar wancan ciwon ba yake nema na da in dasa wani, “Shin shi wannan bai ma da tausayi ne Ummi?” Na tambayi Ummi a yammacin wata asabar. “Wai da me zan ji ne? Yeah! I would love to marry a stranger, but he must be from far..... and he’s a stranger but not from far....”

Don haka na rika yin baya-baya da shi da kora da hali wanda ya fi kora da sanda, duk da mahaukacin son da yake min kuwa. Ba wai don yana da wata makusa ba, dukkan halayen shi ababen yabo ne.

Ni da Ummi mun kasance cikin kewar Zanirah, kullum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Hajjah kanta daurewa take tana sabgoginta, amma rashin Zanirah a gidan ita ma yana dukan ta. Daga mu yi tagumi, sai mu kwanta. Mun daina barin yara su kunna T.V a gidan balle radio. Sai mu ce sun dame mu. Mun dai mai da gidan kamar gidan mutuwa, farin cikinmu ya takaita, ba Zanirah ba Aliyu. Muna cikin kewar da ba za ta misaltu ba, ko yaushe muna kwance a daki kamar tsumma.

Don haka na ji dadi da Hajjah ta kawo shawarar wai mu tafi Kano gidan Yaya Rabi mu huta gajiyar baki kafin fitowar takardun karatunmu mu ci gaba da karatu. Dukkanmu ba karamin mamakin wannan magana ta ci gaba da karatu muka yi ba.

Na yi tunanin ko Hajjah ta yi hakan ne don ta samu na manta da Yaya Aliyu gaba daya. Abin da ba ta sani ba shine, tuni na bude kundi na sanya Aliyu a ciki (as a past tense). Wallahi ko da zan mutu babu aure, babu huldar da za ta shiga tsakanina da mijin Zanirah (other than) ta ‘yan uwantakar da ta hada.

Muka shirya tsaf sai Kano. Yaya Rabi mutum guda har da rabi don zumunci da son dan uwa. Zan iya cewa duk ‘ya’yan Hajjah babu wanda ya kaita kirki. Zama da ita da raha irin ta mijinta Yaya Muftahu ya wanke mana damuwa kakaf. Don sai ya zamanto Yaya Rabi ta cike mana gurbin Zanirah, Yaya Muftahu ya cike mana gurbin Yaya Aliyu. Sai muka kwantar da hankalinmu muka bude sabuwar rayuwa mai dadi.

A irin hirarrakin da muke yi da Yaya Rabi ta kan so a sako hirar su Zanirah, ko da wasa Yaya Rabi ba ta taba sanin mun so juna ni da Yaya Aliyu ba. Irin maganganun da take sakin baki tana fadi a kansu a gabana ya kan kona min rai ya tado wani kwantaccen ciwo da na riga na samu ya warke.

Akwai sanda za ta ce, “Allah kadai ya san irin soyayyar da suke barzaa yana muzurai yana cewa baya so din” Ko ta ce, “Uhm! Su Zanirah ana can Ikko ana romansewa”. Ko ta ce, “A gaskiya Zanirah ta caba miji. Ga kyau ga kuma kyawun hali. Aliyu Mutum ne wanda zai shagwaba matarsa, ya bita da duk yadda yadda ta yi da shi, ba irin Bashir, Fa’iz da Mus’abu bane”. Na kan kau da kai ne kamar ban ji ta ba. Ummi ta yi dariya kawai. Haka nan ban taba tankawa ba sai Ummin.

Tsakanina da Ummi yanzu mun koma mun dinke kamar da. Domin ta lura in har tana son hulda dani to fa sai ta ajiye zancen makiyina Fa’iz a gefe. Ba ta zancen Fa’iz a gabana kamar yadda duk hotunan shi da ire-iren kayan da yake aiko mata ta tattara su ta aje a wata katuwar jakar Hajjah a Giwa. Amma dai ai na ji TAKORI ta ce, “ZUCIYAR MUTUM, BIRNIN SA!”

[6/3, 4:13 pm] Takori: ZUMUNTAR KENAN 2

Washe gari muka raka Momi bikin walimar ‘yar aminiyarta Dacta Ladi, cikin Tudun-Wada. Lancin din da aka yi na ‘yammata a (Congo Conference) ya taimaka ainun wurin rage mana damuwa dukkanmu, kowaccenmu ba ta dawo haka ba sai da saurayi. Suka biyo mu har gida, Momi ce ta lallabasu ta ce su dawo gobe lokacin magariba ta yi ido na ganin ido ya fi. Washe gari kuwa da safe muka tattara muka koma Kaduna.

Har muka kare satin ni da Zanirah kowanne ya kasa sakin jiki da dan’uwansa. Abin da bamu taba tunani ko a mafarki zai taba faruwa a rayuwarmu ba. Kai SO din nan bala’i ne, masifa ne ba karama ba tunda har ya iya farraka (shiga tsakanin) ni, Ummi da Zanirah.

Ranar da zamu koma makaranta mun shirya tsaf cikin uniform. A bakin gate zan shiga motar Baban Kaduna ya ajiye ni makaranta, ita kuma za ta shiga school bus direban Baban ya maida ta Giwa (GGSS Giwa) sai ta riko hannuna. Ta matse gam cikin nata, hawaye ya fito daga idanunta ta yi azamar dauke su da yatsunta.

Ta ce, “Fa’izah ki fidda damuwar dake damun ranki ki yi (facing final exams) dinki yadda ya kamata, wannan ce damarmu ta karshe ta gina (future) dinmu, kada mu bari abin da bai kaita muhimmanci ba ya rushe”.

Na murmusa ina kokarin mai da nawa hawayen na ce, “And you too Zanirah!”

Amma a zuciyata cewa nake, “Kin manta ne Zanirah, an ce “LOVE IS OVERALL!”

To haka rayuwar ta kasance mana ba dadi a makaranta ma, kullum zullumina kammaluwar jarrabawarmu, isowar karshen karatun nan.

Gab da zamu zana JAMB na shiga samun katunan fatan alkhairi daga Yaya Aliyu masu dauke da kalamai masu karfafa zuciya tare da kwantar da hankali.

A kalamanshi ya fi ambata ‘nasararki na nufin nasarata, kwanciyar hankalinki shine tushen samun nasarar, nasara ba ta zuwa da sauki, nasara sai an sha gwagwarmaya ake samun ta. Soyayyar da ba a samu tangarda ko bambance-bambancen ra’ayi ba, ba ta kai wa gaci.

Fa’izah ki sa a ranki ba zamu yi aure bane kawai in dama tun fil azal Allah ya rubuta ba zamu yin ba”

Wannan kwarai ya taimaka min wajen samun nutsuwa na zana jarrabawar JAMB lafiya cikin kyakkyawan zaton samun kyakkyawan sakamako, wanda zai fitar dani kunyar iyaye da masoyana.

Tsakanina da Ummi sai kallo da ido in an haxu a hanya, haka nan kunnuwana basa huta jiye min irin sakonnin da take samu daga Fa’iz akai-akai ba. Daga bakin Naja’atu da Haulatu. Tare da tabbatar min Ummi ta yi nisa a son Fa’iz ta yadda za ta iya batawa da kowa ma a duniya bani ba, don haka in daina tunanin zan iya hanata ko zan rinjayeta ta bi ra’ayina.

Yaya Aliyu ya kawo mana ziyara muna wata biyu da dawowa, bai fi saura sati uku mu kammala makaranta ba kenan. Hankalina ya yi mugun tashi da ganin yadda Aliyuna ya koma kashi da rai, ido a lungu, dama jikinsa fyalan-fyalan babu kwari haka yake, dogon Bamalle mai suffa irin ta Baba Na’ibi.

Baki a bude nake tambaya “Shin Ya Aliyu ulcer din ta kwantar da kai ne bamu nan?”

Ya girgiza kai ya ce, “Ko daya Fa’izah. Illah Hajjah da Baban ABU dake neman zauta ni. Hajjah ta rantse ta kuma ta rantse ba ta san zancena dake ba, ba kuma za ta yi miki aure yanzu ba.....”

A tsaye nake amma sai ji na na yi ragwaf, na yi zaman rakuma a gaban  Yaya Aliyu. Idanuna ke fitar da wasu irin hawaye amsu zafi da yaji da ban taba fitar da irinsu a rayuwata ba, a yayin da nake cewa, “Ni kam Yaya Aliyu na hakura, ba zan iya jayayya da Hajjah ba, na hakura har ga Allah. 

Dama an ce duk soyayyar da ta yi tsayi irin haka da kyar ne take kai labari.... Na hakura..... ko ba komai ba zan yi bakin ciki ba don ka auri ‘yar’uwata jinin jikina Zanirah ba..... ina da yaqinin ban barka a hannun da zan yi tararrabi ba, you are in safe hands,  domin Zanirah nice, ni Zanirah ce, babu bambanci daga kamanni da halayya, sai ma wanda ta fini. Zan so ka yi farin cikin jin cewa Zanirah na matukar son ka, irin son da tunaninka bai taba baka ba......”

Ya katse ni cikin tsawa..... “Fa’izah baki da hankali? Kina hauka ne, kina so ki kashe ni ne? Shekaru goma sha biyu da na kwashe ina dakon soyayyarki, dai-dai da rana daya zuciyata ba ta taba hutawa ba da azabar soyayyarki da abin da za ki saka mini kenan wai kin barwa wata ni?”

Na sunkuyar da kai kasa yayin da hawayen suka sunce a kundukukina suna rige-rigen tadda kasa, aguje suke bulbula wani na bin wani suna masu tuna mini kaunar da Yaya Aliyu ya shekara nuna mini.

Wahala wadda uwa da uban da suka haife ni basu yi min kwatankwacinta ba in an dauke hakkin haihuwa. Duk da bai ambaci wahalar da ya sha a kaina ba sai ‘kauna’ da ‘soyayya’ ya zama dole ni din in tuna da wannan.

To amma babu abin da zan iya a ciki. Tsana ga Zanirah ko kuwa kin biyayya ga Hajjarmu? Gyatumar da iyayenmu ma basa tsallake umarninta?

Ina mai girgiza kai a gaggauce na rarrafa ga Yaya Aliyu yayin da na kama tafin kafarshi ina kuka, na ma manta a cikin ofishin vice muke, ina fadin “Ka yi hakuri Yaya Aliyu, ya ya kake so in yi toh? Kana nufin in baka hadin kai mu yi butulci ga Hajjah da Baban Kaduna da Mama Asma’un da ta tsuguna ta haifi Zanirah amma ta fifitani a kanta? Ko ko Hajjar da ta sha wahalarmu, wahalar da iyayenmu basu sha ta ba? Ba zan iya ba! Ka yafe ni Yaya Aliyu!!

Na san ka so ni, ka bautu a son da kaunata tsayin shekaru, to haka Zanirah ma ta kwashe shekaru tana begen zama a muhalli na. Na tabbata za ta yi maka biyayya fiye dani tunda son ta ya rinjayi naka. Sanin kanka ne Zanirah mutum ce mai sanyi da saukin hali, nutsuwa da hankali tamkar kai, it must surely be a perfect match as usual within A.B family. Nima Allahu ya bani gwarzon miji tamkar kai mai hali da aqida da kamannin Yaya Aliyu. Kundin shafukan rayuwata will be incomplete without the scenes of Yaya Aliyu.....”

Na juya ina tafiya da baya-baya ina masa murmushi ga hawaye na bulbula. Aliyu bai iya ya ce mani komi ba illa buga hannuwanshi duka a jikin garu (bango) ya kifa kai a jikinsu yana rusar kuka, kukan da bai taba yi a rayuwarshi ba, kukan da wani namiji kwatankwacin Aliyu dai bai taba yi a kan mace ba......

“Hajja kin cuce mu..... kin yanke mana buri a dab da wa’adin cikarsa..... kin guntile ingantacciyar soyayyar da aka dasa ake mata ban ruwa ta yi yado ta ba da yabanya ana gab da cin amfaninta..... Anya zamu iya yafewa Hajjah? Meye amfanin soyayyar da take nuna mana tunda a karshe cuta take zama? Babu!!

(Rabuwar mu da Yaya Aliyu kenan).


****

Na yi matukar kokarin ganin na manta da Yaya Aliyu, na fidda son Aliyu a raina, na yi kukan, na yi addu’ar, amma a kullum son Yaya Aliyu ke dawo min danye jagab, sabo fil a zuciya.

Meye sauran farin-cikin ne a yanzu a zama a A.B House a yanzu ni Fa’izah! Ummi mun rabu saboda Fa’iz, Zaneerah mun rabu saboda Aliyu, shin me zan koma in yi a Giwa? In ina da zuciya kare bai cinye ta ba daga yau na bar Hajjah Hadiza Giwa, zan koma gidanmu, ko da uwata da ubana za su kasheni ne tunda Hajja ba ta so na. Zanirah da Fa’izu ta fi so tuntuni.

Wannan haka yake ‘ya’yan Baban Kaduna take so, domin shine mai kudi, shine mai huce takaici, wato masu gidan rana. Yana kaita Hajji duk shekara ko ya ya ne? Shin ma wai me nake tsinta a kauyen Giwa ne da babu a Zaria? Zariar ma muhalli irin (Area One). Ba komai bane illa sabo da su Ummi. Tunda rayuwar ta zo da guguwar sauyi kowa ya koma gaban uwa da uban shi.

Yaya Aliyu! Yaya Aliyu!! Yaya Aliyu!!!

A kullum na tuno irin soyayyar da muka gudanar, a gaba dayan tsayin rayuwarmu, kulawar da ya yi mini, wahalar da ya sha a kaina, sai na yi kuka na gode Allah. Hawayena sun kafe, na kama kukan tunkiya, wanda babu hawaye sai sauti.

Babu abin da ya firgita ni kamar migraine (ciwon kan barin kai guda) da ya same ni a kowanne dare, ga wani zazzabi-zazzabi mai zafin gaske da nake kwana da shi da safe ya wartsake. Ban karanta ba, amma na kan ji an ce wadannan alamu ne na ciwon hauhawar jini (hypertention).


****

Ranar da muka zana takardar karshe wadda ta kasance ‘Islamic Studies’ na daga hannuwana sama na yiwa Allah godiya da ya nufe ni da kammala makaranta lafiya ba tare da na taba karya doka ko guda daya da makaranta ta kafa ba, ba tare da na taba batawa kowa da zama ya hadani da shi ba a kan sani, sai bisa ajizancin dan adam, kamar yanda ban taba yin laifin da aka dauki bulala aka shimfida a fatar jikina ba tsayin shekaru uku.

Na dawo hostel na shiga rarrabar da kayana ga juniors dinmu, na rabar da komai nawa har sutturar da nake amfani da ita a makaranta ban bari ba. Ban bar komai ba sai ‘hankici’ na da sutturar jikina wanda ya zame min tamkar jarabi. Na rufa shi a fuskata a wannan ranar, na yi kwance bisa gadon boarding school kwanciyar dana kira kwanciya ta karshe a sakandire.

Na juya rigingine al’amuran na gifta min tamkar majigi, kamar yau ne Yaya Aliyu ya kawo mu QUEEN AMEENA COLLEGE KADUNA. Yau ga Allah ya kawo mu ranar barin ta. Shekaru uku tamkar kwana uku.

Kwanakin, satittikan, watannin da shekarun sun shude ba za su kuma dawowa ba. Sai dai al’amuran dake cikinsu masu yawa ne a gare ni da ba zan iya mantawa dasu ba. Tunanin tashin hankalin da zan je in taras a gida gobe ya addabe ni.

Kowa ka gani a harabar makarantar ‘yammata ta Sarauniya Amina a washe gari bakinsa har kunne yake, farin ciki ya wadace shi. Sabanin ni da ta kasance bakar rana a gareni. Duk da dimbin tarihin da ranar ta ajiye min mai dadi ga iyaye da ‘yan’uwana.

Baya ga kyautar wadda ta fi kowa Da’a da kulawa da al’amuran addini (Amirah). Ni Fa’izah Ahmad Abubakar Bamalli Giwa, na karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya harsuna biyu mafiya shahara a duniya, wato Turanci da Larabci.

Wannan duk karami ne a kan yabon da na samu a kan kananan rubuce-rubuce na ‘Literature’ Littafina ARE VOWS MEANT TO BE BROKEN? Gwamnatin Kaduna ta saya akan kudi masu yawa, Sarkin Zazzau ya saya, dansa Yariman Zazzau Mansur Modibbo ya saya a kan kudi masu firgitarwa. Galadiman Zazzau ya saya, Iyan Zazzau ya saya duka don rabawa a labiraren makarantun sakandire na jihar Kaduna.

Wai-wai-wai. Ni Fa’izah na ga hasken camera a wannan rana, kamar ta bikin sallah. Haka na hau steps na rungumo kyaututtuka da award dina na literature. Babu abin da ya daga min hankali kamar rashin matallafi ko wani da ya shafe ni da zai karbe ni ya nuna min kauna cikin dangina da ya fito daga dimbin mutanen da ke hall din. Wannan ya tabbatar min daga Giwa har Kaduna da Zaria babu wanda ya zo mana.

A yayin da na ke saukowa daga ‘steps’ din saukowar na tafiya ne dai-dai da bugun zuciyata, hardewa nake ina rangaji kamar zan ci da baki. Kafafuwana da hannayena baki daya sun sage. Ko kowa bai zo ba na zaci Yaya Aliyu zai yi kokari ya zo a wannan rana.

A yayin da nake cikin wannan hali na takaicin rashin ‘yan’uwana, a yayin ne Ummi ta ratso daruruwan mutanen ta iso gareni ta tallafeni ni da kyaututtukana duka ta rungume mu muka karasa mazaunina tare, ana sakar mana hasken camera da saitin vedeo.

Bayan taro ya watse na hangi Ummi can nesa dani tana magana da fadawa. Na cira kafa na ci gaba da tafiya rungume da kayana. Ba wasu kaya bane kyaututtukan da na samu ne da jakar takarduna rataye a kafada ta, sai hankcina a hannun hagu ina mai share gumin babu gaira babu dalili dake shararo min, abin mamaki tun daga tsakiyar kaina gumin ke tsattsafowa yana biyo goshina.

Ummi ta biyo ni da sauri har tana hadawa da gudu-gudu don ta cimmani kamar babu abin da ya faru tsakaninmu, ta ce, “Ya kika taho kika barni Fa’izah? Kinga abin mamaki babu wanda ya zo mana anya lafiya?”

Na kalle ta kawai na ci gaba da tafiyata. Daga bisani ganin ta jeru dani muna ci gaba da tafiya sai na ce, “Ai ina ganin Ummi tafiyarmu tare ba za ta yiwu ba, don ni nan Zaria na nufa”.

Ummi ta dube ni baki sake ta ce, “Ki je Zaria ki yi me?”

Nima cikin mamaki na ce da ita, “Ah! Mutum da gidan ubansa har a tambaye shi abin da zai je yi?”

Ta ce, “Ban fahimce ki ba, amma ko ina dai za ki kafata-kafarki, don yau wata haka-haka nake ganin ki”.

Na ce, “Haka-haka kamar ya ya? Na yi miki kama da sabon kamu kenan”.

Ta ce, “Allah ya baki hakuri, ni ban ce ba, amma muje sai a kaimu Zariyar ko kuwa?”

Na dube ta da mamakin yadda ta manta mun samu sabani a junanmu. A raina na ce “Shin Ummi kina tunanin zamu koma kamar da alhalin kina son makiyina ni da uwata?”

Ban ce mata komai ba muka rankaya zuwa bakin titi. Mun yi tsayuwa fiye da ta rabin awa babu taxi, in ma sun gifta mu a cike suke. Ban so zan yiwa Ummi magana ba, amma hakan ya zame min dole.

“Kawai mu hau okada, tunda ba wasu kaya garemu masu yawa ba”.

Hakan kuwa muka yi.

Ban ga kowa a harabar gidan Baban Kaduna ba, babu motocin Baba ko daya, babu yara ko daya masu yi mana oyoyo idan mun zo! Tun daga nan gabana ya soma faduwa, na fiddo naira dari biyu na baiwa masu okada muka karasa bakin gate muka gai da Malam Hassan maigadin gidan.

Ya ce, “Ku kadai kuke tafe?”

Har muna hada baki wajen cewa, “Eh, wallahi Malam Hassan. Ina jama’ar gidan suka tafi ne? Mantawa aka yi yau muke graduating? Babu wanda ya je mana daga Giwa, Zaria har nan cikin Kaduna?”

Ya ce, “Hala mantawa kuka yi yau ake daurin auren Zanirah da Alh. Aliyu???”

Wallahi baya ga wannan ban sake jin komai ba, ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai tsintar kaina na yi a asibitin Jinya dake cikin garin Kaduna, Ummi na gefen kaina tana mini firfita. Na soma kokarin tuno abin da na ji (DAURIN AUREN ZANIRA DA ALIYU).

Na fashe da wani gursheken kuka a cinyar Ummi, ita ma Ummi kuka take, na tabbata kukan tausaya mana ne ni da Yaya Aliyu, cewa take “Ya aka yi haka Fa’izah? Garin ya ya ni ban san zancen ba? Ya ya aka yi haka? Na dauka ke za a baiwa Yaya Aliyu?”

Na mike zumbur ina layi na ce, “Ummi ya zama dole in je Giwa a yanzun nan,  dole ne in je Giwa kada Zanira ta dauka ina bakin cikin auren ta da Yaya Aliyu ne, ta wuce haka a gareni, tashi mu tafi Ummi”.

Ummi ta share hawaye ta mike, halin da nake ciki ne yasa ban bambance motar suwa muka shiga zuwa Giwa ba, ashe motar Yariman Zazzau ne Mansur Modibbo wanda ke biye damu da abokinsa tun daga Queen Amina har Jabi Road. A kan idonsu na fadi, kuma su suka kawo ni asibiti tare da Ummi.

A hanyar mu ta zuwa Giwa Mansur ya ce, “Shin wace ce ita wannan Zanirah da labarin aurenta ke sumar da Fa’izah yake sanya Ummi kuka?”

Maganar tashi sai ta bamu dariya har ni da ke cikin hali na kaka-ni-kayin zuciya. Ummi ta ce, “Duk wani bayani da zan yi maka a yanzu ranka ya dade ba za ka fahimta ba, Zanirah is our bloody sister”. Ya ce, “To na hakura da jin wace ce real Zanirah sai na dawo. Ni dai fatana Ummi don Allah ki rinka shigar dani kin ji? In na kai ku yanzu juyowa zan yi sai sati mai zuwa zan dawo, saboda zan yi tafiya zuwa Abia State na san kafin lokacin Fa’izah ta dawo normal!”

Ni kam kallon shi ma ban yi ba fuskata na cikin cinyoyina, tunda na rasa Yaya Aliyu babu abin da zan nema a wani Da namiji, domin ko kusa ba zan samu mai hali abin so da irin kyakkyawar zuciyarsa ba. It’s indeed a great loss! Addu’a nake a cikin zuciyata, “Ya Allah ka sanya min hakuri da dangana, ka bani juriya da karfin zuciyar fitar da Yaya Aliyu Haidar daga Zuciyata”.

Dai-daikun jama’ar da na gani a harabar A.B Estate ya tabbatar min har an gama daurin auren Zanirah da Yaya Aliyu! Wayyo Allah ni Fa’izah na rasa Yaya Aliyu kenan, tabbas na rasa shin, na hakura har ga Allah daga yau na bar wa Zanirah Yaya Aliyu.

Sunan Allah Ya zuljalali wal ikrami nake taunawa a harshe da hakorina. Babu shakka zuciyata ta yi sanyi illa jikina dake faman karkarwa, amma a kan fuskata farin ciki ne bayyananne. Ni kadai na yi sallama falon Hajjah domin na baro Ummi waje tare da su Mansur Modibbo wanda su da gaske suke neman iri suka zo gidan Bamalli. Lallai iska na wahalar da mai kayan kara (na fada cikin raina).

Gaba dayansu ‘ya’yan Hajja Hadiza su goma sha biyar in ka dauke Yaya Rabi auta dake Kano, Baba Muntari, Baba Na’ibi, Baba Ibrahim, Baba Barau, Baba Sadi, Baba Sani, Baba Salisu da su Yaya Hauwa, maza goma mata hudu kenan, duka zaune falon Hajjah wanda yake makeken gaske suna tattaunawa ko a kan mene ne oho!

Na tsugunna na gaida su daya bayan daya. Hajjah ta ce, “Yar albarka, kuna raina wallahi, yanzu nake cewa a je a dauko ku don ita kanta amaryar yanzu ta shigo daga tata makarantar?”

Ni dai na ce, “Uhm! A raina na ce, ‘dole ki ce min ‘yar albarka mana tunda kin san yankan bayan da kika yi min, kin barni da cizon yatsa.... ai dole kisa min albarka!’

Amma a fili sai na ce, “Wallahi kuwa mun yi  mamakin rashin zuwa kowa, sai da muka je Jabi Road, Malam Hassan ke gaya mana daurin auren Yaya Aliyu da Zanirah ake yi, shi yasa ma bamu damu sosai ba muka taho da kanmu kawai”.

Na mikawa Babana kyaututtukan da na samu cikin ledar Ghana must go da cheque din kudaden da na samu. Su Baba suka shiga dubawa suna kwararamin albarka tun karfinsu. Sai dai duk abin nan da ake na lura Yaya Hauwa na hankalce da duk motsina da na jajayen idanuwana, tana bina da kallon tausayi da karfafa gwiwa.

Fuskarta cike da tausayi ta ce, “Fa’izah duk wannan ramar ta mecece?” Ta fada tana taba kasusuwan wuya da suka bullutso min da hannun damanta.

Na yi murmushi na ce, “Kai Ya Hauwa kin manta daga kurkukun jarabawa na fito?”

Ta yi murmushi kawai irin nasu na manya.

Ba zato Baba Na’ibi ya ce, “Na yi zaton Fa’izah ce za ta zamo matar Aliyu?”

Duk sai kowa ya yi tsit, yana mai jinjina maganar. Sai Hajjah ta bude baki a hankali ta ce, “Na’ibi!” Ya dago ya dube ta cikin amsawa. A nutsenta ta ce, “Ta ina Fa’iza ta dace da Aliyu?”

Baba Na’ibi a dan daburce ya ce, “Ban gane ba Hajjah?”

Ta yi murmushi ta ce, “Abin nufi a nan, shin Fa’izah ba mace ce mai tsiwa, taurin rai, ginshira, dagewa bisa duk abin da ta kudurtawa ranta (dertermination) kekasasshiyar zuciya a kan duk abin da ta tsana ko mutumin da ta tsana ko halayyarsa. So wanda ya wuce hankali ga duk abin da take so? Shin Aliyu da Zanirah ba mutane ne masu sanyin rai ba da saukin zuciya?

Saboda haka sun dace da juna, za su zauna da juna lafiya, za su ji dadin zama da juna babu hayagaga. Amma halayen Fa’izah ba kowanne namiji ne zai iya zama da ita ba sai NAMIJIN DUNIYA, mai halaye irin nata ba mai sanyin rai irin Aliyu ba. Ma’abocin juriya da karfin jiki da na zuciya baki daya.

Amma in an hada Aliyu mai sanyi da Fa’izah mai tsiwa da jumurda, bakwa tunanin Fa’izah ce za ta zama mijin, Aliyu ya zama matar saboda matsanancin son da yake mata? Wato ya zamo sai yadda ta yi da shi kenan saboda gudun fitinarta da bacin ranta? Kasancewar shi mutumin da bai son tashin hankali da hayagaga ko kankani?

Kuna gani fa tun yanzu duk abin da Fa’izah ta gindaya mishi baya iya tsallakewa duk ya lalace a gindinta, bini-bini yana binta kamar bita-zai-zai wace kalar rayuwa kuke tunanin za su shimfida a gidan auren su? Baya iya musa abin da ta ce, baya iya tsawata mata in ta yi ba dai-dai ba, tun suna yara nake hankalce dasu.

Ina rayuwar aure za ta yiwu tsakaninsu ba tare da raini ya shiga tsakani ba? Aliyu da Zanirah kuwa da wuya za a ji kansu, za ku ga irin rayuwar da za suyi ta namijin da ya isa da gidansa, za ku ce dama na gaya muku ne”.

Gaba daya suka yi shiru suna masu jinjina maganar, haka nima ina mai gaskata kowacce kalama a cikin zancenta. Tuni na gane hikimar hada auren Zanirah da Aliyu da tsohuwar mai tarin hikima da fasaha ta yi. Wato muddin na auri Yaya Aliyu ba zai iya lankwasa ni ba ko kadan, saboda matsanancin son da yake min. Tana masa gudun zama mijin ta-ce ne kawai gara ta ba shi wadda zai iya da ita don son zamar da shi mai kima da karfi a gidansa.

Amma Zanirah halinsu daya (simple personality) wadda ba ta zafafawa cikin al’amuranta. Tabbas halayen Zanirah baki daya irin na Yaya Aliyu ne, hakuri, sanyin rai da sanyin zuciya. Abin da babba ya hango yaro ko ya hau ganuwa da Dala da Gwauron Duste ba zai hango ba.

Sai dai ta wani bangaren Hajja ta yi (underestimating) dina. Ni ina son Yaya Aliyu ne saboda kirkinshi, halayensa da mutuncinsa da son addini. Ban taba tunanin in yi amfani da son da yake mini in mun yi aure in mai da shi sahoramin miji ba (mijin-ta-ce).

Sai na bude baki a gaban Babannina duka na ce, “Hajjah kina da gaskiya. A da kam mun so juna da Yaya Aliyu so ba na wasa ba. Sai dai daga yau wallahi na hakura, na barma Zanirah da zuciya daya, zan kuma ci gaba da binsu da kyakkyawar addu’a Allah ya karkatar da son da yake mini kanta. Ban ga laifin ki ba Hajjah, Allah ya basu zaman lafiya.....”

[6/3, 4:13 pm] Takori: Daki guda Yaya Rabi ta ware mana mai dauke da bayan gida, kananan gadaje biyu, sai jar kilishi da ta malale ilahirin dakin da jan labulaye. Karamin bed-side fridge, sai mudubin dogon yaro mai sheki da kayan shafe-shafe da feshe-feshe, da kwabar adana suttura (wardrove) ta jikin bango.

Kamar yadda mazan Kano samari da magidanta basa ganin kyawawan ‘yammata su kyale, to haka fita ta gagaremu ni da Ummi. Har suna aka sakawa gidan Aunty Rabi a layin wai Gidan Mallawa.

Kiri-kiri muna gani za a gayyaci Yaya Rabi biki ko suna amma mu haramtawa kanmu zuwa muna ji muna gani, domin muddin muka fita, to kuwa la-shakka ba  zamu dawo mu kadai ba maza basu biyo mu ba.

Kofar gidan Yaya Muftahu baya rabo da mota da vespa, wanda mu bamu saba hakan ba sam a namu garin sai hakan ya dame mu ya zamo mana sabo ya takurawa walwalarmu. A hankali na soma fuskantar Ummi na canjawa, ta fara saurararsu.

Da na yi mata magana sai ta yi murmushi kawai har mulmulallun kumatunta suka lotsa, ta ce, “In mun koma inda muka fito ba shi kenan ba? Abu ne na dan lokaci. Namiji abokin rayuwar mace ne ba za ta taba rabo da shi ba”.

Cikin watanni hudu a gidan Aunty Rabi jikina ya soma wani irin canzawa, tsayina ya fito na mike sosai. Yawan kaimu (Zaynab Saloon) da Ya Rabi ke yi a (Mukhtar Mohammed Link) yasa gashina ya ware ya yi tsayi da taushi duk da ba (relaxing) muke ba wankewa ne da (steaming) kawai. Haskena ya dan fito duk da bani da haske. Kamannina na Mallawan usli ya fito sosai, na yi kumatu subul-subul, saboda kwanciyar hankali.

Kugu da kirjina duk sun canza kiyasi, tabbacin budurwa matashiya ‘yar shekaru goma sha takwas. Shin ma na taba gaya muku ko wace ce Fa’izah Ahmad Abubakar Bamalli Giwa??? Ban taba ba, illa kawai kun jera ni a sahun kyawawan Bamalli. To eh, ba zan yi musu ba a nan, sai dai akwai wasu ‘yan bambance which I didn’t clarify (da ban farrake ba) ga masu karatu na.

Ni kaina ban san ina da wadannan qualities din ba sai da na shiga shekara goma sha takwas da zamana a Kanon Dabo. Duka A.B Family ni kadai ce mai duhu (choculate). A yau, kaina na tsurama ido cikin mudubin dogon yaron gidan Aunty Rabi bayan fitowa ta wankan la’asar.

Ina da madaidaicin tsayi, wato ba doguwa ba ce ni, ba kuma gajeriya ba. Doguwar fuska mai dauke da mulmulallun kumatun hutu subul dasu masu nuna bana cikin wahalar rayuwa ko kadan, wadanda Allah bai halacci kwayar kurajen (pimples) ko daya a kansu ba. Idanuwana farare sol da bakin zanen ido mai walainiya na daukar hankali. Madaidaicin baki wanda ba kankani bane can-can ba kuma kato bane, jerarrun hakora farare sol, jere reras a cikin shi. Karan hanci siriri kamar an saka ruler an daidaita mata shi a tsakanin idanunta. Tunda ya taho daga sama a mike yake bai lankwashe ba ya dire kyam saman bakinta. Tsagin Mallanci 2-2 dake gefen fuskar Fa’izah su suka fitar da Mallancin ta sosai da an ganta babu tambaya zuriya’ar Abubakar Giwa ce.

Sumar kaina kan sakko har bisa kafadu, ya kwanta lamban. Wanda kitson shi kwararriyar ma sai ta hada da dabara. Duk da haka kuma cikin kwana hudu ya warware da kanshi ba tare da ta sanya kibiya ta warware shi ba. Don haka ta hakurewa kanta yin kitso kullum sai dai ta kalmashe shi cikin ribbons (bound).

In Aunty Rabi ta daddage ne take kalbace shi yar-yar ta kama bakin ta matse da dutse da roba sannan yake zama. Ba ta taba tsugunnawa wata mace ta kama mata kai da sunan kitso ba tun tasowar ta baya ga Hajjarta. Yalwar gashin kanta shi ya taimaka wajen inganta gashin ido da na girarta. Hakan bai ishe shi ba sai da ya bi ya kwanta a fatar jikinta kafataninsa. Irin wadanda  Sadanis basa yiwa (halawa) ya yin aure.

Don haka a kullum Fa’izah cikin (shower-shaving) take duk sati biyu zuwa uku don fitar da kyan fatar jikinta da kwantaccen gashi ke boyewa. Idan tana tafiya kai ka ce rangaji take, komai ya yi masha Allah, komai nata danye ne sharaf. Jikinta kamar mai shiga wankin fata a inji, domin jikinta ya fi fuskarta haske.

Ga zazzakar murya kamar diyar Shata, Fa’izah mace ce mai tsiwa, don in ta fara tsiwarta da mitarta har hacinta tsattsafar da gumi yake yi. Ba a yi mata ta kyale. Tana da kafiya da taurin rai, ba kankanin abu ke sanyata kuka ba. Tana da wuyar lankwasuwa a kan abin da ta kudurtawa zuciyarta.

Watanni hudu kenan muna zaman garin Kano, ko in ce zaman jiran fitowar jarabawa, zama mai dadi da ma’ana. Hankalinmu a kwance, rayuwar baya duka ta zama tarihi, komai ya zamanto kamar bai faru ba.

Don yanzu har na kan iya zama ayi hirar su Zanirah dani ayi dariya ba tare da na ji komai a raina ba. Zan iya cewa, soyayyar Yaya Aliyu babu ita ko kadan ta bace daga raina.

Zamanmu da Yaya Rabi (accounter) a bakin G.T na Gyadi-Gyadi (branch) mun karu da abubuwa masu yawan gaske. Ga dai girke-girke na zamani muna koyo, kwalliya kala-kala, tattalin miji da nuna masa soyayya mai tsafta mai tafiya da ZAMANI da CHANJE-CHANJEN sa, tsafta, kissa da tarairaya, duk mun nade su cikin kanmu daga gidan Yaya Rabi.

Wai yanzu ma kokari muke Hausar mu (accent) dinta ya yi dai-dai da na ‘yan Kano, domin masana luggogin Nigeria sun tabbatar da cewar Hausar Kano ita ce mafi karbabbiyar Hausa a Nothern Nigeria baki daya. Domin a lokuta da yawa in muna magana Yaya Rabi da Yaya Muftahu da dansu Abdul dariya suke mana, wai “Kauyawan Giwa”. Shi yasa muka yi zuciya muka koya a hankali.

Yau lahadi, daga Yaya Rabi har Yaya Muftahu basa zuwa aiki. Mu kan kasance ne wunin ranar da yamma a shagunan Breirut Road irin su Captano, Arebian Sweets da ire-irensu, ko manyan shagunan Kano irin su Country Mall, Ado Bayero Mall ko Grand Square da Well-Care don yin sayayyar amfanin gida da ta kayan makulashe.

To yau ma hakan, dawowar mu gidan kenan, muka kai ledojin hannayenmu kitchen ni da Ummi, muna adana kowanne a freezer masu bukatar firinji, muna saka su. Yaya Hauwa ta kira wayar Ya Rabi ta sanar da ita jarrabawar mu ta fito. Amma dole ana neman mu a makaranta zamu karbi ‘testimonial’ da ‘statement of result’ ko da zamu duba ‘online’ ne.

Don haka washegari muka nufi Kaduna da direban Muftahu. Abdulrahaman ma ya saka naci sai ya bimu saboda su Junior autan Maman Kaduna mutanensa ne. Muka tattara duka Kaduna ta diba, su kuma kowanne ya nufi office a safiyar litinin kenan.

A Jabi Road komai ya canza, tun daga bakin gate na tabbatar Baban kaduna Allah ya kara masa budi da falala hade da nasara cikin al’amarinsa. 

Hyundai, Jeep-Jeep har guda uku sai neman fashewa suke yi don koshi da kyalli a harabar adana motoci. Haka korran (grass carpet) sun malale harabar gidan da furanni kala-kala masu dadin kamshi. Komai na falon ya canza sai kyalli yake yi. Ita kanta Mama ta kara kirbewa dama ga ta masha Allah tun-tuni, kamar za ta tsage cikin (sofa-bed). Kai! Wadannan mutane suna cikin daular da babu wani cikin A.B Family dake cikin rabinta.

Na girgiza kai tare da sallama, da gudu na karasa jikin Mama a (sofa-bed) muka rungume juna domin mun jima bamu hadu ba, tun bikin Zanirah, ga kuma soyayya mai karfi tun fil’azal wadda ta zarta ta jini kawai, har ma da haduwar jini da Allah ya hada a tsakaninmu.

Mama ta ce, “Oh! Su Fa’izah an gudu Kano don ba Zanirah ko duriyarku ba a ji, ko waya babu, kun kyauta kenan?”

Na ce, “Kin san Baban ABU ya hanamu rike waya Mama, kuma na je ne don na huta na samu nutsuwa. Amma wallahi Mama kullum kina raina”.

Ta ce, “Na sani, na kuma yarda Fa’izah”. Ta dubi Ummi ta ce, “Sai tsohuwa!”

Ummi ta shagwargwabe fuska ta ce, “Allah Mama ki bari....”

Muka sa mata dariya ganin yadda ta yi da fuska kamar za ta barke da kuka. Mama ta ce, “Mutuminki kullum ya yo waya korafinsa daya, yaushe za ki baro Kano? Yau dai ga Ummi a gidan nan, anjima zai yo waya bakina ya huta cewa, ban sani ba”.

Cikin matsananciyar murna Ummi ta makalkale Mama tana dariya kamar ba surukar ba, ta ce, “Allah da gaske Mama Ya Fa’iz na tambaya ta? Don Allah Mama ya muryarshi ta koma? Ban taba magana da shi a waya ba tunda ya tafi”.

Mama ta ce, “Muryar Fa’izu ta karye (kwata-kwata) da Ukrainian language da Belarusian. Da kyar nake fahimtar Hausar shi. Su Shu’aibu ba ma sa ganewa gara ma in yana Larabci ko Turanci”.

Ummi ta yi zugum (her passion for him heightened). Tana duban Mama hannuwa tallabe da fuska ta ce, “Kin san Allah Mama, na yi dana sani tunda fari da na san haka ne da na shiga Arabic Club da Fa’iza tayi-tayi dani in shiga a makaranta na ki, don a ganina yawa ne in tsaya koyon Larabci tunda ba a fiya amfani da shi a nan Nigeria ba”.

Mama ta ce, “Ayya! Kin yi babban kuskure, domin Larabci shine harshe mafi soyuwa a wurin Ubangiji da ya zabe shi a cikin harsunan duniya ya saukar da Alkur’ani da shi. Har yake cewa, “An saukar da shi Alkur’ani BALARABE....” Kuma Annabi (S.A.W) ya ce, “Ku so harshen Larabci saboda uku. Na daya ni Balarabe ne, na biyu Alkur’ani Balarabe ne. Na uku harshen ‘yan Aljanna shine LARABCI!”

Ummi kamar ta fashe da kuka, na yi dariyar mugunta na ce, “Rabu da ita Mama, ba zan taba manta sanda su Ummi suke min dariya don ina Alifun Ba’un ba. Wahid-Ithna-thalatha ban iya 123 da ABCD ba, ga shi na muku wayo.

An ce ana jifan tsuntsu biyu da dutse daya, don a ci amfaninsa. Yau Ummi Turancin me za ku nuna min? Sai dai in nuna muku  LARABCI”. Na yi mata gwalo.

Ummi ta yi zugum, da alama kalma ta kare a bakinta. Na yi dariya mai isata har cikina ya kulle. Ummi ta zo iya wuya ta tashi ta fice daga dakin, muka ci gaba da yi mata dariya.

Mama ta ce, “Sai yaushe za ku je wa Hassanar ku ne?” Tana nufin Zanirah.

Na ce, “Kai-kai! Mama so soon haka? Ai ba a zuwa gidan amare sabon aure sai sun haihu”.

Mama ta lakace min hanci ta ce, “Ai su da yake sun damu daku zuwan su uku duk kuna Kano. Ba kuma don kowa suka zo ba sai don su ganku”.

Na ce, “A’a Mama, da da gaske sun damu damu da sun bimu inda muke. In babu jirgi akwai mota, tsakanin Kaduna da Kano awa biyu ne kacal. Ke dai basu gama amarci bane ma je suna in da rabo”.

Mama ta ce, “Kamar mai gani har hanji an zo ana ta laulayin ciki kamar wadanda suka yi tuntube da shi a dokin kofa. Ku yaran yanzu ko kadan cannot excercise patience. Mu zamanin mu sai amarya ta shekara biyar dakin miji ba ta samu ciki ba”.

Duk da zuciyata ta dan sosu ban bari Mama ta gane ba. In Aliyu bai son Zanirah, ai ita Zanirah tana mutuwar son shi. Za ta san duk hanyar da ta bi ta janyo hankalin abinta gare ta. Sai na samu kaina a yau ina mai dan KISHIN Zanirah Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa!

Karfe tara na dare duka al’ummar gidan na bisa tebir suna cin abincin dare, har mu da muka bakunci gidan. Da tuwon laushi miyar alayyahu da aka wadata da naman Turkey (talo-talo) aka kuma shirbine ta da man shanu dan asalin GIWA.

Na lura Abdul zubi kawai yake ba kakkautawa, ban san sanda na yi dariya ba. Yahya mai bin Fa’iz ya ce, “Kalau kike dariya ke kadai?”

Na ce, “Baka ganin yadda yaro ya samu abincin zage-zagi ya rude baya so ya bari ya fara hadiye na bakinsa kafin ya kara loma?”

Abdul ya yi murmushi, ya san da shi nake. Can kuma ya ce, “Yanzu ba zan ce miki komi ba sai mun koma Kano kina cin bandashe (gurasa da kuli-kuli) tukunna”. Kowa yasa dariya.

Daga daki Mama ta fito tana fadin “Ku yi sauri Fa’izah, cin abincin ne kuma ya koma hira da shewa? Aiken ku zan yi unguwar Sarki ku amso min ankon ‘yar Hajiya Saratu da kun gama, dare yana yi”.

Karar wayar landline dake gefe ya sanya kowannensu yin wurgi da cokalinsa ya nufi inda wayar take, kokawa fa ta kaure domin Ummi, Yahya, Shu’aib da Junior kowanne ya ci alwashin shi zai fara daukar wayar ko ta halin kaka.

Mama ta ce, “Yau ina ganin sakarci, to bari in raba gardamar nan. Duk cikinku babu mai tabbacin kiran nasa ne ko ba nasa bane, tsammani kuke Fa’izu ne, kuma ba lallai ya tabbata shi din bane haka ne?”

Duk suka tsaya suna tsuma, ta ‘kauna’ da ‘doki. “Don haka ke babbar Yaya (ta nuno ni) dauki wayar ki jiye mana waye kamin wani ya dauka don a raba gardamar”.

Na yi dariya cikin ginshira na tsiyaya ruwan FARO mai sanyi a tambulan na soma kwankwada. Sanyin ruwan na sanyaya makogarona, yana taimakawa wajen digesting (narkewar) daddadan tuwon da na ci. Na yagi tishu na goge baki da hannu.

Ummi ta kufula ta ce, “Kina gani fa Mama sai ta gama yi mana yanga”.

Mama ta ce, “Kai, dadina dake gajen hakuri Ummi”.

Na yi murmushin tura haushi sannan na mike na nufi wayar landline da har lokacin ba’a bar kira tana tsinkewa ba, wayar na daga na amsa da “Assalamu Alaykum!”

Shiru kake ji, ga shi da alama ba a ajiye ba. “Hello!” Shima shiru. Na sake sallama aka yi shiru, ina shirin mikawa Mama wayar cikin kufula da mamakin wannan ikon Allah, ka kira waya kuma ka yi shiru kudinka na tafiya a banza. Muryar mai cike da ginshira ke tambayar “Impertinence Fa’izah ko?” (Fa’izah mai tsiwa?).

Tuni jijiyoyi masu ba da jini shi kuma ya yi circulating dinshi ga sassan jiki sun tsaya cak! Da ba da aiki. Jijiyoyin cikin kai masu ba da doka da oda su ma sun yi yajin aiki na (temporary). Muryar da ba zan taba mantawa da ita ba, muryar dan uwa amma MAKIYI. Muryar FA’EEZ, HAFIZIN HAJJAH, FA’IZU MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA.

Ban amsa ba. “Kaif halikum Fa’izah? How are you Fa’izah?” Maimakon na amsa sai na yi azamar cire wayar daga kunnena na mikawa Ummi jin wani mugun fushi ya taso min wanda duk kokarin zuciya ba za ta iya boye shi a gaban kowa ba, including UWA-MAHAIFIYA dake gabana tana karanta duk wani motion dina a kan wayar danta da kyawawan idanunta, masu cike da matsananciyar kauna gare ni. Irin kaunar nan da baki baya iya bayyana ta, domin Allah ne ke assasa ta.

Sai na zare wayar sannu a hankali daga kunnena na mikawa Ummi, tare da zare jikina daga cikinsu na yi dakin Mama don bakin ciki kamar in rushe da kuka.

In da abin da na tsana a duniya to abin da zai tuna mani da shekarun da na kasance cikin fargaba da ukubar Yaya Fa’iz ne. Balle ya tuna min da shi kansa. To gaba daya yau muryarsa na ji a cikin kunnuwana, muryarshi ta dawo min da ranakun can baya marasa dadi da na rufe babin su ta dawo da tsanarsa danya a zuciyata.

Haka na yi sallar isha ina ta sake-sake. Da na idar na bishi da muguwar addu’ar Allah ya gama shi da masifar duniya da ta lahira a can inda yake. Yasa a fatattako shi daga karatun ko garin tukin jirgin, jirgin ya fado ya ragargaje da shi. Amin summa amin. Don kam hakika ni mai bakin ciki ce da duk wani ci gaban FA’IZ GIWA kamar yadda yake a gare shi shima.

A daren Ummi hanani barci ta yi da labarin hirarta da Fa’iz. Da hanzari na taka mata birki.... “Excuse me please. Shin Ummi ina ruwa na ne? Me ya shalle ni cikin wannan al’amarin naki? A duk lokacin da za ki yi hira, ki yi wadda ta shafe ni ban da ta Fa’iz! Na tsani Fa’iz!! Na tsani duk wani abu da ya shafe shi ban da iyayen da suka haife shi da ‘yan uwansa wannan (Individualistic matter) ne (sha’anin mutum daya). A duniya bani da abin ki, abin tsana, abin neman tsari da kariya daga sharrin sa bayan shaidan, sai Fa’ezz Bamalli”.


****

Washe gari karfe goma na safe Queen Amina College ta yi mana, inda muka hadu da malamanmu da muka jima bamu gani ba. ALHAMDULILLAH, takarduna sunyi kyau har fiye da na Ummi, na tashi da Credentials a gaba dayan  ( 9 Subjects) dina. Ummi tana da seven credits, sai dai tana da A a Fine-Art.

A shekarar duka muka samu gurbi a jami’a, inda Yaya Aliyu ya samarwa Zanirah gurbi a jami’ar Lagos (UNILAG), inda za ta karanci likitanci (Medicine). Daga Baba na har mahaifin Ummi babu wanda bai yi mamaki da umarnin Hajjah ba na ta amince a nema mana gurbi a jami’ar Bayero ni da Ummi mu koma Kano da zama wajan Aunty Rabi, sai hutun karshen kowanne zango ta amince mu je Giwa da sauran garuruwan Zaria ko Kaduna.

Yaya Muftahu shi ya shiga ya fita ya samar mana gurbi a fannin da kowacce take so, inda aka bani B.A Arabic, Ummi kuwa B.A Hausa. Duka a Faculty daya wato (FAIS) sai dai tsangaya (Department) da suka bambanta.


BAYERO UNIVERSITY KANO

Rayuwar mu cikin jami’ar Bayero, sabuwar rayuwa ce a garemu da ta zo da sabon salo irin na kowanne JJC (Joiny Just Come) a jami’a. Abubuwa da yawa (which are normal) ga sauran daliban jami’ar (is abnormal to us), irin su shan hannu da maza da wasu matan marasa kamun kai ke yi da sunan jami’anci, shan taba sigari da samari da matasa ke yi wanda ba a yi sam a A.B Estate. Shan lemo a shago a tsaye ga matan aure da ‘yammata, ko saka wando ga wasu matan Hausawa duka abin kallo da waiwaye ne a gare mu kafin mu saba.

Mu kam bamu saba gani ba a inda muka taso, don haka muka shiga dari-dari. Sannu a hankali idonmu ya zo ya bude tangarau muka fahimci (reality) na rayuwar jami’a ba (peer group infuluence) bane (koyo abokan karatu ko tsararraki) kawai (imitation) ne wato (kwaikwayo) ‘to fit together’ (a zama iri daya).

Akwai wadanda karatu ne ya kawo su ba (imbibing) wato kwaikwayon abubuwan da canjin zamani ya kawo ba. Akwai kuma ‘yan ‘imitation’ din ko da a ce ransu bai so don kar a ce musu kauyawa. Irin wadannan su nake gani a matsayin kauyawa ba wadanda suka kalla a kauyawan ba. Su kuma ina kallon su ‘yan ra’ayin rikau. Irin wadannan mutanen a duk inda suka tsinci kansu basa canza ‘doctrines and principles’ dinsu kuma da wuya a rinjaye su daga kan abin da suka riga suka yarda da shi.

Yau bamu fito lacca da wuri ba sai wurin karfe biyu na rana, in ban da kururuwa ba abin da cikina ke yi, don ko karin kumallo ban dauka ba. Babu yadda Yaya Rabi ba ta yi dani ba don in zauna in karya amma na ki, saboda sanin halayyar Dr. Ramadhan Alkali, muddin ya riga ka shiga aji to ka rasa laccar sa kenan. Ni kuma ba zan so in rasa laccar ba, don a cikinta ne zai fadi (exam concentration area) din kwas dinsa.

Tafe nake a hanzarce don kokarin isa ga ‘coke village’ in samu abin da zai warware min hanji. Idanuwana sun rufe saboda yunwa ban kula da budurwar dake tsugune tana goge takalminta da ya yi kura da tishu don ganina ya dushe tsabar yunwar dake addabata, muka yi karon ba zato da budurwar saura kadan ta kifa.

Ta mike a hanzarce za ta yi bala’i. Wa zan gani? Haulatu Shehu, kawarmu (Head-Girl) a Queen Ameena, Haulatu S. Shehu. Na ce, “Haulatu Sani?”

Ta ce, “Fa’izah Ahmad?’

Na ce, “Ya Jamilal Munzar! (wato ya mafi kyawun masu gani)” A guje muka sheka muka rungume juna tare da juyi rikija-rikija muka rankaya coke village tare. Hirarraki da tambayoyi tamkar su kashe mu. Kamin wannan ta kai aya wannan ta antayo tata tambayar.

Ta ce, “Fa’izah kuna cikin garin Kano amma ko ki neme ni?”

Na ce, “Ayya Haulatu, ban san gidanku ba, kin ganni nan bayan unguwar su Aunty Rabi Gadon Kaya (Yarda Avenue) ban san ko ina ba, ban da kantuna da muke zuwa sayayya”.

Ta ce, “Ina address din da na baku tun muna makaranta da phone no?”

Na ce, “Mun baro su cikin littafinmu a Giwa”.

Daga nan hira ta barke. Ta ce, “Lallai ne Ubangijinmu ke nufin mu da zumunci tunda har ya sake hadamu a nan. Allah abin godiya. Ina Ummi?”

Na ce, “Ummi tana makarantar nan ita ma a Hausa Department”.

Ta ce, “Ni ina Mass-Communication, kai ni Haulatu na zo jami’a a sa’a tunda na kara haduwa daku. Tun rabuwarmu babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ban tuna ku ba”.

Na ce, “Duk kin canza Haulatu, kin yi kiba kin kara kyau da haske, ko kin yi aure ne?”

Ta ce, “Har da albarkarsa na like jikina. Matar Abdullahi Yakasai ce. An daura min aure bayan candynmu. Bikin ne dai ba ayi ba har yanzu Abdullahi ya tafi (Law School) sai ya kare nan da wata shida”.

Na ce, “Sunan kanina, Allah ya sanya alkhairi Haulatu. Sunan kanina mai bina kenan”.

Ta ce, “Kwarai, kin taba gaya min kina da kani Abdallah, yanzu ajinshi nawa?”

Na ce, “Abdallah ai an zama samari, yana SS I, Walida na JSS  2”.

Ta ce, “Me kike karanta?”

Na gaya mata harshen Larabci. Ta ce, “Kin burge ni Fa’izah, Allah ya kara fahimta, ya kara mana kaunar Manzo (S.A.W)”.

Kai hirar da muka kwarara ni da Haulatu a ranar tana da yawa. Duk tarihin mijinta Abdullahi wanda ya kasance dan’uwanta ne ta bangaren mahaifiyarta sai da ta gaya mini. Sai da muka yi (missing) lacca guda saboda dadin hira, dama Haulatu uwar surutu ce barin in sun hadu da Ummi. Haduwar Ummi da Haulatu sun kusa shidewa don murna.

Daga ranar amintarmu ta ci gaba da Haulatu daga inda muka tsaya a sakandire school. Naja’atu na ABU Zaria in ji ta. Duk inda ka ga Zarah ka ga wata wato ni, Ummi da Haulatu. Mun je gidansu a ‘Yankaba ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ita ma ta zo mana, har kwana take in lokacin jarabawa ne mu yi karatu tare, musamman da gidan Aunty Rabi ya fi kusa da makaranta. Ta saba da Aunty Rabi sosai.

Albarkacin Haulatu babu inda ba ma takawa a cikin Kano, daman an ce sai da dan gari a kan ci gari. Ummi ta yi manema har ba adadi, ni kuwa rashin sakin fuska da kora da hali wanda ya fi kora da sanda shi ya sanya duk wanda ya zo wajena da sunan so baya marmarin sake dawowa.

Ummi kan ce lokaci ne, lokacin abu ayi shi. Ni ba auren su zan yi ba kawai suna rage min lokaci. Sai in kama baki in yiwa Ummi kallon mamakin yadda jami’a ta sauya ta lokaci guda.

A haka muka kare 100 level bayan jarrabawar da ta kusa tsaga mini kwanya muka fara 200 level. Idon mu ya kara budewa sosai a sanadiyyar ratsawar ilimi da cudanya da masu shi. Hausar bakinmu ta dai-daita da ta ‘yan Kano, kai ka ce nan ce mahaifar mu.

Mu muna using N a muhallin R, wannan shi ke sa Haulatu da sauran abokanan karatunmu ke cewa muna Hausar Giwa. In Haulatu ta tashi tsokanata sai ta ce, “Kin tuna Ummi ranan nan a anguwan sarki? Ba za ku bar wannan maganan ba? Yaya Rabi kin ga Ummi na tsokanana ko????”


****

[6/3, 4:13 pm] Takori: ****

Karfe goma na safe su Ummi suka yi shirin tafiya taren su Bashir a filin jirgi. Tun asuba da na yi sallah fuskata babu walwala, kallon kowa kawai nake zuciyata a cunkushe da bakin ciki da bacin rai maras dalili.

Hajjah yau ko gaishe ta ban yi ba, babu wanda na yiwa magana. Na zubawa allon talabijin ido kuri kai ka ce program din nake saurara, amma ina! Zuciyata ba ta tare da gangar jikina, abubuwa masu ban al’ajabi da ban tsoro kawai take wassafa min masu shirin faruwa dani.

Kafin karfe goma na safe gidanmu ya cika ya batse da dan Adam, sai busa algaita ake ‘yan daurin aure suka fara layin shigowa gai da Hajjah suna fita, ‘yan’uwa ne da abokan arziki. Kafin Babanninmu su shigo sun sha ankon farar shadda (getzner) sai sheki suke.

Suka zube a falon Hajjah suka kwashi gaisuwa suka fita. Ina daga uwar daki ina hango ficewarsu ta taga daya bayan daya. Mintina talatin bayan fitarsu na ji gabana YA FADI! A dai-dai lokacin da dakikar agogo ya nuna karfe goma sha daya na rana, a lokacin ne aka daura aurarrakin masu ban mamaki, da suka ajiye kundin tarihi da wani aure bai aje ba cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa.

Wani maroki mai zakin muryar tsiya yake fadi da murya mai karsashi da kwarzantawa cikin babatun magana “ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!!” Sai da ya fada har sau uku. “An daura auren FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA da FA’IZU MUKHTAR ABUBAKAR GIWA. HADIZA da MUHAMMADU BASHIR, a kan sadaki lakadan ba ajalan ba. Allah yasa anyi a sa’a, yasa anyi sai bakin rai, Allah ya sanya alkhairi ameen.....”da sauran babatu irin na maroka.

Maimakon in kira yi sunan Allah sai na kwarara ihu da iyakacin muryata na zube a wajen a sume. Ban kara sanin me ke faruwa a duniyar ba.

                                   ***

Jirgin Boeng 708 ya sauka a filin jirgin saman Mal. Aminu Kano da misalin karfe daya na ranar da ta kasance Asabar, wato awanni biyu da daura auren. Jirgi ne da ya taso daga Ukrain zuwa Nigeria bayan shafe awanni masu yawa yana keta hazo, kafin ya wulwulo kasa ya tsaya a cyprus ya sha mai sannan ya keto kasarmu mai dimbin albarka.

Sai da passengers kaf suka gama fita kafin Pilots din su fito cikin fararen uniform dinsu. Shine na karshe a saukowa. Fari sol! Mai madaidaicin jiki, zai fi kyau ka ce ba shi da kauri sai fadin kirji wanda da ka kalla za ka san gym ya samar da shi. Ma’abocin wasu ilhamomi da nasibobi da dama da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.

Ya saya fararen idanunshi cikin gilashi mai duhu ainun samfurin ‘KAREN MILLEN. Sajen da ya zagaye gefe da gefen fuskarsa baki sidik kwantacce wanda a da baya da shi bai boye tsagin mallacinsa ba. Sai ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa ya fiddo cikakken Bamallen sa, kuma Bafillace. Dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ya dama, ya kutsa cikin ilmummukan zamani daban-daban.

Dogon hanci gare shi kamar ruler aka sa aka ja shi aka daidaita shi a tsakanin idanunsa. Idanunsa dara-dara wadanda suka dan shige loko kadan farare tar masu sheki da maiko (oily eyes) wadanda duk cikin zuri’arsu maza da mata shi kadai aka ya yiwa wannan ilhamar. Idan lissafin da yake yi dai-dai ne yau shekarunsa takwas da barin gida ba tare da ya sake ko da waiwayarta da sunan hutu ba.

A zubin halitta da kirar jiki ya fi kama da Ahmadu A.B, a halayya kacokan Abubakar Giwa ya kwaso ba wani cikin zuriyarsa ba.

Don haka, ka ce ga hakikanin halayyar FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA, abu ne mai matukar wuya. Za ka san halinsa ne kadai idan ka zauna da shi, zaman ba na kwanaki ko watanni ba, sai dai shekaru.

Shekarun ma sai idan kwana kake tare da shi daki daya ka kuma tashi tare da shi, halin da ake kira halin MAZAN JIYA ba na YAU ba, and difficult to be studied by sociologists and psychologists. Idan aka ce su karanci irin pilot Fa’iz za su yi placing dinsa ne kawai (upon hypothesis) but not a dependent variable.

Daga fitowar shi daga jirgi har shigewar shi wani ofishi (pilots changing room) idanun Khadija-Ummi na kansa, tana mai yiwa Allah tasbihi da godiya mara iyaka da wannan miji da Allah ya ba ta wanda ke ninkaya cikin zuciya da mafarkinta, ba ta taba tsammanin akwai ranar zahirantar mafarkin nata ba. A hankali ta ji danshi a kan fuskarta, wanda ba ta ko tantama hawayen farin ciki ne.

Har zuwa lokacin da ya gama shige da ficensa a (airport) din tare da abokan aikinsa, ya canza kaya zuwa kaftan na farar lallausar shadda (Hilton) da ruwan kasar hula a kansa, takalmin fata dake kafarshi shima ruwan kasar ne. Ya janyo trolley dinsa zuwa inda ya hango fuskokin masu kama da tasa fuskar, wanda komai daren dadewa suna gilmawa cikin idanunsa, wato fuskar zuri’ar Abubakar Bamalli, wanda ya fi so da gani shi ya fara ganin, wato Aliyu Na’ibi.

Da sassarfa Aliyu ya karaso suka rungume juna shi da Fa’iz, rayuwarsu ta baya ta dinga dawo masa tar-tar kamar a majigi. Abubuwa da yawa ba zai manta dasu ba. Cikin taron nan kaf na mata da mazan Bamalli, manya da yara, wadanda ya sani da wadanda bai sani ba, musamman kananan yara, ya hanga ya duba bai ga Zahrar cikin taurarin ba.

Ya ga Zanirah, ya ga Ummi, Mus’ab, Junior Yahya, Shu’aib, Walida, Abdallah da wata karamar yarinya mai tsananin kama da Fa’izah (Khausar), da sauran kannensa ‘ya’yan Baba Barau, Sadi, Salisu, Sani da Na’ibi.

Mutum daya ce kawai babu, wato KANWAR kuma abokiyar fadan da a yau ta juye ta rikide zuwa matarsa ta sunnah.

Ko da wacce irin fuska za ta karbi al’amarin? Ko da wace irin fassara za ta fassara shi? Ko da wanne irin hannu za ta karbe shi? Abin da ya sani ya kuma kwana da da sani ne cewa, Fa’izah! Ba ta da makiyi a duniya irin sa!!!

To amma ai shi sonta yake yi tun can din ma. Har kuma gobe son ninkuwa yake yi irin kaunar da bai taba yiwa kowa a duniya ba, in ka dauke Mama da Baban Kaduna wato iyayensa. This is his own style of love!

To amma da wane language (yaren) zai yiwa Fa’izah bayanin hakan har ta yarda ta fahimce shi, ta karbe shi a matsayin miji a gareta? Ya kuma wanke wancan dattin da ya dade yana yabawa kansa a idanunta?

Don haka kallo daya za ka yiwa pilot  Fa’eez ka karanto matsananciyar damuwa cikin fararen kwayar idanunsa. Duk da yaken da yake yiwa Aliyu da sauran ‘yan’uwansa.

Yasa hannu ya karbi little Fa’izah hannun Zanirah ya dora a kafadunsa yana murmushi, kallo daya ya yiwa Ummi ya bude baki yana mamaki, ganin yadda kibarta ta zaizaye gaba daya, abin da babu wanda ya taba tsammani.

Shi da ita murmushi suka yiwa juna, wanda ga Pilot Fa’iz murmushin ‘yan’uwantaka ne. Kuma ba annuri a fuskarsa har suka shisshiga motocinsu, yana motar Aliyu ne, Aliyun na tuki shi yana gidan gaba, Ummi da Zanirah da ‘yarta a baya.

Sai dai tunda suka hau titin Zaria Road dodar wanda zai sada su da garin Zaria, kowa ya fahimci Pilot Fa’iz Bamalli cikin matsananciyar damuwa yake. Ya sanya fuskarsa cikin tafukansa Allah kadai ya san me yake tunani a zuciyarsa.

Ummi ta yi tagumi a kujerar owner side da take zane. Wane irin mutum Fa’iz ya koma? Wane irin ango ne wannan babu wani alamar kulawa ko kwayar murmushi ga amaryarshi da aka daura musu aure yanzu-yanzun nan? Wane irin mutum ne shi da zai bar kasar haihuwarshi shekaru har shida da wani abu ya dawo babu alamun farin ciki a fuskarshi? Me ke damun shi? Anya Fa’iz na farin ciki da dawowar sa cikin ‘yan’uwansa? Anya Fa’iz lafiyarshi kalau? Anya Fa’iz na murna da auren su kamar yadda take tsammani?

Ta jerowa kanta duka wadannan tambayoyin lokaci guda, ba ta da amsar ko daya, don haka ta sunne kanta cikin cinyoyinta ta soma kuka a hankali.

Daga Aliyu, Zanirah da sauran kannensu dake cikin motar zuwa uban gayyar, babu wanda ya tambayi Ummi dalilin kukanta. Ga Aliyu shi kam abin ne ya zo mishi wani irin banbarakwai cikin sarkakiya. Bai san irin bayanin da zai ma kowannensu ba. Babbar fargabarshi yadda Fa’izah za ta karbi zancen aurenta da Fa’iz.

A karo na farko ya ji haushin kansa kan munafuntarta da ya yi jiya, don me bai gaya mata gaskiya ba? Don me ya rufe mata? In kowa ya rufe mata shi bai dace da hakan ba.

Ita kuma Ummi tunaninta da Fa’iz aka daura mata aure amma ganin halin ko in kula da ya nuna mata ya sanyata kuka. Shin da wane yare zai yi mata bayanin cewa da Bashir ne? Ya ya Ummi za ta tallafi maganar bayan yana da masaniyar cewar ta tsani halayyar Basheer fiye da kowa? Ta ya ya nitsattsiyar yarinya ‘yar kauyen Giwa ta cancanci tantirin dan duniya irin Yaya Basheer?

Kaico da tunanin Hajjah! Kaico da bahagon tunanin iyayensu wurin hada irin wannan rikitacciyar auratayyar zumunci ko bata zumunci? Su kam sun haye! Yanzu na ‘yan bayansu yake ji.

A zuciyar Zanirah cewa take yi, “Ina ma ban zo garin ba kwata-kwata balle in ga wannan rikitacciyar rana......!”

A dai-dai lokacin da Aliyu ya karya kan motar cikin tafkeken (gate) din ABUBAKAR BAMALLI HOUSE.....”


****


WANE NE NAZIRU GALADANCHI?

Major General Sani Galadanchi shine mahaifin Dr. Nazir. Da na farko wurin iyayenshi, kamin haihuwar shi sun kwashe shekaru masu tsaho basu samu haihuwa ba. Da Allah ya kawo Naziru sai hakan ya zamo musabbabin nuna mishi tsantsar gata wanda babu kwaba ko tsawatarwa a cikin sa.

Nazir ya tashi yaro dan hutu tun yana sakandire, sune samarin da ake kira ‘yan (high life) a lokacinsu. Haka nan bayan haihuwar Nazir sai da suka kwashe shekaru takwas zuwa tara kafin su samu haihuwar Haulatu. Daga Haulatu yara ne maza uku daya na bin daya duk bayan shekaru uku.

Duk da jin dadi da sakewar da Nazir ke samu bai sa shi yin wasa da karatu ba, domin ya ga amfanin ilimin wurin mahaifinshi. Ya so ya tafi soja don ya gaji ubansa amma Baban ya dage kan harshen Larabci yake son ya karanta, baya son shi da aikin soja, babu kwanciyar hankali a cikinsa.

Su shan sigari wannan duk a wurin Larabawa ya koya, sai dai sam in ya zo hutu baya sha a gida sai ya koma. Bai fara neman mata ba sai da ya kammala degree ya fara masters a zuwan shi bautar kasa garin Lagos, inda ya yi wani aboki Tim ya koyar da shi mu’amala da mata, don haka da ya koma Taiwan sai idonshi ya bude da hakan.

A can ya kammala PHD ya dawo Kano ya fara aikin da yake yi a Bayero. Rasuwar Tim ta hanyar muguwar cutar (SIDA) Aids bai sanya Nazir Sani kintsuwa ba sai haduwar shi da Fa’izah A.A Giwa.

Bai taba neman kowacce diya mace da niyar aure ba sai a kan Fa’iza, kamar yadda bai taba son wata diya mace tsakani da Allah ba baya ga Fa’izah. Bai taba tunanin zai bar yaudarar mata ba sai a kan Fa’izah. Daga ranar da ya dora ido a kanta, bai kara kula wata yarinya da sunan iskanci ko yaudara ba, domin yana ganin kintsattsiyar yarinya kamar Fa’izah ba ta dace da watsattsen miji kamar shi ba.

Don haka ya kimtsa kansa, tun hakan bai zamo dalilin da za a hanashi Fa’izah ba. Tunda ya tabbatarwa kansa aurenta zai yi domin Allah da soyayya.

Ya yarda ya amince da duk zargin da ake masa na cewa shi din dan iska ne, ya yarda ya kuma amince bai taba musantawa ba, kamar yadda bai taba cewa yana da wani hali na kirki ba. To amma wanda duk yake tarayya ta jiki da Naziru Sani, zai yi shaidar cewa mutum ne wanda baya wasa da sallah, kuma zuciyarsa daya ce da ita yake zaune da kowa, sannan ba shi da tsoro. Baya tsoron uban kowa, sannan abin hannunshi bai rufe mishi ido ba sam.

Daga ranar da suka yi magana da Abdullahin Haulatu, ranar ba ta zagayo ba sai da Dr. Nazir ya gabatar da maganar Fa’izah ga iyayenshi, ya kuma roke su da aje mishi neman auren ta sati mai kamawa.

Hajiyar su Haulatu ta yi matukar farin ciki da Allah ya  nuna mata ranar da Nazir ya kawo mata zancen aure da bakinsa da ranta kafin mutuwar ta. ‘Yammata iri-iri ta sha nemawa Naziru yana fitittikewa, shi aure ba yanzu ba sai ya ci lokacinsa matarshi ma  ba a haife ta ba.

Da farin cikinta da rawar jikinta ta isar da sakon Nazir ga General, shima ya yi farin ciki sosai, suka yi ta yiwa Allah godiya. Tabbas addu’ar iyaye ba ta faduwa kasa banza a kan ‘ya’yansu, ko ba jima ko ba dade. 

A washegari ya tura kanin mahaifinsa da kanensa biyu da wan Hajiyarsu wurin iyayen Fa’izah. Haulatu ce ta ce dasu Kaduna za su wurin Alh. Muntari don shine madaurin auren su, ta karbi address wurin Aunty Rabi.

Tarba ta girma da mutunci Mama ta yiwa iyayen Nazir ita da Baban Kaduna da suka ce daga Kano suke neman auren Fa’iza wa dansu Naziru, malami a inda Fa’izar take karatu. Sai mama ta kalli Baban Kaduna shima ya kalle ta aka rasa mai yin magana.

Tun daga nan jikin dattijan ya fara sanyi. Da kyar Baban Kaduna ya ce, “Na yi mamaki da kuka zo neman aure ba tare da kun yi bincike a kan gidan su yarinyar ba. Ban da haka duk wanda ya san zuri’ar Abubakar Giwa, ya san basa auren bare. Ban fadi haka don yaron wajena ne mijin Fa’izah ba, sai don cewa ka’idar gidanmu kenan da muke bi tun iyaye da kakanni. Ina mai bai ma Naziru hakuri, ya yi hakuri, ya yi hakuri Fa’izah TA YI AURE!!!”

Da wannan bakin labari Hajiyar Dr. N ta tare shi a dawowarsa daga wajen aiki. Labarin da ya yi masa bugun da wani labari bai taba yi masa ba. Ya dauki mukullin motarshi ya nufi kofa Hajiyarsa na kira, bai juyo ba yake fadin “Barni in je Hajiya, Giwan za ni in tambayi Fa’izah dalilin da yasa ni ban yaudareta ba ita ta yaudare ni...... ta san auren gida ake musu amma ta yi min haka.... me na yiwa Fa’izah da za ta zabi ta yi min wannan yankan kaunar ta yi dai-dai da zuciya da farin ciki na?”

Gudun da yake shararawa a kan titin da zai kai shi garin Giwa ya fi kama da na ‘yan sumogal. Zagin duniya ya sha shi daga motocin gaban shi da bayanshi. A dai-dai kwanar da zai karya ya shiga Giwa suka yi arangama da motar shanu ta bi ta kan motarsa ta murkusheta irin murjewar da sai wani babban ikon Allah za a fidda mai rai a cikinta.


****


GIWA

Ban motsa daga inda nake ba, tun daga lokacin da na fadi na suma. Karar da na yi ya janyo hankalin Hajjah da sauran mazan dake zarya a tsakar gidan. A guje Hajjah ta shigo har tana tuntube da kofar daki tare da su Baba Barau da suka shigo a lokacin da ‘yan kanzaginta su Inna Kubra.

Hajjah ta tsugunna da hannuwanta biyu ta girgiza ni tana kirana “Fa’izah...... Fa’izah!!” Baban Giwa (Barau) shi ya fita ya zo da ruwa a kofi ya shiga yayyafa min amma ban motsa ba, ga idanuna a bude ina kallon su tarrr!

Hajjah ta shafi fuskata zuwa idanuna shima ban motsa ba, ta kama hannuna ta ji shi sanyi kalau, jijiyar ta saki. Ta dubi fuskata babu alamun rai a tare dani sai ta rushe da kuka.

Inna Kubra ta soma karanto addu’a tana tofa min a fuska. Ya yin da Baban Giwa ke tofawa cikin kofi, ya kammala ya shara mini duka a kaina, sai na kwanto sharaf jikin Hajjah kamar matacciya. Ko dan yatsana na kasa dagawa, babu wata gaba dake motsi a jikina. Wannan ya tabbatar musu da cewa dogon suma na yi, irin wanda shock ke sanyawa, mai wuyar farfadowa.

Hajjah ta rungume ni tana kuka ta ce, “Na shiga uku ni Hadiza, me ya yi zafi Fa’izah? Muddin kika mike Hafizi na isowa za a warware auren nan, ba zai yiwu garin neman gira a rasa ido ba. Wayyo ni Hadiza, wallahi na manta shaf da kiyayyar Fa’izah da Fa’izu da ba a yi auren nan ba”.

Baban Giwa ya zauna gefe ya zuba min ido duk sunyi tsuru-tsuru, ya ce, “Uhm! Ai na fada Hajjah babu wanda ya saurare ni, yanzu in ta mace ai shi kenan hankalinki ya kwanta. Tun lokacin na Aliyu na gaya miki kada a kara aurarrakin nan kin ki ji. Yanzu ai an dau darasi ko?”

Baban ABU wato mahaifina ya daga labule ya shigo yana cewa, “Zancen banza kake Barau, ba suma ba, ko mutuwa Fa’izah ta yi babu mai karya dokar Abubakar Giwa ko bayan ran Hajjah, mu zamu tsaya a kan wannan principle har karshen rayuwarmu. Tashi ka fita ka baiwa mutane wuri sakarai matsoraci girman wofi tun ranka bai baci ba wallahi”.

Baba Barau ya kwantar da murya ya ce, “Nima ban ki hakan ba, amma a dinga duba soyayya tsakanin yaran nan kafin a kara kulla kowanne aure tsakaninsu. Fa’izah da Fa’izu basa ga amciji tun tali-tali har zuwa girmansu. Baban ABU rai! Yana gaba da komai, sai da shi ake komai”.

Fa’izun ne ya bankado labulen dakin ya shigo a sukwane kamar an jefo shi tare da Yaya Aliyu, don tun fitowarsu mota Khalid yaron Baban Giwa ya ce dasu wai Fa’izah ta yi kara ta mutu!

Bai iya ya ce komai ba duk da ya ji kadan daga abin da suke tattaunawa, illa bin Fa’izar da ke yashe a kasa mushe ko mai rai da kallo. Manyan fararen idanuwanshi gaba daya sun fito waje sun yi jawur, har wani brown-brown suka koma. Jikinsa sai mazari yake bakinshi na motsi, amma ya kasa magana.

Aliyu ya ce “Shin Baba me kuke yi haka dukkanku tun dazu da aka rasa mai kaita asibiti? Fa’izah ba mutuwa ta yi ba!”

Sai ya sunkuya ya ciccibe ta gaba daya, Fa’iz ya hade girar sama da na kasa ya ce, “Ko da ban karanta ba na san maganin wannan suman...”

Da sauri Yaya Aliyu ya dire ni gefen gado ya yi baya, ya ce, “To likita mai mata Bismillah”

Ya yi waje abinshi. A ranshi kam dariya ma abin ya ba shi yana ta yin ta ciki-ciki, wai matar dake tsakanin rai da ajali ake ma kishi? Bai san gara ta dauwama a suman ba da ta farfado ta ganshi. Ya karbi diyarshi da ke ta tsala ihu hannun  Ummi a falo ya yi waje.

A hankali su Baban ma suka shiga ficewa daya bayan daya ba tare da kowannensu ya sake tofawa ba.

Hajjah ta share hawaye ta ce, “Yanzu Hafizi ya za ayi Fa’izan ta farfado?’ Fa’iz cikin jin haushinsu duka ya ce, “Ban sani ba Hajjah”. Ita ma a fusace ta ce, “Amma ka hana a kaita asibitin?”

Ya fiddo ido ya ce, “Hajjah bakya gani  daukarta ya yi ne?”

Hajja ta hasala ta ce, “Zancen banza zancen wofi, yau ga sakaran kawai. Sannu mai mata, hala gawa za ka aura? To in gaya maka gaskiya auren nan kunce shi za ayi ba zai zama sanadiyyar rasa ran Fa’izah ba. Da na san haka abin zai zama tun farko da ban saurare ka ba.....”

0 Response to "ZUMUNTAR KENAN Hausa novel"

Post a Comment