Duba Mahimmancin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu
Duba Mahimmancin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu
Yadiya: 'Raina kama ka ga gayya'. Yadiya wata ciyawa ce ko 'ganye mai yado' tana nan kaman ganyen dankali. Wannan ciyawar ba shuka ta ake yi ba. Tana fitowa ne a bayan kasa da ikon Allah. Ciyawa ce mai matukar muhimmanci ga al’umma wanda kuwa tuni wasu suka dauka a matsayin magani mai taimako, musamman mata masu juna biyu.
Amfanin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu
Da zarar mace ta samu juna biyu, kuma ya kai wata bakwai (7), yana da kyau ta samu ganyen yadiya ta tafasa ta mayar da shi ruwan shanta har sai ta haihu. Domin kuwa yana zubar da duk wani datti dake tattare a mara ko zakin da mace ta sha lokacin da take dauke da juna, wanda wannan zakin duk zai zuba kafin ta haihu. Sai ya ba wa yaro damar fita cikin sauki. Sannan yana wanke dattin jikin jariri tun yana ciki. ana haifar jariri za a ga jikin shi ya yi tas.
Allah sa mu dace.
0 Response to "Duba Mahimmancin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu"
Post a Comment