-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Gwamnan Jihar Kano

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Gwamnan Jihar Kano

Awa Daya Bayan kisan Dan Majalisa a Jahar Zamfara : 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Gwamnan Jihar Kano 

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan fashi ne sun kaiwa ayarin Gwamnan na Kano, Abdullahi Ganduje hari, inda suka bar ‘yan sanda uku suka samu raunuka Harin wanda ya afku bayan ayarin motocin na kan hanyarsa ta zuwa Kano daga jihar Zamfara, inda aka gudanar da taron gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Talata. Gwamnan na Kano ya je jihar Zamfara ne don tarbar gwamnan jihar, Bello Matawalle zuwa jam'iyyar APC. Majiyoyi a gidan gwamnatin sun tabbatar da harin amma sun lura cewa Gwamnan baya cikin ayarin motocin lokacin da suka ci karo da ‘yan bindigan. An bayyana cewa, Ganduje ya bi ayarin mataimakinsa na Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, bayan taron gangamin da aka yi a Gusau. wata majiya a gidan gwamnatin, wacce ta nemi a sakaya sunan ta. "Kun san saboda wurin ya kasance a jere bayan taron wanda gwamnonin jihohi da dama suka halarta, SHI (Ganduje) ya bi sahibin abokinsa (Badaru) kuma dukkansu sun isa Kano sa'o'i kadan kafin tawagar ta Kano ta iso," 'Yan bindiga da dama, wadanda suka tare hanyar, an ce sun bude wuta nan take suka hango jerin gwanon motocin.

Source: Gistlover.com

0 Response to "'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Gwamnan Jihar Kano"

Post a Comment