Siffofi da hanyoyin gane mace mayaudariya da illolinsu
Siffofi da hanyoyin gane mace mayaudariya da illolinsu
Macce mai yaudara a soyayya
Allah ya kawo mu wata zamani wacce ke tafiya da salsala daban-daban akowani bangare na rayuwa. Idan muka yi dubi a bangaren soyayya tsakanin mace da namiji, a yau yana da wuya a duk kwarewarka a soyya ko neman aure ka iya gane namiji ko mace mai yaudara sakamakon yanda zuciya ta saje wajen sajewa da ababan kelkelin rayuwa. Mace ko namiji kan iya yin halin ‘hankaka mai da dan wani naka’ ta hanyar aron kaya ko daukar haya. Kamar da shima namiji yake iya sa abokinsa shiga na manyan mutane yaje neman masa aure, alhalin yaudararta zai yi.
A sakonmu na yau, na yi kokari zakulo wasu daga cikin siffofin da hanyoyin gane mace mayaudariya da illolinsu. Gasunan kamar haka:
Siffofin mace mayaudariya
Daukaka kai da kai, ma’ana jiji da kai da kokarin nuna ita wayeyyiyace.
Alakantar da kanta da wasu muhimman abubuwa da ake yayi yayin da take Magana. Misali nuna kusancinta da wani mai kudi, dan unguwarsu, makwabcinsu, mijin yarta ko wani ficeccen dan siyasa.
Karfin hali wajensa manyan atamfa, ‘yan kune, warwaro, takallama ko rike wayar salula mai tsada.
Sayan abin da ake yayi ko ta halin ka-ka, ko yin aro, haya, bashi ko sata a dakin saurayi ko gidan buki.
Kwarewa fagen roko cikin hikima
Shiga bokaye ko malamai don nasarar zama kan tubalin data gina rayuwarta
Kallon karancin wayewa ga wadanta suka tsaya iya matsayinsu.
Yin samaruka daban-daban don dorawa kowa hidimar da zai rika mata.
Kaskanta abin da ta samu a matsayin ba komi bane.
Gindaya sharuda ga manemanta
Wasu daga cikin hanyoyin gane mace mayaudariya
Yin binciken asalinta (idan kaima ba mayaudari bane)
Son yin samaruka masu hawa motoci irin na zamani.
Son yin kawance da ‘ya’yan manya.
Son ziyartar dangi masu kudi kawai, don maida gidajensu adireshinta.
Son afi ganinta daga cikin taron maza ko mata.
Yin iko cikin kalamanta ko nunawa a fuska yayin da take waya a cikin mutane.
Kauracewa zance aure duk lokacin da aka tinkareta da shi.
Ga kadan daga cikin illolin mace mayaudariya
Takan kaskantar da iyayenta musamman in basu da abin duniya
Tana sara mijin aure yayin ta bukaci auren
Tana rasa ragowar imaninta sakamakon harka da bokaye
Tana shiga mummunar walakanci koda ta yi aure.
Asalin halittarta na iya durkushewa sakamakon shafeshafe.
Tana zubarda kimar iyayenta.
Akarshe takan yi mummunar karshe.
HATTARA DAI IYAYE MATA…! Za a iya duba: Alacewar mace ta madigo da sauransu.
..mun gode da wannan aiki naku
ReplyDelete