Hanyoyin Magance Cututtukan Da Suke Damun Al'aurar Mata, Wato (Vaginal Disease)
Hanyoyin Magance Cututtukan Da Suke Damun Al'aurar Mata, Wato (Vaginal Disease)
Kamar yadda bincike ya nuna cewa akwai cututtuka da yawa masu damun al'aurar 'ya'ya mata, kama daga balagarsu zuwa fara xaukar ciki har zuwa dina al'adarsu. Kamar:
(1)Warin gaba (odour):- Warin gaba na 'ya'ya mata yana samuwa saboda wasu dalilai da suke jawo shi kamar haka:
1- kwana da pant
2- qin wanke farji bayan jima'i.
3-qin wanke farji da ganyen magarya da misali bayan an yi al'ada.
4-barin wando ya kai kwana uku a jiki.
5-kama ruwa da ruwa mai sanyi qarara.
6-Qin wanke gaba bayan an tsuguna a Masai. ko wanke gaba da sabulu, anfiso ki wanke farjinki da natural ruwa.
7-Mace ta ringa biyawa kanta buqata da hannu ko wani abu.
Ki sani cewa wari yana fitowa daga gurare uku kamar haka:-
Hammata.
Farji.
Baki.
Saboda haka lallai ne ki bada kulawa ta musamman a wannan gurare.
FA'IDA; Mace mai son kar miji yaji wari a gareta yayin saduwa sai ta nemi:
a)Miski. b)Ambar c)Ganyen magarya d)Rihatul Hubbi. e)Zam-zam. f)Ma'ul – miyahi
Ki haxasu guri xaya ki tafasa kaxan in ya huce ki zuba a buta ki qar ruwa dashi kuma ki shafe gefen farjinki da cinyoyinki da qirjinki to zaki mamaki yadda mijinki zai riqeqi da kyau da nuna soyayya a gareki.
(2)KUMBURIN GABA (INFLAMMATION)
(3)ZAFIN GABA (Pain)
(4)ZUBAR RUWA (Leaking) Mai zubar da ruwa a gabanta sai ta samu:- Saiwar zogale. Saiwar rai xore. Garin tafarnuwa. Barkono da daddawa. A dakesu ayi yaji ta ringa sanyin da baki sani ba sai ya fita.
(5)RASHIN HAIHUWA (INFERTILITY) Wannan ma matsalace wadda take samuwa daga waxannan abubuwa:-
(6)SANYI KO ZAFIN MAHAIFA: Waxannan suma suna hana mace ta samu ciki saboda illolin, da suke tattare da hakan.
(7)NAMIJIN DARE: Wani aljani ne wanda yake aurar 'ya mace kuma ya hanata samun cikin da zata haifar. Alamominsa sune:-
Mafarkin jarirai.
Mafarkin wani na saduwa dake.
Vacin rai da faxuwar gaba.
Mafarkin ruwa.
Yawan ciwon kai.
Jin motsi a ciki.
Lalacewar maganar aure ga budurwa.
Damuwa da rama ko qiba marar misali.
MAGANI:
kici gaba da rokon ALLAH ta hanyar Kitabu was Sunnah
QARIN BAYANI:
Akwai cututtuka da yawa da suke samun al'aurar mata saboda bata rabuwa da danshi wanda ta nan ne wasu kwayoyin halitta suke samun zama a cikin al'aurar tasu ana kiransu (Micro – organism) da turanci. Kusan cewa shi farji da ake magana akan cututtukansa shine wanda Allah ya halitta da wani sinadari na mayen qarfe da wata tsoka kuma tana da baki guda biyu hagu da dama. yayin da sha'awar mace ta motsa sai ta riqa motsi dai-dai kuma tana iya yin rauni ita wannan tsokar har ta daina motsi. Wannan tsoka kamar fulogine a jikin mace yayin da dauxa tayi mata yawa sai ta kasa motsi. A daga nan sai sha'awar 'ya mace ta xauke domin ita wannan tsoka itace ke feso wani ruwa wanda shike sauko da wani ruwa da yake daxaxa jin daxin mu'amalar jima'i kuma yake sa wani zaqi tsakanin mace da miji. Kuma wannan motsi da yake naman akwai wani sinadarin kitse wanda Allah yasa akan saman kaciyarsa da namiji idan sha'awarsa tai motsei sai kaji yana motsi dai-dai, lokacin da namiji ya kawo zata ji yana wannan motsi kuma shima namiji yana iya jin motsin na mace yayin da ta rigashi inzali ko kawowa.
Waxannan motsi guda biyu su ake cewa: jauharatul jima'i idan na xaya daga ma'aurata ya sami matsala sai kaga auren yaqi zaman lafiya.
Amma idan ba matsala sai kaga ana zaune lafiya cikin shauqi da annashuwa.
Sannan mafi yawa mata masu ciki suna kamuwa da cututtuka daga wasu kwayoyin halitta dake riqe al'aurar mata saboda gabansu baya rabuwa da danshi, waxannan kwayoyin halittu sune:- Bacteria, fungi, da sauransu.
Alamomin masu nuni izuwa kamuwar cutar al'aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawoshi.
Kadan daga ciki:-
Zafi yayin fitsari. (burning during urinate).
Ciwo daga wajen a'aurarta (Itching out side the vagina).
Canzawar gaba ba kamar yadda ta saba ganiba.
Zafi yayin saduwa da miji (discomfort during sexual intercourse).
Qaiqayi da ake kira da (Irritation).
to idan wannan alamun sun tabbata a gaggauta tuntubar likita ko zuwa asibiti
0 Response to "Hanyoyin Magance Cututtukan Da Suke Damun Al'aurar Mata, Wato (Vaginal Disease)"
Post a Comment