-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kane da Pogba da Aouar da Ramos da Tierney da Varane da Lingard, Ramsey da Jorginho

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kane da Pogba da Aouar da Ramos da Tierney da Varane da Lingard, Ramsey da Jorginho

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kane da Pogba da Aouar da Ramos da Tierney da Varane da Lingard, Ramsey da Jorginho



Ɗan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27, ya shaida wa wakilansa ƙarara cewa yana son sake kasancewa da Mauricio Pochettino a Paris St-Germain. (90min)

PSG za ta gwada sa'arta wajen neman ɗauko ɗan wasan Manchester United asalin Faransa Paul Pogba, mai shekara 28. (Le Parisien - in French)

Arsenal za ta yi ƙoƙarin sayen ɗan wasan nan mai shekara 22 da ke taka leda a Lyon asalin Faransa Houssem Aouar, kuma tana shirin gabatar da £100,000-kowanne-sati a kwantiragin. (Sun)

Akwai hasashen Sergio Ramos ya koma Manchester United, PSG ko Sevilla bayan ɗan wasan asalin Sifaniya ya yi bakwana da Real Madrid.(90min)

Mai buga tsakiya a Scotland Kieran Tierney, ya amince da sabon kwantiragin shekara biyar a Arsenal wanda zai sanya hannu nan gaba kaɗan. (Football.London)

Ɗan wasan Real Madrid da Faransa Raphael Varane, mai shekara 28, har yanzu bai bayyana makomarsa ba, yayin da ake tunanin zai tafi Manchester United ko Chelsea. (Goal)

Manchester United ta zaƙu ta saye Varane, da kuma ɗan wasan Atletico Madrid mai shekara 30 wanda ke bugawa Ingila baya Kieran Trippier. (ESPN)

Chelsea ta bi sahun Arsenal a farautar ɗan wasan Real Sociedad Alexander Isak, mai shekara 21. (AS, via Express)

Wakilin Jorginho ya ce manyan kungiyoyin Turai sun nuna zawarcinsu a kan ɗan wasan mai shekara 29 da ke buga wa Italiya tsakiya sai dai kamar da wuya ya bar Chelsea. (Radio Marte, via Mail)

Ɗan wasan Juventus Aaron Ramsey na iya koma wa Arsenal. (Eurosport)

Liverpool ta kwadaitu da dan wasan Sassuolo da Italiya, Domenico Berardi, mai shekara26. (Gazzetta dello Sport, via Express)

Yanzu haka mutum 8 ake nazarinsu domin maye gurbin kocin Everton sai dai Rafael Benitez da Nuno Espirito Santo aka fi sha'awa. (Sky Sports)


Mai bugawa Arsenal tsakiya Matteo Guendouzi, wanda ya shafe kakar da ta gabata a zaman aro a Hertha Berlin, ya amince da yarjejeniyar Marseille. (Fabrizio Romano via Sun)

West Ham ka iya miƙa tayi mai gwaɓi kan ɗan wasan Ingila Jesse Lingard, domin tabbatuwar zamansa a kungiyar daga Manchester United. (Football Insider)

Watford na zawarcin ɗan wasan Arsenal Ainsley Maitland-Niles, mai shekara 28. (Mirror)

Arsenal ta shirya tsaf domin kashe £250m kan aƙalla ƴan wasa biyar a wannan kakar, domin Mikel Arteta ya sake ginata. (90min)

Jerry Yates na Blackpoolna cikin ƴan wasan da Blackburn ke son maye gurbinsa da Adam Armstrong, mai shekara 24, da ake alakantawa da West Ham, Southampton da Norwich City. (Sun)

Wolves ta tuntubi ɗan wasan Sporting Lisbonmai shekara25 Joao Palhinha. (Football Insider)

Lazio's ta shaida cewa tsohon ɗan wasanta na gaba Stefan Radu, mai shekara 34, ya aince ya tsawaita zamansa a ƙungiyar. (Goal - in Italian)

0 Response to "Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kane da Pogba da Aouar da Ramos da Tierney da Varane da Lingard, Ramsey da Jorginho"

Post a Comment