Shugaban ƙasa Buhari ya buƙaci kamfanin MTN ya rage farashin Data
Shugaban ƙasa Buhari ya buƙaci kamfanin MTN ya rage farashin Data
Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci kamfanin sadarwa na MTN da ya rage farashinsa na “Data“ da kuma yin ƙira da sauran abubuwan da kamfanin ke samar wa a Najeriya.
Shugaban ya sanar da hakan ne a a yau Juma‘a cewa tun da Najeriya ce ƙasar da MTN ya fi samun kasuwa a Afirka, ya kamata kamfanin ya sassauto da farashin hajarsa.
Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2020 ne gwamnatin Najeriya ta sanar da zaftare farashin data da fiye da kashi 50 cikin 100 bayan umarnin da ta bai wa hukumar kula da kamfanonin sadarwar ƙasar nan ta NCC na fito da matakan aiwatar da hakan a hukumance.
Ministan sadarwa Dakta Isa Ibrahim Pantami, ya ce matakin ya yi daidai da umarnin da ya bai wa hukumar ta NCC na bijiro da matakan rage farashin Datar domin sauƙaƙa wa jama’a.
Sai dai masana a ɓangaren na sadarwa na ganin cewa gwamnati ba ta da hurumin ƙayyadewa kamfanonin sadarwa a ƙasar nan farashi, hasalima aikinta shi ne bayar da shawara a kan farashin da take ganin ya kamata a yi amfani da shi.
Wani aiki kuma da ake ganin shi ne ya rataya a wuyar hukumar kula da kamfanonin sadarwa ƙasar nan shi ne tabbatar da ƴan ƙasar sun samu sadarwa mai kyau, tare da kare haƙƙokinsu da kuma tabbatar da cewa kamfanonin ba su yi wani abu da ya sabawa doka ba.
Idan kuwa hukuma ta samu wani kamfani da yin wani abu da ya saɓawa doka, tana da damar cin tararsa, kamar yadda a shekarun baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin MTN biliyoyin daloli.
Abin jira a gani shi ne yadda kamfanonin sadarwar Najeriyar za su karɓi wannan al’amari
Turawa Abokai
Why You Dont Pay me???
ReplyDelete