'YAR KWALLIYA Hausa Novel
WRITING BY HIS ECCELLENCIY NOVELS GROUP..
'YAR KWALLIYA Hausa Novel
Page 1-5
March 07, 2018
'YAR KWALLIYA ..
Bismillahirrahmanir
Rahim
.
Wannan kirki raren labarine
nayi shi dan fada karwa da
nisha dan tarwa ban yishi dan
wani ko wata ba Written by Jabeer..
.
Wata yarin yace 'yar shekara
15 kafa fururu komai babu
fuska kuma tasha Jan baki da
hoda harda gazal ta fallo da
gudu kanta daukeda tulo
tadebo ruwa a guje ta fada
gida Tana shiga ta saki tulun
yafadi ya fashe Nidai gaskiya
bazan yar daba hikenan ni
banda kata bus hine fa ya bini
har inda zan debo ruwafa
inna yana cemin *YAR*
*KWALLIYA* kafa ba mai
fuska tasha ado hine
nakamahi da danbe na fasa
mihi baki hine dan bahida
kunya ya biyoni gida Yasin
bazan yarda ba inna kalli
yanda bakina yake zubar jini
inna Abu muguwace wlh Kayi
hakuri kaji kaima da naka ina
ruwanka da tsokanar ta kuma
kasani sarai bazata barkaba
Au abinda zaki ce kenan to
shi kenan zan turo me rama
min Kayi hakuri mana kai
baka jin hakurine Ina
kotsayawa beyiba yatafi Inna
ki barhi ki barhi nace kaje ka
kawo bindiga karhe kenan
Yanzu Abu Wannan rayuwar
kika zaba to shikenan
zandena tsare miki wlh tinda
ke bakida hakuri yanzu
Wannan gabjejen kato kika
kama da fada Inna hinefa ya
nemi tso kanata fa Yanzu
ruwan da kika debo ma gashi
kin fasa tulon kaini inna ina
zansa kaina Inna Wannan fa
laifin tulun kine ina ruwanhi
dani nan naso na ajiye hi hine
ya fadi ya fahe sai hakuri
Kamarya sai hakuri Abu girkifa
zan Dora yanzu ya kikiso ayi
To ni kome ma za ayi ayi
tuludai yafahe nikuma na gaji
bazan iya komawaba
.
Kin isa komawa kamar kinyi
kin gama ga wani tulun can
jeki dauka kidebo wani
ruwan Kai inna kinemo wani
ya debo kinga janbaki da
hudana ya kare sonake na
zagaya baya na siyo I dan har
baki debo ruwan nan ba ba
inda zaki Abu kin jini da kyau
hikenan zan debo Abu ta
dauki tulun tatafi Rake
yauwa bari naga maya finda
ke daure a kugunta ta kwance
ta Ciro Hamsin ta mika wa me
rake Yabata rake da canji
tana tafe tana sha harta
karasa rafi Yauwa wana
kama wato jiya kika watsa
min kasa kika gudu ko yanzu
wana kama cewar Abu Ke
Abu kinga diban ruwa aka
turoni ba fada ba matsa na
wuce cewar binta Ke binta
me kike nufi ni wasa aka
turoni kenan bari kiga wasa
cewar Abu Hannu tasa ta
ture tulun dake kan binta
yafadi kasa yafashe Yauwa
kinga wasa nan nafasa banza
ko kinada abinyi ne Kaiiii ni
kika fasawa tulu wallahi kinyi
karya saina rama Abu kome
kike takama dashi kin tara kin
samu ni binta saina gyara
miki zama Binta na gama
fada tasa kafa ta daki tulun
Abu yafashe Nanfa Abu ta
daka tsalle ta dire ta kamo
wuyan Binta suka kama fada
da kyar aka rabasu Aina fada
miki Abu ni Binta nice dai dai
ke saina gyara miki zama
Tohi kenan idan baki gyara
min zamaba nizan gyara miki
kuma saikin biyani tuluna
kona daka ki a gurin nan
wlh Allah ko Abu bazan biya
ba kiyi abinda kika gadama
koda me kika zo ni Binta na
fiki haka kikace ko to
hikenan Kallon ta Abu take
tana gyada kai da buga kafa
Banga wanda ze fi karfinaba
ni Abu wai saiwata banza
bazara iskar damuna binta
wlh kintarowa kanki aradu da
ka Hannun ta Abu ta kama
ta sakar mata cizo dagudu
tabar wajan Binta tabi
bayanta da gudu haka suka
yanka cikin unguwa dagudu
harzuwa gidansu Abu Abu ta
boye a bayan inna Inna ki
matsa Wannan fadan ba naki
bane kimiko min Abu na nuna
mata abinda binta zata iya ni
kika ciza dai ko cewar Binta
Yar gidan marasa tsoro
mekikeyi a bayana aina fada
miki ni nadena bada hakuri
kinga Binta gata nan zoki
mata abinda kike so cewar
inna Gadan gadan Binta
tataho Kinga Binta tsaya Abu
ina ruwan dana aikeki kidebo
cewar inna Inna asara kika
aika dankuwa ni Binta nice
nan na fasa tulun *'YAR
KWALLIYA* tafasa min nawa
shine nima na rama wata
tsiyarce cewar Binta Ahh
babu bakomai kinyi daidai
yanzudai kiyi hakuri Binta
kibari idan tafito kuyita takare
mutuwama tana tsoron idon
ma haifi cewar inna Inna
kenan kince haka ko to ina
waje ba inda zanje kekuma
Abu zaki fito kisameni hoda
bawanka kidinga Wanka idan
zakiyi kwalliya Binta tajuya ta
fita Inna ki matsa kibar ni da
ita kina jin metake cemin
Karya tayi Abu gaskiya tafada
yau kwananki nawa rabonki da
kwanka Inna batun wankan
nan kibarhi aikyan kwalliya
kayihi batateda wankaba
gawani kamhin turare na
musamman dayake tahi a
jikina gahi turaren babu a
kasuwa me yafi raina shine
zan tsaya inta batawa kaina
lokaci wajan yin kwanka Dalla
rufemin baki kazamar banza
kazamar hufi ina kyau Anan
*HODA BA WANKA* Baki
tabude ta gir_giza kai ta
dunkule hannu inna harda ke
yasin duk wanda yasake ce
min hoda ba wanka na dena
raga mihi yasin cewar Abu
Yanzu da kika dunkule hannu
damben zakiyi dani nima
cewar inna Jifa tayi da
takalmin kafarta ta debo
kayan Kwalliya ta zube a
gabanta tadauki Wannan
tashafa ta ajiye takalli kanta a
madubi tayi dariya
.
Inna jiya da naje dan dali aka
dinga tambaya waye yafesa
turare nayi shiru tsabar kanhin
turaren jikina hanci suka
toshe Niko kayan nan ma
bacanzasu zanyi ba Wanka
kuwa nadena Kaza kankida
motsi afakaice suka zageki
baki saniba ba abinda kikeyi
sai bugawa kitemaka ki ajiye
kayan kwalliya kiyi Wanka
kekanki zakiji dadi Tab tab
aaah waii saidai wata Abun
badai niba wanka nida hi
munyi hannun Riga inna kifara
sabon lissafi daga nan
harranar sallah nida Wanka
Haka kikace to Allah
yashigoda yayanki da malam
su insun isa dake Sa saki kiyi
tinda ni kin rainani dan Allah ji
yanda kika cika mana gida da
tsami cewar inna Kinji ko
inna kinji irin kamhin turarena
ko hakama wani saurayi yajiyo
kamhin yace yana sona nace
bana son hi ni fako inna har
bana son fita dik inda nabi
ansan nice saboda turturarena
cewar Abu Waiyoo waiyoo
tasa kafa tayi koli da kayan
kwalliya inna ban fada
mikiba yau ake cin kasuwar
gangare natafi Tayi fice
warta Badan Allah yasa akwai
sauran ruwa agidan nan ba da
Abu ta gama dani cewar Inna
Tafiya take a hankali tana
tafiya tana yanga acewarta tafi
kowa haduwa ga turaren
jikinta yafi na kowa kanshi
tana tafe tana cin gyada
hannun takuma rikeda sandar
rake ga wuwar danmara tasha
a kugunta binda na labe tana
kallon ta Abu nakara sowa
inda Binta take Binta tariketa
Wana kama yasin saina
dagargaza bakinki zan kyaleki
yanzu ina inna take balle
kibuye a bayanta cewar Binta
Yasin Binta kanki baya aiki
kalli yanda kika rike min Riga
a gaban mutane gasamari a
gefe kalan ki zubarmin da
mutunci a idonsu haba kidena
abinda kuda zebiki Karsan
kuda nice mangoro kobakijiba
cewar Binta Janyota tayi
zata daka bashiri ta saketa
tatoshe hanci Abu
dagaskene abinda ake fada
kenan Wannan warin daga ina
lallai kinci sunan ki huda ba
Wanka sammin raken mana
Abu taraba shi2 ta bata
Yauwa nagode gyadar fa
Tadiba tace Gahi kibarni zaki
rakani cewar Abu Eh ni yanzu
kawarkice gaskiya kinada
hankali Abu Dariya tayi tace
ko nasani suna tafe suna
shirme harsuka siyo suka
dawo
.
Atare suka shiga gidan Inna
na ganinsu ta fara salati Abu
mekika kuma yiwa Binta
cewar inna Inna ai yanzu
Binta tazama kawata cewar
Abu Ina baze yiyuba ban
yardaba wlh dama ya kike
bare ankaraki da binta waye
besan bintaba cewar inna
Kinga Binta jeki gida zanzo na
same ki cewar Abu To inna
sai anjima cewar Binta
Sallama Alaikum inna ina
wuni Lpy kalau Nura sannu
dazuwa kaga Abu tayi
sabuwar kawa mara aji irinta
Ke Abu yatoshe hanci inna
meya yake bugawa haka
cewar Nura Wacce inbanda
*'YAR KWALLIYA* Fari Abu
tayi da ido tareda
juyawa New writer's
Taku husba'ahfama
.
Yaya Nura a hekaima kaji
kanhin tiraren nawa Dalla
kanshi ko wari kazama kawai
dubi yanda gidan nan yadauki
warin jikin ki Wari karyama
kenan Yasin kanhi kaji cewar
Abu Yau sai kinyi Wanka
bazan iya zama dake kina
wariba wlh inna bani ruwan
nan na kusa dake cewar
Nura Banga abinda zesa nayi
wanka ba Yasin kalan kanhin
turarena ya tafi Nura ya
dauki ruwan yasa a bandaki
yakai mata soso da sabulo ya
karyo bulala yarike Shiga kiyi
wanka Yaya Nura ina ganin
gir manka fa cewar Abu
Yadaga bulala bashiri ta fada
bandaki tayi zamanta Kayi ka
gaji yaya ba wankan da zanyi
cewar Abu Tana tawasa da
ruwan kamar tana wanka
tawanke fuska da kafa da
hannu Kate makeni ina
fitowa zan cika fukata da
KWALLIYA na raka Binta tallar
gurjiya hahhh Tabude ta fito
ta harareshi tashige daki tayi
KWALLIYA ta tafi gidansu
Binta taje tasamu Binta ta fito
tallar gurjiya A hanyarsu na
tafiya Abu tayi ido4 dawata
taci ado da KWALLIYA tayi
kyau sosai harta bace Abu na
kallon ta Ke mekike kallo
cewar Binta Kinga yanda tayi
kyau tafi yanta kayanta komai
yayi Nanfa Abu tashiga yin
irin tafiyar Kibar Wannan abin
Abu kinsan daga ina take
cewar Binta A'a cewar Abu
Daga birni take haka suke
tasu KWALLIYAR dasa kaya ba
irin nakiba HODA BA WANKA
.
Yasin yanzun nan bakinki
zeyi jini Binta nizaki cewa
haka nifazanyi fada da duk
wanda ya kirani da Wannan
sunan kowaye hi cewar Abu
Maida wukar nataba zuwa
birni sau1 yanada kyau ginin
su ba irin namuba kinga baze
yu nabaki lbr ba saikin gani da
idon ki cewar Binta Kai nima
inaso naje zaki kaini dan Allah
cewar Abu Inna inna ce
matsala Abu damunje yasin
cewar Binta Kinga bawata
matsala ki kaini kawai inzaki
kaini ya kika ganni zanyi kyau
a birni ko cewar Abu Ehhh to
ban saniba saikinje tukunna
saboda gaskiya tsoro zaki
basu kalle kifa tab cewar
Binta Waike hikenan bakida
magana sai kice na kalli kaina
me zan gani kodai ciki baki
kike min ne cewar Abu Ko
daya KWALLIYAR takice abin
tsoro ga kafarki Fari fat
gaskiya bazan kaikiba saikin
waye cewar Binta Abinda
Binta tafada yabatawa Abu rai
yasa tayi gaba ta barta a
baya
.
Wani yarone yazo siyan
gurjiya gun binta Binta zuba
min gurjiya Karki zuba mai
cewar Abu Tinda na ganka
nadawo mekace min jiyama
Meka ce mata Eh cewar
Binta Shiru yayi yakasa cewa
komai saida ya gano
yayanshi yace ' *YAR
KWALLIYA* nace Ohh me
dadtin dankwali itace *'YAR
KWALLIYA* cewar Binta
Barshi dani yanzu nanuna
masa kalata Yasin harni zaka
tsokana ka gudu anhi kudin
nahi Binta cewar Abu Binta ta
ansa tace kuma bazan siyar
maka da gurjiyan ba na
karfine Gaya mihi binta waihi
Wannan dame yake dakama
ne naga saiwani jijjidakai
yakeyi cewar Abu Kasa ta
diba ta watsamai a ido Binta
tasamai kafa ya fadi suka
rufeshida duka abin mamaki
kato a kasa mata na duka
abinda mutane ke cewa
kenan Yayan shina kara sowa
ya daka musu tsawa Suka
bar dukanshi suna Harar shi
Lpy kaikuma meya kawo ka
kasan muko suwaye cewar
Abu Suwaye Ku inbanda
kucakai marasa hankali dalla
dubeki kafa furu furu komai
be ganiba dubi kayan jikinki
fuska saikace Aljana waike
kinyi KWALLIYA Ap abanza
yafi na tsohuwa kaga ka
gaggauta barin gurin nan inba
hakaba kuma hmmm cewar
Binta Karkusake suce zaku
yimin haukan da kuka saba
danni bazan daukaba wlh Ko
Binta mu gwadamai aiki dan
nakula saimun koya mishi
hankali cewar Abu Waige
Binta tafara can ta gano dutsa
tace haryanzu bakinka be
mutuba ko tsaya ka gani
Dutsen ta dauko da buga
mishi a kai Banza a banza
cewar Abu Jini ya fara zuba
a kanshi Abu da Binta suka
zuba a guje suka wuce
gidansu Binta Umma ga
gurjiyar ki yau an hana talla
inji me gari cewar Binta Ke
Binta waya fada miki cewar
umma Umma Nifa ganauce
ba jiyauba Gashi can ya baza
yan *DOKA* A gari cewar
Abu Kunga bana son shegan
taka waca tsiyar kuma kukayi
na sanku da kyau cewar
umma Wani ne ya nemi tso
kanar mu hine muka fasa mai
kai cewar Binta Eh banjiba
naji kamar kince fasa kai
Allah na gode maka daka bani
Binta nidai shikenan bakina
baze zauna shiru ba saboda
inada Binta cewar umma
Kofar gidan su Binta aka siga
duka da karfi Kufito mana
dasu ko mushigo yara sun
gagari kowa wlh yau zamu
sharewa kowa hawaye kufito
dasu cewar mutanan da suka
zo Kuna jiko yara kunzama
dan kuka mejawa uwarsa jifa
Umma kinga jeki kiji dame
suka zo idan da sulhune
kusulhunta idan kuma akasin
hakane kikira womu katkenan
cewar Abu Kushiga ciki bari
naji dasu
.
Wai baza a fito dasu bane Eh
mumafa yan zama nine kofar
suka bude suna kokarin
shiga Haba dan samari gidan
matan aure ne fa Nasani ina
'ya'yan Allah banin nan suke
Binta da Abu Basa nan sun
fita Karyama kenan ina ganin
su suka shiga gidan nan dan
haka ki fito dasu kawai mu
baza mu hakuraba dan
uwanmu suka fasawa kai
gashinan sai zubar jini yakeyi
yanzu haka yana Asibiti Allah
yabaku hakuri kuje idan sun
dawo nida kaina zan kawo
muku su cewar umma Eh to
na yarda dake saidai be
kamata mu tafi haka ba bari
mu bar miki sheda idan sunzo
ki nuna musu Yadaga gora
ze sauke mata dagudu tabar
gurin ta shige gida tarufo
kofa Yauni umma naga ikon
Allah ina kuke Umma sun
bar miki sheda banzaye
sokaye sun yarda ba ma nan
gamunan muna jinsu kuma
cewar Binta da Abu Au kujin
dadin kune a bar min sheda
saboda kun amsa sunan Ku
Binta da Abu ko Allah yate
makeku suna nan suna jiranku
kuna fita sai abinda hali ya
yiwu cewar mama Basu isaba
yanzuma ba barinsu zamuyiba
narike muryar su zan ne mesu
1 bayan 1 cewar Abu Umma
kawo mu kai miki dan dali
cewar Binta Gashi nan kutafi
amma dan Allah karku nemi
tso kanar kowa kuma Ku
canza hanya karsu ganku
cewar umma To sai mun
dawo suka fada gaba dayansu
suka fita
.
Suna fita umma taji wani
hadeden wari Umma taja
dogon nun fashi Wannan
wani sabon yayi ne kuma Abu
irin Wannan bugawa haka
nida Allah yasa kar Binta
tadau Wannan halin na rashin
Wanka Suna tafiya suna
waka suna ciye ciye suna
neman tso kana Abu ta gano
bishiya tace Binta ajiye
gorjiyar nan muhau bishiya
kinga yanzu basu fara zuwaba
zuwa anjima sai muje dan
dali To muje suka tarar da
yara a jikin bishiya suna
wasa Kubar gurin nan Abu
da Binta sunzo ko sokuke jiki
yayi tsami cewar Binta Tinkan
Binta ta karasa magana yaran
suka bar gurin dan sunsan
halin Abu da Binta Suka cire
takalmi suka haye bishiya
suna wasa kamar yara Wasu
yan mata suka zo wucewa
suka gano Binta da Abu suka
kwashe da dariya Abu na
ganin su ta sauko Binta ma
sauko wa tayi Wakuke wa
dariya Eh daku nake magana
Abu ta fada tana dungure
musu kai Karki sake dun
guremin kai kinsan kowaye
babana kuwa A garin nan
.
koma waye hi beda meniba
abinda yasa kika kallemu
shine yanzu ze Ja miki dukan
tsiyama kuwa cewar Binta
Jiki ko kayama baki iya
sawaba ji hodar fukarki
janbakin ma tsohon yayi ne
amatse ciki asai sabo cewar
Abu Kaji wai harkurace zata
ce da kare maye jiki kalli
kafarki kalli fuskarki ji wani
wari mara dadi da kikeyi
gaskiya kinci sunan ki HODA
BA WANKA Nanfa Abu tayi
kukan kura ta rufesu da duka
Binta nadukan daya Abu ma
na dukan 1
.
Duka sukai musu bana wasa
ba harda yaga riga Cikin
muryar kuka yarinyar tace
saina nuna miki bakida wayo
Saikin ga gatana Abu tace
Jeki turo duk wanda kika
gadama ni Abu ina jiran hi
banza qazama Eh nice
qazama idan ni kazamace ke
kuma fa fada min cewar yarin
yar Bakinki be mutuba ko
Abu saimun zubar mata da
hakwara tukun na cewar
Binta Kuyi duk abinda kuke
so lokacin kune yanzu nima
lokacina nanan zuwa cewar
yarin yar
.
Tana gama fada ta mike ta
debi takal manta a hannu ta
kalli kawarta da suke tafe
tare Tace 'YAR KWALLIYA
suka zuba da gudu
Matsoratan banza kawai harni
zakibawa tsoro da baban ki
Wannan kalmarta zakiga me
rama min yazama tamkar
tatsoniya a gurina ni Abu naci
dubu sai ceto Sukayi dariya
Kinga dauki tallar mu karasa
dandali yanzu kowa yazo
zamusha kallo kai ni harnaji
ma bana son zuwa cewar
Abu Binta tace meyasa
Tiraren jikina Akoda yaushe
shine matsala ta dana je
dandali daga kallo sai tohe
hanci a gurin sama ri cewar
Abu Binta tace dagaske kike
Abu warin najan hankalin
samari Abu tace bana son
wula kanci binta wayace miki
warine kanhidai nibama nason
irin kallon da sama rin suke
min nasani nafi matan dandali
kyau da kanhin tirare sosai ma
nice kadai nasan sirrin
Nanfa Binta ta tafi tuna ni Ke
tina ninme kikeyi Abu gaskiya
nima zan fara fashin Wanka
konima turaren jikina zefito
kwana nawa zanyi banyi
wankaba Abu tace yauwa yar
gari kinga bake ba Wanka
indai kinaso tiraren yazauna
tareda ke duk inda kika higa
ansan kin higo Binta tace To
hi kenan nagode kawata
Tadauko farantin gurjiya tace
debi kici iya San ranki aikin
bani sirri babba Abu tace
Bakomai yiwa Kaine Binta
amma ya zakiyi da umman ki
idan tagane kin dena kwanka
Kibari kawai nikaina bansan
abinyi ba mutafiko kinga
yamma tayi kar a fara
bugawasa bama nan Abu
tace ga aiki zan saki indan
mun higa dan dali ki ki zuba
ido kiga abin mama ki gurin
sama rida yan mata To
hikenan muje Abu
Suka je dandali hakan kuwa
akayi Abu nazuwa masu toshe
hanci nayi masu dariya nayi
Abu harda sake tafiya
Kawata Abu gaskiya nima na
rike sirrin nan hannu 2
Sukayi dariya suka tafa
Suka sha kallo sukayi tsokana
iya son ransu suka koma
gida Daga ina kike Waye
Wannan Abu tace tana daga
kai taga Nura Daga dandali
nake Yariko hannunta
yawuce da ita ciki ya watsar
da ita kamar kayan wanki
Nura ya fara shin shine shin
shine Yace Inna bana
tunaninda Abu ta shigawanka
tayi Inna tace Ko hmm zata
aikata nasani Wannan nan
gaba kadan nizan fara yimata
Wanka da kaina
.
Abu tace Waaa niii tab
bawanda ya isa dan bakin ciki
turaren nawama rabani dahi
za a yi Nura ya Wanka mata
mari tafashe da kuka Inna
abinda ya dace kenan kifara yi
mata da kanki tinda ita bata
yi Nifa bawanda zemin wanka
Nifa yaya anyi walkiya na
ganka bakin ciki kawai ka keyi
dani dakaji kanhin tirarena
saika dinga yamutse fuska
saboda bakin ciki Tirare ko
wari kinga kidena shiga cikin
mutane kina kiran waikin fesa
tirare dariya zasu miki
Wannan warine warinma mara
dadi qazama cewar Nura hi
kenan Inna kina jinhi ko ni ya
kira qazama tafara timami
akasa Nura yace Inna kice
mata ta tashi kokuma yanzu
jikinta ya fada mata Bashiri
ta mike tana gunguni harya
fito fili tace nagaba yayi gaba
kanshi kuma nayi bawanda ya
isa yakwace Ehhhe Waye ze
kwace inbanda Wanka Inna
duk sanda kika tashi wankar
*'YAR KWALLIYA* kitanaji
kwalin sabulu saboda tsoro
Inna saida safe Yana fada
yayi fice warsa Allah
yakaimu Inna kinji shi ko
Yasin yaya kajawa budur
warka Allah ya hadani da ita
Kinga Abu bana son neman
tsokana karki sake kitaba
musu 'ya kisamu wanda
yamiki badai itaba ki kwanta
saida safe To Inna Allah ya
kaimu WASHE GARI DA
SAFE Abu ta fito tana
hamma
.
Inna Allah dai yasa kin gama
abinci dan yau yunwa
nakwaso abaccin Bagai
suwa ba komai sai Neman
abinci baza kiciba saikin goge
baki kinyi sallah tukunna
cewar Nura Tamatso kusa
dashi tace yaya a gidan nan
kaine kwai matsalata yanda
sauran suka tafi suka barini
kaima zaka tafi ko ince kagaji
kabarni Yatoshe hanci tinda
tafara magana harta gama
Nura yace Wai Wannan bakin
naki Abu ai sai ya kashe me
rai yaushe rabonki da goge
baki AF anzo wajan nikaina
na manta gawayin da gihirin
na ban wuya Yasin hiyasa na
dena wankewa yawan goge
baki na kahe hakori Nura
Yana nesa da ita yanda bazeji
warin bakin ba Injiwa Yau
saikin goge baki yaushe
rabonki da sallah dan Inna
tace rabonda taga kin kalli
gabas harta manta cewar
Nura Eh hakane yaya hadasu
nakeyi hiyasa bata ganina
Hadasu kamarya Abu Nasati1
nakeyi a rana1 sauran
ranakun kuma ina hutu tafada
tana dariya Nura yace Abin
ma dariya yabaki ko Abu
amma kin dena zuwa isilamiya
ko Tab tsohon zance tin
yauhe nadena zuwa bari kaji
laifi nayi yace ze dakeni
nikuma nace be isaba shine
yasa yara suyimin waka
waini *HODA BA WANKA*
hine na sace mai tayar keke
hine fa yake ne mana ruwa a
jallo
.
Tana fada tana Sosa kai da
jikin ta Inna haka lamarin Abu
ya kara lala cewa cewar Nura
Inna tace kaji da kunnan ka
kakuma gani da idonka yazu
kuma abin zekara finnada
tinda ta hadu da Binta Ido
yazare yace Binta gagare Ita
dai yanzu kawartace sosai
duk inda Abu take zakaga
binta Cewar inna Dole nakara
samiki ido Abu jeki kwanke
baki kiyi Alwala kizo kiyi sallah
a gabana kuma ma inbanda
rashin hankali irin na Abu a i
na akace miki hada sallah a
keyi kowacce ana yinta akan
lokacin ta kina jiko cewar
nura Abu tace Yashiga tanan
ya fita tanan bayan kai ba
malami bane me zaka fada
min nayarda bayan sanin ma
nafika Na yarda jekiyi alwalar
kizo Taje tayi ta zo
gabanshi tace yaya na hutar
dakai dama yau nake hadesu
guri guda barima nayi ka gani
Nura yace Ke bana son hauka
fa sallar Asuba raka'a
nawane Lallaima yayan nan
nawane inbanda 2 Sallama
Alaikum Nura yajiyo sallama
daga kofar gida girgiza kai
kwai yayi yatashi yatafi Nura
ya Inna taku Lpy kalau cewar
nura To Alhamdulillah
megarine yace kuzo dakai da
inna dakuma Abu Allah
daiyasa lpy cewar nura
Ehhhhhto lpy ba lpy ba saidai
koma meye idan kazo fada
kaji To gamu nan zuwa yace
yakoma ciki Inna yarinyadai
tasake ballo ruwa megarine
yake Neman mu To Bakomai
bari ta idar da sallah saimu
tafi cewar Inna Abu tace Inna
Nifa ba inda zani idan banci
abinci ba Ehhhhe Waiba
sallah kike yiba Abu cewar
Inna Abu tace Inna kwantarda
hankalinki na idar bani na
bawa cikina tukunna Inna ta
bata ta ansa tana hannu baka
hannu kwarya harta gama
Tasha ruwa Tace Inna saura
kwalliya idan banyiba bazan
iya sa kafata wajeba Nura
yace kin isa waye ze zauna
jiranki Inna tace kai kanka
kasan hakan baze yiyuba
kabarta tayi mutafi Abuta
baje kayan KWALLIYA tayi
kamar yanda ta saba fukarnan
kamar Aljana Inna mutafi
naga ma Warin bakinta yadoki
hancin Nura Kaiiiiiii Abu baki
wanke bakiba ko Eh ban
wankeba bakina ko naka
.
Tayi gaba abinta sukuma suna
binta a baya harsuka karasa
fada kowa na gaida megari
amma banda Abu Megari
yace Ke Abu me yarin yata tai
miki kika daketa jiya tareda
bakuwar gidana Tawatsawa
yarin yar harara tace kuma na
dake ta nadaki banza ba uwar
dayasa tace min HODA ba
Wanka Ke Abu baban nawa
kike fadawa haka cewar yar
megari Anfada mihi ubanki
ubanane cewar Abu Kaji
yarinya mara kunya me garin
kike fadawa haka Ayi hakuri
yarin yace cewar Inna Abu
tace Inna saboda ni karki fara
karya niba yarinya bace
hekarata goma shabiyar Inna
nayimata alama tarufe baki
amma ina zance kwai Abu
take saki..
Writing By Jabeer Rabiu Idris..
Whatsap Number..
07034488635...
'YAR KWALLIYA Page 6-10
.
Can saiga Binta ga gare
sarkin kwadayi da umman ta
suna ta howa Yauwa Allah
na gode maka ga binta cewar
Abu Dan rainin wayo da
sassafen nan a aiko gidan
mutane ace suzo ko uwar me
za a mana cewar Binta Abu
tace Kema dai kya fada
gamunan ana surfo mana
zancan banza Eh waye yake
zancan banza ke kuma Binta
ba a koya miki gaisu waba
bakya ganin manyane a gurin
nan cewar liman dake zaune
a gefen me gari Binta da
umma suka samu guri suka
zauna Abu tace Wanda
yatsargu dahi nake Babba
bangan shiba saidai naga me
gari tinda ba a barni naci
abinci ba nazo nan to kowa
yayi hakuri da abinda zeji koya
gani cewar binta Liman yace
kaji yara da rashin kunya
Barsu dani liman cewar
megari Umma ta gaida me
gari binta kuwa aikin gun guni
kawai takeyi Sauran mutanen
gurin hanci a to she sun kasa
cewa komai daga liman sai
megarine kawai suke magana
Binta kinji wai dan mun daki
wa yancan 'yaran hine aka
kawo mu nan gasu 'ya'yan kuli
da mai cewar Abu Binta tace
Kan uba Yasin bazan zauna
ba akan su aka hanani cin
abinci tafiya zanyi Yasin
karki yarda binta kanki tafi
kizo ki daki rabon ki zan taya
ki cewar Abu Sukayi kansu
zasu daka liman da megari
mutuwar zaune sukayi wato
kanhin jikin Abu dana binta da
itama tafara hawa layi sukaji
sukayi lup kamar basa gurin
Megari yace Karku sake Ku
tabasu kuna jiko wai warin me
nake ji haka ina kuke kusa
baki mana meye aikin ku
liman Caraf Abu tayi da
cewa nice nan kanhin tirarena
babu inda baya zuwa megari
ka gode Allah tinda kaji
kanhin tirarena Megari yace
Tirare kuma tab Wannan uban
warin shine tirare
.
liman ba lbr yakasa cewa
komai sai kallo da ido sauran
ma sunyi shiru Megari cikin
bacin rai yace waime nake
gani haka kun dena magana
ne kuma banson sha shanci
kunwani zuba min ido me
kuke nufi Me gari sai hakuri
binta Abu kuzauna cewar inna
da umma Binta hannu a dun
kule tana shirin kai naushi
take cewa Inna kubar mu
dasu yanzu mu koya musu
hankali Nura cikin muryar
tsawa yake cewa kuzauna
karku bari na kara magana
Ganin fuskarshi ba alamar
wasa yasa suka zauna
Megari yace gaskiya yaran
nan abin naku azimun ne
kuma da laifinku wajan bata
yaran nan kuduba fa Ku gani
baruwansu da babba koyaro
duk wanda ya musu yi mishi
zasuyi Me gari ayi hakuri
zamu gyara insha Allah cewar
umma Me gari yace To shi
kenan gaskiya kudau mataki
inba haka ba ni da kaina
zandau mataki Wani yaro ya
fito daga gidan me gari
hannun shi rikeda samira
Tinkafin ya karaso Binta
sarkin kwadayi tafara hadiyar
yawu wayanda suke kusa da
ita saida sukaji karar Yaron
ya gaidasu ya ajiye kwanon a
gaban liman Binta idonta na
kan kwanon ko kiftawa bata yi
ta janyo kwanon kusada ita
Kanshin abinci yadawo da
liman daga dogon suman da
yayi Liman yace Ke me kike
nufi yajanyo kwanon gaban
shi Binta ko magana ta kasa
hankalinta nakan kwanon
Liman Allah ya yanka maka
binta taga abinci ranta ya biya
dan haka ka bata taci cewar
Abu Liman yace In naki fa
dawani bakinki dayake zuba
wari anya kina wanke shi
kuwa Abu tace Yasin wanke
baki kahe hakori yake hiyasa
bana yi liman kaida kanka
kace hi bakin me azumi
kanhin Almuski yakeyi hiyasa
nima na dena wanke baki
saboda Almiskin yazauna a
bakina nafita daban daku
nawa basai ina azumiba ta
fada tana Dariya Liman baki
yasaki yana kallon Abu
Megari yace ke Abu anya kina
da kai kuwa Abu tamika
mishi kanta tace shafa kaji
Inna ta rufe bakinta tana
kallon Abu Megari ina fada
maka saika dauki babban
mataki akan Abu da binta
cewar liman Bakomai kubani
lokaci zansan abinyi kuna iya
tafiya amma kubar binta da
Abu liman ze musu fada
cewar megari Waaaanii
gaskiya babu abinda zan iya
fadawa wayan nan yaran
banshirya takun saka da suba
sunyi nisa basa jinkira cewar
liman Yi shiru liman nagama
magana cewar megari
Inna,umma da Nura suka tafi
Binta batama San tafiyar suba
itadai burinta taji abinda ke
cikin kwanon a cikinta Liman
kabata abincin nan taci yasin
tanada cutar duka idan aka
hanata abinda takeso hine
suke tahi cewar Abu Liman
Ya kalli binta dake zaune
hannu a dunkule ido akan
kwano tana sude baki Liman
yace Me gari Abuya tabbata
duka zatayi kalli kaga
.
Liman karka zama soko mana
kayi musu fada sutashi su tafi
ita kuma binta ka bata taci
cewar megari Kwanon ya
miki mata ta ansa tabude tana
ci kamar kura yaga nama
Binta ta gama ci tasa kafa ta
ture kwanon ta kalli 'yar me
gari tace jeki kawo min ruwa
Niii kalle ni sama da kasa nayi
kama da 'yar aikin gidan Ku
cewar yar me gari Zancen
banza meye dan kin debo min
ruwa yan matan garin nan kaf
yan aikina ne saboda na fisu
haduwa cewar Abu Ya isa
kunutsu kuyiwa kanku fada
kungirma aure zakuyi gidan
wani zaku kuyiwa Allah
kudena abinda kukeyi Dariya
suka yi suka tafa kinji wai
aure cewar Abu Binta tace
kaika sanshi nidai tinda ba a
bani ruwaba bangode ba taso
mu tafi To tace suka tashi
zasu tafi Binta tarike ciki
tace washiii cikina ya
motsa Binta tayi nishi
saiga tusa ya biyo baya
Megari yatoshe hanci yace
liman Sa a kamo min yarin
yarnan Binta da Abu najin
haka suka sa gudu
****
*WACECE BINTA DA ABU*
ABU 'yace ga munzali
malam munzali fatauci ne
sana arsa shikadai yake tafiya
inya tafi saiya jima kafin ya
dawo sai matarsa Suwaiba
yaranta na kiranta da Inna
yaransu 4 Ramatu itace ta
farko tana aure a garin da
suke me suna *DARAUDAU*
sai zulai itama tayi aure sai
Nura da Zainabu Abu itace
auta
ABU yarin yace mara tsoro
duk girman mutum inya mata
saita mai farace tas amma
qazanta ya maida ta baka dan
qazanta kokitso intayi saiya
dankare layin ya bace kafin
inna tai mata ta karfi ta tsefe
Binta 'yace ga murtala
Malam murtala mahaucine
Allah ya masa rasuwa tin
Binta tana karama a hannun
ma hai fiyarta ta tashi sunan
ta Baraka binta kadai ta
haifa BINTA yarin yace
mara nutsuwa ga kwadayin
tsiya idan taga abinci jikinta
har rawa yakeyi itama bata
barin ta kwana dan haka tasu
tazo 1da Abu gasuda
taurinkai
*****
Binta da Abu na cikin gudu
wata yarinya kanta dauke da
buhu ta tsaya a gaban su ta
shaki wuyan Abu Ke meye
haka a ina nasanki cewar
Abu Tace idan maye ya
manta uwar diya bazata
mantaba nice wadda kika
daka kika cimin gyada kika
kuma zubarda sauran Abu
tace Kinsan abin da yawa
yanzu me kike nufi da kika
shaki wuyana Dukanki zanyi
na kwashi saura nakai
gidanku cewar yarin yar
Banga Alamaba ance da
kuturu a gama lpy ni Abu
banga wanda ya isa yamin
abinda kika fada ba ba a hai
fehiba Binta tace ke ware
inba haka ba hmm jiki zeyi
tsami Ke waya sa dake ni din
nan da kike jida gani ban
tinkare kuba saida na samo
makarin ki ke binta dan
nakula kema matsalace ta
daban cewar yarin yar
Makarina kuma ni binta
banganshiba anan gurin yau
banga abinda zesa na bar
kiba batareda na sosakida
bulala ba Ko to shikenan nida
ke za a ga me gaskiya yarin
yar ta Bude buhun taciro
goriba,kurna,magarya da
gyada Tinda ta Ciro Binta ta
hadiyi yawu kamar yanda ta
saba tabi hannun yarin yar da
kallo Abu tace Ke karki sake
ta rudeki da abin hannunta
Binta nizan siya miki fiye
dahi Ko jinta binta bata yiba
Tamika hannu alamar ta bata
harya rinyar ta miko mata
saita janye Binta tace meye
haka kuma bana son irin
Wannan Kina zaton kai tsaye
zan baki batareda na kafa miki
doka ba Meye dokar cewar
Binta Yarin yar tace zakiyi
Alkawarin cewa bazaki sa
hannu a fadana da Abu ba
inkikasa hannu zan kwace
abina Binta ta kalli Abu ta
kuma kalli ledar hannu
yarinyar da irin abinda ke ciki
Nan tashiga raba
idanu
.
Jikin Binta sai rawa yake
Na amince bani Yarin yar
tace in na baki ki tafi ko
juyowa karkiyi Binta tace to
bani dai Tana ba binta
tawuce ta tafi Yarinyar tace
yanzu daga ni seke Abu
tace hakane kuma zam miki
dukan tsiya kamar mu2 muka
miki Yarin yar ta kama Abu
da duka Abu na ramawa Abu
ta Bude baki ta sakar mata
cizo a hannu Waiyoo kika
cizeni Yasin bazan yarda ba
koni koke a gurin nan cewar
yarin yar Saukar duka yarin
yar taji bazata koda ta juyo
Binta ta gani zatai magana
binta ta dauketa da mari binta
da Abu sukayi mata taron
dangi saiga yarin yar a kasa
wanwar tana kuka Abu ta
bude buhu ta leka taga garin
tuwo tayi dariya Binta ta daga
ta juyewa yarin yar a jiki
Inkinje gida saikiyiwa tsohuwa
bayani yanda Akai da garin
tuwo cewar Abu Suka tsalla
keta suka wuce Binta tace
Abu kina jin abinda liman yayi
mana dan yaga me gari
waimun girma aure zamuyi
Rabu dashi nasan abinda za
muyi mihi damu yake magana
ba a taba mubama munyi fada
bare ka ta bamu zomuje
cewar Abu Ina zamu cewar
binta Zaki gani cewar Abu
Koda suka tafi basu tsaya ko
ina ba sai gidan liman Abu
tace Sallama Alaikum goggo
me tuwo Goggo me tuwo ta
amsa da Wa'alaikumus salam
Abu Binta yaukune agin
namu Eh wlh cewar Binta
Goggo me tuwo tace Gashi
kuma ban gama tuwonba
yanzuma na dora Bakomai
mu abindaya kawo muma
daban ne bansan ta yanda
zanfara fada mikiba goggo
cewar Abu Kar kuji komai
kufada min idan baku fada
minba wazaku fadawa bayan
nasan Ku tin kuna yara nan
kuke zuwa cintuwo cewar
goggo Binta tace Hakane
munsan da wannan goggo
hine dalilin da yasa mukejin
nauyin abinda zamu fada
miki Binta Abu kufada min
bakomai komai girmanshi
zansan abinyi Abu tafashe da
kukan karya taceTo hikenan
goggo kiyi hakuri da abinda
zakiji sai Abu takara sautin
kun da takeyi Binta ma kukan
karya takeyi tace yi hakuri
Abu bakomai sakai yar daze
mata kenan Nanfa hankalin
goggo ya tashi tace kunga
kufada min duk kunbi kun
daga min hankali Abu tace
goggo dagir manki da komai
liman ze miki kishiya Gogo ta
mike tsaye tarike kirji tana
huci
.
Ni liman zewa haka zezo ya
sameni bemin kishayaba tin
ina yarinyata saiyanzu dana
tsufa Goggo abinda ze kara
daga miki hankali hine irin
kalaman da yake mata idan
yaje zance cewar binta tafada
tana kuka Dan rahin mutunci
hine ta aiko mu da kala man
soyayya muzo mu fada mihi
Takuma ce karya manta yau
yazo zance ita kadai tasan
abinda ta tana dar mihi cewar
Abu Kafar goggo ya haurawa
taji juwa na ibanta tajin gina
da bango ta ciji lebe a nan
gidan ze kwana daiko
badamuwa ina jiranka cewar
goggo Binta takara sautin
kuka tace babban abin hine
mahaifin yarin yar yace liman
yaturo anbahi ita Suna fada
goggo ta zube kasa ba
nunfashi Munhiga 3 Abu
munyi kisa cewar binta Abu
tace ke bata mutuba tsabar
kihine kawo ruwa kigani
Binta takawo ruwa Abuta
watsa mata taja dogon
nunfashi tabude ido tana
Cewa ina yake kumiko min
shi Abu tace goggo aibaya
nan bari zahigo saiku yita
takare Goggo tace bakomai
zaka dawo kasa meni liman
nida kaine yau agidan
Goggo mu zamu tafi Nagode
muku binta da Abu Allah ya
muku Albarka Goggo me
tuwo macace me kishi akan
kishi zata iya yin komai sanin
hakane yasa Abu da binta
sukazo gurinta sunsan ita zata
hukun ta musu liman yanda
suke so Ameeen goggo
aiyiwa kaine suka ce suka
nufi hanyar fita harsun sa
kafa zasu fita Abu ta gano
liman yana ta howa da alama
gidan zezo da sauri ta riko
binta suka boye cikin wani
duhuwa dake zauren gidan
liman Liman yayi sallama ya
fada gida kai tsaye ya nufi
bandaki Goggo na jinshi
binta da Abu Suka dauke
sawun takalmi suka matso
tayanda zasuji kuma suga
Abinda ke faruwa Liman
yafito yashiga daki yasa
sababbin kaya yafesa tirare
Nanfa kishi ya turnike goggo
me tuwo tashiga waigen
Abinda zata samu tarike ta
hukun tashi dashi Me gari ya
fito yana gyara hula yace in
na kike na fito zan tafi Goggo
tafito tana huci tace nasani
kagai sheta wato danka raina
min hankali nika ajiyeni a gida
kaikuma ka fita kana neman
aureko har ance katuro Yace
ni liman a ina kikaji zan cen
nan wlh bana ne man aure a
ko ina ni liman ke kadai kin
ishe ni Tace karyar banza ba
abinda zaka fada min na
yarda bayan nasan komai
yanzu kayan nan dakasa
kafesa tirare ina zaka Abuda
binta na labe suna ji kuma
suna ganinsu suna dariya
Yace daliban malam rabi'u ne
zasuyi sauka yau shine aka
gai yace ni na shirya yanzu
zan tafi Bata gamsu da
abinda yace ba yasa tafara
buga kafa tana tsaki
.
Tace malam malam ni goggo
ni zakai wa kishiya Tana
juyawa taga murhuna cida
wuta ta Ciro icen dayafi ci
tasa mai ababban Riga wuta
yafara ci liman na ihon
temako yana kokarin cire
baban riga dakyai ya samu ya
cire abin beyiwa gogoba ta
dauko tukunyarda ta gama
hada kayan hadin miya ta
kwaramai a fara ren kayan
shi Binta da Abu dariya
harda faduwa Ta rarimo
bokiti tana jifan shi dashi
ganin abin nata bana Kare
bane yasa liman ya mike ya
zuba da gudu Binta da Abu
suka Tsaya a gaban shi
Abu tace liman mun girma
aure zamuyi ko toga auren
mun gwada maka tafada tana
dariya Binta tace waiyoo
cikina liman mezan gani haka
yazaka gudu kaida yadace kai
mata fada kamar yanda kayi
mana dazu Amma dai yaran
nan kwai shedanu kune kuka
hadani da matata bakomai
dani kuke magana Abu tace
gogo me tuwo gashinan
Liman yasa gudu binta da Abu
na dariya Raina fesa cewar
binta Duk wanda yace ze
higa harkarmu to yadebowa
kanhi kwarkwasa cewar Abu
Sukayi dariya suka tafa Suka
nufi gidan su Abu Liman be
tsaya ko inaba sai fada gurin
me gari wayanda suke tareda
megari ganin liman yashigo
da gudu suma suka mike
zasu gudu Megari yace
kudawo Ku zauna liman
mezan gani haka da girmanka
da komai Allah yabaka
yawan rai ai duk abinda ya
sameni kaine sila saida nace
ba fadan da zanwa Binta da
Abu kace kaisam saina
musu gashi abin daya jamin
dagir mana da komai na yanko
ta cikin unguwa da gudu kowa
na kallona Yanzu binta da
Abune sukai maka haka a
garin nan cewar me gari
Liman yace hmmm ni nasan
su sarai shiyasa tin farko naki
kadage kace sainayi yanzu
gurin saukarma ba halin
zuwa ta kona babban rigar
sukuma wayan nan kaga dai
yanda tai musu harda manja a
jiki kamar za a Kada miya
gashi badamar na koma gida
yanda ranta yake a bace Kai
kutashi kuje Ku ne mo min
su A'a kudawo Ku zauna
Allah ya baka yawan rai
nayafe Abarsu kawai nidai
goggo me tuwo itace kadai
damuwata ita taimin hakafa
.
Nan yakwashe duk abinda
ya faru yafada wa megari
Shine zakace a barsu gwara
mu koya musu hankali cewar
megari Eh Bakomai a barsu
cewar liman To shi kenan
zansa a kiramin gogo me
tuwo zan mata bayani karka
samu damuwa To shikenan
godiya nake Allah ya baka
yawan rai Kai tsaye suka
shiga gidan ba sallama
Yaushe zaku girma abin naku
kara lala cewa yakeyi ko Abu
da Binta cewar Inna Saida
suka samu guri suka zauna
sannan sukace salama
Alaikum Inna tace Allah
nagode maka binta da Abu
Nura yatafi maka rantar boko
Yinme inna cewar Binta Inna
tace Yaje saku a maka rantar
boko daga nan yamai daku
isilamiya dan harda rashin
ilimi a abinda kukeyi Abu
tace Boko tab ba inda zani
Inna bokoko awuta kike nunfin
zamu toko su yan bokokon
Awuta tsoron bokon sukeyi ba
inda zani saidai ko binta gata
nan Waaaaniii tab namutu
Allah yasani awuta ba bokon
da zani cewar Binta
.
Wlh baku isaba haka kuke so
mu zauna daku a jahirce
cewar Inna Yasin bazani ba
wuta tsilim cikin sauki bokoko
Awuta bada niba cewar Abu
Binta ta tashi daga inda take
ta koma kusa da Inna Tace
Inna kisa baki akahe maganar
nan dan baze taba yiyuba
Yasin haka kawai ze Kaimu
lahira da kanhi Kanshi kanshi
inna taji yana tashi A jikin
Binta Tato she hanci tace
Binta warin me nake ji haka
kardai kema kinhau layin
rashin yinwanka Dariya Abu
tayi tace Inna nice nan
nadorata alayi tam bayeta kiji
ita kanta tafijin dadin jikinta
yanzu fiye da da Rufemin
baki sakarai qazama nayi
dake *'YAR KWALLIYA* Binta
kiyiwa Allah karki bari Abu ta
koya miki rashin Wanka da
Wannan maya taccen
KWALLIYAR nata Inna saidai
kar a kuma dankuwa karatu
yamin qanhi yabi jiki bakiga
irin kallon da megari yake
minba nikadai nagane meyake
nufi cewar Binta Abu tace
Nagani rabu dahi binta ze
fado hannu banda hima ya
tema kawa kanhi besa bakiba
aida tuni munkoya mihi
hankali kamar yanda muka
koyawa liman Oohni Inna ina
zansa kaina nan nasamu lbr
anga liman yana zuba gudu a
gari har ana zaton ya Hauka
ce ashe ba Hauka cewa
yayiba gamo yayi da 'ya'yan
Aljanu binta da Abu babban
gamo yai cewar Inna Abu
kwaso kayan KWALLIYAR
muyi muje gidan Amaryar da
aka kawo nan bayan layin ku
cewar Binta Abu tace Hakane
fa banjeba kuwa Tashiga ta
dauko ta ajiya a gaban binta
Inna tace shiyasa tin farko
banso qawan cen kuba wlh
nasani sarai cewa abinda kuke
da NA yanzu saiya fishi kuma
gashi na gani Suka kafe inna
da idanu Inna tace bance
komai ba ni badaku nakeba
Allah yabaku hakuri Suka juya
suka cigaba da KWALLIYA
Salama Alaikum inna nadawo
Wa'alaikumus salam gonda da
Allah ya kawo ka Yi shiru
Inna nasamu lbr komai inaji
nasan sune zasu aika tawa
liman haka komai yazo karshe
na sasu amaka rantar boko
hakama isilamiya ga kayan
maka rantar nasu
Alhamdulillah shikenan
kurinkus kandan bera boko
Saikun je kokuna so ko ba
kwaso cewar Inna Abu tace
Boko Boko dai hikenan naji
duk abinda ake fada akan
boko ance yan wutane hine
mu za a kaimu saboda ba a
sonmu Ba a San naku gobe
zaku fara zuwa daga nan idan
kuntaso saiku wuce isilamiyar
malam rabi'u Binta ta tashi
ta daka tsalle tace rabi'u
Yasin ba inda zani Wannan
bakin mugun baki da Wannan
kan nahi dayake kyalli kamar
an cirohi A tandun mai
Malamin naku kinga binta
nasan irin takun sakar da
kukeyi da malam rabi'u idan
kika bari yakawo min karar ki
kikuka da kanki irin dokan
dazan miki baze faduba harda
ke Abu cewar Nura Abu tace
hikenan dai zamu leka wutar
bakomai amma idan mukaji da
zafi bazamu sake koma
waba Tsaki Nura yayi yatafi
ya basu guri Sukaci uwar
KWALLIYA suka fice basu
cewa Inna komai ba
.
WASHE GARI Abu tana tashi
tasa kayan maka ranta ta
janyo kayan KWALLIYA zata
yi Nura yace karki sake kiyi
KWALLIYA makaranta zaki ba
dandaliba Abu tace Tab yaya
Nura gaskiya bazan iya fita
banyi KWALLIYA ba ga kanhin
tirare i nayi Amma ba
KWALLIYA a fuska ta Nura
yace Eh ba a KWALLIYA idan
za aje makaranta Abu dole
kidena wasu abubuwan yanzu
tinda kinfara zuwa
makaranta Binta ta shigo ba
sallama agaban kayan
KWALLIYA ta zauna zatayi
KWALLIYA Nura yace ke
Binta ba sallama Bakomai
kiwani zo gaban kayan
KWALLIYA Binta tace yaya
Nura tinda nafito banyi
magana da kowaba Gahi
yanzu kasa nayi magana
Almiskin bakina yafita Hanci
yatoshe yace naji Almiskin
kice kema kinbi layin qazantar
Abu ko makaranta zaku zakuje
kuga yanda Ake safta Binta
tace *'YAR KWALLIYA* mezan
gani haka meyasa bakiyi
KWALLIYA ba Abu tace Binta
kibarni kibarni kwai ni Abu
*'YAR KWALLIYA* ni za a
hana yin KWALLIYA badole
kiga haka ba Binta tace
shine kike daga hanka linki
ina Inna Abu tace tana ciki
Binta tace yaya I na bayanka
gwanda daka hanata bani
kayan KWALLIYAR NA shiga
dasu au baza kibaniba bari na
dauka da kaina Binta na
shiga ta juye kayan
KWALLIYAR a Jakarta tafito
Binta tace bata cikifa Abu
tace hakane yanzu ta fita
zomuci Abinci bayan sun
gama cin Abinci Nura ya
kaisu maka ranta Duk wanda
yaga fuskar Abu ba KWALLIYA
sai yayi mamaki dan bata taba
fita ba KWALLIYA ba Suka
shiga Aji Binta tace Abu
Albishirin ki Abu rai a hade
tace goro Binta ta bude
Jakarta tace kalli Abu cikin
mamaki tafasa kara ta
rungume binta ta tsalle a
aji Hankalin daliban ya
koma Kansu Abu tace muna
fukai me kuke kallo da sannu
duk zanyi maga ninku
.
Daliban Suka dena kallon su
Suka baje kayan KWALLIYA
sunayi malami ya shigo aji
akatashi ana gaisuwa banda
Abu da Binta KWALLIYA kawai
suke yi Malamin ya karaso
gurin su yace Ku meye haka
kwalliya a cikin aji me kukeyi
a nan aji bantaba ganin kuba
Abu tana shafa Jan baki tace
baza kasan muba hime maka
rantar be sanar dakai komu
suwaye bako hege wato ya
cinye kudin ko to hikenan
Yace bagane me kuke nufiba
fa Binta tace kaga waimu sa
babbin dali baine kuma nanne
ajin mu kana jiko jeka to
Yace kee Nifa malamin kune
kibani girma bakowana
magana zaki dinga fada
minba Abu tace inji kaba
girma idan karike girmanka
mutayaka rikewa idankuma
kaki rikewa mubi takai mu
wuce Malamin yayi
murmushin keta yace kugoge
fuskarku sannan kubani kayan
KWALLIYAN Abu tace tab ba
abinda zamu baka kuma ni
Abu bazan goge KWALLIYA ta
ba Binta tace nimadai bazan
gege ba malam kabar daliban
naka a tsaye fa Yace kuzauna
yayi murmushin yaje gaban
Allo yafara koyar dasu kamar
yanda ya saba Abu tace
gaskiya nagaji baza a yi wani
abin bane bayan Wannan kazo
ka I hemu da surutu Binta
tace a he kekina jin hi tinda
yafara har I yanzu banji
komai ba ni yunwa ma nakeji
Yace Anya karatu kuka zoyi
kuwa Abu tace waya sani
Abu a duhu Nifa karatun higa
wutan nan beda meniba dahi
da bahi duk1ne bokoko
Awuta Binta tace gaya mihi
kadai koyarda su dan naga
kamar suna gane wa Yace
anya Ku muta Nene kuwa ke
dawani fuskarki kamar aljana
waya gaya miki karatun shiga
wuta nake koyawa Binta tace
baka jiba bokoko a wuta hine
zakace bakaratun higa wuta
bane Yace kutashi Ku fita
daga ajin nan kufita kuyi shir
menku a waje Abu tace
seme danka koremu kahiga
wutar kaika dai kacike gurin
karkabari asa wani Yace keni
zaki fadawa haka Tamurguda
baki Yadauko bulala ya zuba
mata Tasaki kara
.
Binta tace meyasa ka daketa
kai ko a qauyen mu mune
muke yiwa maza duka
hmmm Yace me kike nufi
nima dukana zakuyi kenan
Abu tace meze hana tinda ka
dakeni saina rama Yace waya
gaya miki idan malami yadaki
daliba tana ramawa Binta taja
hannun abu Tace Abu rabu
dahi zomu fita ze fito ya same
mu damu yake maga mekoya
karatun higawuta dole mukoya
mihi hankali Suka fita
Abu kinga ya aika a siyomai
abinci Abu tace waye
ya aika asiyo mihi abinci
mekoya karatun higa wuta
Binta tace Eh hine zomuje
Yaron ya siyo abincin zekai
wa malam binta da Abu suka
tsare shi Abu tace Kai bamu
abinci kaje kadebo min ruwa
zansha kagani ba quwace
Yace malam ya aikeni bari
nakai mishi nadawo saina
debo miki Binta tace harna
hadiyi yawu banga abin dake
cikiba amma nasan zeyi dadi
tafada tana dariya.....
0 Response to "'YAR KWALLIYA Hausa Novel"
Post a Comment