Cikakken bayanin yadda budurwa ko bazawara zata dawo da martabar nononta bayan ya fadi
Cikakken bayanin yadda budurwa ko bazawara zata dawo da martabar nononta bayan ya fadi
idan muka ce gyaran nono akasari ba kowace mace zata gane me muke nufi ba saboda basu dama da gyarawaba, alhali kuma rashin gyaran ba karamar illa yake yi masuba amma su basu sanhakanba, to gaskiya yana da matukar muhimmanci da tasiri ga mace AMARYA ko UWARGIDA,
BUDURWA KO ZAWARA, da ku gyara nononku, karki bar nononki hakanan sharaf ba kyan gani, sai kaga mace ta bar nono a zube, in tana shara mai gida yaga sona ta reto kamar anratayo agwagi a bayan keke, idan kuka lura sai kuga matan wadansu yarurrukan wadanda ba hausawa ba (kamar LARABAWA KO TURAWA) matansu sun tsufa ko sun manyanta amma martabar nonuwansu nanan daram ta yadda ko nonuwan wata budurwar a nan baza ka samesu a hakaba, to hakan zai iya rage maki tasiri wajen maigida, hanyoyin da zaki bi don kada nononki ya fadi ko kuma idan ya fadi kuma kina son ya tashi sune zaki samu:
- alkama ki rinka yin kunu da ita kina sha safe da rana
1. ko kisamu garin hulba
2. da garin tsamiya
3. da zuma farar saka
4. da lemun tsami
sai ki hadasu guri 1 ki rinka shafawa a nonon, bayan awa daya ko ( 30 minutes) sai ki wanke ki shafa man zaitun, malama zaki sha mamaki.
CIKAKKEN BAYANIN YADDA BUDURWA ZATA DAWO DA MARTABAR NONONTA
wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema intana bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinshi, yanda akeyi shine za a samu.
1. garin waken soya
2. garin alkama
3. garin zogale
4. garin bawon lemun zaki
5. kunfan maliya
6. da zuma
sai kica kudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan 30mtn ko sama da haka sai ki wanke,sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki
YADDA ZAKI DAWO DA MARTABAR NONONKI DA GIRMANSA
ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata samu
1. ganyen sabara mai kyau
2. da 'ya'yan alkama suma masu kyau
sai ki rinka nunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko ko ko duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka
0 Response to "Cikakken bayanin yadda budurwa ko bazawara zata dawo da martabar nononta bayan ya fadi"
Post a Comment