Me ke sa idan ana ciwon taifod ake samun ciwon jiki da ciwon kai mai tsanani?
Me ke sa idan ana ciwon taifod ake samun ciwon jiki da ciwon kai mai tsanani?
Nakan yawan samun zazzabi, ana mini allurori amma a banza shi ne nake neman maganin da zan je in samu a kyamis
Daga Aliyu Muhammad
Amsa: To ai dalilin da ya sa a wannan shafi muka fi mai da hankali kan hanyoyin kariya ke nan ba magungunan cututtuka ba. Tunda ko a makon jiya mun yi bayani a kan dalilan da kan sa wasu magungunan ba sa aiki sosai.
Saboda haka hanyoyin kariya za ka dauka ke nan, kamar kwana a cikin gidan sauro kullum da yawan sa safa a kafa idan dare ya yi da riga mai dogon hannu don kada sauro ya samu wurin cizawa. Shi ne za ka yi maganin matsalar ko mu ce rigakafinta.
Me ke sa idan ana ciwon taifod ake samun ciwon jiki da ciwon kai mai tsanani?
Daga Muhammad Auwal Sani Kaduna
Amsa: Ai ka san kwayoyin cuta ne su kwayoyin taifod (typhoid) din ko? Su ne suke shiga kowane sako da lungu na jiki tun daga hanji inda suke fara shiga, sukan shiga jini a kai su kai da sauran gabobi su je su ci karensu ba babbaka, su makale suna sa maka ciwon jiki da ciwon kai. Mai yawan samun ciwon typhoid shi ma yana bukatar ya nemi hanyoyin kariya wadanda muka sha fada a nan domin ya yi rigakafin matsalar.
Me ke kawo mutum ya rika ganin digowar jini bayan ya gama fitsari?
Daga Garzali I. Darmanawa
Amsa: Ko dai shigar kwayoyin cuta mafitsara, kamar kwayoyin ciwon tsagiya, ko wani tsiro a mafitsara, ko tsakuwa ko kumburin halittar prostate, duk za su iya sa wannan ka rika ganin jini na biyo fitsari. Don haka mai samun wannan bai ga ta zama ba, sai ya je an binciki dalili a magance shi.
Idan na yi fitsari sai in kai rabin sa’a ina jin zafi. Shin mece ce mafita?
Daga Abubakar Kabiru, Bauchi
Amsa: Eh, kai ma kamar wancan da alama akwai matsala. Sai ka je an duba.
Mene ne fa’idar shan ruwan zafi da safe? Kuma me ya sa baki ke bushewa da sanyi?
Daga Ummi Hidaya
Amsa: Fa’idar shan abu mai zafi da safe ita ce warwarere hanji. Shi kuma bushewar baki lokacin sanyi saboda bushewar yanayi ne.
Ko karin kumallo da ruwa kafin mutum ya ci wani abu yana da wani alfanu?
Daga Bashir Musa Kura
Amsa: Eh, za a iya sha mana, ba wata illa, amma dai wadansu idan ba na zafin suka sha ba da sanyin safiya, sai cikinsu ya kulle, ko kuma a ranar su kasa jin dadin cikin.
Idan na ci abincin dare na koshi to idan na tashi da safe nakan ji yunwa sosai amma idan na ci daidai sai in tashi ba na jin yunwa. Me yake kawo haka?
Daga I.U.J
Amsa: Abin da ke kawo haka watakila shi ne sinadarin insulin. Idan mutum ya ci abinci mai yawa ana sakin sinadarin insulin da yawa wanda yakan sa a tsane komai cikin daren. Amma idan ka ci daidai, sinadarin insulin kadan za a saki.
Kusan shekara takwas ke nan ba na son cin abinci sosai sai kuma rama. Ina neman shawara.
Daga Aliyu Muhammad Azare
Amsa: Eh, kana bukatar likita ya duba ka.
Ina fama da ciwon hawan jini ne da na zuciya. Ga tari da haki da kumburin kafa da saurin gajiya. Ina zuwa asibiti duk wata amma ba sauki.
Daga Maman Musty
Amsa: A’a wannan ba na zuwa duk wata ba ne, zancen kwanciya ne a asibiti har sai kumburi ya sabe, haki da tari da saurin gajiya sun tafi. Duk likitan da ya ji wannan ya san sai an kwantar. Watakila suna rubuta miki kwanciya ba kya yarda. Idan kuma ba su rubuta kwanciya ba a nemi wani asibiti mai likitan zuciya, inda za su kwantar.
Idan ina motsa jiki sai in ji wani abu a keyata, idan na gogo shi sai in gan shi fari kamar gishiri. Ko matsala ce wannan?
Daga Saminu A.
Amsa: Eh, gishirin ne, tunda a gumi ake fitar da shi idan kana motsa jiki. Ai idan ma mutum na motsa jiki ba ya fitar da wannan to motsa jikin bai ratsa shi ba, don haka ba matsala hakan ma aka fi so. Sai dai kawai da ka je gida ka watsa ruwa.
Game da amsar da ka bayar ga mai dan maraina daya a ciki. To idan ba a sauko da shi ba mutum ba zai iya haihuwa ba ke nan?
Daga Shehu M.K. IBB Market
Amsa: A’a zai iya haihuwa mana in dai dayan lafiya lau yake. Kawai dai akwai hadarin zai iya zama wani tsiro ne a ciki idan ba a sauko da shi ba.
Ina yawan shan maganin sa cin abinci amma da na fara ci bayan ’yan kwanaki sai in dawo ba na son ci. Ina mafita?
Daga Salisu Umar ’Yankwashi
Amsa: Eh, sai ka koma wurin likitan da ya ba ka maganin ka yi masa bayani ko zai canja maka.
A shekarun baya a makaranta wani ya taba buge mini ido, to sai a yanzu ne nake ganin hazo-hazo. Shin zan iya zuwa kyamis don samun magani?
Daga F.U.M
Amsa: A’a ba kyamis ba dai, asibitin ido za ka je a fara dubawa a ce maka ga takamaiman me ya samu idon.
Sai tambayoyin masu matsalar fata ta kuraje da kaikayin fata da nankarwa (stretch marks) da tsagewar fata da amosani da sauransu, wadanda mun sha fada musu sai sun je sun ga likitan fata ya ga irin kurajen ya tantance kafin a ba su magani
0 Response to "Me ke sa idan ana ciwon taifod ake samun ciwon jiki da ciwon kai mai tsanani?"
Post a Comment