Manyan Kadarorin A A Rano
Manyan Kadarorin A A Rano
Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, wanda aka fi sani da A.A Rano haifaffen garin Lausu ne da yankin ƙaramar hukumar Rano a jihar Kano, ya sha kwaramniya kala-kala a rayuwa, kafin ya kai matsayin da ya ke
2. A.A Rano ya fara harkar mai ne a shekarar 1994, ya kuma fara gina gidan man sa na farko ne a garin Ƙarfi da ke kan hanyar Kano zuwa Zaria bayan ya bar harkar tireda, ya shiga harkar man fetur gadan-gadan.
3. A.A Rano shi ne Ubangidan Alh. Abdulkadir Musa mai kamfanin Rahamaniyya Oil. A.A Rano ne ya ɗauke shi aiki, ya kuma sakar masa dama. A yanzu kamfanin Rahamaniyya na da ma’aikata sama da dubu biyar, albashin su ya tasamma miliyan 56 duk wata.
4. A.A Rano ya mallaki gidajen mai kimanin 200 (ko sama da haka) a sassan ƙasar nan. Ma’aikatan sa sun haura dubu biyar. Kuma yafi ɗaukar ma’aikatan sa a gurin daya gina gidan man sa domin ragewa al’ummar wurin zaman banza.
5. A.A Rano na da matattarar taskance tataccen man fetur da ake kira Depot a unguwar Ijegun dake jihar Lagos. Wannan matattara gagaruma ce wadda ake sauke litar mai kimanin miliyan sittin, daga nan kuma sai a rarraba shi izuwa gidajen mansa, a kuma siyarwa sauran ‘yan kasuwa.
6. A.A Rano ne wanda ya gina cibiyar yaɗa addinin Islama mai suna ‘Darus Sunnah’ wadda take a Unguwa Uku ta garin Kano. A wannan cibiya ana karantar da ilimin addinin musulunci, ana kuma gabatar da manyan taruka da shirye-shiryen da suka shafi addinin musulunci kamar misalin Tambaya mabudin ilimi da Sheik Ibrahim Daurawa ke yi, attajiri Alh Sani kwangila kuma yake daukar nauyi.
7. A.A Rano shi ne shugaban A.A Rano Foundation, gidauniyar da take tallafawa ɗalibai da kuɗin karatu, tare da biyawa marasa lafiya kudin magani ko kudin aikin tiyata.
8. A.A Rano ya kan ragen farashin litar mai a gidajen man sa a kowanne watan Ramadana domin sauƙaƙawa alummar ƙasa.
9. A. A Rano ne attajirin farko da ya ke dukan kirji wajen samarwa.
MUN CIRO DAGA SHAFIN ALFIJIR HAUSA
0 Response to "Manyan Kadarorin A A Rano"
Post a Comment