-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

RABUWA CE  SANADI Hausa Novel

RABUWA CE SANADI Hausa Novel

 . . . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI Hausa Novel *  

     


                 

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣1❣                    


             


*©Mymounerh Basheer*


*®NWA*


*littattafan marubuciyar*


*soyayya gamon Jini*

*Raheena*

*kishiyoyina*

*habibullah*

*noor ala noor*

*Na Aminta dake*

*gimbiya maimunatu*

*Akan kaskon suya*

*Zeenatu*

*Ashe haka so yake*



*Queenmeemi.WordPress.com*



***************


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM



  *_k'aramar hukumar bunkure,dake jihar kano_* 

  

  

Babban titin dake garin bunkure wanda ya cika da d'aukacin jama'a kowanne ka kalli fuskar sa arazane yake wasu kuma gudu suke ci,ga wasu a kwance dai-dai kusa da wata Babbar mota na gano yarinya

Yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniyaba a zaune kusa da wata mota sai ihu take,Jikinta sai karkarwa yake kukan natan  Sam baya fitowa sabili da taci kukan harta k'oshi.



       Daamm!!!  k'ara  ce ta kuma tashi, take mutane suka hau guje-guje yarinyar da Bacci ya fara d'ibanta ta tashi firgigit ta k'wala k'ara ba wanda yasan tanayi gudu ta hauyi irin Na yara bawanda ke  Kula taa kowa ta kansa yake ,ke sai kiran momy take da dady ,wata mota ta gano gurin tayi aguje

 taje aguje tana bubbugawa dady! dady! neman iyayenta take Amma ko alamarsu Babu ga wajen ya hargitse kowa takansa yake Saboda tashin bomb din da akaji wanda yazamo tamkar wata jaraba gun wani mutumi ta yi ta baya da gudu tayi wajensa tana dady.

 juyowa yayi a tsorace yayi arba da ita , yana  shirin magana k'arar bindiga ce tafara tashi tas! tas! tas!  tas! kakeji nan da nan waje ya kuma hark'ewa hayak'i ko ta ina.

 yarinyar da duk Jikinta yajike da fitsari ga bakinta Na jini ,mutumin nan ya falfala yafara gudu ,yarinyar tabiyoshi dady! dady! sojojine suka tawo aguje suna harbi nan da  nan mutumin yai wata kwana yarinyar tabishi tana ihu inda ya b'uya taje ta tsaya ta dafa shi "dady momma"  hankad'eta yayi  yace "Yau naga jaraba ke ina iyayenki? ana wann nan  tashin hankalin  don sakaci", tureta yayi  yace ta bar wajen, tafiya tayi da gudu tayi wani waje  tai kwana tana  sangal-tangal  saboda ciwo dataji  a k'afa wani yaro ne ya arto yana haki yai ciki da ita ta fad'i k'asa d'agowar da Zatai akai harbi Allah ya taimaketa ba aharbeta ba Amma tsoro yasa ta suma ganin hakan tausayi yakama mutumin ya fito Daga mab'uyar sa ,yazo ya  d'auketa ya

 runtuma  aguje yana gudu seda yayi nisa yaje motar sa dake ajiye  ya ajiye ta agaban mortar  dayake motar d'aukan kayace  yara su hud'u ya ganni  a bayan motar sai ihu suke ya kallesu yace " ina  iyayenku"? D'aya ne mai wayo yace "nan mukazo muka b'uya",Sauran kwa ba wanda yayi magana sai kuka duk jikinsu k'ura da d'an Jini-jini ajikin su,jin- jina kai yayi kawai ya shiga motar.

 

 

      

************

     *K'auyen mangalu*

                            

 Jan motar yayi ya fafara aguje nan yiyi hanyar k'auyensu tafiyar awa d'aya da rabi ya kaishi k'auyen mangalu wanda yake a k'ark'ashin k'aramar hukumar bunkuren, Bayan yaje k'auyen nasu su, take bai zarce ko ina ba sai tasha,ya bud'e motar ya fita yaran yad'ebo, ya sauke su gaban motar yaje don d'auko yarinyar wayam ya nemi yarinyar ya rasa neman duniya yayi bega yarinyar  ba mamaki k'arara  afuskarsa "kode aljana ce tsuka yaja inajin Aljana ce

sede ko sauka tayi",nan yayi ta dubawa bai ganta ba 

Sarkin kasuwa ne yazo aguje  "Malam lado me nakeji ne agari wai cikin gari bomb ya tashi da Gaske ne kuwa"?


"Tabbas! hakane Sarkin kasuwa Ni kaina wallahi abun yaban  tsoro, lodi fa nake zan kai kaya kasuwa kawai mukaji k'arar tashin bomb ai Wallahi munga tashin hankali don an mutu agun ,dak'yar Na sha,kaga kuwa abin tausayi harda wata yarinya dana gani

 agun  sai karakaina take tana neman iyayenta kawai sai yarinya  ta dinga bina tausayinta yasa Na d'auketa abin mamaki munzo nan Daga sauka din na sauke  yaran can na duba bangan taba".


"Allahu Akbar Allah ya k'ara kiyayewa" sarkin kasuwa  yafad'a Yaran nan su hud'u malan lado ya mik'awa Sarkin kasuwa da  bashi dubu d'aya kan akaisu Police station da ke cikin garin bunkuren ko za asamu iyayensu , sarkin kasuwa yace wa wani d'ahiru ya rik'e yaran ya basu abinci shida MLM lado suka hau dube-duben neman yarinyar nan ,Amma basu ganta ba ,nan suka dawo lokacin yaran Sunci Sun sha MLM lado ya deb'e su sarkin kasuwama ya shiga motar .

    

Sun fita titi caraf idon sarkin kasuwa ya gano masa yarinyar nan gefen titi da Rabin bread a hannu tana ci tana kuka,yace "hala dai ita ce waccan"?  Malam lado yace "ita ce" direct motar ta tsaya suka fita abin tausayi 

jikinta zafi zau suka d'auketa,sunje police station suka bada yaran kan b'atansu a dalilin tashin bomb d'in ,sunayensu a ka d'auka da hotuna,da yake gidan sarkin kasuwa anan yake yasa aka bar yaran a gidan nasa,su kuma 'yan sanda suka hau sanarwar neman iyayensu. malam lado ma ya tafi kan duk yanda akai  Skasuwa  ya Sanar mai.

    

    

    *by Queen meemi*




. . January 2017 Queen meemi

⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣2❣



*©Mymouner Basheer*



*®NWA*

    

    

    *Queenmeemi.WordPress.com*

    

    

 wajen yamma MLM lado ya je gida a gajiye shigar sa gida ya Tarar da gwamma na tsinkar zogale d'agowa tayi tace ''MLM Yau kayi nisa da yawa" ,ruwa ya d'ebo a randa ya sha San nan ya zauna atabar mar da gwamma ke kai,yace "ai Yau munsha da k'yar nan ya labar ta Mata dafe k'irji tayi "kai Amma ka auna arziki' ,dama naji labarin birni bai shiga ta Dad'i, gashi yazo garin nan yanzu" alamar jimami ne fuskar sa,yace "ai kede bari gwamma Allah ya kyau ta dai" kallonta ya kumayi "wai Ni ina jummai ne"? tab'e baki gwamma tayi "ai kasan ayawoma ce Sam bata zama agidan nan muddin kasa k'afa ka fice".murmushi yayi don inda sabo ya Saba da halayen gwamma wajen yiwa jummai sharri,sallamar jummai ce ta katse musu hirar da harara gwamma ta sauki jummai da murmushi d'auke a fuskar jummai ta tsugunna tace "malam Barka da dawowa ,naje gidan kaka ne gaida ita Batada lafiya" nan yace bakomi jummai nasan da dalili ai " gwamma tace "tab! Lalle malam ka sakarwa jummai da yawa ace Mata ta fita bada izininka ba, Amma bazakai Mata fad'a ba,ita ga matar so" tashi jummai tayi ta d'auko kwanon abincin malam ta aje mai da ruwa daya ke itace da girki Yau, nan ya hau ci dama yunwa ce ke cinsa.

    

    

    

    

   *BAYAN SATI D'AYA*

                    

    

MLM lado na zaune a soro yana jin radio domin tun lokacin da bomb ya tashi bai koma cikin gari lodin kaya ba, don yaji labarin wajen ansa masu tsaro , kuma gashi saboda tsoron karyaje tsautsayi ya afka dashi, sallamar sarkin kasuwa ce ta katse mai jin radio d'in da yake da fara'a ya zauna suka gaisa mudi D'an MLM lado  mai kimanin shekara goma ya kawo mai ruwa,sarkin kasuwa yace "wato MLM lado yaran nan cikin ikon Allah duk anga iyayen su biyu a asibiti akaga nasu iyayen sauran kuma duk yan uwan su ne suka karbe su duk ta dalilin faruwan tashin bomb dinne yara suka bata ,kuma duk Daga wani garin suke,wani hanzari ba gudu ba ,yarinyar nan Sam! ko alamar wanda ya Santa ba agani ba balle su zo",gaban MLM lado ne ya fad'i cike da tausayi yace "ikon Allah yanzu ya za ai ke nan sarkin kasuwa yace ai police sunce mu rik'eta agunmu zasu cigaba da dubawa gashi Ni kuma zan tafi garin gabas jibi" ,mlm lado yace "to ai ba matsala ka kawota gurina muga yanda Allah ya yi ,haka sukai sallama ya tafi.

    

    

    

         *WASHEGARI*

                  

 wajen k'arfe goma sha d'aya saiga sarkin kasuwa nan da  yarinyar suna tsaye sai ga Shi ya fito musabaha sukai da Shi nan yace "to MLM lado gata nan godia malam lado yayi mai ya tafi Shi kuma ya d'auketa suka shige ciki.

 

      

 gwamma na hura ice jummai kuma na tankad'e MLM lado ya shiga kallo suka bishi da shi ,murmushi ne Akan fuskar sa gwamma tace "malam wan nan yarinyar fa"? ,kallonta yayi yace "Dad'i na dake wutar ciki, to 'ya na samu" nan ya kwashe duk yanda abun ya faru ya gaya musu jummai harda kuka saboda tausayin yarinyar gwamma kuwa tace "to rik'eta zakai kenan"! MLM lado yace "to ya zanyi Allah ne ya had'ani da ita" nan ya kalli jummai yace "ga 'ya na kawo miki ki na Kula da ita, kafin Aga iyayenta,da murna ta karb'eta dama bata da yaro tun lokacin da yarta hansai ta mutu har yanzu bata K'ara haihuwa ba,kallon yarinyar tayi tace "ya sunan ki ,batai magana ba sai D'an motsa baki da tayi,malam yace "kinga jummai kisa Mata suna na wucin gadi sai ana kiranta dashi kan Aga iyayenata".

           

           

   "MLM zan ce Mata hansai sunan marigayiya",gwamma tace "Amma ke kan jummai anyi solob'iyo    ayi dai mu gani Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i" MLM lado yace" kinga gwamma ban San neman magana tunda bake na bawa ba baruwan ki" tab'e baki tayi ay ba tun Yau nasan kafisan jummai dani ba ,me zanyi da tsintacciyar mage, nan ta buga cinya ke kuma jummai dani kike zancen".......   

   

                                                                                                                                  *By Queen meemi*

   



[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣3❣

           *Jan 2017*



*©Mymouner Basheer*




    *®NWA*




   *Queenmeemi.WordPress.com*

   

       

   

haka jummai ta d'auki hansai  ta shigar da ita d'aki ta fito ta D'ora Mata ruwan zafi tayi Mata wanka San nan ta wanke kayan ta ta shanya, d'akin nata dake d'auke da azara ta shiga da  hansai ta ajeta, tana na zaune tayi zuru nan ta d'aura Mata zani ta bata abinci ta ci,gwamma ce ta shiga d'akin "to gulmamma sai ki fito ki tuk'a tuwon da miyar" jummai ta d'ago "to yaya gani nan" madafar taje ta duba kayan kad'I bata ga kuka ba, nan ta fito tace "yaya ina mudi yazo ya sayo kuka" gwamma tace "ke bazafa ki  ta kurawa yarona da aike-aike ba,yanda kika Saba fita sai kije"  haka  jummai ta d' au mayafi ta shiga Mak'ota siyaowa

  

  

bayan fitar ta, gwamma ta shiga d'akin jummai, hansai na tsugunne tana rawar d'ari tsayuwa tai  ta k'ura Mata Ido "oh malam da kwashe -kwashe ko ina ya kwaso wan nan yarinyar oh" d'aga  kai hansai ta kalle ta gwamma tace "ke Maida idon ki k'asa wa yasani ma ko mayya ce ke" wani kwano ta dauka ta fita dai-dai lokacin jummai ta dawo nan ta D'ora girkin ta shirya hansai.

  

  

        *MALAM LADO*

               

malam lado asalin sa d'an nan garin bunkuren ne  yana zaune anan mangalu d'in ne tun iyaye da kakan ni ,su uku ne agun iyayen su, Daga Shi sai k'anin sa sai k'anwar su wanda duk  suna garin suma da iyalansu,yana sana'ar tuk'in mota yana lodin kaya zuwa gari- gari,gwmma itace matar sa ta  tafari haladu shine d'ansa na farko da ita Amma Allah yayi masa rasuwa sai mudi da aka haifa bayan haihuwar sa da shekara uku ya auro jummai, zaman lafiya suke yi farkon kawo jummai Amma bayan samun cikin jumman, sai gwamma ta uzzura Mata ta tsangwameta ,Allah yayi gwamma da fad'a ga San girma da son komi ace itace  a kai ga k'yashi ,batak'i ace jummai tana mata biyayya ba don ma malam tsayyye ne shiisa take D'an ragawa jummai bayan haihuwar jummai shekarar 'yar ta hansai d'aya  aduniya tace ga garinku, tun Daga time d'in bata kuma samin ciki ba.

  

  

 wan nan dalilin ne yasa gwamma ke shuka Mata tsiya Musamman wajen aike sai dai taje da kanta badai ta aiki mudi ba, hakan yasa take lullub'i ta tafi da kanta ,inkwa aka samu mudi yaje aiken to sai ta bashi kud'i wan nan ke nan.     

      *bayan wata d'aya*

       *karfe 8:00 da safe*

        

hansai ce tsaye bakin famfo jummai na k'ok'arin dafa Mata ruwan zafi saboda sanyin da ake ga kuma koko da take San damawa gwamma ce ta fito ta bud'e tukunyar ta kamfaci ruwan jummai ta d'ago "yaya fa ruwan wankaan hansai ne fa ,kuma Dana koko".

  

gwamma ta juyo da harara Akan fuskar ta, "na d'iba d'in mudi ne ke San wanka Yau kwanan sa hud'u bai ga ruwa ba, don zakiwa wan nan figaggiyar yar shine zaki magana kan na d'ibarwa D'an gida,koko kuwa dole ki dama"   tsaki tayi afujajan ta yi hanyar band'aki.

  

jummai bata ce komai ba sai ma d'aukan hansai tayi ta Goya ta ,malam dake fitowa da buzu ahannunsa zai je soro ya tsaya yace "kaga jummai da yar ta" murmushi tayi tace "wallah MLM gata da hak'uri sai dai tana yawan cewa wai mamma da dady" ,alamar tausayi ne a idon malam yace "Allah sarki, wallahi kullum naga yarinyar nan sai naji k'walla a idona saboda nasan duk inda iyayen ta suke basa hayyacin su" ,jummai tace "Allah dai ya sa agansu. MLM yace "ameen" nan ya fita ,sai wajen 11 hansai ta samu wanka.

    

lokuta sunja haka watanni Yau kimanin watan hansai shida, Babu amo ba labarin iyayen hansai haka malam yace yaji ya Gani zai rik'e ta amana son yarinyar yake kamar me komai ya samu itace nan ta koma cemai dady duk ganin sa take shine ba banta haka jummai tamkar 'yar cikin ta nan tace tana ce Mata inna sosai - sosai yarinyarta ware,ganin irin kulawar data ke samu  nan gwamma ta kuma tsanar hansai ko gunta bata San zuwa da taje zata kwad'eta tace tafi can tsintacciyar mage mudi kuwa cin zalinta yake shiisa bata zuwa inda yake.

    

    

haka dai rayuwa taci gaba da tafiya da k'alubale da dama Yau ga hansai nada shekara bakwai ahanun goma a hannun malam lado wanda in aka had'a da shekaukun ta shekarar ta goma kenan,hansai ta zamo yar da suke so kullum tashin duniya MLM ya kalleta sayya ji kamar yayi k'walla, (haka ake San bawa mai yawan tausayi)  wanda ta zamo jinin jikin jumai da mlm.

      

Sallama hansai tayi ta shigo da Allo ahannunta ta dawo Daga makarantar Allo ta dawo ta yamma. Nan taci karo da mudi take ya kai Mata mari wasu wuta ta Gani nan ta durk'ushe tana kuka gwamma  dake b'arar gyad'a tana watsawa abaki tace "kayi min dai- dai ita  ba Mara kunya ba, wai waccen munafukan marik'iyar taki itace ke zugaki har Kina had'a hanya da mudi" ,jummai tace "Haba yaya yanzu ai bai Dace ba kamar mudi yayi Mata wan nan Marin,saboda  ai kwarin su d'aya ba", gwamma tace rufen baki  mai rik'on wahala tashi tayii ta janyo hansai ta mik'ar da ita, had'a Ido sukai da gwamma  nan ta yiwa hansai dak'uwa, "daina kallona da Ido kamar gujjiya".

      

 d'aki suka shige jummai tace "hansai ki hak'r kinji mamanki  gwamma  ba wai sanki ne batai ba, kawai haka take" ,hansai ta jin-jina kai "ai inna na sani" Amma azuciyarta Sam tarasa mesa gwamma ta tsane ta.

      

  Zama tayi tana tilawar karatun ta, jummai ce ta shigo rik'e da rubutun tsari tabawa hansai ta shanye wanda kullum sai an bata ko Tai Mata tofi aruwa ta sha ,yanzu izifin hansai arba'in, domin malam ma yana da sani dai de gwargwado yana koya Mata.

        

Akwai wata makarantar boko a bayan gari ita hansai ke tafiya tana aji d'aya 2 na fimamare duk da yaran garin basa zuwa karatun, a ajin  nasu basu fi su goma ba domin wataran ma a bakin bishiya suke zama ahakan hansai ke dagewa domin wataran malam shike takawa da k'afar sa ya kaita San nan ya dawo ,yana so tayi karatu koda secondary ne daya ke malam nada wayewar ilmi sabili da yawan tafiyar sa ,mudi kuwa Sam baya San karantun shiisa inaga shekara d'aya kawai yayi yana zuwa ya daina Shi isa MLM ya turashi gona da yake malam  yanzu baya tuk'in motar shiisa ya koma gonar.

     

 hansai kuwa duk lokacin da jummai Keda girki to tare suke yi, tana koya Mata shiisa jummai bata da damuwa kokad'an, ga tsafta sabili da jummai na da tsafta shiisa hansai ma ta tashi cikin tsaftar Sam bazaka ganta futu-futu irin sauran yaran kauyen ba,sai ka d'dauka sune asalin iyayen ta saboda kulawa.

  

      

ganin hakan yasa gwamma ta bud'e huta kan sai hansai ta dawo hannunta, jummai bata iya fad'a ba, Amma aranar tace Sam bazata bawa gwamma ba ,malam dake shiga  gidan ya shiga yace "Haba gwamma yada haka bakya tunanin lalurar dake jikin ki" nan ta fasa kuka ,"ai MLM dama nasan kafi San jummai shiisa ganin hakan yasa ta samu damar yimin habaici,wai tana da yar huce takaici lo bata haihuwa" don na rok'eta kan hansai ta dawo hannuna saboda cikin dake gareni yanzu ban iya komai shine ta bud'e min wuta" .

    

    

jummai kuwa in Banda kuka ba abinda take saboda tasan k'arya ta Mata. MLM yace "duk hakan bata taso ba, naga hansai ko agunwa take, wata zata iya sata Aiki, to meye abin tashin hankali" gwamma tace "nikam malam ka bani hansai kawai idan ana San zama lafiya ta dawo guna kawai" . Malam yace "Haba gwamma ki zama mai adalci mana sai da kika ga yar ta fara zama mutum San nan kizo kice a baki? bayan ga wanda taci kashin ta".

gwamma ta shige d'aki tana kuka jummai tace "malam na yarda ta koma tunda nasan ba rabuwa Mukai ba", k'ank'ameta hansai tayi ni inna nafi San gunki". MLM yace hansai 'yata ki koma gun ta kinji kan ta haihu Kinga k'ani zaki samu", saida jummai ta lallasheta San nan ta yarda.

da gudu taje soro tana kuka innar ta kawai take so Sam bata san gwamma Amma ba yanda zatayi dole ta koma

tunda ma suna tare.

     

     *BY Queen meemi*

     

         

        

        

        

        

        

.

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣4❣

     

*©Mymouner Basheer*

  *®NWA*

*Queenmeemi.wordpress.com*



  _Salamu Alaikum fans masoya littafina ina mik'o gaisuwa gunku,na gode da kulawarku_

  


        *Sati biyu da komawar hansai dakin gwamma*

        

komawar hansai d'akin nan gwamma ta shiga takura Mata da  tsangwama. kullum cikin aiki ada hansai Sam bata zuwa rafi Ko yo itace domin jummai bata saka ta koda deb'o ruwa ne Amma gwamma da gayya zata aiketa deb'o ruwa Ko ita cen sabili da malam baya so.

yau ma da ake rura uban sanyi wajen k'arfe takwas na safe,hansai na kwance tana barci gwamma  ta d'akawa hansai duka  tare da kai Mata hauri ,firgigit ta tashi tana zare Ido, da k'arfi ta fad'a "inna" jummai dake zaune tana gyra  ta mik'e ta fito tsakar gidan a tsaye ta  tarda hansai,na rawar d'ari da botiki  a hannu,gwamma ta fito "ke hansai tafi rafi" jummai tace "haba yaya ina hansai ina zuwa rafi" .


tsaki gwamma tayi  "to munafun- fun yara nawa suke zuwa rafin, su dama suke "yan gida balle ita tsintacciyar mage daba galihu gareta ba" ,tsawa tayiwa hansai tace "shige muje Ke Kuma," haka suka yi hanyar soro gwamma tace saura ki Dad'e ga su tsahare can za su je".

nan ta dawo ciki har lokacin jummai na tsaye nan ta kalli gwamma tace.

 

 "Amma yaya kin San dai hansai tafi k'arfin tsintacciyar mage Wlh hansai agarin nan bata da maraici, malam da zai tafi rano sai daya jaddada kar a Aiki hansai rafi Amma kikayi sabili da kinsan gurin ba tsaro".

   

"lalle jummai wuyanki ya isa yanka, ina fad'a Kina fad'a Ko? ,to kisani yanzu hansai ba a hannunki take ba sai yanda na yi da ita Wallahi".

   

 jummai tace "yaya hansai 'ya tace domin jinta nake har b'argo na don haka ina nan bazan bari ta cutu ba, domin Amana ce awurin mu .

 tsaki gwamma tayi tace "JUYA Kawai"littafin Feenaat ja afar) San nan ta shige daki jummai da rai sakato ta juya cike da jin haushi sa b'acin rai na kalmar juya data kira ta.

    

    

    

    *Hansai*

    

 tun fitar hansai take kuka nan taja birki kusa da wata bishiya ta zauna ba yaran data ga ya fita iyan zu sai ita, saboda yanda ake sanyin nan, ga rafin da nisa tashi tayi ta hau gudu cak! ta tsaya ganin cakau sunan wata akuya ce mai tunkuyi a garin k'ahonta cako- cako data ga yara Mata zata bisu tana tunkuyi, jikin hansai bai Dena b'ari ba gudu tasa akuyar ta hau binta.

Muntari dake tawo wa ya tsaya cak! take ya kori akuyar ya kalli hansai yayi murmushi "kema tsoron cakau kike"? "Eh wallahi agaba na ran nan ta fasawa d'ahiru hannu" murmushi yayi keba k'anwar mudi bace"?

"eh nice" ta fad'a a tsorace .

"Ina zaki"

"rafi zani d'ebo ruwa"d'aga kai yayi yace  "kai da sanyin safiyar nan, duk yaran ma ban ga kowa ba ana sanyi fa.

muje na rakaki"haka suka je ya d'ebo ruwan ya d'auko mata suka juyo yana rik'e da botikin har ya kaita k'ofar gidan su ,San nan ya koma.

 

tana kai ruwan ta koma ta fara hura wuta gwamma nadaga d'aki tana Shan koko yunwa duk ta ishi hansai sai data gama San nan ta bata koko da k'osai biyu tasha ,gyangyadi ne ya kama gwamma nan hansai ta sulala tayi d'akin jummai(inna) tana zuwa ta kwanta kusa da ita suna ta hira ta K'ara Mata abincin taci.

ji tayi an kai Mata shuri gwamma ce tsaye tace "Ke hansai wancen wankin nawa wazai miki ehe"?

idon hansai ya kawo ruwa tace "mama gwamma bazan iyaba sunyimin nauyi"

 

dundu ta kai mata "Dan gidanku a banza zamu na baki abinci ina lefin rik'on da ake mike, tashi kona masge ki" hansai dake shiga rud'ani duk lokacin da gwamma tace Mata rik'on ta suke, Ko tace Mata tsintacciyar mage,sai taita tunanin kodan tsanar da rai Mata ne yasa take Mata hakan, tashi tayi tana matse hawaye,

 

jummai ce tace "yaya kawo wankin nayi saboda hansai bazata ita ba" .

 

"oho can ta matse miki jummai nidai Naga kaya awanke dan me nace ta dawo d'aki na" .

 

wani uban wanki ne ta tulo jummai ta jin-jija kai tace azuciyan ta,  ran nan inaji mudi yace bazai Mata wankin ba ,Amma da zalunci yarinya k'arama ace ita zatayi wan nan uban wanki, haka tayi wankin nan tayi  ta shanya .

 

 

    *Washegari*.

    

washegari malam ya dawo,sunyi murar dawowar sa  yayi farin cikin ganin hansai da dare yana zaune suna hira ya fito da wani takalmi me kyau irin na roba me ado ya bawa hansai yace "ga tsarabar ki" nan gwamma tace "ina na mudi" kallonta yayi "haba gwamma ya kike haka ne? inaga mudi saurayi ne mai zan bashi in Shi bai bani ba? hansai kwa yarinya ce"

 tabe baki tayi  tace "ayi dai mu gani"

 

 tunda malam ya dawo ta daina aiken hansai rafi sai de aikin gida duk ta fige ta rame ran nan malam ya shiga gidan yaga hansai na wanke kayan gwamma kwalla kiran gwamma yayi ta fito yace "yanzu don rashin imani har hansan nawa take da zata wanke manyan kayanki, ina mudi ai shi ya kamata yayi" gwamma tace "ita nayi niya haba! sai kace 'yar gwal ba dangin iya ba na baba".

 

malam yace d'a  de ai na kowa ne hansai de 'ya tace  ina k'aunar hansai har raina kamar yanda nake son mudi, don haka  karki Kuma sata Aiki me wahala . k'walla kiran hansai yayi yace  taje gun jummai ta zauna Ko taje waje tai wasa da tsahare.

Ahankali ta fita taje can waje ta zauna tana ..kubiyoni.

  

  

  

  *by Queen meemi*

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣5❣




*®NWA*




*Queenmeemi.WordPress.com*


       _*sadaukarwa ce ga Bashir usman family's*_

        

        

    _sis Marwa Phart bb ,Anty maijidda ,Nazifa Ngd Ngd sosai da kaunar book nawa,San nan  'yan group Dina na QUEEN MEEMI FANS ina godia da kaunarku agareni sosai kuna nunan kauna nagode Nima ina sonku luv u_

        

        *****

tana zauna tana kuka Muntari dake tawo wa Daga can ya ganota yazo kusa da ita yace "hansai meya sameki"? da sauri ta share hawayen daya zubo Mata Babu komi ta fad'a juyar Dakai yayi tabbas yasan da matsala can k'asan zuciyar sa yana tausayin hansai Ko acikin yara bata da kuzari ,"kina jina? kiyi hakr kinji yanzu ya makaranta?" ya tambayeta bata bashi amsa ba sai ma d'agowa da tayi ,yace "Ko bakya zuwa kema? kin zama su tsaharen?" da sauri tace "Aa ina zuwa ajina 4 a firamare Yawwa hansai ki dage Kinga Matan garin nan basu damu da zuwa ba, har mazan ma, ki dage kina zuwa  ki zama gwania acikin su," tace "to" yace "San nan kullum kina zuwa gun sahura (kanwar sa) ina koya muku karatu," Dad'i ne ya kashe ta tace "to" mangwaron dake ledar hannun sa ,ya zaro ya bata ta amsa tana mai murmushi.     

                

                                                                                              Muntari D'ane agurin mai garin ,garin mangalu a gidan su shine d'a na uku a ciki yayansa duk Mata ne sai maza kannen sa da Autar su mace,matashin saurayin k'auye ne D'an shekara goma sha takwas Allah yayo Shi da San karatu duk gidan su Shi kad'ai Ke zuwa, har ya kammala firamaren sa ,ya shiga secondary ta maza yana aji biyar ,duk k'auyen Ko acikin Samarin ya fisu ilmi ga kirki,tun ganin sa da hansai yake jin tausayin ta haka kawai ba don komi ba, hakan shine farkon alak'ar su da hansai.     

        

                                                                                             Bayan kwana biyu a tsakani yau ma MLM ya fita gona gwamma ta aiketa rafi wajen k'arfe hud'u na yamma ta d'au botikin ta tafi ,da d'an nisa sosai haka taje zuwan ta rafin taga yara birjik.Daga gefe ta tsaya tana d'iban nata ruwan ,wata Daga cikin su tazo taja kan hansai "Ke waya baki izinin d'iba,? bayan Kinga ana fad'a" hansai tace "to ni meye ruwana daku" fitsararriyar yarinyar tace "to duk nan na Riga kowa zuwa Kuma ba wanda zai d'iba sai ni" ,hansai tace "tabdi" kande tace "hansai sahura fa yar gidan mai gari ce fa!".

                                                                                       

                                                                                             hansai bata saurare su ba ta d'iba ta juya, jitai an jefar da botikin juyowarta, taga sahura na huci hansai zatayi magana sahura ta kamata da fad'a ,da yake sahura tafi hansai k'arfi ta jefar da ita a k'asa ,santsin k'asar gun taja ta tajita cikin rafi ,tinjim! kake ji k'arar fad'awar ta,Yaran gun duk suka saka ihu idanuwa sahura suka Rena fata,hansai kuwa sai ihu take duk tasha ruwa dai-dai lokacin Muntari ya taho yana zuwa yace "Ke sahura haryanzu aikenne? ga inna can na nemanki,"ganin suna kuka ya tambaya dije tace "sahura ce ta wulla hansai rafi" a kid'ime ya yi wajen ya ganta har ta daina motsi cikin ruwan ya shiga ya d'auko ta, ya fito da ita gefe yaran duk suka zagayeshi ya danna cikin hansai ruwa sai fitowa yake Amma duk da hakan bata farfad'o ba. haka ya d'auketa yaran suka bishi abaya duuuu.    

                                                                                              

                                                                                                          malam dake zaune sai fad'a yake "bana ce adaina aiken hansai rafi ba,? haba gwamma mai sa bakyaji ?gwamma dake zaune ta had'e rai "haba mlm "wai duk yaran garin nan tafi su ne? da za'ace bazata ba",mlm yace "eh tafi su ,ace tun k'arfe hud'u har yanzu shida dai- dai Babu alamar ta" ,jummai tace "malam Nima hankalina bai bani lafiyaya ba" . 

                                                                                                          

                                                                                                                                                                                                                                       Sallama aka doka mlm ya amsa Muntari ya shigo da hansai a hannu jummai tace "la haula ,mai ya sameta Muntari ? yace "ai fad'a wai sukai a bakin rafin itada sahura, shine ta fad'a rafi" kuka jummai tasa ta k'ank'ame hansai, mlm yace "Muntari na gode sosai" bayan fitar sa ya dawo kan gwamma "Kinga ABINDA AKE GUDU (littafin batul mamman) ko, gashi kin gani dai Ko"! d'aki ya shinga ya fito da magani yasa a raunin hanun ta da k'afar nan yasa jummai ta D'an gasa jikin hansai ,haka dai sukayi ta treatment d'inta sai wajen k'arfe Tara ta farfad'o tana kuka yau a d'akin jummai ta kwana.

                                                                                                                                                                                                                                       

                                                                                                                                                                                                                                        Washegari dak'yar ta taka, saboda yanda k'afarta Ke ciwo ,sai da aka gasata da ruwan zafi San nan ta samu sa'ida ,muntari ne ya shiga shida sahura da leda a hanun yayi ya jikin hansai, San nan ya  umarci sahura data bawa hansai hak'r badon Taso ba,  suka tafi.

                                                                                                                                                                                                                                        yau 3 kwana kenan, kullum Muntari sayya zo duba hansai Kuma yazo ya jata da hira shak'uwa ce sosai ta shiga tsakanin su sosai bayan warkewar ta sai Muntari Ke zuwa yana biya Mata karatu irin su hadisi sira ,kawa'idi,alkurani,da tauhidi. (da yake da da yake D'an karami Dan shkear goma ankai Shi makarantar almajirai yayi shekara daya sai aka dawo dashi ya shiga boko Kuma daya dawon ya cigaba da d'aukan karatu gun malamin makarantar Allon su hansai).

                                                                                                                                                                                                                                        

                                                                                                                                                                                                                                        haka ya fara koya Mata da amincewar mlm, ba haka gwamma taso ba, don  yamma k'arfe 4 yake zuwa asoron gidan su hansan,yana da k'wak'walwa sosai haka ya Farai Mata harda na bokon, kullum Kuma sayya zo da kayan k'walam ya bata .Daga baya ma sai sahura tazo shima ya had'asu yana koyawa,haka dai rayuwar hansai ta kasance yau fari gobe baki,cikin wata safiyar laraba gwamma ta haihu ta samu mace tunda ta haihu bayan anyi suna yarinya taci suna khadija suna kiranta dije, sai ya za mana duk wani Aiki hansai akeyi wanda ma yafi k'arfin ta ga yawan dukanta da mudi keyi yayi tai Mata wasan banza sai de inta ganshi ta gudu d'akin jummai.  

        

        

                                                                                                                   *BAYAN SHEKARA HUDU*     

        

        

                                                                                                 wani busa Ke tashi a tsakanin duwatsun dake wajen hansai Ke busa Shi tana murmushi taci irin kwalliyar su ta k'auye Masha Allah hansai ta K'ara girma kyanta ya dad'a fitowa duk da ban tab'a suffanta muku ita ba .

                                                                                                   hansai 'yar farar yarinya ita ba irin gau d'in nan bace, ita Kuma ba za a kirata bak'a ba tsaka -tsaki ce'yar lawai-lawai bata da kib'a sosai sai de Allah ya horema ta kuturi(hips tun ma bata K'ara girma ba Ke nan ,shiisa jummai take bata hijab tasa domin tasan tana da baiwar da daukacin Mata Ke so,Kuma hakan shine ya kamace ta duk da yaran k'auyen kamar ta wasu basa yawo da mayafi.

                                                                                                     Sam hansai in ka ganta bazaka ce zatayi k'arfi ba komai a sanyaye ta keyi, siriryar fuskarta wadda Allah ya wadata ta da Dan dogon hanci siriri da bakinta madaidaici sai gashin Ido da suke gazar -gazar dogwaye tamkar tasa eye lashes ,idan ka kalli jikinta duk gashi ne ajiki sai de bata dayawan gashi kai tana da de na fakin Amma gaban goshin ta cike yake da gashi a kwance luf-luf hansai Ke nan😉

                                                                                                     Muntari dake saman bishiya yana murmushi Shi kad'ai ya d'ago da idon sa, "Anya hansai duk k'auyen nan A kwai me kyanki kuwa"? dariya tayi "haba dai ka dad'a bincika yace to ni dai masoyiya ta tafi kyau,tun bayan shekara d'aya kenan suka fara soyayya shida hansai wanda kowa ya sani agarin, kullum nan ne wajen hirar su cigaba tayi da busa usur d'in .D'an dogo wa tayi ta kalli saman bishiyar lokacin muntari ya juya, kallon Muntari tayi azuciyar ta tana sonsa, domin ya taimaketa arayuwa, ya Sanar da ita ilmi da yawa ya taimake ta sosai, magana yayi firgigit ta dawo Daga duniyar data tafi tare da jin kunya da gudu tayi hanyar gida .......

                                                                                                    

                                                                                                    

                                                                                                    

                                                                                                    

     *By Queen meemi*

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . .

⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣6❣

        *JAN 2017*


*®NWA*



*Queenmeemi.WordPress.com*


       

*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usaman family's_*



              *ABUJA*

                               

A fafare Zuby ta shigo da motar ta ta faka a tafkeken filin  gidan su.

Ruby dake bayan motar ta fito a zafafe suna hararar juna kowacce d'auke da jaka sukai ainihin cikin gidan  wanda Ke d'auke ta kafcecen falo, wanda Ke d'auke da  K'ofar shiga part guda hud'u falon dake tsakiya wanda yake a circle ga manya manyan kujeru na leda masu D'an karan kyau, d'aukacin falon an kewaye Shi da labulaye masu kyau, ga wani site dake yamma da falon an k'awata gun tafkekeiyar plasma ce awajen tana ta aiki,ga wani kuku na k'alk'ale tile d'in falon. 



Shigar su Zuby da Zuby kowacce tayi part nasu .Ko wacce ka shiga part d'in nasu wani falo ne shima again d'auke da kujeru lintsuma- lintsuma ga decoration me kyau a falon, sai plasma tv da dining area da kitchen San nan jerin d'akuna guda uku,kowanne part haka yake duk gidan,d'akin mama. Tashiga  ( hajiya khadija) tana zaune bakin tamkeken gadon ta, wanda ya malaye Babban d'akin ta zauna kusa da ita ,Mama tace "zuby har kun dawo"? "eh wallahi Mama gashi yunwa nakeji, sai de Kuma raina a b'ace yake" tayi tsaki ,"wallahi Mama wataran saina fasa bakin Ruby" Mama tace "haba Ke Bakya rabo da fad'a, Ruby ai kin San bada fad'a, dama Sumy kika ce ne da saina yarda".



 "Mama wai akan driving yarinyar nan zata min rashin kunya, dan taga itace babba,Allah ni banso dady ya had'ani mota da ita ba" ,dai-dai lokacin Sady ta shigo tana rawa mama tace "har abada dai Sady bakya rabo da shirme" sady tace "mama wallahi wak'ar ce da dad'i ,nan ta kalli Zuby  tace "ya zuby mai naji kina cewa ne? inde zan cen mota ne wallahi mu had'u muje ga dady Kowa a sai mai dai -dai, ta yaya za ace kamar mu Kowa sai ace su biyu ne a mota d'aya. jiya fa haka sai da Sumy ta lalato motar ta, bayan na hau tace ni na lalata har sai da umma tayi min fad'a"    


                                                                                                  Zubi tayi tsaki "gaiskiya Ya Ruma ta huta ita kad'ai da motar ta" ,mama tace "to sai kuyi hakr, ai ruma dai yayar kuce dole abata girmanta". D'an fita zuby tayi ta tafi Babban falo ta zauna tana kallo Rabia ce ta fito Daga nata falon itama ta zauna, Zuby tace "Anty Rabia ina gajia" batai mamakin jin yadda Rabia ta gaisheta ba tamkar ba matar baban su ba, "lafiya tace" ,da dai- dai da d'ai-d'ai Matan gidan da 'ya'yan suka fito sukai birjik a falon, gidan Alhaji tanko kenan.                                                                                                                                                                               .                            


                                                                                                                       Alhaji tanko Babban Dan siyaya ne, da yayi shura yana zaune a garin Abuja,yana zauna A maitama yana da kud'i na fitar hankali ,yana  d'auke da muk'amin minister na kudi ,yanzu hakan yana da matan aure guda uku Hajia khadija itace matar sa ta farko ,tana da 'ya'ya da Shi Rumasa'u (Ruma) itace babba sai Zubaida (zuby) San nan Sadiya(sady). Wan nan sune na b'angaren ta San nan Hajiya Karima itace matar sa ta biyu, itama tana da 'ya'ya da Shi Rubayya(ruby) itace babba awajen ta sai sumayya (sumy) itace Ke binta wan nan sune iya 'ya 'yanta, sai Amaryar sa daya auro shekara 5 kenan tana da 'ya'ya da Shi khalili shine babba sai Mubarak, duk a gidan Ruma ce babba mai shekara 25, sai Ruby mai 23 San nan Zuby mai 22  sai sumy da sady sa'annine suna 20 sumy ta bawa sady wata biyu,sai khalil Dan 4 yrs San nan mubarak Dan 2 'yan gata ne sosai suna jin d'ad'in su San ransu ga gadara   



                                                                                                                           

          *MANGALU*

                                                                                                                                       Shigar Hansai gida yasa gwamma ta kwad'o mata murfn kwano a k'afa take ta dafe gun tana kuka gwamma tace "wallahi Hansai zamusa k'afar wando d'aya dake,  kin gansame agari ba mai aurenki, duk sa aninin ki an aurar ,hatta ita tsaharen ankaita d'akinta  bara Amma Ke. Kina nan shekara goma sha hud'u god'ai god'ia dake duk ba sa aninnki sai wanda kika girma,kullum sai aukin sa hijab tamkar matar liman,Ke ga malam ya tsaya miki wai sekin gama makarantar gaba da furamare ake cewa kome, to ayi Dai mu gani duk ran da aka fara saka ki A wak'a ai maji,ni b'acen da gani kar na ballaki ki,na k'arashe k'afar, je ki min wanki",tana d'ingishi ta tafi jummai ta fito lokacin itama Allah ya bata ciki ta kusa haihuwa tace "haba yaya hansai fa tana k'ok'ari miji Kuma ai lokaci ne Kuma ai D,an gidan mai gari ne Ke Santa, kin ga kuwa ai lokaci muke jira" gwamma tace "ayi Dai mu gani ba" dije ce ta shigo 'yar shekara hud'u gwamma ta kamo ta tace 'yar lele ina kika je ?tace "rafi kamo kifi" ,da sauri ta rufe bakin ta jin muryar malam dake k'ok'arin ya shigo ,tace "Ke yi shiru kin san malam baya so yi maza shige d'aki.   

                                                                                                                                                

                                                                                                     Hansai da kafar ta keta jini  wajen da gwamma ta wulla Mata murfi,Daga gefe sai kuka take ga wunya dake d'ibar ta tace "mama gwamma zan d'auraye k'afata jini"  tace "Dan k'aniyar ki sai da kikaga malam zaki ce haka to bazaki wanke ba gulmammiya kawai" jummai dake kusa da ita tace hansai zo na d'auraye miki sai kici abincin," da gudu gwamma ta taso "Ke karki tab'a ta domin Salam munafinci",Malam dake shigowa yace "Aa meye haka nan kukayi cirko -cirko.

                                                                                                     

                                                                                                     

               

               

        *by Queen meemi*

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . . . . 






⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣7❣



*®NWA*



*Queenmeemi.WordPress.com*


*_sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_*


 _happy birthday  *MIEMIE BEE 👄*Wish u more years ahead ,GOD bless u🎉_

       ****

Sun tsaya cirko-cirko Malam ya k'araso yana tambaya da sauri gwamma tace "Aa magana muke kawai" hansai da kanta na sunkuye gwamma na harar ta MLM yace "Ke Kuma meye kike d'ingishi"? jummai tace "ai bigewa tayi" yanki ya d'auko ya bata ta d'aure gun yace ta koma gefe ta tafi tana d'ingishi,gwamma haushi tamkar ya kasheta ga wankin  da bata k'arasa ba kenan, domin tasan malam bazai K'ara fita ba tun daya shigo, haka ta duk'ufa tana K'ara sawa.  


                                                                                                      Washegari da jummai ta fita asibitin cikin gari Malam ya fita gona sai hansai da gwamma kawai ganin,hansai da uniform gwamma tace "Ke bazafa ki je ba, kizo ki d'eban ruwa"hansai tace baba gwamma yunwa nake ji" "baza ki ciba ki fita kawai wallahi"  haka ta aje jakar buhun dake hannun ta,ta d'au botikin ta fita sai sauri take har taje rafin, ba kowa agun sai wasu mitsi-mitsin yara acan gefe suna wanki d'iban ruwan tayi ta d'ago kenan ta ci karo da lawandi k'irjinta ya bada dam! tayi gefe, bin ta yayi yace "Ke hansai"! taki tsayawa sai sauri take fit! taji ya ja hijab d'inta nan ta tsaya yace "Ke hansai don baki da rabo ina maki magana Amma bakiji don ina sonki kikemin wulak'anci.

                                                                                                      

                                                                                                       tace "kayi hkr inada masoyi" yace k'arya kike da kina da Shi bazaki zauna Ke kad'ai a gari ba duk kamar Ke an aurar sai kace mai bak'in jini, koda yake wa zai auri yar tsintuwa" da sauri ta juyo "kadaina jifana da munanan kalamai saboda da iyayena dariya".yasa  dariya "tafi can ki farka tun dare bai miki ba" ,don ma zam taimakeki duk kyan nan naki ace ba mashinshini" tace "wallahi karya ne da iyayena malam da inna dariya yayi "kinsan dai ni abokin mudi ne, don haka ya gayan Kuma nasan bazai miki k'arya ba"

                                                                                                       

                                                                                                       fuu ta juya ya zata tafi ya   cafko ta nan  tahau ihu yace "bari na kwashi rabona tunda kince baki sona" k'ok'arin cire Mata hijab yake ta k'walla ihu dama kowa yasan lawandi a k'auyen bashi da mutunci shammatar ta yayi ya fisge hijab d'in ,kuka take sosai "kayi hk'r na tuba" jinjina kai yayi ya turza k'afafuwan sa a k'asa "gaki da kyan jiki Amma kullum arufe" hannun sa ya kai jikinta yaji an mauje hannun, Muntari ne Ke huci ya nuna lawandi "ka shiga taitayinka iskancin ka bai tsaya ba har akan budurwata, to wallahi duk k'auyen nan za'a jimu  Kanmu" mazga ya kaiwa lawandi take shima ya rama suka nan suka hau naushe -naushe da gudu hansai ta juya ta yi hanyar gida tana kuka



shigarta gidan ta tarar da jummai na tsintar shinkafa,lokacin bata Dad'e da dawo wa ba sai ta shige d'akin jummai tana kuka, cike da jimami jummai tajata tace "meya faru hansai"? nan ta fad'a Mata abinda lawandi yace da ita ,hankalin jummai ya tashi ta tuno lokacin da Malam Ke shaida Mata karta bari hansai ta San basu ne suka haifeta ba to waya gayama lawandi nan tayi ta lallashin hansai tace zata gayawa Malam .



Makarantar daba taje ba kenan ,gwamma ta shiga d'akin jummai tana masifa "bafa zan d'au asara ba dole a biyani botiki na" ,hansai tace "kiyi hk'r tsautsayi ne yasa ya fad'i ,fizgo ta tayi ta fito da ita waje ta hau jibga hansai na ihu jummai ta janye ta tana haki "wallahi karki Kuma dukanta gwamma don Kinga Banda lafiya shiiisa kwanan nan kike dukan ta" ,gwamma tace "jummai dani kike zancen wallahi sai kun gane kalata ta kwanan" nan tayi k'wafa ta fita. jummai ta kamo hansai suka shiga d'aki tana bata hkr.

    

    

Muntari da Lawandi kuwa sai da suka ji jiki San nan suka rabu lawandi yace saiya ga bayan Muntari inde akan hansai ne. Hatsaniya sosai sukayi har wajen mai gari ina waje d'aya ya Tara su lawandi da muntari na agaban maigari yace "kaga kai D'ana ne Muntari, kai Kuma lawandi kai Nike jagorantar ka meya had'a ku"? .



Lawandi ya furzar da huci yace "yarinyar dana keso wai ita yake so" maigari yace "wake nan"? Lawandi yace "Hansai ta gidan Malam". Maigari yace "ayyo na gane" nan ya juya gun Muntari yace "haba Muntari na san ka da hankali ya da fada akan yarinya"? Muntari yace "baba wallahi tin hansai na shekara goma muke tare, atambayi Malam ma da ita Hansai d'in.


nan maigari yace aje akirawo malam , yana gona akaje kiran sa ya tawo suka gaisa a soron gidan maigari d'in, yagan su nan maigari yace "Malam ya maganar 'yar wajen ka hansai"? cikin lawandi da Muntari wake Sonta malam yace "Allah ya gafarta Malam ai Muntari na sani tun da dad'ewa".

"To kai kaji lawandi cewar maigari sai kayi hkr, karna K'ara jin wani tashin tashina anan" .Lawandi dake tsuke baki ya tashi ya fita yana mai k'wafar kota Halin k'ak'a sayya samu Hansai


       

       

   *ABUJA GIDAN ALHAJI TANKO*

 Sady ce da Sumy sukayi shawarar zuwa gun dady .yana  wangamemen falon sa mai d'auke da kayan K'awa  ,Anty Rabia taci uwar kwalliya tana gefe tana had'a mai tea zuby ta zauna daga gefe haka Sumy ma  suka gaidashi " dady dama muna da complain akan mota wallahi yakamata ace kowa nashi dai-dai aka sai mai ,sady ta cafe "eh wallahi dady kullum baama jin Dad'i da sake wa ga frnds" har dariya suke mana A school" dariya dady yayi "har kun manta, Amma kafin na sai muku wan nan motoicin ai da kowa tasa yake hawa yawan yawonku ne yasa na had'a ku mutum 2 a daya".

   

  Sumy da alamar zaak'uwa tace  "dady pls wallah zamu gyara ,kamar mu big girls a School Ace muna had'akar motor" Anty rabi ta kalle su lalle su Sady sai na ga hakan yafi dacewa" Sumy tace ni fa bansan sa ido don dai ba su khalil aka ce bane Shi isa mutum zai sako eyes" tsawa dady ya daka musu Dan baisan atab'o mai rabi saboda sonda yake Mata yace "inde rashin kunya zakuyi to ba wacce za a canjawa" Sady tace sorry Anty tab'e baki Rabia tayi ta fice nan suka bashi hkr yayi musu alk'awarin kowa d'ai- d'ai sabbi .

   

da gudu suka fice direct public room d'insu dake Babban falon gidan ,inda nan suke zama da rana ,da rawar shoki Sady ta shiga Ruma da Ruby suna Aiki kan computer Zuby na checking phone d'inta, Sumy tace "yau sharr muke dady yayi alk'awarin new car kowa dai-dai take kowacce ta how murna.

   Zuby tace "wallahi saina rainawa su ramla hankali inde nayi sabuwar mota don aranar da dadyn ta ya bata new car har wani d'agan head take" "Allah yasa masu zafi zai bamu" inji Sady, Sumy tace "ai uploadin zan yi  a Instr su gani na basu surprise" tsaki Ruma tayi tace "ku yaran nan abinda ya dame ku kenan ko"? Ruby tace "barsu 3 month fa da canjamana mota Amma sun koma don tsabar k'arya" dariya suka sa dukan su.

   

   *by Queen MEEM*

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣8❣



*_Sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_*


 *®NWA*

 


*Queenmeemi.WordPress.com*


             *******

Misalin k'arfe goma na safe.Hansai na gefe a zaune tana dafe da cikinta dake k'ugi kallon d'akin jummai tayi taganshi da kwad'o don tasan ta tafi Asibiti.

gwamma ce Ke can gefe tana wak'e -wak'e sallama akayi delu ce Daga bakin k'ofa tace "gafaranku dai" .Gwamma ta washe hak'ora  "dele ce yau agari!.Gaskiya kinyi nisan kiwo",delu tace "wallahi sai jiya na dawo daga D'an lasan," zama tayi kan tabarmar suna hira ,d'umamen tuwo ne sai tururi  yake ta Matso Mata dashi. kuka Hansai tasa,gwamma ta juyo tace "au barin aikin kikaii"? sunkwi dakai tayi,nan suka cigaba da cin d'umamen da ita da k'awarta delu  suna ci suna shewa hansai ta tashi tace "mama gwamma cikina murd'awa yake yunwa nakeji".



Delu tace "tab lalle 'yar nan kin samu sake ,gwamma ai Naga saka cinki " "to ya zanyi bayan malam shike tsaya Mata" tulun wanke-wanken ta nuna Mata "jeki wanke min banza gansama mai bak'in jini" kuka tasa "au bazakiyi sauri ba! ,Salan malam ya dawo ya hau fad'a" cigaba da shewar su sukayi.



haka ta hau wanke wanken ,cikinta na hautsina sai Misalin12 ta gama lokacin ta gama galabaita ,San nan ta bata ragowar tuwon nasu. Delu tace "wai ni har yanzu ba Aga iyayen ta bane"?,gwamma ta tab'e baki gata nan, waya sani ma ko bata da iyayen". Delu tace "kede ki tashi tsaye don yanda Naga take taken sa sayya iya bata gado tun bai mutu ba, ai kina ban mamaki gwamma,duk kin sakwarkwace".



 Loma biyu hansai tayi duk tana jiyo su.Amai  ne ya biyo baya haka taita kwarara amai gwamma tazo ta tsaya kanta "munafuka kawai ,kima tsiyayar da kayan hanjinki, ni bai shallen ba,shaidaniya ai wallahi ko zan yawo tsirara sai kin bar gidan nan, har akanki malam bai damu da dije ba,da mudi"dundu mai  rai  tayi Mata hansai ta durk'ushe.Delu tazo zata fita tace "gwamma sai na jiki".

 

 

Wajen azahar jummai ta dawo.Hansai na gefen d'akinta a kwance tana kuka tana ganin ta ,ta rungume ta tace "inna ku gayan so biyu Ke nan Ana cemun Banda iyaye. don Allah ku sanar dani ,kuka ne ya kubcewa jummai ta bud'e d'akinta suka shiga .

 

 

Zazzabi ne ya rufeta ta kwanta, sai bacci sai  wajen la 'asar ta tashi tayi sallah ta fito tsakar gidan, taga Malam na Jan carbi da alama Sallah ya idar, da kuka taje ta sameshi "baba don Allah wai dagaske ba kune iyayena ba? kuka take saosai, jummai ta fito "Malam na rasa Inda hansai taji" ,hansai tace "mama gwamma ce Kuma ba yanzu ba, tun da dadewa,lawandi ma sai daya gayan,don Allah ku gayan ko na samu saida" ..Malam da idon sa yayi jajawur alamar bacin rai ya d'ago idon sa cike da tausayi ya kalli hansai,"tabbas bamu ne iyayen ki ba" tana zaune ta kwanta,nan ya cigaba bomb shine Sanadin rabuwar   ki da iyenki "nan ya labar ta Mata duk abinda ya faru, luuu hansai ta fad'i alamar ta suma.

 

 

 Nan suka yayyaafa Mata ruwa, ta farfad'o tana kuka ta rungume jummai tace "baba har Ababa kaine babana Gaskiya samun irinku sai an tona, baba ka nunan k'auna kaida inna insha Allahu zan cigaba da yi maku biyayya ,Wan nan rayuwar danayi daku itace dama wadda Allah ya shirya min,nikam banyi maraici ba.  Amma tabbas Nagd wa Allah daya wad'o dani cikin ku nagode inna da baba" cike da tausayi baba yace "hansai Allah yayi miki Albarka "jummai ce taja ta suka tafi dakin ta.

  

  

 fakam- fakam gwamma ta shigo gidan malam ya dakatar da ita,yace  "ki koma Inda kika fito gwamma tunda kin zamo mai karya Alkawari ,kin b'atan rai kije sai na neme ki,".Salati ta hau "yanzu akan yar tsintuwa shine zaka ce naje gida to ai shike nan zan dawo ai",nan ta d'aga murya" jummai wallahi kin tab'o gwamma sai na yi miki rashin mutunci,nasan Ke kika had'a gurmi".  

   

    *BAYAN WATA UKU*   

                                                                                                Bayan wata 3 dangin gidan su Muntari suka zo aka tsaida auren Muntari da hansai zo kuga murna gun hansai da muntarin duk tsiya hankalinta ya kwanta dalilin gwamma bata gidan. kuma gashi ta cigaba da zuwa makarantar ta,yanzu tana aji biyu na secondary dake cikin garin bunkure ,acan take zuwa ta dawo duk nisan ga muntari na k'arfafa Mata gwiwa.

                                                                                                 kwatsama cikin daren ranar juma'a jummai ta haihu ta samu d'a namji zo kuga murna gun hansai ranar suna aka samai suna Abdullahi ,suna kiran sa d'an jummaii,lokaci yana ta tafiya.  Har jummai tayi arbarin hansai Ke Kula dashi tana jin k'aunar sa.

                                                                                                

                                                                                                 Washegarin Arba'in d'in jummai sai ga gwamma ta dawo inda da k'yar da sid'in goshi malam ya maido ta.                                                                                                                                     Ganin yanda hansai tayi kyau abinta ya bak'anta ran gwamma, dama taji labarin auren su da Muntari nan ko ta d'au damarar yak'i da hakan muje zuwa.    

                                                                                                

                                                                                                

  *BAYAN KWANA 2*     

       *da yamma* 

                                                                                                                                                                                                            Tafiya hansai keyi tana sauri zata gidan sahura k'anwar Muntari ,lawandi ta gani agaban ta ,da sauri ta kauce lawandi yace "ki tsaya mana!, da gudu ta arta ya bita Allah ya ci da ita   taga wasu mutane akan jakai take lawandi yayi baya hamdala tayi ta tafi.

                                                                                                                                                                                                                                   

      *k'arfe goman safe*        

                                                                                                                                                                                                                           washegari mudi na zauna a d'akin gwamma se yau ya  ya shigo,satin sa d'aya bai lek'o suba ,gwamma tace "ai ni yanzu burina wan nan yarinyar tabar gidan nan",mudi yace "Yawwa ni akwai wani abokina lawandi yana Santa,kwanaki ai har fad'a sukai da muntarin" ai da hankali na bazan bari ta auri muntari ba,haka kawai saboda banso ta samu rayuwa mai kyau, kace gobe lawandi yazo" mudi yace "ba matsala".

                                                                                                                                                                                                                                   

                                                                                                                                                                                                                                   da yamma hansai na soro itada munatari yana Mata K'arin karatu gwamma ta fito da botiki ,cike da ruwa ta kwarawa Muntari tace "kai kam anyi Mara rabo, shikam dayake tsaye jiki na d'igar ruwa ,hansai kuma na gefe jikinta na rawa ta kalleta, tace "wuce muje 'yar banza" nan ta bita da dundu ,ta dawo kan Muntari tace "to kai yanzu karasa wa zaka aura sai 'yar tsintuwa 'yar daba asan iyayenta ba"?.

                                                                                                                                                                                                                                   "Amma ka bani mamaki ,kasan dalilin dayasa tak'i auruwa kuwa? to cikin shege tayo aka rufe a bun" idanuwan Muntari kam sunyi ja yace "haba mama gwamma yada jifanta da irin kalaman nan Sam ban yarda ba"  "to baka yar daba kenan? to wallahi da gaske nake" kansa ne yaji ya fara juyawa ya dafe shi yana waswasi.

                                                                                                                                                                                                                                   

                                                                                                                                                                                                                                   *by Queenmeemi*

       *Queenmeemi.WordPress.com*

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣9❣

           *JAN 2016*


*Queenmeemi.WordPress.com*


*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_*



 Nagode da bibiya @* *ummu yusra*, *Amiener* *Ngileruma ,Maryam* *Shettima,Ummie*  *Maryama Niger*

*khadija lagos &Ashnur tnks* ❤





Muntari baice komai ba sai ma waje daya yi gwamma 

"tace tafi can wallahi sai na rabaku".

komawa ciki tayi tahau wak'e- wak'e .


Mudi kam Bayan ya gayawa lawandi sak'on gwamma baiyi wata -wata ba sai gashi da sassafe .Bayan malam yafita yazo gwamma ta fito soro suka gaisa tace wa lawandi "ka ce kana son Hansai ko"? yace "eh to karka samu damuwa Amma kafin nan sai na saka ka Aiki. kuma kayi a k'arshe zaka ga yanda komai zai tafi dai- dai lawandi yace "ai ko ba so tsakani zan iyayi miki" nan tace "so nake ka d'auke Hansai kaje can wani wajen ka b'oye ta,kana jina"? murmushi yayi lallai fad'uwa tazo dai de da zama, ya d'ago yace "to yanzu yaushe za ai,? tace "ko yau ma, kaide wajen uku  kabi hanyar rafi zan ai keta yo jida".




Sallama sukayi ya tafi Misalin k'arfe uku gwamma tace wa hansai tazo tana zaune a bakin d,akin jummai ,goye da D'an jummai,  gwamma tace "Ke jeki sauke wan nan bushashen yaron," Hansai taje ta sauke Shi ta Koma wani k'aton buhu ta bata, "gashi so nake kije ki yo mini jida a gonar Malam kalla".Jummai na d'aki ta fito "haba gwamma kinsan wajen da nisa, kuma jida har me zata samo Bayan duk an gama", gwamma tace "bari kiji ko jiya saida lantana 'yar wajen larai taje yo kalen Dan baki ga gyad'ar data samo ba ,don haka dole Hansai tayo mini jida ,wallahi ko na kileta". Jummai tace bafa "zata je ba, gwamma tace "dani dake aga wa zai bi wani" wawuro ice tayi tabi Hansai aguje tayi waje da buhu a hannu .



Haka Hansai ta  santali hanya tiryan- tiryan, tana tafiya hawaye na bin kuncin ta,sai wajen hud'u da rabi taje ta hau kale Babu komi da k'yar ta samo kad'an tayi kwana tana sauri saboda gajiyar da tai ,ji tayi kawai an sure ta K'ara ta k'walla buhun ya fad'i ,wani dutse ta d'auka ta kwad'awa lawandi, tace "Amma kai kayi asara, ka rabu dani nace," binta yayi ta hau gudu ita da zatai hanyar rafi sai tayi wata hanyar da k'yar takai wani gida ta tsaya tana haki,ji tayi an rufe bakin ta' an d'aga ta sama sai ihu take Amma baya fitowa ,Mari lawandi ya faska Mata sai data ga wuta d'if ta some nan lawandi ya tafi da ita.   



                                                                                                  K'arfe bakwai dai de malam da jummai ne tsaye suna neman hansai, ba inda ba a duba ba. Amma ba alamar ta .Jummai kam kuka take hankalin malam idan  yayi dubu  ya tashi ,komawa gida yayi yace da gwamma "mai yasa ne kika aiketa kale? haba sai kace bamu da abin sawa abaka" malam sai hak'uri, Nima tun d'azu hankalina atashe yake" .

                                                                                                  

                                                                                                  

                                                                                                   Wajen takwas na dare sai ga Muntari ya zo zance ya gun hansai da wata leda a hannun sa, zuwan sa k'ofar gidan, ya tarar da malam a  tsaye nan suka gaisa malam yace "D'ana Muntari ko kaga Hansai"? a fargaba  ya d'ago "Aa malam miya same ta", malam yace "ai tun k'arfe 3 ta fita wai kale har yanzu shiru ba labari"  da jimami Muntari yake magana a gigice, "ina zuwa" malam ya  sanar da Muntari ya shiga ciki shiga ciki .

                                                                                                  

                                                                                                  gwamma dake lab'e ta fita soron tace "amma kwa Muntarii anyi sahorami, yanzu ba kaji abinda na gaya ma jiya ba ko? ka d'auka k'arya ne  ko"? Muntari yace "Ni ai ko ma mene Hansai tayi koda ta da wani batare da aure ba ita nakeso kuma zan aura  kuma haka nake santa ko da duk kowa zai ce baya sonta".Gwamma tace "ka rabu da hansai Muntar",  "mama gwamma hansai fa kamar 'yar ki take kina yi Mata zaton Alheri"

                                                                                                  "lalle Muntari ka fitsare ko girmana baka duba ba ,kake gayan wanga magana ,dani kake zancen dole ka rabu da ita" muntari da ya share zufa duk sanyin da ake alokacin Amma gumi yake saboda zafin da gwamma ta had'a mai yace*_"rabuwa da Hansai ,tabbas  zai iya zame min matsala,haka  Sanadin Rabuwa da ita zai jefami a mawuyacin hali wallahi Ita nake k'auna _* gwamma tace "tab! anya kana da kai, lalle dole ne na Ke gidanku" .da sauri ta fice don jin da yayi kansa na juyawa. Ledar da ya shigo da ita ,ta d'auka ta duba taga soyayyan kifi, "hmm da wan nan cimar zan k'yale Hansai ta aure ka ,inaji ina gani Hansai ta auri d'an maigari ta shiga daula ,ai dole na tashi tsaye ,ai idan yasan wata bai san wata ba.Juyawa gidan tayi ta shiga d'akin ta suka ci ita da dije.

                                                                                                  

                                                                                                    . haka Muntari yayi ta yawo baiga inda take ba ba inda baije ba, har wajen 9 na dare yana yawon nema harda k'walla don yanda yake jin Hansai a ransa.                     


                                                                                                                                                                                                                              

            ******                                                                                                                                                                  Al amarin hansai kuwa, bayan da lawandi ya sace ta bai zame ko ina ba sai wani gida wanda ba kowa a ciki sai wata tsohuwa ,aje ta yayi a d'akin tsohuwar ya d'ago yace "kaka ga ajiyata nan" dafe kirji tayi!" kai D'an nan yau ma jafa'in ka jawo? har ka fara satar bil adama". Lawandi yace "kede kaka ba ruwanki ki sa Ido kawai" fit ya fice daga gidan.

                                                                                                                                                                              

                                                                                                                                                                               Bayan fitar sa ,Hansai ta farfad'o ta hau kalle- kalle kuka ta kuma sawa, "na shiga uku wayyo baba, wayyo inna" ,tsohuwa tace "yarinya mai ya had'aki da lawandi"? Hanai ta kalleta "wallahi iya ,ya nace yana sona Alhalin an saka min rana da wani ,in dai zan fita sayya biyo ni, yau ma tsautsayi yasa naje jida ,shine ya d'auko ni don Allah kaka ki taimakan".

                                                                                                                                                                               tsohuwa tace karki samu inaga Allahu gobe zan bud'e ki tafi,ina kike" ta tambaye ta ,Hansai tace a mangalu"tsohuwa tace "ai bamu da nisa ma" dadi taji tsohuwa tace ta tashi tayi Alwala haka tayi ta dawo ta zauna.Tai tsuru-tsuru tana jimami.

                                                                                                                                                                               tsohuwa tace "ai lawandi kwai tak'adari wallahi tunb yana shekara goma nake fama, jika nane ni na haifi baban sa,babar sa tazo haihuwa ta mutu baban sa kuma ciwo yayi ya rasu, sai rikonsa ya dawo guna neman fada doke doke ba irin wanda bai ba daya fara girma ya tsiri dauke -dauke, har ya girma bai nutsu ba sai ma janyo fada wanda ya sha kwana gun masu kayan sarki('yan sanda) har yanzu sai adda'a domin kullum sayya yi wani abun rashin da'a,tun da nace ya samo Mata nai mai aure  kowa nutsu ,shine ya satoki ko? kiyi hak'uri gobe- goben nan, zan saki a hanya ki Koma mangalu" Hansai tace "iya dama cikin gari ya kawo ni"? iya tace "ai nan cikin garin bunkure ne".kuka hansai tasa kaka na bata hak'uri.

                                                                                                                                                                               

                                                                                                                                                                               

                                                                                                                                                                               *By Queen meemi*

                                                                                                                                                                               

                      

                      .

[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣10❣

             *JAN 2017*





*Queenmeemi.wordpress.com*



*dedicated  this page to sis marwa &sis Ameener*



 _jinjina gareku, *Anty maijdda* *Anty sis,Anty sadyjegal* *LubieD*, *Hapsert NM, Kursiyya* *yusha'u ,Aneesaty*, *respectable* *& Princess Amra*da sauran wanda ban fad'o ba duk kuna raina_



Washegari da sassafe sai ga lawandi nan tunda dama ba kwana yake a gidan ba ,kokon da kaka take sha ya d'auke ya d'ad'd'aka. Hansai kuwa rakub'ewa tayi a gefe ya kalleta .Hansai gani gaki sai yanda nayi dake zaki raina kanki keda ba gata gareki ba ,kaka tace" kai lawandi tsiyar ka da rashin da'arka ya kaini bango wallahi zan sab'a maka"  lawandi yace "to kaka bake kika ce na samo aure ba, don haka ga Mata na samu" harara Hansai ta galla mai tashi yayi ya fita.ya rufe k'o far ta baya .


Hansai tace "kaka yanzu zan tafi "kaka tace "bakya ganin ya rufe", kuka tasaka ta tashi ta fita tsakar gidan ta ta zaune shikwa Lawandi yana waje ya kasa ya tsare don yasan dole hansai zata nemi guduwa.



Acan gida kuwa hankulan malam da jummai atashe yake ganin har safiya ba labariin Hansai yanzu ma da suke zaune jummai kamar Mara lafiya tace "yanzu shike nan 'yar da na k'wallafa rai akanta ta bata"? .Malam yace "ki daina kuka ai na sanar da Maigari yanzu anjima za naje ,kuma ina addua sabida tamkar amana ce Allah ya bani" gwamma dake d'aki tayi tsaki "kwayi kwa gama ai, kunyi bankwana da hansai ".


 

Wajen k'arfe 11 Malam ya fita gona, sai da ya fara biyawa ta gidan Maigari ya kumai mai tini kan maganar San nan ya suce gonar.



Al a' amarin Muntari kuwa yana d'aki yak'i fita sai matsaar k'walla yake, Maman sa ladidi sai karakaina  take don ya karya don tun jiya takula bashida kuzari da abinci jiyan ma baici ba,da k'yar yaci ya fita nai man hansai har gun su da suka Saba zama yaje bai ganta ba ya Dade a gun San nan ya kuma nausa neman ta.    



                                                                                                                  Hansai kam durfafar k'ofar fita tayi ta sakace ganin ba lawandi agun ta kalli gabas da arewa nan tayi gabas tafara tafiya kenan ta k'unshe hannunta a cikin hajib sai ga lawandi yasha gaban, ta yace "Ke hansai koma"! tace bazan Koma ba", nan yace ai kinshigo kenan dole ki soni, kuma sati mai zuwa za a d'aura aure".Wallahi bana sonka muntari nake so shine jarimina" hannu yakai zai damk'o ta tace "karka k'ara tab'ani! domin Naga kai baka San dokar musulunci ba",wata siririyar wuk'a ya d'auko a gefen wandon sa ya nuna ta da ita ki Koma ,konai miki kwale a fuska ,duk kyan nannaki ya b'aci" hawaye ta fara ganin ya nufota ta juwa ta shige gidan, kaka na zaune tace "Ahh! ya kika dawo?...Hansai tace "ya k'i bari na na wuce har wuk'a ya nunan" kaka tace "barshi sai na nuna mai b'acin raina".       

                                                                                                                  

                                                                                                                                                                                                            *Bayan kwana 5*

                                                                                             Maigari ankai report guron 'yan sanda dake cikin garin bunkure ,saboda ganin yau kwanan hansai shida ba labari,jummai har zazzab'i tayi saboda sabo akace Turken wawa Shi kansa Malam d'in daure wa yake haka akaita nemanta.   

                                                                                                   


        *RANA DUBU*

                                                                                          _*(Hausawa na cewa rana dubu ta b'arowo rana d'aya ta mai kaya)*_  yau  lawandi wajen 12 ya fita don zuwa wani waje kaka tana sane ta kirawo hansai tace "yauwa hansai ga naira D'ari ki tafi kiyi sauri kan ya dawo ko ya rufe k'ofar ki jijjiga ta " godia tayiwa kaka ta fita.Allah da ikon sa sai gashi k'ofar abud'e saboda ya sakankance hansai ba zata gudu ba, da sauri Hansai ta fita tana kalle- kalle gudu ta hauhi,ganin wasu mutane taje gunsu tace "don Allah wane ina zanyi ya kaini titi "nan suka nuna Mata wata hanya haka ta yi ta gudu  har taje , nan tana tsaye kan titin taga wucewar lawandi ai sai ta b'oye don kar ya ganta, wata mota ce Ke shiga mangalu duk sati taji Ana ambatar mangalu! mangalu! ai da gudu ta shiga akaja,cikin ikon Allah wajen k'arfe 1, sai ga hansai a mangalu godia tayiwa Allah,ta yi hanyar gidansu.     

                            

                                                

                                                                                           Gwamma na tankade tana wakar _ahayye yaraye_ hansai tayi sallama tashi gwamma tayi tana tafa hannu "Ke 'yar nan sai yau kika dawo daga yawon tambad'ar? oh ni! gwamma duk k'auyen nan ace Ke kad'ai ce ba aure duk sai k'annen ki ai dole ki yawo".Jummai ce ta fito tazo ta kama hansai tace "Hansai ina kika shiga"? kuka ta saka Jummai ta jata d'aki.

                                                                                           

                                                                                            gwamma kuwa mamaki tayi yadda akai hansai ta tsallake rijiya da baya, Malam ne ya shigo da sauri Jummai ta fito tace Malam sannu da zuwa, ga Hansai fa"! da sauri ya bita d'akin Hansai na zaune na kuka yace Hansai ina kika shiga"? eh ransa a b'ace yake maganar tace "baba lawandi ne ya sace ni ya kaini cikin garin bunkure gidan kakar sa, wai sayya aureni" tafa hannu Jummai tayi tace "baide miki komai ba ko" ?tace "eh" ran Malam  abace ya fita  A fusacee bai  zarce ko ina ba, sai gidan maigari suna soro a zaune yaje ya nemi izini akayi mai Iso,nan ya sanar da dawowar hansai da sacewar da lawandi yayi mata, ran maigari ya b'aci yace tabbs sai na b'atawa lawandi  bazai rikitan gari ba,yace dole 'yan sandan za a gayawa". Haka kuwa akai .Washegari aka sanar musu dama sosai suke da case da lawandi nan suka hau neman sa.       


                                                                                                         Zo kuga yadda gwamma ta tashi hankalinta domin lokacin da malam ya Koma yana ta fad'a agabanta yake maganar an sanar da 'yan sanda nan ta shiga rud'ani ta San dole asirin ta zai tonu,haka taita kaikawo tana habaice -habaice "haba ko dije a ka d'auke ai Malam bai ci kai wan nan gigicewar ba, Amma kan 'yar tsintuwa duk ka d'imauce" ,haka taita surutan ta.

                                                                                                         

                                                                                                         Cikin sa'a aka kamo Lawandi sai da suka zo gun maigari .Maigari yace "kai yanzu lawandi abinda kayi yadace ne? haba! ai nayi maku tsakani da Hansai ko to kuma har da d'auketa ko"? ,lawandi ya tsuke baki ranka ya Dad'e nasan ina son Hansai, Amma banyi niyar saceta ba, sani akai".Maigari yace "waye ya saka? yace "gwamma matar malam". Malam dake durk'ushe ya d'ago tabbas matar nan ta rainani , duk sai yaji kunya ta kamashi. Maigari yace "ai sai Malam kai ne zaka hukun ta ta, kai kuma lawandi sai atafi da kai". haka kuwa akai masu kayan sarki suka tafi da lawandi .        



                                                                                                  Afusace malam ya shiga gidan, gwamma ya k'wallawa kira saida hanjin cikin ta suka bada k'uuuuu !ta fito "Malam gani  tace "yada wan nan kira haka"? yace "kin tozarta ni, kin badani acikin wanda Ke ganin mutuncina, gwamma kin addabeni kije ni a yanzu bazan ce ki je gida bako wani Abu  kawai na datse alak'a ta dake ba ruwanki da hansai ko jummai, nima karki shiga tawa ki zauna agidan nan Amma saina waiwayeki ,abinci kawai na baki izinin ci shima sammaki zan" kuka tasa "yanzu Malam duk sosyyyar dake tsakanina dakai akan hansai kake min haka"? ,afusace ya juyo yace "Ke ko akuya Kikaiwa haka saina hukunta ki Ballan tana Mutum" dije ta fito tana zumbure baki jin anawa gwamma fad'!  duk gwamma tana koya Mata halayen ta Malam yace "Ke dije je ki d'auro d'ankwali zunb'uro baki tayi tak'i tafiya, malam yace "kinga halayenki ko! gwamma gashi kin koyawa yarinya,Allah ya shirya" .gwamma sai fatar hanci take tana kuka ,Jan dijen tayi suka shige d'aki....

                                                                                                  

                                                                                                  

                                                                                                  Muntari kuwa dad'i ne ya kashe Shi ganin hansai ta dawo ,cikin gari ya shiga ya sayowa hansai hijab guda 2 yazo gidan su hansai ta fito sunkuye da kai harda d'an murmushin ta na ganin muntari zama sukayi yayi ta tambayar ta tana bashi amsa duk yanayin data shiga a sacewar da lawandi yayi Mata.Muntari yace "hansai tabbas kin fita da yaran kauyen nan shiisa nake sonki kina da nutsuwa dad'in dad'awa kullum jikin ki arufe sab'anin sauran yaran dake yawo gandak'ai.Murmushi tayi "innace tace na dunga sawa, ai yanzu ni na sabama" mik'a Mata leda yayi to ga wasu a K'ara sakawa" haka sukai ta hira yanai Mata K'arin karatu wan nan Ke nan..kubiyoni

                                                                                                  

                                                                                                  *By Queen meemi👑*

                                                                                                  

                                                                                                  

                                                                                                  .

[7:43pm, 15/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣11❣

              *JAN 2017*


*Queenmeemi.WordPress.com*



*_Sadaukarwa ce ga basheer usman family's_*


_dole na miki Gaisuwa gunku, *Miss hafcy ,Mamu,Anty Ybk,zahra,mum's gurl,Autarhajiya,Futha besty, chuchu Ammani,waheeda* San nan 'yan group d'in *qasaitattu Mata*_





     *Bayan sati daya*     

                                                                                                           Duniya tayiwa Gwamma zafi sosai abubuwa sunyi Mata yawa ta rasa yarda zatai ga Malam ya kafa mata Doka.Abinci sai Jummai tayi ake yafa Mata ga Malam ya daina kulata baya shiga Dakinta.  

                                                                                                                                                                                                              Yau ma data Ke kaikawo don neman mufita Abu yaci tura ga d'aci da ranta keyi, sabili da ganin Malam da Jummai a zaune suns Hira.

                                                                                                                                                                                                              Malam na bata Labarin wata tafiya daya yi da dad'ewa da irin Gwagwar mayar da suka sha sai dariya take. 

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                    Da sauri ta d'au Buta ta shiga band'aki ta fito ta Koma d'aki gashi tana San fita Amma ba dama ta zauna Ke nan taji Malam nace wa:    

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                  "Ai Hansai so nake ace ta gama Makaranta. Amma Allah baiyi zata gama ba, tunda bikin saura wata Hudu."

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                  Jummai tace "tabbas haka ne Malam" .

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                  kiran Hansai yayi datake d'aki ta fito ita da Dije 'yar Gwamma .kallon Hansai yayi yace "aji nawa kike.?

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                             Sunkwi dakai tayi tace "ajina Uku".

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Hamdala yayi yace "ko a hakan kika tsaya ai kin samu .

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Jummai tace "Malam ai se a saka Dije ma tunda kaga tayi Girma".

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Malam yace "anya ba'a bari ta kai goma ba ,ko bakwai."

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Da gudu Gwamma ta fito "wallahi kar wanda yakaimun yarinya makaranta".Malam ya d'aga Mata hannu "waya saka dake ehe?,meye naki aciki? nayi maki tsakani damu don haka Ke 'yar kallo ce, idan kinga bazaki iya ba,ga k'ofa nan abud'e take".

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Jiki a sanyaye ta Koma.Haka dai rayuwar ta kasance a yanzu hankalin Jummai da Hansai ya kwanta, har k'iba sukayi.

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Hansai kuwa soyayyar su ta dad'a ninkuwa itada muntari domin bala'in son Junan su, suke d'aya baya son rabuwa da d'aya ,arana sai muntari yazo gun Hansai so uku ga Shi komi yagani sayya sayo mata ,duk da shima ba sana 'a yake ba. Amma yana zuwa gona,tun Bayan gama Secondary d'in sa yana son cigaba .Amma tunda baiji Maigari yayi magana ba shiisa yayi shiru .

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Hansai kuwa ta b'angaren iLimi sai nace Masha Allah ,duk k'auyen ayaran Mata,domin ta dage kullum Malam na k'arfafa Mata Gwiwa Musamman na Addini sai san barka. 

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                              Sam bazaka ce Hansai daga K'auye take ba,tun Bayan da malam ya dakatar da Gwamma sai ya ce Dije ta Koma gun Jummai haka Dije ta fara nutsuwa ,gashi Hansai Ke koya Mata karatu Sun saba sosai ,sab'anin da sai de ta tsaya k'ofar d'akin su tana hararar Hansai duk da yarinya ce mai Shekara Hudu.

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                               Gwamma kam tana gani ba damar magana don Malam yace duk randa takarya doka inta bar Gidan to har abada bazata dawo ba. shiisa tai shiru saboda tana k'aunar zaman Gidan domin tabbs tasan Malam yana da kyautatawa da yawa.

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                Matan k'auyen na surfe sukam Malam bai bari suyi gashi har kud'in kashewa yake basu ,wad'an nan dalilan su suka sa Gwamma tayi lamfa.haka dai rayuwa tayi ta tafiya har su Hansai suka zana Jarabawar Junior Secondary school,ayanzu Hutu suke.  

                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                               

   BAYAN WATA UKU                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                        Bikin hansai da Muntari yana ta k'aratowa ayanzu saura wata d'aya,nan gari ya d'auka saboda an Dad'e ba ai biki gidan maigari ba ga kuma Hansai da ake ganin ta dad'e.San nan gashi soyayyr su mai Asali wadda ta kaisu ga Shekara hud'u da rabi kenan shiisa kowa Ke zumud'in Bikin.   

                  

                                                                                                                             (Bari mu waiwayi Lawandi muga wane waina aka toya tun lokacin shigar sa gun 'yan Sanda).   

                                                                                                                                                                                                Bayan da suka tafi dashi dama suna da case dashi sai direct suka kaishi cell saboda dama andad'e Ana neman sa, bisa dalilin satar da sukayi wa wani D'anfulani ,sai lefin nasa ya zama biyu gana satar yarinya gana kayan D'an fillo ,kawai sai aka sashi cell na wata uku ba beli .

                                                                                                                                                                                                To ayanzu wata ukun ya cika ya samu ya fito .   Zuwan sa gun kaka lokacin tayi fishi dashi tace ya bar Mata gidan ya Koma gun Dangin Maman sa kaka sai kuka take hakan yasa ta d'akko wata Jikarta suke zama tare Shi kuma Lawandi ya had'a kayan sa ya cale Lagos neman kud'i ,acewar sa sai kaka ta neme Shi .

                                                                                                                                                                                                kaka tace "nikam nayi nan kayi can .Allah ya bada sa a can yayi tafiyar sa. 


                                                                                                    Al amuran Gwamma kuwa tayi ladaf din k'arya don har ciwon karya tayi domin ta jigata matuka.                                                                                                                                                 Malam na zaune tazo ta zauna sai matsalar k'walla take "Malam kayafeni na tuba bazan K'ara ba na jigata tamkar a Kurku ku nake ,ka taimake ni ba donni ba.

                                                                                                     Malam ya kalleta "Ashe har kin horu" Gwamma tace "na horu Malam."

                                                                                                      "To kije na janye. Amma idan sab'anin hakan ya kuma faruwa zanyi mai gabad'aya."

                                                                                                      "Malam aina saduda".

                                                                                                       Tashi yayi ya fita domin Shi kam yasan tuban muzuru Gwamma tayi.

                                                                                                       

          *Bayan sati daya* 

                                             

 Kud'in da Malam Ke tarawa dama na bikin da wasu awakan sa daya sayar ya had'a jumulla dubu d'ari dashi za yiwa Hansai siyayyr kayan d'aki. 

                                                                                                                      Wajen k'arfe 9 na dare  ya shiga d'akin Jummai lokacin ta na zaune ,ya zauna gefen tabarmar ya kalleta. 

                                                                                                                      "Jummai kinsan dai bikin Hansai ya matso yau,saura sati daya ko! to shine Allah da ikon sa ga kud'in da za'a sai Mata kaya, yanzu sai kuje keda iro har kano sayo Mata duk abinda ya samu."

                                                                                                                       Godia Jummai tayi itama ta d'auko nata ajiyar, nan duk suka had'a, Hansai na kwance tana bacci d'an tashin datai taji suna maganar, kuka takeyi A hankali tabbas babu wani sarki sai Allah mai had'a bayin sa duk inda yaso, gashin ya had'ata da Mutane masu kyautayi, tana daga kwancen ta rok'i Allah ya bata abinda zata rama d'umbin  Alherin da sukai Mata. 

                                                                                                                                        Duk maganar Kud'in da sukai akunnen Gwamma nan hankalin ta ya tashi ta kasa tsugun komawa d'aki tayi ta rafka tagumi.

                                                                                                                                         "Lalle nayi sake D'an zaki ya girma ,dole na san abinyi kud'in ma ba za asadani ba lalle dole na tashi tsaye" ,haka taita Sumbatu tana jira safiya tayi ta San abinyi.tooohhh muje zuwa dai.....             

                  

  *By Queen meemi*  

           

           .

[4:00pm, 17/01/2017] 👑Meemi🔸: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣12❣

             *JAN 2017*

 *®NWA*



*Queenmeemi.WordPress.com*



  *Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's*



      _TUNATARWA_


 _Ya 'yar uwa ko d'an uwa, ka/ki kiyaye harshen ka/ki, domin shine wakilin Zuciyar ka/ki.Kuma shine hallakarka/ki take jikin sa, karka/ki rik'a sakin sa,sai akan Alkhairi ko abinda Zai Amfaneka/ki_

 


                **********

 Haka kuwa akayi washe gari da sassafe kuwa Jummai da iro suka tafi can kano don siyayyr kayan d'akin.    

                                                                                                  Misalin k'arfe 11 Gwamma kuwa Bayan fitar Malam itama ta fita, dama ba tambayar sa take ba,bata zarce ko ina ba  sai Gidan Maigari .

                                                                                                   Da Sallama ta shiga, Ladidi tana zaune tana hira da bak'uwa tacee "Ah! lale da Gwamma" dariya Gwamma tayi tace "wallahi kuwa" nuna Mata waje tayi suka kuma gaisawa, haka sukai sallama da bak'uwar ta tafi, nan ta juyo gun Gwamma tace "yasu Dije da Jummai" ta amsa da Alhamdlh gyara zama tayi "Ladidi dama magana nazo da ita kan Hansai.

                                                                                                    Ladidi tace "Eyyya ya shirye- shirye?" tab'e baki tayi batace komai ba, d'an juyowa tayi ta fuskanci Ladidi tace "wato ranar wanka ba a b'oyen cibi dole idan kaga za acuci Mutum ka sanar."

                                                                                                     Ladidi tace "ban gane maganar da kike ba,"tace "ai In gaya miki Hansai de ba 'yar gidan mu nan bace."

                                                                                                     "Asalin ta tsintar ta malam yayi, ba asan iyayen ta ba ,to ku kam kwaso had'a iri da ita.?

                                                                                                      Ladidi tace "haba dai Gwamma idan kikaji wani na maganar nan ai seki kwab'eshi ,nasan Hansai ai 'yar k'anin Malam ce".                                                                                                 Gwamma tace "wa din? to wallahi aga bana ya shigo da ita,kinsan badai zan miki k'arya ba."

                                                                                                      Shiru Ladidi tayi tace "tabdi Amma wan nan magana da mamaki! zan sanar da Maigari nan Gwamma tace karde kice nice na fad'a don Allah"

                                                                                                       Ladidi tace "haba dai sai kace wata yarinyaa."

                                                                                                        "Yawwa bari na tafi."

                                                                                                        Haka Gwamma ta tafi,tana tafiya tana maijin dad'i.

                                                                                                        Da misalin k'arfe Hud'u Maigari ya shiga gida Bayan ya huta Ladidi ta zo mai da maganar da Gwamma rltazo da ita, Murmushi yayi "wan nan ai magan- ganun Mutane ne" ita wan nan Matar dama bata son Yarinyar ,don haka abar Maganar kar ma kowa yaji."

                                                                                                        Haka Ladidi ta hak'ura tabar maganar Amma abin na ranta.

                                                                                                        k'arfe shida su Jummai suka dawo ba laifi sun sayo kaya da yawa,  k'aramar motar d'aukan kaya da gado aciki na katako duk k'auyen Hansai ce  Malam ya fara yiwa,  duk a wanda akaiwa aure ba masu irin sa duk da wan nan d'in ma bamai tsada bane can,lalle ta cika yar gata littafin( Miemei bee) Malam yayi farinciki ganin kayan .

                                                                                                        Gwamma kuwa sai dariyar Mugunta take ganin ta had'a gurmi, haka dai sukai ta shirye- shiryen su.

                                                                                                         Bayan sati d'aya Gwamma taji shiru ba alamun cewa an fasa auren, sai ma shiri data ga anayi a irgen da tayi yau saura Sati Uku bikin,hankalin ta ya tashi.                                                                                                  Yau ma da takasan ce ranar Laraba Gwamma na zaune ta rafka ta gumi zumbur ta mik'e cike da wani tunani, ta yafa mayafi ta fice bata zame ko ina ba sai Gidan Delu,ta shiga Delu na zaune tana cin Zogale ta taso tace "lalle daga ganinki ta ciyoki."

                                                                                                          Gwamma tace "sosai ma ai mufita nake nema."Delu tace "ai Labarin Bikin Hansai ya karad'e K'auyen nan ,ina zaune a nan nace kinyi sake".

                                                                                                           Gwamma tace "yo ai lokaci bai k'ure ba."

                                                                                                           Delu tace "tabbas yanzu kawaii kizo muje Gidan Boka na gaban K'auyen nan, da Zafi-Zafi akan bigi K'arfe.

                                                                                                           Gwamma tace "yo ai matsalar ta Kud'i ce."

                                                                                                            Delu tace "ai ba damuwa kije ki had'a su Kud'ad'en ki ,sai muje.

                                                                                                             Gwamma tayi shewa "shiisa nake sonki Delu haka kawai yarinya ta zame min sai kace 'yar kishiya"! haka suka gama Gwamma ta tafi.

                                                                                                             Fafutukar samo Kud'in Gwamma tashiga yi ,kurd'a- kurd'a, kullum tana yawon rancen Kud'i har wata Akuyarta, ta sayar nan ta had'a dubu Goma ,ta shiga kuma neman cuko dak'yar da Sid'in Goshi ta had'a Kud'in a sati d'aya ,hakan yayi dai- dai da  Sauran Bikin Hansai sati Biyu.

                                                                                                             Da sas safe Bayan Malam ya fita ta fita ,dama bata tambayar sa unguwa, ba bata zame ko ina ba sai gidan Delu tana zuwa suka tafi Gidan Boka.

                                                                                                              Sunyi tafiyar Awa d'aya San nan suka hau Mota ta aje su adede Dajin da zai kaisu Gidan Bokan, Surk'uk'in Daji ne gun. Amma haka  suka Shiga.

                                                                                                               Sallama sukai boka ya daka tsawa yace "ba ai masa Sallama( saboda tsabagen tab'ewa irin ta Boka) haka suka shiga Gwamma tace "Boka dama akwai wata Yarinya ce da mijina ya tsinta tunda tazo na shiga Matsala ayanzu hakan D.an Maigari zata Aura ,ni kuma ban so ,dalilan daya sa nazo ne akan a rusa Auren karya yiwu ,San nan Kishiya ta sai abinda nace Mata, shima Mijina ayi min abinda kome nayi bazai ga laifi na ba."

                                                                                                               Dariya ya kwarara "tabbas kina da sa a azzaluma mai son kanta, wan nan Aiki Sam bashida wahala,Amma fa kin cika muguwa ki tuba"  dariya ya kurma yayi surkulle nan Hayak'i ya fuuuu !  ya d'auko wani Garin Magani yace "gashi ki yi abinci kitabbatar Kishiyarki da Mijinki sun ci .

                                                                                                               San nan kuma Aiki akan auren can Zanyi shi .Godiya sukai ya kwarara ihu "ba aimun Godiya tab'ab'b'u kawai, ni ai na gama shiga ha'ula'I gashi kuma kun biyo Layi ,dariya ya saka .(meemi tace sakarkaru kawai Allah dai ya kiyashe mu tab'ewa ya shiryi masu hali irin na Gwamma).Aje Kud'in sukayi suka tafi... .kubiyoni

                                                                                                               

       

       

 *By Queen meemi*                                                                                                         

     .

[3:58pm, 18/01/2017] 👑Meemi🔸: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣13❣

         *JAN 2017*



*®NWA*


*Queenmeemi.WordPress.com*


_*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's*_

.


  _TUNATARWA_


 _Ya 'yan uwa ,Mu yawaita neman gafara awajen Allah domin Allah gafururr Raheeem ne.Mu yawaita tasbihi domin samun kusanci ga Allah_


************


Tun komawar Gwamma gida sai ta tsiri faran-faran da Jummai Malam kuwa har wani canja Ladabi tayi mai da yake itace da girki bata sha wahalar bad'a Maganin ba.

D'aki ta koma tana Murmushi "sai ni Gwamma mai Mugunta ba dalili" can sai ta yatsine fuska "haka kawai ai sai inda mai na ya k'are."



Washegari kuwa Gidan Maigari Ladidi ta damu da Maganar can k'asan ranta taji bata k'aunar Auren (Da alama Bokan Gwamma yayi tsiya)sai kai-kawo take tasa aka kira Mata Muntari Lokacin yana can Gidan da zasu Zauna da Amaryar sa yana Gyarawa,haka nan yazo Ladidi ta tareshi.



"Muntari nikam wai kai bakasan Hansai ba 'yar Gidan  nan bace?"

 Gabansa ne ya fad'i yace "haba Gwaggo kidena damuwa da jita- jita." 

 "Kai Muntari  ba wani Jita- Jita sai Gaskiya.

 Dai -dai Lokacin Maigari ya shigo ya tarar da su a tsaye nan ya tambayi ba'asi Gwoggo tace "Malam nikam ayi bincike kan auren nan nifa Gaskiya ina juya maganar Gwamma ,shiru yayi  baice komi ba can yayi gyaran murya yace "nima kawai ji nake bansan Auren gabana har fad'uwa yake. Amma yau zan samu shi Malam d'in akan Maganar.      


                  

                                                                                          *Bayan Awa Hud'u*

                                                                                   Malam ne tsaye Shida Maigari suna Magana, idan ka kalli fuskar Malam tsab zaka Zakulo razanar dake kai .Amma sayya dake yace "wato ranka ya Dad'e Maganar Gaskiya Hansai ba 'yata bace nan ya gaya mai Asalin Had'uwar su San nan yace "Kaga kuwa mai Asalice Rabuwa ce kawai Sanadin daya sa bata tare dasu iyayen nata, idan akai duba da yanda abun ya faru, ayanzu nine matsayin uban ta."

                                                                                   Maigari yace "Lalle Abin tausayi ce .Amma zan gayawa ita Mahaifiyar yaron aji ta bakinta.

                                                                                     "Toh! toh! ba damuwa" inji Malam.Jikin sa asanyaye ya shiga gida .

                                                                                     Shikam Maigari yajewa da Gwogg Maganar nan tayi tsalle ta dire kan D'anta bazai Auri wanda ba asan iyayenta ba, shima Maigari d'in baya so Amma kunyar Mutane yake ji, nan suka k'ark'are kawai  Afasa Auren.Turk'ashi! wata Sabuwa kenan inji 'yan caca.



                                                                                                                                                                                   Washegari kamar k'arfe Goma na Safe Malam na shirin tafiya Gona akai sallama dashi ya fita, Yaron Maigari yagani saida K'irjin sa ya buga, nan Yaron ya gaidashi sa'an nan yace da Malam Maigari na neman sa, tare suka jera nan sukaje Maigari na Zaune kan tabarma Asoron Gidan sa, ya shiga suka gaisa .

                                                                                                                                                                                   Sai da yayi tsai San nan ya tashi ya Zauna yayi Gyaran Murya yace "wato Malam komai dama Muk'addari ne daga Allah, Matar Mutum Kabarin sa, kayi Hak'uri Auren nan abarshi, tunda uwar Yaron tace bataso, haka 'yan Uwa da Azo daga baya Ana kace nace! .Gwanda A Hak'ura.

                                                                                                                                                                                   

                                                                                                                                                                                    Dumm!! Malam yaji akansa Idon sa yayi ja "yace bakomi dama Matar Mutun kabarin sa, Allah ya had'a kowa da rabon sa". 



Maigari yace "Amin ,Amma aimin afuwa" Malam yace "Haba de wanda baisan k'addara ba shine zai damu" .

Haka ya fita yana tafiya a Hanya yana Magana har yaje tsakar gidan sa, Gwamma na gefe tana shara Jumma na d'aki kawai sai ya zauna bakin Bishiya ya dafe kai. 

Gwamma ta taso "Aa Malam ya na gan ka haka?" Shikan Malam yace "An fasa Auren nan, Maigari yace ba zasu Aura wadda bata da Asali ba".


D'ora Hannu tayi a ka kamar zata kurma ihu Malam yace "Aa meye haka? sai kace wanda akai Mutuwa". Gwamma data juya ta yi dariya ganin hak'an ta ya cimma ruwa tace "Allah sarki Hansai .       


                                                                                   Nan Jummai ta fito tana Malam Lafiya haka?"

                                                                                     Gaya yayi  take ta hau kuka, "shike nan na shiga uku yanzu abinda Zasuyi mana kenan! yau saura kwana takwas wayyo Allah" .

                                                                                     Hansai dake shigowa Gidan da leda A Hannu  ta aje da sauri ta tari Jummai tace "Inna Mayya faru?".

                                                                                      Jummai tace "an fasa Aurenki da Muntari". Hansai taji kanta na yuuu saboda Mamaki. Luuu tayi k'as Asume.

                                                                                       Da sauri sukayi kanta Gwamma kam D'aki ta Shige tana rawa, yay yafawa Hansai ruwa sukayi take ta Farfad'o da kuka, nan Jummai ta shige da ita D'akin ta, ta kwanta tana Mata nasiha ita kam Hansai son Muntari ne taji ya nunku kuka ta fasa.       


                                                                                                                                                    Can kwa Gidan Maigari Muntari shima Kukan yake saboda tsananin son da yakewa Hansai da shak'uwar da ke tsakanin su, Shekara biyar kenan daya k'wallafa ransa akan ta ,haka sukai ta lallashi shikam yace haka yake sonta koda bata da kowa d'aki ya shige ya kulle ,suka bishi suna bugawa Amma  yak'i ya bud'e.                                  

                                        

                                        

                                                                                            Haka dai wad'an nan rayukan masu tsananin son juna ,suka rayu a kwana biyun nan cikin k'unar Rai ga gari ya d'auka ai Hansai bata da iyaye an fasa Auren ta, ko ina Maganar abuga k'auye.

                                                                                            

                                                                                            "Jummai inaga zanyi huce Haushi kawai domin duk Lokacin Dana sa Auren baza a fasa ba, sai a d'aura da Mudi".

                                                                                             Fit Gwamma ta fito "Aikuwa badai a Gidan nan ba, wai abada Auren D'ana da wan nan abar, to sai de ko Bayan Raina".

                                                                                              Malam yace "to sai de Muga ni dake Waye yafi iko da shi."

                                                                                              Buga k'afa tayi "Ai wallahi sai de wani Amma ba Mudi ba,don kaga Yarinya ank'i Aurar ta, shine zaka Lak'abawa Mudi, haka kawai yo dama Mutum mai Hankali ina zai yadda D'ansa, ya Auri Hansai ba asali,gashi d'ai-d'ai shekarar ta goma sha biyar ace ba Aure"

                                              

                                                                                                            Malam yace "ya ishe ki haka Gwamma! domin zan huce akanki wallahi,kisani Hansai babu K'ashin tsiya agareta kawai haka Allah ya shirya,kuma in banda ke da bak'in cikin ki,Abinni Akwai Mata 'yan talatin 30 basi Auren fari ba Amma dan anan Anayi Masu aure da wuri shine zaki takurawa yarinya ,to wallahi gwamma ahir d'inki Aure ne sai anyi da Mudi ki fad'i ki Mutu shashashar banza" Afusace ya fita.

                                                                                                             Gwamma tace wallahi ba zan yardaba"  ta kalli Jummai tace "Almunafum-fum kawai " ta juya ta shige band'aki

                              

                             

                                                                                       Ita kanta Jummai bata son had'in domin tasan Mudi basu dace da kamilalliyar yarinyar irin Hansai ba, cutar ta kawai zaiyi .

                                                                                       Duk wan nan budirin da ake Hansai na d'aki tana sharar Hawaye domin son datakewa Muntari jitake kamar yana k'aruwa gashi taji Ana zancen had'ata da Mudi.

                                                                                       Malam da kan sa ya shiga dakin Jummai Bayan da ya sake shiga gidan,ya zauna kusa da Hansai yace "kiyi hak'uri 'yata komi Muk'addarii ne daga Allah ,dama Allah haka ya shirya ,kiyi hak'uri kinji sai de bansa ni ba idan na miki katsalan dan Arayuwa wadda nake ganin shine kad'ai zai sa na Huce haushi na had'aki da Muntari, duk da nasan bakya son sa."

                                                                                        Dumm!! taji k'irjinta ya buga ta d'ago tace "tabbas Baba basai nayi tunani ba, ni ai ikon ka ce kayi duk abinda ya dace dani ka cancanci hakan Insha Allahu zanyi Biyayya agareka".

                                                                                        Dad'i ne ya kashe shi ,yace "Allah yayi miki Albarka Hansai, ya Baku zama lafiya, tashi yayi ya fita Ita kam Hansai ji take Numfashin ta na gudu tana kamo Shi.......

                                   

                                                                                        

           Auren nan zai yiwu kuwa??

           ya Rayuwar Hansai zata cigaba da kasancewa?

           Anya Hansai da muntari zasu Hakura da juna kuwa?.

           Gwamma fa !!kudai cigaba da bin Queen meemi da sannu za muje inda muke San kaiwa.                                                                            





*By Queen meemi* .

[1:04pm, 19/01/2017] 👑Meemi🔸: . 



⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣14❣

        *JAN 2017*

 

 

 *®NWA*

 

*Queenmeemi.WordPress.com*

 

 _*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's*_

 

 

 _Ban kanta daku ba *Nana* *fiddy, Husy, Maryam* *Ahmad,Neesah,Maman Ramlat ,Maman Rahma,Feedoh 'yar ficika*_

 

 ***********

Haka Nunfashinta yayi ta neman kufcewa ta Kwanta Ahankali ta Sami nutsuwa har bacci ya kwace mata. A b'angaren Muntari kuwa tunda ya rufe d'akin ya Kwanta kamar Matacce sai tunanin Rayuwar su da Hansai yake Zumbur ya mik'e lokacin karfe 9 na safe ya fita .


Gwoggo na ganin sa tace Muntari ,bai waiwayo ba sai ma K'ara Sauri da yayi bai zame ko ina ba sai bayan Dutsen da suka Saba had'uwa da Hansai nan ya k'urawa wani gun da Hansai ke zaama.


"Yace tabbas bazan iya rayuwa babu ke ba Hansai" kamar wani k'aramin yaro yana Magana "ya za'aimin haka! maisa sai dana sa rai dake, za a hanani ke, wallahi ina sonki" haka yayi ta Magana kamar zautacce.

                               

                               

                                                                                             Mudi kuwa wajen 1O ya shiga Gidan da sauri Gwamma ta tareshi "Zonan d'an Gwamma" nan ya bita d'aki suka zauna tace "abinda zan gaya maka ka saurareni, kasan kuwa Malam yace zai had'aka Aure da Hansai"?.

                                                                                              A mik'e ya tashi "kamar ni ace zan Auri Hansai bazata sab'uba." Gwamma tace "yawwa haka nake sanka ,ina zaka iya da ita ,yarinya  da ba asan Usuli ba, ko da Malam ya maka Maganar kace baka son ta."

                                                                                               Ganin wuce war Hansai Mudi ya bita da kallo shikam yasan Hansai nada kyau ga jikinta na birgeshi, wani tunani ya canja ya juyo "to Mama ki bari kawai na Auretan mana"! ai ba damuwa.

                                                                                                Gwamma ta d'aga kai "Lalle kacika shashasha "to wallahi sai nayi maka baki akan hakan, kai me zakai da Yarinyar da ta gama tambad'a" .

                                                                                                Mudi yace "to Mama ba damuwa nima dama ba wani sonta nake ba kawai don Naga baba yace dole ne."

                                                                                                Tashi yayi ya fita suka had'u da Hansai Asoro yace "ke zo nan!"

                                                                                                 Zuwa tayi ya Nuna ta da Yatsa "kifa gane ni ba sa anki bane nai miki zarra, me zan dake Gwanda ma kicewa Baba bakya Sona ,don in ba haka ba wallahi zaki gane kurenki."

                                                                                                 Hansai tace "idan ba biyayya ba nima me zan dakai, wallahi darajar Baba kaci zan Aureka ne kuma wallahi bazan tab'a cewa bana son Auren ba."

                                                                                             Kai Mata hauri yayi tayi baya tana kuka,dama da Hijab d'inta ,kawai se ta zarce Bayan dutsen su tana zuwa ta zauna da abin busa d'inta, tanayi idon ta na b'ulb'ulo da hawaye ,domin ta tuno Muntarin ta, kamar Amafarki yaji sauti .

                                                                                             Firgigit ya mik'e daga baccin daya kwashe shi,tsai ya ganota durowa yayi daga kan Bishiyar ya je kusa da ita ya tsaya, yace "Hansai an rabamu ko?

                                                                                              Da sauri ta juyo suka had'a Ido tace "Muntari yanzu shikenan Mafarkin mu ya zama ba Gaskiya ba?". Muntari yace "nikam bazan iya babu ke ba".

                                                                                               Hansai itama tace "nima haka Muntari .Amma ba yanda muka iya". Kuka ne ya kubce Mata da gudu tayi baya ya bita, suka tsaya yace "har abada Hanasi kece Masoyiyata, ina Sonki Sona Gaskiya dama zasu Amince da Auren namu".

                                                                                                Tace "Muntari mu fawwalawa Allah shine zai iyar mana" haka sukai ta hira. Suka rabu cike da k'unar Rai.

 

 

                                                                                                                                               ********                                                                                                                                           Bayan kwana 2 anyi rigingimu a Gidan inda Gwamma ta kek'ashe baba ma ya kafe .

                                                                                                                                               Yauma da take tsaye tana tunani "yo wai ni ko Maganin da boka ya ban baya Aiki ne? Naga Malam baya yarda da Magana ta" nan Taje ta duba kwanan ajiyarta,Mamaki ne ya cika ta Ganin Maganin da Bokan ya bata ,tace "kodai bashi na zuba ba!".                                                                                                                                          "Lalle dole mana Malam yana min musu" da sauri ta d'auka  Mayafinta,ta fita Gidan Delu, zuwanta ta Sanar da ita, Shine Delu tace "yanzu Shikenan kin b'ata Aikin ki da kanki".

                                                                                                                                                Gwamma tace "to ni yazanyi ,yanzu?" Delu tace "ki kawo wani Kud'in na koma ya had'a wani Gwamma tace nikam wallahi ban da kud'i sai dai ki ran ta Min".

                                                                                                                                                 Tace "ba Matsala zan baki" nan suka K'ark'are zata je anjima haka ta tafi tana Surutai A hanya. 

                                                                                                                                                 

                                                                                                                                                                                                                        Wajen k'arfe 8  na dare sai ga Delu har  taje gun bokan. Gwamma suka kule ad'aki tace "gashi Boka yace ki tabbatar ayau da daddare kin amfani dashi Hayak'i Zakiyi kamar turare, inde suka shak'a kin samu kansu."

                                                                                                                                                                                                                        Da rawar Jiki Gwamma  ta boye a zanin ta,sukai Sallama da Delu ta tafi. Bayan Dan Lokaci ta turara Hayakin duk suka shak'a .

                                                               

                                                                                                                                                                                                                        Washegari kuwa Malam ya tsare Mudi yace "kaga yau saura kwana 2 D'aurin Aurenka." Mudi ya kada baki yace  "Baba ni bana son Auren nan".

                                                                                                                                                                                                                         Gwamma dake d'aki tace "yawwa".

                                                                                                                                                                                                                          Baba ya sunkwi da kai "yanzu kai bakaji kunyar gayan Maganar nan ba na ko?! ai shike nan dama ai babarka tace bata so kuma nasan ita ta kitsa ma. Amma komi Mutun yayi Shi za ayi mai.

                                                                                 

                                                                                                                                                                                                                           Mudi kam wata jakar bagkoy ya  d'auko, ya tsaya "ni na tafi Lagos neman kud'i baba dama yau na tsara tafiyar".

                                                                                                                                                                                                                           Gwamma ta fito "Yawwa mudi yau ka biyani". Baba yace "ni kam ina Umartar ka A matsayina na Mahaifinka kar kaje duk da nasan ba ka Maidani komai ba." Gwamma tace "wallahi Sayyaje". Mudi ya d'uri jaka yace acan zan hadu da Lawandi ya fice.              

  Gwamma tayi shewa "Ahayye yaraye  nanaye"                                                                                                                                                                                                                   

                                                                                                                                                                                                                                                                                               Kuka hansai keyi saboda tausayin Baba, tace "Baba kayi hak'ur. Baba yace "bakomi Hansai ina Alfahri dake Allah ya baki miji na gari" ya tashi ya fita.      

 

                                                                                                                          Haka Malam duk ya sanar an fasa auren nan nan gari ya hau tsogwami anata Gulmace- Gulamace ko fita Hansai tayi sai a fara ga Hansai mai bak'in Jini "da kuka take dawo wa, sai da Malam yaje yayiwa tufkar hanci ,San nan aka sakar Mata Mara.                                                                                      

                                                                                                                            K'anin Maigari ne dake zaune a kano yazo mai suna Alhaji Salisu, Shi ya tashi a hannun k'anin Babar su Maigari to ita abirni take Aure shiisa ta d'auke Shi ya tashi yayi Boko ,yanzu hakan yana aiki A NNPC Manager ne, yana da 'ya'ya da Mata Biyu.

                                                                                                                            

                                                                                                                            Zuwansa Gidan ya tarar Ana tak'addama akan Muntari kan ya kafe bazai Auri wata Lantana da  Gwoggo ta kawo ya Aura yace tunda anraba Shi da Hansai ba 'yar da zai Aura, to ganin hakan Alhaji Salis yace zai tafi dashi can Birni ya cigaba da karatu ,Jin an ambaci karatu yasa ya Amince zai bishi.                                                                                                                                                                                      bankwana .. .

                                                                                                                            

  *BY QUEEN MEEMI* .

[12:55pm, 21/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣15❣

           *JAN 2017*

 

 

 

 *Queenmeemi.WordPress.com*

 

 

 *_Sadaukarwa ce ga  Basheer Usman Family's_*

 

 

 _TUNATARWA_ 

_'yan uwa muna hak'uri da rayuwa aduk yanda tazo mana,hak'uri maganin zaman duniya ne ,komai ya sameka mujarrabi ne daga Allah_

 

 

 ******

 *Misalin k'arfe 9 na safe*

 Shirin sa yayi tsaf ya had'a Jakarsa tunani yayi dole yayi bankwana da Hansai, hakan ya tashi ya tafi gidan su, ikon Allah adai-dai Lokacin Hansai ta fito, turus tayi suka K'urawa Juna Ido nan yace "zo muje bayan Dutse."

 

Haka kuwa akai  ta bishi a baya har suka je ,nan ya zauna yace "Hansai birni zan tafi" dafe kirji! tayi ta  Mik'e "na shiga uku." Muntari yace "gwanda na tafi Idan na zauna ina ganinki Zuciyata zata iya bugawa."


Saboda nasan an raba mu soyayyarki tana nan a Araina kece ta Farko Dana keso."

Hansai tace Rabuwa da kai Shine Sanadin cin Fuskar da na ke fuskanta daga gun Mutane da Ammana Aure da hankalina kwance,ba wanda zai min."


Kuka ta kuma fashewa "Wallahi bazan so kowa ba sai kai" Shima da k'walla ya fito mai yana jin Zuciyarsa kamar zata fashe. "Hansai da inada dama da sai na gudu muyi Aure. Amma ba dama San nan nama fasa tafiya Birnin ma, Zan Zauna na Jajirce har su yar da subani ke ko."

Hansai ta mik'e tsaye Muntari karkayi hakan ka tafi kawai. "Allah ya k'addara Saduwarmu."


Kollonta Yayi da Siraran Hawaye suka Zubo yace "Idan da rai da rabo.Hansai inde da rabo a tsakanin mu gaba zami Aure."

Murmushi tayi "Allah yasa"

Nan suka tafi a tare sun zo kwanar su yaga Maigar da Alhaji Salisu an saka Jakar sa a Mota kuka ne ya Kubcewa Hansai.


Maigari ya kwad'o Mai kira tafiya yayi yana waiwayon Hansai .Maigari yace Au gurin "Yarinyar can kaje? Iyayen naci ai gwanda ka tafi Birnin kowama ya wuta Soyayya ba Alkunya." Dariya Alhji salisu yayi yace "Zamani ne ai, Amma mai yasa Baku basi Auren ba.?


Maigari yace "Yarinyar ce ba usuli .

Dai-dai Lokacin Muntari ya K'araso Maigari yace "tafiya zakuyi." Idon sa yayi ja yace "baba na fasa" Maigari yace "saboda kaga 'yar Gwal ko? to dole ka tafi" sharshar hawaye ke sauka ya tashi ya Shiga gida don sallama da Gwoggo. Wata Takarda ya d'auko da wata Leda , bayan sun sallama da Gwoggon. D'ahiru kanin sa ya bawa ya kaima Hansai.


Tana nan tsaye inda ya barta can ta tusa Hijab Baki tana Kuka saida ya tsaya ya k'ura Mata Ido ya share Hawaye ya shige Motar ,Maigari yace "Allah ya kiyaye ya bada sa' a ".


Ganin an tada Motar Hansai ta durk'ushe agun tana gurshek'en kuka. Tamkar ance Baba ya Mutu Muntari, yana ganota ji yake kamar yayi tsalle ya kamota, D'ahiru zuwa yayi ya mik'a Mata "gashi inji yaya" da sauri ta karb'a sai da taga tafiyar su San nan ta tashi kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta shiga gida.


Gwamma na d'umamen tuwo tace "ke zo nan.? ko kallonta batai ba ta Shige d'akin Jummai. Zazzabi Mai zafi ya rufeta. Allah sarki Soyayya.


Saida Hansai tayi kwana 2 tana ciwon love Hankulan su Malam atashe. Allah da ikon sa ta samu sauk'i .


Hakanan Gwamma ta bud'e shafin Cusgunawa Jummai da Hansai. tunda yanzu ta Shanye Malam baya iya katab'us a gidan, koya ga Abu baiyi ba ,da yayi Magana zata hayayyak'o mai.


Hansai kuma ad'an Lokacin nan ta gane shayi ruwa ne don azabtuwa  da take domin Gwamma ta bud'e Mata huta. Yauma data tasheta tana bacci "k!e ke! tashi kizo ki min talllan zogale."


Mutsitstsike I'do  tayi. Gwamma tace banza Gansai ni tashi ki tafi."

Hansai tace "talla kuma! ni aiban iya ba."

Gwamma ta kai Mata duka yaran gari dake yi finsu kikai?


 Tashi Jummai tayi ta  Shiga d'akin "Haba Yaya wane talla kuma? ai kinsan ba'ai  agidan nan."

Gwamma tace "to kan Hansaai za a fara, haka ta taso ta agaba wata Jibgegiyar Langa ce ta d'ora mata. Malam ne ya fito Jummai tace "Saboda Allah Malam ace kamar Hansai za a aiketa Talla?.

 

  Malam yace "haba dai ai baidace ayi  ba Gwamma tace "wallahi bazan asara ba dole taje" Malam yace "to shike nan. Hansai Allah ya kiyaye kiyi hakuri ya fita Jummai na Mamakin canjawar Malam kwanakin nan Sam kamar tsoron Gwamma yake baya tanka mata.

  

Haka dai rayuwa tayi ta tafiya yau Fari gobe Baki Acikin hakan ba irin taskun da Hansai bata shiga ba, saboda Malam yanzu bai fiya Magana ba ,hakuri ne yazamo tushen Rayuwar Hansai.


   BAYAN SHEKARA DAYA

               

               

 kudakace ni fans ga wan nan ba yawa saboda Banda caji.

 

 

 *By Queen Meemi*

[12:31pm, 22/01/2017] 👑Meemi🔸: .






. .





⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣16❣

             *JAN 2017*


*®NWA*



     _*Queenmeemi.WordPress.com_*



*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's_*



_TUNATARWA_


 _Cikakkiyar Nutsuwar Ruhi ta tabbata ga Mutuncin da Tunanin Laifukan sa ya hanashi hangen laifin wani ,'yan uwa mu daina aibata 'yan uwan mu, mu guji yi da wani da aibata Shi, batare da hak'k'in sa ba._



              *Abuja*


Sumy ce tsaye tana jijjiga "ke kandala" ta k'wala kiranta a karo na 2 Jikinta na rawa ta tawo "gani Anty Sumy" tsaki taja "wato na baki wanki baki ba, ina kika tsaya?"

"Mopin nayiwa Antyn mubrk" Sumy tace "awajenta kike ko gun Umma?" 

"Aa gun umma"

 "To kar na k'ara ganinki acan, gashin can kije ki wanken Under Wears d'ina a Washing Machine" Jiki da b'ari ta tafi ita kam Sumy side d'in Anty Rabi taje, tana zaune tana karanta Novel ta tsaya "Anty sako daga Umma tace adaina arar Mata  'yar  Aiki, course ba ke kika d'auka ba, Anty Rabi ta had'e rai to mara kunya naji".

 Sumy ta fita tana k'unk'uni "inbanda Shima Dady da aure- aure Anty Rabi ai sa'ar Ruby ce" mtwss taja tsaki tayi side nasu.


Anty rabi kuwa inda sabo ta saba nan ta k'uduri Aniyar Dady na dawowa zata sanar mai itama zata d'au 'yar Aikin.


Haka kuwa akai A round 6 :pm tajiyo dirin motar Dady data guards din sa ,Zuwa tayi ta fesa wanka da kwalliya San nan ta tafi.

Mama da Umma ta gani kowacce a Hakim ce agefen sa Murumushi ya sakar mata "mum's Boys y gida" zama tayi tace "fine Dadn Boys".

 Mama tace Alhaji kenan idan an girma ai a sani tashi Sukayi suka fita, dayake girkin Rabia ne Hug ya bata, nan ta fara hidima da shi bayan ya kimtsa tace "Dady dama inason nai samu 'yar Aiki Saboda Shiru Side D'ina kuma gashi kowacce nasa sai a ce ba aso  ka kira.

 "Mum's boys ba damuwa ki nema" Dad'i ne ya kashe ta  tace tana zuwa.


After Some Minutes Rabia tayi dialing layin Maman ta ,bugu d'aya aka d'auka nan tace "Mama dama ina son Mai Aiki ne" daga can Mama tace "ba damuwa zan baki Nomber din Lami ki kirata, bari na turo miki" cike da jun dad'i ta kashe kirr sai ga Msg ya shigo.

Nan ta buga Layin din Lami daga can ta d'auka suka gaisa  tace "Rabia ce 'yar Maman kano" Lami ta washe baki "ranki ya Dad'e" nan suka gaisa tace tana son mai Aiki. Amma me D'an girma ba k'arama can ba." Lami tace babu damuwa Insha Allahu za asamu nan suka kashe.




     ***********

Bayan kwana 2 lami ta tafi gidan k'awarta shiga da sallama ta amsa "Aa Rai kanga Rai" nan suka b'arke da hira Lami tace to nikam Ana neman mai Aiki kin San ni k'anana nake kaiwa 'yan 11 zuwa 12 to tace 'yar me girma nake so" Delu tace tooo Zan Bincika miki ba damuwa."

Bayan tafiyar Lami Delu tayi tunanin kawai taje Gidan Gwamma.


Bayan kwana d'aya da Maganar. Delu taje Gidan Gwamma .nan hira ta b'arke na yaushe Gari zance har ya kai kan Hansai nan Delu tace :

 "Hmm haba da Sake ta yaya za'ace ki Zauna da katuwar Budurwa bakya Morarta.

Kibani ita Mutafi Abuja ta nemar miki kud'i ko Samira kya sai mata, sai kace ba Inna Gwamma ba mai Mugunta ba Dalili" .Ta bata hannu suka tafa tareda shewa


"Waima ina Hansai en take ne"? Delu ta tambaya.

 "Na aiketa rafi d'ebo tafasa cewar Gwamma

  Dede lokacin Hansai tashigo ta tsaya tsaye


       "Gashi Mama".



Gwamma ta kalleta "ke Hansai baki ga Delu bane? kin tsaya gansai ba gaisauwa. Mai suffar Munafukai waima waya baki izinin dad'ewa?

   

Jummai ta fito daga d'aki "ni nace tabiya ta sayo kuka"

Gwamma tace na gaji da Gulmarki Jummla tam".Ke kuma Hansai Algunguma Nagaji da Zamanki haka tafiya Dole ce ki nemar mun kud'in hidimar Bikin Dije inya tashi ehe.


Saura naji kingayawa Malam nida kene tayi k'wafa Shige ki  ban Guri."

ta shige sum -sum tai Daki Delu k'awar Gwamma tace

"Kai Mutuniiyata ,wan nan baza Umarni haka?" 

 tafawa sukai "ke to ni ta wasa ce ai barni da Munafukai sun isheni  nafisu na fiso dagani sai 'ya 'ya na....

 Tana shiga D'aki tasaki kuka tana Surutai tana cewa narasa  mena tsarewa Inna Gwamma wannan tsana haka tayimin yayi yawa dame zanji ya Allah ka kawomin D'auki takwanta akan karauni tabarmar dake D'aki Dakin kamar kurkuku babu daban kasa Saman sa sai A zara ga cinnaka ba k'warin dababu aciki ga Shirgi,duk wan nan Gwamma ce tayi bayan ta zama mai fada aji agidan tasa Hansai ta koma d'akin shirgin.

 


*****

  

  Acan tsakar Gidan kuwa Bayan tafiyar Delu ,sun gama K'ark'are Maganar Gobe za a kai Hansai Aiki 


  Taa   baje A K'ark'ashin Bishiya ana ta yiwa Jummala Habaici inda Sabo Jummala tasaba jin wannan dan haka tak'i kulata taci gaba Aikinta na had'a Danbu  A Zuciyar tana cewa Allah  ya shiryata Mata kamar Shed'an bata da Magana sai

ta sharri bayan ta gama taraba ta bayar  aka kaiwa Malam Gona ta.


   Jummai ta faki ido ta shiga D'akin Hansai ta tarar da ita tana ta kuka abun  tausayi Ta tasheta tace "haba Hansai meye abin kuka? sai kace saban  abu kullum fa kinsan sai Anyi haka a Gidan nan tashi kici Abinci miyi Magana dak'yar ta tashi kan ta nasara Mata Kamarya  tsage tafara ci Hannu baka Hunnu  baka Hannu k'warya tas ta cinye Rabanta da Abinci tin na safe Gashi yanzu kusan La'asar bayan tagama  tasha ruwa tadawo D'akin Jummala tace "Abinda zan gaya miki.

   

   

 Kinga tunda wannan Matar tafara wannan Maganar  ta kaiki aiki to sai tayi  ki tsare mutuncinki. Yadda Matar nan takeso taga wani abin kunya yasameki ki kula

 Da Sallah da Addua Allah ya tsare ki da ina da iko da na hana Amma ko Malam bai isaba bareni zan dinga yimiki Addu'a Allah yakare.

 

  Suna cikin Magana sukaji Ihun Dije nacewa  "Mama suna  ta  Zaginki ."

  nan  Gwamma tayin kukan  kura ta tashi tace "barni da Shegu yau zasuga tijara agidan nan ta Dauko ittace taiyo,D'akin a fusace tana zuwa tad'aga ice zata Makamusu Malam yayi Sallama da Gudu ya zo ya kwace ice yace "haba Gwamma kullum kebaki da Aiki sai fad'a kishiyar da Yarinya."

  

 Tace "dalla can "Malam matsa kabani guri sahurami kuma wallhi sai na suburbud'i Hansai a Gidan nan ko tai bacci Zatasan sunhad'u suna zagina."


Jummai tace "wallhi ba Zaginta Mukeba".

 Allah sarki Hansai tini tarude sai Rawar Jiki take saboda tasan Gwamma da Mugunta Dije

sai Gwalo take mata .


Malam yace "baki isa kidake taba ba wallhi babbar

banza Mara Girma saina Jiki."


 Gwamma tana kad'a jiki Malam yace jummai kama Hansai kuje  d'akinki".

 

 Gwamma tace Malam "Gobe Hansai zan kaita Aiki har min Magana da Lami za akaita Abuja."

 

Cak! Malam ya tsaya baice komai ba Yace "Naga yanda za ai taje Allah ya kaimu goben."





*By Queen meemi*




.

[7:08am, 23/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣17❣

               *JAN 2017*

*NWA*



*Queenmeemi.wordpress.com*




*_This page Dedicated to Anty Maijidda Musa Tnz A a lot_*




_TUNATARWA_

_yawai ta istigfari Awurun Allah ,yana saukaka Samun biyan bukata_ 



******

Washegari kuwa da Asubayin fari Gwamma ta fito da Hansai ko gama wartsakewa batai ba ta tulo Mata wankin ta tace tai maata na k'arshe kan Rana ta gama fitowa, ga sanyi hakan tayi sai 7 ta gama.


 K'arfe Goma Hansai ta gama Shiri sai kuka take Malam ya fito "Gwamma nadai gaya Miki Yarinyar nan baza taje ba, wallahi in taje ranki sai ya b'aci."

  Gwamma tace sai de ya b'acin ,haka kawai Ga hanyar samu sai na zauna tunda ita ba Aure dole ta nemar mun kud'I. Don baka ga Laran Gidan Toka ba sai busha sha Suke da Kudin Aikin nata."

  

 Malam yace "to ki kai Dije ,Amma ba Hansai ba tunda ba ' yarki bace, Hansai Jeki maida kayan nan." Cike da D'oki da Jin Dad'i ta koma D'akin ,Shi kuma ya Fita Gona."

 

 Bai dad'e da tafiya  bada ,sai ga Delu ta Shiga gidan. Da Zumud'i Gwamma  ta tare ta,nan taje ta fito da Hansai "fito Algunguma komai Malam zaiyi saide yayi sai kinje."

 Jikin  Jummai a sanyaye ta kalli Hansai tacea "Hansai ki Rik'e Allah ki kiyaye Mutuncin ki ki Zauna Lafiya dakowa, Allah ya karemin ke" Rungume Jummai tayi "Inna banason tafiya"

 

 "Fito ko na zo na makeki da duka" cewar Gwamma Jummai tace "Amma dai Malam ai ya hana. Gwamma tace "tafi can wayake take" nan ta kalli Hansai "ke kuma d'auki kayan nan ki D'ora akai, wallahi idan kiyaje bakya Aiki sosai sai kinci na Jaki.

 

 Delu tace sai kizo mu tafi" kuka Hansai take tamakar taci babu da k'yar ta tafi, Jummai ma kuka suna fita Gwamma Tai shewa "wayyo Ina daga zaune kud'i suna zuwar min." 


Delu kuwa suna tafiya sai hantarar Hansai take har sukaje Gidan Lami dama Jiran su ake yara ne su biyu Hansai ta uku .Amma duk ta fisu Girma Lami na ganin Hansai tace "Yawwa kinga wan nan zata dace da Alama zatai tsafta". D'ari biyar ta kawo ta bawa Delu "ga Ladanki" nan sukai Sallama har ta tafi ta dawo "Yawwa Lami kinga Hansai sai kin Jamata kunne domin bataji.". Lami tace "yo ai dama duk 'yan Aiki sai na Jamusu kunne" sai wajen k'arfe Goma Shabiyu suka tafi,in Banda kuka ba abinda Hansai keyi.



Malam kuwa yana komawa Gida yaga Jummai na kuka ya tambaya tace "Ai antafi da Hansai." zama yayi yace "Amma Gwamma Allah sayya yimin sakayya duk abinda kike Allah zai saka mana" Jummai muyiwa Hansai Addua, Allah yasa hakan Shine mafi Alheri agareta ,Allah ya bata kwanciyar hankali" Jummai tace "Amin."


Sunje tashar mota suka shiga fuuu Mota taja sai kano ta Dabo Tunbin Giwa kodame kazo Anfika ,sai la' asar sukaje nan Lami taje duk Gidan dake bukatar Yaran takai musu ta k'arbi Kud'in sallama Dana kowo su.Hansai ce ta k'arshe ta kaita Gun Maman Rabia dake kanon tamfatsetsen Gidan suka shiga Hansai nata Raba Ido shigar su Falo yayi dai-dai da fitowar Mama tace "Aa Lami kece da Yamman nan!" Lami tace "wallahi."


Au! har an Sami 'yar Aikin Lalle Lami agaishe ki" nan ta zauna tacii Abinci San nan tai shirin tafiya nan ma mama ta bata Kud'in kawo wa ta fita


Idan Hansai ne suka kawo ruwa Lami ta kirata tace "ke hansai wallahi karnaji karna gani  Banda sata da k'azanta zan zo d'aukanki Ganin gida in kikai watanni "nan tayi tafiyar ta.


Mama kam Umartar Hansai tayi data yi wanka hakan kuwa akai ta kirawo iya mai Aikinta tace ta duba kan Hansai nan ta tsefe mata wajen 8 na dare aka wanke kan tayi wanka sosai ta ci Abinci tayi Sallah  ta kwanta bacci.


*washegari*


Da safe Hansai ta karya da breakfast mai Dad'i nan iya tayi Mata kitso Mama na kan kujera Rabia ta bugo waya tace "an samu! Mama tace "gata nan kuwa Masha Allah, an samu" yanzu sai ki turo driver yazo ya d'auke ta, Rabia tace "to Mama Amma sai gobe, saboda yau yana da uzuri" Mama tace "ba matsala" nan ta kashe .


Ta kalli Hansai tace "ni meye Sunanki na Gaskiya ne? Hansai tace "Hansai Shine na Gaskiya" iya tayi Dariya "Hansai ai ba Sunan Gaskiya bane" Mama tace "A toh".


Amma kinayin Makarantar Allo Acan? Hansai tace "Eh ina Makarantar Allo, Nayi Izifi Arbain" Mama tace "Masha Allah.Boko fa" iya tace ai kinsan k'auye basu damu da boko ba,Na Addinin Ma wasu ko ansasu basa yi" Hansai tace "Nayi boko Ajina uku a Secondary" Mama tace Lalle ki Godewa Allah.


Bayan an agamai Mata kitson Mama ta kuma sata tayi wanka nan tace kinga Abuja za'a kaiki kina tsafta ,duk da naga balaifi." Hansai tace "to" Hansai kuwa duk bidirin nan zuciyar ta na kukan tuno inna da baba haka tayi yinin nan har ta dad'a fes ba Tsangwamar Gwamma.


Washegari kuwa wajen 12 sai ga  Ashiru driver bayan yaci Abinci nan Hansai tasaka kayanta bayan motar suka d'au Hanya sai Birnin Tarayyya.


Bari na D'an huta kan su Hansan su sauka.

    Sister's kuyi Hkr ba kullum zakuna jina ba saboda matsalar ba wuta ngd.

    

    

    *By Queen Meemi*



[9:52am, 26/01/2017] 👑Meemi🔸: . . .




⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣18❣

         *JAN 2017*




*Queenmeemi.WordPress.com*



*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_*



_Sakon ku ya iso gareni masoyana na gode da kulawa❤_

*****

Sai wajen k'arfe 6 dai -de su Hansai sukaje Lokacin taci bacci ta k'oshi Hon din da Ashiru nayiwa Maigadi ne ya tashe ta ta bud'e Ido tayi tozali da k'awataccen  Gida juya baya tayi taga duk Layin da suka shigo kusan hakan Gidajen su ke .Maidadi ne ya tashi ya bud'e zirif Ashiru Driver ya shiga yayi parking a gurin adana Motoci ne Reras a ajiye, ahankali ta fita  Ashiru ya fito Mata da kayanta daga bayan Motar, nan tayi Duru- Duru sai kallon gidan take wanda ada tana ganin na Maman Kano mai kyau ,sai taga ko Rabin kyan wan nan be kaiba da Girma da k'watuwa.



 Ashiru ne yayi gaba tabishi suka danna door bell da dad'ewa wani Namiji yazo ya bud'e  ya basu Hanya suka Shiga ya cigaba da goge -gogen sa y Mamaki k'arara akan fuskar Hansai,Masha Allah ta kira azuciyar ta Sakamakon Tozali datayi da had'ad'd'en falon wanda dukan sa acircle yake Ashiru ne ya tsaya can sai ga Anty Rabi ta fito daga Part nata da D'an saurin ta d'auke da Murmushi saman fuskar ta ,tace "Aa Sannu Ashiru kunsha Hanya!" Alamar russuna Mata yayi yace "eh Wallahi Maman tace agaishe ki" nan ya juya ya fita Rabia ta kalli Hansai "muje ko" zungi zungwi ta bita sai kallon waje -waje take tana Mamakin tsaruwar Gidan Ahankali ta furta "Aljannar Duniya"

 

 

 Jikake ta guum! ta  k'ume da k'ofar Shiga paty d'in Anty Rabia da Hanzari Anty ta jiyo "Aa kiyi ahankali fa" nan suka shiga b'angaren Antyn baki sakin baki Hansai tayi ganin wani falon wanda yafi kyau ,nan tayi ta k'auyancin ta zama tayi gefen kujera ta kafawa Tv Ido tana kallon film d'in da ake ga sanyin Ac na hurowa had'e da sanyayan turaren wuta zo kuga yanda Hansai ta langwab'ar da kai gefen kujera kamar tai bacci.

 

 

 Anty Rabia kam dawowa tayi d'auke da Khalil a Hannu ta zauna tace "ya Sunanki ne?"  Hansai ta sunkwi da kai Sunana Hansai .

 Anty tace "Madallah Garinku fa?"

 Tace "Bunkure".

 kina Makarnta tace "eh Ajina Uku a secondary" (oh su Hansai Ana ji da Aji ukun din nan da akai)Anty tace "Madallah, tom kinga yanzu Aiki kikazo na Farko banason k'azanta na Biyu Banson Gulma kinga da 'yan Aiki wajen biyu  A Gidan nan Kamar ki da tsohuwa ga Namji mai Goge -Gogen Babbann falo,  ki Kame kanki,Banda shiga inda ba hurumin ki ba, Zakina min Renen boys D'ina  Mubarakh da khalil ,San nan Zakina Wanke-  Wanke da Gyaran kitchen, nan falon Zakina Shareshi da Goge kujera ,zakina Goge  kayansu Tv vedio ,center Table su Dining Teble duk kiyi sai ki  Moping  tile d'in da D'an abinda baka rasa ba. Shine kad'ai iya Aikin ki, Maganar kud'in Aikin ki Kuma dama Munyi Maganar da Lami."

 

Dadi ne ya kama Hansai Jin Aikin bame yawa ba don ak'auye wanda take ya ninka wannan ,nan ta d'ago "Insha Allahu Anty zanyi abinda kika ce finsa Ma" Anty Rabia tace "yawwa yanzu kije zan nuna Miki toilet kiyi wanka duk da ba anan Zakina kwana ba akwai Shashin Masu Aiki" Hansai tace "tam Anty." 

                                                                                                                                                                                        

                                                                                    Dai-dai Time d'in aka kira Sallah nan ta tashi tayi gaba ta bita suka fita Daga part d'in suka koma Ainihin Big Falon, San nan sukayi wani dan sako daga Arewa nan suka Shiga wani korido San nan suka shiga wangamemen daki da Madaidaitun katifu Guda Hud'u aciki,Gefe ga wasu akwatin Katako Babba Doguwa kayan su  ne aciki.

                                                                                    

                                                                                     Kande ce da Karime suna Alwala a Band'akin dake Cikin D'akin Anty tayi Magana nan suka fito duk suka Zube.

                                                                                      Anty tace "ina kuke kwance? wacce katifa ce Empty Kande tace "waccen ta Lokon e babu ,wan nan ta Tsakiyar nice akai sai ta Gefen Karime waccen kuma ta iya Abu ce sai ta Lokane ba kowa."

                                                                                       Anty tace "ok naji ke Hansai kije waccen nan zakina kwana ki aje kayanki Acikin Wan nan doguwar Kwatin tunda nasan akwai inda babu komai aciki, Bayan haka yanzu ki fara wanka kan ki sallar tunda ba a tayar ba."                                                                                                                                             Idan kinyi Sallaar kizo side Dina."

                                                                                        Hansai tace "to" nan ta fita zuwa kuwa  tayi ta aje kayan nata Acikin akwatin ta zauna kan Luntsumar katifar San nan ta tashi tashiga band'akin tayo Wankan ta fito .

                                                                                        Lokacin su kande na zaune sai hira suke ta canja kaya tayi Sallah San nan ta kalli su Karime tace "Sanunku" sukace "yawwa" suka D'an tab'a hira San nan ta tashi ta fita.

                                                                                         Sai hanyar ta kauce Mata ta Manta part din Anty tarasa ina yake  sai zagaye  falon take duk girman Shi, take nan tayi part din Dake Gabanta b'angaren Hagu Alhalin ita Anty tana side na Dama shiga tayi a hankali ta Danyi sallama  ta shiga Zuby ce ta d'ago "waye?.

                                                                                          Hansai tace "nice" sai Lokacin ta gane ba gun bane Zuby tace "ke daga ina?".

                                                                                           Hansai tace "nayi Makuwa ne!! gun Anty Rabia zani."

                                                                                           Zuby tace "oya get out ,ba nan bane."

                                                                                            Haka ta juya sai Lokacin ta gano gun ta shiga da Sallama Anty na Sallah ta d'au Khalil tana mai Wasa sai Dariya yake bayan gama Sallar Anty tace "Jeki kitchen akwai abinci ki d'auka" ta nuna mata.

                                                                                             Tashi tayi tabi ta Gefen Dining ta yi kitchens d'in sakin baki tayi tana kallo nan ma kamar ba Kitchen ba ga had'uwa ga Girma sai kalle -kalle take San nan tadauka ta fita, tace Anty na d'auko"

                                                                                              Anty tace "ok."

                                                                                               Hanyar fita tayi  tace "dawo ki Zauna anan kici nan ta zauna tana ci Dad'i ya cika kunnen Hansai sai Hamdala take ,nan ta tuno Inna da Malam tad'an Share hawayen da suke neman zubo Mata,tas ta cinye takai kwanon Kitchen.

                                                                                               Ta fito tace "Anty ina Omo zan wanke kwanukan" Anty tace "habade! kije kawai ki kwanta ki huta."

                                                                                               "Hansai tace Anty bari nayi kawai" nan ta shiga ta nuna Mata sinck ta nuna Mata inda zata matsu Ruwan San nan ta fita .

                                                                                                Cikin Mintuna ta wanke komai ta kife ta fita ta tsugunna tace Anty "na gama" Anty tace "to Hansai ki je ki Huta."

                                                                                                 Nan ta fita bata b'ata ba Saboda ta Gane gun yanzu sai Hira su Karime, suke nan ta Zauna Lokacin Iya ta shigo Iya tace "Aa Kande kuce Sabuwa Muka Samu?"

                                                                                                  Hansai tayi Dariya ta Zauna Iya tace "to Sannu da zuwa 'yata Hansai" tace "yawwa" Nan da nan tabi su Karime sai hira suke kamar sun dad'e da Sabo dama 'yan aiki in sunga Juna akwai Saurin Sabo wan nan ke nan.

                                                                                                  

                                                                                                  kubiyo ni

                                                                                                  

                                                                                                  *By Queen meemi*

[12:16pm, 27/01/2017] 👑Meemi🔸: . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣19❣  

              *JAN 2017*

®NWA


*_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_*



_My fecebook fans ina miko gaisuwa gunku nagode da kulawa_


********

Yau kwanan Hansai uku haryanzu agajiye take yauma sai wajen 9 Hansai ta tashi taga d'akin wayam duk basu Kande da Sauri ta tashi tayi waje Part dinsu tayi tana shiga taga Anty na breakfast tsugunnawa tayi "Anty kiyi hakr na Makara."


 Da Murmushi Anty ta juyo "Ai nasan baccin gajiya ne ,yanzu sai kiyi" da sauri ta mik'e tai kitchen ta fara Aiki sai wajen 11 ta gama San nan tayi break tafita nan taga iyalan gidan a big falo nan Gabanta ya bada Ras! tazo zata wuce Umma ta kirata taje duk suka zubo Mata ido, tace "ke 'yar Aikin Anty ce? tace eh  Mama tace Gata kwa kyakkyawa Sumy ta tab'e baki ta kafa uban d'auri da alama school zata "yauwa ke ya sunanki? ta fad'a Sumy tace "biyoni" salo -salo ta bita ta Shiga d'akin su ta dauko mata under wears da bra ta wanke ta kalleta "kifa wanke tas bansan Almundaha na" tace "to Anty" k'was- k'was ta fita Hansai ta mik'e tayi part d'in Anty tana zaune tana bawa khalil tea ta tsugunna "kinga Anty d'aya daga cikin 'yann Gidan nan  tace na wanke Mata" tsaki Anty tayi "oh wad'an nan yara ba kunya Bra ma din  sai an wanke musu duk gayun tsaki tayi, ni sun hanani Kula nasu Amma bakomi je kiyi."

 

 

Nan ta tashi taje can D'akin su ta tarar da karime na ninke kayan ta tace karime don Allah ina ake wanki karime tace acan bayan D'akin nan ne bari na Nuna miki nan ta tashi ta fita ta bita ta zagaya da ita ta nuna Mata hakan ta zauna tad'au wani boket ta zuba tana wankewa tas ta wanke ta shanya.


 Ta koma D'akin su tayi wanka Bayan awa uku Sumy ta fako motar ta ta shigo dai de Sady ma ta fako Tata ta shigo Hansai Lokacin na zaune a kusa da flowers Sumy tace "ke d'ebon kayan" shaf ta manta da gudu ta tashi tayi bayan nan taga duk sun fad'i k'asa sun b'aci tsaki tayi ta d'auka takuma wankewa.

 

 San nan ta koma ta shiga d'akin nasu birjik kowacce daga ita sai shimi tace Anty na wanke Amma na koma kayan duk sun b'aci ran Sumy ya baciallema 'yar Aikin nan! ni zaki b'atawa kaya" ji kake kauu ta kai Mata Mari Ruma tace kai Sumy me tai miki kin fiya zalinci" Murgud'a baki tayi Aiki nasa ta ta b'atan."

 

  Nan ta kalleta "Get out kona Mauje ki Stupit kawai" kuka Hansai take tafita gaanin Anty Rabia zaune a big falo yasa ta D'an kawar da fuskar ta nan kwa ta ganta "tace zo nan" taje ta tsugunna meya sameki nan ta gaya Mata cikin b'acin Rai Anty taja Hannun Hansai suka tafi d'akin ta shiga tace "ke Sumy me yarinyar nan ta miki?.

  

 Sumy tace "Aiki nasa ta."

 Anty tace "ke tsaya kiji karma wanda ta kuma sata Aiki tunda Baku kuka d'auke ta ba."

Sady ta turo lips "Dady ne ai ke biyan Albashin ta, don haka dole musaka ta."

 Anty tace "Nadai gaya muku" ta fita afusace Dariya Sumy Sady da Zubo suka saka "Lalle Matar nan zamusa k'afar wando d'aya da ita."

 Ruby tace "ni bakuga bana shiga harkar ta ba don gani nake sa'ata ce."

 Zuby tace "yar Aikin  nan munafuka kullum tana Sanye da Hijab sai kace Matar Liman."

  Sumy tayi tsaki "zan San ya zan ,dole a bamu 'yar Aiki d'aya kuma wan nan yarinyar muke so tana mana wankin k'ana nan kaya, inga Anty sai ta mutu"

  Sady tace "Good idea tawan."

  

Yaya Babba Ruma tace 'kukam Anyi banzaye ace har sai me Aiki ta wanke muku su bra Anji kunya" ,Ruby tace "haba Anty Ruma Lokacin Abu ayishi."


    *Bayan wata d'aya*

    

 Hansai tad'an Saba da Gidan har D'an K'iba tayi Skin colour d'in ta yafara fitowa sai tayi kyau dama wahalar Gwamma ce ta dafar da ita ,tana zaune agefen kujerar falon Anty tana kallon wani Film BARAUNIYA sai Dariya hansai ke ga Mubarak agefe shima yana taya ta kallon tunda ba School yau weekend. 

 

 Anty ta fito cikin Shiri oya Hansai tashi Mutafi Hjab dinta ta saka ta dau khalil suka fita.Mubrk na Dan tsalle- tsallen sa don zasu Unguwa ba kowa a Big falo duk suna d'aki bacci.

Nan su Anty suka fita harabar Gidan inda d'aukacin Motocin Gidan ke suka doshi motar Anty duk suka shiga ta bata wuta suka fita daga Gidan tun zuwan Hansai sai yau ta Lek'o wajen wata d'aya kenan sai kalle- kalle take ganin yanda garin yayi Mata kyau .


Wani Supermarket suka je zuu suka tsaya a harabar kantin suka fito Anty tace "Hansai fito Mana" nan ta fito suka shiga nan k'auyancin Hansai ya Motsa sai Duru-Duru take Anty tace "kifaa nutsu Hansai."


kayan aka jidarwa Hansai irin yan kantin nan masu iri d'aya masu siket manya San nan aka d'ibar Mata atamph,da bra su pant da body spray  wajen biyar masu kyau akai counting Anty ta biya suka fito nik'i nik'i da kaya. 


Direct wurin wani tailor d'inta taje ta bada a d'inkawa Hansai nan ya Gwada ta yace 1 week zai gama sai wajen 1 suka dawo gida a gajiye saboda gajiya Anty tace Ashiru ya gyara Mata parking d'in Motar suka shiga.

Sumy ce da Sady sai tirk'ar Shoki suke a tsakiyar falon suna kwaikwayar yanda na tv d'in keyi kowacce da jins da tsht , domin vedio din suka saka. Anty ta tab'e baki sukai side dinta.


Hansai kuwa d'aya daga cikin kayan da Anty ta sayo mata ne Anty tace ta saka ta daina sa wadanda tazo dasu daga k'auye zo kuga yanda sukai dab'as ajikin Hansai dayake Allah ya wadata ta da hips me d'aukan hankali Anty tace "dole kinasa hijab kici gaba da sawa shine dai-de."


Hansai tace "to" nan ta d'auko mata wani k'aramin Hijab d'inta tace duk ta daina sa wad,ancan kan a d'inko Mata Sabbi .Hawayen Dad'i ne suka zubo Mata tace "Anty na gode" tace "no ke Amana ce agareni."


 Da zumudi ta tashi ta tafi b'angaren su, kande da karime nata hira ta zauna "kuuu! zo kuga kayan da Anty ta sai min" ta yaye musu Hijab tace kunga d'aya ta bud'e Leda tarik'a zaro su wajen kala biyar, San tace kuma akwai d'inkin wasu."

 

Kande tace" Lalle kin cab'a dama nice gun Anty" karime tace "hmm mu kam ba wacce ta tab'a saimana kaya daga Sallah sai Sallah sai kuma kwancen su Sumy."


 Hansai tace "kunsan kowa da irin kyautar sa."

 

 Karime tace "Hansai kin sanme? Hansai tace sai kin fad'a! tace "ina zuwa" nan ta Lek'a kudu da Arewa bata ga kowaba ta dawo....

 

 

 *Queenmeemi.WordPress.com*

 

 *By Queen meemi👑*

 

 

 .

[12:16pm, 28/01/2017] 👑Meemi🔸: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣20❣


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



*********


 "A 'ya'yan Gidan nan wallahi kinga Sumy wuta ce Saboda sa Aikin ta da fad'an ta, Zuby kuma isah Ruby kuma Zuma ce ga zaki da Harbi Anty Ruma kuma" Shiru tayi ganin yanda Kande ke karkarwa Hansai kuma Tai k'asa da kai ad'arare Ta juya Zuby ce tsaye tana kallon su ta saka wani Material me Blue da Pink fuskar nan sai k'yallin Make up take sai tashin kamshi take tace "Lalle karime kinsamu sake kinji jar miya kin Tara su kina Gulmar mu ko? dole nay punishment dinki next bazaki ba."


kuka take "kiyi hkr" tafiya ta fara ta kalli Hansai "ke zo ki min Aiki" Jiki na rawa ta mik'e ita kam tsallan kwad'o tasa karime acan waje, itakam Hansai d'akin baki Zuby ta kaita tace ta dad'a gyara shi ta sa Room fresh haka ta fara ko ina sai data goge ya dawo fes sai wajen 4 ta gama taje d'akin su Zuby tace to "Anjima zan bak'o Idan yazo karki bari nai Magana kije kitchen ki had'o Drink da Cup da Cincin kingane" tace "eh Anty ,zan iya tafiya?"

 "well zaki iya" fita tayi ta tafi Bangaren Anty .

 

 

 Bari mu leka b'angaren Su Gwamma muga wai nar da suke toyawa

 

        *MANGALU*

           

kuka Gwamma keyi tace "Amma kuwa Delu kin badani akan bashi shine zaki taran Mutane!" Delu tace "eh na Tara lokacin da kike so na baki har Gida kikaje don biyan buk'atarki Amma don ke dama taurin bashi gareki yau wata d'aya kenan ina son ki bani kink'i, to wallahi yau sekin bayar".



 Gwamma ta share Hawaye bazan bayar ba, kinjiko,Delu duk abinda zakiyi kiyi."

 Nan ta koma gidan ,Delu ta bita suka tsaya tsakar gida tace baza fa ta sab'u ba, ki bani kud'i na, uzuri gareni."

 

 Ke kika sani Amma wallahi Delu bazan bada ba sauke Mayafi Delu tayi tasha damara tace "yo kinyi Asiri kin Raba Masoya kin had'a gurmi amfasa Auren shine zaki ce haka ko, da komai ya kammala."

 

 Jummai dake d'aki ta dafe kirji dama Gwamma ita ta Raba Hansai da Muntari tashi tayi ta fita lokacin Gwamma da Delu sun kaure da fad'a Jummai tace "Subhanallah! ya da abin yara?"

 

 Cizo Gwamma ta akaiwa Delu tace "Lalala kika cijen?"

 Dayake Delu Jibgegiya ce tafi Gwamma girma ta naka ta da k'asa ta hau kan ruwan cikin ta tana duka sai ihu Gwamma take Dije ta fito tana dukan Delu ta baya nan ta hamb'areta.

 

 "ki bani kud'ina Idan ba haka ba wallahi sai kin gane ban da kyau" Gwamma data Jigata  sai kitan Malam! Malam!!  take .

 

 Jumma tace "Delu kiyi hkr"

 

 Delu tace "ke yimin shiru wallahi Idan bata ban Kud'in nan ba sai na kaita gun 'yan sanda." Adai-dai time d'in Malam ya shigo "Me zan gani haka nan, Delu ta mik'e 

Gwamma ta Jigata ko Hannu batta iya d'agawa yace Meye haka nan  da Girman ku ba yara ba."


Delu tace "kudina zata biya ni bashina" yace "Nawane? tace "dubu Goma" ya jin-jina kai a "yanzu da ake wiyar Rayuwa Gwamma kika ciwo wan nan bashin? to ita ku sai kibiya ta."


 Gwamma ta tashi ta face Hanci wallahi kin daki Kud'in ki Koni ko ke."

 Delu tace mu zuba D'an Halak ka fasa Jarababbiya afusace ta fita Gwamma ta shige d'aki tana huci Jummai ta fasa dariya tare da cewa "Allah ya kara" ni meemi bace "Ameen"

 

 Ga wan nan ba yawa fans Sakamakon hannu na dake ciwo shiisa banyi da yawa ba.

 

 

 *Queenmeemi.WordPress.com*

 

 

 *By Queen meemi*

 

 .

.

[8:33pm, 30/01/2017] Miemee: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣21❣

            *JAN 2017*



*®NWA*



*_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_*




*_Sakon Nuna kulawar ku gareni  masoyana duk ya iso mun, Nagode da kulawar ku, kuma na samu saukin hannun nawa nagode_*



*********


 Wajen k'arfe Biyar bak'on Zuby yazo tana d'aki zaune sai fesa kalolin Perfume take masu dad'in k'amshi Ring d'in wayar ta ce ta hau Ruri nan ta D'anyi Murumshi ta D'aga "Hello habiby" daga can ya amsa da yana D'akin bak'i, Ruby dake kwance Rigingine idon nan yayi JaJawur tana Chatin ta Juwo "wow see u Baby, Amma kin had'u sai ina haka?"

 

 Zuby tace "fawwz ne yazo" Ruby tace "ok Ki gaidashi" k'was k'was ta fita kamar mai zuwa Gidan Biki tazo ta wuce Hansai na zaune a Big falo tana yankewa Sady farce ,Zuby tace "ke Hansai ki kawo Drink nan da 2 mints" Sady ta d'agawa Zuby hannu tace sai Zubyn mu irin wan nan wanka haka" Zuby ta farfara Ido ya San ranki Part of my Life yazo ai Dole na Gwangwaje" ta tafi tana juyi.

 

 

 K'ara Sady tasa "Lalala kika yanken Hannu!" Mangari ta kaiwa Hansai Fool Girl kawai, ni ina ganin cikin Kande da Karime kamar kin fisu Dama dama ashe kema hakan ce." Hansai kam Raba Ido take  "yi hkr Anty" tsaki Sady tasa ta Maida air piece Kunneta ta tashi ta bar gun Hansai kuwa da bak'in ciki ne ya cikata, ta tashi Jiki a Sanyaye ta shiga kitchen ta had'o Drink a Cup da Cincin tayi hanyar D'akin bak'i da sallama ta Shiga taje ta aje Zuby dake zaune suna hira tace "ke Hansai zo nan wazai zuba mai."

 

 Juyowa Tai ta d'au cup ta Murda Juice d'in ta tsaya ta mika mai kallonta yayi "thks" kan ya Amsa ta saki ji kake fas! a kas.

 

 Hannu tasa abaki na d'imauta Zuby tace "ke wai baki da hankali ne?" ta kai Mata Mari bar nan aguje ta fita Zuby gun sa  "Sorry my Fwwz" nan ta Goge mai yace ba damuwa.

 

 fawwz kenan Dan kwalisa sai basar wa yake ita kuma hakan da yake sai yake birgeta.

 Hansai kuwa gurin Anty taje tai Mata Aikace Aikace San nan ta dawo falo ta d'au khalil da mubrk suka tafi can harabar Gidan taanai musu wasa Sam tama Manta da wasu Zuby k'arfe Shida dai-dai Motar Dady ke shiga harabar Gidan asan nan lokacin kuma saurayin Zuby suka fito zai tafi.

 

 

  Da gudu Mubarak yayi gun sa "Oyoyo Dady" Khalil dake Hannun Hansai sai ihu yake yana San zuwa Alama yayi da Hansai ta kaishi ,da sauri taje bakin Motar Dady ya karb'eshi ya D'an kalleta a fakaice.

  

 Jikin Zuby ne ke rawa Ganin Dady da tayi Domin ta San kwanan zan-cen da D'an sauri fwwz yaje ya gaida Dady ba yabo ba fallasa ya amsa ya had'e Rai nan yayi wa Zuby Sallama ya ja Motar sa ya fita daga Gidan da gudu tayi cikin gidan.

 

 Cike da b'acin Rai ya mik'awa Hansai yaron ya shiga cikin Gidan duk da Part nasa bata nan ake bi ba Amma so yake ya Sab'arwa Zuby da k'araji ya Shiga "Ke Zubaida! Zubaida! 

 

Tana daki Jiki na rawa mama d'ake daki ta fito haka Umma sai Anty daga karshe sun San anyi lefi inde Dady akaji yana kiran nan.Zuby ta fito yace ke" wace irin Yarinya ce? ba na hanakiw tsayawa da wan nan Yaron ba? ko so kike ubansa ya rena ni to wallahi ki shiga taitayinki ba wan nan bama bance ba yarinyar da ta isa ta tsaya da saurayi ba sai kun gama Degree.


Nan  su Sady ma duk suka fito jiki na rawa yaci gaba bakwa koyi da Rumasa'u abinda nace Shi take yi yanzu ba gashi saura watanni ta gama ba to wallahi zan muku fata- fata yanda nake Babba agarin nan, ba kowa nake so yazo Gunku ba sai D'an wane da wane kuna jina?"



 Suka "eh" San nan ya kalli Mama da Umma yace Last warning da zaku bar wata Yarinya ta tsaya da Saurayi" ran Mama daya b'aci ta tashi ta bar gun Anty rabia tace "haba Alhaji wan nan da ba" ..D'aga Mata hannu yayi ya fita .

 

  Zuby kuwa d'akin Mama ta shiga ta fad'a Jikinta tana kuka "Mama Gaskiya nikam ina son fawwz, shima fa Dad nasa me kud'i ne."

  Mama tace "Zuby ki bi Komi a sannu ki dakatar da zuwan sa atoh kin San Dad  Bai iya fad'a ba agaban kowa yi zai yi idan Ransa ya b'aci".

  

  Ruma ta shigo tace "Zuby juyo ki kalleni, kin san dai ni nice babba anan Gidan Amma kina gani ina bin abinda Dad yace ki kiyaye" Sady ta shiga "oh Zuby ke meye yanda kike 'yar Manya ace kina wani son fwwz ,kin san de Baban sa yaron Dad ne nikam sai na zaba" Zuby ta bige bakinta. "Bansa dake ba yi mun shiru" nan ta juya ta cigaba da kuka.      


                                                                                AD'akin Umma kuwa Ruby ce ke tsaye tana Jijjiga Umma nifa na Rasa gane Ra'yin Dady duk wanda yace yana sammu sayya ce Bai masa ba, haba" Sumy tace "atoh" Umma tace "kudai kubi a sannu musammm ke Sumy mai rawar kai" tace "kai umma."

                                                                                                                                                                                              Anty kuwa dake ta tunani tace tabdi gaskiya Dad yana da daukan dala sai kace wanda zai jika Yaran yasha Sai kace wasu hurul'ain saboda kyau tsaki tayi. lokacin Hansai ta shigo ta mik'o khalil tace "Yawwa zo."

                                                                                                                                                                                              Zaunawa tayi tace to "Anty" nan ta zauna tace abinda nake so dake tun lokacin da aka kawo ki Allah ya Doran tausayin ki Iamatsayin kanwa nake d'aukanki yanzu kinga watanki 2 agidan Nan inaso ki dada nutsuwa ki bi duk wata Dokar gidan nan kinga su Sumy ba kunya garesu ba tunda sukaji Dad yace duk wace yar,Aiki zasu iya sata Aiki ina sane nasan Salon yanda suke saku Aiki na fitar hankali  Musamman ke tunda suna ganin kina da tsafta kuma kin fi su kande wayewa to ki dada kiyayewa kinji."

                                                                                                                                                                                               Hansai tace "to Anty tace Ngd Anty ,bari naje d'aki" tunda ta fita take kuka sakamakon jin dadin Yanda Anty ke kyautata Mata, tuno Malam da inna da tai sai kuma Gwarzon ta Muntari ko ina yake Allahu ya Alam, sai kuma can ta tuno ita fa ba'asan iyayen ta ba, da sauri ta kori wan nan tace Malam da inna sune Murumshi tayi ta shiga side nasu.

                                                                                                                                                                                               

                                                                                                                                                                                                ji tayi su Kande da Karime na Gulma ta zauna tace "kunga ku daina Gulmar su  babu kyau barin  ke Karime kin manta wuyar da kika sha ran na." Kande tace "hakane fa" nan sukayi  shiru.

                                                                                                                                                                                                

                                                                                                                                                                                                Hansai kuwa akwatin ta ta bud'e tasa hannun ta nan ta zaro wata Leda ta rasa ta meye Lokacin duk su Karime sun fita wanke -wanken dare jiki na rawa ta bud'e  ledar kud'i ne a ninke a ciki sai farar takada da hoto ahankali ta juya Hoton Ganin fuskar Muntari tayi nan tasa Murumshi ta tuno Lokacin da zai tafi birni ya bata tsai ta k'urawa hoton Ido ta tuno Lokacin dayaje Birni ni ya d'auka da Sallah sai Kud'in data irga taga dubu biyu ne Hawaye ne suka subo Mata ta warware wasik'ar tun Lokacin da da k'anin sa  ya kawo Mata, sai yau  wajeen Shekara D'aya da wata biyar Allah ya nifeta da Bud'ewa nan ta bud'e ta fara karantawa kamar haka:

                                                                                                                                                                                                

                                                                                                                                                                                                *By Queen meemi*👑

                                                                                                                                                                                                *Queenmeemi.WordPress.com*

[3:28pm, 31/01/2017] Miemee: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣22❣

             *JAN 2016*



*®NWA*



_Sadaukarwa ce ga Basher Usman Family's_



**********


Bud'e wasikar tayi tafara karantawa kamar haka:


 _Hansai soyayyarki bazata taba Gushewa a Raina ba, kin zamo tamkar Jinin Jikina, wallahi Birnin da zani babu wata 'yar Birni da zata Rud'eni na manta dake,ina sonki Muyi hkr da Rabamu da akai domin Rabuwar tamu ta zamo Sanadin tafiya na Birni don Sanun Ilmi,San nan nasan ab'angaren ki ina ji A Jikina kema zaki samu Ilmin komai rintsi Ina tare dake.Karki manta dani ina Ji A Jikina ke tawa ce na d'au wan nan Alk'awarin ,San nan Hansai Masoyiyata ina so ki Jajirce kicigaba da neman Ilmi na Addinin Dana Bokon idan Allah ya sake had'amu dake zanyi Alfahari dake,duk wahalar da Gwamma ke baki ki jure da sannu zata Girbi abinda tayi,Hansai ina sonki sosai d'an digon Hawaye tagani adai-dai gun, nan tashafa gun bisssalam Hansai Allah ya sadamu da Alkairin sa I luv u & miss u so much._

 

 

Kuka mai tsuma Zuciya tayi tayi ta sa wasik'ar ahannunta ta duk'un-kune ta maida A kwati, kud'in kuma ta rik'e a Hannu. Iya ta shigo Aa "yata Hansai Meyasa kike kuka?".

Nan ta share Iya na tuno su Inna ne, tace Eyya sai hk'r kowa da yanda Rayuwar sa Allah ya tsara sai hk'r ai nan da watanni zaki gansu  d'an Murmushi tayi tace Gaskiya ne .    



                                                                                      Washegari Hansai taje ta kaiwa Anty kud'in tana zaune ta shiga tace "Yawwa Hansai Jeki min blandin kayan miya" da sauri taje tayi ta dawo ta zauna ta mik'awa Anty kud'in tace "Anty gashi ki aje min agunki tun agidane da aka ban na manta sai yau" tace "ba damuwa sai ki sayi kayan Makeup dasu ko?" Hansai tayi dariya Anty wane kwalliya?

                                                                                       "Tace haba Aidole kinayi gashi Allah yasa ked'in Kyakkyawa ce" tace to "Anty."

                                                                                        kamar ance ta fita taga Sumy zaune kan Kujera ga Kande da Karime duk a durk'ushe Sumy tace "kema zo nan!"

                                                                                         Asanyaye taje ta zauna Sumy ta fara Magana inaso ku sani daga yau babu wacce zata saka kayan Gida sai Uniform, kun gane nan ta zaro su guda Uku Riga da Wando Rigar iya gwiwa tace su zasuna sawa kullum ta kalli Hansai "banso ki maka Hijab kin gane Aiki kika zo Iyayi ba,ko me za kalla Jikin ki! atoh kuje ko wacce tasa ina nan kuzo."

                                                                                          Haka duk suka d'auka suka tafi Shigar su D'aki Hansai tace nikam kayan sun Birgeni Karime tace "tab! yanzu shikenan Mundena saka kayan mu!?

                                                                                           Kande tasa Dariya kide zauna Surutu Cas kayan sukayiwa Hansai kyau gashi sun D'an kamata daga kasa kamar ba ita ba,shape dinta ya fito daram tsakiyan cikin ta ya d'ame ga kirjinta har dan fitowa yayi, dogon wuyanta ya fito ya dace da beautiful face d'in, tsaki tayi "jifa yanda kayan nan sukayi mini? ni kam dama tabarni Nasa Hijab d'ina."

                                                                                            Karime tace "kai Hansai duk yafi miki kyau"Kande tace "eh wallahi" Karime tace "duk gayunsu wallahi kin fisu kyau" Kande tace "eh dande tana rufe Jiki ne."

                                                                                            Nan suka fita Sumy na zaune tana kad'a k'afa suka zo suka tsaya tayi Dariya "ko kufa yanzu kuka dace da 'yan Aiki Musamm ke Hansai kinga Anty ta tsaya miki har Super Holland kike kwancen ta  to Daga yau ta kau, oya kowacce ta tafi nata guri nan suka juya."

                                                                                            Bin Hansai da kallo tayi tab! dama haka yarinyar nan take! dole ta rufe Jiki d'an tsaki tayi ta mike.

                                                                                            

                                                                                            

                                                                                                             *MANGALU* 

                                                                                             'Yan Sanda ne ak'ofar Gidan Malam, Dije da sauri ta shiga ta kaiwa Gwamma tsogwami nan ta shige d'aki ta gark'ame Jiki na rawa Fad'an- Fad'an Delu tazo tace bari na shiga Gidan.

                                                                                             Tashiga tana k'wala Sallama Jummai ta fito Delu tace  ina wan nan Muguwar ta fito wallahi yau ko ta ban kud'i ko atafi da ita."

                                                                                             Daga can d'aki tace "bazan fito ba Wallh" Delu tace "yo ai bafin k'arfin kikaiba nan ta Danna K'ofar nan kwa ta bud'u ta Janyo Gwamma tace "kudi ko tafiya" tace "ki bari Mudi zai yimin aike."

                                                                                              "Ban yarda ba." Gwamma tace "ke bafa tsoronki nake ki ba wallahi bazan ma bayar ba" a fusace Delu ta fita ta Sanarwa 'yan Sandan nan suka Shiga soron Gidan sukace Gwamma ta fito dak'yar ta fito tana yafa Mayafi suka tasa k'eyar ta har waje yara ne dam! a tsaye nan ta tsaya tana huci tace "Delu munsa k'afar wando d'aya dake."

                                                                                               "Tink'is -Tunk'is aka tafi da ita D'uu yara na binta.Jummai kuwa sai tafa Hannu take "oh! su Gwamma an fara tab'ab'arewa." Malam ya shigo Jin Labari da takaici yake tambayar Jummai ta sanar mai yanda akai yace "Al amarin Gwamma Sam ba Allah aciki, ta wulak'anta Rayuwar ta kuma wallahi ba inda zani Sanda sukai niya sa sako ta."

                                                                                                Jummai tace "Allah ya kyauta Malam yace "nikwa yau watan Hansai nawa?" tace "ina Kin Uku Malm" yace "Allah sarki Hansai muna Kewarta" Jummai tace "nima haka."

                                                                                                

                                                                                                 *ABUJA*

                                                                                                  *Bayan wata d'aya*

                                                                                                  Yau ya kama Sunday duk 'yan Matan na Gida suna zaune kowacce da abinda take Zuby ta  kira hansai da yake Anty ta sai Mata wata Aitle shiisa duk wacce ke da aiki kir zata kira ta. Hansai tazo gani Zuby ta Aiketa ta had'o Mata drink ta tashi ta tafi ta d'auko Jitayi an watso Mata Bra Sady ce ke Jin wak'a tace "Jeki wanken" ta tashi ta tafi sai wash take Saboda tunda ta tashi suke sakata Aiki har ta gaji Allah yaso ma Aikin Anty bame yawa bane, dawuri take gamawa.

                                                                                                   Tas taje ta wanke ta shanya k'aryar ta ta tashi har sai Sun gama bushewa San nan ta deb'e sai wajen 2 ta dawo rik'e da su,ta shiga wangamemen d'akin nasu duk Sunyi wanka Sun fece Sumy ta kalleta "ke anjima zaki rakani Shopping" Ruma tace "oh no! ku kam wai mesa kuka takurawa yarinyar  nan  komai ita duk baga su Karime ba."

                                                                                                    Sady tace tab! wad'an nan k'azaman Ji Uniform din su kullum datti sai Dana sa Iya ta sasu suke wankewa kullum , kinga kuwa ita kullum nata agoge shiisa nafi san Aikin ta Ruby data k'urawa Hansai Ido tace "Gata kuwa so beautiful" Zuby tace "LOL" .

                                                                                                    Sumy tace "nikam Anty Ruma Dady na nan? tace "eh mana yana garden" tace "nikam kayan make up D'ina ya k'are da perpums gashi duk nayi searchin new a Goggle" Sady  tace !tab ai kuwa nima hakan."

                                                                                                     Sumy tace "Nifa bansan gasa Sady tace k'afata k'afar ki" Sumy ta "kalli Hansai dake tsuggune ta Sunkwi dakai ke ki fa shirya zaki rik'en kaya". Hansai tace "to Anty Amma da wad'an nan kayan zani ? Dariya suka fasa su duka, Sumy tace "to da dame zaki? meye Amfanin ki ba 'yar Aiki bace ke? dole ki bada Alama da hakan."

                                                                                                      Anty Ruma kam akwai Sauk'in kai tace "no baza ai haka ba, itama fa 'yar Adam ce taje kawai ta saka kaya masu kyau ,ke ba abin kunya bane aagareki ta tafi da uniform na aiki." 

                                                                                                      Sumy tace "kai Anty Ruma!" ta kalli Hansai "oya Jeki wanka kisa kaya me kyau." 

                                                                                                      Hansai tace "to" ta tashi a salub'e ta fita D'an sauri take Ojuku ya tsareta "pls baby Do you love me?  Hansai ta harare shi "ni ka matsa meye ruwa na dakai, ka takuramin"

                                                                                                      Yi hank'uri Baby me kyau" wucewa tayi yabi bayan ta da kallo yana mai wani had'e Ido, cigaba da Goge tiles d'in yayi yana wak'a baby love me ! love me."

                                                                                                      Sumy da suka fito zasuyi part din Dady ta wullawa Ojuku key "pls ka wanken Motata saboda anjima zani Shopping" yace "Okay Maddam" Look ban. Hanaka  cewa Maddam din nan ba?" yace "Sorry Hajiya" tsaki tayi Sady tace "ke komai fad'a" tace "nayi."

                                                                                                        Part din Dady suka Shiga Sunkai tsakiya sukaga Anty tana magama "pls Dady's boys a D'aukarwa Mubarak me Lesson" yace "ba komi Amaryata" Sady tace "Aikin kenan komai boys, Don taga su Mama sun d'aga Mata legs" Da sallama suka shiga Sady da yake yar gaban Goshin sa ce da saury taje kusa dashi ta zauna "Dadyna" yace "Uwata ya dai?"

                                                                                                         Sumy tace "Dady kayan Makeup d'ina ya k'are da Perpums" yace "kai Yaran nan bakwa Rabo da kwalliya Last 2 weeks na Baku fa" Sady ta Marairaice Don Allah Dady yace "oke Don worry" ya tashi ya bud'e kit ya curo bandir ya bawa kowa 20k suka had'a baki "Allah ya K'ara Budi Dady."

                                                                                                          Suka fita nan ya juya  yace "Maman Boys Insha Allahu Next week zai fara zuwa tace "Ngd Dadyn kids"

                                                                                                           K'arfe 5 dai-de Hansai tagama shiryawa tasaka atamph da Mayafinta black da Anty ta bata Sumy ta fito tace "Sady wai ba zaki sayo ba?" Sady tace "ke ni fa dama ina dasu Sumy tace "Amma bakiyi ba shine kikaje kika ragen yawan.samu" dariya tasa D'aukan Jakar ta tayi ta sak'ale a Hannu tasaka after Dress pink Dubai products me adon Blue sai Mayafinta Pink shima me Adon blue ta bazo Gashi gefe tayi linin Mayafin abayar Sumy tayi kyau sosai ga Jakarta blue da flat Shoe blue nan ta fita ta kalli Hansai taga ta zambada Red Jambaki ba Lefi tayi kyau.

                                                                                                           

                                                                                                            Tace "ke zo nan! Hansai taje "oya Goge Jambakin nan na bakin ki, Nasa Jambaki kema kinsa" da sauri ta Goge suka fita. Ojuku sai dad'a k'alk'alar Motar yake ya k'urawa Hansai Ido kamar maye Harara ta buga mai ya washe baki nan ta bud'e baya ta zauna. Sumy tace "ke waye driva ki? fito dawo nan, Mtsww komai aka had'a da Villager saiya ci Kara."  A hankali ta fito ta bud'e Gaban a d'arare ta zauna Lokacin har Maigadi ya bud'e Get,din da Gudu ta ja Motar suka fita.....

                                                                                                            

                                                                                                            *By Queen Meem👑i*

                                                                                                            *Queenmeemi.WordPress.com*

[5:14pm, 01/02/2017] Miemee: . . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣23❣

           *JAN 2017*



*®NWA*



*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_*




**********

 Cikin mintuna suka je Supermarket d'in Parking Motar tayi suka fita Hansai na binta abaya kanta a sama ta shiga  kantin Basket tasa Hansai ta d'auka nan tayi wajen Perfumes ta dunga zab'ar irin Wanda take amfani dasu Hansai sai binta take abayaa tana sakawa a  Basket d'in haka b'angaren kayan Makeup shima ta saya sun gama ta juyo Hansai tai Karo da wani Saurayi ta d'aga Manyan idan ta ta kalleshi "ke wane shashanci ne wace iriyar Yarinya ce bakya kallon Gabanki?"

 

"Kayi hkr don Allah" cewar Hansai Sumy ta juyo "Sorry fa 'yar k'auye ce shiisa" Saurayin ya tab'e baki "no wonder." Hansai kam kamar ta kurma ihu haka suka je gurin Counting  ta biya suka tafi tun data shiga Motar Sumy ke Mata balai' har sukaje wani D'an wajen Shan iccream  sumy ta fita tana waya gani nan fa na shigo" haka ta tsaya tana ta yatsina can sai ga Saurayin ya tawo yaci Swags dama duk Samarin Sumy  Swag ne tafi San irin su,acewarta sune manyan yara, ya tawo yace "my Sumy" tace "my Nazi kaga nan yafi safe" suka sauna kan wasu kujeru yace "wai meya sa Dady naku baya barin aje Gidan ku gurin ku?" tace "Dady karatu yake so muyi kuma ba kowane mutum yakeso mukula ba" Nazi yace well Nikam nasan zan samu guri" tace "sosai my nazi" kurb'ar leman dake gabansa yayi "yanda nake Sanki ai bazan iya barin ki har na 2 days ban ganki ba."


 D'an Murmushi tayi  tace "Allah? yace  "yeah of course" wayar ta ta d'auka ta kira Hansai "to 'yar k'wama kawon bag d'ina" ta kashe Hansai da tai  tsuru- tsuru Amota ta fita D'auke da Jakar Sumyn, tunda ta doshi gun Nazi ke kallonta tayi mai kyau nan Sumy tace "me kake kalla?" Nazi yace "Sorry wan nan fa?" 

 

 A Lokacin Hansai ta mik'a Mata Jakar, harara ta bata "oya tafi can ki zauna kin wani je Mota kin k'wame" ,ta juyo ta kalli Nazi "yar Aiki ce".

  Yace "kai Amma fa tana da kyau Sam bata dace da Aiki ba, wan nan in ta samu wanka za ai Hot Baby." Wani kallo tai mai "shut up nazi, ya agabana kana yaban 'yar Aikina haba"

 "Sorry tawan kin sani ni bana Rufi". Tabbas tasan halin sa ,nan tace "ok Amma karka kuma, ai saika sa ta raina ni."

 

 *NAZI* wani Matashin Saurayi ne mai tashen Money baban sa Alhaji wada shahararren D'an siyaysa ne Wanda ake ji dashi har yamafi baban su Sumy Naira ,Nazir su biyu ne a gurin iyayen su daga Shi sai k'anwar sa D'an gata ne nak'in K'ara wa ga Fafa baya 6 Month da mota ake canja mai wata duk abonkasa 'yan Swags ne akwai Shi  a Kwai San Mata duk wacce yagani sayya yaba, sun had'u da Sumy ne A Uni Abuja yana Lavel 4 ita tana 2 nan suka d'inke suka fara Soyayya Sanin Dady Bai barin su zance yasa suke bi park -park duk Lokacin da suke san ganin Juna ko su had'u a School wan nan kenan.

 

Hansai kuwa duk ta gaji Manyan yara ne kawai ke giftawa sai binsu da kallo take,ta tuno ak'auye yanda batai aure ba akace tayi girma sai gashi abirni yar yarinya ce akan yan matan  birnin,bacci ne ya d'auke ta Jitai an d'aka Mata duka ta mik'e Sumy ce da Nazi tsaye tace "kin share baki kina bacci Useless kawai Hansai taji zafin kalmar don ta San Ma'anarta (dadin karatu kenan) kallo Nazi yabi bayan Hansai dashi yana k'issima abubuwa da dama.


Nan sukai Sallama da Sumy ya shiga Motar sa kiran benz ya fita itama suka shigaa suka tafi sai 6:30 sukaje Lokacin har Dady ya dawo ad'arare Sumy ta shiga gidan, Nik'i Nik'i da kaya Hansai ta bita d'akin su ta Shiga ta aje ta fita.


 Zubewa Sumy tayi a Aininhin d'akin ta tana Murmushi domin tana ganin  ta samowa kanta mafita.

 

Itakam Hansai tun shigarta  Anty ta tsare ta sai yanzu? Hansai tace wallahi munje wajaje ne". Anty tace Allah ya kyauta wallahi bansan janki yawo da suke don sunga kinada juriya."


Wani irin bacci takeji tun karfe 7 na safe take galaulawa nan ta koma side nasu na 'yan aiki,  tayi Alwala tayi salllahr magrb da yake an kira kwanciya tayi sai bacci , kamar daga sama taji Ana tashin ta ta Bud'e Ido Sady ce tsaye akanta tace "ke tashi ki dafan indomie, kamar ta kurma ihu ta tashi taje main kitchen din gidan tana had'awa sai Magagin bacci take yi .


Ji tayi an cakumeta ta kurma ihu ta juya da sauri Ojuku ne ke ta murmushi "my love sorry na baki soro ko" hararar sa tayi "ni ka tafi kaban waje me kake har yanzu a shashen nan kuma ni ka daina tabani saboda ni addinina yayi hani", Allah idan baka fita ba zan maka ihu dogare Hannu yayi ta bud'e baki zatai K'ara da Sauri yayi baya .


Haka ta yanka Attaruhu k'anana da Albasa ta d'ora ruwa tab'are indomie 2 ta zuba magin ciki ta K'ara Rayco daya tasaka curry kad'an da Dan mai ta rufe ta tsaya jiran ta dahu, tunda ta tab'a dafawa Sady indomie taji Dad'i shikenan take Uzzura Mata duk dare sai ta dafa Mata.


 9:30 ta gama taje can part din su Sady ta shiga ta tsugunna duk suna falon suna kallo dayake da dare kowa part d'in mahaifiyar sa yake tafiya da yake d'akunan baccin su anan yake, da rana ne suke da wangamen dakin su a big falo to nan suke haduwa  'yan matan gidan.

 

 Mik'a mata tayi  ta k'arb'a "Weldone" takai Loma har Hansai takai k'ofa Sady tace" ke wai waaya koya miki dafuwar indomie haka"? tace Anty ce ta koyan" Mama ta juyo "lalle kuwa",San nan ta kalli Sady "ke yanzu girkin 'yar Aikin kike ci ke ko, bakya ganin k'azantar da suke?"


Sady tace "Banda Hansai tana da tsafta har so biyu take wanka fa shiisa na ke bata wasu abubuwan tana min",Mama ta kalli "Hansai data tsaya "ko wan nan ma Antyn ce tace kina wanka biyun ?" 

"Eh itace"

 "Lalle jeki kawai" ahankali ta fita

 

 Sady ta kalli Mama tace Mama ya kamata kema kina saka kande tana tsafta kinga ke kika d'auko ta" Mama tace "'Yata ce da zance sai tayi tsafta! nide taimin Aiki wan nan kuma jikinta tunda ba kuwa shashena take ba k'ark'ari taimin moping da wanke -wanke ta fita"

 

 Sady tace "Mama bari naje na hau computer inada Assignment"  tace "ok" ta fita.

 

 

 

 

 *Queen meemi*

 *Queenmeemi.WordPress.com*

 

 

 . . [2:18pm, 03/02/2017] Nene: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣24❣

              *JAN 2017*




®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION




_*Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's*_



 *Wan nan page naki ne ANTY MAIJIDDA MUSA Tnz 4 d care And support*


*************

 Hakan rayuwa tayi ta tafiya akwa na Atashi yau watan Hansai Goma agidan ta dad'a kilewa tayi fes Sam bakace itace Hansan Gwamma ba fatar ta tayi kyau da yake tana sa mai masu kyau wan nan kuwa duk Aikin Anty ne don ta d'auketa takmar kanwa,ga kanta ma ya dada tsawo saboda samun gyara da take kai bakace yar aiki bace ta saba da wahalar da su Sumy ke bata,cikin kankanin lokacin ta iya abubuwa da dama.

 

 

 Yau ma da take zaune a bayan d'akin su tana kuka sakamakon tafiyar su Kande duk anzo D'aukar su Amma ita shiru yau satin su d'aya ke nan ji tayi Anty na kiranta ta mik'e ta fita Anty tace "Hansai yau munyi waya da lami tana tafe gobe sai ki shirya" kamar tayi tsintsuwa tace "ngd" Wayyo Dadi nan ta tafi daki da gudu ta duba akwatin ta taga wayar da tasaiwa baba 'yar dubu uku tana nan tun kud'in da Anty ta bata haka ta aje shi gefe d'aya.

 Wani gefen kuma tana Jimamin tafiya saboda Gwamma. Sha Tara ta Arxiki Anty ta had'a Mata ,da atampha da takalmi dasu shadda.

 

 

  Washegari da sassafe Ashiru ya d'auketa tana kukan missn din Mubrk da khalil Anty dake jadda Mata sati biyu kawai zatayi Hansai tace to Anty nan Motar taja suka dau Hanyar kano tafiya yankin Azaba tun Hansai na kalle -kalle har ta kwanta bacci sai wajen azahar sukaje gidan Mama.

 Mama ta Rungume Hansai tace "Lalle Hansai Kece haka kamar bake ba?" ta sunkwi dakai "kekam Abuja ta karb'eki" nan Ashiru yaci abinci ya koshi yayi sallah San nan ya koma har Mama ta bashi kayan kadi ya kaiwa Anty Rabi ita kam Hansai bayan tayi sallah ta huta sai bacci don ta san sai La asar Lami zata k'araso ilai kuwa sai la asar d'in tazo.

 

 itama ta yaba canjawar Hansai tace "lalle  kinyi kyan gani." Mama tace ice dai zaki dawo da ita don nasan halin ku duk 'yar Aikin da zataa tafi bata dawo wa" Hansai tai caraf ai nikam zan dawo Mama".tace aike kam kin zama tamu sai wajen 4 suka tafi da k'arfe shida dede sukaje suka sauka atasha .

 

 Lami tace hansai ki d'au Jakar mana" Hansai tace "Aa zan rik'e" Lami tai dariya "Lalle birni ke kam ya karbe ki ,da Dane ai ka zaki dora" suna tafe suna hira sai kallon Hansai ake har sukaje k'ofar gidan su. Malam yana Alwala Hansai tayi magana ya d'ago "Aa Hansai Masha Allah" nan suka shiga ita da Lami Jummai na tuk'in tuwo Hansai ta Rungume ta ta baya ta juyo 'Lalla wa zan gani kai lalle mutan Abuja Hansai kin canja' murmushi tayi tace ina Abdullahi Jummai tace yana can waje dai dai lokacin Malam ya shigo Lami ta zaro dubu ashirin tace ga kidin aikin ta ni na dauki kudin lada na nan da sati 2 zan zo na maidata ta yanzu sauri nake ta fita.

 

 Malam yace "Allah abin godia Jummai kalli yanda Hansai ta dawo fes da ita" Jummai tace "wallahi kuwa kamar ba itaba." kudin ya irga yace "wan nan sai a aje maki." Gwamma dake band'caki ta fito da sauri ta fisge kud'in "lalle nayi Mata hanyar Aiki anga kud'i nan ta d'au dubu goma "bashin da ake bina zan kaiwa 'yan sanda" ta soke dubu biyar ta mik'a musu "ga wan nan tace ya isheku" Malam yace "ke kam har yanzu baki saduda ba duk kwanan da kikai a guron 'yan sanda besa kin hankaltaba"  "Malam ka k'yale ni haba Yau wajen wata shida Ana kawo min farauta zuwana gun yan sanda uku duk dan bashi yanzu ga kud'i dole nai wadak'a" da sauri ta shige daki Hansai ta tab'e baki suka shiga daki.

 

 Da saafe ta fiddo taarabar su ta basu har yar Gwamma Dija ta D'auko wayar baba ta bashi yayi murna tace baba nima kaga tawa Anty ta ban inna kuma inna kuma samu zan saya mata."

 

 Gwamma tace lalle hardasu waya tace dole ke ki zauna yanzu Dije ce zata wlh itama ta samon Arzikin bawanda yace Mata komai,haka da yamma taje gidajen da take shiga suka gaisa duk inda taje sai an yaba ta har wajen da suke zama da muntari taje tasha kuma agun san nan ta tafi.taji dad'in zaman domin Gwamma bata kulata da sun hadu sai zagi ita kam Hansai daga gaisauwa bata fita don Jummai tace kar tai abinda zai ja ta dake ta .

 

 

 

   *Abuja*

 

 Acan abuja kuwa tun bayan tafiyar Hansai su Sumy duk wani Abu bassai dama Hansai ke gyara d'akin big falo yanzu kuwa kaca -kaca bra din su nan sun Tara hili sai ta dawo ace warasu ta wanke ga su kande basu dawo ba kullum sai de su fesa wanka asheka uwar makeup atafi schools.

 

 

 B'angaren Anty kuwa kewar Hansai ya dameta ga kullum Mubrk ina Hansai sai de Anty ta lallase shi.

 

 

 Bayan kwana 2 Ruby ke tsaye tana tunani ta dago tace "Ruma agasky idan ku zaki jure nikam bazan iya ba wallahi ba abinda ke burgeni sai aure don bakuga frriend dina last week tayi Aure nikam ko a haliita ina bukatar Aure."

 Ruma ta d'ago ta zare Glass dake fuskar  ta  tace "Ruby kina son bata ran Dady ko? ya fiso sai mun gama degree San nan 'ya'yan manya Amma ke fa Naga Nuradden  ke San ki tabbas kin San Dady ma yafi Baban sa Naira, hakan Shi Aikin sa ba mai tsoka bane" Ruby tace "nifa ba ruwa na da hakan "ki kalla shekarata 24 ai ina bukata" Ruma tace haka Amma ai na girmeki ko?" Ruby tace "nifa dake ba d'aya ba atoh dole zan gwada sa a ta ko Allah ya sa na dace don Nuradden sona yake da aure.

 

 Ruma tace Allah yasa mu dace" Tace Ameen


nan tafita tayi wajen Ummin ta don samun mafita.




*By Queen meemi*


*Queenmeemi.WordPress.com*



.

[2:18pm, 03/02/2017] Nene: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣25❣

          *JAN 2017*




®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION



*_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_*



*ANTY SIS sakon gaisuwa gareki  ,da Masoyan Rabuwa ce Sanadi na Tnz 4 ur love & support*


***********

Shigar Ruby d'akin ta tarar da Umma na waya ta zauna umma ta d'ago "wai ina Sumy ne? Ruby tace "ta tafi Birthday d'in frnd nata" Umma tace "Okey Motata tad'auka ko?"

Ruby tace "eh" tace na hana ta d'aukar mun, kome ta ta take? zata zo ta samen ne." Ruby tayi Jigum Umma tace "meye fa."



Sunkuyar da kai tayi "Umma Nuradeen ne ya damu yana so Magaba ta su shiga cikin maganar mu wai

 da Aure yake Sona."

Umma tace "tab! ke kam kin d'auko Dala ba Gammo kina ganin Ruma Masters take yanzu Amma ke har yanzu ko gama Degree baki ba" tace umma Carry Over nake ta samu fa"! tace 'Allah ya kyuta nikam ba ruwana a zancen sakkowa tayi Mama me zance mai? tace kice ba yanzu zaki Aure ba, tashi tayi ta fita tana Hawaye."



Wayar Nuradden ta d'auka tayi mai waya ya d'auka "My life" tace "Naam" yace "ya Maganar mu" tace "Dady baya gida sai ya dawo anjima Zan Maganar yace ok I'm waiting suka akashe a tare.


Ruf da ciki tayi ta rufe ido har ta fara sleep kamar 10mints Zuby ta shiga tace "sis kizo inji Dady" tashi tayi tace "ya dawo?"


 Tace "Eh Man kede kizo" Suka fita can falon sa Sumy na gefen sa da Sady Sumy suka zauna ya D'ago "wato ku bakwa ji ko?"

 Ya kalli Zuby "ke ran nan na kori wani ko" yanzu Sumy tazo min da Maganar Wanda ke santa to na yarje muku zance Amma sai nayi Screening"

 

Ya Kalli Ruby "ke wake sanki?" tace "Nuradden ne" yace "waye uban sa  anan?" tace ba nan yake ba D'an kano ne Aiki de yake Anan Abuja.


Kallonta yayi yace "ki rabu dashi meyaci meya baki, duk daular Dana Baku in kinje balalle ki samu ba."kuka tasa wlah Dady yana da kirki"



kallon Zuby yayi "yace ke dama na yanke Magana kar yaron nan ya kuma zuwa saboda bama jetuwa da Ubansa, kuma akasa na yake don haka ki Rabu dashi ,sai ke Sumy D'an Alhaji Wada na yarje miki ya dinga zuwa."


ya kalli Sady "kefa uwata?" nan tace "ni Dady Banda kowa" yace "to akula da karatu,  ku tashi ku tafi" sanyaye suka mik'e.


Ruby da Zuby kam kuka suke Zuby ta zube afalo "nikam bazan iya Rabuwa da Fawwz ba, I can do without him."

Sumy tace "Sorry sis kiyi ta Addua" Sady tace "nikam har now banga choice d'ina ba" Ruby tace "duk naku mai sauk'i ne nikam Banda tacewa zanbawa Nuradden hkr kawai.


Sumy ta dau phone dinta tana latso kiran Nazi ta sanar mai ya fara zuwa ko yaushe.



*Mangalu*


kwanci tashi ba wuya a wurin Allah Hansai tayi Sati biyu, yau ta tashi sai wankin tafiya take sai yamma ta gama taje ta siyi kayan tsaraba ta dawo.


 Washegari da safe ta shirya da wuri K'arfe takwas Gwamma ta fito da Dije ta shirya Gwamma tace "ke Hansai fa ba zaki koma ba, wlh Dije ce zata amatsayin ki."

  Jummai tace "wata Sabuwa haba ke kuwa?" Gwamma tace "ke rufen baki bansa dake ba, k'arfe goma Lami tazo ta tarar da husuma Gwamma tace "Lami da Dije zaki koma Hansai ta zauna."

   kuka sosai Hansai keyi domin tasan da biyu Gwamma ta ce hakan sallamar Malam ce ta katse hayagagar Gwamma yace "meyafaru?"



Jummai ta gaya mai yace "Gwamma hawainiyar ki ta kiyayi rama ta, idan ba haka ba wallah zan d'au Mummunan mataki akanki" ya kalli Lami yace "ki,tafi da ita Allah ya kiyaye hanya" Hansai tace "baba zamuna gaisawa ta waya" yace "Yawwa Hansai ai naji dadin wayar na gaisa da Mutane da muke kasuwanci da."

Nan Lami tayi gaba Hansai bi bayan ta.Dije ihu tasa domin k'auyen gasar kai yara aiki ake Malam ya daka Mata tsawa ta shige daki.


Yau kwana Hansai 2 da dawo wa Abuja inda ta hau hidima da su Sumy Su kande ma duk sun dawo sati d'aya da dawowar ta Hansai taje Anty  a d'aki tace "don Allah Anty taimako nakeso da kudin Aikina inaso zan koma Makarnta dashi sai Ana biya da kudin Aikin.

 Dariya Anty tasa tace "ai duk Makarantar nan ta kudi ce ovar yanzu idan nace Alhaji ya sakaki wata jarabar ce Amma mai lesson din Mubarak idan yazo zan mai Magana sai tmyana koya miki har kisamu kiyi waec" Dadi ne ya ishi Hansai tace ngd"

  Anty tace kudin Aikin kuma yana nan da k'arfin jiki ta tashi tana mai godia ga Allah tabbs duk wahalar da su Sumy ke bata tasan zuwan ta ABuja Alkari ne agare ta ko  wani Abu dama da sana dinsa.

 

 

 

 

 *By Queen meemi*

 *Queenmeemi.WordPress.com*

[4:03pm, 11/02/2017] Nene: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣26❣

          *JAN 2017*




_Sadaukarwa Ce Ga Basheer Usman Family's_ 




*_Alhamdlh Masha Allah ,komai yayi Normal Ngd da kulawa Fans ina tare daku akoda yaushe_*




Tunda Hansai ta fara zama Lesson din Uncle Abba ya zamana ta dage dalili Mutumin nada kirki farkon fara zuwanta su Sumy suka hana acewarsu Aiki tazo ba karatu ba saida Anty ta bud'awa idonta toka tace "ai ni na d'auko ta, don haka ba ruwan ku, aiba kullum zatanayi ba weekend ne idan yazo yiwa Mubarkh sai tana yi."


Saida Umma da Mama suka ce su Zuby su k'yale Maganar san nan suka hak'ura wan nan duk don saboda Dan dafe dafen su ne datake musu da aiki dole sai ta gama suke sakata.


 Yau ma da yazo suna zaune akan kujera irin fararen nan mai Dining Roba Jibga Jibgan Littafai ne Wanda yasan 'yan SS1 na Amfani dashi yake koya Mata sai an gama da Mubarkh ya dawo kanta dad'in Shi Hansai tana da ganewa Dan ma Turanci na Mata tsiya tunda karatun k'auye Dana Birni ba d'aya ba, hakan yake koya mata har turancin wajen k'arfe 1 ya gama ya tafi Hansai ta.koma gida da Littafai cike da jin dad'i tabbas Burin ta zai cika .

 

 D'akin su taje su kande nata kuka ta zauna "wai meye ."

 Kande tace "nikam na fara gajiya kullum kamar Jakai yanzu wan nan Sadyn ta Samu Aiki don na kuskure ta maren ta had'a har da Karime."

 

  Hansai tace "kiyi hkr" karime tace 'wai me ake koya miki ne?" tace karatu kema kina zuwa" kande tace "tab kema ba munga ta yanda aka barki kikaje ba, aike kin sa ar me rik'o wllahi karime" tace "ni fa ban taba zuwa Makarnta ba, sai ta Allo itama d'in in naje yawo nake tafiya shiiisa Babata ta kawo ni Aiki wai na samu na kayan d'aki."

  

  Kande tace "ni kuma Matar Babana ne ta kawo ni k'anina kuma Almajiranci aka kaishi."

  

  Hansai tace "nikam kunga Babana shiya dage nayi karatu har nakai Aji uku ,nima ta Sanadiyar Matar Baba nazo nan,"haka dai sukai ta hira har iya ta zubo musu Abinci suna ci.

  

  Ruby ce A captaria itada Nuradden tana Shan Drink haka shima da Alama ziyara ya kawo Mata School d'in,"Ruby plss karki bari a Rabamu, ina Sonki" 

 "Tace Nuraddn Dady na ya Rantse don karkace Yaudara ne shiisa nake gaya ma."

 Shiru yayi yace "hakane Allah ya zab'a mafi Alheeri" tace "Ameen" haka yaza me mata sai a School suke zance da Nura bayan ya tafi ta tashi ta tafi Hostle din wata frnd d'inta sai hira suke.

 

 Frnd din nata mai suna kubra tace ke "Next week bikin fareee" Ruby tace ymm! "Amma nayi Mata murna ,Amma nayi Mamaakin Yarinyar itada bata san Aure."

 

"Kubra tace ke kinsan 'yar Gombe ce tana karatu Annan ta hudu da wani Sugar Dady barin kud'i kawai yake mata, nan da nan ta Amince ke kinga Motar daya sai Mata! da akai Engaged."


 Ruby tace "tab! to kema ai yakamata kiyi" kubra "tace niwa tab! ba Aure a lissafina yanzu kayan takaici."

  Ruby tace "Look nikam ba abinda nakeso inba Shi ba Sbd ina k'waruwa" kubra tace tab! ai seki dage" hakan dai sukai ta hira Ruby ta fito ta shiga Motar ta ta tawo gida.

  

 Tana dawo wa ta tarar da fad'an da Sumy ke idonta yayi ja ga Hansai na kuka dafe da kunci Zuby Sady suna zaune kan kujeru tace "yau kuma Uwar masifa dame aka tashi ?

 

 Zuby kam Dariya tasa Sady tace "wayyo cikina kinsan meya faru wai Nazi Saurayin Sumy yau 2 weeks kenan tun sanda Dady ya bada izinin zuwan sa to idan yazo Hansai ke kai ruwa shine fa kullum in suna Night call sai ya tambayi Hansai,to shine wai d'azu yace anya ba had'asu zai ya Aura da Hansai ba." 

 

 Ta kuma fashewa da Laugh Sumy tace "Sady karki bari na yo kanki bar nazi kayan takaici Dirty Girl din nan zai had'ani da ita don yama Raina ni" ta kalli Hansai "Stupid kawai Munafuka wlh kinyi kad'an inma Asiri kikayi ,me zai dake kucaka to ki saurareni wallahi daga yau kar na kuma ganin kin sa kayan nan."

 

 Ruby ta wulla Ipon d'inta kan kujera ta zauna tana Dariya tace "OMG! wlh wan nan Girl nada matsala bake kika yo musu Uniform ba, Allah ne yayiwa yarinyar me kyau dole taja Ra ayin Nazi me san Mata aini na san Labarin son Matan sa balle yaga Hansai Ak'alla bazatafi 17 ba."

 

 Sumy tace "ya isa Ruby nikam ku barni na Lakad'a Mata na Jaki" Janta can bayan Garden tayi ta sata kamun kunne Hansai kuwa idon nan ya bushe da Hawaye ga Shi ta Hanata Magana sai Addua take Allah ya kawo Anty don sun tafi Osokoro Murnar Haihuwa .

 

 Zuby tace ke kam Sumy ki kyale Yarinyar nan sai nake gani kamar ba Laifinta bane da kin barta da Hijab d'inta da Shi yafi Sauk'i Amma ki ga sai Dan kwali kawai ba mayafi haka fa suke yawo nan nan ina ganin Ojuku na yawan kallon ta."

 

 Sumy tace "kunsan yanda nake san Nazi kuwa? to wallahi zan iya wulak'anta ta ayau zataga canji Dady tace "ke kika jiwo" haka kowacce tayi d'akinta aka bar Sumy na jijjiga .

 

 Anan baya kuwa Hansai ta jike da gumi sai kuka take daga baya ma sai Sumy ta d'auko kujera ta zauna a Garden din ,ga can Kande da Karime kuwa sai zaginta suke suna yi suna kallon baya sai wajen 3 Su Anty suka dawo aykuwa ko zama batai ba Karime taje tana kuka Anty tace "meya faru?"

 

  Tace wlh Anty Sumy ce tun wajen 1 ta sa Hansai kamun kunne a Garden sai kuka take kuma bata co abinci ba bayan ta mata duka Anty ta fita a xuciye....




By 

Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com

Join My Facebook group #QUEEN MEEMI NOVELS .

[4:05pm, 11/02/2017] Nene: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣27❣

             *JAN 2017*




_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_



*******

Bayan Garden d'in Anty taje ta ga Sumy na waya gefe ga filet da Drink  tana sha.

 A k'ufule tace "ke Hansai tashi" da k'yar ta mik'e ko tsayuwar kasawa tayi ta koma ta zauna Anty ta kamata Sumy data mik'e tana kumburo baki.

  Anty tace "Amma ke kam kin cika Muguwa wallahi me tayi miki? Sumy tace "Anty abinda tayi min Babba ne" tace "koma dai meye ai ba kya sa ta haka ba, Ai Mutum ce don haka karki K'ara saka ta wani Aiki naki de na kanki na soke inga yanda zaki."

   Ta kalli Hansai muje." 

   

 Sumy afusace ta bi ta k'ofar baya tayi gun Ummi tana huci ta zauna Ummy tace "nikam ban tab'a ganin Masifaffiya irinki ba." tace Umma "wai ni yau Anty ta nasha zagi akan Hansai har Aibata ni ta Ringai" Ummi ta tashi zaune "me kikai Mata?" nan ta kwashe komai ta gaya mata.

 

  Lallle yanzu tana 'yar aikin? Ruby dake danna waya ta d'ago nikam aganina Sumy ba Hansai ya kamata kiwa ba, Shi Nazi d'in ya kamata saboda shine yace hakan,Alal hakika yarinyar nan bama ta san Shi ba, kuma kom meye kece sila."

  

   Sumy tace "ay don ba ke bace" Umma tace hakane ni ban san neman fad'a da har kinsa zan shiga gun Antyn Amma Naga kece silar komi saiki hkr." wayar ta keta Ring taga kiran Nazi taki d'auka kit ma ta kashe wayar .

   

  B'angaren Anty kuwa! tambayar Hansai tayi  tagaya Mata akan komeye, Anty tace "ita taja ai daga yau kar na kuma ganin kinsa Unform d'in nan Ki koma sa hijab naki Hansai tace to ,sai datayi kwana 2 san nan k'afarta ta saki Tana zaune sai ga wayarta na K'ara da sauri ta d'aga Muryar baba taji nan ta fasa tsalle tace "Baba ya gida? ya inna da Abdullahi? nan duk suka gaisa har da inna taji dad'i sosai .

  

  *****

 yanzu taka tsan tsan take da Sumy wani tsoronta take wajen yamma Anty tace taje neibour din su don kaimata sako taji dad'in fita wata iska ke ratsa ta dai de Lokacin Nazi ke sako Hancin motar sa cak! ya tsaya ya fita yaci Swag yace "ke Hansai ta jiyo Jikinta ya fara b'ari.

 

  Yace "zo nan" ad'arare taje yace kina sona? Dam! taji Gaban ta ya fad'i tsugunnawa tayi "Don Allah kayi hkr ni me Aiki ce idan Anty Sumy taji Duka zata min ka kyale ni don ina da Miji a k'auye."

  

 Magana take sai kallon bakinta yake yana Mamakin wai tace yar kauye don shikam baiga Alama ba, yace "ko bakya Sona ni kam ina son ki".

 

  Tashi tayi ta shiga Makotan da sauri Aranta tana cewa nikam ba Wanda ma nakeso sai Muntari nan ta knocking door , Matar gidan mai  kirki suka gaisa ,Hansai ta dade don bata so ta kuma ganin Nazi sai hira suke da me Aikin Matar sai wajen 6 ta koma tayi Hamdala kanin suna dakin bak'i da Dauri ta shige .

  tun shigar Nazi yake ban hkr har Sumy ta hakura Amma kasan Ransa yana Mutuwar son Hansai

  

  *******

  

  kwanci tashi ba wuya awurin Allah ,Hansai ta samu shekara daya da rabi Agidan Aikinta inda ta fuskanci k'alubale da dama tare da Nasarorin da take ganin ta cimma su,ciki harda k'okarin zana waec d'inta Wanda Uncle Abba yayi Namijin kokarin tare da taimakon Anty Wanda komai A Account din ta ake diba inda tace da na kowa ne dole ta taimakawa Hansai.

  

 Zaune Hansai take sai karatu takeyi saboda Jarabawar da zata zama next week.

  

  B'angaren su Sumy kuwa Ruma ta gama Masters nata yanzu su Zuby ke fama itada Ruby suna level 4 sai de wani hanzari ba gudu ba Sam Ruby yanzu bata maida hankali kan karatu kullum Carry Ova,Zuby kuwa soyayyar Fawwz ke nuk'urk'usar ta domin har yanzu suna tare Sun kasa Rabuwa kullum cikin damuwa So kenan.

  

  Al Amarin Sumy kuwa yanzu Soyayya suke zubawa san ran su ita da Nazi.

  

  Sady Kuwa duk Saurayin dayazo gunta to sai ta kore Shi Musamman idan bashi da naira.

  

  

  11:PM

  Gidan tsit kowa na bacci Hansai ta mik'e tana ihu jin Ana tab'a ta jin karar Hansan yasa aka fita aguje,nan ta kunna fitila taga Karime da Kande na Sharar bacci Iya kam sai Munshari take,a salube ta koma bacci tana kamo addu'oi.

  

  

  

  By

  Queen meemi

  

  Queenmeemi.WordPress.com

  

  Join my facebook Group# QUEEN MEEMI NOVELS

  

  . .

[4:19pm, 13/02/2017] Nene: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣28❣

           *JAN 2017*


NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION(NWA)




*_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_*




*Sakon Gaisuwa ga Queen Meemi Fans Allah ya bar kauna❤*



*************


Tunda ta tashi daga Bacci ta Rasa sukuni bata gayawa kowa ba tai shiru da bakinta.

Suna zaune itada Kande suna hira Lokacin Gidan Tsit kowa ya tafi harkar Gabansa ta ce "nikam Kande Jiya kinji motsin shigowa?

 Kande tace "Aa kinsan ni nauyin Bacci gareni."

 "Hmm kinsan me wallahi jiya atsorace na kwan domin an Shigo d'akinmu naji Anata tab'ani Baccin da ban ba kenan, Amma na rasa gano abun".

  

 Karime ta k'araso ta zauna Kande tace wai kinji Jiya anbud'e D'akin mu?"  Karime tace "wlh naji Likimau nayi ai Jikina na rawa" Dariya suka saka Karime tace "nifa ina Ganin Ojuku ne ya shigo kinsan yana Sonki."

 

 Da sauri Hansai ta d'ago "tome ze kaishi har Lokacin? bayan kinsan ba a Gidan yake kwana ba."

  

Kande tace "nima na yarda shine sede yau musa Ido" Karime tace "haka za ai."


Kuka sosai Zuby keyi tana Rok'an Mama data saka baki kan Maganar ta da Fawwz Mama ta D'ago "Toni mai zance ne? kinsan yace baison Yaron nan  ba, Gaba suke da Uban sa."


 Zuby tace Mama "wai wace irin rashin Jetuwa?"

 

  Mama tace "kisan tun kuna k'anana kinsan dai Dady ya Dad'e yana Siyasa to aLokcin da ya tsaya takarar D'an Majalisar Tarayya to shima Baban Fawwz ya tsaya Shi Dadyn ki a Jam'iyar *PRR* Shi kuma Baban Fawwz yana a Jamiyar *KMK* to Alokacin Dadynku yafi Magoya baya da yawa, to Lokacin da akai Primary Election, a zahiri Dadynku yafi samun K'uria sai akai Magud'i wajen  Tantancewa aka bawa Dadyn Fawwz to tundaga Lokacin suke 'yar tsama to kunji don haka ki cire komai aranki na gaya miki."

  

 

Kuka tasa "Mama Don Allah kimai Magana ko za adace."Mama ita kanta a Ranta tanaso ai Maganar Amma yau zata Gwada.



*Gidan su fawwz*


 Yana zaune a Falon babansa Honourable Muktar da Momynsa agefe sai D'an gyara Hula yake Momy tace "Fawwz kaga Kaine Babba ya kamata kai Aure" Hon yayi Dariya "kana da Matar ne? ya Sosa k'eya "Eh Sunan ta Zubaida suna Maitama Okay waye Dadyn ta?

 Yace "Alhaji Tanko Minister" da sauri ya d'ago kai kaga ka Rasa dawa zaka had'ani suruki sai Wada da yake gaba dani, karka ma soma Domin banson harka dashi ba Party din mu d'aya ba."

 

 K'irjinsa ya bada damm! yace "ayi hakuri nan ya tashi ya fita yana mai Jin d'aci Aransa.

 

 

 ***********

 

 *Bunkure Mangalu* 

 

Gwamma ce ke ta kururwa duk k'auyen Anfito an tsaya gefe ga Mudi k'afa Akarye duk Jikinsa yanka kuka take kurmawa "Wayyo Mudi wallah Magauta ne na sani shiisa akai maka haka.


Jummai hk'r take bata tace "kimin shiru kece dama kikai k'ulli ban yafe ba" Malam da kansa ke sunkuye yace "kimin shiru duk halin daya shiga ke kika Jawo kin d'auka zaman da suke  A Lagos din na Dad'i ne? to wlh ba hannu na aciki duk balain da ya Janyo kece don haka ki ta k domin nansha Ganin aiken kud'in sa Ana kawo miki,abinda zanyi kawai na kaishi Asibiti."


kuka ta saka "Malam dama nasan baka sonmu" da 'ya'yan Jummai ko waccen 'yar tsuntuwar da tuni ka mik'e to wlh bazan yarda ba."


 Shikam Mudi in Banda nishi ba abinda yakeyi da karfi tace "Mudi kayi Magana wai Meya faru? kaine akaima haka? Wayyo ni Gwamma." Da sauri ta shige Daki.

 

 Ganin Dije aciki yasa tace tai Mata  wanke- wanke tace "ni fa Inna Nagaji." Au Bazaki ba? tace "wallahi bazan ba."

 

 D'an Jummai da ke zaune D'an shekara Hudu yace kawo nayi maki?

   Gwamma tsawa ta daka mai "kai yimin shiru Dan Magulmaciya" 

 

 Jummai dataji haushi tace "Atoh da anyiwa Yarinya Tarbiyya me kyau ai da tayi." ta shige d'aki.

 

 Dai-dai Lokacin Malam ya shigo da me Taxi aka d'auki Mudi Ranga -Ranga Gwamma sai kuka tana yarfe zani .Bayan su Malam ta bi  "bansan ki bini balle ki mana haukan." 

 

komawa tayi ta Shige D'aki Jummai kuwa sai Jimami take sai zagaye take tana jiran taji yanda abin ya faru.



*Abuja@8:PM*



Mama ce zaune tana a gaban Dady yana kwasar Dinner ya d'ago "Nasan da Magana a Bakinki tace "sosai kuwa Dady. Agaskiya ya kamata ace an Kauda Rumasa'u  kai har ma Zuby Da Ruby, Saboda kaga fa har Ruma ta gama Masters."


Ya d'ago to wake zuwa gunta? Mama cike da ta kaici "ai yanzu ba Wanda ke Zuwa gunta! domin duk Samarin Datai da wasu ma sunyi Aure har da 'ya'ya ,Alhaji bayan kaike koresu ban mantawa  Akwai Wanda har Marinsa kayi kan bashida kud'i ya Nace yana kuwa ga Ruma Lokacin tana 18 yrs tai Farinjini ,Amma yanzu d'if kekeji ba Mai zuwa Dande mai hkr ce, Amma tanaso wlh yanzu bamai zuwa gunta ta" ta share Hawaye.



Dady yace "naji ni na kore su Amma yanzu zan samo Mata miji Wanda Naga ya dace kuma dama irinsu nake so ba Talakawa ba."

 Tace "sai kuma Zuby Alhaji yarinyar nan ka kyaleta da yaron can tana son sa, hannu ya d'aga Mata karki fara banson zancen so nake ta samu wani Amma Banda Dan Hon Muktar. ita Ruby Yaron Banyarda da ingancin kudin Ubansa ba mai yaci meya ba."

 

 Mama tace "to Allah dai ya kyauta" ta tashi Jiki Asanyayae tanaso tai Biki itama bata tab'aiba duk 'ya'yan k'annenta wasu an musu Aure kuma duk basu kai nata 'ya'yan shekaru ba, itakam ba Ruwanta da sai masu azabebben kud'i ,donma Umma tak'i bata Hadin kaine ta kula itama mai idon cin naira ce, tsaki tayi don kana da kud'i dole sai 'ya'yanka Sun Auri finka a kud'i ni narasa irin wan nan Abu! sai Maganar zuci take har ta koma Side d'inta.

 

 

  *D'ankin su Hansai@10:30 PM*

 

Yau Hansai da su Karime basi bacci ba Sun kunna Fitila sai Raba Ido suke iya ta tashi daga katifar ta tace "ku Yaran nan ki kashen Fitila kunsan bana iya bacci da Fitila" cike da tsoro suka kashe Ganin Goma da Rabi tayi .


Can wajen shad'aya dai de duk su Hansai an Lula Duninyar bacci nan sukaji Ana Lalubar su Kande ta juya ALamar Gyara kwanciya Saboda Nauyin.baccin ta.

 Hansai kuwa jin an Janye Tigar ta ta tashi da saka k'ara nan duk su Karime ma suka mik'e yau basuji fitar ba, sai kuka iya ta tashi kai "Meye?" nan suka k'ank'ame Juna ,tashi tayi ta kunna Fitila duk sanyin Fankar dake kad'awa sai Gumi suke tace "meye?"

 

 Hansai tace "wlh kullum sai Mnuji Ana Lalubar mu a Jikinmu yauma Munji" iya tace "tohhh kode Mutam B'oye ne? nan ta zauna kuyi hkr da kunji Motsi ku hau cewa *(Innahu Min Sulaimanu wa Innahu Bisimillahr Rahman Rahemm)* suka ce "toh iya"

 "Karime tace kuma fa mun Rufe k'ofar" iya tace "Duk Al amarin Aljanu ne" tsuru suka kumai Hansai na kamo Addua suka kwanta.

 

  Nima Meemi na aje Biro zuwa Safiya.

  

  

  BY

  Queen Meemi

  Queenmeemi.WordPress.com

  

  . .

[4:04pm, 14/02/2017] Nene: .

⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣29❣

              *JAN 2017*




®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


.

**********

Misalin karfe Goma na safe Motar Hajia Babar Alhaji ta kunno kai a harabar Gidan. Maigadi ya bud'e driver ya faka ya budewa Hajiya ta fito.


 Mubarkh ne yafara ganin ta da yake yau weekend suna Gida ya Rungume ta yayi yana oyoyo Grandmother tace "jairin yaro ni cikani Mak'alk'aleta yayi suka shiga falon su Sady sukai ta murnar ganinta akwatinta driver ya shigo Mata dashi ta zauna sai hira suke dukkan su sai  gaida ita suke .

 

 Ta kalli Ruma "oh Rumasau har yanzu Bazaki Aure ba? to wlh wata daya zan Agidan nan dole asan abinyi."

  Sun san halinta da fada nan aka kaita dakin da ta saba sauka. Wajen 12 Dady ya shigo cike da jin Dadi Hajia ta farai mai fad'an barin yara ba Aure yace ai Hajia basa kawo wanda suka dace" tace "kai rufen baki idan aka biya ta taka bazasi ba don haka ni nasan abinda zanyi."

  

  Yau kwanan Hajiya kamar karfe 8 na Dare Dady ya kira Ruma ga Mama da Hajia agefe yace "wato dama akwai Wanda zai fara kuwa gunki Alhaji musa" hajiya tace "ko kaifa" mama kam sunkwi dakai tayi dama tasan k'arshen zencen a had'a ta da aboki, nan ya sallamesu ."

  

  Ruma kam ba yabo ba falllasa don tana da hkr ga Biyayya Hajia tace "to Ruby da Zuby fa? Alhaji ya sunkwi dakai. Hajiya "ba su Kara sa Makarantar ba sai sunyi Masters tab'e baki tayi "ka d'au Al adar Bature ka d'orawa kanka yara na kwad'uwa kana Ganin Ruby kasan Aure take so Allah ya kyauta." Yace "Hajiyaki hkr "ta mike ta fita.

  

  

  *Bayan kwana biyu* 

  

  10pm Hansai Sun gama shirin kwanciya don kwana 2 Sun saki Jiki ba'a tab'a su,duk Sun hangame baki sai sharar bacci suke. Hansai taji an Rungumeta an matse nan tafasa ihu  da sauri su Kande suka mik'e Suma suna ihun, iya ta mik'e ta kunna Fitila dafe kirji sukai don ganin  wadda ke tsugunne ihun su karimen ne ya taso 'yan Gidan har Hajia sukayo paty din  masu aikin cirko -cirko sukai ga Hansai na kuka.

  

 Umma tace "meya faru? ke kuma Ruby me kike a dakin nan? sunkwi dakai tayi iya dake tafa Hannu  tace "Abu dama ba a fuska yake ba.".  Hajia tace "kai kuyi baya ni" nan Hansai ta karanto tun Lokacin da ake Lalubar su har yau, salati Hajiya tayi "abinda nake gudu kenan" Umma da ta fara Hawaye "Ruby d'abiar da kika koyo ko? duka takai Mata Zuby tace "kiyi hkr" kuka Ruby keyi Anty taja Hannun Hansai tace suje side dinta .

 

 Hajia kuwa in banda fad'a ba abinda take Gidan kamar rana Umma kuwa kukaa take tayi a daki tunda ta koma. Mama kuwa dama bacci take.

 

  Ruma tace "Haba Ruby ban tab'a sanin kina aikata haka ba, da hankalin ki haramun" Zuby tace "haba Ruby mesa haka? Sumy da Sady dama basu tashi ba Ruma tace "yanzu don Allah dabiar da wasu Matan ke fama da ita har tazo inda muke?

  

   Ruby dake ta kuka "ba halina bane ba wallahi kubrace sila kunsan ni Allah ya Sani a Jerin masu san Aure to ina wahala gashi Dady yace Wanda na kawo bai masa ba, nikam ina azabtuwa Ranar nan a School Muna hira da Kubra taga idona yayi ja sai nake tambayar ta idan tana jin shaaawa ya take sai tayi dariya tace "ke yakike?

    Nace Mata yakwa zanyi hkr zanyi ,sai ta ce "nikam ina da Hanya" nan Nace "ko azumi kike? dariya tasa "haba ba wan nan ba".

    

    

  Nan ta tashi ta d'auko wayarta ta bud'en vedio na 'yan les hankalina ya tashi Nace "yanzu ke kubra wan nan fa Allah ya tsinewa masu yi" Dariya tayi Ai akwai istigfari nikam nace baki san ranar mutuwa ba nide baruwa na."

  

 Tace min to zauna nan tashi nayi na tawo gida kwana 2 mukai bamu hadu ba sai Ana uku naje Hostel din su ina shiga dakin su Naga kubra na kissn din wata yarinya ni nasan kubra 'yar Suniya ce akwaita akwai barkatai din k'awaye shiisa suka tsundumata. zan juya ta kamo ni ta hau kissn d'ina shedan ne yarinjayen tun banso har na biye mata tundaga Tanar muke yi da ita to tunda mukai hutu kuma sai nake azabtuwa ba da wanda zan.Shine nake shiga dakin su Hansai musammn Hansai din."

 

  Salati Hajiya tasa Sam basu san tadawo falon ba kuka sosai Ruby keyi Zuby tace wa Ruma "nikam dama Sam bansan k'awancen Ruby da kubra domin an gayan Halayenta kawai don nasan kona gaya wa Ruby bazata sauraren ba."

  

 Ruma tace Amma kuwa Ruby wan nan abun bamai kyau bane yanzu kinfiso Allah yayi ta tsine miki ?" ni yanzu meye banaji sai de nai ta azumi na karki Kara barin shedan ya rinjayeki.

 

 "Nayi Dana sani Wanda nayi ma zanta istigfari don Allah ki tayani da Addua ."

 

 Hajia tace "yawwa Allah dai ya karemu don abin yayi yawa a Al ummar nan, kuma duk don anbar koyar war mazon Allah  S.A.W ne sai kaga Yarinya k'arama tana Irin harkar nan."

 

  "Allah ya karemu" inji Zuby (to gareku iyaye Mata ku dinga bibiyar irin kawayen da 'ya'yan ku keyi ki sa ido a Al amuransu ,san nan kusan abinda suke muradi) Allah ya karemu da karewar sa. .

  

  

  

  *BY*

  *Queen meemi*

  *Queenmeemi.WordPress.com*

[4:49pm, 14/02/2017] Nene: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣30❣

             *JAN 2017*




_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usaman Family's_





®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION




*********


Washegari kuwa Hajiya rai ab'ace ta fito Ruby kuwa sai Fafautukar Yafiyar Umma take har gun Anty taje ta bada hkr kan abinda taiwa Hansai din.

 Hansai tace ta yafe .Umma Sam taki Kula Ruby

 

  Balli Hajiya ta tashi dashi Tai b'angaren Dady tun da yaga Ranta abace ya sha Jinin Jikinsa tace "Tanko karka bari na saukar da fushi na akanka!" nan tace "wallahi idan baka Aurar da Ruma Ruby da Zuby ba zan Mummmunan Sab'a maka kazo Babban falo na side din Matanka na tarasu can suna jira."

  

  Juyawa tayi Dady ya bita Umma Mama Anty ,Ruma Zuby Sady Ruby Sumy kowa tayi tsit tana zama ta k'wala kiran Hansai  ta tawo Jikinta na rawa tace kazauna aGidanka Ana ta'asa baka sani ba, to ka Jibge yara k'aramar su itace yar shekara 20 suci me kyau susha me kyau Jiki da jini dole suji b'ukata haba"

 Takalli Hansai "kalli yarinyar nan Amana ce de aka kawo koda Aikin take 'yarka Ruby ke Bibiyar su cikin dare saboda tsabar sha'awar dake ranta to kayi masu Aure ."

 

 Dafe kai Dady yayi Anty tace hansai ta koma ciki wani kallo yayiwa Ruby batai Aune ba taji saukar duka atsawace "irin tarbiyar da na baki kenan ? Mai sa bakwa koyo da Ruma ne?

  kuka take sosai tana bada hkr Hajia tace "ba wan nan ba yanzu nakeso ka tsaida Ranar da zakai musu Aure" yace Hajia Ruma dama ma had'ata da Alhji musa ita kuma Ruby akwai wani Manager Nnpc sai Zuby D'an Gidan sanata kuma nan da wata 2 ."

  

  Hajiya tace "dayafi maka"  ba Wanda yafi mama Jin dad'i Hajiya tace suma Sumy da Sady don kar abin yayi yawa ne da har su" haka suka watse kowa yayi side nasa.

  

  Da k'yar da sid'n goshi Umma da Dady suka yafewa Ruby suka haramta Mata kawance da kubra,istigfari take tayi.

  

  Bayan Sati biyu yau Hansai ke final Exams na Waec tun tana Rubutuwa take kuka saboda murna suna fitowa ta bugawa Baba da murna ta sanar dashi yace "burina ya cika Hansai Allah ya taimaka sai kuma Aure ko" kunya taji batace komai ba suka gaisa da Inna da Dan Jummai.

  

   Driver dake d'auko ta ya kaita Sun sha kwana Round about da zai kaisu Hanyar Maitama taga nazi dai- dai inda take sukwi dakai tayi Sun fara tafiya Nazi yasha Gabansu Ashe ya gansu da yake yasan driver din nan ya zaro 2k ya bashi ya bud'e side da Hansai take "ke Baby kince bakya sona ko? to kisa aranki se kin soni kuma sai na Aureki ba Sumy kike tsoroba karki damu."

   

  D'agowa tayi "kayi hkr ni fa inada miji agarinmu" dukan gaban Motar yayi "shut up kin maidani sakarai, kin kwa san yanda matan Abuja ke sona kuwa? su sa suke ma Gig Girls."

  

   Tace "ni ka k'yaleni wlh bana sonka" Dariya yayi yace "zan baki Mamaki ne ya shige motar sa yaja. itama driver yaja itakam ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Mangalu Sam tun lokacin abinda ya faru  taji gidan yafita a ranta. 

   

   

   *Mangalu*

   

   Baba ne a tsaye gefen dakin sa ga Gwamma na huci yace "dama duk abinda kaga wani D'an nayi wasu iyayen ne basi masu kyakkyawar tarbiya ba Ashe tun tafiyar Mudi Lagos suke sata shida Lawandi daya ke akwai Wanda suke kaiwa shine shi Mudi ya ce ya dai na kai musu fad'a ya kaure tsakanin su suka yayyen ke Shi kuma ak'ark'ashin Gada suke kwana a ikkon, Shi Lawandi ne bayan abin ya faru ya gudo dashi shine bayan Sun zo kano dama akwai yaransu anan suka kuma yimai duka suka Jimai Rauni shine kika Ganshi haka."

   

   

Dama tun tafiyarshi Jikina bai Aminta ba Amma Gwamma kika Nace ai ga irinta nan."


 Jummai tayi Jimami tace "Allah ya kiyaye Gaba." Gwamma kuwa duk bata yardaba acewarta da sa hannun jummai.

 

 Malam yace "dole fa Dije ta Dena tallan nan ta na zuwa Makaranta yanzu Jbi Hansai jiya taimin waya tayi Jarabawar gama Secondary."

  Gwamma tace "ai dama ba san su kake ba! yace meye banyi ba ran nan Dije har kusan zagin Maalam na Allon su tayi, Allah yagani na basu Tarbiya kin bata,wlh Gwamma kawai kinci darajar wadan nan yaran ne Amma da tuni na sallameki."

  

  Hakan Gwamma take jinyar Mudi duk ta kare ga Masifar bashin dake kanta kullm sai anzo an fada akan hakan ga ciwon hannun da take yi duk tayi wujiga- wujiga .



By

*queen Meemi*

*Queenmeemi.WordPress.com*



. . 


. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣31❣

            *JAN 2017*



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_



®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION




 *_'YAN GROUP D'IN QASAITATTUN MATA ADAD'E ANAYI SAI GASKIYA. GODIYAR NAKU NE ALLAH YABAR ZUMUCI_*❤


***********



Tunda Dady ya Yanke Hukunci Zuby ta shiga Matsala saboda tsagwaran san datakewa Fawwz kullum suna Manne awaya abinda ya dada sadda da Rashin gamsuwar ta ga Mijin Da aka bata sabili da zuwan da yayi Sam sai taga kamar batai mai ba yana basarwa had'e da nuna isa.



 Agabanta yayi waya da Budurwar sa wacce yakeso bai wani nuna naam da ita Zuby ba La akari da tai watakil shima dole akai mai tundaga nan Jikinta yayi sanyi kullum kuka inda taje ta Samu Hajiya kan Maganar tace sai de tayi hkr.

 

 

 Bangaren Ruby kuwa ba yabo ba falllasa sun dai-daita kansu Mutumin nada 'ya'ya biyu ba wani Babba ,ne sosai da Alama yayi Mata ,itama tayi mai tunda yaganta d'agwas- d'agwa kaji abin Manya  k'warya tabi k'warya .

 

 

 Itakam Ruma nata Suga Dady ne Babba ne yana da manyan yara Baban d'an sa ya Girme mata,itama tayi Naaam don Biyayya inda Shi kuma gani yake ya samu dami akala sai b'arin Naira yake wan nan kenan.

 

 Shirye- Shirye ake inda Manya aka saka Ranar 22 ga watan March 2017 inda shine d'aurin Auren.

 

 

 Zuby sai kuka take tana zaune ta D'ora kan ta akan cinyar Mama tace "na shiga uku Mama nifa wulak'anci yake min da Alama ban masa ba, kuma nima bai mun ba ,ki taimakeni."

 

  Mama tace "kiyi Biyayya ki hkr" ba yanda ta iya ko waya ya bugo Mata sai de yayi tsaki yace ykk ba yanda ta iya tace Lafiya ahakan har aka suke waya.

  

  Yauda suke zaune anata tsara Bikin ita kam Zuby kanta ke ciwo Ga Soyayyar Fawwz dake nuk'urk'usar ta kullum damuwa Sede su had'u dashi a School.

  

  Zaune take Adaki taci kuka, bakin ciki ne yayi Mata yawa ta fita wajen Garden tana kuka kiran wayarta ne ya motsa ta dauka daga can Dan Sanata yayi tsaki "idan bazaki Magana ba zan kashee."

  Haushi ya isheta "ka kashe mana Waya damu da kai ,duk abinda kake tak'ama dashi nima hakan" yace "bana Sonki don haka ki Sanar da Parents naki" kit ya kashe.

  

  Tunani ta fara Lokacin da wani kb ke sonta da sukaje Jigawa k'ark'ari ta Dinga cewa bata Sonsa har kuka yayi agabanta ,ta Buda kasa a idonta tace bata Sonsa face to face, sai yanzu taji Ciwon abin ashe haka kb yaji? duk da ita tasan bata san Dan Sanata Amma taji d'acin kalmar na Bai Sonta.hmm Abinda kai Shi za ama.

  

 Komawa Gida tayi tace Hansai ta dafa Mata kunun Gyada saboda bata iya cin Abincin.

 

 

 *Bayan Sati 2*

 

  Zuby ciwon so ya kwantar da ita itace har Asibiti nan hankalin Mama da Dady ya tashi kai kowa ma na Gidan, direct bayan treatment dinta da Doctor yayi ya kira Dady inda yace "ranka ya Dade 'yarka hawan Jini ke neman kama ta saboda damuwa da yawan tunani ya kamata ta samawa kanta salama."

  Dady yace "okay ba matsala" yau kwanan ta 3 a Hospital Su Dady shida Mama na zaune Dady "yace yanzu Zuby kan na Rabaku da Fawwz shine Sanadin Sa damuwarki har ta ke nema ki jawa kanki ciwo? 

  

  Mama tace "Aa yarinyar nan fa D'an D'anata baya Santa koni wani Zuwa da yayi na zo zan fita naji yana gargaya Mata Magana kullum kuma sai tace min ga abinda yace Mata to ga Wanda takeso an Rabasu haka kuma Shi Wanda ake son had'asun yana yimata hakan Dole damuwa tai Mata yawa."

  

  

   Shiru Dady yayi "yace ba Matsala zami Magana da Sanata d'in kan Maganar .

   

   

   Satin Zuby D'aya aka sallamota duk ta fige Dady kuwa sunyi Magana da Sanata ya sanar mai abinda yake faruwa Sanata yace "ay 'ya'yan zamani sai ahankali, yanzu tunda abin yazo da hakan mu Janye had'in kawai, Allah ya had'a kowa da Raban sa, Amma wani hanzari ba gudu ba Minister ya kamata ku dai-dai da Baban Fawwz domin koba komai Gaba ba kyau kodan ka ceci Rayuwar 'yarka ,Amma ni da kaina zanje har can wajen nasa insha Allahu." Dak'yar Dady ya hkr.

    

    

    

    BAYAN Sati D'aya Da k'yar da sid'in Goshi Baban fawwz ya sakko duk da dama Dady ke Gabar dashi ,ba yanda zai yi haka ya hkr yace Ayi daman shima Fawwz din duk ya rikicemai wan.nan shine Silar shiryawarsu nan akai maganar Auren aka Maida kan Fawwz Nan shirin ya kuma kankama.

    

   Zuby ba Wanda yakaita jin Dad'i Auren Masoyi akwai dad'i su Dady an Rikice sai barin Naira ake komai daga waje ya wayar ai order Su ,ya'ya sun Samu irin Mazan da yake so.

   

    Sumy anci K'uzun Bikin nan, Mama kuwa Mutanenta kowa Nason zuwan sa haka Umma to Bikin 'ya'ya Uku wasa ne! hansai ba abarsu abaya ba wajen son Zuwan Bikin Wanda Jikinta ke bata tabbas wani Burinta zai cika agun Wanda yayi dai-dai da Saura Wata d'aya cir.

    Bari na tsagaita Anan .

    

    

    By

    Queen meemi

    Queenmeemi.wordpress.com

    

    

    . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣32❣

         *JAN 2017*




®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION_



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


***********

Gida kowa shirin Biki yake kai hatta su Hansai ba abarsu abaya ba an musu kaya da yawa kowa ne event da za agabatar suma an musu nasu kalar anko da su head din su duk iri d'aya .


ABangaren  su Sumy Da Dady kuwa ba a cewa komai domin kaya na gani na fada suka dinka  duk na event .


Amare kuwa ba a cewa komai. Lokaci na tafiya Bikin na dada K'ara sowa Ankawo Lefen kowacce aciki  set  24 tamkar had'in baki kaya turmus kamar abude kanti .


D'aki d'aya aka ware musu nan aka d'auko 'yar Maiduguri tana Getta su masha Allah kowacce sai kyau suke ,yau da akewa Zuby Sady ta shiga Tace "Anty Ruma ya  Za'a ai  preparation na frnds event d'inku sa frnds naku?"


 Zuby tace "no wan nan ai akwai masu yi ki bari kawai" Sumy ta shigo "wow gaskiya dole ai mini nima don na Rikita Nazi." dariya Ruma tasa "tab! nikam keda nazin nan kuna ban Dariya."

 

  Sady ta tashi tana waya tafita don karbo dinkin ta hatta gidan sai da aka getta su duk an canja wasu kayan yau ta kama saura sati d'aya Bikin Hajiya ta duro da sauran Dangin Dady ,haka Dangin Maama da Umma suma suka duro. Anty kuwa k'annen ta ne zasu zo Amma sai anfara Event.

 Nan fa Dida ya kacame Dangi kota ina Dady sai barin Naira yake tunma ba A faraa Bikin ba ,ga Gift da yake karb'a gun Abokanan Siyasan sa.

 

 

 Shi kanshi katin Rabo kala -kala zaka ganshi Amare kuwa ko Giftawa sukai sai kaji kamshi kai gashin kansu ma ba abarsa ba ya ba wan nan kenan.

 

 Ranar Talata shine Ranar fara Biki inda za ayi Dinner da dare wajen k'arfe 7 dai- dai aka fara talle Amare cikin wata me makeup ce tazo ta yimasu kwalliya me kyau kamar dawisai haka suka fito A tsadaddun Amare, kowacce taci latest gwan inda wani shegen matrial ne me d'aukan ido da less ajiki abu na manya idonka Shi zai tantance maka yawan kudin sa, Golden ne da red akai adon sa kuma dukkan su iri d'aya suka saka, sai de Head d'in Ruma red ne ,nasu Zuby da Ruby Golden.

 

 

  Angwayen ma haka suka saka D'anyar Shadda Golden ,Ana gamawa aka fara kwasar su Frnds Na Amare ,Su Sumy da Sady  kuwa Su Suka kwashi nasu frnds d'in a motocin su, Shigar nasu yayi kyau kamar  Ka sace su ka gudu sun Balain kyau sai iyayi suke kowacce da  hadaddun frnds nata.

  

  

 Hango Hansai nayi ita dasu Kande sun kafa head masha Allah sunyi kyau musammn Hansai kyanta ya fito kayan sun karbi jikinta hakan aka dunga daukansu Ana kaisu tafkeken hall din da za a Gabatar haduwar gun da fadar sa Sayya b'atan Lokaci.

 

  Cool Music ke tashi ga k'amshi ma na tashi nan MC ya fara Aikin sa,ko ina ka kalla wal -wal wan nan na wane wan can haka aka ci aka sha aka taka rawa aka gama aka Raba Atampah Super Holland da Calender dake manne Pictures d'in Amare.

  

  

  Washegari Ranar Laraba shine Mothers Day nan fa Su Mama karfe 3 Aka fara inda Mama da Umma da Anty sukayi Ankon kaya iri d'aya me makeup ta yi masu duk sunyi kyau sunkafa head Sai tarbar Manyan mata suk.

  

  Amare kuwa shigar wani kwantaccen Less sukai mai Manyan flowers da Stone Pink ne da ratsin Green inda Ka nad'a musuu head Green me adon pink  suka saka wani a kafad'ar su ,Buba ce da zani sunsa wani hil Shoes Green sun Balain kyau Lokacin da suka fito ai nan da nan Masu vedios da Masu Photo suka fara Aikin su, Flower Girls suka? rakasu wajen zama wajen ya k'ayatu Su Sady ma sunyi kyau Sai tar bar frnds suke.

  

  

 Mawak'in Nan Audu Gwanja ke watso wakar sa yauma Hansai sunyi kyau kamar ba 'yan Aiki ba.

 

  Wajen 4 Pm Wata Sumammiyar Mota ta faka a harabar hall d'in.

 Wata Had'add'iyar Matashiyar Budurwa ce ta fito bayan ta kashe Motar ta kulle akalla zatai 21 yrs bugaggiyar wayar ta ta fiddo a Jakar  me kyau,tayi shigar wani material Ash tayi balain kyau, dole ka kalleta ka Kara gani nan ta danna kiran Sady tace tana harabar Hall ta fitoo Su shiga.

 

  

  Kamar 3mint saiga Sady ta fito duk sokeken shoe da ke k'afarta besa ta tawo aguje ba inda suka Rungume Juna da Budurwar "wow Suhaima kin ganki kuwa!" Suhaima tace "ke ni k'yaleni Ina Anty? Sady tace "ke Anty banganta ba tana cikin mutane , ban d'auka zaki zo Mana ba Lokacin da na fada miki ai kuna Landonn ,yaushe kuka dawo daga Landon din? Suhaima tace "ke ni kyaleno muje kawai."

  

  Karo Sukayi da Hansai nan Jakar Suhaima ta fad'I ,Head d'in Hansai ya fad'i Sady ta wanka Mata Mari "bakida hankali ne bakya ganin ina tare da  bak'uwa?

  Hansai tace "kiyi hkr banganku ba."Dallah Matsa Fool Gal kawai,ki bata hkr kona kuma Mazge ki Saida Gaban Hansai ya Fad'i tace "kiyi hkr" tare da share Hawaye Suhaima da taji hansai ta birgeta kuma ta bata tausayi, tace  "bakomi."

  

  

   Da sauri Hansai tayi gaba Sady taja Hannun Suhaima sukayi Gaba.Biki yayi Biki Gwanja sai samun naira yake ya rikice sai watsowa Amare wak'a yake yan Mata kuwa sai cashewa suke k'arfe  bakwai dai de aka gama.

   

   Sady ta rako Suhaima nan sukai sallama da Sady , "Suhaima tace  banga frnds namu na Secondry ba! ,Sady tace "nakai musu inaga ko sai na gobe" suhaima tace "okay nikam ina yarinyar dazu? Sady tace Wan nan Dirty Gal din 'yar Aikin Gidan mu ce fa!

  

 Suhaima tace "yarinyar she's so beautiful  kawai naji ina sonta", Sady tace "ke rabani da wan nan ai kema me kyan ce ,Zaki zo goben?"

 

  Tace "eh kinsan fa Gidanmu duk suna Landon nima Hutu Nazo Saboda na samu Hutun School nima Ina Gwarinfa Gidan Kanwar Mami  Aikinga kuwa dole nazo,yanzu ma inason zuwa Bakery ne kicewa Anty ina gaisheta Gobe zamu had'u,nan sukai sallama ta tafi.

  

  

  

  By

  Queen meemi

  *Queenmeemi.wordpress.com* .

  

  

  . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣33❣                                                               .         *FEB,2017*



®NAGANTA WRITERS ASSOCIASION(NWA)



_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's_



_Sak'on gaisuwarki ya iso gareni *MAMAN SAFYAN*nagode da kauna da kuma bibiyar book dina ,da duk masoya masu turon da sako NGD.❤_


*********


 Washegari Alhamis shine ranar kamu inda wajen k'arfe Hud'u Atafkeken filin Gidan su akai Decoration na Gargajiya su kwarya ,tum-tum,su Ludaya ,Fai-fai da sauran kayan Gargajiyar yayi kyau don masu tsara irin gun aka d'auko ga Masu kid'an k'warya ne da yan Gad'ar su aka dauko nan suka zo, yau duk shigar Gargajiya sukayi inda Amare Suka sa Super Sharaton Babbar Aka d'aura musu Gwaggwaro(head)da Atampar rigar akai Buba suka dora zanin akan Rigar sunsha Makeup sunyi kyau kamar ka D'auke ka gudu Amma yau kowacce da kalar tata Sai d'aukansu Vedio ake idan DJ ya kada sai mai kid'an k'warya tabuga.

 

 Su Sady Kamar kai ya tsinke ko ina ka kalla sai walwali yake Ga yan Gada sai yi suke su Mama sai liki suke wa Hajia dake tsakiyar fili da Sauran Dattijai sai rawa suke , ko ina wadace da kayan motsa baki kowanne tebur.

 

 Dai de an fara Kamu Ana ta zuba Uban guda wayar Sumy ta buga nan ta d'auka Nazi ne yace yana kofarar Get ta fito zai bata sak'o,tafita sai yauk'i take kugun nan yasha Murjani ,tana zuwa ta tsaya "my Nazi How far?" yace "fine dear ya Biki?" tace "Alhmdlh."

 

 Nan ya mik'o Mata Gift Ga "wan nan ki bawa Sisters namu Gudunmawa, Dad'i taji tace 'oh! dear Sun Gode" yace "they diserve more" Murmushi tayi  "Jirani na dawo" Juyawa tayi tana Mirgina Ukwu binta yayi da Ido ,kamar ance ya Juya Hansai ta fito daga Mak'ota da wani Makeken flaks akai da sauri ya fito zuciyar sa kamar ta fad'o wani irin Bugawa datayi tayi fat! fat!, "Hansai" taji ankirata cak! ta tsaya juyawa tayi Ya kafa  Hula yayi shigar Abuja Boys ,yace "ke ya Biki?" Jiki na rawa  tace "Lafiya"

 

  Dariya yayi yace "ke bakya sona ko? dara daran idanuwanta ta d'ago ta zuba mai "I can't love you"

  

 Shafa gemu yayi "Lol Yarinya kinfara Jin Speak ashe ,Harara ta watsa mai ta tafi ,ya rik'o maya finta, dai de Lokacin Sumy Ta fito rik'e da flaks da kayan take Away.

 

  "Tab jar Ubban can!" tsawa ta dakawa Hansai "me kike anan? Jiki na rawa tace bkmi Anty" harara ta kaiwa Nazi yace "Sorry Princess tambayarta nake."

   Mari ta kaiwa Hansai har da bugu ta dumata Dundu abaya, Durk'ushewa tayi tasa fasa kuka Nazi ya had'e rai "wait Sumy ki daina dukanta."

    idonta yayi ja saboda kishi tace "ya zaka zo kana nuna Mata so bayan kasan banso wallahi hansai sekin ganekuren ki, in banda son matanka me zakai da hansai ,Ai se Nuhu maigadi, ki sani wild duk randa Na kuma ganin ki dashi sai kin koma kauyen ku."

    

    Wani kallon masifa Tayiwa Nazi karma kazo kana ban hkr domin bazan Saurareka ba.A fusace Nazi ya shige Mota da Gudu taje mai take  away a gaban motar afusace ya ja nan ta dawo kan Hansai "tashi banza ko yaushe akanki nake samun matsala da Nazi rankwashin ta tayi mai zaiyi dake adauri kashi ko abata Igiya."

    

     Motar Suhaima ce ta Danno kai ta yau ba irin ta jiya bace motar hon tayi ganin Gidan cike ba Space yasa ta Dan matsa gaban Gidan tai Parking Motar ta fito Yauma tayi kyau kana ganin ta kasan hutu ya ratsa yau kuma shigaright Purple tayi, tayi Masifar kyau. 

     

    Sumy ce ta ganota "Oyoyo Sis Suhaima Welcm" idanuwan Suhaima ne suka sauka kan Hansai tayi Murmushi "meya faru yau kuma?" Sumy tace "Rabani da wan nan banzar 'yar Aikin tunda Saurayina ya k'yalla ido ya ganta Raina ke b'aci Agabana yake nuna Mata so bazan iya d'aukan kowane irin Nonsense ba wallahi."

    

  Tausayin Hansai ne ya kama Suhaima tace "Sorry Aiba  Lefinta bane" Sumy tace ai sena renama Nazi hankali.

  

 Kamo hannun Hansai Suhaima tayi Ta d'aga ta ta mik'e nan ta dau flsk din Ta kalli Suhaima "Nagd" Duk yayin da ta kalli Suhaima se gabanta ya fad'i nan suka shige Gidan .

 

 Biki yayi Biki gud'a ko ta ina nan aka bawa Suhaima Mazauni Lemo kawai tasha Sady Tazo ta jata Gun Frnds nasu sai yau shegamo suke domin An dade ba ahadu ba, sai kiran wayar Anty take ta nan sukai waya ta tashi ta doshi cikin Gidan Direct side d'in Anty tashiga.

 

  Anty yau bata fita ba sakamakon kanta dake ciwo Da dugu Suhaima ta Rungume Anty tace "I mssd u Anty" Dariya Antyn tayi "Saukar yaushe? dama kuna Nigeria? Suhaima  tace "no Anty hutu Nazo" duk Family suna can Amma Suma zasu zo hutun."

  

  "To Allah ya kawo su cewar Anty."

  

  Suhaima tace "nikam Anty akwai wata 'yar Aiki tun jiya Naganta yauma Naganta." Anty tace "wake nan? Kin san suna da yawa."

  

   Tace "Kinga wata 'yar fara haka yar Doguwa bacan ba  mai Manyan Ido da dogon hanci ,tana da Gashin Gira Da yawa harda Wushirya."

   

  Dariya Anty tasa "Tamkar kanki kike Suffan tamin ai" 

  

  "Aa walh Anty  aikin ga ni Banda wushirya kawai de haka take."

  

  "Kode Hansai kike Magana?" kamar da had'in Bakin Hansai ta shigo da Khalil A hannu  yana kuka .

  

 Suhaima tace "yawwa kin ganta" Anty tace Au Hansai ai 'yar Aikina ce"

  Suhaima tace "tana Birgeni Ga hankali saide ko yaushe saina ci karo ko Sady da Sumy na dukanta."

   tace "ai haka suke sai hkr" .

   

   wurin Bikin suka koma Haka akayi akagama aka watse 

   

   Washegari ta Kama Friday inda Amare da frnds Nasu suka hada lunching Nan ma ba a magana Na chase Inda Nura m inuwa yayi barin Wak'okin Bakin.

   

   *Washegari  Ranar Daurin Aure*

   

   Nan ma Washegari Ta kama Saturday aKa D'aura Auren *RUMASA'U DA ALHAJI MUSA*

   

   *RUBAYYA DA MUSTAPHA*

   

   *ZUBAIDA DA FAWWZ*

   

   Aka shaida Akan Sadaki Lakadan ba ajalan ba Kowacce dubu Dari Biyu.

   Lalle burin Dady ya cika domin garin Abuja sun san Ana Bikin, ko ta ina mutane.

   Su Mama kuma Suka Zarce Da yini Nan ma Faty Niger  ce Tazo ta wak'e Amare.Haka akai biki Lafiya aka Gama sai fatan Zaman Lafiya.

   

   Washegari Ta kama Ranar Sunday Aka fara shirin Mik'a Amare Zuby Anan Abuja Gidan ta Yake Haka Ruma ,Ruby ce zaa Mika ta Lagos ita se Washegari.

   

   Amare sunci kuka sunkoshi kowacce akai musu Nasiha aka mika ta Had'dden Gidan ta.

   

   Litinn Da safe aka tafi kai Ruby,Sai de muce Allah ya bada Zaman lafiya.

   

   kudakace ni Fans sai kuma gobe In kowa ya huta da gajiyan Biki.

   

   

   By 

   Queen meemi

   Queenmeemi.WordPress.com



. . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣34❣

            *FEB,2017*



_®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASSION_



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_




**********


Gida an Gama Biki an watse sai su Hajia da sai tayi Sati 2 san nan zata tafi ,sai su  Sady sai hutun gajiyar biki suke haka su hansai keta aiki ko ina agidan saboda harkar biki sai an  bata gu,Hajiya da Umma da Mama ke break fast A babban Falo tace "ku yanzu bakuji Dadi ba! jin kamar kun sauke Wani nauyi da Allah ya D'ora muku,musamm idan.mace ta isa Aure kuyi Mata inde ta isa Dan Sauke Nauyin Da Allah ya D'ora maka."


Mama tace "Wlh kullum sai nayi wa Allah Godia Saboda min sauke wani nauyin ." Umma tace kedai Bari Allah dai ya bawa yan baya maza na gari."

  Hajiya Tace "Ameen".

  

  

 *Bayan wata D'aya*

 

 B'angaren Amare kuwa sai san barka Musamm Zuby Soyayya suke kwasa da Fawwz Dan sun tafi Honeymoon Dubai,haka Ruma tana zaune Lafy da Alhaji Musa Saboda Gidan ta da ban kuma sun fahimci Juna, sai B'angaren Ruby ma hakan take.

 

 

Sady ce zaune  ta kafawa waya I'do tace "Sumy wlh inada damuwa! kin san wan Handsome din nan Wanda muka had'u dashi a Bikin Futha 'yar Minister ,wlh na Kamu da Sonsa."

 Sumy ta d'ago da gud'a "yirrrrr! Lol Amma nayi farin ciki yanzu duk Irin Mazan dake sonki duk basi maki ba se yanzu nikam Zanso Naga wan nan Guy."

 

  Sady ta FarFara Ido "ai suma zakiyi Idan kuka had'a Ido, keni fa Numfashina har neman sark'ewa yake yayin da na kalle shi ki,ba abinda ke Birgeni dashi sai basarwa d'in nan."

  

   Sumy ta tab'e baki "ayi dai Mugani." 

 Hansai ce ta shigo da Mopper ahannu zatai Guga  Sumy ta Harareta "Get out" Juyowa tayi ta koma Sumy tace "ban san Yarinyar nan Cuz duk ta Birkitan Nazi."

 

  Sady ta k'yalk'yale da Dariya "tab! Amma Sumy kin fad'o kina Big Gal, Amma ace tsami Hansai zata kasa ki koda yake tafa kile yanzu, ahakan ma bata son sa kenan."

  

   Sumy tace "Barni kawai kin san Nazi yanzu se yayi me gaba d'aya!"

    Sumy tace "to ni wai kinsan Sunan shi Saurayin da kike so? tace "Aa" 

    

    "Aa! kinada Wahala sai ki dage."

    

     Sady tace "Futha zan tambaya kawai!"

  tace "daya fi maki," wayar Sady tayi K'ara ta d'auka Ganin number waje yasa ta daga "Aa Suhaima!" tace "naam"

   "kin koma ashe!" tace "eh hutun ya k'are ai se kuma nan da 3 Month zan kammala Degree zamu dawo da har su Dady". Sady tace "Allah ya kawo ku," 

  "Ina Hansai kuwa? tsaki Sady tayi "ke kin Mak'alewa 'yar Aikin nan tana can tanayi"

  Tace "Okey ki Gaida" ta nan sukayi Sallama.

  

  

  *8:Pm*

  

   Nazi ne a d'akin wani Abokin sa suna kallo "yace Khalid kasan Sumy?"

   yace "eh man!

  yace "to Gidan su akwai wata Yarinya wlh ban d'auka Sonta nake da Gaske ba, kwanakin nan duk ta dabaibbayeni,kuma matsalar batta sona."

  

   khalid yace "haba naga Sumy ce Budurwarka! yace "eh Dan so ina son Sumy, Amma Soyayyar Yarinyar nake sosai."

   Yace "tab! zaka had'a Jalala kasan ba yarda Sumy zatai ba"

    yace "sosai so nake kaban Shawara," shuru Khalid yayi kawai  ka hak'ura da d'aya"

    

     "Nida Sumy zata hkr ai nafison hakan" yace "Haba kai ma kasan Dadyn ka bazai so had'a iri da 'ya'yan talakawa ba ,naji kace 'yar Aiki ce ma"

     Nazi yace "ni ba ruwana da wan nan inde akwai so is okey" khlid yace "my Fnd kawai ka rik'e Sumyn ka  so me sonka" yace "zan Gwada."

   

   

   

   * After 2 Weeks @4pm*

   

  Juyi Sady keyi adaki don kuwa duk ta tashi hankalinta Domin Sosai take son Dream Guy nata Ganin ba sarki sai Allah yasa ta watsa kiran Futha 

   Ta dauka "Amarya bkya Laifi" tace "ya San Ranki" D'an Jimm tayi "nikam  Futha a Bikin ki ai Naga wani Handsome Guy duk Samarin gun sai de Subi bayan sa wajen haduwa"

   Tab'e baki Futha tayi "Banda Mijina dai!" Sady ta sa Dariya "haba dai Futha ai ko Mijinki Al barka, Pls kin san  Shi ?"

  Tace "ke ni ta ina zan sanshi" nan tayi taimata kwatance bata gane ba tace "aidama bazakii gane ba" tace "eh naji" nan suka kashe.

   

   

   Kande ce ta shiga D'akin tace "Anty Sady wai kin bak'o awaje" tab'e baki tayi "naji" mikewa tayi ta Dan fesa turare tayi  waje sai cuno baki take ta fita.

   

    Yana zaune akan 'yar Rumfa a kusa da Parkin Space Tsaki tasa tace "Dan naci kaine? d'agowa yayi haba "Sady meye Laifin me sanka? 

    

    kaga! Hannu ta daga "kai Faruq ka fita way D'ina don bana Sonka haba adauri kashi ko a bata igiya? na farko Bakada Naira na biyu ba Good Dress ko mota bakka da ita."

    

    Murmushi yayi "haba Sady  ni inada rufun asiiri, ni Dan kaduna ne Aiki nake a Abuja din nan kuma kin san ai aganka da Aikinka ai yafi baki san inda Rana zata fadi ba."

    

    Hansai ce ta fito da Roba ahannu k'walla kiran ta tayi taje "oya zauna kuyi hira da Shi , da ita kuka dace ni nayi nan" juyawa tai suka bita da ido .

    

   Gaidashi Hansai tayi tace "kayi hkr Aiki nake" yace "ba Matsala dama tafiya zan ma nide ki tayani Addua Allah ya ban Sady" tace "Amin."

  

   Nan suka Rabu ta koma Gida cike da mamakin  wulakncin da Sady kewa Samari kowane yazo sai tace bata son sa haka dai Rayuwa tacigaba da tafiya har... .........

   

   By

   Queen meemi

   Queenmeemi.WordPress.com

   

   

   

   

   . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣35❣                                   .             *FEB,2017*


             

®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION(NWA)



_Sadaukarwa ce Ga Basher Usman Family's_



 ***********


Rayuwa nata tafiya da k'alubalai masu Buri suna son ya cika ,wasu kuma suna cikin bakin ciki haka Rayuwar take yau Baki Gobe fari .          




Yau Me d'aukan su  Kande da Karime tazo tafiya dasu da yake gari daya suke. "Mama ta kalli Kuluwa Tace yanzu tafiya zakiyi dasu?

 Tace "wlh Aure za a musu" Umma Tace "ai ma wad'an nan sun Dad'e kisan k'auye basa barin yara sukai har sha takwas ba Aure".


Kuluwa Tace "wlh kuwa yanzu duk ba sa'anin su,suma Dan sun Samu nan ne shiisa,baga sunan sunyi fes dasu ba." Nan aka had'a musu kud'in Aikin su tare da shatara ta Arziki .kuluwa na Jadda da musu kan zata kawo musu wasu 'yan Aikin.


Acan Farfajiyar waje suka had'u da Hansai tana kuka zuwa tayi ta Rungumesu "Shekara Biyu muna tare   Mun shak'u yanzu zaku tafi ku barni."


Kande ta Matse k'walla zamu had'u bamu Rabu ba ,ki bamu Number D'inki kinga bamu da ita idan Munje zami samu waya Mi miki nan ta bata,karime  kuwa ta kasa magana.


Kuluwa tazo "se  kuzo mu tafi Garinmu da nisa fa," da k'yar suka rabu Suka tafi da Abin Arziki da yawa, wan nan kenan.


Suk'uk'u Hansai ta dawo Bayan tafiyar su, sai da iya kad'ai suke hira kawai kamar Mara Lafiya,nan ta hau tunani jitayi Gidan yayi Mata rashin dadi side din Anty taje Ta shiga tana zaune tana waya ta juyo tayi ma Hansai Iso data zauna .

Zama tayi Anty ta d'ago tace "Jiya Uncle Abbas ya kawo Mini Result naki" Mamaki ne ya kama Hansai tare da Murna tace "wayyo Dadi"

Tashi tayi ta fito da Result din ta zaro ta nuna Mata Gashi 8, Credit kika samu saboda Dadi kuka ta saka Hawaye shab'e -shab'e ta daga hannu sama "Allah na Godema" Anty tace "kawo na adana miki nan ta mik'a mata 

Anty tace sai Abinda zan gaya miki ki dawo nan kawai kina kwana wan cen D'akin.

 Kinga iya k'aramin D'aki zata koma itama ,can yayi Girma tunda Su karime sun tafi." Dadi ne yayi ma Hansai yawa tace "to Anty."


Can waje ya fita ta zauna sai washe baki take tana kad'a kafa tace  burin Baba kenan da  Muntari  Abinda sukeso nayi kenan Wayyo Allah Nagode maka kasa na had'u da Muntari." 

Haka tayi ta magana ita kad'ai nan ta Lula tunanin   irin Soyayyar da suka zuba da can Allah ka kawo min Muntari Dariya tayi kamar wushiryarta yafito tamkar tana tare dashi.



Tana nan A zaune Get d'in Gidan ya bud'e Sady ta danno Hancin Motar ta a Fusace ta fito daga Motar a 360 idan ta na tsiyayar Hawaye ta kalli Hansai ta wulla Mata key "dalla Gashi kaiwa Ashiru ya wanken mota" da sauri Hansai ta D'auka tana Mamakin Sady.


Da gudu Sady ta Fad'a kan Bed ta fashe da kuka Sumy dake kwasar Sleep ta, Mutstsike Ido ta mik'e tace "Sis meya faru?"

 kuka ta kuma fashewa dashi Ta tashi zaune ta zauna "Sumy."


"Ehen ina Jinki meya faru?" Sady ta Lank'washe k'afa kamarni Sady wai Namji zai yan k'wana Impossible."


"Ke in zaki gayan Ki gayan" Sumy ta fada Sady tace "wai kin san Handsome d'in nan na gani a 212 yana Zaune Acikin Motarsa irn na fito na gano shi Lokacin ya fito sai na bige ban saniba  yana D'agowa Yace wai ina dubawa ina kallon hanya na bashi hkr ya tab'e baki."


Sumy ta sa Dariya "Weldon kinga ai yanzu Kayi hkr dashi ,tace "no nifa Shi nakeso wlh ,yan zuma kawai na fada miki ne Amma bana jin haushin sa kawai tsananin sonsa ne ke sani kuka." tace Allah dai ya kyauta" Sady tace "yanzu number d'insa nake nema wlh."


Sumy kam Daria ta yi "nikam da zaki bi ta tawa da kin hkr da Samarinki Ki zabi d'aya aciki."


"Kai Sumy kinsan Dady bai son Talakawa kun manfa yanda akai dasu Zuby ne! don haka wan nan guy din ta koina yayi."

 "Be a Lady mana haba karki bada Mata kina Jan Class." Sady tace "sekiyi kuma" nan ta mik'e ta fad'a toilet don wanka.Haka itama Sumy ta shiga Dayan Toilet don Nazi zai zo.


*5:30*


Hansai kuwa yau tsimin son Muntari ya motsa haka ta d'auko dogon abin Busar ta tun na k'auyensu tana Dan busawa  tana tunano irin Soyayyar da suka sha da Dalilin Rabuwar su, hawayenta ne keta diga kan cinyar ta, Mangaron dake Garden din taje tadan tsinka ganin ya nuna tazo tana Goga Shi a hannun ta.



Dariya taji a bayan ta tajuya

 da sauri sukai Ido hud'u da Nazi Shida Sumy ne zaune kan kujeru Ta fesa uwar kwalliya sai kwai nane take. shikam Hansai ya kafawa ido Sum sum Hansai ta mik'e tazo ta wuce a hankali ya furta I luv u babe" Tsawa Sumy ta dakawa Hansai ta tsaya tace "come" 


Nan tazo ta tsaya ta kalli Nazi "ka kalleta san Ranka wlh akanta zan huce" Murmushi yayi "Madam Sumy in kika dake ta ai kamarni kika daka." K'ululun taji na bak'in ciki tace "Nazi ka dai na mun irin haka! haba banso ,ke Hansai ayau agabana inaso Ki ce bakyason Nazi yaji."


Dago Kai tayi ta ce "nifa Anty inada Miji akauye kawai ni bana sonsa,Ki daina damun kanki ma." Murmishi tayi "kin fanshi kanki yarinya don bana son raini Bar nan ."


Asalub'e ta Juya Nazi ya bita da ido ,Sumy tace "yanzu Nazi agabana kake son wata haba watan ma 'yar Aikin Gidan nan yanzu ace ita kake so Alhalin kasan Maganar mu dakai har ta Kai ga Manya dama baka sona ko!?" ta share Hawaye.


Yace "Sorry Sumy ina Sonki But!

"But what? Nazi plss nifa akan hakan wlh sena hk'r dakai na dole, don ban san Yaudara."

 Yace "sorry Daga yau na dena"

 Dariya tayi "okey" nan suka cigaba da hirar tasu.



BY

👑Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.


. .

. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣36❣

          *FEB,2017*




®NAGARTA WRITERS ASSOCIASION(NWA)




_Sadaukarwa ce Ha Basher Usman Family's_




*************


Da k'yar da sid'in Goshi Sady ta samo Number d'in Handsome agurin Futha domin damun ta data taimata Mata yasa ta tambayi Mijinta ganin bata gane ba yasa tace Sady taje gidan nata.Acikin vedio na Bikin ta nuna shi nan Mijin  Futha yayi Mata kyautar Nomber din sa, taji D'adin Karba tace ya gaya Mata sunan sa Yace Aa ganin ta samu Number yasa ta hkr.



Tunda ta amshi number din sai Abin ya zamo kamar me kullum ta kira a kashe. kamar ta kurma ihu yanzun ma kira take tayi  Amma Shiru.


 Abin Haushin ma ta d'ora Number din a  whtsup taga ma ba'a  tab'a bud'eta A whtsup ba, kamar tayi kuka


 Tana kwance Hansai na Gyara mata farce ta kira wayar k'irrr ihu tasa Jin ta shiga ta kalli Hansai "Get out  anjima Kya k'arasan" sai datayi kira sau wajen 10 san nan aka d'auka daga can Mace ce tayi Magana "plss yana Aiki ne a office Later Kya kira" tsaki Sady tasa Tasan sakatariya ce ta d'auka nan ta juya baya tayi mai text msg ta aika.



Haka fa take ko yaushe cikin Msg ko kira, so daya ya taba d(auka bayan Sallama ta fad'a A kwainane "Yace plss I'm so sorry don Allah Ki daina kirana" d'if yakashe. kamar ta fashe a wan nan saboda Haushi ,time faruq ya kira tayi tsaki  tama kashe Phone din agaba d'aya.



  *After 2 month*


Fad'a sosai akai tsakanin Nazi da Sumy Shi ya nace kan yana san Hansai don har Dena d'aga kiran Sumy yayi, da yake Sumy nada fad'a yasa ta biye mai sukayi kaca-kaca Yace bazai  kuma zuwa gunta ba hakan itama tace inde hakan ne sede su Rabu domin bazata yarda yana kunya tata ba, dama ta san Mayaudarin ne yau satin su d'aya kenan.



********

Wan nan damar ce tasa ya saki jiki ya juya akalarsa Bangaren Hansai ,har saida ya samo Number dinta,haka ya tasam ma kiranta ba dare ba rana, yawan kiran Hansai da yake a waya yasa take sata a silent domin ta rasa inda ya samu sai dare yake kira tsoro ke cika ta domin tun d'aukan da tayi daga farko ta gane shine bata sake ba ,hakan sai karaci kiraye -kirayensa ya Hakura.



Umma Mama Sumy da Sady duk suna suna zaune a babban falo inda suke hirar Amare su Zuby watan su Shida da aure suna kallo Suna hirar su. Anty ma ta shigo ta zauna Anayi da ita.



Hansai kuwa tsaye abayan Sady agefe tana yi mata tsifar kai  wayatar ta  dake sak'ale a bakin zanin ce ta tayi k'ara, ta zaro ta sai kiran ya d"auke,ganin ya katse sai ta aje a bakin kujera.



Wani kiran ne ya kuma shigowa Sumy kam a kusa da wayar  take nan idon ta ya kai kan Screen din 'yar k'aramar wayar nan tayi tozali da Number d'in Nazi domin ta hardace ta tsaf wani tashi tayi  har ipon dinta ta fadi k'asa.



"Ke Hansai wan nan number waye?" cike da tsoro Hansai ta hau in ina ,"ba dake nake talk ba?" Hansai tace. "Nima ban sani ba."


"Uhum baki sani ba me idona ke gani ehe?"


Hansai tace "Yi hkr wlh bansani ba, Don contacts 6 ne A wayana Daga na Anty sai Baba sai taki da ta Sady da Uncle" wani Zazzafan mari ta bawa Hansai,karamar k'ara tasa ta D'urk'ushe akasa tana kuka.


Anty tace "me tayi maki Sumy? Mama ta juyo "haba Sumy me tayi maki?"


Ragwaf Sumy ta zauna tace "Mama tun Randa Nazi yaga Hansai yake min A binda ya gaya dama,yanzu kusan watan mu d'aya da B'ab'ewa, dalili Yace wai dole yana son Hansai nikam  ba irin Fadan daba mi dashi ba kan hakan Tun kan bikin su Ya Tuna,ni kam bazan iya had'aka da itaba na Rantsa."


"Shiisa yanzu Naga ya daina kirana Ashe Sun had'e yana bugo mata."


 Umma ta Had'e rai "ke Hansai har wuyanki yayi kauri da zaki had'a kafad'a da Sumy har kinyi Gogewar da zaki k'wace Saurayi! to wlh Ki kuka da kanki Ki tsaya inda Allah ya barki domin bakida wani gata kina "yar aiki."



Ran Anty ya b'aci tace "ke Hansai gayan Gaskiya tace "wlh Anty ban san cewa Shi bane kullum Ana kirana da Number ban tab'a d'auka ba kuma ban san cewa Shi bane kuma bana Sonsa."


Sumy tace  "shut up! me Nazi zai dake to wlh Ki kuka da kanki."


Anty tace "Tashi muje" 

Nan Hansai ta mik'e tana kuka.


Umma ta bisu Galala da kallo "yo dama 'yar aiki in Banda Sangarta har da waya ita da Aka kawo Aiki!


Anty ta juyo "Umma kenan sai kuma akace 'yar Aiki ba Mutum bace ,ba fa Wanda yafi wani, face mafi tsoron Allah."


 Mama tace "ku bar Maganar, ke Sumy ku shirya kawai tunda su Dady basu san cewa bakwa tare ba."


Umma tace "yadai kamata."

 


*Bayan satittika*


B'angaren Nazi kuwa ya rasa yanda zeyi Saboda kin D'aukan kiran Hansai duk ya fita Hayyacin sa gashi harga Allah yana missn Sumy sede fad'anta ke hadashi da ita. Amma dole ya kulata domin yasan Dadynsa bai san Sun b'ata ba.


dama  Ummansa keso yayi Aure ko ya Dena shigar Swag,tabbs yasan Auren sa da Hansai ba mai yuwuwa bane tunda batta sonsa gashi kuma yar talakawa Amma tabbas yana son ta.


K'ara kiran ta yayi jiyayi ta dauka farin ciki ya samu kansa ciki ,siririyar Muryar ta ta doki kunnen sa ya lumshe ido.


Nan Ta fashe da kuka "Don Allah kadena kirana ,sabili da kana had'ani da Mutan Gidan mu,kana cutana kadena banso kayi hkr ka rike wadda ke sanka ni na gayama inada Miji ku ni ba yar kowa bace face yar talakawa, pls ba donni ba don Allah kadena kirana Ngd da soyayyarka gareni." kit ta kashe wayar


Tsai yayi da wayar a hannu ya daga kai sama idon nan yayi ja sosai.yadan mike dole nabi Shawarar Abokina  na koma gun sumy mu shirya, Bazan so A dinga k'untatawa Hansai akaina ba, domin so mai sonka, son maso wani kuwa k'oshin wahala ne.



hakan kuwa akai ya nemi wayar Sumy Sam taki d'agawa.


Wajen Kwana 2 yana Try Amma bata d'auka da kyar da Sid'in goshi Abokinsa ya shirya su ta hak'ura suka koma Soyayyar su kamar da.




By

Queen meemi👑

Queenmeemi.WordPress.com.


.



[5:52pm, 23/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣37❣

            *FEB,2017*



®NAGARTA WRITER'S ASSOCIASION(NWA)



_Sadaukarwa ce Ga basheer Usman Family's_




***********


 RANAR MURNA


Wajen K'arfe 12 na Rana  Lami ta dira A abuja Hansai na Tsifar kai A kusa da Fulawowi Ta gano Lami nik'i da kaya ta shigo da sauri Hansai ta je ta Amshe ta tana Murnar Ganin ta. Lami tace "ja'ira to tafiya nazo nayi dake."


Tsalle ta daka "haba Wayyo Dadi" Nan suka shiga side din Anty itama tayi Mamakin Ganin Lami tace "Aa Lami kece haka da tsakar rana kinsha hanya" zama tayi Wallayi kuwa tafiyan Gaggawa ce ta same Ni Shi Baban Hansai da kansa yaje guna yace amaida ita za'ai Mata Aure wlh kuwa,shiisa kika ganni."


Jikin Hansai ne yayi sanyi hakama Anty.

Bayan taci ta huta tayi Sallah Anty tace "Amma inaga sai de Gobe zaku tafi kinga yau Alhaji be sani ba" Lami tace "bakomi yau da Goben Ai duk dayane."

Hansai kuwa suk'uk'u ta dawo Jin cewa za'ai Mata Aure Sam se taji bata san komawa bata san wa za'a Aura Mata ba Amma ta basar.

 har ta gama karfe 5 dai -de Iya tayi mata kitso me kyau.


Washegari Misalin k'arfe Bakwai suka gama Shiri Anty ta fito da kayan tsaraba hili Atamph, Shadda su Takalim kaya de turmus da sarka k'aramar Akwati tayi Mata tace taci Biki dasu .


Kuka sosai Hansai take taje sukai sallama da Umma da Mama su ma suka bata Atampha kowacce, taje gun su Sumy da Sady ma sukai Sallama sabo akace turken wawa koda ba zaman Dadi suke da itaba sunji rashin tafiyar ta .


haka dai duk sukai Sallama Anty ta bada kudin Aiki 200k san nan ta bawa Lami Dubu Goma da kudin Mota su Mama suka bawa Hansai dubu Biyar,da kuka ta tafi .Anty suka tafi Driver ya tafi kai su tasha.


Shekara uku kenan da zuwan Hansai Abuja yau Gashi zata koma don Ai Mata aure ,to muje zuwa.



*Mangalu*


Sai wajen 2 suka Shiga Mangalu A gajiye taxi ta aje su a k'ofar Gidan Suka Firfito da kayan wasu yara suka daukar musu suka shiga ciki, tun A soro take Jin Maganar Jummai tana Maraba ganin yara na shiga da kaya da gudu Hansai ta Rungumeta har da kwalla.


Jummai tace Lami "kede sannu ya hanya?" nan Lami ta fito da 200k "ga kudinta Ni dama tun acan aka ban nawa, ta dauki wasu kayan tace na tafi domin so nake nake gida na huta."

 

Jummai tace to "angode Lami Allah ya saka da Alheri d'awainiyar da ki kai da Hansai" tace "Amin."


Bayan firar ta Jummai tace "naji Dadin ganinki fes Hansai kamar dama can A birnin kika rayu, sai k'amshi kike" Dariya tayi suka shiga daki .


Tayi sallah taci Abinci suna hira da D'an Jummai da ya dawo daga Boko Jummai ce ta shiga d'akin Lokacin Hansai nata fito da kaya.


Tace "inna wai ina Baba Gwamma ne? Nasan dai Baba ba yanzu zai shigo ba.wai Da gaske Aure Za aimin?"



Jummai tace Eh Haka dai naji Malam ya gayawa Lami Amma de Anjima maji Dalili."


 Zaunawa tayi "Lalle Hansai na yarda Dan Adam ba abakin komai yake ba,duk iskancin Mutum to akwai ranar kin dillanci ,wato Ranar da hajjar Maigari ta cika,duk zalincin Mutum Karshensa bai da bai kyau."


Hansai tace "Gaskiyane Inna"  


"Ai In gaya miki tun Lokacin da Larura ta samu Mudi na fadan da sukai da. Abokan sa, da suka yayyanka Shi, Gwamma ta tashi hankalin ta gani take kamar Ni nayi mai Asiri har abokan suka samu dama akan sa, akan hakan ta sai da Akuyar ta taje gun boka, wai ya bata Maganin da zata samun don na nakasa ,duk wan nan Abu da take bata san nasan Abinda take ciki ba, domin da kunne na naji tana Gayawa Mudi dake kwance yana jinya kan sai ta dau fansa akaina."


"Hakan tayi Abinci ta zuba min duk don naci nikam tana kawo wa na zubar , tun tana zuba ido ta ganni daram nan ta dada tsangwama ta nikai Addua naketa zubawa kan Allah ya kawon Dauki."


"Bayan kwana biyu Mudi ya warware ya koma gun shedanin A bokansa sati biyu tsakani fad'a ya kaure kan kud'i inda mudi Yace bazai bada na wajen sa ba,domin bai dena Halin nasa ba na bunsu sace-sace, nan suka tasar mai Yace kudin nagun Maman sa."


 "Washegari sai gasu kuwa! Lokacin bakowa Gidan Dije ta tafi Tallah ,nima na fita Malam baya nan sai Gwamma kawai ,suka shiga Mudi ya kasa ta ya tsare Gwamma Daga d'aki ta dinga d'uro musu Ashar wai ba zata bada kud'in ba ta cinye in na karfi ne su kwata."


"Da yake su 'yan zamani n,e sukace idan ba zata bayar ba se Sun illata ta, mudi Yace ta bayar kawai ya hkr, domin yasan halin su, Gwamma har da buga tsalle tace ba zata bayar ba tana zagin su kan kace me! Sun zaro Adda da wuka nan suka hau fada da Mudi .Gwamma har da d'auko tab'arya ta kwad'awa wani akai, kan ya fashe Jin zafi ya Shammaci Gwamma ya Lafta Mata Adda a hannu da k'afa dayan ya yanki Mudi a hannu ganin Gwamma ta Fad'i k'as kamar mara yasa suka arce."


"Ba adade ba, aka kaiwa Malam Labari ya dawo aka kai ta Asibitin cikin gari."


"Satin ta d'aya suka dawo duk ta fita Hayyacinta mai hali baya fada halinsa, tana cikin ciwon ma bata daina Rashin kirki ba, hakan ta cigaba da yiwa Malam abinda ta ga seda tayi wata daya san nan ta warke ,nan ma ta kuma sai da akuyar ta wadda ita kadai ta rage mata ta tafi gurin boka."


"Adalilin zuwan ta gidan Boka ne, Mota ta Bigeta m wan war tayi atiti, badon ta da  nisan kwana ba data shura,nan aka kaita Asibiti,gashi wanda ya buge tan ya gudu, ganin yanda k'afarta daya data dagargaje aka yanke taci kuka ganin tadawo Gurguwa."


"Satin ta Daya da fitowa A Asibitti ,Malam ya zaunar da ita yana Mata fad'a,kan tayi hankali ta dawo Matar kirki, tashin farko ta Lailayo Ashar ta danna mai tare da Ambato babarsa da ta Dade a kushewa ta zaga, Harkuka yayi shikam Yace inde Itace Autar Mata ya saketa bazai  iya zama da ita ba."


Ta b'ata tarbiyar 'ya'yanta Dije duk kauyen nan ba Wanda take shayi ga fada da maza ko ita Gwamma din ce tai Mata magana zaginta take.Duk halin gwammar ta kwashe sarai.Malam so biyi yana sata makarnta tana cire akanta,Mudi kuwa yazama Abinda ya zama baya kwana agida ma,ba irin fadan da Malam be mai ba kan kin karatu da sana a yaki har kaishi gun bakanike yayi don Ya dinga koya yaki ,duk sa aninsa Sun san me suke wasu ma sunyi aure,To ta Riga ta bata musu Tarbiya."


Hansai taja Numfashi "Allahu akbar Wanda yadau Duniya da zafi haka zata zo mai."


Jummai tace "yo ai Duniya tafi bagaruwa iya jima. Wanda Yace tukunyar wani bazata tafasa ba to nasa ko dimi bazaki ba."


Hansai tace "to yanzu tana ina?"

 "Jummai tace "tana Gidan iya sema kin ganta abin tausayi ga ba k'afa duk ta Rame, iya kam sai hantara ce ke shiga tsakanin su ,Dije kuwa ko kallon ta batai balle ta taimaka mata sai de yawo.wataran Haka zata zauna da yunwa,se Iya ta samu take bata."


Hansai tace "Allah y kyauta."


Adai-dai time din Baba ya dawo yayi Murnar ganin Hansai, don Hansai har da kuka Tayi saboda aganin sa.

Baba ya zauna Yace "Allahu k'adirun Ala man yasha 'u tabbas abinda Allah ya shirya babu makawa tsaiya faru.


ya kalli Jumaai jiya bangaya miki Dalilin dawo da Hansai ba ko? to  Dama dalilin dawo da ite shine Anga iyayenta na Asali."


Jummai  ta mik'e tsaye tare da dafe k'irji! "da gske Malam? kai Alhamdlh."


Ita kam Hansai suman zaune tayi.



By 

Queen meemi👑

Queenmeemi.WordPress.com.


.

[10:38pm, 25/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣38❣                         *FEB,2017*


             

_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



*Fans  kunjini Shiru ko? whtsup nawa ya samu Matsala ne shiisa Amma yanzu Normal ,hope kuna fyn,thanks for support nd care,😘*


***********


Kusan mintuna ta d'auka san nan ta d'ago kai cike da Hawaye tace "Allahu Akbar" Baba Yace "ki godewa Allah."

 Hansai kan cinyar Jummai ta dora kanta tana Matsar Hawaye.


Jummai tace "Malam to ya abin ya kasance? taya aka same su?"


Dariya yayi "aike dai Jummai bar ikon Allah,Shekaran Jiya Sarkin kasuwa Yazo mani da Maganar, ina Gona yaje can da yake kinsan Ni bana zuwa  kasuwa.

To ya zo mani da Maganar wani bawan Allah da yazo dai+ dai Babban Titin nan me kud'i dashi yana kuka Acikin motar sa kuma motar baud'e, su dai Sun rasa dalili yasa sukaje suka same shi.sarkin kasuwa Yace Alhaji meya faru?


Juyowa yayi Yace bakomi bawan Allah kawai wani abu nake tunawa anan hanya, Malam ban mantawa da wan nan Hanya Domin shekara Aru- Aru hanya tace duk shekara sai naje wani kauye gaba nan Dan tai makon bayin Allah Marasa k'arfi."


Akwai wata shekara da Tsautsayi ya afka Bomb ya tashi da Tsautsayi nazo wucewa dani da Matata da yarana Biyu to anan ne muka rasa D'aya har ila yau da nake maka Magana bamu sake jin D'uriya ba shiisa koyaushe nazo wucewa sai na koka saboda tunowa da Gudan Jini na.


Jin hakan Sarkin kasuwa ya shiga tunani na tsawon Lokaci nan ya tuno da ita Hansai dake guna yace zai Gwada sa a ko Allah yasa adace ,shine fa Mutumin ya Gigice Yace akaishi gun Mutumin, haka muka gama Magana kan cewa nan da kwana 3 zasu zo don tantancewa.


Yanzu dai Shi muke jira watak'il Gobe ko Jibi."


Jummai tace "Allah kasa su zamanto cewar shine iyayen nata da nafi kowa jin Dadi Malam Yace "wlh nima haka."


Hansai kuwa kuka take mai tsuma rai kamar ranta zai fita "Baba Yace Hansai keda zaki godewa Allah kuma kike kuka."


Ta d'ago "baba kayi hk'r Ni kune iyayena bana son Rabuwa daku." dariya Jummai tayi ai mu dake mutu ka raba ,Amma hankalin mu zai fi kwanciya in muka gansu Hansai,yau kiyi ta Addua Allah ya tabbatar da Alheri."


*8pm*


Hansai da Jummai na zaune sai hira suke ga Baba agefe yana cin Tuwo Abdullahi yana bacci Hansai ta fito da kud'in hannun ta dama ita suka d'amkawa  ta mik'awa Baba tace "Gashi Baba kayi Jari dasu."


Baba Yace "haba Hansai kije ki wahalar Aiki mu daci"


 Dariya tayi "Aini ba abunda zan dasu" Jummai tace "naki ne fa! nan baba Yace to ba matsala Angode" Hansai tace "baba ka daina Godiya Saboda Ni na cancanta na Maida muku da Alkhairi da kukai mini domin kun Nunan duk-kan k'auna."

Baba Yace "Allah ya miki Albark" Hansai tace "Amin."


Kamar An wullo Dije ta shigo Baba ya daka Mata tsawa "me kike awaje yanzu?"


Turo baki tayi "banjin bacci" Baba Yace "Allah ya shirya" tashi tayi zata kuma komawa "baba Yace "ina kuma zaki?"

 Tace "Innarmu."


Hansai tace "haba dije Baban Kike gayawa Haka?  gashi kinga dare ne fa! 


"Eh  to ina ruwanki ,naji inna tace na koma me zan tunda ba uwata agidan."

Ta fita tana gatsina.

Malam ya aje kwanon cike da damuwa Yace "Gaskiya Gwamma ta cucueni, duk ta batan tarbiyar yara yanzu ace ina magana Dije bata ji?" Jummai tace "sai hkr fa da Addua."


 Gidan iya Dije tayi ta shiga d'akin da Gwamma ke ciki k'afarta da aka guntile na ciwo tace "Dije zo ki rik'eni zan mik'e"?"


Tace "nifa Bazan ba karki takuran."

Gwamma tace "Ni kike gayawa haka?sai kace sa arki." ko magana bata kumai ba tayi zamanta.



Gwamma ta matse k'walla halin da take ciki kenan ba mai Kula da ita kowa ya gujeta hatta iya hantarar ta take gashi yayanta ma nayi mata saboda rashin Tarbiya.


Mudi ne ya shiga yana fito  Gwamma tace "Yawwa mudi, kayiwa Dije fad'a kan abinda take min."


Ya juyo "Nifa Gwamma ba ruwana da harkanku abin Babana ya ishen."


Kuka ta saka da k'yar ta mik'e ta shiga Band'aki. iya ta fito "yanzu ke Dije uwar taki kikewa haka?" 

Dije tace "nifa banyi komai ba."


Iya tace Aa kyace baki komai mana tunda baki da tarbiya."


Nan Gwamma ta fito "yawwa iya ki gayawa mata ko taji."


"Yo Gwamma  ai dama duk uwar dabata bawa yaranta tarbiyya ba ,tace 'ya'yanta sukad'ai ne 'ya'ya to wallahi abin kanta zai dawo, kede Gwamma kin b'ata Rayuwarki data yaranki,uban yara ya sasu Makaranta ta Allo ma kin hana, ba abinda suka sani haba kin musu Tarbiyar banza, ai wlh kad'an ma kika gani kin d'auka ban san bin Bokayen da kikai ba,kika mallake Miji da kishiya ko,har 'yar ruk'on nan ma haka kikai ta zalintar ta, ke 'ya'yanki ne yara miji an maida Shi hotiho, to ai ga irin ta nan ki fara tuba ga Allah tunkan ki kaiga kushewa."


Gwamma cike da haushi tace "to naji."


Iya tace "ai baki horu ba.

Ke kuma Dije uwarki komai rashin kirkinta to ki bita domin Allah ne Yace abi iyaye."


Nan ta juya ta shige D'aki.

Gwamma ta zauna da Guntulalliyar k'afarta zuciyar ta na danasani Amma Girman kai bazai barta ta nuna ba.

Domin aganin ta ta fad'o (lalle Gwamma baki horu ba).


*Washegari.*


Tun safe su Malam ke Tsammanin zuwan baki Amma shiru duk Jikinsu yayi sanyi waya ya bugawa sarkin kasuwa ko Sun zo yace mai Aa.


Haka aka wuce Ranar Amma shiru ba Labari sai kuma Hansai Jikinta yayi sanyi sai kallon Hanya take har dare ba Labari,cikin sallar ta sai rokon Allah take Allah yasa burin ta ya cika.

Cike da Jimami ta kwanta.


    

*Washegari Da karfe goma Ranar Laraba.*


Hansai tayi wankanta tayi kwalliya tayi kyau kai kace zuwa k'auyen tayi ta Tambayi gun Jummai zata je ta D'an zaga gari.


Tafiya take Ahankali tana tuna irin Rayuwar da tayi baya ak'uyen Muntari ne ya fad'o Mata kawai sai tayi Hanyar bayan Dutse wurin nan kamar yanda yake sai sassak'e wasu dutsunan da akai.


Zama tayi tana ta tunani da Murmushi ga iska na kad'ata ,tayi kusan Awa d'aya a zaune yasa ta mik'e don ganin Dad'ewarta tayi Hanyar Gida.


Daga can nesa ta gano wasu shimfid'ad'dun  Motors guda 2 ak'ofar Gidan su,Badon tayi zaman Abuja ba, da sai ta tsaya ta Lailaya su.


Gaban ta ne let dukan uku- uku har taje daf da Motar ta tsaya bakowa aciki yasa tayi hanyar shiga Gidan a sanyaye.


Tun shigar ta taga Mutane Birjik a Babbar tabarmar Baba dake zama Asoro.


Cak! ta tsaya tare da k'arewa Mutan gun kallo har tazo kan wata d'anyar D'aby wadda taga kamar ita.


Kuka taji an fasa "Wallahi ko ban ga shaida ba wan nan Baby Husy ce!" kallonta ta maida kan me Maganar taji wani irin Fad'uwar gaba.



BY

Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.



.

[11:19pm, 25/02/2017] 👑MEEMI💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣39❣                         *FEB,2017*


             

_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



*************




Rungumeta tayi ta d'ago hab'ar Hansai tace "tabbas wan nan itace" dai de Lokacin kyakkyawar Budurwar ta shiga Gidan Dady yace "Daga d'auko Album kin zauna ko?"


"No Dady ke ne ban gani ba Amotar sai dana duba."


Juyawa Hansai tayi sukayi Ido hud'u da budurwar Suhaima tace "You!"  nan ta yar da Album d'in data d'auko ta Rungume Hansai "Mum wlh itace wadda nake baki Labarin suna kama da Arif wadda na ganta a gidan Anty."


Jummai ce ta fito rik'e da wata leda ta tsugguna ta aje Gaban Malam da smSarkin kasuwa, nan ya d'auko ya bud'e hoto ne guda biyu  Daya ajiki Hansai ce da Malam aka d'aukesu a Ranar da aka tsinceta sai D'ayan kuma ita kadai ce nan ya mik'awa Dady ya karba Yace Allahu Akbar."


 Nan ya d'auki Album ya duba sak! itace ce ba makawa Hansai 'yar su ce .Domin shigar Jikinta an Musu hoto ita da Hassanar ta.


Malam ya d'ago wato 'yan biyu ne kenan!" 

Baba yace "tabbas twins ne" .


Sarkin kasuwa yace "mun godewa Allah."


Nan Dady ya kalli Suhaima yace "wan nan itace first Born dita Suhaima, sai su Twins Hassana Da Hussaina,sai kanin su Arif gashi nan."


Hansai dake bunsu da ido tana sharce k'walla sabida Jin wani sonsu da take.


Mum (Fatima) shine sunan ta ,ta d'ago ta kalli Suhaima tace "Amma ace kije Gidan Anty ki kasa gano kamar da suke da Hassy haba Suhaima."


Suhaima tace "Mum wlh tunda Naganta naji ina kaunar ta Sam abin bai kawon ba,don naji Ance ta Mutu."

Dady yace Aikin san dama su basa kama da Junansu, sosai Hussaina tafi kama da Mahaifiyar ku, ita kuma hassana da ni shiisa."


Baba yace "Masha Allahu komai de Daga Allah ne."


Nan Hassy ta zo ta k'urawa Hansai Ido ta  d'an tab'a Hancin Hansai ta Rungumeta  tana Hawaye I Missd u dear ,I luv u my Twins sis."


 Itama Hansai ta Tungumeta ta na Tsiyayyar Hawaye "Me too sis."


Nan aka zauna sai Maida zance ake Hansai sai kallonsu take A ranta tana yaba su dukkansu Masu kyau Ashe wan nan finest Baby din Yayata ce Arif kuwa D'an Lukuti sai satar kallonta yake ,Mum Ma  sai satar kallon Hansai take Ganin kamar da suke da ita.


Dady yayi gyaran Murya "yanzu yaya Sunanta? Malam yayi dariya sunan mu na k'auye take karb'a."



Jummai tace "Hansai

sunanta" dariya Arif yasa 

hassy ta zungureshi, Hansai  tayi Murmushi ganin yanda suka Birgeta ashe itama haka take ta yan uwa Masu kyau had'ad'd'u.


Mum tace "dama ba acanja masu suna ba,Hassana da Usainar su ake ce masu Sai mu da muka tak'aita muke cewa Hassana Hassy."


Malam yace "itama 'yar tawa tunda ga sunanta Wato Husaina sai Ana cemata hakan."

Dariya suka saka dukkansu.


Dady sa bakinsa yak'i Rufuwa yace "ai Malam karkaji irin dad'in da nakeji da ya zamanto irin ruk'on da kukai mata kun zame yan uwa domin Husaina 'yar kuce."


Sarkin kasuwa yace "Masha Allah ai tun Lokacin b'atanta mukai ta bada cigiya shiru."


Dady yace "ai A lokacin Bama hayyacin mu, domin duk asume muke Direct kano aka wuce damu sai da Mukayi 3 weeks akwance Domin Hassana ma mun d'auka Mutuwa zatai itama domin mun Saddakar Husaina ta mutun, Amma duk da Hakan bayan warkewar mu sai da Mukazo munka bada cigiya sai aka cemana ai da dama yara Sun mutu dai Muka hkr.


Amma Mahaifiyar su kullum Maganarta ai na hussaina na raye da yake Munfi zama a Landon to duk Lokacin da Mukazo Nigeria sai na biyo hanyar nan domin ina tunawa da ita."


Malam yace "ikon Allah domin shike k'adarta k'addara Allah abin godia."


Nan sukayi sallar azahar se kuma suke shirin tafiya.


Malam yace Hansai ta had'a kaya ta bisu nan tasa kuka dum da farin cikin dake gareta,Jummai ma kuka take tace "Hansai kibi iyayenki ai bamu Rabu ba.


Mum tace "iyayenki ne suma ai" Dady yace "lalle me iyaye hudu" aka sa Dariya nan taje iban kayanta Mum tace ta bar su a bawa wadanda basu dashi.


Haka Suhaima da Hassy suka k'an-k'ame Hansai Arif na gefe yana binsu Mum da Dady suka tsaya ya fito da check ya Rubutawa Sarkin kasuwa 1million, Malam kuwa check na 2million ya mik'a mai duk  suka k'i karb'a k'arowa yayi ya Rubutawa Jummai na 500hundredk haka sukace su bazasu karb'a ba domin Hansai 'yar su ce  komai sunyi ne don Allah da k'yar da sid'in goshi suka karb'a."


Dady Yayiwa Wani Driver din sa Magana kan ya karb'i check din yaje ya ciro musu.


Shamsu yace "oga driving din fa?" 

yace "no Madam ta tuk'a, ka tsaya koba yauba har zuwa Gobe in Sun shirya sai kuje tare kacire Musu."


Da k'yar aka B'anb'are Hansai daga Jikin Jummai tana kuka tana kiran Baba da Jummai dak'yar tayi ta saduda suka fita.


cin-cirindon Mutane ne cike a awajen Motocin kan al' ajabin cewa wad'an nan First class d'in sune Familyn Hansai haka Hansai Da suhaima da Hassy da yasir suka shiga mota d'aya Driver yaja.


Mum da Dady suna Mota d'aya itake tuk'a su Jummai da baba sukai ta D'aga musu hannun da Alk'awarin dawowawr Dady gun Baba kan wani Aiki da zai Sama mai.


Fuuu! Motocin suka fita daga k'auyen Mangalu suka mik'a kan Titin Bunkure suka santali Hanyar kano.


Note -Hansai yanzu ta koma Husaina Husy ,don haka zakuji Ana cemata Husy.


By 

Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.


.



. [11:25pm, 26/02/2017] 👑Meemi💋: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣40❣   



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


                    

*_Wan nan page din naki ne @Ngileruma Tnz for ur luv nd care❤_*



*********



 Direct Gidan Maman kano sukaje wajen k'arfe Biyar Jikin Husy yayi sanyi game da Mamakin meya kawosu Gidan Maman Anty Rabia.



 Tana zaune Ita da Dan Autanta suna hira Suka shiga Falon Maraba tayi Masu, tace kuce da Ibrhm d'in kuka Mum tace Eh wlh Mama,nan dukkan su sukabo lafiyar kujeru, tace Aa Arif Dan lukuti har yanzu kanacin kayan fulawar ne?"


Dariya yayi , Tsai ta tsaya da maganar tace "to Hansai yana ganku tare ikon Allah sai naga kin saje kuna kama dasu ,keda akace Aure za'aimiki kodai Gidan Aiki kika canja?" 


ba Wanda yace kala sai da suka zauna suka huta.

Dady ya kallai Maman kano yace "ikon Allah Husaina ce yar wajena data b'ace da dad'ewa wadda akace ta mutu."


Tafi Mama ta dunga Amma naji kunya yarinyar nan so biyi tana zuwa gidan nan inde za a kaita Aiki abuja ko za a maidata kasan gun Rabia tayi aiki.

Ashe ni nan Jinina ce ban sani ba ,shiisa nake k'aunar ta mana,koda yake ai duk mun Sadak'ar ta mutu ne shiisa Sam ban kawo ba

ikon Allah  hansai zo nan Naji d'iminki."


Arif yace "no Maman kano yanzu sunan ta Husy not Hansai." Dariya aka saka dukka nan ta kamo Hussaina tace "wlh se yanzu nake ganin kamarta da Arif ikon Allah Ashe ba baya ba kike da kyau kunya ce ta kama Husy."


Haka sukai ta Maganar anan ta d'au waya ta Sanarwa Anty Rabia har da kuka tace Mama wlh shiisa nake k'aunarta har Raina Ashe Jinin mu ce."nan mama ta bawa Husy (hansai) waya suna ta waya tana tambayarta su Mubarak.


Bayan sun gama wayar Mama tace ni din nan da kike ganina Husaina Mahaifinki K'anina ne Uwa da d'aya Uba daya.


Mu 'yan Asalin nan kano ne Fulanin Garko Amma iyayen mu duk anan  cikin kwaryar kano muke.


Kinzo cikin Arxiki Domin dukka familyn mu kowa nada Hannu da Shuni.

Babanki ya rik'e muk'amai A Nigeria irin Lucky Man din nan ne tun yana yaro shiissa tashi d'aya yazamana Done ku kanku a Landon aka haifeku acan kuke da zama yanzu hakan Ambassador ne na Nigeria to London,kuma yana kasuwanci Akwai taimakon ma kasa dashi ,Allah yasa kuyi koyi da Halin sa na taimako.


Mahaifiyar ki kuma ita Asalinta 'yar Adamawa ce fulanin can ce iyayenta Malamai kuma suna da abin hannu kakanninki duk suna nan na gun uwa Amma na Dady kuma saura Kaka mace Mahaifiyarki nada kirki da son jama'a batta k'yamar talaka kinga an raba ke kike kama da ita Hassy da Dadyn ku."


Dariya suka saka Dady yace kai Maman kano duk wan nan bayani haka?"


Tace yo Meye aigwanda na sanar Mata tunda ya zama dole.

 tace  yanzu dai sai an kwana 2 kyaje ki ziyarci Dangi."



Dady ya mik'e to ni na tafi Masallaci,Bayan fitarsa dukkansu sukayi wanka Saboda gajiya wajen k'arfe 9 na Dare kowa yayi bacci Abinsa na gajiya in Banda Hansai dake ta Sallah tana kai Godiyar ta ga Allah.


Sai Suhaima dake waya da Saurayinta.


*Washegari*


Hassy da Hussy na zaune sai D'an hira suke,Hassy ta ce ki saki Jikinki Tweeny"


Suhaima dake gefe tana taje kai tace "nikan Husy kinyi School ko?"


Tace "eh mana nayi Junior Class sai natafi Aiki Amma acan Anty ta d'aukon me Lessn har seda nayi Waec."


 Hassy tace "Weldone Amma banso kikai Aiki ba",Husy tace "sis Ai ba yanda Mutum zai kaucewa k'addarar sa"


Suhaima tace  "tabbas" "Hassy plss ban phone naki zan duba wani abu"

 hassy tace kai "Ya Suhaima chatin nake"


"Ok dama bakya gajiya ai"

Hassy tace "sorry sis take it"


Husy sai kallonsu take sun bata sha'awa .Mum ta shigo tace "Oya kowa ya shirya 9 zamu tafi" haka kowacce ta shirya Hassy ta d'auko wani Material me kyau da tsada me ratsin Pink ta bawa Husy itama ta dauko wani ta saka cif sukai Ma Husy da yake kusan Jikinsu iri d'aya ne Suhaima tayiwa Husy kwalliya Hassy tace "wow my twin sis kinyi kyau"



Murmushi tayi "thnks Sis"



Hassy tace " Oya zomi Selfie🤳🏻 nan Hansai ta tsaya Hassy ta saita Ipon dinta ta daukesu sunyi balain kyau sai kamar su ta fito Rad'au.

Direct ta dora su kan Instrgram tana she's my twin sis.


Sai Dariya suke Arfif ya shugo yace wow "kunyi kyau Amma ya Suhaima Ai Husy tafi Hassy kyau ko?"


Hassy tace Lallema Lil Bro nidin?"


 "No Hassy ai gaskiyane kefa bakki da Wushirya" Gwalo yayi mata.


Hassy tace komai NO Mr No kawai"


Yace "Naji tadai fiki kyau"


"Ai sekayi tayi" 


Suhaima tace "zancen Gaskiya husy tafi ki kyau."


Hassy tace "Wayyo koma dai  me zakuje Tweeny Dina ce munfi kusa kano da 

Jigawa."


 Ita dai Husy Dariya kawai take yi sai kallonsu take. Nan duk suka fita sukayi Breakfast Dady ya kalli Husy yace ya kika kwana My Lovly douter?"


 Tace "Alhamdlh Dady" Mum ta kamo ta zo nan my Twin" nan Husy ta agida ta.


Hassy tace "shikenan ta k'wacen fada" dariya Arif yasa dama Dan adawar tane yace "sede ki hkr."


Dady yace "haba keda ita ai duk d'aya ne nan suka gama suka d'au Damarar tafiya Mama ta Rungume Husy "Allah yayi maki Albarka" ta bata wani Leda nan suka tafi.


Direct Gidan Kakan nin su suka tafi nan ma Sai ganin Husy ake yar dangi kakarta kuwa harda kuka tamkar ta Maidata ciki sai wajen 12 suka dau Hanyar Birnin 

Tarayyya,hansai ta kunshe kai tana kukan tuno su Malam da Inna Jummai.


Muje Zuwa Dai


By

Queen Meemi👑

Queenmeemi.WordPress.com.




.

[4:33pm, 28/02/2017] 👑Meemi💋: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣41❣                    



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_

      

       

*Wan Nan page din naku ne Aneesa rimi (Anee)  Swt Anty Maijidda & Fatyma Nagode da kaunar Da kuke ma book nawa Oneluv❤*





 ********


Tafiya akace yankin azaba hakan su Husy suka yi tayi har suka je Abuja direct Osokoro sukayi ainihin Gidan su Wani Babban Gida suka dosa Hon sukai Maigadi ya wangale gate Nan Motocin suka shiga da gudu mai bawa Fulawowi Ruwa ya bud'e Musu "Barka da dawowa Oga" Dady yace "yawwa."


Su Hassy ma duk suka fito Husy tasbihi tayi Azuciyarta domin ganin Gidan tamkar ya fad'o kansu saboda Girma da kyau tamkar da kwali akayishi,duk haduwar Gidan su Sady sai taga yazama Mara kyau akan wan nan ,Lalle kafi wani wani yafika.


"Twinny  tawo mana!" sai Lokacin ta dawo da kanta kansu Arif yace "idi kaga Husainar Hassy" zaro Ido yayi "haba ikon Allah ko itace wadda ta bace ko?"


Arif yace "yeah"


Nan Maigadi ma ya tawo yace "ikon Allah gashi kuma kamar su d'aya" nan suka yiwa Mum da Dady barka suka koma.


D'uruwa sukayi cikin Gidan  Husy ta kuma sandarewa domin falon ma kamar ba a Nigeria ba, Matatta kalar bene 2 ne a falon Wanda kowanne da Decoration din sa Dady da Mum sukai d'aya su Suhaima kuma sukayi d'ayan Husy ta bisu a baya suka hau, nan taga d'akuna Ajere Guda Hudu a gefen kowane d'aki Flower ce Masu kyau Jikin bangon kuma wasa Frames ne masu kyau, can gefe kuma Dan karamar Dining table ne me kyau Black me kujeru 3 nan Arif ya shige nasa D'akin, haka Suhaima Har ta shiga ta fito.


 "Sis Husy Bari na nuna miki d'akin ki don tun jiya Dady yayi waya aka shirya Miki shi."


Nan suka shiga bud'e baki tayi don duk haduwar d'akunan su Sady wan nan ya zarce nasu (sawun giwa ya zarje na Rak'umi ) wani gado ne Purple madai-daici da Cover da Mudubi Fentin d'akin ma purple ga Decoration masu kyau. Nan Hassy tace "nikam tare da Husy zamuna kwana ki dawo dakina kawai."



Husy tace "Nima dai Nafison mu kwana  mu 2"



 Suhaima tace ai gadon daya ne can sai de  akoma da komai naki can." Mum ce ta lek'o My husy d'akin yayi maki ko a canja?"



Tace "Aa  Mum yayi" Hassy tace "Mum so Muke akomar da komai nata d'akina na munfi son mu biyu."


 Tace "Okey ba damuwa tunda dama d'akin nada Girma zai cinye."


D'akin Suhaima suka shiga Mum ta kira masu had'a Funiture waya yace nan da awa d'aya zai zo.



Husy sai kallon D'akin Suhaima take ko ina Hoton Suhaiman ne  Lik'e a bango Gaban Mirrow kwa kayan Makeup ne turmus  nan duk suka zube a gadon ta Suna hira.


Wajen kamar k'arfe 6 ya zo su 2 kamar injina suka Fidda kayan dakin zuwa dakin Hassy suka jera yayi kyau na Hassy Pink nata Purple 7 suka gama suka tafi.


Nan suka koma dakin  Hassy tace "wow yanzu ma yafi kyau" husy kam Godia take ga Allah kan Niemar da yayi mata, nan sukayi Sallah tare da wanka Hassy ta bude wardrobe d'in Husy gefe abaya ne da Pakistan sai Atamph da shaadda su Materials wanda ba d'inkakku ba, ga takalma da Jaka nan duk suka fito da Jakunkunan da takalmin suka kai su Mazauni .


Hassy tace "Twieeny yanzu Gobe sai muje akai din.kunanki" husy tace "ok sis.


 Arif ya shigo "food is Ready."


 Garam ya koma.


Dariya suka saka dukan su suka fita, Suhaima ma ta fito "hi sisters."

Sukace "ya gajiyar  tafiya sis?"

Tafe "fine"


 Itama tayi wankanta nan suka jera suka sauka k'asa.


K'amshin Girki ne ya doshi hancinsu sai lokacin Husy ta kalle Falon tas iya had'uwa ya had'u tv 2 ce aciki sai Aiki suke ga wani Gabjejen hoto na Art work  Dady ne da Mum sai Suhamina Hassy da Arif akasa sunyi bala'in kyau me Art d'in ya iya. Murmushi Husy tayi suna Lura da ita Dady yace "Lovely Douter kema za 'a yi maki za'a dauke wan nan Ayi sabo wanda hardake."


Dariya tayi tace "Ngd Dady" Suna tacin abincin su har suka gama Dady yayi Gyaran Murya "Godia ta tabbata ga Allah Wanda ya k'addara Rabuwar da gudan Jinin mu gashi kuma ta dawo to ku zama Tsintsiya Mad'aurin ku d'aya ku zama Masu san Junanku da Girmama Juna kai Arif Banda raini ku kuma ku soshi Banda Wulakanta Mutane."


Mum tace "ai yaran nawa sai san barka Musammn Husyna."


Dady yace "Husaina ya batun karatu kinyi Secondry ne?"


Tace "eh Dady nayi  acab Anan Abuja na karasa." 

Au kinyi Zaman Abujan nan?"

 "Eh Dady nayi Aiki Gidan Antyn Maman kano"

 Nan yace Rabia Matar  Alhaji tanko?"


 Yace "eh."

 yace "ikon Allah."


Mum tace "Allah Sarki 'yata Husaina, d'an bamu Labarin Rayuwar ki."


 Husy  ta sunkwi dakai kamar zatayi kuka nan ta fara basu Labarin tun bud'e idonta a Mangalu har yau.


Kuka Suhaima da Hassy keyi na tausayawa Rayuwr Husy idanuwan Mum yayi tana matsar hawaye hakan idanuwan Dady ma yayi ja.


Hassy tace sis Duk da  *RABUWA CE SANADIN* shiga Hali wannan dalilin ne yasa duk kika shiga wancen wahalar, da ace kina tare damu dabaki shiga haka ba."


Dady yace "Hassana karki d'auka Rabuwa damu ne yasa haka! to Daga Allah ne shiya tsara  hakan don Gwada imanin mu da ita Husaina Dana wanda suka riketan, koda tana gaban mu ma hakan sai ta iya faruwa, wani abun shine Sanadin wani dama ita Rayuwa yau bak'i gobe fari,kin gane?"


Tace "eh Dady"


Suhaima tace "Nikam wan Nan Gwamma ke ban haushi wlh Muguwa ai gashi nan taga k'arshen Mugunta,kuma hakan ma bataga komai ba."


Arif yace "ni kuma su Sumy da Sady ke ban haushi Mugwaye don tayi aiki Gidan su."


Hassy tace "hmm Tweeny da tuni fa kina da Aure da Muntari."


Husy  batace komai ba sai sunkwi dakai tayi jin gabanta ya Fadi


Suhaima tace "Aikuwa Su Sady sai na Raina musu hankali."


Arif yace "Amma wan nan Lawandin Mugu ne Allah ya kareki, wai Shi wan nan bad Mudi din shine harda wani wulak'antaki wai yafi k'arfin ki,Arif yace kece Ma ai kika fi k'arfin sa." Arif ya sunkuyar dakai cike da Haushi.


Hassy tace "nikam wlh duk nafi tsanar Gwamma."


Suhaima tace "Baba da Inna kuwa Muna k'aunar su sun so Jininmu."


Dady ne yace "ya isa hakan komai yawuce kud'au komai k'addara kuma duk wani Mugu k'arshen sa baya kyau."


Mum tace "hakane Ku manta da komai" ta kalli Husy "sannu Husaina Allah yayi maki Albarka da dukkan ku" suka ce "Amin."


Dady yace "yanzu kan karatun Husaina zan samar mata."

Mum tace saura fa 3 Month mu koma London!ko Anan zatayi?"


Dady yace "Aa"  acan d'in nake nufi" tace "maddala."


Sai wajen 10 kowa ya koma side din sa,da tunanin Labarin Hansai (Husy)




*Washegari* 


Suka mike Sukayi wanka Husy ta sauka kasa ta shiga kitchen Mum ce tsaye tana yiwa Dady Farfesu nan Husy ta gaisheta ta hau taya ta don karasa breakfast.


Mum tace "Husy Kin ganni  nan banida masu dafa Abinci nike Yima Dady."


 Husy tace "Yawwa Mum ki kawo ina mana"

 Mum tace "haba ai Dalilin daya sa ban d'au yan Aiki Masu Girki ba kenan Saboda su Suhaima su koya, kinga mu ba Mazauna bane shiisa ma ban d'auka ba sai Mai goge-goge kawai kullum tare da Suhaima Da hSsy Muke Hada breakfast."


Husy tace "Mum Tunda Gani Yanzu kawai koba zamanki muna yi kawai."


Mum tace "Yayi kyau douter."


Suhaima ce da Hassy  suna suka shiga Suna kirchen din Nan suka saka hannu sunayi suka gama aka kai Dining sukaje suna breakfast.


Wajen 10 suka mike kowacce suka sake wanka suka fesa Makeup,Mum sai kallinsu take Musammn Husy tana godewa Allah.


 Falon Dady duk sukaje Arif Na danna computer Suhaima tace zasu Kai dinkin Husy kuma zasuyi Mata shopin .


Nan yace Suhaima ta tuka  bai san tukin Motar Hassy  saboda tana da Tsoro,sai nan da 1 yr kin dada k'warewa"


 Dariya Arif Yasa "Dady wallahi koni na fita iyawa" 


Harara ta kaimai "Oho dai Mr No kawai."


Dady yace Hussaina ma Zan kawo Motar ta Sai afara koya mata"


 Kudi ya zaro ya basu yace  "kuje ku taya Husaina shopin" jin Hakan Arif Ma ya Bisu Nan Suka Lodu a Benz din Suhaima ta kwashe su Gwanin sha'awa,Kyawawa dasu.



Haka sukaje Shoprite suka jido Mata kaya san Ransu suka biya ta gun tailor dinsu Suka jidemai kaya kan Suna san yayi masu express ya gaya masu kudi suka bada deposit,suka biya suka sha icecream san nan suka koma Gida agajiye wajen 1.



Kowanenn su yayi sallah sai bacci Husy kuwa Sabuwar Wayarta ta Kurawa Ido wayar data ke ganin ta hanun su Sady Ashe itama da Raban ta riketa.Murmushi tayi har Wushiryar ta ta fito ta kwanta kan Luntsuman Gadon ta,nan ta kira Inna dama ta bata wayarta sanda zasu tawo.


Daga can ta dauka nan Husy ta fasa kuka "inna Jummai"

 Tace "Allah sarki munyi kewarki Husaina"

 Tace "ina baba?"

 Jummai tace "ya fita?" tace "Dan Jummai fa"

 Tace "yana Allo kullum sayya yi kewarki"sun dade suna Waya san nan ta kashe.


Gadon Hassy ta kalla taga sai kwasar bacci take nan itama Batasan sanda ya d'auketa ba cike da farin ciki.




By

Queen Meemi👑

Queenmeemi.WordPress.com.



.

[11:00pm, 01/03/2017] 👑Meemi💋: . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣42❣                    



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


      

*Ban manta kuba wan nan page naku ne@ Maryam Oumiey,Juwairiyya, Ummen Yusra & Aysha Maman Umayma❤*



*********



 Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta wurin Hussy domin Rayuwa take cikin 'yan uwanta cike da 'yanci da walwala Uwa uba soyayya gaya ake nuna Mata sosai. ko tari tayi sai suce meye sis, ko meye Douter wan nan sakewar yasa Husy ta fito ta kara kyau fatar ta tayi kyau hatta gashin ta yasan ta samu canji shima ya dada kyau haka ta sake tsakanin su ta ware dasu komai nasu iri daya ita da Hassy abin sha'awa.


 Ganin tana son computer Dady ya d'auko wani ya koya mata nan ya sai mata laptop kirar Apple Already dama su suhaima nada ita ga dalleliyar Motar ta mekyau Red cikin 2 weeks ta iya Rayuwa kenan.



Yau Dady ya sanar ma Mum gobe zasu d'aga Landon don Hutun su Arif ya k'are shida Hassy, dake Yniversty acan dama ita Suhaima ta gama.


Nan suka hau shiri wajen 1 sai ga driver Anty nan yazo zo kuga Murna gun Husy Rungume Anty tayi tareda yaranta.


Anty tace "lalle Hansai!" Husy tace Anty "ai wan nan Old name ne"dariya Anty tasa tace "wlh naji dadi Husy tace wlh Anty nayi missn naku tace ai dole.


Nan Hassy ma tazo suka gaisa dasu Arif suhaima ce bata nan ta tafi saloon.


Hassy tace "Yawwa Anty karki gayawa su Sadyn nan Husy yar uwarki ce ki barsu kawai zami basu Suprise" tace to ba Masala hakan sukayi ta hira har Dady ya dawo suka gaisa sai dare Anty ta koma gida.



*Washegari*


Da Asuba kowa ya gama shirin sa k'arfe 9 duk sun gama komai shi duk sun kulle Gidan Sukai sallama da Maigadi Suka d'uru A Family Motor Driver yaja suka tafi 10 sunje Abuja International Airport Dady ya Juya baiwa Idi sak'o kan ya je Bunkure ya kaiwa Malam.


Husy taso ace taje sunyi Sallama da Su baba da Inna Amma ganin ba time ta kyale nan jirgi ya d'aga dasu Sararin Samaniya.



*Gidan Alhaji Tanko*


Sumy ce tsaye kan Sady A Runfar wajen aje motoci kuka take sosai sumy tace "haba sis yanzu kan Shi Handsome d'in kike kuka ai wan nan abun kunya ne."


"Sumy kina ganin Na buga mai waya yayi man Wulakanci wai baison mace Mara kamun kai,Wai nadena kiransa."


 Tsaki Sumy tayi "ai sekiyi tayi dama D'an nacinki ne yazo faruq yanzu Dana fito nan Maigadi je gayan na can waje a waje."


"Bazani ba Cuz I hate him" 


Zubaida ce ta shigo da Mota Adaide Lokacin Tayi faka tafito rik'e da Baby boy a hannunta Dan 3month data haifa.

Gano su tayi yasa ta je wajen ta kalli meya sameki Sady?"


Sumy ta gaya Mata ta kalle ta "lalle Sady kina son kiyi Saki na dafe great man irin Faruq ga kyau meye aibun Faruq Kodan kinga Dady na cewa sai masu Naira."


"Hmmm wlh wani Auren me kudin wahala ne azamanin nan ki Auri me sonki da yawa Shi yafi domin wani Namjin wallahi komai kudin babanka sayya taka ka,Naga ishara akaina."


Sady tace "Nifa sis bana sonsa, haba ya k'yaleni kofa Mota baida ita meyaci meya bani,gashi bai iya dressn ba."


ta kalli Sumy ke yanzu bagashi da Nazy kike luv kuma ba kinsan baban sa me Naira ne,ba wlh bazan taso a wadata ba Kuma nakoma talauci"


Zuby tace "Dalla shut up ur Mouth ,ke naki Baban ba mai kudi bane ba, haba wlh Nikam na dawo daga rakiyar wai sai me Naira wallahi ka samu mai sanka shine."


Akwai sirri da ban tab'a gayawa kowa ba wlh kun ganni nan kunsan dai Auren so mukai da Fawwz ko, ina balain sonsa to sai da Mukayi Auren na tabbatar nafi sonsa domin da Gangan yake mini abu yasan son danake mai da wuri zan huce, wataran se mi 3 days muna fushi dole ni zan bashi hkr yana basar dani,himm wlh ina baki shawara ki Auri Wanda ya fi sonki domin Faruq Masoyi ne kusan fa shekara kenan kina mai wulakanci!"


 Sumy da Jikinta yayi sanyi tace Zuby "Nikam na kad'e."


Zuby tace "akan me?"


"Maganar da kika fad'a mana don alal hak'ik'a Madam nasha wahala gun nazi dole na canja salo tumma ba ai auren ba."


Zuby tace "atoh ki zauna kina hauka akansa."


Sumy tace Wlallahi Sady ki rabu da wani Handsome karki ki 2 -0


Tashi tayi a Fukace ta fita Zuby tace Allah ya kyauta "iska na wahalar dame kayan kara." nan suka mike sukayi cikin gida.



*LONDON*


Sun sauka a katafaren Gidan su ma can bayan sun huta yan Nigeria Mazauna Landon sukazo Sunaima Ambassador nasu barka da dawo wa.


Husy tasha kallo bata tab'a zaton zata bar Nigeria ba Lalle ikon Allah yau gata A landon.

Nan ma Husy da Hassy daki daya suke kowa ya kwanta baccinsa na gajiya.



*Washegari*


Bayan sunyi breakfast Arif ya tafi Makarantar su inda yake SS1 Hassy ma ta shirya Driver ya kaita Cumpus na su.


Haka Suhaima ta shirya zata shiga School karb'o wasu Ducument nata Harta fito Mum tace ta tsaya Husy ta rakata saboda kar abarta ita daya Agurguje ta shirya suka fita.


Dady ma ya fita Office sai Mum kad'ai agidan ta kishingida Bacci.


Acan kuwa Suhaima kuwa Cumpus dinsu tayi don ba School Nasu d'aya da Hassy ba ,turawa keta wucwa Wanda suka Santa suna Hi Suhaima Har sukaje office Husy ta tsaya abakim Bishiyaa sai k'ikkifta ido take.

wani siririn Saurayi ne yazo ya tsaya gabanta "Hi Baby".


Ko kallonsa batayi ba,wani abokinsa shima yazo wucewa ya d'aga murya "Bobby come here!"

What Wrong frnd?

"See beauty"  ya nuna mai Husy nan ya matsa kusa da ita Jikinta  sai rawa yake neman kai hannu Jikinta suke Suhaima ta k'araso ta harare su.


Dariya suke suka bar wajen Husy tace "sukuma haka suke dama ance fararen nan 'yan iska ne!"

 Suhaima tace "no koda ba Musulmai bane Amma ko ina akwai na gari dama wad'an nan basu da kirki kin san me sis duk abinda kika ga Namji yayiwa mace ita ta bada dama suma sun sani kuma su Al adarsu ba wani abu bane su rike mace don haka inkin fara zuwa School karki sakarwa kowa fuska tunda Al adunmu da nasu ba daya ba."


Husy tace "Gaskiya ne inasha Allah zan kiyaye."


Bayan ta gama komai taja su suka tafi gida suna komawa suka shiga taya Mum Aikin Girki.


Suna zaune Husy tace "nikam ya inason layi zan kira Nigeria" nan Suhaima ta bud'e wata Jakarta tace "ga wani Empty" ta karb'a tayi Godia don so take ta kira su Baba.


"Ya Suhaima Nikam ban san yayan namu ba" kashe ido daya Suhaima tayi tace "lol bari na bashi ku gaisa."


Nan ta kira domin acan Nigeria kusan dare ne nan ya d'auka tace "my safwan ga Twin din Hassy zaku gaisa"

 yayi mamaki tace mai "ai ta dawo" karba husy tayi.


"Yaa Safwan ina maka barka da dare" yace lafy k'anwata, Inaga sai na biyoku Landon ganin ki" tace "Aa ahakan ma yayi basai kazo ba"

 Suhaima takarb'i wayar  tace "ko na bugo maka ta Imo ka ganta?"

 yace "eh."

Nan ta buga mai ta Imo Lokacin yana zaune kan kujera yana Shan tea Husy tace "ya Suhaima nima zai ganni kamar yanda nake ganin sa?"

Dariya tasa "kai husy yan zuma Ai yana ganin ki"


 karbar wayar tayi Suhaima tasa dariya.


Dak'yar ta bud'e har da Dan sunkwi dakai ta gaidashi yace "Lahhhhh kaiii zankadaziyya ashe k'anwar tamu ta kudi ce."

 Dariya tasa haka sukai ta hira yana kallonta tana kallonsa nan tabawa   Suhaima Suka cigaba.


Bayan ta gama Husy tace "ya Suhaima Allah yasani kunya" tace "haka yakema Hassy ma D'an shaftane."


Husy tai Dariya Wushiryar nan ta fito tace "Amma kundace."

 Suhaima tace Tnks sis, Wai kuma fa so yake asaka Rana."


Husy tace "ai gwanda Musha Biki Dan kallonta Suhaima tayi "lalle sis Kema A ce."


Sai 5pm Hassy ta dawo agajiye.


*Washegari.*


Dady Bayan sun gama break Dady yace Monday husy zata fara zuwa cumpus din su Hassy" tsalle sukayi itada Hassyn cike da murna .



*4:30*


Kowacce tasha Makeup Husy da Hassy sun saka wata Riga da siket ,Rigar  Red ce haka Siket din black sai suka dora Top black,sun nad'e kansu da Red d'in Gyale sunyi kyau sosai Manyan takalma suka tsikara.Dak'yar Hussy ke takawa saboda tsinin sa tunda ba sabawa tayi ba sai da Hassy ta koya mata.


Nan Suhaima tasa wata bak'ar Abaya Anyi shape din ta tad'an bazo da gashinta gaba ta na nada Mayafin abayar Akanta gashin yadan fito ,tasa no Respect Glass ta kwashe su suka fita zaga Gari.



Sunje Super Market suka D'an siyo abun Motsa baki end suka je gurin shak'atawa suka Shimfid'a Carpet sai Selfie suke suna Dan ciye- ciye da drink.


*BAYAN WATA DAYA*


Hassy ce ke Zaune a 'yar Runfar Gidan su ta shak'atawa sai Murmushi take ita kad'ai Husy ta d'ago d'aukeda Fruit Salad A cup ta zauna tana sha tana kallon Pictures a instr .d'agowa tayi ta kalli Hassy .


" Tweeny" ta dago "Naam sis."

 Tace "ya naga sai Murmushi kike ke d'aya."


Tace "kin san me sis? wallahi ba abinda yakai so dadi Musammn in ka samu wadda ke sanka kake sansa."


Hussy tace "tabbas" Hassy ta matso Dan gaba tace "bantab'a gaya miki inada Saurayi bako? to ina dashi .


Husy ta tasa dariya "ya Sunansa?" tace sunan Yasir"

  tace "kai yanzu yana Nigeria ne? tace" Nop a Cumpus namu yake Last yr yayi Graduation  yanzu one yr kenan da fara Soyayyarmu farkon shigana School."


Husy tace "Wayyo Amma nayi maki Murna, ki tayani da Addua Allah ya had'amu da Muntari na domin yazama heartbeat dina,Allah yasa ya rike Amanata duk da rabamu akayi tayiwu yayi aurema.


Share Hawaye tayi Hassy ta taso ta Rungumeta ta baya.

 tace "ai insha Allahu zaku had'u Ameen" 


Haka rayuwa take gudana ga wad'annan Family' kowa nasan Dan uwansa fans in kunga Hansai to sai kun tsaya kun sake kallonta tamkar wadda akaiwa wankan inji ta kile ta sake wayewa ga kwalliya su Hassy duk sun koya mata tun sanda ta fara shiga school.........



*fans Caji yayi tsiyar ya kare banzo inda nake san tsayawa ba Amma dai ku biyo ni.*



By

Queen meemi

Queenmeemi.worldpress.com.




.

[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣43❣                                                *FEB,2017*



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_

      

       

_*Wan nan Page naku ne dukkan 'yan NAGARTA WRITERS ASSOCIASION onluv❤*_





*********


Bayan wata Uku da fara zuwan Husy School Aka saka Ranar Suhaima Nanda 3 Month Lokacin su Husy sunyi hutu Alokacin zasu tafi Nigerian don gudanar wa Murna gun su Hassy ba Magana Sai shiri suke abinda Hankali kwance.



Husy da Hassy ke zaune a Garden na School suna karatu Wayar Hassy tayi K'ara ta d'aga Ganin Sunan Yasir yasa ta d'aga da wuri "haba kazo Landon ne."


"Ok sai kazo."


Juyowa tayi ta kalli Husy "kinsan me? Husy ta dago "Aa" tace "to Yasir yazo tun jiya Yanzu zai zo ya ganni kinga dama kina son ganin sa."


Husy tace "ai kuwa domin hirar sa Harta isheni Hassy tace yau kwa zaki Ganshi wallahi Mundace."


Bayan kamar 1 hour Kiran sa ya K'ara shigowa "Yawwa kazo?" yace "eh" 


Nan tayi mai kwatance da suna Garden, direct yasan wajen dama ya tawo Hassy harda d'an Goga Powder Shigowa yayi Garden d'in daga can ta gano Shi ta tashi tana Murmushi.


Yana Jingine kusa da Wata bishiya sumar nan tasha k'yalli yasa tshrt black da farin wando sai agogo fari da shoe black wani d'igon sonsa ne ya motsa Mata sallama tayi ya juyo suka yiwa juna Murmushi yace "I Mssd u dear na" tace "me too."


"Oh ina Tweeny namu ne inason mugaisa" ya tambaya, tace "woo ai itama kai take son gani tare muke tana can zaune."


Anutsue suka jero Husy kanta na sunkuye tana karatu ,har sukazo inda take hassy tace "Tweeny ga yasir."


Dago kai tayi Eyes nasu suka had'u a razane ta kafa mai ido shima sakin baki yayi yana kallonta  kallon Hassy tace "dama shine yasir din?" Hassy tace "eh kun san juna ne?" Husy tace "no"


Da kyar ya bude baki yace "Amma kunyi kama" kirjinsa ne yaji yana bugawa sabili da jin wani irin Abu tabbas yasan Hansai din sa ce Mamaki ne ya isheshi taya haka ta faru bayan Malam yace Aure za amata, Jiiyayi kamar ya cire kansa saboda zafi da yayi .


Husy kuwa Hawaye ke neman zubowa tayi saurin tare su,  ba yabo ba fallasa ta gaidashi, tace "Tweeny bari na tafi Ana jirana zami Lucture in kun gama kimin waya sai na fito mu tafi."


Binta yayi da ido cike da Razana akan face nasa.


Bayan class taje ta tsaya sai kuka take harda d'ora hannu aka tana kuka "wayyo ashe Tweeny Muktar ne saurayin nata" can Wata zuciyar tace Mata kefa wan nan sunan sa yasir nan taji hankalinta ya kwanta kanta har ciwo ya fara ta fito ta ta shiga class. 


Sai wajen 3 ta fito Lokacin Hassy na jiranta suka tafi.


***********


Yau kwana 2 kenan sa had'uwar su ya kasa Sukuni domin tabbas yasan Hansai ce yana Mamakin meya kawota Landon kuma yaji Hassy na cemata sis dinta to dama Hansai ba yar can bace duk wan nan tambayoyin ya rasa amsarsu.


Duka gwiwowinsa yayi ya dau phone dinsa yana tunanin wazai kira a Nigeria,k'anin sa ne ya fad'o mai da yake shima yana Secondary yanzu yasan yana da waya kuma yana Aiki.


Nan ya buga mai yace "wai ni na tambayeka? ya Labarin Hansai ta Gidan Malm tsohuwar budurwata da aka fasa auren mu ? Tana ina ne wai?"


Daga can Musa yace "ai yaya kwanakin baya naji Labarin anga iyayenta har Sun tafi da ita abuja ashe ba yar gidan bace" Dam! gaban Muntari ya fadi.


Yace "ok ba matsala" kwanciya yayi a kan gadon sa ,yana dafe kirji kansa duk ya daure


Husy kuwa kwana biyu duk tayi suk'uk'u zuciyar ta takasa sukuni zuciyar ta na gaya Mata shine domin tabbas ko da cikin duhu zata nuna Shi duk da yayi D'an kiba da tsawo Amma kuma taga sunan sa yasir .


Tana zaune tana Latsa waya cike da k'unar rai Hassy tashigo "Tweny na" ta zauna "yanzu muka gama waya da yasir baijin dadi gaban husy ne ya fadi  tace "eyya Allah sarki" "wallah hussy duk na damu Domin Soyayyr dana kewa Yasir daban ce domin shima yana sona sosai saboda yasha gayan wai ina kama da wata first lov dinsa shiisaa yake balain sona.


Husy tai dariyar takaici domin wan nan Maganar ta sa ta dad'a tabbatarwa shin Amma kuma dole taji daga bakinsa tace "haba Tweeny yanzu bakya kishin saboda kamar ku daya da wata yake sonki?"


Hassy tace kai Tweeny to meye ai dama badole sai ya dade da itaba."


Suhaima kam duk ta zama busy sai shirin yanda zata gudanar da bikin ta take suna zaune kan kujeru dake kewaye a falon Mum na kallon wani film .


Husy ta shigo da Gudu ta fad'a kan Mum tana kuka hankalin Mum ya tashi tace "meya faru?" kuka take na fitar hankali tace "wai ke meye? tace Mama su baba nake missn Dariya Mum tayi kai Husy shagwab'a.


Tace "karki damu ai saura wata biyu bikin yayarku kinga Idan muka rankaya can sai ki je bayan gama biki."


Husy ta kwanta jikinta tana maida zuciya domin son Mukhtar ne ke dawainiya da ita ga kuma yanda Hassy ke san sa tabbsa tasan da matsala.


Suhaima ce ta shigo da Album "mum kinga irin kayan nan nakeso" Mum tace "kai suhaima ba kunya agabana" sunkwi dakai tayi "yi hkr mum" .


Dariya tayi bakmi ai gwanda ki zabi irin kayan da kikeso" ,Arif ya shigo yana neman Hassy Mum tace tana bedroom bacci.


*BAYAN SATI D'AYA*


Husy ce zaune a Garden din da ta Saba karatu domin yau Hassy bata da lucture Ganin Mutum tayi agabanta ta d'ago.

Muktar ne ya zauna daya kujerar kauda kai tayi .


Yace Hansai ashe zanganki a Rayuwa? 

Kallonsa tayi kawai sai ya koma Mata Muntari k'auye kuka tasa harda shashsheka sai datai mai isarta.

 Muktar yace kiyi hkr idon sa shima yayi jan "abubuwa Sun faru.Muktar tayaya kasan ja suna? kuma yaushe har ka manta dani ka fara soyayya ni ina ta Dakon son ka!"


"Am so sorry Husaina"


 Bayan Rabuwar mu kinsan dai kano na koma gidan kanin Hajiya to anan na zauna nafara sana'a sosai daya yana  legs yace zai  mani cuku cuku don cigaba da karatu"


"Dalilin Sanja suna na kuma shine:

Hatsari ya faru dani da Dan Alhaji mai suna yasir Lokacin zamu wani gwaji da za ai mana duk credentials D'ina da nasa na tare to nawa yana hannu na nasa na jaka, Munyi hatsari sai Allah yayi mai Rasuwa saboda motar ta kone ni kuma fad'owa nayi Asume waje.


To abinciken Motar ne sai aka gano takardunsa a jaka Allah yasa bata kone ba. komai nawa ya kone to wan nan dalilin ne yasa kikaga na canja suna Sabili da duk da komai nasa Alhaji yayi Mani cuku- cuku na samu Scholarship na tawo nan karatu shine nake amfani da sunan yasir anan."


To karshen shekarar da zan gama ne muka had'u da Hassy ita lokacin Zata shugo ,nayi Mamakin ganinta irin kamar da kuke da ita komai naku iri d'aya yananyi dukka sai de abinda dai bambancin kadan  ita yar Birni ke k'auye."


"Soyayyr da nake miki ce ta darsu naji ina son ta.


Ban kulataba har saida na koma hutu Nigeria Naje Bunkure har gun Malam naje na tamaye ki yace ai an kaiki aiki kuma ma Aure za'amiki da jin hakan nasan Malam be manta abinda akai maki ba,haka nai jinyar Rashin ki na hkr"


"Wan nan Dalilin ne yasa na hkr ,Amma Still kina Raina domin True Love Never end.

Ganin kamar kun yasa nace  inason  Hassyy saboda ganin ta nake tamkar ke."


Kiyi hkr Amma wlh kece Araina  domin ance kama da wane ba wanen back.kuma ganin ki yanzu yasa Soyayyrki ta dada ninka da naji bazan iya ba."


Kuka Husy keyi sosai domin tasan tabbas bai da Lefi kallonsa tayi cike da k'auna tace "kayi hkr Tweeny blood Dina ce abinda take so ina son sa don haka na barka da ita kucigaba."


Domin bazanso abinda zai shiga tsakanin mu ba Muktar yau na tabbatr Rabuwarmu itace Sanadin Abubuwa da dama ni gashi na samu iyaye na ta hakan ma na  samu ilimi.


Juyowa yayi burinmu ya cika husy saura Daya domin bazan iya rabuwa dake ba"

Ya zakayi da Tweeny to kasan hakan bazata sabuba?

 kansa ne yaji ya d'au zafi ji yayi bashida mafuta.

 Sallama yayi mata ya tashi yayi ya tafi.


Tace "OMG! Matsala tabbas ta tunkaro ni,domin tasan yanda Hassy ta mato kan Muktar.

 



By 


Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.


.

[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣44❣                      *FEB,2017*



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_

      



*NWA*



*Nagode Waheeda da kulawa Allah yabar zumunci👍*


***********


Tunda abun ya faru Husy ta shiga neman yanda zata Manta Muntari sai de hakan ya faskara daurewa kawai takeyi.


B'angaren Muktar kuwa har wani Dan rama yakeyi saboda rad'ad'in da zuciyarsa ke ciki domin koda Hassy ta buga mai waya bai dauka aganin sa yanzu ya zama dole ya yakice ta. 

Ammawata zuciyar na tunatar dashi inyayi hakan kamar zata ha yaudarar ta yayi.



Yauma d suke zaune suna hira ad'akin su Hassy tace kin san me sis? na rasa mai yasa yanzu Muktar yake shareni"

 Hussy taji gabanta ya fad'i tace 'kiyi hkr tayiwu ko yana Busy Hassy tace Allah dai yasa."



Tunani hussy ta hauyi tabbas dole na San yanda zan don bazan so sis taji ba nan tad'au wani layi ta saka ta awayarta ta d'au Number din sa a wayar Hassy Direct tayi mai text Msg kamar haka:


_"Muktar ka manta dani saboda hakan Allah ya kaddaro akanmu balalle sai mun zauna inuwa daya ba wato aure, kadaina wulak'nta sis Dina plss ,kuma karka bari tasan mun tab'a soyayya karka nuna mata kaine muntari na idan ma ta sani to sai kun aure ,ka kyaleni kawai dama ba komai Mutum keso ya samu ba ,Matar Mutum kabarinsa wani baya Auren matar wani Bye"_


Yana gaban Computer yana wani project sak'on ya shiga nan ya d'auka ya karanta ji yayi kansa na bugawa ya daki Bench na gaban sa .


"Tabbbas kece farin cikina bazan iya babu keba Amma zan d'au shawarar ki na daina kin d'aukan wayar Hassy Amma ki sani ke tawace"Shi kad'ai yake Maganar kamar da wani.


Ita kuwa tana gama tura.Msg din ta cire Layin ta Maida nata,da Gudu Hassy ta shiga "Tweeny!"

zo kika wani d'anyan Material da Dady ya sai mana" nan ta nuna Mata "wow Amma sunyi kyau",Suhaima da Arif suka shiga nan suka baje kowa yana fad'ar irin Bikin da za a gudanar.


*Bayan 2 weeks*


 Su Hassy Exams suka fara tukuru haka Hussy ma  ta bangaren Hassy kuwa hankalinta yad'an kwanta ganin Mukhtar na kiranta yanzu,damma ya koma Nigeria domin fara shiga office Aikin daya nema ya samu.



Yau suka Gama Exams dukkansu cike da samun nasara,nan fa suka fara shirin tafiya inda suke ta siyo lates kaya Wanda zasu ci biki dasu, Ranar Asabar itace ranar da suka d'aga kasarmu ta Gado wato Nigeria.


Sun sauka Abuja da misalin 6 na yamma Mota 2 ke jiran isowar su suka kwashe su suka je gida Agajiye duk suka zube don Gajiya.


**********


Yau saura Sati biyu Bikin Suhaima, dinki kawai suke kaiwa Ana musu tsaddadu abinka da yaran manya.


Ganin da sauran sati hakan yasa Hassy ta damu zata Bunkure .

Dady shida Mum na zaune a falonsa suna hira ta shiga ta gaidasu Ta zauna Dady yace "Douter da Magana abakin ki" tace Dady ina son zuwa Bunkure ne?" Mum tayi dariya "ai tun a Landon harda su kuka zata" yace "ki shirya gobe Idi ya kai ku keda Arif."


 Hassy kuma zata taya Suhaima rabon kati ,kema sati d'aya zakuyi ku dawo saboda Biki."


Dad'i ne ya kamata nan ta sanar da Arif yace ba Matsala Amma Shi ba sosai yake son zuwa k'auye ba harara ta kaimai ,"dole kaje yaro."


*Wshegari*


Hussy ita da Arif Idi driver ya tafiwkaisu da tsaraba Jingim musalin k'arfe 5 suna Bunkure.



Tun shigar su garin sai kalle kalle take ganjn wani gun ya canja sai 5:30 suka k'arasa Mangalu,tsayiwar su ak'ofar Gidan Husy tace Baba idi ka manta Gidan ne? yace "Aa nan ne ai" Mamaki k'arara afuskarta ganin yanda gidan ya koma Ginin bulo yaci fenti.


Abdallah ne zai shiga gida tace Dan jummai Juyowa yayi shikam bai gane ta ba Arif ma ya fito suka shiga gidan.


Nan ma taga yasha gyara dakuna Shima harda tile an canja tsarinsa, Jummai ta fito itama har dan kiba tayi "wa nake gani kamar husaina?"

 Tace "nice inna" zama tayi tace "naga gida ya canja?"


 Inna tace "kedai bari Dadynki ne da wan nan Aiki wlh ai sede godia domin Malam ma yana cikin gari kantin kayan Masarufi yake siyar wa."

Husy saboda dad'i harda kuka.


Inna ta kalli Arif "Dan lukuti ba magana kayi shiru" Murmushi yayi ya gaida ta.nan ta bud'e ciki da rumfa ne da malam nan aka budewa Arif Rumfar ya shiga.


Tsaraba husy ta fito da ita duk ta warewa kowa nasa "gana Baba wai yana ina?" Jummai tace "ai Malam sai 7 zaki gansa."


Gidan aka shigo aguje Dije ce ke rusar kuka tace ku taimaka Mama zata mutu."


Sam bata gane Hansai ba ganin kamar an canja ta inna tace "to Husaina Dan jeki ni kinga ba damar fita tunda Malam baya nan." bin Dije tayi tana tafiya Anutse  Suka shiga Gidan, d'akin Gwamma sai tashi yake k'afar da aka Guntule ke ciwo Sai kuka take ga iya agefe suka shiga.


Jin k'amshin turaren Husy yasa suka d'ago dafe k'irji Gwamma tayi "wa nake gani kamar Hansai!"


Tace "nice"

 kuka Gwamma ta fara "don Allah kiyi hkr kan abubuwan Danai miki, nasan na zalunceki gashi nan ina Girba yau wata biyu kenan k'afata ke ciwo har Ruwa take futar wa, ga bak'in cikin Mudi se yayi wata baya lek'oni, Ga Dije ko Samari Sun Dena zuwa gunta kowa bai sonta, saboda rashin tarbiya da fada da Maza,don Allah ki yafeni domin naga izina ba irin gorin Aure da ban maki ba, gashi na ga ishara ga 'yata domin ita akwai Wanda ma ya kusa yi mata Fyad'e irin Mazan da takewa rashin kunya koda bai Matan ba ya Cuceta dalilin da yasa kenan ba mai zuwa Gunta kowa cewa yake ta gama lalacewa. Malam yace bashi ba ita, Nasan nice sila domin ni na b'ata taribyar su, dama ance kak'i naka Duniya taso shi Hakan ka soshi Duniya ta kishi."


Iya tace "ke yimana shiru duk wanda yaja ruwa ai shi kan doka."

 Hussy tace "ba komi na yafe" Gwamma tace "yanzu kece kika dawo haka! tamkar Balarabiya.Ashe! ke yar Manya ce."


Hussy tace "yanzu insha Allahu Gobe za a kaiki Asibiti."


Dije kuwa bin Hussy tayi ta Rakata ta dawo tana murnaa.


Husy shigarta kuwa Malam har ya dawo nan yayi Murna sosai da ganin su Arif na gefe yana Latsa waya, haka sukayita hira har ta mai zancen Gwamma yace Shi ba ruwan sa da Gwamma ,Husy tace Baba kaban izini na taimaka Mata" kallonta yayi yana cewa dama 'yar sace ta cikinsa,Amma ahakan ma yana Alfahri da ita matsayin 'ya yace "ba komai 'yata ai Rama Alkhairi ga Macuci."


*Washegari.*


Wajen goma aka taro taxi aka tafi kai Gwamma Asibitin ciikin Garin kano wani k'anin iya ne ya kai ta.kudi Hussy ta ciro a Accnt nata aka kai ta akace sai am Mata aiki a k'afar inda hali ma asaka Mata k'afar Roba.


Da yake duk wata Dady na zuba masu  Hussy kowa dubu d'ari a Acccnt yasa Hussy ta bud'e bakin Accnt nata akai wa Gwamma Aiki aka sa Mata k'afar roba.


Tun daga nan Dije taji tana k'aunar Husy sai hkr take bata kan abubuwan data yi mata tace bakomi, ta bata shawarar zuwa islamiyya Harta bokon ma.



Jummai da Malam sai San barka suke da ita Sam bata duba sharrin da Muguntar da Gwamma tayi Mata ba, gashi ta rama tayi Mata Alkhairi.



(Shiiisa akeso ka rik'e Mutum tsakani da Allah Musamm irin Matan dake rike D'an kishiya suna Musguna mai kod'an ruko, 'ya'yansu sune 'ya'ya to bakasan wa zaka Mora ba ba Lalle ka mori d'an cikin ka ba ,sai dai ka Mori na wasu, shiisa akeso ka Maida D'an wani na naka, Domin Masu iya magana nacewa D'A NA KOWA NE  Allah yasa agane)




*Ina busy ne fans ga Wan nan ba yawa.*



By


Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.





.

[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣45❣                    *FEB,2017*



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_

      

       

_*Wan Nan page din naki ne Surayya ngd da kaunarki agareni ngd sosai nima ina kaunarki ngd da support❤*_



*********



Yau suka shiga sati a Mangalu nan suka had'a inasu inasu sukayi Abuja.


Tunda suka koma basa zama kullum suna kai d'inki da  rabon kati kuwa duk Sun gama inda sukaje aka fara Gyaran Jiki ,ba Amarya ba hatta Husy da Hassy an musu Amma kwana biyu Sun fito kamar taurari Amarya kuwa kullum na kunshe Ana Gyara ta .


Wasu frnd nata su 2 suka zo suna tayata don su yauta Mata,Mum kuwa wasu k'annenta su 2 daga Adamawa sukazo  sauran Dangi duk sai ran laraba zasu zo ,Ga Anty Rabia ita kullum tana gidan don gudarwa abubuwan tunda su basu da yawa.


Gidan su Ango ma ba abarsu abaya ba, shiri suke sosai Dady ma shiri yake su Masu mutane komai atsare ake ma'aikata ne aka d'auko duk wani Prepartion su ke gudanar wa .


Hassy kwa koyaushe suna mak'ale a waya da Muktar kullum Maganar sa d'aya abasa Husy su gaisa shima yayi Alk'awarin zuwa.



******


Yau data kama Ranar Alhamis aka fara Gudanar da Kamu da Walima wajen k'arfe hudu da rabi aka kwashe su zo kuga kyanda Amarya tayi.

 Tayi shigar Golden Colour  abinka da me kyau sai ita da kayan suka haska Juna ga k'wararriyar me Makeup ta tsantara Mata .Ango ma shigar Light golden shadda yayi.


Su hussy kuwa shigar wani Black nd Red Less sukayi sunyi buba da zani  Sun dora zanin kan Rigar Sun balain kyau Me Makeup ta matso masu kyan su ,haka Arif ma yayi shigar sa black nd Red shadda combination yayi kyau shida yaran kanen Mum nan aka kwashe su.


Fati Niger ce ta wak'e su ko ina sai san barka Musammmn su hussy duk inda suka Gifta sai an kallesu.



Haka aka gudanar aka watse.


*Washegari*


 Ranar Jumaa shine aka gunar da Mothers Event Manyan mata kuwa in banda kece less ,less da Manyan atampopi da Tsaddun Materials ba abinda suke, wan nan na Wace wacccan kowacce ka kalla zabba ne fal ahannun ta matan Ministoci Sanators nd others duk sune gun, wuyan nan yasha english fasion ,Indian, etc duk sunci Gwara Gwarai duk k'awayen Mum ne da 'yan uwanta.


Lokacin da Amarya ta shigo kallo ya koma kanta domin ta had'u ta hade ga Twinss agefen ta sunyi shigar  Ash colour kamar ka sace ka gudu haka, Arif ma yasa Ash colour na shadda da wasu bayan su Frnda din suhaima ne Dana hassy suka rako su.


Husy sai kashe selfie suke da Hassy Musammn da frnds na Suhaima don Sun basu sha'awa.


Mum ke kiran Husy tazo fita Sai idonta ya gano mata Mama da Umma Matan Alhaji tanko suma ita suke kallo Musamm ganin Twins ne .


Umma tace "kai Yarinyar nan tamakar mai Aikin Anty Suna kama dande wannan tafi haske ne da wayewa.Mama tace wlh tun dazu nake kallonta cikin sani.


Murmuahi  Husy tayi ta zata wuce ta sunkuya ta gaaida su  ta wuce don shigo da bak'i.


 Arif kuwa tsakiyar fili ya shiga sai Rawar shoki suke shida frnds nasa nan kallo ya koma kansa sai sakar Musu Lik'i ake Amarya ma ta fito tana mai Liki don ya Birgeta ga Hassy na d'aukansa video, sai da Mum tazo ta fidda shi.


Haka akayi akai ciye-ciye akasha aka watse.




*****

*Washegari*


Ranar Asabar kuma aka gudanar da Dinner kwalliyar yau da akayi masu dukkansu sunyi kyau Amarya tasa Blue Dark tayi balain kyau Gwan din kamar ka dauke saboda tsaruwa an adon Ash ajiki sai walwali take .


Shi kuma Ango yayi shigar Light blue shima yayi kyau.


Su Hassy kuwa shigar wani Materls sukayi Light pink sukayi duka an musu adon Dark pink hakan head nasu  ma, Arif shima yasa Ligh Pic D'anyar shadda anyi mai dede Shi sunyi balain kyau Musammmn husy.


Frnds din Amarya kuma Sun shigar ankon su mai kyau Material Brown sukayi abokan ango kuma sukayi Brown shadda wow sunyi kyau .


K'arfe 7 Manyan motoci suka kwashe su aka kaisu hole da za a gudanar.


Husy ce ke Driving sai Hassy a gaba sai Arif a baya da wasu 'ya'yan yar Anty maza su 2 .


Shigar su Filin hole din Motoci ne Birjik fitilu sai walwali suke ,Big gals ne da had'addun Maza keta shiga,Husy ta tsaida Motar .


Hassy tace "ke kalli can ga wad'ancan 'yan Matan pls ba sune su Sady ba?"


Hussy tace "eh sune" hassy tace wlh nasan Motar nan taki ta tafi dasu kin san fa Motarki tafi tawa kyau ,jibi tasu irin Tsohuwar ta ya Suhaima ce data canja."

 

Husy tace "hmm Tweeny kede ki yishiru ki k'yalesu" Hassy tace "to ai ba Magana zan masu ba kawai ina son kima canja tafiya nasan zasu gane ki." Dariya husy tayi kawai


Arif yayi tsaki "ni ku bud'en plss!" Hassy tace "anki kaji kid'a ka rikice."


Atare suka fita Hassy na yatsina Husy kam kawai fitowa tayi  suka jera.



Sady ta kallli Sumy "ke dama Hassna twnss ne? Sumy tace "ke dalla bakya ganewa wai bama ki ga kamar da suke da Hansai ba?"

 Sady tace "haka kuma fa."


Hassy Sun gifta su tace "Hi" Sady tace "yaran fa Sun Birgeni wai ni,Kinga motar su irinta fa nace Dady ya saimun wai tayi tsada, Sumy duk had'uwar ka kana ganin ka kashe kala in kazo gun biki sai kaji d'ar."


  "Babies din nan na kill me wallahi sun balain kyau",Sumy tace "agidan su fa ake Bikin."

Allah ko ba agidan su ba,nasan Sun kai mak'ura

Ni bama wan nan ba dama twnss ne ?"

Ke ni kije ki tambayesu kindamen zo Mishiga ai Anty tazo sai mu tambaye ta."


 Nan suka kulle Motar suka tafi wata mota ce Black ta danno hancinta cikin farfarjiyar.


Sady tace "ke wlh Handsome ne amotar can wow yau Nazo a sa'a" Sumyn tace "bada kanki dai!"


Janta tayi sai waiwayen sa take ganin ya sako k'afarsa waje alamun zai fito wani dafe k'irji tai "I luv dis Man wallahi" .


Ak'ofar shiga sukaga Hassy na waya Alama kwatance take suka shige.



To fah!




By Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.


[6:21pm, 08/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣46❣                    


*March 2017*




*NWA*



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



 *_Godia marar adadi masoyana masu kirana awaya da text msg sakamakon jina shiru, hakan ya faru ne Wayana samu Matsala amma yanzu komai normal,ngd da soyayyarku gareni Allah yabar zumunci❤❤_*


********


 Anutse yazo ya wuce wani Bugaggen k'amshi ke tashi nan ya shige ciki waje ya tsaru ko ina ka wulga had'ad'd'un Mata ne. Sady tunda ya shiga take kallon sa, aganinta ba ishi aduk Mazan wajen.


MC ne yad'au Lasfik'a ya fara Magana kan Amarya da Ango su fito tsakiyar fili nan suka fito take waje aka hau Ruwan Naira sai takawa suke ganin Handsome ya tashi Danyin Lik'i Sady tayi wuf ta mik'e tana tafiya har taje filin nan ta hau rawa ta gefen sa tana lika sai satar kallon sa take tana sane ta d'an bige Shi ta d'ago "oh Sorry" yace "no Problem" Dadi ne ya kamata ganin yayi Mata Magana sajen sa ne ya tafi da ita bak'i Sid'ik sai shek'i yake komawa yayi ya zauna .

"Shuriem" wani abokin ango ya kira sunan sa.


Waigowa tayi cike da D'an Murmushi akan face nata "wow nyc name" komawa tayi ta zauna ganin Amarya da ango sun koma daga can ta k'ura mai Ido Wanda bai san tanayi ba sai basarwa yake .


"Sumy kinji sunan Handsome kuwa?"


 "To 'yar wahala ya sunan sa?"

 tace Shuriem tab'e baki Sumy tayi dole ki Mato kan Saurayin don k'arshe ya had'u Amma duk had'uwar sa ki kame kanki keda kike mace ce."

Sady tace "oh wa azi zakimin kenan! ko?"

 hmmm tsaki Sumy tayi


Ganin Anty yasa Sady tace "Anty wai waccen Lady ta nuna Husy dama twins ne imean kannen Suhaimaa" dariya Anty tayi "eh mana ba adad'e da ganin ta ba kunsan b'ata tayi."


"Wai ku ce Baku gane ko Wace ba?"

 suka ce "eh"

 tace "tab! to Hansai na ce wadda tayi mani aiki."


Safe kirji sumy tayi "Hansai kuma?!


"Haba Anty wan nan 'yar k'auyen!"

Dariya suka sa itada Sady "gane min hanya."


 Dariya Anty tayi "to wlh Hansai nace now ta koma Husy."


Sady kam kamar Mutum Mutumi ta dawo sai nanatawa take Anty ta kirawo Husy ganin ta tawo suka k'ura Mata ido yanayin tafiyar ta duk sai sukayi kamar sun Raina kansu.


Ta k'araso hatta lafuzzan bakinta ta yanda take furta Magana ya canja tace "Anty Sumy ya kuke.?"


Da in ina suka ce "Lafiya" tace yayi kyau Anty tace ."kun Gasgata ko? sady tace "hmm ni da wushiryar ta na gane" Anty tace "to anan kwa gane D"an Adam ba abin wulak'antawa bane kowane irine bakasan waye shi ba."


Aduniya ma kenan kinga duk abinda kuke tak'ama tana dashi wani ma ya zarce naku to inaga in Lahira idan ka wulk'anta Dan adam kana ganin sa a wulak'ance baka san Darajar da Allah ya yi mai ba to Sai ku Gyara."


Nan ta tafi Sumy tace "kaji Anty da wani abu sai kace wani abu Mukai."


Sady tace tab! gaskiya nayi Mamaki Jibi Hansai ce wai takoma haka wlh Jinai duk na Raina kaina."

Sumy tace "hmm wai har tazo tana sanya kayan da ya zarce namu,koda yake Dadyn Suhaima  fa yafi Dadynmu kud'i."


Haka sukai ta zan tuka da Jin haushi Da hassada. Mc ya kira twns k'annen Amarya da Arif kan suzo su taka yasa suka Mai da hankulansu gun.


Hassy Mazari ta kamo Hannun Husy dak'yar ta mik'e domin kunya take ji tun kan su k'arasa Hassy tace a samusu kujerar tsakar Gida domin tace batta san wan nan Cool Music d'in chasewa zasuyi don tana balain son kujerar tsakar Gida.


Nan Mc yasa Ga police band na buga kid'ansu suma suka tsaya tun ahanya ta fara Rawa har sukaje filin dai deokacin Muktr ya iso Caraf idanuwansa suka sauka kan Hassy da Hussy 


Itakam husy ta kasa Rawar kawai sai D'an takawa take.Shuriem dake zaune nan  yaji Husy ta tafi da Ruhuinsa cuz yana son Mace me kunya Murmushin ta yake kalla ganin sai K'ara kyau take Dan jingina yayi yana kallonta daga nesa.


 Daga can Muktar ita yake kallo,duk gani yayi itada hassyn ba bambanci Amma husy dabance.


Nan Ango da Amarya suka hau musu lik'i da sauran 'yan uwa ahakan ta zare Jiki ta fita ta koma wata kujera can baya ta zauna don jitai kanta na ciwo saboda kid'a.



Tsam ya mike Sady na Kula da motsin sa nan ta kurawa tafiyar sa ido  ganin ya wuce yasa ta juya direct gun husy yayi yaja kujera d'aya ya zauna.Hausawa sukace Abari ya wuce.



Atsorace ta d'ago Manyan idanuwansu suka had'u nan gabansu ya hau fad'uwa Itakam kwarijin yayi Mata da kyawunsa .


Yace "sannu ko" tace "Yawwa."


"Number ki nakeso" 


Gabanta ne ya fad'i tace "no bana bada Number."


Murmushi yayi ya shafa gefan fuskar sa, so pls Bani idan kina da ita ,ni bana takurawa Mutum kan abinda baiso."


Nan kawai tai shahada ta bashi Murmushi yayi yace "tnks" ya mike cike da k'asaita ya tafi.


Duk abinda suke idanunwan Sady na kai yayi Jajawur kamar ta Fashe da kuka ganin ya fita waje inaga tafiya zai  yasa ta mik'e itama ta fita.


Muktar kuwa sai Laluben Husy yake be ganta ba da k'yar ya ganota tana ganin sa ta b'ace don batta so yazo yayi Mata Maganar so Hassy taji.


Can Waje Husy ta fita ta shiga Motar ta ta zauna Sady ce tsaye sai yarfe hannu take domin kan tazo Hansome ya shige Motar sa yabar Gun . Ganin Husy yasa tai waje afusace ta lek'a ta window d'in Motar tace "Lalle Hansai kin kile."


D'agowa tai galala tace  ba sunana Hansai ba kin gane."


Sady haushi ya kamata tace  ai kan Mage ya waye "to wallahi kinga Saurayin nan wlh na wane ba naki ba don haka ki fita harkarsa."


Dariya husy tasa kin san ni sai dai kazo badai na kai kai ba.in banda abinki aibacewa yayi yana sona ba."


Rufen baki maidani gaula ko banga kin bashi no ba!"


Husy batta san fad' a Amma dole ayita kare ta d'ago "Anty Sady idan game ki keso abuga to mu,zuba aga wazai Wining."


"Okey haka kikace ni sady wlh sai na fad'o dake k'asa ko mai de cigaban  Mutum sai dayayi Aiki agidan mu."


Husy tace "badonn k'addara ba ai kin san nafi k'arfin Gidanku,kuma bana bak'in cikin yanda Rayuwa ta ta kasance wai don na samu niema  ayanzu,domin nasan rayuwata agun Allah take",tana gama fadar haka tasa karatun Qur ani Tana ji ta Rufe Ido.


Ido Sady ta k'ura Mata tace "dani kike zan-cen."

 Afusace ta koma hole din tamkar ta fasa ihu Sumy tace "ina kika je? tace "kizo mu tafi plss zan iya fasa ihu  anan."


Tashi tayi suka fita suka zarce mota.



******

Husy na tssye a jikin Motarta Gefe Hassy ce da muktar Harara Hady takai musu Hassy ta yatsine fuska Nan suka shige Motar Sady taja aguje tabar wajen.



Hassy ta Maida kallon ta gunsu Muktar ne ya kurawa Husy Ido Juyowar Hassy yayi saurin kauda kai ,kirrr aka kira wayar Hassy nan tayi cikin hole d'in hakan ya bawa muktar dama yace:



"Yanzu husy ni kike guda? karki manta nine first luv naki wani furzar da iska yayi why Husy??"


D'ago kai tayi "Am so Sorry Mukatar u ar my luv ,kuma kai nakeso kai nake burin Aure tunda kaine first luv dina ,Amma wani abin na kore wani dole na d'au hkr saboda adalilina bazan sa sis Dina a damuwa ba."


"Mun rabu ka fara Soyayya da ita to ganina be dace a ganina kace zaka dawo ba."



Dafe kai yayi ya Jingina da Motar asanyaye karki Manta Soyayyrmu a baya nine Masoyinki na hak'ik'a kodan kinyi sabon Saurayi!"


Hawaye ta share don kawai daurewa take Musammn inta kalli kwayat idonsa tasan tabbas da damuwa tace "na sani bazan iya son kowa bayan kai ba Wanda kake kira Saurayina yau na fara ganin sa."


Muryarsa ce take rawa ganin tana kuka yace plsss karki haramta mana abinda Allah  ya halattta plssss husaina I can do with out you."


"Muktar *RABUWA CE SANADIN" karka manta rabuwan mu ce dukka wan nan da ace bamu rabu ba da tuni muna inuwa daya Amma karka Manta Rabamu akai kan ba ason ka aureni ,haka muka hkr Allah sai ya had'a ka da Hassy komai fa bayin kanmu bane daga Allah ne."



"Shut up  Husaina Wlh dole na Aureki an Rabamu yanzu kuma mun hadu don haka ba gudu ba ja da baya,yana gama fadar haka yayi hanyar Motar sa ya fita.


 Tsugunnawa tayi gun tana ta kuka ganin kiran Hassy yasa ta mike.


Karfe 10 aka tashi kowa ya watse tun komawarta gida taketa kuka domin toilet ta shige tasha kukanta ta k'oshi san nan ta fito.


Bacci k'auracewa idanuwanta yayi kowa sai sharar bacci yake duk 'yan biki sai hasken wayar Hassy dake ta doka tsaki jin hakan yasa Husy tace "Tweeny meye matsala ne? Naga sai tsaki kike"


Tace sis wajen 10 missd call muktar bai d'auka ba na kuma fa ko sallama bai mun gun Dinner ba, na rasa dalili k'arshema sayya kashe wayar."


"Sorry siis Inaga ko bai da caji gobe ai sai ki kiji Dalili ba."


Tace "hakane kuma Good nyt.


Asanyaye Husy ta kwanta tana tunani.


Can b'angaren Handsome Shureim kuwa yana zaune sai buga Murmushi yake shima ya kasa bacci Number din Husy ya d'auko ya gwada kira k'irrr yaji ta shiga jin and'auka ya zauna



B'angaren Mukhtar kuwa kai kawo yake don zafin daya kejia mind nasa Hotunan Husy ne tun na k'auye yake kalla kamar yayi kuka.


Hmmm Sady kuwa kuka take ci kamar me don ta kasa bacci itama adai-dai lokacin ta buga wayar Shureim taji busy nan ta sadakar da Husy yake waya.


Allah Allah take Washegari tayi ta d'au mataki.


To wata sabuwa kenan.

Sunan wani book badakala( Na Kwaiseh Maryama).


Kudai biyoni.



By 

Queen meemi

Queenmeemi.WordPress.com.





.

[4:33pm, 09/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣47❣                    *March ,2017*


             

Sadaukarwa ce Ga Bashir Usman Family's



_*Wan nan page din naki  Zahra Abdullah ngd da soyayyrki agareni❤*_



**********


A sanyaye ta d'au wayar cike da sallama wani sanyi yaji ya ratsa Shi yace "wasslm" Shiru sukayi gaba d'aya, "dawa nake magana" Husy ta fada.

Gyara kwanciya yayi "ur husband mana."


"Toh!"


 Nan yayi dariya "so kina  waya da shuriem,na karb'i number dinki a hannunki dazu gun Dinner."


"Oh na gane" cewar Husy yace "ok finest fatan za a bani masauki" dan dariya tayi batace komai ba.


Muryarsa ke ratsa kwanyar ta tace "ba damuwa zanyi tunani" ,bari na barki idan kinyi tunanin sai ki gayan "uhubbiki finest bye."


Bin wayar tayi da ido wani irin Abu take ji a jikinta nan ta kwanta.


Shuriem kuwa komai na Babyn na Birgeshi ji yayi bazai iya babu itaba komai nata Birgeshi yake dama atsarinsa bai son budurwa mai hayaniya.


*Washegari*


Ranar Asabar aka d'aura Auren Suhaima da Safwan akan sadaki dubu d'ari.

D'aukacin Jamaa suka shaida.


Nan mum ta zarce da yini inda da yamma aka hau shirn kai Amarya tasha nasiha kan zaman Aure kuka sosai su Arif da Hassy suke na shak'uwa.


Husy ma haka duk da ba wani shak'uwa sukayi ba Amma tana son Suhaima su uku suka k'ank'ameta dak'yar aka tafi kaita nan kukan Husy ya zarce da biyu.domin tinowa da Matsalar ta da tayi.



Haka gida ya watse tas kowa ya koma inda ya fito nan gida ya dawo tsit suna ta Missn Suhaima.


Yau kwana sati d'aya kenan da gama Biki Hassy da Hussy na tafiya A mota zasu Gidan Suhaima Shan gaban su akai da sauri Hassy ta taka Birki Sady ce da wata k'awarta suka fito dai de windown da Husy take, ta tsaya "ina dad'ai miki kashedi wallahi bake babu Shuriem kin gane."


Hassy ta cika ta batse "ke Sadiya shiga hankalin ki mu ba sa'anin ki bane kin gane."


 k'awarta tace "See dis gal ke a ido ai kin san mu yayunku ne ko a Girma don haka zamu baku Mamaki" su Sady harda dungure kan Husy.


Fauu kikeji  Hussy ta bawa Sady  Mari Mamaki ta saki Husy tace "kad'an kika gani da da yanzu ba d'ayaba wlh kifita hanya  ta atoh."


Tazo Ramawa Hassy ta rik'e  hannun Sady "be carefull" nan ta ture hannunta.

 taja su suka bar gun.


Sady tace tab! wlh saina rainawa yarinyar nan hankali" K'awar tace "ai Naga sakacinki."


 **********

Zuwa tayi ta aje k'awar agida itama ta koma gida domin bakin cikin abinda su Hassy sukayi mata.

 Faruq ne zaune kusa da Maigadi yana jiranta tayi tsaki kayi ka gama.


Da gudu Maigadi yaje ya tareta Sadiya Ga bak'o can na jiranki" cike da haushi tace "wai bana ce a daina kirana in Wancen abun yazo ba?"

 Ayi hkr yar Dady juyawa tayi kamar ta tashi sama

Bata dad'eba ta dawo nan ta hau  da ruwa a jug tana zuwa ta juye Maj ajiki d'an naci Wanda baida zuciya wallahi ni ba sa' ar  auren ka bace nafi karfin ka ka kalle sama da kasa na wuje ajinka."

zazzagamai Masifa take san ranta tare da bala'i.


Kamar yayi kuka domin yasan shiya kawo kansa kiyi hkr Sady pls ki soni"


 "Wallahi faruq bazan so kaba saboda baka daga cikin Wanda nakeso" hkr yake bata kamar Ana zugata "don Allah ki soni Bani na sa soyayyarki A raina ba plss" tsaki tayi ta koma cikin gida.


Maigadi duk najin abinda tagama yimai yazo ya dafa faruq "kai kuwa kaiwa Allah kaiwa Annabi ka k'yale yarinyar nan ai inde yarinya ta nuna bata sonka ka hkr domin ba Amfani."


Ngd Baba maigadi insha Allahu daga yau bazan K'ara zuwa inda take ba  Amma ni saboda Allah nake santa na rabu da ita insha Allahu"


Yawwa ka sai wa kanka mutunci yaro"

kudi ya zaro ya bawa baba Maigadi ya tafi.


**********

Su kuwa su Hassy suna zuwa gida suka dire a d'aki sai tsaki Hassy take tace "sis wai meya had'aki da wan nan sadyn ko duk tsanar da sukai miki ne?"


"No sis kawai don a Dinner ya Suhaima wani mutum yayi mani Magana har na bashi no D'ina to tun data gani ta dinga yarfan tsiya tun awajen inaga ko sonsa take ne da alama ko bai sonta, shine fa duk wan nan tsiyar."



Hassy tasa Dariya "Lallema wan nan ai sis kawai wan nan hanyar zaki rama kawai ki Amince da Soyayyr Mutumin kodan ki bak'anta Ranta."


Husy tayi tsai zuciyar ta na zugi tace "to sis hakan za ai."


*Bayan Sati 2*


haka Shuriem yake kiran Husy har suka saba domin itakam husy ta danne soyayyr data kewa Muktar domin tasan San sa ajininta ne Amma dole ta koyawa kanta son Shuriem domin in had'uwa ne yafi Muktar nesa ba kusa ba,kuma ganin sanda Hassy take ma Muktar yasa ta saki jiki da Shuriem don ta manta Muktar.



Yau Shureim ya buk'aci yana son zuwa Gidan su Husy kamar wadda laka ya fashewa ajiki domin bata san amsar da zata bashi ba Domin zuciyar ta har lokaci tana a muktar.


5 dai de yana k'ofar Gidan su cikin Motar sa, yayi kiran wayarta d'auka tayi tareda sallama yace "finest nazo fa" tace "okey."


Nan ta Umarci Arif daya bud'e  falon bak'i, pink abaya tasa ta Lining kanta simple Makeup ne  a face nata, nan ta d'auki wayarta tafita gun Mum don ta tambayi izini.



K'amshin Turaren sa  ne ya bugi Jancinta tareda Ya gauraye da AC dakin.


Zama tayi a daya da kujerun suka gai sa D'an dagowa tayi ta kalleshi yau shigar k'anann kaya yayi.


Tsaf yayi Mata kyau dago idunawan sa dake fad'ar Mata dagaba yayi ya dora kan nata caraf suka had'a ido.

Tayi saurin d'aukewa

Murmushi yayi "finest yau dai  inason amsana."


Tana Mamakin yanayin Maganar sa d'ai- d'ai kuma a takaice,ji tayi ya birgeta


"Finest"


Sunan yana Mata Dad'i inya fada yace "plss tell me" 


Murmushi tayi wushiryar ta suka fito tace

"Allah yasa alkairi a tsakanin mu."


Aje cup yayi "Weldone Finest."


Wani kallo yayi Mata take wanda taji ya tafi da ita.


Agogo ya duba "Okey ni zan tafi zan lek'a office d'auko wasu takardu."


Mik'ewa tayi t "Okey"

 yace "yanzu sai yaushe?" tace "sati biyu."


Murmushi yayi yace kina so Ambulance ta d'auke ni ko?"


Dariya ya bata tace "sai Minyi waya."


Ido ya kura Mata wani irin sonta dake ratsa shi badon yaso ba ya tafi.



Koma warta daki taga Hassy na kuka tace "me ya faru.?"

Hassy tace "Mukatr namin wulak'anci yanzu ban san me nayi mai ba yanzu tunda ya koma kano ya shareni."


 Husy taji gabanta ya fad'i wato ni yana yawan kirana Amma ita baya kiranta. tace "Sorry sis kiyi hkr" .


"Haba husy ya zakice hakan wlh ina son sa saida ya koyan so san nan zai gujeni dama maza Mayaudara ne."


Husy tace "karki damu" nan ta tashi ta shige d'aki ta dau phone nata ta tura  Text Msg  kamar haka:


haba Muktar ban cancanci haka daga gareka ba! Mayyasa zakana wulak'anta sis d'ina? Ai yaudara ce wan nan haba, idan danni kake hakan nace ma da matsala"

.


Ganin text d'in ya maida Mata Martani "ke nakeso" kawai ya tura mata.

 Harta cire kayaa Msg ya shigo dafe kay tayi ganin abin da yace,tunani ta keyi yanda zata warware Matsalar Amma ta kasa.




Ku dakaceni fanz ga wan nan ba yawa.




By

Queen meemi.


.

[5:27pm, 10/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣48❣                    


   *March 2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_




 *********


 Bayanda ta iya domin abin yafi k'arfinta ganin Msg d'in sa kamar tayi Kuka itaba k'awa balle ta gayawa Mata ta bata shawara,ba wacce ta fad'o Mata sai Suhaima nan ta d'au phone dinta ta Latso Layin "Hello ya Suhaima?" daga can Suhaima tace "yadai Husyna."


Kuka ta Fashe dashi "Sis ina cikin Matsala Amma Maganar bata waya bace gobe Zanzo muyi Maganar."


"Okey kizo fa da wuri Aamma wan nan kukan ya kamata kidaina","Yawwa sis ngd" sukayi sallana ta kashe ta kwanta.


*Washegari*


Wajen k'arfe 10 na safe Ta Shirya Mum da Dady na break fast Arif da Hassy ma haka.


Mum ta kalleta "Aa Husyna ina zaki haka? ko karya wa! kamar tayi kuka ta gai da Dady da Mum d'in,tace "zani gidan ya Suhaima ne kuma can zan karya"

"Aa ko kewarta ne ya tashi? cewar Dady dariya tayi "eh Dady yace to "adawo lafiya."


"Tweeny zaki?Husy tace da Hassy tura k'wai tayi baki "no tweeny kije  my regard to her." Dadi husy taji tace "bye Mum da D'an sauri ta fita Direct Motar ta shiga ta faka Maigadi ya bud'e Mata ta fita.


10:30 ce ta kaita k'ayataccen Gidan Suhaima da sallama ta shiga Suhaima na zaune itada Safwan suna break tareda yar Soyayyr su.


"Oyoyo my sis" Murmushi tayi "Safwan Aa sis namu se yau a gidanmu?" tace "Alhmdlh sun D'an tab'a hira dashi ya tashi ya fita nan taje Dining ta karya san nan suka shige d'aki itada Suhaima.


Zubewa sukai kan Bed Suhaima tace "ina Jinki sis meya faru ne?"


Dan Matse Hawaye tayi "sis kin san na gaya miki  na tab'a Sauryi a k'auye ko." 


"Eh na tuno"


"To shine suke Soyayya da Hassy kinsan dama mun rabu to wai sun had'u da Hassy a landon a school ganin kamar mu daya yasa ya fara Soyayya da ita shine fa yanzu ganina ya dawo wai ya komo da tsohuwar Soyayyr sa kuma wai ba gudu baja da baya sai ya Auren, yanzu wulakanta sis yake kuma banso ta sani.Ayanzu hakan nan nayi Sabon Saurayi kuma na amince da soyayyr sa ,nikam bazan iya haka ba sis nason sa amma so yake ya samu a Matsala aganina ai wan nan salon yaudara ne da ace basu fara luv da tweeny ba da zan amince."




Suhaima taja Numfashi "lalle matsala nasan bakisan Hassy ba wlh shegen k'wak'wa ne da ita wlh adalilin hakan zata iya kwanciya domin in tasa abu arai da tana da  wuyar cirewa."

 Tabbas hakan da kikai shine dai de,shikam Muktar kamar Yaudarar Hassy yayi indai yayi hakan kuma wallahi saide yayi biyu babu."


Husy tace "kinga Hoton Shireim" karb'a  Suhaima tayi "kai charkwad'i! wan nan ai yama fi Muktar had'uwa nesa  ba kusa ba duk da banganshi ba Amma dai ruwa biyu ne ko?"


"Sis ban sani ba tunda bamu dad'e ba."


"To ni dai shawarata agareki tun da abin yazo da hakan ki lallab'a Shi, Shi Muktsr din saboda inde baki Lallab'ashi ba Hassy zata iya sani kuma inta sani cewa zatayi ta bar miki abinki Amma kuma abin na ranta sai de kiga tana ta rama ni nasan ta ciki da bai."


"Ai sis tun tuni na cire Muktar a zuciya nasan da Matsala."


Haka sukayi ta hira tana bata shawarwari har wajen shida takai agidan ta tafi.


Ahanya ta tsaya agefen Titi ta d'auko wayarta sai kiran Layin inna take shiru da alama ba Ntwrk sosai tunda k'auye ne 10times tana kira dak'yar layin ya shiga "hello inna!"

daga can tace "naam Husaina"  bayan sun gaisa ta gaya Mata dalilin kiranta.


Haushi ne ya kama inna tace lallema to karma ki soma amincewa ko kin manta iyayen sa su sukace bazai aureki ba! Sai yanzu kuma ya dawo duk da nasan ba laifin sa bane yaron nada kirki alal hakika nasi ya aureki.Amma tunda yanzu abin yazo da haka dole daya ya hkr."

 "Eh inna ai dama ban aminceba kinga kuma a ganina inyayi hakan bewa sis adalciba yawwa hakan Shi yafi nan sukayi sallama ta kashe wayar taja Motar tayi gida.



**********


yana zaune a tangamemen Office d'insa sai k'amshi yake.


Yana Jingine jikin kujerar sa yana kurb'ar Copee knockin Door akai yayi Dan guntun tsaki "yes".Sakatariya nan bata san aikinta ba.


Cike da karairaya ta shiga office din Left hand nata sak'ale da jaka direct kujera taje ta zauna bai d'ago kai ba saima limshe Ido da yayi ya kalli sama.


Wani D'an small Dream Sady ta tafiyi ganin gata ga Shureim suna zuba yar soyayya suna ciyar da juna.


"Me kike so?" firgigit ta dawo daga k'warya-k'waryar Mafarkinta cike da Murmushi a kwance kan face nata ya kalleta kamar yasan face din sai ya basar.


Sady tayi ta maza dama naji labarin garabasar wan nan Company ne yasa nazo abani ga takarduna nan ta zaro su, Amma b'angaren computer nakeso saboda nayi diploma akan computer yanzu kuma ina degree ina a Level 400."


"Well ! Amma bata nan ake fara neman aiki ba sai kin bi wasu offices na kasa idan takardunki sunyi kyau sai a baki ,Amma waya baki izinin shigowa ta nan direct?. tsaki yayi ya hau kiran Sakatariya da gudu tazo ban hanaki barin kowa shigo min office ba?"


"Sorry sir na shiga toilet ne shiisa."

 "Ok last warning,domin kinada sakaci."


Nan ya kalli Sady "oya muga takardun naki" cike da d'oki da zumudi ta mika mai Dan dubawa yayi yace ok da wuya in d'aukeki Aiki domin mun rufe dauka"


Tsugunnawa tayi tamkar saliha "kayi hkr ni don Allah" har dasu hawaye tausayi ta bashi kawai yasa yace ok zakina min Typin kullum hope kin iya?" da sauri tace "eh" ganin ta samu dama.


Nan ya nuna mata Wata computer yace Tomorrow zaki fara zamuna baki Albashi kamar tayi tsalle tace ok." Amma sir ina yin Lucture 12 kullm tab'e baki yayi koma yaushe ne idan kina son Aikin sai kiyi da wuri ki ware."


Tamkar ta Mak'al-k'aleshi takeji wani,shauumin Murmushi tayi da sannu zan kafa gwabana tina kuma na goge alak'arka da Waccen banzar.


Tashi tayi "Ngd sir" nan tafita kamar ta yi tsalle don Murna.


Ni meemi nace lalle Sadi kin daukota da zafi ayi dai mugani in sabulu zai toya kosai.




By

Queen meemi

[5:34pm, 12/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣49❣                     


*March,2017*




_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_



_*Masoyana wlh banda word din dazan gode muku kun nunan kauna Musamm Ummu Khadija,Halima sadiya,Aysha Nuhu Zahra Abdulla ,Surayya,maman Shureim da 'Yan group na Maman Shakur ,da sauran wadanda ban fado ba duk kuna raina.Godia ba adadi Lv u so much❤*_


*********


Tunda ta fita take daga office d'in take Murmushi "tabbas ni mai sa'a ce" bayan ta koma gida taga Gidan acike su Ruby duk sunzo zama tayi "yau gidan namu da kyau" duk sunyi birjik afalo suna Lunch Sumy dake tsakiya tace "yawwa sisters kuyiwa Sady fad'a ta nacewa wani saurayi yanzu kullum itace buga mai waya yayi ta Mata wulaknci ga Faruq dake santa Allah har kuka yake mata Amma indan ku kaga irin wulak'ancin data keyi mai saikun tausaya mai jiya Maigadi har gaya mini yayi ta watsa mai ruwa a jiki."


Sady tace "ai kin san bana failure  nikam innace inason abu,ba makawa saina samu"

 "Lalle Sady kin d'aukarwa kanki wahala cewar Ruma wallahi Mazan yanzu ba irin na da bane wlh tun Ana zuwa sai kinzo an Dena zuwa, jibar ni duk da Dady ne ya hana alokacin tun Samari na zuwar mun har suka zo basa zuwa kuma ban tab'a wulak'nta kowa ba asali ma Dady ke korar su Amma kinga k'arshe ba zab'ina na Aura ba sa'an Dady ne. Amma ke yanzu baki da Aiki sai wulak'nta samari kin k'wallafa rai ga Mutumin Dabe San dake ba haba ki hankalta Mana."


"Ya Ruma duk masu zuwa Guna fa wlh basu da naira haba adauri kashi ko abata igiya ai yanda nake yar gaye sai Dan gaye mai nera dan kwalisa Wanda zai kashen be jimami ba"


Zuby tace hmm wlh Sady ki karatun ta nutsu atoh, domin ni yanzu wlh kowacce Mace kallonta nake idan ma Rawar kai kike kidena.


Ruby tace "karma tayi ga Mata nan birjik a gari ke din wa.Allah yasa ma kar Faruq din ya dawo wa gari ya waya" ta kai Mata harara.


Ruma ta kalli Sumy "kefa? sumy ina Nazi d'in ??"


Hmmm kawai tace San nan ta tab'e baki "ai ya Ruma ban san haka maza suke ba sai yanzu kiga yanda nakeson Nazi Amma Shi kaco kam ashe yaudarata yake sai da Umma tace ace ya fito yace ba yanzu zai aure ba Alhalin duk masu sona da Auren duk ya kore  Jibi case din da mukai dashi kan Hansai (yanzu data koma husy) amma wai ni zai tulawa k'asa a ido,yanzu ma baya kasar."


Zuby tace "tab! Ai ni dama nasan Nazi Mayaudari ne tun time da muna cumpus son Mata gareshi da yaudara ba agabanmu yace yana son Hansai ba! nasha gaya miki Alokacin kina mayen son sa baki gane ba."


Sumy tace "ai last week Wani abokinsa ke gayan Sabuwar budurwa yayi"


Dariya Ruma tasa "Amma kwai D'an iska Nazi yanzu kenan baki da kowa???"


Sumy tace "gamu nan dai Muna nema."


"To Allah ya kawo na gari."


Zuby tace "ke bani Labarin Jansai d'in naji kince ta koma Big gal garin yaya bayan 'yar k'auye ce".


Hmmm "Zuby kin san dai Suhaima Beauty 'yar yayan Babar Anty ta nan gidan ko?" tace "eh"

 "to yarsa ce wan nan Ambassador Nigeria to London."


Ruby tai sak'alo tana ji "to garin yaya hakan?"


Nan ta gaya Mata iya abinda ta sani Wanda Anty ta gaya musu.



Zuby ta sauke ta gumi "tabdi jam! lalle in daranka kasha kallo D'an adam ba abin wulak'ntawa bane."


Sumy tace "ke kinganta yanzu tab! Wlh duk gayuna ta kereni kinsan Suhaima beauty badai Gayu ba Ga Hassanar ta ,ai dole ta waye acan london din ma fa take karatu! Kinga Motar da takeja duk nan ba wadda take hawan irinta,ina irin wadda sukace Dady ya sai mana yace Tayi tsada!"


Zuby tace "eh nagane ta"

 "to wlh ita take ja."


Kunsan Karin wani haushin ma wai saurayin Hansai Sady ke Mutuwar so,Shi kuma Hussyn yake so"


Ruma ta tafa hannu "Amma kuwa  Sady kin fad'o ai bakida sauran fangima wlh Gwandama ki dawo hayyacinki."


Sady tace "Nifa ak'yaleni Naga zan iya cire wando taka! haba dadyma  ya bani Go ahead na kawo Wanda raina keso."


Zuby tace "ayidai mu gani,Agabanki ba irin feleken daba mi ba mu sai kaza Amma gashi yanzu sai manage Sady bakisan life ba sai kin aure."


Haka sukayi ta bata shawara Amma ko ajikinta.


**********


Zaune Husy take ad'akinsu tana Chatin da Shuriem domin yanzu zuwa luv suke kamar me,k'irrr wayar hassy tayi k'ara lokacin tana toilet da sauri ta fito ta d'auka "hello dea!"


"Plss mai sa kake basar dani ne? bata san me yace ba ta kashe. Juyowa tayi ta kalli Husy "Muktar ne wai zai zo gobe" husy tace Allah y kaimu.


Shikuwa Muktar acan so yake yazo ayita ta k'are domin bazai zauna yana gani  a 2 times ya kuma rasa Husy ba.


Jikin hassy in banda b'ari ba abinda yake, "Tweeny mai zanwa dea na tarba ne?" husy tace "sis pls don Allah kina basar dashi Mana! kefa Mace ce ,hakan da kike ne  yake basar dake."

 Hassy tace "ni kaina tweeny wlh bansan hakan da nake kawai daurewa nake don wallahi sonsa yayi mani yawa."


Husy tayi Murmushi koma dai meye kina Jan class  domin samun mazauni  ni na gaayamiki Allah da kanshi zai dawo yana nemanki Amma bawai ki shareshi ba kawai de ki daina nuna damuwar da yawa agabansa" tace" to sis."


Husy da tausayin hassy ya kamata tace "wlh duk son da yake min bazan aminceba domin farin cikin Tweeny.



*Washegari*


Da wurwuri Sady ta mik'e k'arfe takwas tayi Mata a Companyn su Shuriem taje k'ofar shiga Sakatariya ta tsaida ita "kina da Appointment ne? Sady tace "yh kije ki tambayeshi" da sauri sakatariya ta shiga Lokacin bai dad'e da zuwa ba nan ta dawo "yace ki shiga."


Gyara Mayafi tayi ta gyatta d'aurin ta, ta bud'e Jakarta ta fito da Powder ta dada fente fuskar ta maida duk abinda take sakatariya na kallonta domin ta saba ganin irin 'Yan Matan insun zo suna hakan,ta d'auko turare ta fesa.


Da karairaya ta shiga sai girgiza take wani shocking taji a jikinta ganin yanda yayi balain kyau yaci fararen kayansa komai fari fuskar sa tayi fes wow ta ambata a hankali.


"Good Morning sir"


Nan ya dago "Morning 2"  zama tayi kan kujera nan ya mik'o Mata wasu takardu  hada Ido sukai ta saki mai fari kauda kai yayi ta koma ta zauna.


Tana yi tana satar kallonsa komai nasa Birgeta yake bak'in Glass dinta ta d'auko ta kafa a ido don taji dad'in kallonsa ,Shi kuwa sai aikin sa yake .



Wajen awa d'aya batai Aikin kirki  ba,Dan tsaki yayi ya Mike ya d'auko wayarsa Murmushi yayi ganin test msg na husy. Kiranta yayi bugu wajen 3 times bata d'auka ba duk abinda yake tana satar kallonsa can sai ga kiran ya shigo ya kashe ya kira ta.


"Oh my finest ina kika shiga ne?? 

Kin san ina missn voice naki" Murmushi yayi love u so much babe."

Da alama yana jin dadin hirar.

Murmushi yayi tareda shafo sumarsa "finest anjima zanzo ganin ki domin samun sukuni a Mind d'ina."


Tamkar ta kurma ihu don ta gane da Husy yake waya D'ora hannu tayi aka da k'arfi ta buga bench d'in .

 

Waigowa yayi Mata kallon raini nan Jikinta ya saki ya dad'e suna waya San nan ya kashe.


"Ke idan bazaki iya aikin nan ba U can go bansan Matsala."


"Sorry sir" 


Nan ta fara ko rabi batai ba ta d'ago "12 tayi sir time na Lucture yayi"


"Are u finished?" 

"No sir."


"Okey to ya?"


Fari tayi  da ido dan samun shiga "bari na k'arasa" nan ta tayi sai 12:30 ta gama ta tafi.

 

Tana shiga mota ta kifa kai kan sitiyari da Dan tsaki

Fushi taji mai tsanani ji take kamar ta kauda Husy tunani take yanda zata b'ullo sanda taje har an fita daga lucture daga nesa ta gano  lubna janta tayi sukaje bakin bishiya.


K'awa "Handsome yak'i saurara ta plssss say Something na rasa idea."


Dariya Lubna tayi "hmm kawai ki sanar mai" Sady tace "so kike ya koreni daga office nashi?"

"Ke dalla zauna nan garin kallon ruwa.....ai abari ya wuce Shike kawo da rabon wani.Sady tace "nifa ban san hakan domin namiji yace yana sonka ma ya Allah ya cika,balle kace kana sonsa."


Lubna ta tab'e baki "nikam itace shawarata" Sady tace "Okey to ta yaya?"


"Kimai text msg tunda yanzu nasan yasan Number d'inki in kuma bai sani ba ki k'ok'arin karb'a ki kirasa ya gane kece wadda ke aiki gunsa kamar one week haka saiki samar mai."


"Good idea lubna" Dadi ne ya kamata suka tafi.


*******


K'arfe Biyar Mukatr na gidan su Hassy suna zaune kusa da flowers kan kujeru suna hira yana son tambayar ta Husy Amma ya kasa sai kallon kofa  yake.


Hassy na lura dashi "yadai Muktar? yace "no problem" kurb'ar lemu yayi San nan yayi ta maza ina hussina ne?

 "Tana cikin gida tana shiri.cuz bak'onta ne sai zo" dam! yaji gabansa ya fadi .


Kamar da 30 mint haka Maigadi ya wangale gate had'addiyar Motar sa ya danno ta cikin farfajiyr fitowa yayi yau yayi shigar white din jins da tshrt white sai black din shoe sai agogo black can kamar Mintuna sai ga Hussy ta fito cikin shigar Red tayi bala'in kyau wani kwantaccen Murmushi ke fita daga bakinta wushiryarta na K'ara Mata kyau.

tsayawa tayi wani kallo yabita dashi don ta rud'ashi kunyarsa taji tace ina zuwa.


Nan tayi wajen su hassy wani Mahaukacin kishi ne ya kama Muktar zuwan taa yasa ya sunkwi da kai "Tweeny ga Shuriem su gaisa da Muktar" k'ura Mata idanuwa yayi dai de Lokacin shureim ya k'araso gun ya mik'awa Muktar Hannu kamar ya naushe Shi ya keji idanuwansa sunyi ja da k'yar ya mik'a mai Hannu suka gaisa kallon Hussy yayi cikin ido ta d'auke kanta suka bar wajen.



Hassy kuwa da Mamaki take binsa da kallo kamar me domin ganin ya canja mata,cup d'in lemo ya d'auka jikinsa har wani rawa yake cup din ya fadi kasa ya fashe ,rikicewa hassy tayi wai Muktar Menene? Akaro na 2 ta tambayeshi kamar da tsawa yace ta k'yaleshi k'arshema yace zai tafi haka sukayi sallama ba yabo ba fallasa zuciyarsa na tuk'uk'i.



Hassy Asanyaye ta koma gida domin abin yayi Mata ciwo koma meye yake b'oye Mata zata sani.


Husy kuwa ranta yad'an baci duk sai Jikinta yayi sanyi.Shureim kuwa jifanta yake da mayataccen kallon sa Wanda ke d'imauta ta tana Son salon Shureim saboda ko bai Magna ba yasan yanda zai aika sakon sa cikin salo da k'warewa.


"Finest"! ta d'ago "naam"

 "wai yaushe zamu zama inuwa d'aya ne ki bani dama Manya su shiga ciki mana" Dariya tasa "har yaushe daren yayi?" Murmushi yayi ashe kin iya magana haka to ai mu Soyayyarmu ta da ban ce bazamu cinye soyayyr awaje ba sai kin zama wife d'ina."


"Nida nake karatu ai sai na gama."

"Anya finest?"

K'ayataccen murmushi ta saki batace komai ba

"Gaskiya finest kina da kyau"

"Har nakai ka?"

 "ina wani kyau a namji" tace "hmm haka dai kace.Amma ai kafini kyau."


Satar kallon sa tayi taga yana kallon ta tare da "Lumshe ido finest bakya iya dagowa na kalleki sai de ki ta zuban kalamai ta k'asa ko?


K'unshe kai tayi a gyalenta ta kasa d'agowa tana jin heat nata na fat -fat.


K'arar Msg ne daya shigo wayarta, ya dawo da ita daga duniyar data tafi  wayar ta duba k'irjinta ne ya buga ganin abinda ya k'unsa kamar haka:


_Ki sani ba gudu ba ja da baya_

_nayi dakon sonki tun kina k'arama sai wani daga baya zai zo ya k'wacen ke domin ni nake miki true luv ayanzu hakan zan turo iyayena ayita ta k'are_

_Ur husband Muktar_


Kashe wayar tayi gaba d'aya ta d'ago suka had'a Ido da Shuriem "Subhanallah Finest meya faru! Naga idonki hawaye? 

Shafawa tayi bata San sun zubo ba "Aa abune ya fad'an ido" "sorry angel" Handkerchief ya zaro ya mik'a Mata ahankali ta karb'a k'amshin sa ya bugeta taji wani sanyin dad'i ta share yace "finest bari na tafi na barki ki huta kinji?"


Tace tam wani sansa taji ya k'ara shiga ranta afuskarsa taga damuwa sai data shigar sa mota ya d'ago Mata hannu San nan ta tafi.


Bata taba sanin zata so wani bayan Muktar ba sai gashi ahankali son Shureim ke shigarta ,da gudu ta shige gida ta haye saman bene domin taga ba kowa afalon k'asa d'akunasu ta shige tayi ruf da ciki tana kuka kamar me.


Hassy ce ta shigo itama idanuwan ta yayi ja da sauri ta k'arasa "sis meye? husy ta dago "bakomi dear ke ma meyasa kike kuka" hassy tace kinga abinda Muktar yayi mani ko nikam inaga zan hk'r dashi ba dole dama wasu Mazan Mayaudara ne."


Gaban Husy ne ya fad'i "tweeny nima abinda ya sani kuka kenan domin ni dake d'aya ne abinda ya faru dake tamkar dani ya faru" Rungume juna sukayi suna kuka.

Bayan sun tsagaita

Hassy tace "sis na tafi Mum na kitchen" tace "nima gani nan."


K'arar Ringtone na wayarta ne ya buga nan d'auka ta duba taga sabuwar Nomber ce Da sallama ta amsa wayar. "Yar aikin gidan mu ki sani Karona dake bazaiyi kyau ba wlh, ko ta halin k'ak'a sai na rabaki da Handsome saboda dani ya dace wlh na dai gaya miki."


Kan tayi magana ta kashe Tabbas tasan Sady ce sai Duk barazanar da zatai bata tsoro ba,ayanda takeji bazata iya ba Shuriem ba kuma in ta rabu da Shuriem kamar ta bawa muktar k'ofa ne ga kuma Tweeny dole ta shiga damuwa wullar da wayar tayi cike da haushi domin ji take kamar tasa ihu.


*Waye Shuriem*


Shuriem d'ane a gidan Alhaji Kabeer da hajiya Khadija. Alhaji kabeer shahararren D'an kwangila ne wanda yake samu ta hakan ,inda kuma yake kasuwanci ya tab'a rik'e Muk'amai a gwabnatin tarayyya San nan yana da Company anan Abuja da sauran Jahohi ayanzu hakan yayi ritaya shureim shike gudanar da duk harkokin sa.


Shureim shine d'a na biyu a Gidan su, inda yake da yaya Mace Maryam dake Aure a lagos sai k'anwar sa Nawwara itama tana Aure anan Abujar sai Autansu Sadiq dake karatu.


Yayi karatunsa a Oxford University inda ya karanci Accounting bayan ya kammala ne sai Mahaifinsa ya bashi Ragamar komai nasa ganin ba irin nan ya karanta ba, bai San wasu kasuwancin ba, yasa yayi wani Course a uniAbuja kan Bussness.


Allah ya bashi farin jinin Mata sai de duk basi mai domin Shi bai san mace tace tana sonsa ,shiisa ma duk masu sonsa baya kulasu don basi masa ba.


'Yan Mata da yawa wasu har gida suke binsa wasu office Musamm Mata masu kwad'ayi ganin yana tashen Naira wasu kuma don kyansa.


Shuriem yana da son tsafta ga da son turare da son Fararen kaya bai da Magana sosai sai Murmushi kad'an kenan daga Shuriem.



Tunda Muktar ya koma kano yake cike da damuwa duk ya canja ganin hakan yasa yatafi Mangalu domin zuwa gun Malam don ya taimaka mai


To fa muje zuwa.


by Queen meemi👑 





.

[2:04pm, 13/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣50❣                    


*March 2017*




_Sadaukarwa ce Ga basher Usman Family's_



_*Wan nan page din naku ne Maman haneef ,Maryam oumey, Ameera Mahmoud,Maman rahma,Rabia Alhasan, Nana fiddausi, Muhfaz,Maryam Ahmad,nabila ladan,Maman yasmeen & Zeenat tukur. Tnz❤*_


******


*Mangalu@11am*


"Ya kamata ace kayi Aure haka Muntari" cewar Goggo "ai Goggo da Maganar nazo ma shiisa nazo ma ayita kare."

"Hakan shine dai-de Muntari gashi nan duk sa aninka da yara a ina yarinyar take ne?"

"Ai gogga kinma Santa Hansai ce fa" Goggo ta zaro ido haba idan d'a ya manta ai uwar d'a bata manta ba kamanta baya yanda mukai musu mukace bata da asali ai yanzu muka je sai ace don ance iyayenta masu kud'i ne kwad'ayi ya kaimu."

 "Goggo ataimaka" suna cikin Maganar Maigari ya shigo "Aa Muntari hira kuke ne? gogg tace aifa kajimin d'a wai Hansai yakeso anema mai Aure ai da kunya mukoma."

Maigari yace "too nikam bazan shigema gaba ba sai de in wata ce Amma ai da kunya."


Kamar yayi kuka ya tashi ya fita sai gaisawa suke da tsofffin abokansa nada sai sha'awarsa suke suna dama suma sunyi karatu bai Zame ko inaba sai gidan Malam,yana k'ofar gida tsaye suna hira da wani Mutum.


Dan tsayawa yayi suka gaisa kan Mutumin ya tafi Malam yace "Muntari Kaine a gari?"  "eh wlh Malam dama magana nazo da ita kan husaina."

"to wata matsalar ne?" Muntari ya sosa kai "dama Aurenta nake so akaro na biyu." murmushi Malam yayi masha Allah amma ai Muntari ai an bar Maganar tun abaya ko ka manta maigari yace Aa, ai maganar bai dace ka Taso da ita ba domin ni inada taka tsan- tsan balle yanzu ma kaga ba a guri na take ba ,ina Baka shawara ka hak'r ka nemi wata tunda kaga ba'ai Auren ba to ba Alheri duk wacce kake so zan shige ma gaba."


Tunda Malam ya fara magana Yake zufa kamar me idon sa yayi ja yace "Malam ngd Allah ya saka" akasalance ya mik'e ya tafi Malam ya bishi da kallo cike da tausayi.


*Abuja@ 4:00pm*


Tsaye Husy suke itada hassy zasu Super Market goslow ne ahanyar yasa suka tsaya da yake yau weekend duk Motoci na fita wasu zasu visiting Akusa da motar su Sady ce itada Lubna. Lubnan ce ta fara ganin su Ta nunawa Sady alokcin aka bada hand nan suka fafara Sady ta bisu abaya har sukaje Super Market d'in.


Firfitowa sukai shiga iri daya sukai nan suka shiga Sukayi side na makeup da perfumes,yana tsaye yana duba wasu lates agogwaye wajen yana gefe.

 Shiya fara ganinsu wani k'ayataccen Murmushin sa yasaki.Hankulan su Husy na kan d'aukar abinda sukeso ji tayi kawai an k'arfe basket ta d'ago suka hada ido atare suka sakar wa juna Murmushi "Finest da nasan zakuzo siyayya ai Dana Zo na d'aukeki ban san kowa yana gane wan nan fuskar."

 Murmushi tayi "Habibi kenan barka da yamma." "bana amsawa sai yanzu  ma zaki gaidani." "Kaina bisa wuyana habibi"

Murmushi yayi ahankali yad'an sunkuyo kamar zai d'au Abu iluv u Swt finest."


 Lokacin Hassy ta k'araso gurin perfumes din ta gama da Makeup site  Dan dariya ta saki "Aa kice da Masoyin aka hadu."


Su Sady kuwa sai A lokacin suka k'araso suma suka shiga karaf idanuwan Sady yakai kan Handsome dake rike da Basket na husy wani Mahaukacin kishi ne ya deb'ea taje ta wanke Hussy da mari mai zafi.

'yar k'ara ta saki saboda zafi da sauri ta kalli wacce ta mareta ganin Sady yasa ta matso kan ta rama taji an wanke Sadyn da mari.

  itama an bata wani dagowa tayi sukai ido hudu da Handsome yana wuci "ke kina da Mental problem ne?"


Zaki zo kimare ta d'an karamin tsaki yayi bansan problem wlh. Hassy kuwa sai harare harare suke da Sady  "anji kunya ba ason mutum ya nace ."


Jan hannun lubna  Sady tayi ta kalli hassy "dani kuke zancen."

har sun fita Lubna ta dawo tayi side da Shuriem yake don itama yana birgeta Amma tunda k'awarta ta rigata dole ta basar.wani kallon Shureim tayi Tace Sady me k'aunarka ce domin babu wacce takaita sonka kuma sai inda mammu ya k'are",da sauri tafita don ganin yanda yake huci.


Hanunn sa ya daka ganin yanda husy ke zubar hawaye "sorry My Queen" da k'yar ya lallasheta yayi counting suka fito sai day aga tafiyar su San nan ya shiga Motar sa ya tafi.


*Monday @ 8:09*


 Da k'yar Sady ta shiga office d'in cike da tsoro burki taja domin yau shigan da yayi yafi na jiya abinda ke dada rudarta gashi kenan akwai tsafta da ado.


"Morning sir"


Bai d'ago ba sai ma D'an.Rubutunsa da yake yana waya ta dad'e a zaune ganin hakan yasa. Tayivta maza tace "sir aikin."


Wani wulak'antaccen kallo yayi Mata tare da Murmushi ta gefen Lips nasa yace "ke!

Get out of my office"


"Sorry sir wlh bazan kuma ba wlh dama tsautsayi ne wlh."


Kuka ta fara shab'e -shab'e plss sir bazan kuma ba kallonta kawai yake yana juya kujerar sa ,da mamaki fal zuciyar sa wai sonsa take sai yanzu ya gane dalilin neman aikin ta D'an tsaki yasa I said get out of my office  yaune last da zan K'ara ganin ki a office na kin gane."


Jakarta ta tad'auka "pleaes sir!"


"Security"


Da sauri yazo nan Shureim ya nuna Sady "fitar da wan nan karka barta har sai kaga tabar harabar Companyna."


Da gudu ta fita Sucurity na binta ta galla mai harara "Malam sai ka k'yakeni haka ko! Tunda ba maula nazo ba" nan ta shige Motarta ta kwasa aguje.


Tana ta fiya tana kuka gefen titi ta tsaya tana dukan sitiyari tayi "wlh dole ka soni Shuriem bazan barka ba akan wan nan kile war kwanan nan zakana wulaknta ni, ke kuma husy sai kin gwammace kid'a da karatu.


*************


Kwana 2 hassy ta rage neman Muktar don Jan ajinta .yau ma suna zaune Dady ya shigo duk suka mai barka da zuwa "yawwa dama ke husaina da hasna inason sanar daku ba daku za a koma London ba saboda Na dawo da karatunku nan abuja a uniAbj saboda Suhaima kar mu tafi mu barta ita daya duk da ga Anty . Mum naku kawai zamu tafi da ita sai Arif."

Hassy kamar zata sa kuka "Dady yanzu mu kad'ai zamu zauna a wanga memen gidan nan! Yace habadai Goggo zata zo Ita zata zauna daku( k'anwar Maman sa ce)akwai dalilai ne Amma idan be muku ba sai mu tafi ke Hussyna me kikace?"

  "Dady zamu zauna d'in Allah yasa hakan yafi Alheri" "Yawwa 'yar Dady."


Mum tace nima fa nafi san zaman nan Dady yayi Mata wani kallo Wanda shiyasan ma'anarsa kauda kai tayi  "to my twinss ku Kula banda shirmen k'awaye ku zama masu kula kun gane?,bamu yarje muku kawo ko wane saurayi yazo zance gunku ba, illah ke Hassy Muktar ke kuma husy Shuriem su na sani suna zuwa.ban yarda ku tsaya da wasu ba bayansu suma din ku kiyaye."

Sukace "tam Mum."

 Dady yace kowaccen ku level data ke shi zata cigaba ke Hassy dake level 2 nan zaki shiga haka ke Husy dake 1 Kema nan zaki shiga."


Arif dariya yasa yana musu gwalo harara suka kai mai ya gudu Dady yace "sarkin tsokna.Yanzu jibi zamu tafi Gobe Goggo zata zo ga Idi nan kun san dai amanar dake tsakanin mu dashi tamkar Dan gida duk wani babban abu da kuke so kwa bashi yana sayo muku ,zai dawo nan suna kwana a boys quaters saboda tsaro." Nan duk ya sallamesu suka haye sama.


*Washegari @12am*


Sai ga Goggo ta iso da murna suka tare ta tace kai ni karku karya ni ina kakarku" Mum tafito Aagogoji kece? Sannu da zuwa" zama tayi kan d'aya da kujerun.


Wani saurayi D'an kimanin shekare 23 ya shigo da tulun kaya "Aa harda kamilu akazo?" goggo tace "ai k'afata kafar sa saboda bakowa gidan."


Hassy tace "kai duk girman sa!" kamilu yace "aini d'an Auta ne" suka dariya.


D'akin dake kusa dana su Haassy aka bata komai akwai aciki su funiture.

Shi kuma kamilu aka bashi dakin dake k'asa empty gado ne aciiki zai wardrobe mai 2 sai toilet duk suka shigar da kayansu.


Washegari kuwa su Mum 7:00 Am suna Airpot da kuka su Haassy suka saki itama bata san barin su ba yanda ta iya ne haka suka Rungume Dady da Arif suna nan tsaye Jirginsu ya d'aga asanyaye suka koma gidan.


Gidan yayi masu fadi sai da Goggo ta jawo su kasa suna kallo suna hira har kamilu nan suka sake da take kamilu Dan shafta ne nan sukai ta hira.wayar Hassy ce tayi K'ara ganin sunan Muktar yasa ta kauda kai Husy tace "meye tweeny?"  "wan nan Muktar dinne mana."

Dariya husy tasa "lalle sai da dare ki ishemu kina.missn sa ko?"  ganin kamilu da goggo na kallonsu yasa ta dauka tayi sama .


"Helo" daga can ya amsa nan yace Mata zai shigo kamar bataso tace to Jikinsa yayi sanyi kit ta  kashe.


Yana zaune ya tashi yana zagaye daki zuciyarsa na mamaki taya zan samo kan husy ne kode hk'r zan na rike Hassy no huusy itace life dina msg ya tura Mata kamar haka: _ya tauraruwta ki sani amincewarki itace zata bani damar aurenki domin malam yace akaro na 2 sai kin amince domin pls ki taimakeni ya tura mata_


Dariya suke sha itada su Goggo kan wani Labari data basu d'aukan wayar tayi jin karar msg Murnushin jin dadi tayi don kin Amincewar malam,tabbas Tasan dole ya maida hankali kan Hasssy hakan take fata.


Martani ta Maida mai Muktar ka sani Bafa komai Mutum keso ke samu ba ka yaki zuciyarka kamar yanda nayi da tawa duk son da mukema juna domin Bakomai mutum keso ke samu ba,idan kuma amincewa kake nema to nikam bazan aminceba tunda baka tausayin sis nawa,tamkar ka yaudareta ne" 


Tashi tayi ta fita  tace Goggo ina zuwa can garden taje ta zauna bakin bishiyar Mangwaro tana kuka domin duk son Shuriem da zuciyarta keyi har yanzu Muktar na ranta yana bata tausayi bayan ta gama kukan kiran Shuriem ya shigo nan ya mantar da ita bacin ran data ke ciki.




 By 

Queen meemi👑👑


.

[1:29pm, 15/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣51❣                    


*March 2017*



_Sadaukarwa ce ga Bashee Usman family's_



_*Wan nan page din naku ne Sis Marwa &,Ameena Oneluv❤.......san nan Masoyana masu nunan so da kauna har kullum kuna raina tnz for ur support😘Queen ce*_



**********


 Yau ta kasance Monday Husy suka tafi Lucture da yake duk time d'aya yau suke da ita tunda su kaje kowacce ta tafi nata Fuculty bayan kamar awa 2 Husy suka fito. Bakin wani bishiya taje da kujera irin ta dutsen nan ta zauna tana duba littafanta.kamar daga sama taga Sady akanta da wasu Frnds nata 5 tafa hannu tayi "wajen zaman namu shine kika zo?

Bama wan nan ba dama da tamu dake akanki an Mareni ko? to wlh akanki zan rama" kallon k'awayen tayi kun san "duk kyann yarinyar nan da wani bud'awar da take wlh tayi aiki agidan mu. Ummi wata daga ciki tace kai Sady ni kam ban yar daba haba ai wadda tayi aiki ma tafita daban." Lubna tace "ku wlh da gaske ne yanzun ma cigaba ta samu ne sauran 2 din sukace "tab! ke ai baki da fangima."

kallon su tayi ta tab'e baki Ummi tace "ke yar aiki" nan duk suka kwashe da dariya Sady ta tuje Mata D'an kwali "wlh idan baki rabu da Hansome ba sai nai k'asa -kasa dake" haushi ne ya kama husy ta bugawa Sady Mari ta daura Dan kwalinta tace "samu yafi iyawa if Allah say yes. No body can say no.

Ku kalleni sama da k'asa kunsan duk cikin ku na zarce ku ba yabon kai ba in banda ma shirirta kufa kun Girmen kamatayi kuja girman ku, ke kuma Sady wlh kin d'auko Roman dafa kanki ki sani wlh da ina tunanin hkr da Shureim Amma wlh yanzu kin sama sai na Aureshi kuma wlh sai na k'unsa miki bak'in ciki idan neman miji kike kizo zan miki hanya useless jobless kawai" nan tabar wajen.


Da mamaki suka bita da kallo  suka saki dariya Ummi tace Ammafa yarinyar ta hadu inafa tantama da kikace yar aiki ce" Sady kuwa k'wafa tayi tace "kuzo mu tafi, wallahi koni ko ita kunsan dai ko aschool bana missn abinda nakeso"


Husy kuwa Motar ta ta shiga ta zauna ta kifa kai tana kuka dole ta takawa Sady birki Murmushi tayi ta latsa kiran Tweeny daga can ta d'auka tace gata nan kamar 30 mint sai gata nan ta shiga Gaban motar suka ja.



Hassy tace "tweeny muje musai icecream Husy tace "Okey dea" sunje sun saya suka zauna suna sha husy tace hassy "dama School namu Sady take? "Nima bansani ba kinsan bazata wuce nan din ba"  husy ta cije leb'e "Hmmm yau taso tozar tani agaban k'awayenta ni bansan me natare mata ba" hawaye ta share.Hassy tace tweeny kin Mata kafa ne tanasan saurayinki shiisa ta takura miki so take ki bar Mata Shuriem."

Husy tayi dariya "nikam wlh bazan bar mata ba." Hassy tace "Weldone dea kodan hakan ma ki dage har ai Aurenku da shi domin sai mun bata mamaki" husy tayi Murmushi nan suka gama suka tafi gida.



Suna zuwa kamilu ya ta resu hannnu duk fulawa Husy tace "bro meye hakan?" yace "Gogggo ke D'an wanke shine fa nake taya ta mai nake toyawa" Hassy ta rik'e ciki "wayyo Namji da suna Hajara" kamilu yace "se kunzo kuna Lashe hannu" koma wa kitchen yayi ya d'auko su tumatur  da Albasa yana yan kawa Gogggo na saki.


Wanka suka je sukayi suka fito suna Goggg abamu d'an wake tace "yara Musammmn ke Hassy ba Saba ci kikai ba, yanzu zaku coi Dad'i zama sukai aka zubo  musu Aka matsa leman tsami da yaji suna ci sai santi suke Hassy tace "Goggo za musa rana kina koya mana girkin Gargajiya irin wan nan Lagwada haka,duk da nasan Husy ta iya wasu tana Mangalu" kamilu yayi dariya sis santi kike fa! Kin ganni nano ba abinda ban iyaba ba Bording nayi" suka saka Dariya Hassy tace "Allah Goggo saboda kinga Husy ta iya nikam zaman waje mukai se Aslow, sai de girkin gayu muka iya." Goggo tace "yo ai dole nane so nake Na kai ku d'akunan Mazajen ku kowacce ta k'ware akan girki, nima sai kuna nunan na zamanin." haka suna hira da raha suka gama suna santi.


***********


Bak'in ciki ke cin Muktar yana Office Amma ya kasa tab'uka komai  dalili Husy taki daukan wayar sa har Hassyn ma, tsaki yayi komai ta fanjama- fanjam yau ze sanar da Hassy shine Muntarin Husy yasan zata hak'ura ta barwa husy din, da wan nan shawarar yayi ya gama ya koma gida.



Text msg ya aikawa Hassy ta email adresss ya tura Mata yasan ya yiwa Huusy lefi Amma bazai zauna ya cuci kansa ba.


Hassy na zaune tana game candy crush taga sak'o na email ya shigo nan ta bud'e gaban ta ne ya fad'i nan Hawaye suka fara zarya.tashi tayi ta fita tana k'wala kiran hussy Suna zaune suna kallon wani film sai dariya suke kwasa Goggo tace "Aa yaya dai da wan nan kiran?" hassy taja hannnun husy sukayi sama suna shiga ta kulle d'akin.


"Haba sis ashe kin san Muktar shine Muntarinki  kuka barni cikin duhu wan nan dalilin ne yasa yake mun wulak'nci" kuka tasa "haba sis Keda abinki me kike tunani daga yau na bar miki abinki,domin bazan Auri Wanda baya sona ba! kuma duk sonda kukayu dacan atsakanin ku baici na cigaba da kasancewa da shiba saboda kece aransa."


Husy tace "tweeny ina kika sani? tace shiya gayan  nan ta nuna Mat a sakon daya turo mata. wayar ta karb'a ta karanta .Zama tayi bakin gadon tana kuka ka karya Alk'awair Muntari maisa ka canja hali daga Muntarinkana asali haba."


D'agowa  husy tayi "sis ai ya Riga ya wuce domin Munrabu tunda kuma kinga yanzu inada saurayi ke kuma kun fara Soyayy sai Naga kamar yaudararki zaiyi."

Hassy tace "no sis bazan so farin cikina na danne naki ba, nasan kina san sa na hak'ura dashi kawai."

 fita tayi aguje tana kuka datan d'akin ta shiga husy ma kukan take nan ta buga wayar Muktar yana kwance yaga kiranta ya washe baki.

Da hanzari ya d'aga.


"Yanzu muktar kayi mani adalci kenan? ba haka mukayi da kai ba fa! haba yanzu me kake so sis ta d'aukeka ka yaudareta bakajin tausayinta to wan nan dalikin ba zaisa na Aureka ba bawai don munyi soyayya abaya ba yanzu kace dole sai mun koma, ba haka Rayuwa take ba don haka ni bazan Aureka ba. se kayi hk'r tunda har ka iya yaudarar sis nawa k'it ta kashe phone din.


Wani sandarewa yayi ya kama kai " OMG!"



Husy Ta tashi tabi bayan Hasssy kuka ta ganta tanayi tace "sis bazan kuma luv da Muntari ba kai duk wani namji ma don mayaudara ne wasunsu, dama  Muntari naki ne kiyi hkr ki yafen" husy ta ce  "sis ya kikeso nayi da Shuriem ko kin manta artabun dake tsakanin mu da Sady kuma kin san ba hkr zai ba sis ke kike ban karfin gwiwa na Auren Shuriem yanzu ban san ya zan ba plss sis."


Hassy tace "tweeny koda ba zaki Auri Muktar ba toni kan na Rabu dashi har abada Allah ya gani dana san shine Muntarin ki da ban bari sonsa ya mini illaba."

Kuka suke husy tace "wlh Hassy bazan Aureshi ba Shuriem na keso danke aka haliccci Muktar shiisa Allah bai k'addara auren mu dashi ba tun abaya. duk wan nan k'alubalen ya faru ne kawai saboda haka Allah ya tsara."


Hassy tace "na sani sis Amma na hk'r da shi" ke kuma yanzu sai ki zab'a koshi ko Shuriem Amma ba hakan na nufin wai Mubar Sady ba sai inda manmu ya k'are. Ke Allaurar ruwa ce mai rabo ka d'suka."


Haka sukai ta kukan su suka gama san nan suka koma k'asa.


*Bayan Kwana 2*


Shi kuwa Muktar duk ya tashi hankalin sa domin dukkan wayar tasu inya buga baya samu duk ya fita Hayyacinsa duk ya kod'e ya Rame ganin ba mafita ya fita gari don zaga yawa ak'arshe yaje gun abokin sa da sukayi karatu tare.



Lemo ya kurb'a. Yace "Aboki ina cikin Matsala na rasa gane kaina plss help me."


Mahmud yace "meye matsala ne? nan ya kwashe komai ya fad'a mai Mahmud yace "tab! Amma kanaso ka had'awa kanka xafi fa domin abinda ya wuce ya riga ya wuce da kasani ka rike ita hassanar tunda kaga ita hussainar dalilin kana Soyayya da Hassy din tace "Aa" kasan tunda blood siaters ne dole ka samu problem  to tunda abin yazo sai ka hkr da ita husaiina kadau kaddara ka rike hassana."



Muktar yace "wlh baksan sanda nakewa yarinyar  nan bane! na kasa cireta araina idan nace zan tsaya don kamarsu d'aya to zan cuci kaina wlh domin kama da wane bata wane Matslar yanzu duk kan su sun juyan baya."


Mahmud yasa dariya to badole ba Jana neman zauta yara, sai ka nemo wata bayan ga mata nan agari kyawawa. Muktar yace ni ai in ba itaba sai Rijiya."


Mahmudu yace "so da dama Mutum yayi ta hak'ilon abu ba shine alkairi agaresa ba. Shawara kayi istikhara wato neman zab'in Allah idan zaaka so akwai  wani Malami  da yake istikhara sai yayi ma idan kai baz akai ba sai ya baka wata shawarar ma tareda addua."


Jikin Muktar ne yayi sanyi yace "ni bansan zuwa gun Malaman nan 'yan duba fa!" Mahmud yace "wlh wan nan Malami ne kawai addua yakeyi koya baka  kayi da kanka bisa koyar war addinin Musulunci, kai de kazo muje."


Muktar yashafa kansa yace "yau ina busy Amma gobe sai kayi mani waya after na dawo daga aiki sai muje......




By 

Queen meemi👑

[3:10pm, 16/03/2017] 👑Meemi💋: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣52❣                     


*March2017*


*®NWA*



_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



_Ummyn Khadija agaskiya banda bakin Da zan gode miki sai de nai miki fatan Alheri tnz da kauna❤_


*********


Washegari kuwa bayan komawar Muktar daga Aiki Mahmud ya kira Shi kan zuwan sa, nan yace ya sameshi a gida Direct gidan yaje lokacin har yayi Wanka suka rankaya Unguwar Mandawari.


Zuwan su kuwa ba kowa A gun sai Malamin yana karantar da wani yaro ganin su  yasa ya sallameshi,Mahmud suka gaisa Malam yace "mahmud kana nan dama?" yace "eh walh Malam yauma abokina na kawo" ya nuna Muktar Malam yace "Masha Allah Meke tafe daku."


Mahmud ya gyara zama "."Malam mas'ala ce akan neman Aure Shi wan nan abin yazo masa abai-bai nan ya sanar wa Malam san nan ya d'ora Da ya naso ayi mai istikhara ta Aure neman zabin Allah.


Malam yace "MASHA Allah hakan shine dai- de hakan ko yarwae Manzon Allah ya uwarcemu kan mi istikhara a sha'anin Aure sai  kaga Mutum yayita bulayi kaga Abu ba alkhairi ne gareshi  ba. Nan ya tambayi sunan sa ya ce sudawo nan da 3 days zaiyi Istikhara wanda Annabi ya koyar(duba littafib hisrul muslim akwait aciki).abinda naa gani zan sanar dak Godia sukayi suka aje kudi yace Aa suje yayi don Allah ne da k'yar ya karb'i d'ari biyu.


********


Tunani take Amma tak'i bari husy ta gane Da sun hada ido zata basar Husy na kula Da ita.

Tashi tayi taje wajenta ta zauna kusa Da ita "sis ya kamata ki dai na tunani komai yayi zafi Maganin sa Allah nasan kina k'aunar Muktar kawai b'acin rai ne yasa kika ce kin hk'r Amma nasan yana manne aranki,Amma ta wani sashin ni nafiso ki nuna b'acin ranki kan abinda yayi maki ki nuna kema macece" Hassy tace "hakane na d'au shawarark kuma na dena tunani" tace "yawwa sis akanme wani namiji zai saki kina tunani? ai yanzu an dena hakan" dariya Hassy tayi "kaji husy kamar kece yayata ko,sai wani karyar dakai kike wai irin big yaya din nan, Allah sai yaso nice babba" dariya itama tasa "yo meye Marabar dambe da fad'a".nan ta mantar Da ita suka shiga hirar duniya Da yake yau ba lucture.


******

@4:pm

Sady kuwa tana zaune sai tunanin irin abinda za taiwa Husy take Amma ba idea sai kwancewa take tana sakawa. Sumy dake taje kai tace "dama wani d'an adam d'in shike d'orawa kansa wahala." Sady tace "baruwan mutum Naga zan iya ne"😏


Sumy tace "ayidan mugani dai-de lokacin wata mai Aiki ta shigo "wai Ana sallama Da Antysady" tsawa ta daka Mata Da sauri ta fita ,sumy "tace Abari dai ya wuce, wlh kiyi amfani Da damarki kan ta kubce miki atoh!kalleni nan yanzu cizon yatsa nake mistake danai yana damuna bamai lek'o ni danma ina zuwa school to kazo ka gama ba mashin shini wanda da can Allah ya baka kayi wasarai rai dashi Allah Nazi ya cuceni duk shi yasa na kore samarina masu sona Da gaske kan zai auren Amma she nan kwa shine Mayaudarin Allah bazan yafe ba."


Sady tace "ke dani not desame don haka ba lalle yanda ta faru dake ba ni ta faru dani."


Nan ta mike don fita ganin Wanda ke sallama Da ita tun daga k'ofa tayi tsaki dan nacin yaki hkr wlh yau senai mai wulak'ancin Da Shi akacee ya ganni ahanyama bazai kulani ba.


Zuwa tayi ta tsaya "Faruq gani" yace "ya gida"  lfy"  san nan tace "yanzu don naci ba zaka rabudani ba ? Wai nikad'aice mace a Abuja n?"

 Yace


 Bawan nan bane ya kawo ni nasan ina sonki Dan so tunda kin k'ini dole na hkr domin son maso wani koshin wahala, tuntuni na hkr kawai de zan sanar dake daurin aurena next week  don na samu nima mai kaunata" Nan ya zaro Iv ya bata yace "Allah ya k'addara saduwarmu ya baki wanda kike so" nan ya juya ya tafi.


Kallon katin tayi ta tab'e baki "da ya fi maka don ni ba tsarar ka bace tayiwu kucaka ce irin sa" mtsww tayi tsaki ta shige gida ganin Sumy afalo tace "ke ashe wai faruq Aure zaiyi har Da kawon iv" Sumy tace tab kinyi saki na dafe amma" tace "ke ni ba sonsa nake ba sai Handsome" tab'e baki Sumy tayi tace Allah ya kyauta.


*********


Bayan kwana 2 su Muktar suka koma gun Malamin yayi masu bayani kan istikharar Da yayi yace "agaskiya lamarin  nan kan ita wadda kake so tabbas ba Alheri agareku Da ita hatsaniya ce sosai, sai de ita dayar Naga kamar Da sauki abun naku Da ita a tunanina ya kamata ka hkr Da ita husaina saboda kwata -kwata ba Alheri a tsakanin ku. Duk wata Soyayyar ta da ka keji ka fawwalawa Allah domin shike tsara lamuran mutum don ya jarabashi so Da dama abinda ka keso ba shine Alheri agareka ba, sai kaga Wanda bakaso din shine domin Allah shine Masanin gai bu shiisa Annnabi S. A.w ya koyar damu wan nan istikhara din.

Shawara Da zan baka ita hasanar ka koma wajenta ku sasanta idan Da rabon amAure a tsakanin ku sai kaga anyi san nan kayi ta Addua kan Allah ya cirema soyayyr dake ranka domin ba Alheri atsakanin ku."


Tunda Malam ya fara magana yake zufa sai Mahmud ne yace Nalam "mungode kuma insha Allahu zamu bi abinda kace Da shawarar daka bamu."


Malam yace "madalla kai Muktar kayi hkr haka Allah yaso Matar Mutum kabarinsa idan baka samu wan nan ba sai kaga Allah ya baka mafi alheri agareka Mahakurci Mawadaci Allah yana k'aunar masu hk'r" nan yace "ga adduo I zan baka kaje kanayi na samun nutsuwa aranka" nan ya basu takarda sukayi godia suka tafi.



Tun a mota yake share kwalla Shi kansa Mhamud Muktar ya bashi tausayi domin bai taba ganin irin azamanin  nan wanda keson budurwar sa kamar yanda Muktar keson husy haka  ba yayi ta bashi baki ,Muktar yace "tabbas Allah shine sarki mutum bai san komai ba insha Allahu zan k'ok'arin cire husaiina duk Da nasan santa ajini na yake .Zan k'ok'arin Maida shi kan Hassanar Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" Mahmud yace Ameen haka yaje ya sauke Mahmud agida shima ya koma gida agalabaice d'akinsa ya shige ya kwanta kamar mai bacci kamar mara lafiya.



*Bayan Sati daya*



Satin Muktar d'aya yana ciwon so Da k'yar da ban bakin Da Mahmud kemai Da kuma adduoi Da ya keyi yaji zuciayar sa ta samu nutsuwa.


Yau yana office ya gwada kiran Hassy sai ring take bata d'auka ba daga karshe ma aka kashe dafe kai yayi shikansa ya rasa mesa yake kaunar su nan yasa aniyar gobe sai je Abuja don ayita face to face.



Washegari kuwa k'arfe 12 tayimai a Abuja ya sauka inda ya Saba sauka in yazo sai kamar 4 san nan yayi wanka yayi fes  mike ya tafi Osokoro.


Maigadi ne ya ganshi suka gaisa kamilu dake gefen Maigadi shima suka gaisa nan ya rufe gate din muktar ya fito daga motar sa ya cewa kamilu ya sanar Da su Hassy yazo nan kamilu yaje.


Suna zaune Goggg na basu Labarin wani buzu mai saida shayi kamilu ya shiga "yaufa saurayin d'aya yazo yana nemanku." kallon juna sukayi Hussy tace "nikam bami da Shuriem zai zo ba, kode Sabon smSauryain ki ne Hassy ?"


Dariya Hassy tayi "ai yace zai zo nace Aa kinsan bansanar Da mum ba." Gogg tace kudai je ba dadi haka nan suka saka hijab suka fita.



Kujeru 3 kamilu yakai musu wata yar rumfa me kyau Hassy na ganin sa ta had'e rai zata koma Husy tace "sorry sis zo muji dame yazo"haka sukaje sai kallon su yake suka zauna kamar me in ina sai de yayi ma Hassy kyau Amma bata nuna ba, yace "nasan nayi katob'ara Amma ku yafeni domin wlh abin ne yayumin yawa. ya kalli husy na janye Maganata Husaina na yarda Da kaddara Allah dama beyi zamu aureba an bani shawara na dauka." San nan ya juya kan hassy "yace kiyi hkr wlh ba asan raina nayi ba insha Allahu kulawa Da Soyayyata zan tattarasu akanki." Dadi ne ya isheta Amma a fili ta tab'e baki Murmushi yayi yace "Husy ki bata baki ta yafeni"


Husy Da taji komai yayi Mata sauk'i taji dadin matslar ta tafara kaucewa tace "karka damu insha Allahu komai zai daideta kaima sai kayi hkr kan abinda zatai ma domin tayi zuciya."


Yace ngd Husaina nan ta tashi tace "na barku lafiya".d'an binta Da kallo yayi then yadawo Da kallonsa kan Hassy dake latsa waya ta hade rai..




By

Queen Meemi👑



.

.

[4:21pm, 18/03/2017] Queen: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣53❣                    

*March 2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



**********


Sun zauna Jigum-Jigum magana yake Mata amma kanta na duk'e sai latsa wayarta take ,d'an shiru yayi ya sunkwi dakai d'an satar kallon sa tayi  ya d'ago ta juya da sauri  murmushi yayi ta tab'e baki "am Hassy kiyi hkr bisa abinda ya faru tabbas bazan miki k'arya ba naso Hussy Amma naga abun bamai yiwuwa bane haka Allah ya tsara.But now kece nake so dalili dama can ina kallon ki a Hussy pls mu dawo luv na mu."


Dakatar dashi tayi tace "wato ma ba zaka soni don Allah ba sai ta dalilin sis ko? wan nan dalilin ne ma yasa kaga na hkr dakai nikam ka kyaleni" fuuuu ta tashi zuciyarta na tuk'uk'i Da haushi d'an tsayawa tayi gefen fulawa ta saka kuka Allah ya gani tana son Muktar Amma tayi Dana sanin sanin sa tunda sis natane aransa kawai zai Manage da ita as Hussy da gudu ta shige gidan har tana bangaje Kamilu dake tsaye afalon binta da kallo yayi haka ma Goggo dake zaune sai Husy dake karanta Jisnul muslm mikewa tayi zata bita sai kuma tayi waje yana zaune ya had'a kai Da gwiwa tana zuwa tace "muktar" d'an d'agowa yayi yace "hussy ban san meyasa take fushi ba."

 "Hmmm ai dama sai da na gaya maka karka fad'a kace kaine Muntarin da mukai Soyayya dama nasan za asamu wan nan matsalar,shiisa Amma kaki."


"Hussy tun lokacin Da malam ya bani addua ta istikhara bayan yayi mani tasa nima ai naje inayi alal hak'ika idan nayi game da alakar mu da hassy ina jin nutsuwa araina Amma kinga sai da aski yazo gaban goshi komi ya baci.domin ni yanzu na daina Zurfafawa akan komi domin kama taka ne Allah na nashi."


Husy tayi murmushi  "hakane maganar ka Amma karka damu komai nada sila Matar Mutum kabarin sa karka damu zan tattausheta." juyawa tayi ta tafi yace nima na tafi d'an tsayawa tayi ta kalleshi na scan shima haka nan ta girgiza kai jitayi kamar zuciyarta ta karye ahankali ta fada "RABUWA CE SANADIN koma meye daba a rabamu ba da duk wan nan bata faru ba,sai de komi nufin Allah ne" shigewa ciki tayi direct saman benen ta hau gunjin kukan Hassy taji tana shiga ta zauna kusa da ita.



 "Haba hassy kiyi hkr mana tunda ya nuna yayi maki lefi kuma ya hak'ura sai ki yafe duk  maisa ba zaki duba Rayuwata bane tun farko  kinga na abinda yayi silar rabuwa ta da iyayena na fada wani hannun sai Allah ya had'ani da masu sona da kuma wadda ta azzabi rayuwata kinga duk wahalar da nasha rabuwa da iyayena ne ya jawo Amma kinga haka Allah ya tsara kuma nayi hkr lokacin Dana san gaskiyar wace ni,san nan Soyayyr mu da Muntari munyi kamar ba zamu rabu ba munci burin Aure to Allah bai k'addara zamuyi Aure ba rashin yiwuwar Auren mu yasa Shi yabar garin ya tafi karatu,ni kuma kinga har cewa akai na Auri mudi alokacin bana sonsa amma saboda Biyayya yasa na amince hakan ya gudu ganin  bai so na ta dalilin hakan yasa na kuma shiga damuwa da k'unci da wahala Wanda aka kaini aiki kinga Sanadin hakan Naga iyayena daba don duk wad'an nan abin da suka faruba ai nasan da tuni da Auren Muntari akaina toin Allah bai nufa ba,kuma tun rangini ran Zane."



Numfashi ta d'aanj san nan ta cigaba mak'sudin zan cen nan kuwa! Allah yayi kinga Muntari bazai Aurenba Amma kinga Allah sayya sa kuka hadu Wanda kinga tsatson mu  d'aya kinga ni dake twins ne shiisa Allah ya saka masa sommu .Allah mai girmaa mai shirya lamura yanda yaso kiyi hkr Muktar yana da matsayi aguna ko badon so ba ya taimaken abaya plss ki hkr."


D'agowa Hassy tayi "naji zan cen ki sis na gane insha Allahu zan gyara" rungume juna sukai. hassy tace "amma fa sis dole naja class saboda yad'an famin wulakanci" Husy tace kija kad'an don karya tsinkei" dariya tasa suka  tafa sukai san nan suka sauka k'asa.



Goggo tace "oh ni "yasu! wad'an nan yara sautari d'aya daga cikin ku sai tahau sama tana kuka amma sai ku sauko kuna shewa" Hassy tace "Gogg ai kin san twnis akwai had'in head." dariya tayi tace "ja'ira randa za akaiku gida jenku Naga yanda zakuyi"


kamilu ne ya tawo da Wata 'yar roba ya mik'awa Gogg lallene ya kwab'o mata rik'e baki husy tayi "kaide kamilu komai ka iya!" Goggo tace "kamilu kenan ai nida Shi agida muna aiki muna hira ai shiisa ki kaga ko ina k'afata k'afarsa" hassy tace  ai dama na mamajo ne lokacin da zai Aure naga yanda zaki."

Kamilu ya d'ago muna tare domin duk kudin dazan yi to inna tashi gina gida da shashin Goggg agidana" Goggo tace "Allah sarki Autana."

Husy tace "yawwa juya Dady yayi waya da Mum lokacin kina bacci Goggo sunce agaida ke" Goggo tace "ina amsawa"



Hassy tace "sis ya kamata fa gobe muje muyi k'unshi ko bak'i ne da Saloon" tace "oke sai goben."



Washegari weekend ta kama Saturday basu da lucture a Round 3 suka tafi CUTE ZAHRA BEAUTY SALOON & HENNA shago ne Babba suna Saloon gyaran jiki k'unshi, da dai sauransau 'yan mata ne wajen 5 awajen ko wacce da abin da ake mata suna shiga dama matar Musulma ce ta tawo "welcome my special customer" murmushi sukayi ta kalli hassy long time ina Suhaima Amarya? kun b'uya" tace "wlh bama nan ne Amarya kuma sun tafi Honeymoon itada mai house nata."


 

 "Eyyya! wan nan sister naki ce  ko ? Hassy tace "eh" nan ta tambayesu mai za amusu su kace k'unshi da Saloon nan Zahra ta kirawo wata daga cikin yaranta tace ta fara musu Saloon hira suke kad'an- kad'an suna 'yar dariyar su. Jin k'ararar taunar cingum sukayi kas! kas! fus! fus! suka juya Sady ce da Lubna suka Shigo  zama tayi Sam bata kula dasu ba sai da Zahra ta tawo "welcm Sady" me za'ai miki? tace "Steaming" nan idonta ya sauka akan husy taja wani wawan tsaki.

D'an kauye yazo birni" suka sa dariya itada Lubna.


Hassy ta had'e rai suka basar wata ce tazo dan shafa Mata man da ake steaming ta Zame d'an kwalinta kan nan ba tada gashi su hassy suka kwashe da dariya gwi da yara kenan!.


Sady ta k'ulu sosai don tasan da ita suke don dama bata da gashi.

Bayan kamar 1 hour aka gama musu Saloon aka fara k'unshi yayi balain kyau abinka da farar fata,k.k'irr wayar Husy ta kama ruri ta d'auka a slowa ganin Handsome ne a wani yanayi tace "Husby" Sady ta d'ago gabanta na fad'uwa ganin yanda husy ke waya tabbas tasan da Shuriem take nan taji kamar ta shak'e husy.


Jitayi husy tace "oh dear I missd u ,i want see u" Dan Murmushi tai "Okey dea i'm waiting" ta kashe wani d'an fari tayi tace "tweeny yanzu Shuriem zai zo ya ganni wai dama yana kan titin nan zai koma gida" Hassy tace "Weldone dear"



Sady ji tayi zaman ya isheta Allah Allah take agama mata ta k'addamar wa da Husy tsiya.


5:00 aka gama musu sunyi kyau lokacin Shuriem ya k'araso suka  mik'e wayarta tayi K'ara "okey dea gani nan" mik'ewa tayi ta kalli Sady tai murmushi ta fita.


Afusace Sady ta mik'e "Zahra ina zuwa plss "tace oke 


Tana fita taga Shuriem shida Husy a  farfajiya Shagon tsaye sai yaba kyan fulawar yake, gani tayi sun juyo  alamar zata koma shagon ,yana wan nan tafiyar tasa wadda ke fusgar Sady.Zahra ce ta fito zata aje abu Shuriem ya tabmbayeta list d'in abunda za'abiya ya tambayi Zahra tace "oga ai an sun biya tun damu" Sumar sa ya shafa  "no karbi na baki kyauta ne don  naga Amarya ta ta fito sosai" washe baki zahra tayi "Thank u oga" ta koma ciki Tace "Hassy ur Sister agaskiya tayi sa'ar boy frnd gashi handsome ga kyauta."


Hassy tace "eh wlh Zahra ai shiisa Mata ke sonsa Shi kuma yace sai sis Hussy ko garin ba kowa." Zahra tace "ai Sis naki tana da kyau sosai har ta fiki kyau fa!" hassy tace "kai zahra ai kamar mu d'aya."


Sady kamar ta kurma ihu Lubna ma haushi ya isheta afusace ta futa taje ta bayan Hussy ta juyo da kafad'arta 'yar k'ara Husy ta saki don jin kafadarta tayi zafi domin da kyau taja. Juyowa tayi taga Sady na Jijjiga tana harar ta idanuwan ta sunyi ja.


Shuriem kuwa wani banzan kallo ya bita dashi da mamaki akan face nasa irin k'arfin halinta yana huci...


My fans ga wan nan ba yawa abubuwa sun min yawa shiisa bana post kullum..



By

Queen Meemi.👑

[5:32pm, 19/03/2017] Queen: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣54❣                    

*March 2017*


_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_



***********


Zuciya ce ta d'ebi Sady ta kai hannu zata Mareta. Jitayi an rik'e hannun nata da k'arfi an kai mata mari juyawa tayi sukai ido biyu da Hassy fusge hannun ta tayi zatai magana hassy tace "ba kida word da zaki fad'a domin komi akai miki ke kika janyo."


Husy dake sosa wajen ta wurgawa Sady harara itama ta wulla mata tace "wlh duk me zakiji sai de kiji domin Shuriem yayi maki nisa nawane kibi wani sarkin domin nawa ya miki nisa,dafa da yanzu ba d'aya ba karki k'ara saka dirty hand naki ki tab'a ni, ko ki dakeni haba! kizama mace me class mana, ai wallahi da nice ke sai de son Saurayi ya kasheni dana nuna mai ballan tana ina hauka agaban sa wai don ya soni Mutunci ai madara ne,don Allah ki gane  mana  mutum na k'ara girma yana shiga dawa."


D'aga hannu tayi zata mareta tace "kul! Ahir dinki karki K'ara kai hannu Jikina kingane don naga ke saurin hannu gareki."


Sady tace "ke ki sani wlh sai na rabaki da Shi koda bazan Aureshi ba domin kwata -kwata bai dace da yar kauye irinki ba." dariya hassy da hussy suka saka san nan suka tafa hassy tace "ai baby kinyi sake d'an zaki ya girma ,domin wlh d'an hakin daka raina shikan tsone ma ido gashi kuwa tweeny ta tsone idanuwanki,koda yake hausawa sunce samu yafi iyawa.'


Shikam yana  jikin motar sa cike da takaici wani wulak'ataccen kallo ya yiwa Sady domin bai da time d'in magana da ita sai de dole ya taka Mata birki gurin Hussy yace "finest ni zan tafi wacceen yarinyar ta b'atan rai plss kema kubar wajen don zan iyayi Mata kwaf d'aya inta kaini end."


Daria hassy tasa hankali taiwa Sady gwalo.

Hussy tace "Okey dear semin waya" motar sa ya hau ya figa haka hassy ma taja hannun husy suka fad'a tasu motar suma suka ja.


Kamar gunki Tai atsaye ta kasa motsi huci kawai take lubna tazo ta dafa ta "frnd ya da ajinki kina biyewa wadan nan yaran banso kikai magana ba, domin bada kanki kike agaban sa hakan fa bashi zai sa ya soki ba kinyi kuskure don ba kiga yanda 'yan matan can suka fito ba suna kallo haba sai dariya suke suna cewa gaki big gal amma kina abin yara, har cewa suke Husy tafi birgesu."


Sady ta fashe da kuka ban san kalmar da zan miki explain domin sonda nake ma Shuriem wlh ban san ya zan ba , kishi ke cikani duk yayin dana gansu tare plsss help me."


 Liubna tayi dariya "kece ance tun-tuni ga Simple way farat daya zasu rabu kin zauna waike mumina kibar komi ahannuna ko kin mantani ne hmmm."


Sady ta tsaya tace "koma meye ayi wlh sedai ayi biyu babu domin da narasa Shuriem gwanda ko wama ya rasa." da k'yar taje aka karasa musu suka tafi gida.


**********

*Bayan wata daya*


Rayuwa sai dad'a tafiya take komai na wakana daki- daki inda tsakanin hasssy da Sady akoda yaushe husy ke wining sady taci alwashin saita Rabasu  ita da lubna sai shige da fice suke Wanda ni ban san meye ba sai de mungani.


Ayau su Husy  suka gama first semester exams,shiri suka shiga yi domin tafiya k'auye hutu sun bugawa Dady da mum suna son zuwa Bunkure nan Dady ya turo musu da Kudi ta accnt don suyi tsaraba domin Washegari rankaya wa za suyi har su Hoggg inda zasu sauka a kano su kuma awuce dasu.



Washegari da safe misalin karfe 10 suka d'au hanyar kano basu su kaje ba, sai 2 bayan sun sauke su Gogg da kamilu sunyi sallah driver ya wuce dasu Mangalu.



K'arfe 5 sukaje K'ofar gidan malam suka tsaya suka fir-fito suka shiga driver ya bisu da trolley nasu da tsaraba bayan yayi Sallah ya kama hanyar komawa kano.



Jummai ce kad'ai atsakar gidan da gudu husy ta Rungumeta Jummai tace mutan Abuja sai yau tace hassana ya kika tsaya runfar ta suka shiga harda kayan kallo lalle su Jummai anci gaba ko ina fes fes hira ce ta b'arke a tsakanin su da gudu Dan jummai yazo ya samesu yana oyoyo husaina ta rungumeshi suna dariya basu dad'e ba akai kiran sallah sukaje sukayi suka  ci abinci kafin isha malam ya dawo yayi murnar ganin su husy taji dad'i ganin su kowa fess don malam har babur ga reshi nan duk suka firfito da tsara suka basu don har ta gwamma da Dije suka  bayar hassy tace "yaude zanga muguwar nan" Jummai tace ay yanzu ta zama abin tausayi hussy tace tab! Allah ya kyauta hassy tace "ke gobe muje muga k'wak'waf hussy tasa dariya "kai hassy."

Itama dariyar tayi "yo koma meye ai ita ta jawo" Jummai tace "wlh kuwa hassana."


Washegari wajen 11 sukayi wanka suka fita d'an zaga gari Sun wuce ta gidan su Muntari husy tace "yauwa ga gidan surukanki hassy" dariya tayi "to meye saima na shiga" husy tace "ai kuwa da kin bar abin fada".sunje gidan iya suna ta sallama shiru daga can suka jio kamar magana sai suka shiga d'akin iya ce kwacr da alama bacci take taji sallamar su ta tashi "wanake gani kamar husaina" tace "nice iya" tace sannu 'yar albarka suna d'an tab'a hira Husy tace "ina kwa gwamma" iya ta tabe baki kede yar nan kina da kyan zuciya har kike nemanta, ta tafi Bara kin san tunda ta rasa k'afarta shikenan kuma ta tsiri Bara cikin bunkure suke shiga suda sauran mabaratan."


 Jusy tace "Allah yayi mana mekyau" nan ta aje turmin atampha  guda 2 da kudi tace na  gwamma haka ta bawa iya ma sai godia take tace duniya kenn.


Suna fita hassy tace "ke dak'yar nake hadiyar miyau gaskiya suna kazanta" husy tace "ai dama gwamma nada k'azanta hassy tace inna jummai kuwa wlh kamar ba akauye take ba,ga tsafta ga iya girki. Amma naso ganin ta wan nan Gwammar muguwa." husy tace "ai kan mutafi zaki ganta."


Sun koma gida suka zauna husy tace "ashe Bara gwamma keyi? jummai tace tun yaushe wataran ai da dije take tafiya." husy tace Amma "ai Naga dije na zuwa Makaranta. Jummai tace ke tadena taki" "to ina mudi" jummai tace "ai Mudi yayi aure da kyar malam ya sashi agaba dole sai da ya nemo matar,tunda akai auren kullum cikin sulhu malam yake har saboda fad'a kamar kaji ai ni se yanzu nasan ilimi nada amfani domin wlh da ace mudi yayi duk bazai na irin hakan ba har dijen ma ai samun maslaha yanzu tare da malam suke tafiya kasuwa domin Mahaifinki wani zuwa da yayi ya tarar da fad'an duk dama rashin sana'a ne ya bashi jari" husy suka kalli juna da hassy "dama Dady na zuwa? Jummai tace "ai yana yawan zuwa ko yayi aike kafin su koma ai mukam ba abinda zamuce Sai godia." hassy tace "mune da godia."


Husy tace "to yanzu inna Mudin sun Dena fad'an?" tace "eh man yanzu ai yana sana'a sede abinda ba'a rasaba...


 Wayyo Battery low fans ga wan nan ba yawa





By 

Queen meemi.

[4:44pm, 21/03/2017] Queen: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣55❣                    


 *March 2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_




*******


 Tunda Muktar yaji labarin zuwansu Mangalu shima ya tarkato ya tawo, tun da yazo bashi da aiki sai aukin lallashi yake gun hassy har ya samu  ta saki jiki .yauma da suke zaune a soron gidan  gidan Malam suna hira Muktar yace "Hassyna kafin ku tafi nake son turo magabata na, kawai ayita ta k'are."  katsahan taji Maganar tace "haba de?" yace "wlh da gaske don an matsan agida" ta juyo suka had'a ido yace "ki amince" tace "senai shawara domin kasan su Dady basa nan" yace "na sani Amma ai akwai 'yan uwanku kosu sa karb'a" murmushi tayi "dear kabari nai musu waya duk abinda sukace I wll tell u" yace "tnx babyna."Bayan ya tafi ta shiga ciki lokacin har inna Jummai ta sauke dambun da suke itada Husy da gudu taje ta rungume husy tace "albishirunki tweeny" tace "goro" Dan dariya takumai "yau de Muktar yace zai aiko maganar auren mu" husy tace "ke dan Allah!" nan Jummai ta d"ago "me ake cewa ne?" nan suka sanar Mata tace "hmm lalle Matar Mutum kabarinsa Allah yayi bada Husy bace." Nan husy tace ay inna dama komai nufin Allah ne, yanzu sai agayawa su Dady aji mai zasu ce ko?" Hassy tace "nima haka nace mai. Bayan sunci sun sha Husy ta bugawa Mum waya ta d'auka nan ta sanar mata tace abari nan da 1 week zasu dawo domin Arif sunyi hutu Dad'I ma haka yace. husy dake mak'ake da waya ta daka tsalle "Allah ya kawo ku lafiyya" tana gamawa tace "tweeny Mum tace abar maganar next week zasu dawo sai ayi" Jummai tace "hakan ma yafi kuwa."



*Bayan sati daya*


*******

Su Dady suka sauka A Nigeria sai da sukai kwana biyu Wanda yayi dai-de da saura kwana d'aya biyu hutun su Hassy ya kare san nan suka zo Mangalu malam yayi masu tarbar arziki, bayan sun huta Dady yayi maganar Wanda ke san ita Hassy nan ya umarceta data bugama Shi  Muktar d'in waya hakan kuwa akai tayi mai waya bai ma Dade da zuwa garin ba. Direct gidan Malm yaxo asunkuye ya shiga ya ga idasu sun yaba da shi yayi masu bayani Dady ya kad'a baki yace "naji yace shidan me garin nan ne inace shine wanda aka kusa Auren sa da husaina abu bai yiwuba" malam yace "shine" Dady ya had'e rai "Sam ba zata sab'uba" ya kalli Muktar "yaro kayi hkr domin kaga tun farko babanka yace baya so, kaga yanzu idan yaji 'yar uwar d'ayar ce bazai yarda ba" zufa ce take ta karyowa Mukatr wan nan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa Malam dafe hannu yayi domin dama yasan za'arina a sanyaye Mukatr ya tashi ya fita kamar zaiyi kuka Hassy kuwa tana d'akin Jummai tana kuka domin taji yanda akayi sai hkr husy ke bata tace insha Allahu zai sakko.



*****

Shirin komawa Abuja sukayi suma su Hassy suka bisu su Malam sun yi kewar Su ,sunkai dai de titin da zai fudda kai babban titi husy taga Gwamma da taron mata suna bara nan tace  wa Dady Adam tsaya zata bada sadaka tunkan su tsaya su Gwamma sun cika gun, ta zaro 1k ta mikawa Gwamma suka had'a ido Motar su taja. Gwamma sai kuka take tana domin tayi danasanin rayuwar datai abaya.Tafiya akace yankin azaba sai wajen k'arfe 7 suka je Abuja Hassy wani k'aramin zazzab'ine ya rufeta.

Ab'angaren Muktar kuwa hankali tashe yaje gida Goggon sa na zaune ta Ganshi abirkice tace "yadai?" yace "Goggg kunga ni ko! da tun farko ba ai haka ba wlh da Dadynta bazai hanani ba" tace "wai meye ne? Kake abu kamar zararre" zufa ya Goge "yace bazai ban Aurenta ba  saboda da ance bazan Auri bazan auri husaina ba don ba tada Asali yace tunda Jininsu daya,shima bazai had'a iri damu ba sedai nai hkr." Goggg tace "hmm matsala ni na rasa mesa kake san wad'annan mutane wai to yaran nan su kadaine mata? Haba ga 'yar yayata nan Aliya tana sonka kana watsar da ita." Muktar yace "haba Goggo yarinyar da karatun sallah ma Inaga bata iya ba,bafa ta zuwa makaranta" tab'e baki tayi 'kai nifa ba ruwana domin ai da kunya ma muje muce abaka Auren 'yarsu bayan da munce bama kaunar dayar  ai sai suce kwad'ayi ne, sai de ka bari Yabanka yaje" ji yayi garin yayi zafi ya tashi ya shige d'aki kamar mara lafiya.




By

Queen Meemi

[5:20pm, 21/03/2017] Queen: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣56❣                    


*March 2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



********

Kwana biyu duk ya zabge domin son Hassy yaji na shigar shi, ganin hakan ya dage da Addua kullum Sallahr neman zab'in Allah kan idan Auren nada alfano Allah ya tabbar .Amma kullum ji yake yana dada san abun,da k'yar ya koma kano cike da k'aunar Hassy ji yake duk kaunar da yayiwa husy shafar mai ne kan wan nan ,jikinsa na bashi muddin ya rasa ta to zai iya shiga wani hali.

Ta b'angaren Hassy kuwa kullum kuka yauma da take kwance ad'aki tana aukin kukan Mum ta shiga "yanzu ke hassy kan ance ba zakuyi aure ba shine kike kuka karki manta fa Dady yace kar ya kuma jin ambton sa abakin ki." husy ta shigo da Panadol Suhaima abayan ta da tsohon ciki suka zauna Suhaima tace "mum ni ina gani kawai da Dady ya hkr" husy tace "eh wlh Mum ni nasan ta dalilina ne abun ya faru Amma kunga ita da ban ni da ban .Misali da ayanzu ne ai nasan ba zasu k'i Auren ba ,tunda kinga da Usulina Mum ki taushi Dady." Suhaima tace "mum kin san Hassy da sa Abu arai wlh yanzu seta fige" Mum tace "kusan Babanku da wuyar sha'ani musammm aka tab'oshi amma zan taushe Shi" nan ta fita husy tace hasssy ga Magani kisha" dai de lokacin wayarta tai k'ara sunan Muktar ne akai Husy tace "ga shi kuyi magana" jiki asanyaye ta karb'a ta kara akunne can yace Hassyna I missd u so much wlh, u are on my mind & in my heart ban san word dazan miki explaining ba,yanzu hakan  gani Banda lafiya, plss meye shawara."  Hassy ta share hawaye saboda jin dadin kalamansa "yanzu muyi ta addua" yace "ko jiya saida Babana yaje gun Malam shima yace baruwar sa" Hassy tace "insha Allahu zai sakko" Nan sukayi sallama ya kashe.



**********


Kwana 2 tsakani su Malam da Maigari suka tafi abuja domin muktar  ya damu kansa, kullum zarya gun Malam kan ya shige mai gaba ya dawo kamar mara lafiya don har zazzab'i yayi ganin hakan yasa hankulansu ya tashi  musamman Maigari sukaje gun malam sun bada hkr kan abinda ya faru da malam yace sai de suje Abuja a sami Maslaha wan nan dalilin ne yasa suka tafi k'arfe 11suna can sabida da wuri suka tafi yau ne farkon zuwan Malam gidan su husy tabbas sun san Dady ko a masu kudin ma gwaska ne , musammn Ganin irin gidan. ya Tare su a mutunce nan sukaci abinci mai rai da lafiya san nan. Malam ya fara da ban hak'uri ya gayamai mak'sudin zuwan sa. Maigari yace "Alhaji muna neman afuwa da abamu Auren yarinyar nan, domin munsan munyi kuskure bisa rashin sani yanzu hakan yarona yana nan ba shida lafiya  duk akan hakan." Dady yace "banji dad'in abunda akaiwa jinina ba ,duk da labari akaban Amma naji haushi sosai m;Malm yace Alhaji ayi hkr koni nan abin yayi min ciwo domin ba irin k'alubalen sa bamu shigaba ba Amma tabbas nasan Matar Mutum kabarinsa dama haka Allah ya tsara shiisa nima na sakko na hkr." Dady yace tabbas Malam kai me iya bayar da auren yarana ne domin kimar ka da girmanka da nake gani saboda hakan na amince." .Maigari yace "mungode Allah  domin ku kun nuna girma wanda ada ni ban nunaba ngd Allah ya saka" Nan sukayi haramar tafiya husy ta fito suka gaisa da Malam tana murnar ganinsa sunyi hira da Malam san nan ta tafi inda Dady yasa driver ya tafi kaisu.


***********

Farinciki da walwala da samun kwarin jiki Shi ya wadatu a jukkunan wad'an nan masoya, nan duk suka ware suka cigaba da harkokin su inda dangin Mukatr Wanda ke zaune akano wato inda Muktar yayi karatu suka kai kayan Mungani Munaso gidan kakan ninsu Hassy tare da tarba ta arxiki.Nan fa hankulasu  suka huta  suka cigaba da zuba Soyayyar su Nan Dady yayi Umarni da itama husy saurayinta ya motso, bataji d'ar ba alokacin da Mum ke gaya Mata domin tasan Handsome kullum maganar sa yaushe zai turo ,nan ta cewa mum cike da kunya "ai dama ko yaushe yana mun Maganar, Amma idan ya kumai mun! zan gaya mai" Mum tace "tom 'yar Mum .da hayaniya Hassy da Arif suka shigo falon "kinga kibani ipon dina" tace "bazan bayar ba sai na ga wani abu" haushi yaji yace "ai gwandama duk ku k'ara gaba dama kun cika mana gida" Husy tace "ka gaji damu ko? sai muntafi zakai missn d'in mu" Mum tace "atoh sai de yayi ta bin gidajenku."



B'angaren Shuriem kuwa...




By Queen Meemi👑



[5:44pm, 24/03/2017] Queen: ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣57❣                    


*March 2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



*_Fans kuna hkr wlh wutar muce take lalacewa shiisa bakwa ganin ina typin kullm amma in aka gyara komai zai nomal .Da tuni mana gama book. Godia nake masoyana Masu support Dina Allah yabar kauna.❤❤_*



*********


 B'angaren Shuriem kuwa yana zaune a office aiyuka sun hade mai yana so ya kira husy ba dama, nan yayi sauri ya gama ya mik'e cike da kasala ya umarci sakatariya data getta gun Da sauri ya fita dai -de lokacin Sady na cinno hancin Motar ta, ta glass ta gano Shi yana k'ok'arin shiga motar sa da sauri ta fito amma kafin tayi magana yaja motar sa @360 yabar gun.

D'an tsaki tayi ta shiga tayi ribas tabi bayan sa, b'at ya b'ace mata nan tad'au wayarta ta kirawo shi ganin ring yayi tsaki yak'i d'auka don yasan 'yar nacin ce. ganin bai d'auka ba yasa ta kirawo Lubna daga can ta d'auka "helo Sady" tace "k'awas da matsala fa wlh Sam munyi sab'ani kinga yanzu ina dialling no d'insa baya d'auka." Lubna tace ba akwai whtsp ba? ki tura mai tanan tunda akwai a wayarki dayan  ba matsala bace gobe ma rana ce" Sady tace hakane dea shisa nake sonki ngd" nan suka kashe a tare.



********


Direct gidan su ya tafi da mMaminsa yaci karo tace "yawwa D'an halak kaji ambato yanzu muke maganarka nida Dadynka kande magaanr aure yace "Momi har guda nawa neke" tace "tafi can" murmushi yayi  ya zauna "me kuka dafa yau mami?" "ba irin cimarka bace Alala nayi" yace Mami bani naci I'm feeln hungry" kallon sa tayi "kaine ance kayi Aure ka zauna ruwan ido ga 'yan Mata na sonka kojiyan nan wasu sunzo gaisheni suka ce kai ogansu ne nikam nasan da biyu" Shuriem yace "Mami suwaye?" tace "kaini rabani idan zaka fito da mata kayi domin kaga azumi ya kusa nafiso ace da aurenka." Dan sosa K'eya yayi "mum lokaci kawai nake jira amma na samu yarinyar anan Abuja take." Mami tace "Allah yasa dai domin in bakai Magana ba sai de kaga Amarya ad'akin ka." Dariya yayi san nan ya mik'e ya shige bedroom nasa, tunani yake yaya ma za'ace wata tazo shidai yasan ba finest bace saboda tana da tarbiya da kunya amma yana tunanin ko Sady ce Dan tsaki ya saka "dis gal na da problem wlh" k'arar Msg ne ya shigo aka rubuta kamar haka: ka bud'e whtsp naka kaga abin mamaki.bai kawo komai ba ya bud'e msgs suka shishshigo can yaci karo da wani picture daya razana shi bai Gasgataba sai daya kuma k'ura ido tabbas itace amman Sam ya kasa Gasgatawa take kansa ya fara ciwo nan ya tura Ma husy hoton ak'asa yasa husyna meye wan nan? dama yaudarata kikeh? Bayan ya turamata ya tashi yana kai-kawo idansa yayi ja tare da dafe kai abincin da baici ba kenan.


********


Dariya suke k'yak'yatawa da alama sunji bauri domin wani Film suke kalla na Comedy k'arar msg d'inne ya shigo kan wayarta  Wanda alarm d'in Special ne ta sawa Shuriem nata  da sauri ta bud'e taga yace ta bude whtsp bud'ewa tayi na d'an mintuna ya shigo d'an baya tayi ganin Hoton nan hankalinta ya tashi. d'aka Mata duka hassy tayi "kinga kalli nan" jin batai magana ba yasa ta juyo taga tana hawaye husy tace "hassy kinga me akaimin?" Karb'ar wayar tayi taga Hoton Hassy ne itada wani saurayi Wanda ma bata san shi ba ya mak'alk'aleta hannunsa na cikin rigarta ja da baya tayi "tweeny plss kece kuwa?" husy tace "nasan kin trust Dina kin san ba ni bace wlh sharri ne" ta fashe da kuka hassy tace "ba mamaki sis domin duniya ta b'aci tabbas za 'aiya abinda yafi hakan domin nasan aikin Sady ne to wlh ba zamu yardaba ai wan nan b'ata suna ne." sai huci take ta karb'i wayar hussaina ta lalubo number din Sady k'irr ta d'auka Wani wawan tsawa hassy ta yiwa Sady "ke hawainiyarki ta kiyayi ramarmu! duk makircin ki wlh ba ki isa ba ,macuciya me farutar saurayi." dariya Sady tasa "ai na riga na gama da ku domin Shuriem ya barta kenan" kafin hassy tayi magana ta kashe dab'as ta zauna kan gadon ta dafa bayan Husy "dama nasan Sady ce to wlh dole mud'au mataki" husy ta share hawaye  "ni na rasa ma tayaya Naga hotona sai de kayan ne kin san bamuda irin sa Amma mayafin jikin kin san ina da ita kuma ga face dina nice" nan ta kuma fsshewa da kuka ta kirawo Shuriem ya dauka husy ta fashe da kuka har ransa yana jin kukan amma bakin ciki ya hana yace komai "wlh bani bace sharri ne yanzu Sady ta gayan confusing ya shiga cuz ga face nata b'aro- b'aro duk da awaye yake yasan tabbas za'a iya had'awa Amma bakin ciki da kishi yake inyaga hannun gardin a rigarta sayyaji haushi sai yaga kamar husyn ce duk da ya santa da tarbiyya bece komi ba ya kashe.



**********

Kuka tasa "shikenan ta gama dani ta cucen haba" hassy tace "barta idan tasan  wata aiba  tasan wata ba,wlh sai mun nuna mata ita k'aramar 'yar Air ce" haka dai sukayi ta fesa maganganun inda hankalin husy ya tashi.

wajen 8pm  husy na zaune kowa na hira itakam ta kurawa tv ido kawai Wayarta tayi K'ara ganin Sady ce yasa tayi maman bene ta d'auka afusace "ke mara kunyar k'arya karki sake kirana" Sady ta fashe da dariya "ai kadan kika gani badai zaki takara dani ba! hmm ke clean din kwanan nan ma, balle ni da acikinsa na tashi, to wlh akan Shuriem sai de komai ya faru ,kuma ki sani saina watsa hotunan a media kowa yayi tir dake." husy da jikinta ya hau rawa "idan baki fasa ba bakya k'aunar Allah da Annabi, ga fili ga maidoki" kit ta kashe ta fashe da kuka. dai-de lokacin hassy  ta hawo ta tsaya husy tace "kiji wai zata watsa a media" hassy ta dafe kirji "tab! wlh dakwa ta jangwalo" Nan suka shige daki sunfi awa suna maida zance .Mum ce ta shigo ta tarar husy na kuka tace "meye?" nan suka kalli juna da hassy tace "bakomi mum idona ke ciwo" tace "kuma shine kike kuka?" "Aa momi hawaye ne" juyawa tayi zata fita "sai gobe da safe kuje adubaki" tace "to momy."

Shuriem kuwa kishi ke d'ibarsa kamar ya kurma ihu tabbas zuciyar sa yasan ba husy bace amma jikinsa ya kasa aminta domin daya gano hannun gardin nan sayyaji wawan haushi,duk da yasan ba ita bace wayarsa ya dauka ......





By

Queen Meemi



.

[5:32pm, 25/03/2017] Queen: . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣58❣ 

                   

  *March 2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_




 *********

 Bayan kwana biyu duk abu ya dagule domin Shuriem ko husy ta buga bai d'auka itama sai ta share Amma zucciyar su na manne basa daina tunanin juna,tana cikin bacci k'arar shigar msg ya shigo ta dauka ta duba Shuriem ne ke shaida mata anjima zai shigo, bai ji mai zatace ba ya kashe Amma ya matsu yaji voice nata.

      5:00 Shuriem ya cinno hancin motar sa cikin gate din ,ganin wani saurayi yayi a d'an nesa da gate din gidan ya basar  da sauri saurayin yazo yana k'ok'arin yi mai magana ganin hakan ya tsaya yace "wa kake nema ne?" Yace "nazo wurin husaina ne" "meye alak'arku juyawa yayi "gal frnd nawa ce" Shuriem yaji mamaki ya kamashi bai sake magana ba yabi k'aramin gate ya shiga inda suka Saba zama  kamar mintuna sai ga tanan ta fito ya k'ura Mata ido santa da kishi ya kuma kamashi kanta ak'asa ta zauna saboda kunya da k'yar take magana yace "husy nasan bake bace Amma xuciyana ta kasa hkr wlh wani kishi nake" dagowa tai ta kalle Shi "am  so sarry dea" yace "nasan wan nan joblesss yarinyar ce Amma karki damu ina sane da ita duk ta gama shirmenta zan maganin ta" nan da nan suka manta batun suka hau hirar su maidadi.



********


Hayaniya suka ji Maigadi da wani nan. husy ta daga kai ganin kamar kokawa yasa ta kira mai gadi ya tawo tace "meye? yace "yar Dady ai wani ne yazo wajenki wai ni kuma ba aban list da Shi ba" Dan shiru tayi tace "ka koreshi saboda ban San shi ba",Shuriem yace "no barshi yazo don tun d'azu na ganshi sa gudu mai gadi yayi ya koma yace ya shiga gyara riga yayi ya shiga farfajiyat gate din ganosu da yayi yasa yadan murmusa ya fito da wata wayar sa ya kira wayar husy nan ta fara ring @ten times yana kira tana kashewa don bata daukan no daba ta sani ba,Shuriem ne ya kalleta "finest ki daga mana"  nan ta d'aga "waye? yace "juyo ki ganni ina kallonki" jikinta na rawa ta juya tare da kashe wayar Shuriem ya jingina da kujera baice k'ala ba, ganin hakan saurayin ya k'araso yace "Aa sweat heart tun a school nake kiranki kin share haba kodan kinyi sabo shine zaki watsar dani" husy ta mike tsaye "niii! Ta ina na sanka,pls kace  ban sanka ba plsss ka fitar mana agida." murmushi yayi "husaina kenan! ba kyau yaudara don kin samu wancan had'ad'den to nima ai ba baya ba ,duk tsiya dai munyi luv sosai don haka ga pictures da muka d'auka duk da kince bakyaso dan gulma nan ya fito dasu ya watsa a kan table ya kalleta beauty sai minyi waya" ya juya ya tafi. Hannu tasa aka wlh ni bansan Shi ba sharri ne d'aya bayan d'aya yake kallon hoton kala -kala wasu rungume da shi wasu suna kallon juna Shuriem kuma Afusace ya mik'e ya watsa Mata pics d'in zatai magana ya dakatar da ita "bana son any word da zata fito daga bakinki, saboda komai na gani da ido na" juyawa yayi ya fita ransa adagule.




*********


Da gudu ta shige gida ta haye bene tana kuka lokacin hassy na aiki kan laptop ta fad'a gadon tana kuka hassy tace "meye?" nan ta nuna Mata hotunan San nan ta kwashe duk yanda akai ta gaya Mata hussy ta fara huci "lalle sady kinyi kuskure."dafa husy tayi tace kiyi hkr gobe zan San yanda zanyi don rana tayi yau."k'aramin zazzabi ne ya rufe husy wan nan kenan.


  *Washegari*

@12am

Hassy ta mik'e tsaye tace "zo muje sis nasan inda zan kai atabbatar min da hakan" husy cewa tayi ba zata ba nan hassy ta cewa mum zata karb'o books nata take ta zari motar ta wani had'ad'den studio taje tana shiga suka gaisa da wanda ke bakin wajen nan ta zauna ta tambayeshi yanda ake had'a picture idan a rabe suke misali mace da namiji da yake sun saba dama dashi nan ya bar aikin ya d'auko wata computer yana nuna mata sample har da zata nuna mai pic d'in sai kuma ta fasa don bata so aga face na 'yar uwarta. Hotuna ne birjik na Mata da Maza sunyi kyau a gabanta yayi editin ya cire kan wani ya sa akan wani saurayin sai kace shine haka ya nuna mata kallonta yayi "kin gane yanzu" tace "eh" nan ta d'an zauna sai tace "nikam ban Naga pics din Naga style masu kyau" mika Mata laptop d'in yayi ta dinga gani zaro ido tayi ganin saurayin da aka had'a pics nasu da Husy kuma ga budurwar agefe wadda aka cire kanta aka sawa Husy hannunsa cikin rigarta wani wawan nishi ta saka tayi murmushi Alhmdlh nuna ma salihu tayi tace ya tura Mata pic d'in  a waya hakan kuwa take ya tura maata ta bashi 1k ta tafi tana murna.


********


Da gudu ta shiga d'akinsu husy na zaune tana aikin dube duben waya sai lek'a groups take tana dubawa Allah yasa kartaga hotunan nan domin tasan Halin Sady zata iya watsawa hamdala tayi ta kashe data k'ululin bak'in ciki ne ya kamata don tunda jiya Shuriem yazo da abinda ya faru ta kasa sukuni ta rasa wane mataki zata d'auka jitake kamar tace ta fasa auren Shuriem din ,kuma da mamakin inda saurayin ya santa da fata tayi ta dago kai "tun dazu naga kina tunani ai kisani komai yazo end na samo bakin zaren"  ta zaro wayarta ta lalaubo Gellary "kalli nan"  da sauri ta karba tace "ke kuwa ya akai kika gano?  hasy tace "haba yanda take da ilimi haka muma" zuwa tayi akai editin aka cire kan wan nan ladyn aka saka naki ai duk ya nuna ke bakya ce anyi wani abu ba" "Amma Allah ya isa wlh ban yafewa Sady ba." nan ta fashe da kuka "gashi Shuriem yana fushi tun abun fa ya faru jiya ai wallahi sai Allah ya sakamin,ni bansan taya ma akai saurayin jiya harda no dina ya kira fa." Hassy tace kede yanzu kawai musan yanda za'ai na nunawa Shuriem ya tabbar da Gaskiya, bayan hakan zamu gano waye wlh bazamu yardaba,kuma dole ta hakura sa Shureim" husy tace "kyaleshi tunda har ya yarda , ni na hkr na barmata Shi bazan iya jidalin nan ba" Hassy tace "kiyi hkr kin san fa makirci dole yaji ba dadi .Amma batun wai ki bar mata Shi bata tasoba saide in shine yace ya fasa" nan ta mike "bari naje nai wanka don na dauko rana duk da a mota nake amma ina dan jin zafi,tsunduma kogin tunani husy tayi wanda bata san bacci ya kwasheta ba tare da mafarkin abin sonta.



By

Queen Meemi.👑

.

. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣59❣                    

*March 2017*

             


_*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's*_



*********


Washegari kuwa wajen 10 sai ga Sady a office d'in Shuriem yana zaune yayi shigar  shadda hartin da wando farare k'al -k'al ya turo hularsa gaba yana ta Rubuce -Rubuce tura k'ofar tayi ta shiga tana karai raya sai kace tarwad'a kujera taja ta zauna bai d'ago ido ba,  tadade a zaune san nan tace "Shuriem kaga abinda nake fad'a ko? kaso mai sonka don hussy ba sonka take ba, domin da idona a sch nake ganin ta da wan nan saurayin" nan ta zaro pic ta aje agabansa. "saurayinta ne sosai kowa ya sani don haka ni Sady ni ce mai sonka kayi tunani idan kayi Accept  you can call me" da sauri ta mik'e har taje k'ofa yace "wait" nan ta tsaya yace "zoki d'auke haukanki kuma ki saurari Punishment dina san nan nace maki bana yinki, plss ki je gun masu sonki su aureki maana! Domin duk wani makircinki sai de ki gama amma mutu karaba nida fines kingane"

Murmushi tayi ta fita Amma ak'asan ranta kamar ta kwanta k'asa tayi birgima haka taje gida. Sumy na had'a wasu kayanta ta  Sady ta zube a gado "sumy nayi-nayi ba irin abinda banba handsome ya kasa ganewa ya nace wa waccen fool gal d'in dame tafini? dame Allah ya rageni? harda zai na min hakan"nan ta fashe da kuka Sumy ta tab'e baki "ai dama duk Wanda yasai Rariya yasan zata zubda ruwa kuma duk abinda kayi za'aima, karki manta irin wulak'ancin da ki kaiwa faruq wlh nasan ko rabin sa Shuriem bai maki ba, nadai gaya miki kiyi karatun ta nutsu kin dace kinada farinjini ma don Naga wani kamal na sonki yana zuwa shima kina wulakanta shi to kiyi ahankali tun kan dare yayi maki."Tsaki Sady tasa ta tashi tace "naji kuma ban d'auka ba" "jiki magayi ai" cewar sumy.



********


Husy kam da safe data tashi sukayi break suka tafi School itada Hassy domin lucture safe ce dasu. Kamar k'arfe 11 Hassy na zaune a Captaria tana try Number d'in Shureim 3 missd call san nan ya d'auka suka gaisa tace "don Allah kazo Cumpus namu akwai wani Abu da zan gaya maka da zaka san gaskiya plss." "Okey hassy zan zo after 2" nan ta kashe ta tafi Lucture.

@2:00 Shuriem ya shiga school din ya faka bakin Bishiya ya kira Hassy dama ta dad'e da fitowa ta fito tazo inda yake ta gaida shi san nan tace "Shuriem hak'ika duk abinda ya faru wlh sharrin Sady ne, domin da bakinta ta gaya mana duk plan ne donta sameka haka saurayin da yazo jiya shima plan ne plss ka gane. bari kaga" nan ta d'auko Pic ta nuna mai ya karb'a yaga asalin pics d,in yace "to na jiya fa? tace shima duk had'inta ne, kaga kenan baruwan husy bai kamata ka d'ora laifi akanta ba" jikinsa yayi sanyi."Hassy ina son sisi naki ne shiisa nake jin kishinta, wlh duk da nasan ba gaskiya bane Amma na samu hujja insha Allahu zan maganin ita Sady." nan tace "yawwa Shuriem." Dai de lokacin Hsusy ta tawo sanye da dogon hijab bata kalli inda yake ba shikam idansa na kanta wani Birgeshi tayi wani d'an Murmushi ya saki ta kauda kai  tayi gaba  ta shiga motar su .Hassy tayi mai sallama suka tafi ya dade a tsaye yana Murmushi ya shiga Motar sa ya d'auki hanyar fita.

 Hasyy dake kwarara gudu a Mota ta kalli Husy tace "yanzu komi Normal, kiyi hkr nasan zai taushi zuciyarki, itakam Sady daga wan nan ta daina domin zami maganin ta".husy tayi murmushi "nifa kaina yau ciwo yake" Hassy tace "ba wani ganin na k'arfen ne ya birkita lissafinki" .Dariya suka saka 3:00 suka shiga gida.




**********


Shuriem kuwa adai-de layin da zai shiga gidan su yaga saurayin nan da yayi pretending as  saurayin Hussy nan ya sha gabanshi Saurayin ya fito zaiyi bala'i yaga Shuriem nan ya sandare don ya ganeshi, a nutse Shuriem ya tako ya tsaya yace "wato han baka kud'i ake ka kashe aure ,ko ka b'ata da d'ad'diyar soyayya ko? to kayi na farko kayi na k'arshe" nan ya d'auko hotunan ya mik'a mai, "kaine ko zakace ba kai bane na asalin  kuma kazo jiya" nan ya dabirce take Shuriem ya bugawa Police dake kusa domin ya damk'e hannunsa ya kasa kwacewa, ba'a dad'e ba sai gasu nan yace atafi dashi anjima zai zo....

Sai da Shuriem ya koma gida yaci abinci yayi wanka yadan matse barcinsa gajiyar sa duk tabi jiki san nan wajen karfe 5 :00 ya mik'e ya tafi police station zuwan sa Sauryain nan ya gaji ga yunwa nan ya zauna yayi wa DPO bayani kan abinda saurayin yayi don ai musu tsakani,  yace ayimai hukunci nan suka tambayeshi dalili  ya fad'a kan Sadyce ta saka Shi yayi aikin ta biyashi.ya d'ora da cewa suyi mai rai domin Shike dawainyar gidansu 

Nan DPO yace "yi mana shiru kune masu d'aurewa karya lasisi" yace ya a kirawo ta nan saurayin yayi kiranta kan tazo ya samu wata idea, 6 dai -de motar ta ta k'arasa Station d'in tana shiga suka gaya Mata abinda ke faruwa nan hankalin ya tashi suka tambayeta sunanta ta gaya musu. DPO yace "wato ke 'yar gidan Alhaji tanko ce ko shine kike haka, lalle kuwa zan sanar mai" jikinta yayi sanyi Kudi ta zaro ta aje ma Wani kurtu sukace Aa Wanda ya kawo case Babba ne sai de tai hkr.Shuriem ya shigo wajen suka gaidashi  ya zauna gefen da Sady take  ya kalleta "yanzu sai kibi wani sarkin don husy ta miki nisa." DPO yazo yace "ya sunan yarinyar da sukaiwa haka ,nan ya fad'a Sunan ta dana babanta hankalin DPO ya tashi yace "wait itama 'yar manya ce ashe!" ya kalli Sady "dole mahaifinki yaji."nan ya dauko zai kira tace "plss kayi hkr karka fada"  "dole na fada domin idan sukace basu yarda ba fa?"

Dady na zaune dawowar sa kenan wajen 7 DPO ya kirashi ya sanar mai cikin tashin hankali ya tashi yace "yanzu zai zo Umma ce dama a d'akin tace "meye?" yace "kinji Sadiya ce ta cangwalo wai suna hatsaniya da yar Ambassado,r komi ya kaita l yanzu Shi saurayin ita yarinyar wai ya kaisu station ita da saurayin da tasa yayi ma dayar sharri, wama ya bata izinin fita da dare?" nan tace subhanallah tashi yayi ya tafi driver din sa ya mika shi.



**********



Sady ido ya raina fata domin Abun kunya ne agareta .DPO ya umarci da Shuriem yace itama Husy tazo Ana nemanta. Shuriem yace basai tazo ba ga shaida duk agunsa. zuwa Dadyn sady duk aka gaya mai aka nuna mai abinda tayi agun ya wanka Mata mari ,yace "ni zaki kunyata da girmana! wato ki b'ata wa wata suna ko? akan son zuciya kuma 'yar Ambassador to ki sani afagen mulki ma yana sama dani donni yanzu bana cikin mulki don haka dole na baki Punishment" "Dady Kayi hkr" yace "yi min shiru" ya kalli Saurayin kai-kuma anyi Sahorami da za'a baka kudi kayi shirme" nan yace wa DPO itama asata a cell d'in kya k'ara  hankalta .

Shuriem cike da girmamawa yace "ba za'ai haka ba, kawai de ta saka hannu nima na saka bani ba ita, kuma ba ita ba husaina domin tana yawan Cusguna mata don haka ai musu Tsakani." DPO ya kawo Paper ta cike tana kuka shima haka Shuriem ya cike shima. Saurayin kuma akai mai afuwa kan ya kuma sai yayi watanni acell nan duk suka tafi. Dady kuwa kamar ya cinye Sady fad'a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.

Saurayin kuwa da gudu ya fita yana mai dana sani domin sun wulakanta shi bai tana zuwa police ba kan wani lefi ba. Shuriem kuwa dad'ine ya kamashi domin yasan ya rabu da naci .


Muje zuwa.


By

Queen meemi👑




. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣60❣                    


_Sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_    




This page 4 u Anty sis much luv❤



 *********


Tafiya suke amota ta inda Dady yake shiga bata nan yake fita ba,fad'a sosai yake mata har driver yayi parkin a k'ofar gidan su ta fito,itakam sharb'ar kuka take kamar me d'akinsu direct ta zarce Sumy na danna waya tace "meya faru sis naganki kina kuka" ta d'ago "na rasa Shuriem wlh ba zan iya rayuwa ba shiba" dai -de lokacin  mama ta shiga d'akin fuskarta atamke tace "sai kuje Dady na kira" jikin Sady ya fara rawa duk rashin kunyartaa tana tsoron Dady ,direct falonsa suka shiga yana zaune sai fad'a yake kumayi Umma azaune tana bashi hkr .

Tsawa ya kuma dakawa Sady Sumy tayi gefe suka zauna ya kallesu "wato Dan kunga na sakar muku ko! shine kuke abinda kuke so Musamm ke Sady Naga kanki rawa yake, yanzu inbanda lalacewar zamani har Sady ta santa had'a tuggu akan saurayi dan zubar da kima, kina binsa yana gudunki, wato har ma sharri kikewa Wacca yakeso ko? to Anyi na farko duk cikinku yanzu kuna lvl 4 ko? to ya isa kowacce na bata 2 week ta fito da Miji in ba haka ba zan mummunan sab'a muku" ya kalli Sady "shashar banza da hofi tashi ku bani gu. Asanyaye suka mik'e suka fice. Umma tace "Amma Dady a sauk'ak'a" ya d'aga Mata hannu "dama ku ke sakar musu suyi abinda ransu ke so to ya kau! wlh duk waccen ta sab'awa Umarnina za taga hukunci bazan zauna  yarinya ta janyon abin fada."



*****



Tunda suka shiga d'aki Sumy hankali atashe ta kalli Sady dake kuka "ni bansan ya zanba babu Wanda fa ke zuwa guna" Sady ta d'ago "nifa inba Shuriem ba bazan Aureba" Sumy tace "ke bakya jin magana kin faye taurin kai, ni kam dama kinga Uzaifa na sona nice dai nake tsoron sakar masa Saboda yaudarar da Nazi yayi mani sai nake gani kamar shima haka ne. Amma kinga yanzu zan kulashi." Sady ba tace komai ba, tayi shiru abin duniya na damunta .



******


Ab'angaren su Hassay kuwa yanzu hankalinsu ya kwanta domin Shuriem y bawa husy hkr sun shirya inda yake shaida mata manyan sa zasu so ai magana, tayi murna ta sanar da mum .Suna zaune suna hira Wayar Husy tayi K'ara taga sunan miji Suhaima nan ta d'auka yake sanar mata Haihuwar Suhaima wani ubn tsalle ta daka ya shaida Mata an Samu Baby Boy dukkansu kowa ka kalla farin ciki wajen k'arfe 2 suka je asibitin lokacin Suna shirin tafiya don an sallamesu hassy ta k'an-k'ame Jariri Mum ta roki Safwan da yabar Suhaima tazo gida wanka, bai musa ba don yasan za'afi kula da itaa agidan,kafin yamma Dangi kota ina don jin haihuwar musammn b'angaren Safwan. Hassy da hussy kamar suke jegon yauma suna zaune Ana shirya baby wayar husy tayi K'ara ta dauka "my husby" yace "ba wani nan!! kin manta dani ko? tace kasan munyi d'a dole kai hkr" yayi dariya "zan kamaki ne  tunda bakya missn dina." "Anjima zanzo barka" tace "to."

Da yamma sai ga shinan yazo yauma fararen kayan ne jikinsa ya dade azaune sai ga husy rik'e da Baby ta shiga d'akin baki yana ganin ta ya tashi ya karb'i Babyn yace "wow Masha Allah Amma babyn me kyau dashi" tace "agabana!" yace "to meye kema next yr da naki" ta rufe fuska "haba dai aini sai na dad'e" dariya yayi yana yaba babyn wata leda ce babba shak'e da kaya ya mik'a Mata "gashi abawa Maijego." Hussy tace "lalle harda hidima!"  "To meye yiwa kaine" haka ya gama ganin baby ya tafi.*Washegari*

 Su Anty da Mubarak suka zo husy tayi murna suna zaune suna hira. Suhaima na gyara baby hassy tace "Anty ina wan nan Sadyn?" tace "tana nan" suka tuntsire da dariya .Hassy tace "ai bata da kirki kin san me taiwa husy kuwa!" Anty ta girgiza kai "sai kin fad'a" nan suka gaya mata tace "biri yayi kama da mutum, ashe shiisa Naga Dady ya kafa musu doka" hassy ta tashi danjin gulma "ai gwanda" tace "ai cewa yayi duk sufito da miji nan da 2weeks" dariya suka sa "Ai maganinta kenan! ba ita mugunta ba" Anty tace "ai Sady sai ahankali kinga da dasu Zuby nanan duk itace ba ruwanta. Amma Ana musu Aure taga fili ta fitsare." husy tace "eh nima.nayi mamaki donfa muna shiri da ita  lokacin dana zauna gidansu." Hassy tace "ita ta sani saita tafi neman miji ai" Suhaima tace "bar 'yar banza ai ni yanzu ba sosai muke wurd'aba duk kan abinda take muku."Anty tace "Allah ya kyauta."





***********


Sati ya za gayo akai suna yaro yaci suna Muhd nan suka cigaba da taya suhaima jego.

Ranar Asabar iyayen Shuriem maza suka zo lokacin Dady na nan su uku akai musu iso nan suka nema Dady ya amince atake suka zaro 200k aka bada kud'in mun gani munaso wato engaged. zo kuga murna gun Shuriem da husy  ,nan Dady yayima Mum bayani tace "Aa kace auren yara 2 zanyi to Allah ya kaimu" Dady yace "Ameen" tunda Sady taji zan-cen kawo kud'in Husy gun Anty yasa ta kuma tashin hankalinta harda su Zazzabi ga Dady ya addabesu su. Hassy kuwa kowacce yanzu Normal suke dame santa suna zuba soyayyrsu inna Jummai taji dadi wan nan kenan.


*Bayan Sati biyu*


Yau satin da Dady ya dibarwa su Sady ya cika. nan ya kirawo su kowacce ta zauna ya kalli Sumy tace "Dady akwai wani Uzaifa mun dai-daita da shi" yace "to umma" tace "amma sai de fa bashida kudi sosai" Dady yace "ai anshani na warke yanzu ga Zuby kullum bani ke taimakonta ba! duk kuma kud'in sa fawwz dana babansa kin san ya zama matsolo baya wadata ta,ni yanzu kawai inde yaro na da mutumci zan bashi kuma zai iya rik'eta" yace "ke Sumayya na gama dake saiki ce ya aiko." ya kalli Sady wacce ido ya firfito "ke kuma fa? ta saka kuka "Dady wlh ban tsayar ba ,don Allah kayafen! nan da wata daya zan samo" da yaki yarda sai da su mama suka sa baki ya amince, nan ta mik'e suka tafi daki Sumy tace "kinga abinda nake gaya miki ko! gashi nan ba shureim ,ga Faruq yayi aurnsa tun-tuni sai kamalu Allah yasa dai baki koreshi ba shima" Sady tace "ke ni ki kyaleni" sumy tace "ki bugawa Kamalu "muji mana"! ganin Sumy ta dameta yasa ta bugamai  ta dade tana ring San nan ya d'auka "ya dai lafiya?" tace "Aa dama kwana 2 na jika shiru ne" yace "ba komi kawai naga bakya sona ne ni kuma bana jurar wulakanci shiisa na hak'ura yanzu haka na samu wacce muka dai- deta an kusa engaged ma Allah ya hadaki da rabonki." dama a hands-free tasa nan Sumy tace "wata sabuwa kingani ko dama na fad'a yanzu baki ga tsuntsu ba tarko" Sady tasa kuka "wayyo wlh ni banso Dady ya had'ani da kowa" Sumy tace "ta baya ta rago dai dama ranar Dana sani ake tsoro ga mara daukan shawara."



By

Queen Meemi👑




. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣61❣                    

_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_




 ********


Haka Rayuwa tayi ta tafiya inda har an samu wata uku cir da maganar da Dady yayima Sady Amma shiru ba mashin shini domin duk samarin dataiwa wulaknci duk sun samu masu sonsu,kuma basa zuwa, kullum sai -de ta rok'i Dady daya k'ara Mata lokaci ak'arshen satin nan ne yace mata nan da sati zai yanke hukunci akanta.kwana biyu tsakani Sady duk ta tashi hankalin ta domin tsoron kar Dady ya had'ata da wani tsohon don yanda yaji haushinta ba lalle ya saurara mata ba.yauma tana zaune wajen k'arfe hud'u itada Sumy suna kallo azahiri ba kallon take ba sai tunani wanda ya Zame Mata tamkar me Sallama sukaji Anyi sallama.Lubna ce ta shigo tana murmushi da gudu Sady ta Rungumeta "Oh! my Frnd I Mssd u lubna" tace "nima haka" nan suka hau hirar yaushe gari Sady tace "ya katsinan" tace "Alhmdlh nafa kusa Aure" Sady tace "ke Dan Allah wazaki Aura? Ashobe ta zaro "gashi anko nan da 3 month sunan mijin Kamalu Sady tace "nunan pics nasa" nan ta zaro waya ta nuna mata dafe kirji sady tayi "me zangani! cin amana" lubna tace "name fa?" "Amma kinsan dai saurayina ne sonawa ina mai wulknci agabanki bayan ke kike ma zugani" lubna tace "lol to don tsohon saurayin kine sai akace ni na wulak'anta Shi alokacin kina mayen son wanda bai sanki shiisa kika kasa gane masu sonki" Sady tace "amma kin asara lubna Allah ya isa muguwa" Tabe baki tayi Amma Sady baki da wayo dame Allah ya ragi kamalu kika watsa mai kasa a ido nikam yayi min don haka kinga tafiya ta in kinga dama kiyi ankon" nan ta aje taai hanyar k'ofa Sady tabita "wlh lubna bani bake, muguwa Allah saiya sakan." Lubna tace wlh sai de ya tsaya akanki domin bance ki wulakanci ba waike gamai farin jini to ai ga irinta nan" ta fita tana juyi da gudu Sady ta koma gida Sumy dake jin duk abinda suke tace "lalle duniya budurwar wawa ai yanzu kyayi hankali Sady,kisan irin kawayen da zakina yi",ita kuwa kukanta take sha na bak'in ciki.



*************



Yau aka saka ranar Su hassy da hussy wata biyu nan fa Murna kamar me su hassy aka hau shiri ta b'angaren mazan kuwa Muktar yayi ginin sa akano  shi kuma Shuriem yayi gininsa dank'arere  A nan Abujar . Lefe kuwa kannen maminsa suka tafi dubai inda aka had'o akwati saiti 24 wane kyau domin tamkar a bud'e kanti mami kuwa ta tama bikin Shuriem bangaren Mum din su Hassy kuwa duk ta shiga busy domin kullum suna kano Sayen kayan k'awa komai 2 take saya domma  Suhaima itama  sati mai zuwa zasu tafi dubai da hassy da husy don sayo kayan fitar biki da wasu sauran kayan.

 Bayan Sati d'aya suka d'aga dubai su uku sun sayo kaya na gani na fad'a na manyan mata domin Dadyn su ya saki kud'i domin daga su bazai kuma aurarwa ba kaya suke jibga musamm husy mai son abubuwa komi ta gani sai ta saya wan nan kenan.

Sai da sukai sati biyu San nan suka dawo Dan ma an musu huutu shiisa abin yazo da sauki.

Suna azaune mum na ganin kayan "kai My twins gaskiya kun iya zab'e wan nan kaya haka lalle" suhaima tace "ai mum komi suka gani sai sun saya musammn kayan kitchen" mami tace ai yarn nawa sun horu da girki shiisa suke saya" hassy tace mum ai dady "yafa bamu kudi sosai" Suhaima tace "yanzu ku Ana zancen auren naku kuke saka baki" husy ta rufe ido "kai Sis Suhaima" hassy tace "hmmm! siis suhaima lokacin bikinki fa! komai ke kika zab'a" mum tace "ku tashi kuje kuyi girki don yanzu dole ku dada k'warewa" nan suka tashi.



***********


Husy ce zaune da Shuriem suna hira inda suka Saba zama Dan kallonta yayi da murmushi d'auke akan face nasa 'Amaryata nan da one month kina gidana" sunkwi dakai tayi "angona Kenan" yace "ki gayan meye bai miki ba agidan a gyara" nan ya bud'e tsaleliyar wayarsa yana nuna mata masha Allah kawai take ambata tace "nikam husby ko ina yayi wlh ai wan nan na zama yar gata" yace "baby kinfi haka ma" haka suka gama hirar su ya tafi.


*Bayan sati daya*



Dangin su Shuriem suka kawo Lefe Motoci ne manya manya ke. fakawa a farfajiyar gidan su hassy. manyan mata keta fita inda katti ke d'aukan jakun kuna suna shiga dashi cikin gidan ma dank'am yake da mata nan aka hau gud'a kota ina Masha Allah aketa anbata "lalle yarinya tayi goshi" su maman kano da goggo duk sun zo nan aka basu tukwici na 200k da Snaks kala- kala amutunce suka gama suka tafi inda aka saka date On 30 April.bayan tafiyar su akaita san barka hassy ta haye d'akin su tace "tweeny gaskiya kinyi goshi kinga kaya! Amarya  kenan." Husy ta dago "kema ai hakan wai yaushe mukatr zasu kawo" tace "shima a dis week" nan suka zauna suna ta shirya yanda event sai wakana.



***********


"Kai muktar yanzu wan nan shirgegen Lefen Shi za'a kaiwa yarinya d'aya ai wan nan sai an kaiwa yarinya Goma in a k'auyen nan ne! Ai dama nasan su Antyn kano su lefen karya zasuyi don sunga yar birni ce shiisa ba akawon na gani ba saida ka gama haba muktar! kodan yar manya ce" muktar dake durk'ushe don tunda aka fara hada lefen ya hada abinsa da tainakon su Antyn kano (inda yake) Su gaggo tun ganin su da lefen suke maganganu kan yayi yawa shiisa ma har yanzu ba'a kaiba.Muktar yace "haba gogg kinsan dai gidan Dana d'auko aure dole komai ai na bajinta kuma falilkahil hamd inada Halin yi."daka tsalle tayi "wallahi sai an rage" nan ta d'ebi wasu atamfofi ta aje agefe da mayafai "haba aje lefe saiti goma sha shida zaka kaiwa mace d'aya wlh sai an rage" kamar yayi kuka don ya dade yana shirinsa. shigowar maigari ya tarar da tak'ardama yace "meye?" nan ta sanar mai yace "kinga ban san haka! ke kinga inda ya samo auren ne? kibarsa kawai tuwon girma miyarsa nama,duk damu k'auye bamu san wan nan k'aryar ba ,to shi abirni yake yanzu dole tunda 'yar can ya samo dole yayi masu tunda yana da hali" nan ya dauke duk kayan ya maida a fusacce ta d'au wani atamph "wlh Banda wan nan" muktar yace "gogg kinga fa akwatinki can da kaya keda baba na ciko muku don fitar biki ga kuma dubu hamsin akai." nan ta washe baki "yanzu naji magana, Amma de duk da haka sunyi yawa" yace "don Allah Gogg kiyi hkr don Allah!" tace "to bkmi Allah ya sanya Alkairi kaga ranar Asabar sai akai" yace "yawwa goggo na." "Inaga su Antyn su zasu kai kayan ko?" yace "eh Gogg" murmushi tayi Allah ya amfana .



By


Queen meemi👑




. . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣62❣                    


 _Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_        


_This page for u my lovers fans❤_


 ********


Ranar Asabar gidan su Muktar suka kai lefe Abuja da ance akarb'a agidan maman kano sai suka ga dacewar sukai Abujar. nan Marik'an Muktar na kano suka yankara suka tafi kai lefen suma sun kawo an yaba akwati saiti sha shida duk da bai kai kyan na hussy da yawa ba Amma itama nata an kashe kud'i lefe yayi kyau sai san barka da zasu tafi aka basu tukwici. 100k tare da Snaks da Drinks abu yayi kyau duk sunyi goshi nan duk aka tsaida date dai-de dana hussy Muktar bayan tafiyar su sun waya da hassy yace kaya sunyi tace "haba dai Muktar ai kaya sunyi wlh" nan yaji dad'i sosai suka taba hira abinsu. Haka fa duk suka shiga Busy ko yaushe suna tafe gurin kai d'inki da shirye -shiryen su,bangaren angwaye ma duk sun shiga busy da yake ma duk suna da abokanan da suke taya su shiri.



********

Can kuwa a mangalu su inna Jummai ne keta shirin tafiya bikin daya ke saura sati d'aya shiisa malam yace suje,hakan kuwa akayi malam yace Dije ma ta shirya tabisu da zumudi ta shiga shiri. Gwamma kuwa taso zuwa malam yace meye had'inta d a ita dama zuwa tayi ta sameshi a rumfar sa lokacin sun dawo daga bara ta sami gefe ta zauna "Malam dama magana biyu ke tafe dani" nan  tayi mai zancen  zata bikin yace basu da had'i don haka ta hkr Dije taje hakan ta hak'ura, har ta tashi ta dawo "yawwa malam dama ina rok'anka Allah da Annabi ka maidani d'akina," wani kallo yabi ta dashi "gwamma ai yanzu bamu da wani sauran zama ko kin manta saki uku nai miki! kije kiyi hk'r kawai" kuka tasa ta tashi tana cangala kafa ta tafi da dana sani fal aranta. su kuwa yau suka tafi wajen karfe biyar suka sauka amAbujar tun zuwan su suka tsinke da ganin gida Dije kam k'auyancin tane ya fito fili suna zaune misalin k'arfe 7 na dare Jummai ta fito da kayan kad'i kaloli da tasa aka daka mata da yawa irinsu kuka,karkashi,kub'ewa bushasshiya,Daddawa da kayan k'amshi duk ta daka ta mik'awa mum gashi kayan kad'i ne duk na amarre ko zasuyi tuwo" mum tace "tuwo ai dole ne wlh kuwa na gode nima zan dib'a kinsan anan abuja wahala suke ga Dadyn na son su" nan ta fito da wasu samiru masu adon blue irin nada d'in nan wajen saiti goma masu biyar- biyar tace "wan nan kuma gudunmawar malam ne" mum tace "oh bakwa gajiya! ai kuwa kinga ajera musu akitchn" wani buhu ta zaro "wan nan kuma na wane dama munyi magana da husy tace tana son kaskon wuta" mum tace masha Allah ubangiji yabar zumunci mun gode, ta kara janyo wata babbar leda wan nan kuma su Mubirgi ne da mara su fai-fai da k'warya su Ludayi da sauran kayan gargajiya" mum ta murmusa Amma fa jummai kin burge yaran naki kinga sai ai musu kitchen kala 2 daya kayan zamani daya na gargajiya ,kinsan irin kayan nan yanzu zamani yazo Sam bakya ganinsu a kitchen amare iyayen anbar al' ada sukuma yaran basaso .Allah ya biya" jummai tace mune da godia ai"  



*********


Su kuwa Amare suna daki kullum basu fita domin yau,kwana biyar  kenan da farai musu dilka (halawa) inda Maryam Alk'ali (mamu) ke musu domin ta k'ware tun daga sokoto aka d'aukota abubuwa kala -kala take musu,jin dadin ma sun saki kudi gurin masu d'inki domin da kansu suke kawo musu idan sun dinka.

Bayan sati d'aya kenan ya kama sati biyu Ana kwaskware su husy hatta magana da yanda zasunaa fidda lafuzza saida mamu ta koya musu cikin salo na daukan hankali kai gaskiya idan kana da kyau ka K'ara da Wanda domin idan kukaga yanda su husy suka dawo sai kun kalla kun k'ara kallo,nan aka sallami mamu da kyauta mai tsoka da alk'awarin zata lek'o bikin tunda tana Abujar lokacin.


   *SHAGALIN BIKIN*


Ranar laraba gida ya cika dank'am da 'yan biki.

Ranar Alhamis aka fara da kamun Amarya inda aka d'auko Maryam Ramat wadda za tana kwalle musu fuska k'arfe hud'u ta gamai musu kwalliya masha Allah sunyi kyau domin fad'ar kayan da sukai b'ata time ne, duk sunci Material black nd ash sun bala'in kyau sun dora wata abaya ne kamar Alkyabba baka ,dangin Shuriem suka zo nan aka gudanar aka akayi kamu aka raba kaskon wuta dasu lalle harda humra me k'amshi  adan wasu dogwayen roba sukaci suka sha aka watsae.



Washegari Ranar Jumaa aka gudanar da dinner da dadare misalin k'arfe 7 dai de angama kwalliya carkwad'i hussy da hassy sun bama Mara d'a kunya domin kayan jikinsu ma abin kallo ne sai walwali suke Jummai harda kuka lokacin da taga yanda husy takoma nan Suhaima tai ta daukan su hoto  da hassy sun saka wani blue green d'in material mai kama da less da golden ajiki tamkar ba yaran hausawa ba, sai kace yaran larabawa haka Arif ma ya had'e da frnds naasa Suhaimaa ta gaji da haduwa itama ita da babynta. Angwaye ma sun had'e suma shigar su iri d'aya suka debe su suna zuwa kallo ya koma kansu Sady da Sumy na gani sunje Sady hawaye ta fara ganin Shuriem da husy sunyi match sun had'e tabbas husy tayi wining akanta,ganin yanda Shuriem ke watsawa husy wani kwantacccen kallon yasa Sady tabar gun domin ji take kamar ta shak'e husy haka akayi aka gama akai rabon calendar me hotunan su key da Atamph Super aka watse.



Ranar Asabar shine mothers event kai gaskiya anyi gayya nan ma k'arfe hud'u angama makeup don mum tace bata son African Time,yauma sunyi kyau tamkar jiya twins ko ina sukai sai an kallesu kowacce sai doka  domin tamkar dawisu suka koma don kyau,k'awayen mami duk sun hallara ,da kawayen Amaryar waje yad'au d'imi kowa yana yaba Dan uwansa ga k'awayen suma sunyi kyau,wayar hassy keta ruri a hannun khadija wata frnds nata ta kaimata lokacin ango na musu selfi tace "ga wayarki Ana kira" ganin sunan miss hafcy yasa ta d'auka hello kawas tace gafa writers sun zo kinsan fa dama da duk nakai musu iv" 

"haba ba naga yawan cinsu su kowacce da garin da take ba?  miss hafcy tace "yap kinsan Ana bikin wata writer frnds nasu kinsan su da zumunci shiisa duk sunzo wasu daga ciki." "Nayi farinciki sai kun k'araso" nan biki yad'au colour ko ina ka kalla kowa na wasa da kaji ga drinks kaloli a time din lokacin writer suka k'araso irin su ,feenat jaafar ,miemie bee ,maman shakur, batul ,Maman hanef sady jegal,Amra, Zahra Bb,bena zir chucu ammani,lubie  phty Bb,sodangi,biebi isah,Auta,pyar ,rufaida omar, yar ficika.da dai suaran wadanda ban fad'a ba ,take akai musu big masauki Anty sis ,da Anty maijidd ma duk sun hallara haka akayi biki cikin farin ciki kowa ya watsae.



***********


Ranar Lahadi aka d'aura Auren HUSAINA DA SHURIEM,HASSANA DA MUKTAR Kan sadaki dubu d'ari lakadan ba ajalan ba waliyai da shaidu suka shaida aka shafa fatiha nan marok'a suka fara aikinsu inda suke wak'e Amare da Angwayensu manyen mutane ko ta ina marok'a kam sun Sami abinda suke so,zo kuga bakin Shuriem da Muktar tamkar gonar Auduga Alkawari ya cika,nan suka zarce da reception.



Mum kuma da danginta suka cigaba da yinin su mai kid'an k'warya tun daga kano maman kano ta dauko su ,suna tayi har wajen 5 aka fara shirin mik'a husaina (husy gidan angonta Shuriem ,ita kuma hassy sai gobe za'a mikata kano hmmm Ranar rabuwa kuka suke ta tasha tsakanin hassy da husy Arif ma kamar me sai kuka yake ita kanta mum matsar kwalla take,lafaya aka nada mata Dady yayi Mata nasiha mai ratsa jiki dakyar aka banbareta jikin jummai da suke kuka aka shigar da ita mota hassy na kusa da ita don zata rakata motoci suka ja tunda aka tafi take kuka har kaje hadaddenn gidan ta maitsari iya tsaruwa gidan mai bene ne falonta na kasa am mai adon golden komai ya tsaru abinka da 'yar manya, da daki 2 sama ma da wani falon Shi kuma adon red akai mai shima mai daki 2 koina cike da kaya wane zeezee yargata,kitchen daya mai kayan zamani daya mai na gargajiya tsayawa fad'ar sa bata lokaci ne,Nan aka aje Amaryar kowa yayi haramar tafiya da kyar hassy suka rabu da juna aka barta ita daya (Aure yakin mata)kan ango yazo.




Washegari gari misalin karfe 11 d'aya su maman kano suka rankaya da hasssy harda Jummai don zasu koma mangalu aka tafi da ita,k'arfe 3 suka isa direct gidan marik'an Mukatr akayi da ita Dangin su ne fal agidan akaiwa amarya nasiha su maman kano suka bada Amanarta san nan aka d'auketa aka kaita gidanta dake Shagari quaters itama gidan ta ya had'u sosai Amma ita flat house ne a tsakiya zai kod'a gidan ake,duk irin kayan dake gidan husy shine agidanta komai ba bambanci k'arfe 6 dai de kowa ya watse aka barta ita daya tana kuka kamar ranta zai fita.




By


Queee Meemi👑




. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣63❣                    


_Sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_           




**********


Bacci take d'irka na ga jiya bata sanma rana har ta fito ba. A hankali ya bud'e d'akin wani k'amshi ya buge shi ya zauna gefen gadon ya d'ora hannun sa dai-dai beauty face nata yana shafawa tare da godia ga sarki Allah daya mallaka masa farin cikinsa .Bayan ta ya shafa nan tayi mik'a ta juya Murmushi yayi ganin yanda take bacci gefen mayafinta yasa yana d'an sawa akunnen ta nan taakai hannu tare da bud'e ido murmushi ya saki "my finest wake up! kinga fa rana ta fito tun jiya bayan kawo ki kike bacci abokaina ma sai sallamar su nayi" sunkwi da kai tayi cike da kunya ganin yanda yake kallon jikinta bargo ta janyo da yake rigar bacci a  jikinta tunano wa tayi jiya bayan ankawo ta kowa ya tafi kafin ya shigo tayi sallahr isha ta kwanta don jiran sa,bata san baccci ya d'auketa ba. Murmushi tayi ta kalli agogo da sauri "wayyo banyi sallar asuba gashi  ba har 6 :30" Shuriem dake kallonta tana bashi shaawa yace duk bar diriricewar nan jeki sallah don jiya na shigo na ganki sai kwasar bacci kike ai inaga na shigo d'akin nan yakai so goma na dauka ma mutuwa kikai,.da Asuba kuwa na tashe ki na fita na dauka ma kinyi" da gudu ta fada toilet tana magana "ai nagaji fa wlh tunda a ka fara bikin nan bana samun sleep" dai- de lokacin ta fito ta shimfid'a sallaya ta tada sallah shikam Shuriem yayi d'ai d'ai kan gadon yana shak'ar kamshin ta daya manne a zanin gadon. Bayan ta idar ta yiwa Annabi salati tayi karatun Al'Qurani ta nad'e sallayar.haka kawai kunyar sa takeji ta kasa hawa gadon sai kawai tayi hanyar waje zata bud'e taji ya kamota ta fad'a k'irjinsa ya riketa gam nan suka shiga wata duniyar yace "husyna zo ki koma baccinki anjima sai mu tashi" juyawa tayi "break fast zan mana" d'an hararta yayi "waya gaya miki Amarya na girki? tace "to meye nidai Amaryata ba zata shiga kitchen yauba kizo mi bacci mami zata sa akawo" janyo ta yayi tana sunne kai suka kwanta Wanda baccin gajiya ya debe su Basu suka tashi ba sai k'arfe 11 na safe ita ta fara mik'ewa ta shiga toilet tayo wanka ganin ba kayanta ko d'aya ad'akin yasa ta fita ta dayan d'akin masha Allah ta ambata domin naira tai kuka ad'akin wardrobe ta bud'e sabbin kayanta me jeras tasan aikin hasssy ne nan ta zabi wata vaila Atamph red tasa ta kashe d'auri jikin nan sai tashin kamshi yake. ta sauka k'asa domin yunwa ta fara kwasarta.manyan flaks ne da kalolin abinci dai- de lokacin Shuriem ya sauko shima ya shek'a wankansa yasa jins da t- shart rungumata yayi ta baya "kinyi kyau finest" ta juyo  tamai fari "kaima haka handsome" janta jikinsa yayi yana shakar kamshi. Suna manne da juna ya ja musu tebur  tayi saving nasu sukai break fast.

Bayan sun gama suka dinga bin d'akunan suna kalla su kitchen daga sama har k'asa  Shuriem yace "yanda kike da kyau haka gidan ki ma"  tayi dariya "haka angon ma yake" ak'arshe suka dire a wani k'aramin garden shuke-shuke ne duk wan nan tsarin husy ne don tana son green ganye sun dad'e agun suna soyewarsu san nan suka koma cikin gidan suka zube afalo Shuriem yana saita musu Tv.





B'angaren Amarya Hassy kuwa kuka tak'i dainawa domin ganin ita gata wani garin bata san kowa ba dadin tama ga maman kano,dirin motoci taji yasa ta dad'a k'unshewaa hayaniya taji afalo Muktar ya shigo "Amaryata ta" ko ihim bata ce ba yaje ahankali ya yaye Mayafin ta rufe idonta gam alamar bata sann bud'ewa dariya yayi "kyama bud'e yad'an ja hancin ta idon arufe tayi dariya ya d'agata "kinyi kyau fa! ga abokanai can zasuyi siyan baki juyawa tayi kasan Banda k'awaye taya Za" shafa sumar sa yayi  "baby kawai addua za'ai" mayafinta ta d'auka suka jera abokan su uku suka hau mai tsiya musammn mahmud yace "Lalle dole kace sai twins din nan ashe ba abanza ba" muktr yace "yimin sharri" suka sa dariya nan sukai D'an nasiha suka aje manyan leda sukai musu sallama suna fita hasssy ta shige d'aki shima ya bita da leda "baby ga kaza nan da fresh milk kici nasan kinajin yunwa" tad'an turo baki "nifa nak'oshi" yace tab! "yau kuwa sai kinci ko d'ure sai na miki"  "Nifa bacci nake ji wlh am so tired" yace "I know dear! kici kad'an saiki kwanta" dan zamo wa tayi ta sakko kan capet suka juye kazar a filet sai tiriri take ya d'auko cup ya tsiyaya musu  cinya ta d'auka ta gutsira ahankali kamar bata san taunar. shikam ci yake yace "lalle wan nan aiba ci kike ba" tsam ya tashi ya koma bayanta ya d'an janyota jikinsa "oya open ur mouth" dariya ya bata tad'an bud'e ta gutsira ahakan suka gama ci yace zai je toilet nasa yayi wanka yayo alwala, yace itama tayi kan yayo.'yan mintuna tayi ta fito ta saka kayan bacci da zumbulelen hijab lokacin ya shigo ya jasu sallah sukai nafila ta godia ga Allah . kokarin tashi take ya kalli k'unshin k'afarta "wow dea wan nan k'unshin yayi mani kyau" ya shafa k'afar taji yarr! Ajikinta ya tashi shima itakam tuni tayi flat a bed taja bargo saboda Ac dake hurowa sosai sai take jin d'an sanyi.kwanciya yayi yana d'an janta da hira sai magana take can kasa "yace hassyna k'arfe tarafa! yanzu ki tashi mi hira Dan mik'ewa tayi suna dan hira harda dariya yana nuna mata pictures na bikin su wayarsa. Nan da nan ta ware taji baccin ma ya tafi hirar su suke ta soyayya yanayi yana shafa gashin ta daya sha gyara d'an abubuwa ya farai mata nan suka fara shiga wani hali  kissn dinta yake take jikinta ya fara rawa shima haka Nan na bar dakin Asuba ta gari Amarya da Ango




By

Queen Meemi👑




. . 

⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

                ❣64❣                    


_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_            




*******


Husy na zaune tayi filo da Shuriem yace "gaskiya kunsha gwagawrmaya finest kamar ba za'ai auren nan bafa!" ta d'ago ta kalleshi "dear donma bantab'a baka full labarina ba da sai kayi mamaki" tashi yayi "my love bani mana" murmushi tayi "to sarkin jin labari" yad'an yi kayatacciyar dariyar sa yace "ai dole indai hira daga bakin kine aida dad'i" lumshi ido tayi tana jin sonsa aranta Shi kuma yana wasa da hannunta nan ta fara bashi tun daga farko har k'arshe tashi yayi ya matseta tsam ajikinsa "lalle na yarda let rabona ce tabbas tsantsan rabone ya had'amu amma nayi mamakin muktar ke dashi bakwa nunawa" tace "to ai kaga komai nada sanadi"  yace "Muktar ya kara girma a idona saboda yabar min hear beat dina" Dan dukansa tayi na wasa "dama can dan juna akayi mu" yace "tabbs baby na ilove u so much tace luv u too" ganin karfe shida dai de ta mik'e dea bari nai mana jallof mai dadi janyota yayi ta fad'a jikinsa ba yau ba har yanzu fa ko 3 days baki ba." Dan ya mitse fuska tayi "dea kabari nayi plsss wlh sha'awar yimaka girki nake" ganin tana alamar shagwab'a ya mik'e "muje finest" suka shiga kitchn nan ta bashi yankan albasa ya dage sai yi yake ita kuma ta had'a 7 dai de tayi sukaje sukai wanka suka fito suna ciyar da juna wani irin nishadi ke shigar su  duk yayin da suka kasance atare da kaunar juna. ko can da nan basa san fita ga Shuriem yasan salo- salo na rikita ta nan da nan suka  dada shak'uwa  D'an jingina tayi yace "finest yaude gajiyarr tabi jiki ko?" ta kalleshi ta sunkwi da kai domin tasan kanun zancen tashi tayi zata gudu d'aki yadam k'ota ta fad'a k'irjinsa zuciyoyinsu sai fat -fat suke k'amshin ta 

Ke rikitashi ga kayan data sa sun mata kyau sun fito da kyanta cak! ya d'auketa sai dakinsu ya bud'e jaka ya dauko Mata hijab sukai alwala suka gabatar da sallah sukayi adduoi na godia ganin yanda yake zumud'i yasa tafara d'ari dari,kalamai masu dadi yake gayaa Mata suke shiga kanta duk jikinta yayi sanyi .gashi ya rikitata da salonsa take hawaye suka zubo mata ganin tana kuka yace "sorry dea iluv u so much nayi laifi ko? tace "no dear bansan daliliba"tashi yayi ya kashe masu fitila suka fada duniyar masoya Asuba ta gari Hussy shureim.



********




Haka Amaren nan suka bud'e shafin soyyayya angwayen su ko fita basa yi ga girki mai dad'i da suke kwasa don mum batai wasa da koya masu girki ba musammn Shuriem da yake san na gargajiya yauma suna zaune husy na game a waya Shi kuma yana kallo ya juyo "zo nan finest" ta noke kafad'a don tasan ramuwa zayyi tsam ya tashi ya zare wayar ya b'oye .fillow ta dauka tana Dan dukansa alamar kuka "ni kabani Allah zanyi kuka" yace "yauwa yi mugani dama ina son ganin hawayen ki" harar sa tayi "Allah nafasa yin wan nan hadin me dadin nan!" yace "ai na iya  bari ma ki gani" tashi yayi yaje yad'au kan-kana da ayaba yayi blandin dinsu suka zama drinks yad'an sa sugar yasa afirj don yayi sanyi ya fito tana zaune ta rufe baki tana dariya "wa yaga kwab'a" yace "finest ai har na fiki iyawa, bari naje na watsa ruwa kafin nan yayi sanyi" yana shiga kuwa taje ta dib'a tasha ta boye saura tana son hadin domin tun agida takeyi tunda yasha yaji dadi yanace mai.,kitchen ta shiga tana yan wake- wakenta tana musu girki tafiyar kasaita yake ya bude firj zai sha yaga wayam da gudu ta fita waje nan ya gano ta ya bita sai zagaye suke afalon yana finest inna kamaki saina cije wan nan lips din" ta tsaya tana girgiza tace "gani" kafin yayi taku ta arce suka kuma kasa tsere caraf ya kamota take yahau cizon lips nata ahankali kawai suka zarce sai numfarfashi suke yace "wa kika shanyewa?" "sorry dea bari naimaka wani ta" kadamai ido ta tashi ya bita da kallo yana mai nishadi.



********


Su muktar kuwa hatta waya kulleta yayi acewarsa bai san damu kwasar luv nasu suke san ransu yau satin su d'aya Goggo babar muktar suka zo gidan hassy da itada wasu tsoffi. suna zaune muktar yana ma hassy tausa a kafa ta dan ji ciwo suka shiga. yana ganin su ya dirirce Goggo ta gani hassy ta tashi tana musu sannu da zuwa suka amsa. muktr yazo "sannunku da zuwa" Gogg tace "lalle muktar ka samu wan nan yarinya haka aidole ta maidaka haka Naga har tausa kake Mata" kunya ta kamashi "Goggg ciwo taji" tace "ayyo" Hassy ta shigo tana k'arai musu sannu da zuwa ta aje try da lemo ga dambun kaza agefe. Gogg sai tauna take ashe ta iya girki "husaina ki kula dashi kaima ka Kula da ita ku zauna lafiya nasan ka muktar banda biyewa mace musammn wan nan Naga yar gayu ce" kunya ya keji ganin tana magana sun d'an jima suka tafi ta had'a su da turare da aTampa bayan ya rakasu ya dawo suka cigaba da hira wan nan kena. Bayan wata d'aya da bikinsu Dady ya biya. Musu  zasu tafi Spain daga can suje Saudi suyi Umara har sai azumi ya kare amatsayin gifts dande suji dadi haka suka d'unguma Hassy da hussy da mazajensu



*************


Kuka take sosai kamar ranta zai fita. "Sumy wallahi ina tsoron wanda Dady zai bani kinga yanzu duk Samarin sun gujeni" Sumy tace "sai hkr"  "kinsan yau zai kirani" suna cikin magana Anty ta leko "Sady kixo inji Dady" jiki na rawa ta mik'e ta shiga kanta akasa ta gaidashi yace "wato Sadiya na baki lokaci yau wajen wata hud'u amma ba magana ko? to yau na yanke magana zan had'aki da Dan gidam kawu wato Bello" da sauri ta d'ago kai alamar zatai kuka zatai magana ya d'aga mata hannu ta tashi ya daga mata hannu gama magana nan da 2 month za ai aure."

Da gudu taje gun Sumy "wayyo Wai kinji bello zan aura!" Sumy tace "tohh to ai Naga bakya sonsa" Sady tace eh mana, kin manta ya tab'a cewa yana sona nace be min ba, saboda Allah ina zan kai Bello tuzuru dashi ni bemun ba" sumy tace "hmm kidaiyi hkr kawai ai tunda ma ya tab'a cewa yana sanki da sauk'i" Sady ta fashe da kuka "ina zan kai k'aton bakin sa jibeshi fa ko kwalliya bai iya ba tamkar bagidaje" sumy tasa dariya "kidaiyi ahankali kawai matar mutum kabarin sa" gun Mama taje tana kuka umma ta kalleta "sai ki hkr domin baki da kaico ,naga yanada ilminsa har masters gareshi ga ilmin addini kawai Dan baya kwalliya saikice meye, cewar da kike mummuna ne ai ba daura Shi akafa zaki ba.ke kika cuci kanki ba irin samarin Daba su soki ba kike wulakanci,kuma kinsan Dadin ku baya magna biyu sai ki hkr." kuka ta cigaba dayi "wlh bana sonsa" jin tafiyar Dady yasa ta shige d'aki aguje ta b'uya ya shiga ya kalli mama "na bawa Sady bello domin dama ya dad'e yana sonta ta nuna bata yi dashi ,ban san wani zance na gama magana zati na sama za asaka rana" ya tashi ya fita.Aguje ta fito "mama wlh bana sonsa ko d'aya baida kyau" mama tace "ai har yanzu baki karatun ta nutsu bako? Meye dashi gashi Dan uwanki kawai ki hkr Allah yasa hakan shiyafi alkairi."tashi tayi ta fita tana ihu kamar me.



By 

Queen Meemi👑




. ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

           ❣65-66❣                    



_Sadaukarwace Ga Basheer Usman family's_        




_Page din naki ne Maijidda musa Nagode da kulawa❤_


******


kuka take kamar ranta zai fita hardasu birgima jin sallama yasa ta mike tai cikin d'aki zuby ce da Ruma sai Ruby hankalinsu ne ya tashi ko b'angaren iyayen nasu basu je ba suka zarce inda take. Sumy ce ke ta bata baki amma kamar k'ara volume take tamkar karamar yarinya, zama sukayi Ruma tace "sis meya faru? wan nan kuka haka! kamar ance mama ta rasu" tsagaitawa tayi "sabida Allah an kyautamin ace wai bello zan aura! Tuzuru dashi ga bai iya wanka ba ga bashida kyau" dariya suka saka ganin yanda tai mici- mici da ido Ruma tace "to saime! ba mutum bane?" Sady ta harareta "Amma dai kinsan bana sonsa kawai ace Shi zan aura" zuby tace "wai to meke faruwa? sady duk samarinki ya akayi haka ta faru?" sumy tace "ai duk ita taja" nan duk ta sanar musu Ruma tace "kinyi wawta ai Allah da kansa ya karrama D'an Adam meya kaiki wulaknta masu sanki,haba gashi Shi Wanda kikeso yayi auren sa ma, ita kuma hussy har kika iyai mata sharri" sumy tace "kudai gaya Mata ba irin shawarar da ban bata bata ba! ta biyewa lubna suka sako husy agaba gashi ta kaiki ta baro ta aure saurayin datai ta zugaki kuna masa wulaknci wlh maza sunkai 4 Wanda tayiwa wulaknci ai shima bellon tayi mai" zuby tace "ina lefin ma in bakasan mutum kabashi hkr Amma sai ki hau wulaknci gashi Allah ya nuna maki karshen me wulaknci don haka ki saki jiki ki rik'e Bello da kyau domin yana sonki kinsan Dady bai magana 2 atoh kuma ki dage ki koyi girki domin Naga k'alubale akansa duk soyyayyar da muka sha da fawwz rashin iya girkina yasa yake mun wani abubuwan, kin san mu nan Sam sede masu aiki suyi girki wallhi duk ciikin mu nan ba wacce ta wani kware sai yanzu da muke zuwa koya, don haka ku dage" Sumy tace "ai dole,lefin su mama ne da basu koya mana ba ai" Ruma tace "ai saiki dage ki koya yanzu" Sady ta tabe baki "aini ba sansa nake ba balle har na dage na koya" Ruby tace "ke kika sani dama aike bakya d'aukan shawara." nan duk suka fita daga falon suka tafi shashin su mama suka barta tana zancen zuci tare da danasanin wulakanta masu sonta da aure da tayi gashi dalilin rashin su za'ai Mata auren dole acewarta.



******??


Rayuwa suke shimfud'awa mai rai da lafiya har sukayi sati biyu a spain san nan suka tafi saudia umara har sai bayan azumi zasu dawo.kullm suna cikin ibada rayuwarsu abin sha'awa muktar da Shuriem sun zama abokai komai atare,yauma suna zaune sunje wani kanti zasu d'an sai sweat wata balarabiya sai kallon Shuriem take da alama ta d'asa. husy ta gano ta kishi ya turnuk'o ta taje ta bangajen matar hassy na kula da ita husy ta had'e rai tana hararta ba shiri matar  tabar gun Shuriem ko in Banda dariya ba abinda yake ganin yanda ta had'e rai kamar zatai kuka yace "ashe babyn tawa akwai kishi" hassy tace "ai kadan ma ka gani"Mukatr yace to ai duk sammakal keda itan" nan gama siyayua  suka bar wajen. haka dai rayuwar su take wakana cikin so da kaunar juna wan nan kenan.





*************


Yau a kazo saka ranar Sady da yake abin na gida ne kowa san abin yake Sady kuwa d'aki ta kullle tana birgima bello sai kiranta yake awaya ta d'aga "pls ka daina damuna na gaya maka wlh kabari akai auren kashinka ya bushe" dariya yayi "sorry sister tuba nake" ya kashe taja tsaki "aikin banza mutum kome zakai mai baijin haushi" haka aka saka kowa ya watsae Sady har k'aramin zazzabi tayi da dare Dady ya kirata yayi Mata nasiha kan biyayya san nan yace "ban k'wareki ba na baki dama. Sady kika take dama amusulunce uba ke zab'awa yaransa miji ina mai baki hkr matar mutum kabarinsa" ya sallameta kuka take yi tare da Dana sani sai yau take tuno Hashim Wanda har kuka yake Mata amma haka take cimai mutunci. ta tuno faruq mai hkr kullum yana tafe ba irin wulakncin daba tamai har ruwa ta watsa mai ta jikashi amma ya nace ta jin-jina kai ta tuno kamalu shima ya sota k'arshe yaga bazai iyaba ya ware. kuka ta kuma fashewa sai yanzu take dana sani "kaico na gashi zan auri Wanda duk suka fishi komai da komai" haka ta koma d'aki tana koke- koke.Washegari bello yazo ba laifi ya d'anyi fes amma sai aslow sai dare baki yake kamar ta fasa ihu ba damar yi masa wulak'nci don Dady yace in tamai bai ya feba shikuwa sonta yake sosai kamar me sai hararar sa take yana Allah ya huci zuciyar Gimbiya. haka ta juya ta koma yayi murmushi ya tafi itama Sumy ansaka ranar sai zaman jiran Lokaci.



*Bayan wata d'aya*


*******

Yau ale kamun su. Sady kuwa sai gursheke take tace "Wayyo D'an hakin Dana raina gashi Shi zan aura" sai lokacin ta bawa su zuby tausayi suna ta bata hk'r da lallashi ganin tayi kukan har ta gaji yasa ta daina magana sai kallo suna zaune misalin Tara na dare. Sady tayi lamo ajikin ruma kanta dake ciwo,Ruma tace  "kinsan yau Dady ya bawa bello mota da babban gida! duk Dan ya faranta miki ki dage kimai biyayya" Shi kuwa bello Dan uwanki ne kuma masoyinki"  bata ce komi ba ta d'aga kai Ruma tace san nan shawara kinsan mace na iya canja namji? to ina baki shawara daki fara canjashi wajen shashi yana irin kwalliyar da kikeso kai duk wani abu wlh da kanki sai kin gode min" kuka ta fashe "na shiga uku" Mama ta shigo "haba sady ke bakya yarda da k'addara ne? haba! kiyi ta addua Allah zai sanyaya ranki" tace "to mama." Mama tayi dariya "keda kikema 'yar gatan Dady har fa mota ya canja miki" su zuby sukace yawwa  ai kodan faranta miiki da yake kyamai biyayya" had'e rai tayi domin gani take kawai an cuceta.



*******

Haka aka  shiga biki gadan- gadan itada Sumy tayi kyau. Sady kam duk tak'i kyau ma saboda yawan kuka don agun dinner data ga yanda bello ke washe hak'ora sai da taji kuka domin kome zai bai burgeta. Shikuwa duk wani abu dayake Dan ita yake.haka aka gama biki lami lafiya kowacce aka mik'a ta gidan mijinta. Sady kamar k'aramin hauka take saboda ihu sai da Dady ya daka Mata tsawa yace "ki Kula sady ayanzu duk abinda ki kaiwa mijinki zunubi ne" kuka ta kuma fashewa tausayinta yaji   ya sauko yana Mata nasiha k'arshe yace "ki hkr kinji Allah yayi miki albarka ya damk'a Mata muk'ulln Sabuwa motar mata suka mikar da ita suka tafi.


Tnz reader for support me luv lodi .


Loading..end



By

Queen Meemi👑




.

⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜


                  ⚜

         ❣ ⚜ ⚜❣

                  ⚜                

  *❣RABUWA CE  SANADI❣*  

                       

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜

              ❣67-70❣                    

_Sadaukarwa ce ga Basheer Usman family's_            



  *KARSHE*



***********


Tunda aka kaita take tsiyataku kala- kala bello sai d'ari -d'ari yake domin har tsoron fad'anta yake. yau sunyi sati d'aya Amma ko kallo bai isheta ba da yake mai hkr ne haka yake sharewa komai ya samu sai ya kawo Mata ko bataso kyautatawa kala- kala idan 'yan kirkin nanan zata kulashi Amma in basa nan kallo bai isheta ba, komi Shi yake ganin Agidan harsu shara domin ko tsinke bata d'aukewa a gidan.yanayin hkrn sa yasa ta d'an fara sakin jiki haka dai zaman nasu ke wakana ta b'angaren sa yanzu har jins da t -shrt yake sawa duk Dan ya birgeta tana kwance zai Mata break fas ya kawo tana ya tsina haka zai ta lallashi irin kulawar da yake bata yasa ta fara d'an tausayin sa take masu girki duk da ba iyawa tayi ba Amma haka yake ci kuma ya yaba komai rashin dad'in sa gashi ko yaushe ya fita sayya zo mata da gift ganin hakan yasa ta dan sassauta.


*********


Lokacin azumi ya k'arato cikin nan jamaa aka fara azumi su hassy cike da jin dadi suke gudanar dashi bautar Allah suke tuk'uru da Adduar neman samun zaman lafiya mai d'orewa.



Ta b'angaren Sady kuwa sai aslow yau data  ta tashi da rashin lafiya ko hannu bata iya d'agawa bello duk ya rikice ko aiki daina zuwa yayi shike Kula da ita yawan ciwon kai take sunje asibiti an bata magani Amma indai ciwon kan ya motsa sai tayi ta kwarara amai haka zata yi a ko'ina bello  Shi zai gyara wajen ba k'yank'yami har cikin dare intayi haka zai ta kai kawo yana taimakonta wataran har kuka yake  idan yaga tana kuka saboda tausayi,cikin ikon Allah aka samo magani wani maganin gargajiya take sha nan ta fara samin sa ida tun bayan warkewarta ta daina mai rashin kunya ganin yanda yayi d'awainiya da ita gashi ko kad'an bai san b'acin ranta d'ari -d'ari yake haka ta sakko suka fara zaman lafiya sai alokacin ta gane bello irin mutanen nan ne da basa nuna soyayya a waje sai anyi Aure soyayya  yake nuna mata kalar wadda take so cikin salo take nunamai irin yanda take so ya dinga gudanar da kwalliyar sa da tsaftar sa sai gashi yayi fes bataji sonsa ba .Amma zaman lafiya suke gudanarwa kullum cikin yawo da ita yake don taji dadi ga cima sai wadda takeso ko ihim tayi sai ya rikice,cikin wata daya suka sake sai ga Sady duk an manta baya ji take da bello Dan yanzu ya dawo irin wanda ta keso hatta turare sai k'amshin da takeso yake sakawa domin da turare baidameshi ba haka kaya komai ma shi kuwa farinciki ke kamashi domin ya samo kan abarsa.




Wani zuwa da sukayi gida dukansu suka ga Sady tayi kib'a nan suka hau tsokanar ta cewar kika ce bakyaso dama gulma ce " tace "ai Anty zuby "sai yanzu na gano dawan garin mace zata iya canja namji kuma ka auri mijin dake sanka yafi domin don bakiga yanda yake min ba ,shiisa nima na sauko nake Kula dashi ,kinsan meye wlh manyan mazan nan sunfi rik'e mace gam musamm Wanda ya dad'e bai aure ba" tafawa sukayi sumy tace Alhmdlh k'ananan ma suna rik'ewa kaide ka samu mai sonka da gaskiya kaima ka rikesu da amana kuskure Ada munyi amma yanzu komai lafiya sai kuma kyautatawa" Sady tace ai nikam na godewa Allah wani hanin ga Allah  baiwa ne ,so nake na fara zuwa gidan kayan girki ma" Ruma tace "ba gashi kinyi biyayya kinga sakamako ba Allah dai ya inganta" wan nan kenan.



******

Yau ake azumin karshe su husy sai shirin dawowa suke. washegari kuwa suka sauka a Nigeria watansu 2 acan sun dad'a kyau kai bakace su husy daga Nigeria suke ba kowacce sai murmushi ,suka saukaa gidan  su mum sunyi murna sosai Dady ma yayi farin cikin ganin su nan duk suka bada tsaraba da yake azumi ne husy ta tafi gida da wuri .hassy kuma sai gobe zasu tafi saboda sallah.



Washegari su muktar jirgi kuwa sukabi jya sauke su afilin jinrgin malam aminu kano direct gida suka wuce nan 'yan uwa da abokan Arzuka sukai ta musu barka da zuwa,nan aka gama azumi aka shiga bikin salllah cike da farinciki.




Sinasir husy tayi mekyau da lafiya da miyan agusi me bushashen kifi da naman kaza sai k'amshi take da drinks kala- kala ta bawa Shuriem yakai abincin sallah gidansu gun babrsa hade Dana  mumyn ta.shima ya kwaso abokansa 2 suka kwashi girki domin ba karya itada hassy sunyi iya girki mum batai wasa ba domin girki shine mace wan nan dalilin yasa ma mazan keji dasu tamkar kwai. Sati daya da sallh husy na zaune taci uwar kwalliya  tana  ta kallo taji Ana knockn mik'ewa tayi da mamaki a fuskarta "mezan gani kamar su karima da Sahura" dariya sukayi suka zauna akan tiles tace "haba ku hau kujerar mana" sai kallonta suke tace "ashe zan sake ganin ku!" suka ce "wlh munje mangalu akace ai kina abuja kuma kinyi Aure kinsan daya muke aure da sahura, shine mukace mukam sai munxo wlh muka saida awakan mu kazo  gidan su zuby yau kwanan 2 ashe! sady ma sun aure" Husy tace "niban ma san tayi aure ba yau satinmu daya da dawo nigeria kum kuwa k kyauta wlh kun rike alk'awari ta" kalli yaran dake hannunsu wad'annan 'ya'yannku ne?"  sukace eh kowacce yaranta biyu" tace masha Allah  nan  ta basu abinci fa lemo sukaci suka sha karime nada waya ta bata number suna gaisawa suka mik'e zasu tafi ta hadosu da turare da turmin atamph dai dai sai kwancen kayanta wasu ma so 2 tasa.wajen kala biyar biyar ta basu ta had'a musu da tsarabar makka sukai ta godia. lokacin Shuriem ya dawo ta sanar dashi ya basu dubu goma -goma saboda dadi harda kukansu suka tafi husy taji dadin ganinsu sai rayuwar da sukai  lokacin suna aiki ke dawo mata  wan nan kenan.




********

Wata daya  ga sallah suka tafi mangalu Shuriem zai gaida su malam sunje lafiya aka karb'esu lokacin suka aje musu tsarabar da sauran abubuwa. suka tarar Ana bikin husy dije  ta bada gudun mawa Kwana 2 sukayi da zasu tafi Abdullah ya nace zai bisu dama Shuriem cikin garin kano ya tafi ya dawo daukan husy ya tarar da hakan .malam harda dukan Abdallah Shuriem yace "baba ka bamu Shi mutafi can dashi sai yayi makarnta acan husy tace "tunda anan wataran kin zuwa yake ba!" Dad'i jummai taji malam yace "zai d'ora muku nauyi fa!" Shuriem yace "haba malam "wane nauyi husaina fa ku kuka rik'eta ai abdallah matsayin k'aninta yake" malam yace "to Allah yayi albarka nan suka tafi dashi suka yi sallama suka tafi.


Komawar su da kwana 2 aka sashi wata primary me kyau da tsada.



*Bayan shekara 2*



Husy d, hassy ne da Suhaima suke birthday din first born din ita suhaiman na 3 yrs lokacin sunyi kyau husy da hassy kowacce da babynta masu kyau turare tas dasu husy namiji shakur hassy da yarta Rauda duk watan su goma am musu kwalliya sunyi kyau su hassy ma sunk'ara kiba su kara kyau cakes ne guda uku za a yanka sai daukan photo suke suna zaune wasu yara yan makotansu bazafi 3 din ba aka kawo su nan aka yanka musu suna ta jin dadi ko ina baloons .


Sallama akai  Suhaima tace "Sady ashe zaki zo! su husy duk suka juya itama tana rike da babynta mace  nan suka gaisa dasu husy suna ta hira Sady ta kalli husy "duk abubuwan da suka faru  abaya kiyafen min na dade ina son had'uwa dake Amma ko yaushe bakwa kasar sai yau. husy tace "bakmi fa!ni nama manta ai ya wuce" sady tayi murmushi "inaso mu cigaba da zumucnci" hassy tace "okey ba matsala" haka akayi aka gama kowacce ta tafi.


 

Husy da Shuriem na tafiya a mota ga babyn su abaya Shuriem na waya driver ya dauko abdallah daga school an tsaya round about  sukaga wani gu a hargitse alamar Ana fad'a duk an had'a goslow suna tsaye suka ga Dan sanda ya fito da wani za'a turashi mota sai ihu yake bashi bane. husy tace "wlh lawandi ne! to meya kawo shi abuja!" tace "husbyna ataimakeshi" ya bud'e motarsa yaje wajen D'an sandan na ganin sa ya sunkuya ya gaidashi domin da yawa an sanshi garin Abuja saboda companynsa dake ci ya tambayi ba'asi Dan sanda yace "gudun gacganci yake a babur ya bigi motar wani shine mutimin yace bai yarda ba  sai an gyara mai mu kuma muka kamashi saboda gudun ma da yake na ganganci." Shuriem yace "fito dashi aka fito da lawandi fuska shab'e -shab'e domin yasan wahalar da yake agunsu bayau d'aya ba aka kamashi yace "wlh bani bane wani ne ya bige motar ya gudu ni kuma lokacin na tsaya abun ya wad'a kaina kuma babur din arone" nan Shuriem ya bada ten thousand kan mutumin yayi hkr ya bada card nashi kan yakai motar inda ya kwatanta a gyara mai duk a ljihun Shuriem. take aka saki lawandi sai godia yake har ya biyoshi bakin motar caraf idonsa ya sauka akan husy ya nuna ta da yatsa duk da tak'ara girma da haske amma ya ganeta yace "hansai kece mijinki ya taimaken? dama na dade ina nemanki" shureim yace "kai nutsu kaji" nan ya sunkuya yace "don Allah kiyafemun nasan da hak'kinki" ma tace "na yafe  Amma yakamata ka nutsu mana duk rashin ilmin ne ka koma makarntar yaki da jahlici" nan ta zaro dubu goma ta bashi Allah ya kiyaye suka ja motar su ya bisu da kallo,da kudiri aransa na gyara rayuwan sa.



Haka rayuwarsu ta kasance dai husy na kwance kan 3 seter shakur na wasa akanta shureim ya shigo da gudu suka mak'alk'aleshi ya cafe shakur yana kissn kumatunsa ya kamo husy "finest Allah yayi muku albarka  keda little boy namu,ina sonki matata ta" dagowa tayi tai fari nagode angona yakai Mata peck agoshi dai -de lokacin Abdallah ya shigo yana jss 1ya  ya gaidasu yayi fes dashi.ya shiga dakinsa dake kasa.

jansa tayi ta tayashi yayi wanka yaci abinci me dadi nan ya janyota jikinsa.

wani agogo Shuriem ya zaro duk an rubuta sunan husy da ruwan zaiba ta ciki amma ya samata ahannu yace "Allah ya Kara mana dankon luv" tace ameeen ya hadasu shakur agefe yana papa itama adayan side din ya sakar musu selfi sunyi kyau.  happy family.



Tammat bihamdlh.


Anan na kawo karshen wan nan book nawa mai suna Rabuwa ce sandi inda nayi kuskure Allah ya yafen inda nayi daide kuma Allah yasa ni amfani da fadakarwar dake ciki . domin nobody is ferpect. Allah ya kara mana kaunar Sayyadi Rasulillah.



Godia ga d'aukacin groups din da suke bibiyar wan nan book nawa ngd Allah ya bar kauna.❤



Fans Dina kunmin komai kun nunan kauna da book dina ina sonku sosai kamar yanda kuke sona.👍❤



GODIA Ga Kungiyar NAGARTA WRITERS ASOOCIATION Allah ya barmu tare.



Wasalllahu Ala nabiyur rahmati wa hali wa sahbihi ajmaen.



Ni Queen Meemi👑 Anan na aje alk'alamina sai kuma Allah ya Kara sadamu daku ga wani sabon book din wanda bankai ga samasa suna ba Allah ya taimakemu Ameen.*fans kuyi follow Dina on Wattap@Queen_Meemiluv*




❤❤❤❤❤ 

.

0 Response to "RABUWA CE SANADI Hausa Novel"

Post a Comment