KISAN GILLA Hausa Novel
KISAN GILLA Hausa Novel
Littafi na Daya (1)
Complete
E-book Suleiman Zidane Kd
Whatsapp 08161272634
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
MARUBUCIN YA RARA DA CEWA,
A wani zamani can baya mai tsawo da ya
shude anyi
wani babban birni mai suna madinatul
haswar
a cikin daular larabawa
birnin madinatul haswar ya bunkasa a kan
karfin
arziki girman kasa, karfin mayaka da yawan
al umma
sarkin dake mulkin birnin madinatul haswar
ya kasance adali mai tausayi da jin kan
talakawa ana kiransa da suna HISHAM IBN
UBAIDA
.
SARKI HISHAM yana da matar aure guda daya
jal mai suna
shamilat wadda ta kasance yar wani babban
sarki mai
mulkin wata kasa da ake kira da hushush
ana kiran wannan
sarki da SAHIBUL HILAYAT
sai da sarki hisham ya auri shamilat da
shekaru goma sha daya sannan Allah ya
albarkace su da samun juna biyu nan fa
sarki hisham da shamilat suka cika da
tsananin farin ciki
domin
a duniya basu da wani buri wanda yafi
ganin sun sami haihuwa saboda a shekarun
baya babu abin da basuyi ba, domin su sami
haihuwar amma abu ya gagara,
lokacin da mahaifin
shamilat ya samu labarin cewa 'yarsa ta
sami juna
biyu sai ya kamu da tsananin farin ciki fiye
da ita
kanta shamilat din da mijinta saboda shi
kuma bashi da burin da yafi yaga jikansa
kafin ajali ya riske shi kasancewar tsufa ya
riske shi
a ko yaushe ta Allah zata iya kasancewa
Al amin Ahmed Misau, Guyson nake magana,
bisa wannan dalili ne sarki sahibul hilayat ya
tashi manzanni da dukiya mai yawa ya aiko
su izuwa ga sarki
hisham yace ga wannan ayi
renon ciki kuma idan haihuwa tazo daf yana
son
shamilat ta je gida ta haihu, yayin da
wannan sako ya isa ga
sarki hisham sai hankalinsa ya dugunzuma
domin
baya son ya rabu da matarsa dai dai da
dakika daya
amma kuma yana matukar jin nauyin
surukin nasa don haka
sai ya amince da hakan ita kuwa shamilat
sai ta kamu
da matukar farin ciki saboda a rayuwarta
babu abinda
take so sama da ta kasance tare da
mahaifinta a ko yaushe
saboda ita kadaice 'yarsa a duniya
sarki Hisham yana da dan uwa yarima
ZAMARU wanda
ya kasance azzalumi kuma mara imani mai
tsananin son duniya
uwa daya
uba daya suke dashi da hisham, a zahiri
yarima zamaru
yana nuna cewa yana matukar kaunar dan
uwansa
sarki hisham amma a karkashin zuciyarsa
babu
abinda ya tsana sama da shi ba wani bane
ya haddasa
wannan gaba ba a tsakaninsu face kawai
hassada da
kyashi da kuma tsananin son KARAGAR
MULKI
TUN mahaifin su sarki hisham na raye ya
futa cewa hisham
ne zai gaje shi daga
wannan lokaci ne yarima zamaru yaji ya
tsani
dan uwansa sarki hisham ya fara tunanin
hanyar
da zaibi ya kawar dashi daga doron kasa
sau bakwai
yarima zamaru yana bayar da kwangilar a
kashe
hisham amma yana kubuta kasancewarsa
sadauki mai
dakawa maza gumba a hannu
Guyson nake magana Al amin Kenan
Lokacin da yarima zamaru yaga ya kasa
ganin bayan
sarki Hisham sai ya
zuba ido izuwa lokacin da tsufa zasu
riskeshi har
rai yayi halinsa
saboda ya tabbatar da cewa indai babu
sarki hisham
dole shine zai hau karagar mulki, ana cikin
wannan hali ne
na jiran lokaci kwatsam sai shamilat ta sami
juna biyu
hm Al amarin da ya kara dugunzuma
hankalin yarima zamaru kenan saboda ya
san cewa idan matar hisham ta haihu to fa
sarautar ta kara yi masa nisa, a ranar da
zamaru ya sami labarin cewa shamilat
ta samu juna biyu sai ya kasa zaune ya kasa
tsaye
har dare ya raba bai rintsa ba
Babban abinda ya kara jefa
shi cikin bakin ciki shine shima matarsa ba
ta taba
haihuwa ba don haka duk ranar da ya mutu
shi
kenan bashi da magajin mulki, cikin tsakar
dare yarima
zamaru na kai kawo a cikin turakarsa ya
kasa barci sai matarsa sarima ta farka
daga barci koda taganshi a tsaye yana kai
kawo saita dube shi
cikin tsananin damuwa ta mike da sauri
tasha gabansa
tana mai rike kafadunsa, tace yakai mijina
menene
ya tayar maka da hankali a yau har ka kasa
bacci?
Koda jin wannan tambaya sai yarima
zamaru ya yi ajiyar zuciya sannan yace
baki da labarin cewa matar sarki ta samu
juna biyu ne?
Sarina tayi ajiyar zuciya tace haba maigida
yanzu
a kan haka ne ka tayar da hankalinka har ka
kasa bacci koda jin haka
sai zamaru ya rufe sarina da fada yana cewa
bata da
hankali bata da kishin rayuwarta,
sarina ta bushe da dariya sannan ta ce ka
kwantar da hankalinka mijina ina so ka
sani cewa ni na san abinda ba ka sani ba
idan har kana so ka san abinda na sani
yanzu ka
tashi mu tafi izuwa can bayan gari wajan
wani bakon boka da yazo
cikin alamun karayar zuciya yarima
zamaru ya dubi sarina yace ke nifa na gaji
da maganganun bokayan nan
tunda an dade ana ruwa kasa na tsotsewa
kuma na gaji da gafara sa har
yanzu banga kaho ba
Guyson nake magana, sarina tayi murmushi
tace aiko bokaye
suna suka tara wannan bokan ya wuce
yadda duk kake
tsammani duk wani bayani da zan yi maka
ba zaka
gamsu ba don haka gani ya kori ji kawai
kazo muje wajansa
yanzu a cikin wannan daren cikin sirri
koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya
cika
da farin ciki kawai sai ya mike zumbur ya
kama shiri
yayi badda kama itama sarina yasa ta ta
batar da kamanninta sannan sukayi
hawa suka fice daga cikin birnin madinatul
haswar a sirrance ba tare da kowa ya
shaida su ba
sai da suka yi tafiyar kusan rabin
Sa a sannan suka iso gaban wani katon
dutse
wanda a kansa akwai wata yar karamar
bukka
abinda ya daurewa yarima zamaru kai shine
ganin matattakalar bene a kan dutsen
tamkar sassake dutsen akayi
aka samar da ita shi dai
zamaru ya san wannan dutse sama da
shekaru
talatin baya amma bai taba ganin wannan
matattakala
a jikinsa
ba tabbas wannan matattakala aikin aljanu
ne
bana mutum ba abinda zamaru ya ayyana
kenan a cikin
zuciyarsa
bayan zamaru da sarina sun tsaida
dokunansu a gaban dutsen sun sauka
sai suka daure dawakan nasu a jikin wata
bishiya sannan suka taka
wannan matattakala suka hau kan dutsen
suna isa gaban wannan bukka sai sukaga
bokan tsulum ya
bayyana a gabansu yana kyakyata dariya al
amarin da ya dan razana yarima zamaru
kenan ya dan ja da baya kadan , shi dai
wannan boka
ya kasance dogon mutum garjeje mai kirar
mutanan
farko jikinsa gaba daya a murde yake alamar
karfi ta bayyana karara a tare da shi yana da
yar
faffadar fuska kyakkyawa cike da kasumba
da gajeran gemu
babu riga a jikinsa face wata fatar damisa
wacce ya yafata bisa kirjinsa ta zagayo
izuwa bayansa
daga cikinsa zuwa gwiwoyinsa a rufe suke
da bante irin na fatar damisar da ya yafa
kuma
takalmin dake kafarsa ma anyi shine da
wannan fatar damisa
gaba dayan damatsansa na hagu dana
dama a cike
suke da gurayen tsafi , tabbas wannan boka
yana da kwarjini da cika ido kai da
ganinsa kasan cewa murucin kan dutse ne
wato bai fito ba
sai da ya shirya
bokan ya dubi yarima zamaru yayi
murmushi yace
kada kaji tsoro ya shugabana ni mai
taimako ne a gareka
ko ince zamu yiwa juna taimako ku biyoni
izuwa cikin bukkata mu zauna domin mu
tattauna sosai
koda gama fadin haka sai bokan ya juya ya
shiga
cikin bukkar nan take yarima zamaru da
sarina
suka bishi a baya ba tare da fargabar komai
ba
da shigarsu cikin bukkar sai yarima zamaru
ya sake cika
da tsananin mamaki domin kansa ne ma ya
kusan juyewa
saboda ya tsinci kansa ne a cikin wata
makekiyar fada wacce
ta kawatu ainun ninkin
fadar sarki hisham sau uku wadansu
kuyangin aljanu sunata hidima da kai kawo
bokan yaci gaba da tafiya a tsakiyar fadar ya
nufi inda karagar mulki take
su zamaru na biye dashi amma basu isa
inda karagar mulkin take ba sai
da suka yi taku dari da arba in, da zuwa sai
bokan ya zauna akan karagar mulki yarima
zamaru da sarina kuwa sai kuyangin aljanun
suka kama hannayansu suka kaisu izuwa
kan wadansu
kujeru dake daf da karagar mulkin suka
zaunar
dasu
nan da nan aka kawowa yarima zamaru da
sarina
ruwan inibi a cikin tambulan na zinare da
kofuna suka fara jika makoshinsu a sannan
ne bokan ya dubi yarima zamaru a karo na
biyu yace lale maraba
da yarima zamaru dan uwan hisham sarkin
gobe
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenan
koda jin wannan batu zamaru ya natsu
sosai
bokan ya ci gaba da bayani yana mai cewa
ka kwantar da hankalinka ya kai wannan
dan sarki
kayi sani cewa matarka tazo nan kafin kai
kuma
mune mukace ta kawo ka
mun san duk abin dake damunka da kuma
burin dake
zuciyarka
tabbas mune zamu magance maka dukkan
matsalarka muddin muma zaka bi umarnin
mu shin ka amince da wannan sharadi?
Koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya
dubi bokan cikin alamun rashin
fahimta sannan yace menene sharadin da
kake so ka gindaya mun
bokan yayi murmushi yace ina so ka dauki
alkawari cewar idan bukata ta biya zaka
raba birninka
biyu ka bani kaso guda na mallakeshi haka
kuma zaka bani rabin dukkan
dukiyarka
lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu
sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa
abin dake masa dadi yayi shiru yana tunani
bokan ya tuntsure da dariya alamun da ya
janyo katsewar
tunanin yarima zamaru kenan ya dago kai a
firgice
ya dubeshi yace ni ne Hizainu ibin Markasi
masanin sirrin gobe,
yakai wannan dan sarki ina so ka sani cewa
babu wani
abu da mutum ke samu a saukake kuma a
banza face
ya rasa wani abu
ina mai shawartarka daka dauki sharadina
ni kuma na
taimaka maka na sanar dakai duk abinda
zaka yi ka
samu biyan bukatarka kuma
yanzu ne kadai damarka
idan ka bari wannan dama ta wuce ka har
abada ba zaka samu wata ba
sa adda yarima zamaru jai wannan batu sai
ya kawo gwauron numfashi ya ajiye gami
da ajiyar zuciya ya sake yin dan guntun
tunani
sannan ya dubi boka
hizainu yace na yarda idan ka taimakeni
burina ya cika zan raba mulkina da dukiyata
gida biyu na baka rabi amma bisa shardi
guda
sharadin kuwa shine sai dai kayi rantsuwa
da girman
tsafi da kuma darajar iyayenka cewar a gaba
ba zaka yi yunkurin
rabani da mulkina ba
domin ka mallaki kasar gaba daya kuma ba
zaka taba cutar
dani ba ko wani nawa
koda jin wannan batu
sai idanun boka hizainu suka zazzaro ya
kamu da tsananin
mamaki saboda bai taba zaton cewa yarima
zamaru zai daureshi ba da jijiyarsa haka, al
amarin da ya jefa
shi cikin shakku da wasu wasi kenan ya
kama muzurai yana
kallon kuyanginsa dake kai kawo a cikin
fadar suna hidama
sai da yayi dan tunani da nazari sannan ya
bushe da dariya
nan take yayi rantsuwa da girman tsafi gami
da darajar iyayansa bisa kan cewa ba zai
taba neman
wani abuba daban a wajan yarima
Zamaru a nan gaba kuma ba zai cutar dashi
ba koda jin haka
sai farin ciki
ya lullube yarima zamaru yace shima ya
amince da bukatar
boka hizaunu
boka hizainu ya kyalkyala da dariyar murna
yace
gobe da safe idan kaje fada zaka iske dan
uwanka sarki hisha,
a kwance cikin cutar ajali kuma ba zai wuce
kwana bakwai ba a kwance rai zaiyi halinsa
abu na biyu da nake so dakai shine a yanzu
haka
matar sarki hisham ta haifi da namiji kuma
har ta
gama wankan jego ta baro can birnin
darul hushush ta taho izuwa nan birnin
madinatul
haswar tare da jaririnta da kuma dakaru
dubu biyar masu tsaron
lafiyarta
wadanda suka kasance zakwakuran mayaka
fasa taro lallai ka shirya
wadansu zakwakuran dakarun da suka fisu
jarumtaka wadanda zasu je su yake su su
kashe matar
sarki ya zamana cewa baka da wata
barazana a mulkinka ina mai
tabbatar maka da cewa a daren da dan
uwanka sarki hisham
zai mutu ne shamilat da jaririnta
zasu iso cikin garin nan
don haka duk yadda zakuyi kusa a tare su a
can cikin daji
kafin su iso kusa da wuri, kuma kada ka
kuskura ka shiga
cikin mayakan da zasu je yin wannan aiki
kuma ka
tabbatar da cewar anyi wannan aiki a cikin
sirri
ba tare da wani ya sani ba lokacin da yarima
zamaru
yaji wannan batu sai hankalinsa ya kara
dugunzuma fiye da ko yaushe ma ya dubi
boka hizainu cikin alamun tsananin
tsoro da damuwa yace yakai wannan boka
mai daraja
yanzu a ina zan samo dakarun da zasu iya
kashe
dakarun da sarki sahibul hilayat masu yiwa
shamilat da
jaririnta rakiya izuwa nan birninmu? Ka sani
cewa dakarun birnin darul hushush mayaka
ne na asali kada su ba wasa bane
boka hizainu ya sake bushewa da dariya
lokaci guda
kuma ya turbune fuskarsa yace babu wanda
zai iya
yi maka wannan aiki face sarkin yakinka
amzadu ibn karlyas
koda jin haka sai yarima zamaru ya cika da
tsananin mamaki gami da tsoro yace
to yaya amzadu zai amince yayi min wannan
aiki alhalin kasan cewa ya kasance
babban aminin sarki hisham wanda a shirye
yake ya
sallama rayuwarsa domin kare ta sarki da
iyalansa
koda jin haka sai boka hizainu ya sake
bushewa da dariya
sannan yace
da zarar sarki hisham ya mutu kaine sarki
komai
ya dawo karkashin ikonka da mulkinka
a wannan lokaci kana da ikon sarrafa komai
da kowa da karfin karagarka
a daren da sarki
hisham ya mutu ka tura akamo sarkin yaki
amzadu da iyalansa a matsayin kana
zarginsa
da laifin sawa sarki wannan ciwon ajali
tunda kowa ya
san cewa dare da rana yana tare da sarkin
bayan an tsare su a kurkuku shida iyalan
nasa sai
kasa a fito dashi shi kadai azo dashi har
cikin
turakarka ka kadaita dashi a sannan ne zaka
gaya masa
bukatarka ta son ya
debi zakwakuran yaransa suyi
bada da kama suje su kashe matar sarki
shamilat da jaririnta
da duk dakarun da sukayi musu rakiya
izuwa nan birnin madinatul hashwar idan
kuma yaki koyayi wani abu ba dai dai ba
sabanin umarnin da ka bashi
zakasa a kashe iyalansa idan kuma yayi aikin
daidai
bisa nasara zaka bashi babban matsayi a
fadarka fiye
da wanda yake da shi a yanzu...
Suleiman Zidane Kd
08161272634
KISAN GILLA
Littafi Na Daya (1)
Part B.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Fiye da wanda yake dashi a yanzu.
lokacin da boka hizaunu yazo nan a
zancensa
sai yarima zamaru ya kamu da tsananin
farin ciki
nan take ya kama kyalkyala dariya saboda
murna sannan ya dubi boka huzainu yace
yakai wannan boka mai daraja hakika ka
cika makiru uban masharranta na duniya
Hm
babu makawa wannan dabara taka saita yi
nasara
shin yanzu ka tabbatar mini da cewa idan
na koma gari zan iske sarki ya kwanta cutar
ajali
koda jin wannan tambaya sai boka huzainu
yayi murmushi yace yau fa
shekara bakwai kenan ina shiri da jiran
zuwan wannan
rana saboda me ma zaka rinka shakku bisa
furucina ku koma
gida kuje ku sha barcinku a cikin wannan
dare lallai gobe da safe za a yi kiranka izuwa
fada kaga zahiri
nan take yarima zamaru da sarina matarsa
suka yi wa boka
hizaunu sallama suka fito daga cikin gidan
nasa suka hau dawakansu suka koma
cikin birnin madinatul hashwar ba tare da
wani ya shaida suba akan hanya
.hakika masu iya magana sunyi dai dai da
sukace
tsafi gaskiyar mai shi kuma maso abinka
yafika dabara
Kashe gari kuwa da sassafe aka tashi manzo
daga gidan sarki ya ruga izuwa gidan
yarima zamaru ya sanar
dashi cewar ya rugo izuwa gidan sarauta
ana nemansa yanzu yanzu
a majalisa koda jin wannan batu sai yarima
zamaru
ya dubi manzon cikin alamun tsananin
mamaki
da tsoro yace lafiya ake namana a fada
da sassafen nan haka
Manzon ya risina yace ai sarki ne ya kamu da
wani irin ciwo
farat daya ko mikewa zaune ma ya kasa,
koda jin
haka sai yarima zamaru ya dimauce ya ruga
da gudu izuwa cikin turakar matarsa
sarina
da shigarsa ya iske sarina a kwance tana
shirin tashi
kenan
nan take ya labarta mata labarin da manzo
yazo dashi
dajin haka sai sarina ta mike zumbur daga
kan gado ta daka tsalle ta rungume
zamaru
tana mai kyalkyala dariyar murna tana cewa
shi kenan
bukatar mu ta biya
nan dai zamaru yayi sauri ya kintsa sannan
ya
bi manzo suka wuce izuwa gidan sarauta
da isar su ya wuce kai tsaye izuwa cikin
turakar
sarki inda ya iske sarki hisham a kwance
bisa gado fuskarsa ta cika
da wadansu irin kuraje babu kyan gani
ga likitoci da manyan bokayan garin nan
sun taru a tsaitsaye a gefen gadon
a daya bangaren kuwa gaba dayan yan
majalisar
sarkine a zazzaune suma sunyi jigun jigun
cikin alamun tashin hankali
koda shigowar yarima zamaru sai sarki
hisham ya
dubi yan majalisarsa da dukkan likitocin sa
da bokayan
nasa har dama duk hadimansa
dake cikin turakar yace kowa ya fita ya
barsu yana son
ya gana da dan uwansa zamaru
a wannan lokaci sarkin yaki amzadu na
zaune daf da sarki ya rike hannayan
sarki yana ta zubar da hawaye kuma ya
kurawa
sarki hisham idanu kodajin umarnin da
sarki ya bayar sai
kowa ya fice daga cikin fadar amma shi
sarkin yaki amzadu saiya kasa mikewa
ya fita har saida sarki ya dubeshi ya budi
baki yace yakai babban masoyina ka
sani cewa a rayuwata ban taba boye maka
wani al amarina ba saboda
kauna da yardar dake tsakaninmu amma
yau kuma bana son ka san wani babban
sirri dake tsakaninmu da dan uwana
zamaru
saboda uwa daya uba daya ya wuce wasa
don haka ina son ka fita ka bamu wuri
koda jin wannan batu sai mamaki ya
turnuke sarkin
yaki amzadu domin irin haka bata taba
faruwa ba
tsakaninsa da sarki
cikin sanyin jiki ya mike tsaye yana waigen
sarki yana
zubda hawaye ya fice daga cikin turakar
kuma ya janyo musu kofa ya rufe
ta
faruwar hakan keda wuya sai sarki hisham
ya dubi yarima
zamaru ya yafito shi da hannu ya sake budar
baki da kyar
yace
matso nan kusa dani ya kai dan uwana
rabin jikina
cikin nuna alamun tsananin damuwa har
idanun
na zubar da hawaye zamaru ya je ya zauna
agefen
gadon sarki daf dashi suka kurawa juna
idanu
har izuwa tsawon yan dakiku
sannan sarki ya dubeshi yace
yakai dan uwana kayi sani cewa a daren jiya
na kamu da wannan cuta farat daya
kuma likitocina da bokayena sunyi iya bakin
kokarinsu akan
su gano abinda ya haddasa wannan cuta da
maganinta sun kasa, tabbas jikina
ya bani cewa
mutuwa zanyia cikin yan kwanaki kalilan
ka sani cewa bani da wani makusanci
wanda yafika sai kuma matata shamilat da
abinda ta haifa
tuni mahaifin shamilat sarki sahibul hilayat
na birnin darul hushash ya aiko da manzo
cewar shamilat da jaririnta data haifa sun
taho nan birnin bisa
rakiyar dakarunsa kuma zasu iso a daren
kwanaki bakwai masu
zuwa
koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai
hawaye ya zubo masa yaci
gaba da cewa
a duniya bani da wani buri wanda yafi naga
dana na cikina
wanda ban same shi ba sai bayan na shafe
shekaru
goma sha daya dayin aure amma gashi
burina ba zai cika ba
domin ina ji
a jikina cewar kafin shamilat ta iso garinnan
ajali ya riskeni
Al amin Ahmed Misau, guyson nake magana
koda jin haka sai yarima zamaru ya
rungume
sarki hisham yana mai fashewa da kuka
yace yakai
dan uwana kayi sani cewa dukka mai rai
baya
fidda tsammani rabo kuma babu wata cuta
wadda bata
da magani a doron kasa don haka ni yanzu
ina so ka bani dama na
garzaya izuwa makotan kasashenmu na
nemo maka magani
koda jin wannnan batu sai sarki hisham ya
busheda
dariya cikin
Matukar karfin hali da juriya, al amarin da
yayi
matukar baiwa
yarima zamaru mamaki da tsoro kenan yaji
a ransa
kamar sarki ya gane cewa yana da masaniya
a kan
wannan ciwo da ya same shi, lokaci guda
kuma sai yaga sarki hisham ya fashe da
matsanancin
kuka na bakin ciki
da kyar zamaru ya rarrasheshi yayi shiriu
sannan ya dube shi yace yakai dan uwana
tunda na hau
kan karagar mulki ban taba kamuwa da
ciwon da ya kaini
ga kwanciya ba sai jiya fruwar hakan ce ta
tabbatar mini da cewar nesa ta
matso kusa ina so ka sani cewa ba wani abu
bane ya sa na sallami
kowa daga cikin dakin nan ba sai domin
muyi wani sirri
guda daya wannan sirri ba komai bane face
ina son na roke ka wata alfarma guda daya
ka sani cewa rayuwa ban taba tauye wani
hakki naka ba
a matsayinka na kanina kuma baka taba
neman wani abu a wajena ba wanda banyi
maka shi ba tun daga kuruciyarmu
kawo izuwa girmanmu a lokacin da
mahaifinmu ya ke raye da kuma ya mutu
koba haka bane?
Yarima zamaru ya gyada kai a lokacin da
hawaye na gaskiya ya zubo masa
domin take yaji tausayin sarki hisham ya
ratsa jikinsa
saboda sanin cewar gaskiyar ya fada sai
yace
hakika ka fadi iyakar gaskiya yakai dan
uwana
sarki hisham yayi dan guntun murmushi
sannan yace
ni kuwa ban taba neman wani abu ba a
wajanka kuma ka taba saka mini da kwara
zarra ba koda karfin jikinka
bisa duk irin abubuwan alherin da nayi
maka a rayyuwa
zamaru ya gyada kai yana mai nuna alamar
haka ne
sarki hisham yaja dogon numfashi sannan
yace alfarmar da nake nama a wajanka itace
idan har matata ta iso birnin nan a raye ita
da jaririnta
kada ka sa a kashesu ko a boyesu a wani
wuri bisa
tsoron nan gaba zasu iya rabaka da
mulkinka
idan har ba zaka iya zama tare dasu ba
kamar yadda na zauna tare dakai tsawon
shekaru talatin alhalin na san
cewa baka kaunata ka tsaneni kamar yadda
ka tsani mutuwarka
saboda karagar mulki
ina son ka tura su izuwa can kauyen limras
su karasa sauran rayuwarsu a can a
matsayin talakawan gari
kawai koda ba zaka taimaka musu da komai
ba
na san wacece matata shamilat macece mai
zuciyar maza ko
babu aure zata iya rike kanta kuma tare da
abinda ta haifa
Guyson Sunana
Koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai
hawaye ya sake zubo masa a lokacin da ya
kurawa
yarima zamaru idanu
nan take yarima zamaru yaji ya kamu da
tsananin kunyar sarki hisham gami da
matukar tausayinsa har shima hawaye ya
sake zubo masa
kawai sai yarima zamaru ya mike tsaye ya
juyawa sarki hisham baya yace nayi alkawar
idan har matarka da abinda
ta haifa sun shigo cikin garinan a raye lallai
zan zamo mai rike su da amana kamar
yadda ka
rikeni har izuwa sa adda mutuwa zata
rabani dasu
koda
gama fadin hakan sai yarima zamaru ya fice
daga cikin turakar yana kuka da fitowarsa
yana kuka yayi arba da sarkin yaki amzadu
a tsaye shi kadai a kofar dakin nan fa sukayi
wani irin kallo kallo na rashin yarda kawai
sai
yarima zamaru ya yiwa amzadu dan guntun
murmushi yyi tafiyarsa shi kuma sai ya bude
kofar turakar
da sauri a dimauce ya shiga ciki
da shigarsa yayi arba da sarki
a kwance kamar yadda ya fita ya barshi
dazu
cikin hanzari sarkin yaki amzadu yaje ya
sake zama daf da sarki ya dubeshi a
firgice yace
ya shugabana me ya faru tsakaninka da dan
uwanka na ga shima ya
fita yana kuka
koda jin wannan tambaya sai sarki hisham
yayi dan guntum murmushi cikin
matukar karfin hali sannan yace Alhini ne na
rabuwa
da juna ya sakaga duk muna kuka
domin mutuwa zata shammace
mu a lokacin da bamu taba zato ba tafi na
sallame ka
wasiyata ta karshe a gareka ita ce ka tuna
da duk
irin abubuwan alherin da nayi maka a
rayuwa
a duk sa adda wata masifa ta taso kada ka
kasance mai
yin butulci a bayana
sa adda sarkin yaki amzad yaji wannan batu
daga bakin sarki sai ya kamu
da tsananin
mamaki kuma ya kasa fahimtar abinda yake
nufi har ya budi baki da nufin ya sake
tambayarsa sai ya kasa
nan dai ya juya ya fice daga cikin turakar
cikin tsananin
damuwa da tashin hankali wanda bai taba
tsintar
kansa ba
.
Daga wannan rana sarki hisham ya ci gaba
da ciwo wanda
ba sauki kuma babu alamar za a sami saukin
har saida ta kai cewa ko motsi da baki baya
iya yi
abinci ma da ruwa idan aka dura masa baya
shiga cikinsa
a ranar kwana na bakwai ne ciwon ya
tsananta
ainun
hankalin kowa ya dugunzuma a tsawon
kwanaki bakwan da sarki hisham ke
kwance
cikin jinya yarima zamaru bai sake zuwa ya
duba shiba
amma sarkin yaki Amzad kuwa dare da rana
yana tare dashi
a ranar kwana na bakwan da magariba rai
yayi
halinsa nan fa labari ya bazu a ko ina cikin
kasar mutane
suka kama koke koke sai a wannan
lokacinne aka
ga yarima zamaru ya shigo cikin fadar a
lokacin da aka fara shirye shiryen binne
sarki ana ganin yarima zamaru hankalin
kowa ya tashi
domin an san cewa dolene yanzu komai ya
sauya a birnin duk irin adalcin da ake yiwa
talakawa
an daina kuma za a matsa musu a kan biyan
haraji mai yawa za a rinka zaluntarsu
babu sauran masu jin dadi da kwanciyar
hankali
face sarakai da attajirai wadanda zasuyi
biyayya ga sabon sarki Yarima zamaru
nine dai Al amin Ahmed misau
Guyson nake
Bayan an gama jana izar sarki hisham an
binne shi a cikin dakin da aka binne
sarakuna arba in da uku na
kasar sai yarima zamaru ya tara gaba dayan
yan
majalisar kasa a dakin taro ya tabbatarmusu
da cewa
gobene za ayi bikin nadin sarautarsa
sannan kuma ya umarci sarkin yaki da ya
tabbatar da tsaro a ko ina
a cikin birni da kewaye kuma ya sanar da
dakarun dake tsaron
kofofin gari cewa ba shiga kuma ba fita
daga yanzu har izuwa gobe sa adda za a
kammala bikin nadin
sarautar tasa
koda jin wannan umarni sai kowa ya cika da
tsananin mamaki
amma sai gaba daya yan majalisar sukayi
shiru suna masu sunkuyar da kansu kasa
saboda
tsoron yarima zamaru aka rasa wanda zaice
kala sai sarkin yaki amzadu
ne ya dubeshi yace yakai sarkin gobe kayi
sani
cewa wannan hukunci da ka yanke baiyi dai
dai ba domin tsarin mulki bai yarda da
hakan ba saboda bai dace ba ka
hana mutane zuwa cikin gari nan ba koda
ka hanasu
fita a wannan lokaci da ake ciki na babban
rashin da akayi na dan uwanka
ka sani cewa mutane da yawa zasu zo ne
domin
su ziyarci kabarin sarki su nemi tabarrakinsa
kuma suyi masa addu a wasu kuma zasu
kawo ziyara ne izuwa
kallon bikin nadin sarautarka,
sarakuna da yawa daga makwabtan
kasashe ma zasu zo wannan gagarumin biki
kafin sarkin yaki amzad ya gama rufe
bakinsa tuni yarima zamaru ya tari
numfashinsa
yana mai daaka masa tsawa yace wanene
kai harda zaka gaya mini abinda zanyi
ka sani cewa in banda kana da matukar
muhimmanci
da amfani da yanzu take zan sauke ka daga
kan mukaminka
na sallameku kowa ya kama gabansa nan
take kowa
ya kama gabansa jikinsa a sanyaye ya fice
daga cikin dakin taron
aka bar yarima zamaru a zaune shi kadai
Al amin Guyson, lokacin da sarkin yaki
amzad ya isa
kofar gidansa sai ya hango kofar gidan
wayam babu dakarun
da suke yi masa gadi kuma kofar gidan a
bude take wanwar al amarin da yayi
matukar razana shi kenan yayi wuf ya sauko
daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa
kawai sai ya ruga da
gudu izuwa cikin
gidan yana mai kiran sunan matarsa
da danta himar wanda ya kasance yaro dan
shekara
hudu amma shiru baiji sun amsa ba kuma
baiji duriyarsu ba
,,,
Al amin Guyson Kenan
Anan Zan dakata
amma Kafinnan
Nidinne dai
AL AMIN AHMED MISAU
guyson inkiya
Admin Na zauran Labarai
08161272634
KISAN GILLA
Littafi Na Daya (1)
Part C.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Yana isa falo yayi turus saboda
tsananin kaduwa
da mamaki bisa abinda yayi arba
dashi ba wani abu ya gani ba face
yarima zamaru zaune akan
kujera cikin shigar yaki ya harde
kafafu daya kan daya yana kallonsa
cikin murmushi abuna farko da ya
daure masa kai shine
yaya akayi zamaru ya riga shi zuwa
nan alhalin a can gidan sarauta
ya barshi kuma yaushe ma ya canja
kayansa har yazo nan din kawai sai
amzad ya baiwa kansa amsa
yace tabbas wannan al amari ne na
tsafi cikin alamun
fushi sarkin yaki ya dubi yarima
zamaru yace ina iyalina
tuni
jikina ya bani cewar wani abu
makamancin wannan sai ya
faru kuma yanzune na tabbatar da
cewar kana da hannu
a kan ciwon da sarki ya samu
wanda ya zama sanadiyar
ajalinsa
lokacin da yarima zamaru yaji
wannan batu sai ya bushe da
mahaukaciyar dariya
lokaci guda kuma ya turbune fuska
yace ina son mutum mai
kaifin kwakwalw
da hasashe irinka
tabbas duk abinda ka fada haka
yake gaskiya ne nine na
kashe sarki domin na sami wannan
karagar mulki
wacce ta gagareni tsawon shekaru
ban zo nan domin muyi doguwar
magana nazo ne domin na sanar
dakai
cewar iyalinka suna hannunmu
kuma mun boye su a inda babu
wanda ya isa
ya gansu ko ya dauko su face mu
da kanmu ina son
yanzu take ka debi dakaru dubu
dari shida a cikin shigar badda
kamanni ku nufi
jeji na bayan gari ku tari gimbia
shaliat tare da dakarun mahaifinta
wadanda sukayi mata rakiya izuwa
nan birnin
ina son duk yadda za ayi ka kashe
su gaba dayansu
ban son mutum daya ya tsira
da jaririn da ta haifa ku tabbatar da
cewa kun kashe shi idan kuka yi
wannan aiki
dai dai zan dawo maka da iyalinka
gobe da safe idan kuma ka ki bin
umarnina gawar iyalanka zamu
kawo maka
idan kunne yaji gamgar jiki ya tsira
kuma shawara ta rage ga mai shiga
rijiya
Koda gama fadin hakan sai yarima
zamaru yayi
girgiza ya bace bata daga cikin
dakin yana mai
kyalkyala dariya tamkar bai taba
wanzuwa ba a ajan
Al amin Guyson nake
nan fa sarkin yaki amzad ya
dimauce
kuma ya fusata ainun bai san sa
adda ya kurma uban ihu ba kuma
ya fashe da matsanancin kuka
saboda tsananin bakin ciki da
takaici daga can sai ya juyada sauri
a guje ya koma
kofar gida ya kama dokinsa ya hau
ya zabureshi da gudun tsiya
A can daji kuwa Gimbia shamilat na
zaune a cikin keken
doki
rungume da jaririnta dakaru sun
kewayeta gaba da baya
dama da hagu ana tafiya saboda
kwarjinin wadannan dakaru da irin
kayan yakin da suke dauke dasu
babu abinda zai gansu bai yi
shakkarsu
ba , da yake duhu yayi gaba dayan
dakarun sun kunna fitilun itace don
haka hanya sai tayi haske
sai sauri ake
tayi saboda an san cewa saura baifi
tafiyar rabin sa a ba
a iso cikin birnin madinatul
hashwar
a wannan lokacinne shamilat na
cikin tsananin farin ciki
sai yawan kallon
jaririnta take yi tana murmushi
saboda tunanin cewa a yau ne sarki
hisham zai ga dan cikinsa da idonsa
abinda ya shafe shekara da shekaru
yana burin gani
bai gani ba
saboda zakuwar da tayi taga an isa
cikin garin har umarni take
bayarwa a kan a karawa dawakai
kaimi
nan fa aka ci gaba da gudu kai kace
hari za a kai
kaico rashin sani yafi dare duhu
ashe
wadannan zuga ba su san cewa
mahallaka suke kai kansu ba
lokacin da tawagar
gimbiya shamilat suka iso
dai dai wani fili mai fadi wanda
tsakaninsa da karshen dajin bai
wuce zira i arba in ba
sai kawai sukaji ana yi musu ruwan
kibiyoyi ta gabas da yamma kudu
da arewa wayyo Ajali idan yayi kira
sai an amsa
babu makawa
Nan fa dakarun da dawakai suka
rinka ihu da haniniya suna zubewa
kasa matattu kafin su ankara an
kashe kaso daya a cikin kaso uku
ita kanta gimbiya shamilat taga
matukar tashin hankali domin ta
gefen idanunta da kunnuwanta
kibiyoyi
suka rinka giftawa da kyar aka
sami wasu zakwakuran mayaka
suka rinka kade kibiyoyin
da ake harbo mata da takubbansu
A sannan ne kuma dakarun suka yi
wata dabara
wadanda keda
garkuwoyi sai suka yi kawanya a
tsakiya suka kare sama da kasansu
aka sanya gimbiya shamilat da
sauran dakarun a tsakiyar da irar
duk da haka sai aka ci gaba da
harbo kibiyoyin
har zuwa tsawon lokaci
a wannan lokaci jaririn shamilat na
ta faman kuka itama gimbiya tana
kukan sai da aka saina harbo
kibiyoyin
sannan shugaban dakarun ya dubi
gimbiya shamilat yace
ranki ya dade yanzu me ye abinyi
ba muga wadanda suka kawo mna
wannan hari ba
har yanzu domin sun boye ne a
cikin duhuwar bishiyoyi
shin zamu ci gaba da tunkarar
birnin madinatul hashwar ne
wanda tazararmu da shi a yanzu
bata wuce zira i arba in ba ko
zamuyi kokarin komawa da baya
ne
domin mu tserar da rayuwarki data
wannan yaron naki
sa adda shugaban dakarun yazo
nan a zancensa sai hawaye ya
zubowa gimbiya a lokacin da
zuciyarta ta buga da karfi
kuma tsoro ya shigeta kawai sai ta
dubi shugaban
dakarun ta ce sarki Hisham ya fadi ''
cikin kaduwa shugaban dakarun ya
cubeta yace
ranki ya dade ya akayi kika sani?
Shamilat ta fara zubar da hawaye
ta ce inda
mijina yana raye babu yadda za ayi
a taremu a kan iyakarsa
domin a hallakamu
abu ne mai hadarin gaske muci
gaba da tunkarar
cikin birninnan yanzu kawai muyi
Kokarin komawa da baya in munyi
sa a mu tsira da ranmu
kafin gimbiya ta gama rufe bakinta
sai kawai
sukaji sukuwar dawakai an
durfafosu kafinsuyi wani
yunkuri dakarun masu yawan
gaske ninkinsu uku sunyi musu
kawanay
gimbiya shamilat ta fito daaga cikin
keken dokinta a fusace
rike da jaririnta domin taga ko
suwaye ne wadannan dakaru da
suka kawo musu hari
kawai sai taga ashe dakarun sunyi
shiga ne irin ta
bakaken kaya ba shigar kayan
yakin dakarun birnin madinatul
hashwar ba kuma duk
sun rufe fuskokinsu da bakin kyalle
idanunsu kadai ake gani
a dai dai wannan lokaci ne
shugabam dakarun gimbiya ya
rugo gareta ya dubeta
cikin alamun tsananin tsoro da
damuwa yace
haba ya shugabata yaya zaki fito
fili haka gaban wadannan makiya
alhalin muna kare rayuwarki da ta
jaririnki
shamilat tayi ajiyar zuciya tace ai
zancen kare ni da
jaririna ya kare ka dubi wadannan
dakaru ka gani ai sarkin yawa yafi
sarkin karfi kuma ba zamu iya guje
musu ba
duk mutuwa zamuyi ni kawai
yanzu ina son na san wanda ya
turo a kasheni kafin na mutu
Al amin Guyson Sunana
don bana son na mutu cikin wasu
wasi
koda gama fadin hakan sai gimbiya
shamilta ta dubi wadannan dakaru
masu bakaken tufafi
ta daka musu tsawa tace ku su
waye kuma waye ya turoku ku
kasheni
mtar sarkin birnin madinatul
hashwas
dajin wannan tambaya sai bakaken
dakarun suka dare
shugabansu ya ratso ta tsakiyarsu
ya matso kusa da ita ya tsaya
duk da cewar fuskarsa a rufe take
idanunsa kadai ake gani saida
gimbiya shamilat ta shaida ko
wanene shi nan take hawaye ya
zubo daga cikin idanunta
ta dubeshi tace yakai Amzad yanzu
dakai za a hada baki aci amanar
mijina
Yanzu ashe dama zaka iya yiwa
sarki butulci aashe zaka iya
mancewa da duk
irin halaccin da yayi maka a rayuwa
sa adda shamilat tazo nan a
zancenta sai sarkin
yaki Amzad ya kwaye fuskarsa sai
ga hawaye na zuba masa a lokacin
da suka kurawa juna idanu shi da
ita
tsawon yan dakiku dayansu baice
uffan ba sannan Amzad yace ki
gafarceni ni ya shugabata idan ban
bi umarni ba nima zan rasa matata
da dana
Koda jin haka sai shamilat ta fashe
da kuka tace
haka ne rai baifi raiba amma kafin
ku kashe mu
ina son ku fada mun iyakar
gaskiyar menene ya faru ga mijina
dajin wannan tambaya sai hawaye
ya sake zubowa sarkin yaki amzad
ya ce mijinki ya mutu
koda jin haka sai jiri ya debi
shamilat ta yanke jiki zata fadi kasa
cikin zafin nama amzad ya daka
tsalle ya dira a gabanta ya tallafeta
tare da jaririnta yana mai baiwa
dakarunsa umarnin su hallaka
dakarun gimbia
kaico Ajali ba a sa ma rana nan da
nan dakarun amzad suka kama
ragargazar dakarun shamilat
wuri ya hargitse banda ihun
mazaje babu abinda mutum ke ji
duk da cewar sarkin yawa yafi
sarkin karfi sai da aka jima ana
gumurzu a karshe dai ragas aka yi
aka karar da gaba dayan daakarun
kowanne bangare ya zamana cewa
babu daya da ya rage a raye face
sarkin yaki Amzad a dai dai
wannan lokaci ne gimbia ta farfado
daga dogon suman da tayi
idanunta suka bude tana mai gani
dishi dishi idanunta na washewa
tayi arba
da sarkin yaki amzad a zaune daf
da ita rungume da jaririnta
gaba dayan dakarun dake wajan na
kwance a kasa sun zama gawa
shamilat ta mike tsaye zumbur ta
rugo iduwa wajan amzad ta miko
hannayanta
da nufin ta karbe jaririnta amma sai
ya tokare da kotar takobinsa a
kirjinta yace ya shugabata
kiyi sani cewa yarima zamaru ya
umarceni da na kashe ku keda
jaririnki in ba haka ba kuwa sai ya
kashe matata da dana ba zan iya
kashe ku ba
domin idan nayi haka naci amana
Koda yazo nan a zancensa sai ya
durkusa bisa gwiyoyinsa agaban
shamilat a lokacin da idanunsa
suka
ciko da kwalla yace ina rokonki
daki bar garin nan kuma karki
koma birnin darul hashbush ki
sanar da mahaifinki abinda ya faru
domin kina gaya masa zaice zai
yaki sarki zamaru kuma kin
sani cewa mayakan mu sun ninka
nasa sau goma a yawa da karfin
makamai
cikin tsananin bakin ciki shamilat ta
fashe da kuka
kamar ba zata daina ba daga can
saita dago kai idanunta sunyi
sharkaf da hawaye tace shi kenan
ka bani dana nayi alkawarin
zan tafi izuwa wata nahiyar daban
na reni dana a can har
abada ba zan dawo nan ba kuma
ba zan taba gayawa dana
matsayinsa ba
koda jin wannan batu sai hawaye
ya zubowa sarkin yaki amzad ya
dubeta yace
ba zan iya baki yarima ki tafi dashi
ba
cikin razana shamilat tace yanzu
kana nufin zaka rabani
da dana kenan wanda shi kadai ne
abinda ya rage mini a duniya
amzad yace
kawar kuwa domin barinsa
awajanki ba karamin hadari bane
nayi miki
akkawari zan reni wannan yaro a
cikin birnin madinatul
hashwar
kusa da karagar mulkinsa ba tare
da ya san ko shi wanene ba
kuma komai dare dadewa in dai
kina raye yana raye nima ina raye
saina sadaku
zan tsare lafiyarsa da ransa kamar
yadda na tsare na mahaifinsa
wannan shine kadai
gatan da zamu iya yiwa kanmu da
wannan jariri
naki idan har muna son mu tsira da
rayukanmu
sa adda sarkin yaki amzad yazo
nan a zancensa sai shamilat ta sake
fashewa da kuka daga can sai ta
matso daf da amzad ta shafa kan
jaririn ta sumbaci goshinsa sannan
kuma ta ciro wata laya dake
wuyanta ta
Daurata a wuyan jaririn ta dubi
amzad tace
ina da laya irin wannan sak don
haka ka gayawa dana
cewar duk ranar da yaga mai irin
wannan laya ba wata ba
ce face mahaifiyarsa
koda gama fadin hakan sai ta karbi
jaririnta ta rungumeshi
a kirjinta ta sake fashewa da kuka
al amarin da ya karyar da zuciyar
sarkin yaki kenan ya ji ya kamu da
tausayinta fiye da ko yaushe
sai da ta jima a kankame da jaririn
sannan sarkin
yaki ya karbeshi ta tafi izuwa inda
keken dokinta yake tana waigen
jaririn nata
tana zubar da hawaye
Wow nIma Al amin Guyson na
tayata haka dai taje ta zauna a kan
keken dokin
ta sakarwa dawakan linzami suka
zabura da gudu suka nausa da ita
cikin
daji suka nufi wani bangare daban
wanda bai shafi nahiyar ba gaba
daya
a sannan ne shima sarkin yaki
Amzad ya tafi da jaririn izuwa inda
dokinsa yake ya kama ya hau ya
nufi
hanyar da zata kai shi cikin
madinatul hashwar
a lokacin da yake bacewa a cikin
duhun daren
tun kafin sarkin yaki ya iso kofar
shiga gari ya boye jaririn a bayansa
tamkar baya dauke da komai kawai
ya wuce gaba masu gadin kofar
garin
ba tare da jaririn yayi kuka ba
ai kuwa yana isowa bakin kofar sai
masu gadin suka tare shi saboda
basu gane shiba
sakamakon yana sanye ne da
bakaken kaya kuma basu ga sa
adda ya fice daga cikin garin ba
tare da dubun nan daakarunsa
saboda ta wata barauniyar hanya
suka fice
masu gadin na tare shi sai yayi
sauri ya bude
fuskarsa don kada su bata masa
lokaci koda suka dallare fuskarsa da
madubi
sukaga shine sai suka yi sauri suka
bude masa kofa ya shigo suna
masu binsa da kallo cikin alamun
tsananin mamaki domin su dai
basu ga lokacin da ya fita daga
cikin garin ba kuma tunda suka
ganshi a cikin shiga ta
bakaken kaya lallai sun san cewa
wani aiki ne na sirri yaje ya gabatar
amzad na shiga cikin gari bai zame
ko ina ba sai gindin wata karuwa
wacce ake kira kimaratu
a wannan lokaci dare ya fara
nisawa kuma sawu ya dauke ba a
jin sautin komai face haushin
karnuka amzad ya kama buga
kofar gidan da karfi
a fusace kimaratu tazo ta bude
kofar tace wanene nan yake neman
fasa mini kofar gida ka kama
gabanka
ina da abokin kwana a ciki
koda jin haka sai amzad ya daka
mata tsawa yace bude kofar na
shigo nine
sarkin Yaki Amzad
jikin kimaratu na karkarwa tayi
sauri ta bude kofar nan take amzad
ya mika mata
jaririn sannan ya danka mata jakar
kudi
cike da dinare yace wannan kudine
dinare dubu dari uku ki rike su ki
reni wannan jariri har izuwa
lokacin da na bukaceshi
idan wani abu ya tafa lafiyarsa a
bakacin ranki
.
SHIN SARKI ZAMARU ZAI CIKA
ALKAWARIN DAKE TSAKANINSA DA
BOKA HIZAINU.??
.
YAUSHENE SHAMILAT ZATA SAKE
GANIN DANTA???
.
ME ZAI FARU IDAN DAN SHAMILAT YA
GIRMA ???
.
MU HADU A LITTAFI NA BIYU
DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI
DAGA MARUBUCIN LITTAFIN
ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
KANO
WANDA NI AL AMIN AHMED MISAU
INKIYA GUYSON
NAYI TYPINGDINSHI
NAKE CEWA SAI MUN HADU A NA
BIYUN
Whatsapp 08161272634
0 Response to "KISAN GILLA Hausa Novel"
Post a Comment