Yusuf Buhari Na Dab Da Angwancewa Da ‘Yar Marigayi Ado Bayero
Yusuf Buhari Na Dab Da Angwancewa Da ‘Yar Marigayi Ado Bayero
Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya aika da tawaga da za ta tattauna da iyalin gidan Sarautar Kano don sa ranar bikin Yusuf, ɗa ga Shugaba Buharin, da kuma Zahra Bayero, ‘ya ga marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero.
Wasu majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa tawagar da Shugaba Buhari ya turo ta ƙunshi gwamnoni, ministoci, da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS. Yusuf Bichi.
Tuni tawagar ta iso Kano ranar Asabar da buhuhunan goro da sauran kayayyaki don sa rana.
Tawagar za ta tattauna da dattijo a cikin zur’ar Bayero, Idris Bayero, da kuma Sarkin Kano, Aminu Bayero, ranar Lahadi.
A halin yanzu Zahra Bayero tana karatun digirin farko a Birtaniya, inda take karantar Ilimin Zane-Zane, Yusuf Buhari kuma ya kammala digirinsa na farko a 2016 daga Jami’ar Surrey, Guildford, Birtaniya.
Turawa Abokai
0 Response to "Yusuf Buhari Na Dab Da Angwancewa Da ‘Yar Marigayi Ado Bayero"
Post a Comment