KUNDIN TSATSUBA 3 Hausa Novel
KUNDIN TSATSUBA 3 Hausa Novel
Shiri kafin mako biyu nan take mayakan suka tabbatar masa da cewa zasu cigaba da shiri har nan da mako biyun batare da bata lokaci ba yayi sallama dasu yadawo gida domin yayi sallama dani awannan lokacin ina daukeda cikinka wata takwas jikina yayi nauyi bana iyayin komai saii daii kuyangi suyimin ina zaune aturaka yabayyana gareni cikin shirin yaki gaba dayan makamansa na yaki natare dashi koda naganshi cikin wannan halin saii hankalina yatashi namike zumbur natareshi ina mai cewa yakai mijina ina zaka yanxu cikin shirin yaki haka mahaifinka yayi murmushi mai taushi agareni yace kwantar da hankalinki ba yaki zantafi ba zankai ziyarane gawani boka wai shi zamarul hakma acan dajin ramlas domin neman taimako akan wani gagarumin yakin dake gabammu koda yazo nan azancensa saii nafashe da kuka al,amarin daya tayar masa da hankali kenan ainun yafara rarrashine yana cewa ina dalilin kukanki ya abar kaunata alhalin gani atare dake dolene nayi kuka domin nasan cewa abunda zan haifa zai zamo maraya yakai mijina kasani cewa duk abinda yafaru jiya afada nasamu labarinsa nasan cewa duk shirye shiryenka na yaki da azzalumi dauwamur huzubur tabbas yafi karfinmu lallai idan kukayi gaba da gaba dashi saii yayi nasara akanka narokeka narokeka dan darajar soyayyar dake tsakanina dakai kajanye batun yakin nan zaifi kyau murungumi kaddara mu kyale dauwamur huzubur yashigo kasarnan yayi abunda ransa yakeso nasan duk haqilo dakakeyi akan rai dayane wato ran Yar uwarka sarauniya shin yanxu zakaso arasa miliyoyin rayuka saboda Yar uwarka sarauniya kenan yayinda yaji wannan tambayan saii jikinsa yayi sanyi hankalin sa yakara dugunxuma baisan sa,adda idanunsa suka ciko da kwallaba Yakama kuka daga can kuma saii yakwala ihu mai firgitarwa har sanda barorin gidan da kuyangi gidan suka hallara agabansu koda sukaga babu komai saii suka koma mahaifinka yadago kai yadube ni yace yake abar kaunata kiyi Sani cewa duk fadin duniyan nan babu abinda nakeso sama da Abu uku .
Abu uku abu nafarko shine Yar uwata gimbiya hashlai nabiyu kuma shine mulkin kasan nan Wanda nagada tun iyaye da kakanni Abu na uku kuma shine ke na rantse da iyaye da kakanni baxan bari wani mahaluki yaxo yaketa al,adanmuba wajibine agareni na natsare sarauniya natsare mutuncinta natsare lafiyanta hakika nayi niyyan aiwatar da hakan babu gudu babu jada baya saboda haka ashirye nake nasalwantar da rayuwata dan ganin bayansu lokacin da mahaifinka yazo nan azancensa saii nasake fashewa da kuka har zuwa dan lokaci shi kuwa bai gusheba yana lallashina har nadaina kukan sannan yace ni yanxu naxone nayi miki bankwana kuma baxan dawoba saii bayan mako biyu
Kodajin haka saii na rungumeshi nace yakai mijina hakika Wanda yayi nisa bayajin kira babu wani kalma daxanyi amfani dashi dazaisa kajanye wannan maganan abunda nakeso dakai shine kayimin sallama irinta mai ciwon ajali ma,ana idan kanada wata wasiyya daxaka bari kafadeta domin inaji ajikina cewa wannan rabuwa daxamuyi dakai itace ta qarshe banyi tsammanin zamu sake haduwaba nan take tausayina yakama mahaifinka yasake rungumeni yana mai zubda hawaye yace Dan mexakice haka alhalin nagaya miki cewa zandawo bayan mako biyu yayinda naji wannan tambayan saii nadago kaina nace yakai mijina inasan kasani cewa ita tafiya kafin kayitane kake da ita amma dazaran kayita to kuwa itace take dakai saii abinda hali yayi nidaii inayi maka fatan alkhairi da samun nasara amma lallai kabarmin wasiyya sannan shima yace yake abar sona mafi soyuwa araina wasiyyata guda daya ce agareki inaso ki kasance mai matukar kaunar abinda xaki haifa idan yakasance namiji kikyautata mishi komai yabukaci kiyi mishi kiyi mishi kar yabukaci wani abu yarasa sannan ki horar dashi bisa rashin tsoro da jarumtaka burina yagkdeni kuma ki rada masa suna MARKAHUS SABUR yayinda naji wannan sunan saii farin cikin wannan sunan domin kuwa ma,anar sunan shine magajin uba nadubeshi nace menene hikimarka akan wannan yadubeni yace ,
>>Azzalumai domin naji irin Gwagwarmayar dayayi da Azzalumai dakuma azzalumi dauwamur huzubur shin yamutune a filin daga kokuwa cuta yayine tazamo ajalinsa ? Meyafarune da yar uwarsa gimbiya hashlai shin sarki dauwamur huzubur yabiya bukatarsa da ita kuwa ? Shin itama gimbiya hashlai bayan da sarki dauwamur huzubur yabiya bukatarsa da ita yakashetane kamar yanda yakeyiwa sauran yan uwanta mata ? Kokuwa cutace takasheta ? Yayinda samaratu taji wadannan tambayoyin daga bakin danta markahus sabur saii ta nisa tace yakai Dana kasani cewa wannan labari mai tsawone kaga tun safe muke zaune anan gashi har dare yaraba yanxu kayi hakuri kaje kakwanta kahuta kodan Saboda gajiyar doguwar tafiya dakasha zuwa gobe saii naci gaba dabaka labarin kuma kada kamance akwaii batun sauran abubuwa guda biyu Wanda zaka nemo yayin tafiyarka ixuwa kogon zuhurum saii goben zangaya makasu markahus sabur yamike tsaye sannan yace yake ummina menene amfanin sauran abubuwa biyun ai zatona tsumin dodo kiryanu yafisu muhimmanci samaratu tayi murmushi tace aa bai fisuba kaidai kayi hakuri zuwa goben zakaji komai nan daii sukayi sallama yatafi dakinsa ya kwanta wannan shine abinda yafaru tsakanin markahus sabur da mahaifiyarsa samaratu bayan ya Isa gida da gimbiya sima da nufin aurenta _______Acan birnin BAHAZUM kuwa wata daulace Wanda al,ummar musulmi suka mamaye aqalla akwaii garuruwa zasu kai hamsin da biyar a karkashin wannan kasa dolene inda kaga rayuwar al.ummar dake wannan nahiya abun yabaka sha,awa domin kuwa ana zaman adalci babu wani bambamci tsakanin attajiri da talaka wadannan mutanen suna tafiyar da rayuwar sune bisa Shari,ar musulunci daga cikin wadannan garuruwa akwai wani dan karamin gari wanda ake kiransa da SAHARU shugaban al,ummar wajen sunansa ABUL UZAIRU ma,ana shine mahaifin jarumi uzairu amma ainihin sunansa shine MAS,UD ,mas,ud nada mace daya rak ana kiranta da suna Maryamu, maryamuce mahaifiyar jarumi uzairu kuma tun daga kansa basu sake samun.
}>>> samun haihuwa ba atakaicema daii rabonsu da ganin jarumi uzairu ya dauki lokaci mai tsawo kuma sunyi sallama dashine akan cewa yatafi yada addinin Allah zuwaga wata kasa Wanda ake kira SULBAYYA kuma zai dawo nan da wata guda indai yana raye kasar sulbayya daulace ta wassu manyan kafurai ma,abota bautan rana dayawa daga cikin mutanen bahazul sun rasa rayukansu akokarin shiga wannan gari don yada addinin musulunci mutanen sulbayya sun kasance masu matukar taurin kai da rashin imani kuma rikakkun matsafane ansha yin yaki tsakanin daular bahazul da daular sulbayya amma ragas akeyi ma,ana kare jini biri jini don haka kasashen biyu suna shakkan juna lokacin da maryamu taga danta uzairu taga yashafe wata hudu bai dawo gidaba sai hankalinta ya dugunxuma takasa samun sukuni dare da rana wani lokacin saii daii tashiga daki tayita kuka batare da ansan halin da take cikiba bawani Abu bane yakesata kukanba saii dan irin tsananin sonda takeyiwa jarumi uzairu shiko mas,ud ko kadan baidamuba tundaga ranar da uzairu yabar gida ya cigaba dayin harkokinsa nayin hidima ga addinin musulunci daya saba bai sakeyin maganan uzairuba ,watarana yana barci cikin dare daya farka sai yaji maryamu nakuka mas,ud yamike tsaye yaje kanta batare data saniba kawai saii jin muryarsa tayi yana cewa yake matata ina dalilin kukanki awannan dare cikin firgici tadago kai tadubeshi gameda goge hawayenta sannan tace babu komai mas,ud yayi murmushi sannan yatsuguna dab da ita yadafa kafadarta yace kadaki boyemin damuwarki kiyi Sani cewa nine mijinki kuma iyayenki sun rasu bakida wani Wanda yafini yanxu aduniya nazamo tamkar uwa da uba yanxu agareki babu Wanda yasan halinki sama dani hakazalika nima babu Wanda yasan halina sama dake iya tsawon zamana dake yau shekara talatin kenan yaune ranata biyu Dana taba ganin kukanki rana nafarko itace ranan da mutanen kasar sulbayya suka kawo hari iyayenki suka rasu ranata biyu itace yau sanardani hakikanin abinda yafaru me
KUNDIN TSATSUBA PART 3F}>>> Yafaru menene yafaru yayinda Maryamu taji Wannan batu saii tayi ajiyar zuciya sannan tace hakika abinda kafada dangane dani gaskiyane dan haka kuwa zanfada maka gaskiyar lamarina akan abunda ka bukata kasani cewa dan mu UZAIRU yayi mana bankwana akan xanje kasar sulbayya dan yada kalmar Allah kuma yasanar damu cewa bazai wuce wata dayaba zaidawo gashi yau wata hudu kenan shiru babu labarin sa nasani cewa idan ya hallaka bisa wannan tafarki domin yayi shahada saii daii natayashi farin ciki to amma abinda yafi damuna shine kullum saii nayi mafarki dashi kuma acikin mafarkin ana nunamin cewa yana nan araye amma rayuwarsa nakokarin shiga cikin hadari wannan shine dalilin dayasa kaganni ina kuka domin bansan yanda xanyi na taimaka mishiba sa,adda mas,ud yaji haka saii yayi shiru yana tunani bayan gushewar dan lokaci saii yadubi maryamu yace yake matata hakika mafarkinki abun dubawane domin nima nataba yin mafarki to babu abinda xamuyi face mushirya mutafi bahazul domin muje musamu shugaba musanar dashi abinda yake damunmu domin yakasance babban malami kuma masanin fassarar mafarki idan yayi istahara zaisanar damu hakikanin halinda uzairu yake ciki sai mushirya muje domin muji daga gareshi nan take Maryamu taji farin ciki ya lullubeta tunda asuban fari suka shirya suka kikkintsa suka kama hanyar birnin bahazul saii da suka shafe tsawon kwana uku sannan suka Isa birnin bahazul dashigansu cikin Birnin Birnin bahazul suka nemi gidan imam Khalid dayake sanannene nan danan akayi musu jagora zuwa gidansa dazuwa suka iskeshi a kofar gida yana bayarda fatawa ga almajiransa koda yaga baki saii yamike yataryesu cikin farin ciki sannan yadubesu yace da maryamu tashige ciki taje wajen matarsa ta huta shikuwa mas,ud saii aka bashi abun zama yazauna sannan aka kawo masa abinci da abin sha yaci yasha sannan yayi hamdala bayan imam Khalid ya sallami almajiransa yadubi mas,ud suka fuskanci juna sannan yace yakai wannan dan uwa hakika ina ganin kamar muntaba
KUNDIN TSATSUBA PART 3G}>>> Kamar muntaba saduwa abaya daga ina kafito kuma meke tafe daku yayinda mas,ud yaji wannan tambaya saii yayi murmushi yace ya shugabana ni mutumin saharu ne hakika muntaba saduwa sa,adda akayi yakin karshe tsakanin kasar nan da kasar sulbayya nine wanda yakawo maka dauki sa,adda wani kafiri ya fincikoka daga kan doki kafado kasa yakawo maka mummunan Sara da tokobi nayi azama nakare saran nasokeshi da mashina yafadi kasa matacce koda jin wannan maganan saii imam Khalid ya rungume mas,ud cikin tsananin farin ciki sannan Yakama hannunsa suka shiga cikin gida gava daya da shigarsu suka iske Maryamu da matar imam Khalid zaune atsakar gida suna hira cikin nishadi su biyun suka dago kai suka dubesu saii suka cika da mamaki domin mas,ud da imam Khalid na rukunkume da juna tamkar yan uwanda suka dade basu haduba cikin mamaki hasiyatu matar imam Khalid tadubi mai gidan nata tace yakai mijina shin kunsan junane kodaii kun kasance yan uwa bamu saniba.
0 Response to "KUNDIN TSATSUBA 3 Hausa Novel"
Post a Comment