Jagoran Ƴan Boko Haram Ya Haɗiye Sim Card, Bayan Yashiga Hannun Sojoji a jahar Borno
Jagoran Ƴan Boko Haram Ya Haɗiye Sim Card, Bayan Yashiga Hannun Sojoji a jahar Borno
Rahotanni na ce dakarun sojin Najeriya sun cafke wani matashi mai suna Wida Kachalla, wanda ake zargin yaron Modu Solum ne. Shi wannan Modu Solum ya na cikin jagororin sojojin kungiyar Islamic State in West Africa Province da su ka dade suna addabar Arewa maso gabas. Rahoton ya ce Wida Kachalla mutumin garin Murguba ne a jihar Borno.
An ce wannan kauye ya yi kaurin suna wajen tara ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin.
Yadda aka cafke Wida Kachalla Sojojin FOB Ngamdi a karkashin jagorancin shugaban rikon kwarya na bataliya ta 154, Manjo DY Chiwar, su ka kama Kachalla a kasuwar Benisheikh a Borno. An yi ram da Wida Kachalla ne tare da wani da ake zargin ya na yi wa mayakan ISWAP jigilar kaya, wannan mutum ya kan kai wa ‘yan ta’addan kayan abinci. Sojoji sun yi nasarar samun wasu wayoyin salula biyu a hannunsa. Da ya ga tashi ta kare, sai ya hadiye katin layin wayarsa saboda gudun wasu asirin su tonu. Dakarun sojojin suka ce: “A ‘yan makonnin nan, mun tare masu kai wa ‘yan ta’adda kaya da bayanai.”
Wida Kachalla Hoto: www.prnigeria.com Source: UGC Mun samu bayanai a wurin Kachalla “Ko da wanda ake zargi ya tauna, sannan ya hadiye katin layinsa na SIM, amma mun riga mun samu duk wasu bayanai da mu ke nema a binciken da mu ka yi.”
“Sauran kayan da aka samu a hannunsa sun hada da buhun fulawa, kwalin biskit, da kwalin madarar ruwa, kwalin lemun kwalba, da kuma wani maganin feshi.”
Jami’in tsaron ya ce har ila yau an samu Kachalla dauke da wasu kayan keke da abubuwan ci. Ba da dade wa bane aka samu labarin dakarun Operation Hadin Kai sun hallaka Modu Solum.
Ana tsammanin harin da sojojin sama suka kai kwanan nan ya yi sanadiyyar mutuwar Modu Sulum, wanda shi yake lalata wutar lantarkin kewayen Maiduguri
Source: Legit
0 Response to "Jagoran Ƴan Boko Haram Ya Haɗiye Sim Card, Bayan Yashiga Hannun Sojoji a jahar Borno"
Post a Comment