Mahimmancin Yayan Itace Ga Budurwa Da Kuma Ma'aurata
Mahimmancin Yayan Itace Ga Budurwa Da Kuma Ma'aurata
Gwanda wata dan itaciya ce daga jerin ‘ya’yan itace da ganinsu ma ya isa ya sa ka dauka ka kai baka. Ferarriyar, lafiyayyiyar, nunaniyar gwanda na da daukar ido da sanya sha’awar shan ta. Ko shakka babu wannan fa’ida ce da duk wani abinci da ya cika sunansa abinci ya kamata ya samu. Shi yasa ake shawartar iyaye mata da a duk lokacin da suka tashi shirya abinci ga yaransu, musamman ma yaran da ba sa son cin abinci sosai, to, sai su kawata abincin da kaloli ta yadda zai dauki ido tare da motsa sha’awar cinsa.
Bayan ga kasancewar gwanda abinci mai daukar ido, gwanda na da zaki a baka, dadi da karawa kuma da tsoka mai taushi ta yadda gutsara da taunawarta ba ya wahalarwa. Har ila yau, gwanda ba ta da wuyar samu. Ana iya samun gwanda a duk kwanakin shekara, kuma babu wani yanayi da ya ke sa tsadar gwanda ta kai mutum ya kasa sayenta.
Banda wannan kuma ga wasu dalilai har dozin guda za su sa ka sanya gwanda a jerin abincin da ka ke ci a kowace rana:
Dalili na 1:
Gwanda na dauke da sinadarin fibre da na bitamin c da ke hana wani nau’i na kitse da ke taruwa har ya toshe hanyoyin jini ginuwa. Wannan kitse ana kiransa da suna Cholestrol a turance. Sinadarin Cholestorol da na lipid wadanda suna da nasu amfanin a jiki, in suka yawaita suna toshe hanyar jini wanda hakan ke komawa ga sai zuciya ta wahala kwarai kafin ta gudanar da aikinta, wanda hakan kuma kan juye zuwa ga ciwon zuciya
Dalili na 2:
Gwanda na taimakawa wajen rage kiba ko taiba, saboda kowace gwanda mai matsakaicin girma na dauke da Calories 120. Calories wani nau’i na zafi ne da ke samawa jiki karfi tare da narka taiba. Kasancewar gwanda abinci maras nauyi kuma dauke da sinadarin dietary fibre da ke taimakawa wajen rage nauyin jiki da kuma yawan bukawa ga abinci, gwanda abinci ce da duk mai bukatar rage kiba ya kara a abincinsa na yau da gobe
Dalili na 3:
Gwanda na dauke da kaso 200 na adadin bitamin C da jikinka ke bukata a kullum. Wannan bitamin C da ke cikin gwanda na taimakawa wajen haifar da kwayoyin halittar antibodies (wasu kwayoyin halitta da ke cikin jini da ke yakar kwayoyin cutar da suke jikinmu da ma wadanda su ke shiga jiinmu a kullum ta hanyar iskar da mu ke shaka, abinci da ruwa da mu ke ci ko sha da ma wadanda ke shiga jikinmu ta kafar gashin jikinmu). Yana da kyau mu fahimci cewa, iya adadin antibodies da ke cikin jikinmu, iya karfin yakar cutar da jikinmu zai iya.
Dalili na 4:
Duk da kasancewar gwanda dan itaciya mai zaki, gwanda na dauke da sinadarai da ke dakile ciwon sikari da hana shi tasiri. Masu dauke da ciwon sikari za su iya amfani da gwanda a matsayin abincin da ba zai tayar da ciwon ba kuma ma yake da tasiri wajen dakushe kaifin cutar haka ma wadanda ba su dauke da cutar za su yi amfani da gwanda wajen karesu daga kamuwa daga cutar.
Dalili na 5:
Gwanda na da yalwar sinadaran bitamin A, beta-carotene, zeaxanthin, cyptoxanthin da kuma lutein. Wadannan sinadarai suna taimakawa wajen wanzar da lafiyar ruwan ido da kuma hana shi gurbata. Sinadarin bitamin A da ke cikin gwanda na taimakawa wajen sanya karfin ido a lokacin tsufa sama da yadda karas da tumatiri ke bayar wa.
Dalili na 6:
Dimbin sinadarin bitamin C da ke cikin gwanda na bada kariya ta musamman ga cutar da ke kama gabobin mutum ta sanya su yi ta radadi da ciwo da ake kira da arthritis a turance. Bincike ya nuna cewa mutanen da ba sa cin nau’ikan abincin da ba sa dauke da bitamin C su ke da hatsarin kamuwa da cutar Arthritis.
Dalili na 7:
Gwanda na dauke da sinadarin papain da ke taimakawa wajen inganta lafiyar sashen jiki da ke da alhakin narka abinci. Sau tari muna cin wani abincin wanda ka iya jinkirta narkewar abinci a cikinmu ko ma ya kawo wani tarnaki ga sashen narka abinci na jikinmu. Sinadarin papain da ke cikin gwanda na taimakawa wajen hanzarta narkewar abinci a jikinmu ya kuma inganta lafiyar ma’aikatar narka abinci na jikinmu.
Dalili na 8:
Haka kuma, sinadarin papain da ke cikin gwanda na taimakawa mace da ke fama da ciwon mara a lokacin al’ada. Ga mace mai fama da irin wannan ciwo na lokacin al’ada, sai ta yawaita cin gwanda gabanin zuwan al’adarta. Hakan zai taimaka wajen rage ko cire irin radadin da ta ke ji a yayin al’adar
Dalili na 9:
Gwanda na dauke da yalwar bitamin E da bitamin C da kuma sinadarin beta-carotane. Wadannan sinadarai na da tasiri wajen hana fata yamutsewa da tattarewa da yin yaushi. Shan gwanda a kullum wata hanya ce da za ta hana tsufanka bayyana. Za ka kasance a kowane lokaci tamkar shekaru biyar kasa da shekarunka na hakika.
Dalili na 10:
Baya ga inganta lafiya da gwanda ke karawa, bitamin A da ke cikin gwanda na samar da wani sinadari da ke habaka girma ko tsirowar suma (gashi), tare da sanya sumar ta yi santsi, sheki da duhu. Kana ta samawa fatar kai danshi ta yadda amosanin kai ba zai samu gindin zama ba.
Dalili na 11:
Yawan amfanin da dan itaciyar gwanda na taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar da ke taruwa su gina sankarar da ta shafi al’aurar da namiji ta haifar masa da gwaiwa (prostate cancer) da kuma sankarar da ke kama ‘ya’yan hanji (colon cancer).
Dalili na 12:
Wani bincike na jami’ar Alabama a Amurka ya nuna cewa gwanda na daya daga cikin kayan abincin da ke yaye ko huce gajiya
Muhimmacin Dabino Ga Lafiyar Jikinmu
Dabino na dauke da sinadarai na ban mamaki. Da na ce sinadarai na ban mamaki, ina nufin sinadaran da ke da matukar muhimmanci ko dai wajen samar da waraka daga wata cuta ko kuma na hana kamuwa da wata cuta ko kuma inganta wasu sassa na jikinmu ta yadda za su gudanar da ayyukansu na yau da kullum daidai wa daida.
Wadannan sinadarai sun hada da: A kowane giram 100 na lafiyayyen dabino ana samun:
Fiber – giram 6.7
Potassium – giram 696
Copper – miligiram 0.4
Manganese – miligiram 0.3
Magnesium – miligiram 54
Vitamin B6 – miligiram 0.2
Wadannan sinadarai na da matukar muhimmanci ga lafiyarmu. Misali: Bitamin B6 din da ke cikin dabino na taimakawa wajen kara wa mutum bukatuwa da abinci tare da bude masa ciki musamman ma ga wanda ya dade bai ci abinci ba. Shi yasa ma Manzon Allah (S.A.W) Ya ke cewa: idan daya daga cikinku ya yi azumi to ya yi buda baki da dabino, amma idan bai samu ba, to ya yi amfani da ruwa, domin ruwa na tsarkakewa. Abu Dawud Ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 2348.
Dabino yana dauke da sinadarin dake karawa jiki karfi da kwari. Dabino na saisaita sukarin da ke cikin jinin mutum wanda yake raguwa sakamakon rashin cin abinci ko sha. Dabino yana dauke da sinadarin iron wanda yake taimakawa wajen karin Jini sannan yana karfafa jini da hantar mutum. Wadanan jawaban su suka sa muka gane abinda ke boye ta fadin Manzon Allah (SAW) akan Hadisin da muka kawo na sama. Bayan tarin magunguna da Dabino ke magancewa.
Ga wasu daga cikin Amfanin Dabino,
1- Yana samar da ruwan jiki
2-Yana taimakawa mata masu ciki
3-Yana kara ruwan nono
4 -Yana maganin matsalar fata
5 -Yana maganin ciwan kirji
6 -Yana maganin ciwan suga
7 -Yana maganin ciwon ido
8 -Yana gyra mafitsara
9 -Yana maganin Basur
10 -Yana magance matsalar Rashin banci
11 -Yana kara lafiar jariri
12 -Yana rage kiba wacce bata lafia bace
13 -Yana maganin majina
14 -Yana karfafa kashi
15 -Yana maganin ciwon hakuri
16 -Yana maganin Gymbon ciki (ulcer)
17 -Yana kara karfi da nauyi
18 -Yana maganin tsutsar ciki
19 -Yana maganin ciwo ko yanka
20 -Yana karawa koda lafia
21 -Yana maganin tari
22 -Yana maganin kullewar ko cheshewar ciki
23 -Yana rage kitse
24 -Yana maganin cutar Daji (cancer)
25 -Yana maganin Asthma
26 -Yana kara karfin kwakwalwa
27 -Yana ciwon baya, ciwon gabbai, ciwon sanyi, wanda yake kama gadon Baya.
28 – Yana kara sha’awa da kuzari
29 – Yana magance cutuka dake damun kirji
30 – Yana karya sihiri.
AMFANIN AYABA GA LAFIYARKA
Ayaban da bai karasa nuna ba yana maganin gudawa
Ayaba na samawa jiki karfi da kuzari
Ayaba na taimakawa wajen canjawa mutum yanayi daga damuwa zuwa nishadi
Ayaba na taimakawa wajen inganta kewayawar jini zuwa dukkan sassan jiki
Potassium da ke cikin ayaba na taimakawa wajen inganta lafiyar zuciya
Bitamin C da ke cikin Ayaba na taimakawa wajen yakar kananan cututtuka
Ayaba na taimakawa wajen yi wa fatar jiki garkuwa daga tsananin zafi da hasken rana
Ayaba na maganin gyambon ciki (ulcer)
Ayaba na murkushe tare da narkar da duwatsun koda (kidney stones)
Ayaba na daidaita adadin sikarin da ke jiki tare da tausasa karfin ciwon sikari
Ayaba na daidaita adadin sinadaran da ke cikin abincin da ka ke ci zuwa yanayin da jiki ke da bukata
Ayaba na magani teba (kiba maras amfani)
Ayaba na magani kwarnafi
Ayaba na taimakawa wajen saisaita bugun zuciya
Ayaba na rage hatsarin kamuwa da cutar bugun jini (stroke)
Ayaba na taimakawa wajen ragen karfin hawan jini
Ayaba na yakice gajiya da damuwa
Ayaba na rage radadin ciwon fitar jinin al’ada
Ayaba na rage radadin cizon kwari kamarsu sauro, kwarkwata, zuma, rina, zirnako da sauransu
Ayaba na rage hadarin kamuwa da ciwon dajin da ke da alaka da koda (kidney cancer)
Yawan cin ayaba na sa mutum ya rage sha’awar shan sikari da yawa
Duk da ya ke karas aka fi sani da inganta lafiyar ido da karfin gani, ayaba ma na taimakawa ido sosai
Amfanin Man Zaitun 10
Man-zaitun ( Olive oil/ Olea europea ) wani irin nau’in mai ne da ake samarwa daga ‘ya’yan itaciyar zaitun (Olive tree). Ana amfani dashi wajen girki, gyaran fata, magani, hada sabullai da kuma man-fitila ( a gargajiyance). Man-zaitun ana amfani dashi a ‘kasashen duniya da dama, musamman kasar Spain, France (Faransa), Italy, Greece (kasar Girka), Syria, Lebanon, Egypt, Libya,Tunisia, Algeria, Morocco da sauransu. Toh amma kasashen da suka fi yawan amfani dashi sune Portugal, Spain, Italy da Greece.
Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2009, kasashe 3 da suka fi yawan samar dashi sune: 1. Spain 2. Italy 3. Greece. Kasar Syria itace ta 4 , sai mai-bimata kasar Tunisia, a matsayin ta 5.Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur’ani Maigirma – Surat At- Tin da Surat An- Nur.
Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar ‘dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka:
1. Yana ‘karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.
2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances).
3. Kariya daga cututtukan zuciya – yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.
4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure).
5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients).
6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis).
7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart’s function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya.
8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata ( protection from skin cancer).
9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).
10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana – safe da rana, cokali daya a kowane lokacin.
~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki.
~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
~ Giris ga ma’aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka.
~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.
~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Allah Ya bada sa’a.
Ko Kun San Zuma Na Da Matukar Amfani
Zuma tana da matukar amfani ta fuskar kara lafiyar jiki, kuma tana magance cuttutuka da dama a jikin dan adam. Allah (S.W.T) ya bayyana mana muhimmancin zuma ga rayuwar ‘dan adam a cikin suratul (An Nahl: 69) kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya bayyana mana muhimmancin ta a wasu hadisai.
Ga Kadan daga cikin amfanin ta;
1.Tana bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji.
2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
2. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus)
3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.
4. Tana maganin gudawa.
5. Tana warkar da gyambon ciki – Ulcer.
6. Tana karfafa garkuwar jiki.
7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).
8. Tana sanya kuzari a jiki.
9. Tana rage kiba. Idan aka sha ta da ruwan dumi da lemun tsami kafin aci abincin safe zai taimaka wajen rage ‘kiba.
10. Tana saukaka narkewar abinci a ciki ga masu fama da rashin narkewar abinci.Indigestion
11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.
12. Tana kyautata lafiyar kwakwalwa.
13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
muna godiya sosai
ReplyDelete