Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa (Koyi Da Kanki)
Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa"Koyi Da Kanki"
MIYA KALA KALA
KPOMO PEPPER SOUP(GANDA)
kisamu gandarki ki yankata , ki kankare ki wanketa sai ki dora har sai t dahu sai kisa niqaqqen tumatir d tattasai , albasa , gishiri maggi, spices, albasa sliced, d green pepper, yankakkiyar albasa , ayanka carrot slice a zuba aciki a bari su dahu sai a sauke aci d shinkafa ko cous-cous
MIYAR OHA
nama tsoka zalla
Ganyen oha, stock fish
Maggi, gishiri
Busasshen kifi
Cry fish, gwandar masar (melan)
Manja Ki tafasa naman kizuba stock fish maggi albasa thyme tafarnuwa kayan qamshi su kuma dahowa ki yanka gwandar masar qanana kamar yankan maggi ki zuba akan namanki zuba busasshen kifi dakakkaken cry fish ki yanaka ganyen oha ki wanke ki zuba kisa soyayyen manja ki rufe idan tayi 15min sai ki sauke in ganyen yayi laushe aci d sakwara ko amala.
MIYAR UGU
kayan ciki
Nama, manja
Ganda, agushi
Stock fish
Cry fish
Ganyen ugu
Tafarnuwa
Thyme
Maggi , curry, gishiri Ki gyara ganyen ugu ki yanka qanana ki wanki ki ajiye ki tafasa nama d kayan miyar aciki ki wanke stock fish kisa gandarki t dahu sosai ki yanka qanana k I zuba naman kayan ciki maggi gishiri curry ko kayan qamshi dakakken cry fish 2 spn ki barta t tafasa sosai sai kizuba ganyen ugu mai yawa ki rufe y tafasa zuwa 10minute sai ki sauke aci d sakwara ko tuwon shinkafa baya ma sakwara in t dawo tayi santsi
馃彽fish source cream馃構
馃彽kifi
馃彽tattasen Leda
馃彽albasa da tafarnuwa
馃彽magi, Cory, tym
馃彽man gyada
kisabtashe kifin kisoyashi sama sama kikwashe.
Kimarkada tafarnuwa da albasa kisoyashi saiki soya tattasen ledan kizuba ruwa saiki bare kifin kifidda kayoyo da fatarsa, saikuma kisaka tsokar aturmi ko blander kidakeshi yayi luqui saikijuye a tukunyar kizubasu magi dasuransu Idon kaurinsa yaimiki dai- dai saiki sauke
馃構馃構馃構yanada dadi kina iyaci daabunda kikayi ra'ayi
MIYAN KIFI
______________
Sukumbiya Danye Me Kyau 1
Tattasai 2
Attaruhu 3
Cabbage
Albasa 1
Curry
Maggi
Mai
:
Zaki Wanke Kifinki Da Lemon Tsami Ko Toka Domin Fidda Karninsa Da Kuma Yaukin Dake Jikinsa Sai Ki Yanyankashi Amma Sai Kinyi Sauri Domin Idan Kankarar Jikinsa Ta Narke Zai Iya Dagargaje Miki Wajen Aikinsa, Sai Ki Barshi Yasha Iska Domin Ya Tsane,in Ya Tsane Sai Ki Barbadeshe Da Magi Ki Jerashi A Farantin Gashi Kisa Shi A Oven Idan Kuma Baki Da Oven Din Sai Ki Soyashi A Mai Amma Karki Yawaita Juyashi Gudun Dagargajewa,
Idan Yayi Sai Ki Aje Ki Ki Dauko Attaruhu Albasa Tattasai Da Cabbage Da Kika Yanyanka Kika Wanke Ki Dora Kasko A Wuta Kisa Mai Ki Soyasu Kisa Maggi Da Curry Idan Sun Fara Hade Jikinsu Sai Ki Dan Sa Ruwa A Ciki,sannan Ki Kawo Kifin Kisa A ciki Yayi Kaman 10minutes Saiki Sauke,ana Ci Da Bread Ko Haka Kawai Da Dan Juice.
*MIYAR ALBASA*
*Ingredients*
_Albasa_
_Tsokar nama_
_Attarugu_
_Tomatoes_
_Curry_
_Thyme_
_Man gyada_
_Salt_
_Maggie_
*Method*
_Da farko zaki tafasa nama tare da albasa da spices da seasoning bayan ya dahu saiki kwashe shi ki daka shi saiki yanka albasa amma mai yawa akeso kamar ukku amma manya manya saiki sanya tomatoes kamar biyu saiki sanya attarugu shikuma kamar ukku ita albasar grating dinta zakiyi saiki soya mai ki zuba albasar tare da jajjagaggun attarugu da tomatoes saiki sa Maggie da salt da curry idan ta dahu saiki zuba naman ki wanda kika daka saiki motsa shi zuwa kamar 5mnts shikenan saiki sauke_
MIYAR KANTU (RIDI)*
*Ingredients*
_Kantu (ridi)_
_Nama_
_Kifi busashshe_
_Albasa_
_Attarugu_
_Ugwu or Alayyahu_
_Maggie_
_Salt_
_Thyme_
_Spices_
_Mai_
*Method*
_Zaki tafasa namanki da seasoning da spices saiki soya kayan miyarki acikin mai saiki zuba namanki wanda kika tafasa ki sanya har da ruwan da kika tafasa naman acikin kayan miyar saiki sanya kifin ki busashshe bayan kin gyara shi da ridin ki bayan kin daka shi watau (kantu) wadda akeson yanwan shi yakai kamar one cup saiki rufe tukunyar ki barshi ya dahu zuwa kamar 20 mnts saiki yanka ganyenki ki xuba ki barshi zuwa kamar 5mnts shikenan kin gama_
*MIYAR OFFORIRO*
*Ingredients*
_Tattasai_
_Attarugu_
_Albasa_
_Nama_
_Stockfish_
_Crayfish_
_Man ja_
_Kayan ciki_
_Seasoning_
_Spices_
_Alayyahu_
_Garlic_
_Maggie_
_Salt_
*Method*
_Zaki wanke stockfish saiki dafa shi ajeshi a gefe saiki tafasa nama da kayan ciki ki sanya albasa garlic seasoning da spices saiki yanka tattasan ki da tomatoes da onions amma a tsaytsaye saiki daura man ja kan wuta saiki zuba kayan miyarki ki soya saiki zuba crayfish dakakke da naman da kika tafasa tare da stockfish saiki sa maggie da salt da spices saiki rufe idan komai ya dahu saiki sauke dama already kin dafa alayyahunki bayan kin gyara shi kuma ba tare da kin yanka shi ba saiki hadashi da miyar saiki motsa._
*MIYAR ZOGALE*
*Ingredients*
_Tattasai_
_Attarugu_
_Albasa_
_Zogale_
_Maggie_
_Gishiri_
_Garlic thyme_
_Seasoning spices_
_Nama_
_Kifi busashshe_
_Man ja or man gyada_
_Gyada_
*Method*
_Zaki tafasa nama ki sanya thyme da maggie da albasa bayan ya tafasa saiki sanya mai a tukunya ki soyashi da albasa saiki zuba kayan miyarki ki kuma sanya naman da kika tafasa tare da ruwan da kika tafasa naman saiki zuwa gyadar ki wadda kin riga kin gyarata kin daka ta da busashshen kifin ki shima bayan ki gyara abunki saiki sanya curry da maggie gishiri saiki barshi yayi kamar 10mnts saiki zuba zogalen ki bayan kin gyarashi anaso ki zuba zogalen da yawa domin anfiso miyar tayi kauri saiki barshi kan wuta yayi kamar 15mnt shikenan saiki sauke_
Miyar Awara
馃彽Kayan miya
馃彽Awara
Uwar gida zaki hada miyarki yanda kikeyin miyar dage dage sai miyarki tahadu saiki yanyanka Awara ki kanana saiki zuba acikin miyar kibata 5 to 6 mnts saiki sauke zaki iya ci da kowane abinci aci lpya.
馃彽miyar kwai da dankali馃構
馃彽poteto
馃彽kwai
馃彽kayan miya
馃彽albasa
馃彽nama ko kifi
馃彽man gyada
馃彽magi da Cory
馃彽tym onga
馃彽zaki soya namanki kijajjaga kayan miya kisoya saiki zuba ruwa, saiki feraye poteto kiyanyakashi kanana kizuba saiki zubasu magi da Cory da tym kirufe Idon yanuna saiki fasa kwai kizuba onga kikada sannan kijuye amiyar saiki yanka albasa kizuba, kinadan motsa miyar donkarya kama had kwan yanuna kisauke.馃構馃構馃構
MIYAR GYADA*
*Ingredients*
_Kayan miya_
_Nama_
_Tantaqwashi_
_Gyada_
_Alayyahu_
_Kabewa_
_Daudawa_
_Mai_
_Kayan qamshi_
_Spices_
*Method*
_Zaki tafasa nama da kuma tantaqwashi da albasa maggie saiki sanya kayan miyarki acikin man da kika soya ki barshi zuwa kamar 10mnts kina soyawa saiki zuba ruwan da kika tafasa naman da tantaqwashin saiki yanka kabewa ki dafa ta saiki daka ta ko ki markada ta saiki zuba acikin kayan miyar da kika daura akan wuta saiki dan qara ruwa saiki zuwa gyadarki wadda kika daka tah sai kuma ki sanya kayan qamshi da daudawa da maggie bayan ta dauki kamar 25mnts tana dahuwa saiki zuba alayyahu shi kuma saiki barshi ya dahu zuwa kamar 5mnts saiki sauke shikenan kin gama miyarki ta gyada_
Kici da shinkafa ko kuskus taliya
ko makaroni.
MIYAR HANTA
By Ameenah sidi
Ingredients
Attaruhu
Albasa
Tafarnuwa
Danyar citta
Curry
Mai
Maggi
ki wanke hantar ki yankata kanana ki sa a tukunya ki dafa da
albasa da citta da magi,ki jajjaga attaruhu da albasa da danyar
citta da tafarnuwa da mai ki zuba akai idan hantar ta dahu,kiyi
ta juyawa kisa magi da curry da gishiri,in tayi ki sauke,idan tayi
miki kauri zaki iya kara ruwa kan ki sauke.
Ameenah Nasidi's Kitchen馃崠馃崡馃嵅
SPICED CHICKEN PEPPER SOUP
BY Ameenah Nasidi
Ingredients
Zabuwa
Kaza
Water
Pepper soup seasoning
Mint(chopped)
Garlic(crushed)
Chillies(chopped)
Crayfish(ground)
Onion(chopped)
Yadda Za'a hada
Wash d meat(zabuwa da maza) and put it in a pot with a little water, season with salt, chopped onion, chillies and crushed garlic and boil for 20 minutes. Add d pepper soup seasoning and continue to cook for another 20 minutes to till chicken becomes tender, add d crayfish and mint leaves, stir and simmer for 8 minutes add season to ur taste and bring it down. Aci Dadi lafia make u no forget Meenah...馃構馃槣
miyan jajjage
_Ababen bukata_
*tattasai
*Attarugu
*Albasa
*carrot
*mai
*maggi
*Nama ko kifi(optional)
*peas
*dakkaken barkono
*curry
*tafarnuwa
_yanda zaki hada_
Zaki jajjaga tattasai da taruhu da albasa da tafarnuwa wuri daya,a daya bangaren kuma kin tafasa namanki,daganan saiki daura manki akan wuta idan yayi zafi sannan saiki kawo jajjagagun kayan miyanki ki juye idan suka fara soyuwa saiki juye namanki da kuma ruwan tafasan namanki aciki ki saka magi,gishiri,curry,thyme da kuma dakkaken yajinki sannan sai carrot,shikuma peas dinki dama kin tafasashi yayi laushi saikawai kijuye acikin miyan kibasu 10 to 15 mnt zagika manki yafito Saika wai ki sauke miya ta hadu saiki dubawa oga dakuma maman Nu'aiym 🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲
Banhana a aikawa yan uwaba amma plss kar a canjamun komai idan kuma anyi ban yafeba.
BITTER LEAF N EGUSI
馃崚Sai kin wanke bitter leaf yfita dai dai to yr test OK
Sai kikawo agushinki nikeke sai kifara haza mai a huta inyayi zafi kidama agushin ki kaman zaki dama koko sai ki zuba a tukuyar da kika haza a wuta da mai sai KIZUBA damai mai agushi da kika dama sai ki suya kaman 3to5 min sai kizuba nikeken kayan miya ki hada su kisoya lokacin ki Riga kin tafsa naman ki sai kizuba a agushin kida kayan MIYA da tun dah kiriga kin soya agushi da kayan MIYA sai KIZUBA nama kisa komai naki su maggi , curry gishiri, da duk abunda kikeso OK Sai last of all bitter leaf naki kibarshi for some time ki kwashe馃構馃構馃構馃崚
*chilled tomato soup*
*kayan hadi*
TUMATIR MANYA 5
ALBASA BIYU
MANKUDI
GARIN YAJI CHOKALI BIYU
CURRY POWDER
MAGGI DA GISHIRI
TAFARNUWA UKU
THYME
*yadda ake hadawa*
1) zaki wanke tumatir dinki da albasa,tareda sauran kayan hadinki harda tafarnuwar,,saiki markadesu a blender dinki,,karki zuba ruwa dayawa daidai misali.
2)zaki zuba manki atukunya,ida yy zafi saiki juye wannan markadannaki,rufeshi zuwa minti biyar,,saiki.zuba maggi gishiri da corry dakuma wannan garin yajinnaki,saiki juya harkomai yahadu,,saiki rufeta kibata kamar minti 5, saiki sauketa insha Allahu lokacin tadawo,kinyi miyarki ta tumatir a saukake👌🏻
*_POTATO SOUP_*
_INGREDIENTS;_
_Fish._
_Potatoes._
_Carrot._
_Salt._
_Maggi._
_Butter._
_Onion._
_Pepper._
*_PROCEDURES;_*
_Zaki wanke kifin saidin a saka a tukunya kisa Maggi,salt da albasa ki rufe sai a daura a wuta,a kankare carrot a wanke,a feraye dankali a wanke sannan a yanka da carrots kanana a zuba a cikin kifin._
_Ki wanke pepper da onion Ki yanka a zuba a ciki su dahu suyi laushi sannan Ki sauke, Ki saka mixer Ki farfasa yayi laushi sosai ko Kuma Ki zuba a blender ki markadesu._
_Ki Sami mazubi mai zirfi ki zuba ki sa butter kadan sai a Sha ko Kuma a ci da biredi._
*_HEALTH TIPS._*
SOYAYYAR MIYAR KODA DA CARROT
KODA
ALBASA
TUMATUR
CARROT
KOREN WAKE
ATTARUHU
TATTASAI
Dafarko zaki sami kodarki ki yayyankata ki wanketa kisa gishiri maggi kayan kamshi ki soya kodar inta kusa soyuwa seki yanka albasarki akai seta fara soyuwa seki barbada fulawa akai saiki zuba ruwa dan kadan seki jajjaga kayan miyarki ki zuba ki cigaba da juyawa sai ruwan yakusa konewa saiki zuba karas din dasu koren wake dasu maggi saiki rufe kibata wuta kadan da haka zata karasa nuna se aci da shinkafa ko sakwara😋😋
FRIED PEPPER SOUP
(Obe Ata Dindin)
INGREDIENTS:
1.Kayan ciki,Eggs
2.Albasa, attarugu, tumatir, tattasai
3.Manja/mangyada
4.Maggi, salt
5.Curry, thyme, crayfish, garlic powder, ginger
powder da sauran kayan kamshi.
PROCEDURE:
Ki sami tukunya ki sa manja, idan ya narke sai ki
sa tafashen nama ko kayan ciki ki soya shi, idan
yayi sai ki kwashe, sai ki juye yankakken
albasanki, sannan ki juye nikakken kayan miyanki,
yayi ta soyuwa. Idan kayan miyan ya nuna, sai ki
zuba su maggi da sauran kayan kamshi, ki barshi
yayi 2mnt.
Daga sai ki juye kayan cikin, ki jujjuya ki bashi
kamar 5mnt, a can kuma already kin dafa kwai ko
guda nawa kike so, sai kawai ki tsumbula su a
ciki idan miyar ta nuna.
Za a iya cin miyar nan za da rice, yam, cous cous
da duk abinda zaki hada shi dashi
Wasu lokuta za ki ga kabeji ya cika gari ya yi
araha sosai har mu rasa yadda zamuyi da
shi. Akwai hanyoyi da dama da ake sarrafa
kabeji wanda yawanci arowa mukayi daga
wasu kasashen, saboda muma bai kamata a
bar mu a baya ba duba da dimbin amfanin da
yake da shi a jiki
Abinci masu kayatarwa da akan yi da kabeji
sun hada da
1- Doluman
2- Miya kala kala
3- Salad
4- Coleslaw
6- zuba ssi a cikin wani abincin domin ya
kara armashi
Da sauran su.
A yau ina dauke da Miyar Kabeji ne. Sai a
biyo ni.
Abubuwan Bukata
1. Nama
2. Kabeji
3. Albasa
4. Attarugu
5. Karas da duk wani kayan lambu da kike
bukata a ciki
6. Man gyada ko zaitun (wanda ake miya da
shi) banda manja
7. Garin Corn flour
8. Ruwan naman kaza wato stock
Yadda ake yi
Za ki yanka Kabejin ki bayan kin cire gurin
taurin, sai ki yayyanka shi yadda ki ke so.
Manyan yanka ya fi saboda kanana yana
narkewa. Ki zuba kabejin cikin ruwan gishiri,
kina iya wanke shi a take ko ki bar shi na
dan wani lokaci.
Ki dora tukunya a wuta ki zuba mai dan
kadan kamar karamin cokali 4 haka. Idan
yayi zafi sai ki sa danyen naman a ciki. Ki
bar shi ya soyu sai ki juya dayan gefen shi
ma ya soyu.
Sai ki zuba Albasa (ki yanka ta san ran ki),
ni markada nawa nayi. Ki dafa ta har ta
koma fara sai ki zuba Attarugu ki juya. Ki
dauko karas ki zuba. Kina iya ba shi dan
lokaci kafin ki zuba Kabeji din ko kuma ki sa
kai tsaye.
Za kiga Kabejin ya cika Tukunya. Kar ki
damu idan bai shiga duk ba, ki juya ki rufe.
Idan ya sauka ki kara har ya shige duka.
Ki dauko ruwan naman kaza (stock) ki zuba
ki jujjuya. Ki kara ruwa kadan idan bai isa
ba. Ki rage wuta ki ba shi kamar minti 30 ko
nama ya dahu.
Saura garin corn flour, shi za ki zuba shi
bayan Albasa ko Attarugu, kuma, ki na iya
bade naman da shi. Kar ki damu idan ba ki
da shi, kina iya kwaba garin fulawa kamar
cikin karamin cokali 1 da ruwan sanyi ki zuba
bayan kin sa attarugu.
Kin lura ban ce ki sa kayan Dandano
(seasoning) ba ko? Ki sa duk abinda kike so.
Gishiri, maggi, ganyen parsley, Curry, har da
daddawa in kina so. Ni ban cika sa
seasoning ba a cikin kayan Lambu amma na
saka ganyen Persley.
Zaki iya cin shi kadai ko da biredi, shinkafa
ko taliya ko da abin da ranki ke so. Tare da
fatan kun fahimta?
CABBAGE SAUCE
Barkanmu da wannan lokaci mai albarka a cikin wannan wata na rahama da ibada, da fatan Allah ya karbi ibadun mu. Wannan girki dai na masu karamin karfi ne irinmu domin mu samu damar canjin dandano a bakunan mu a wannan lokaci mai falala dan haka idan uwargida ta koyi wannan girkin to ko gidajen masu wadata ba zasu nuna mata jindadin buka baki ba saboda tsabar dadi da kamshin dandanon wannan girki sannan ko a ido wani ya kalla sai ya fara santi._
ABUBUWAN DA AKE BUKATA*
1- Kabeji
2- Albasa
3- Koren tattasai
4- Jan tattasai
5- Magi
6- Gishiri
7- Man gyada
8- Nama kadan (idan da hali)
9- Kayan dandano (seasonings)
*YADDA ZA A HADA*
_Uwargida ta samu kabeji babba mai kyau sai ta yanke wannan jijiyoyin masu kauri na jiki sai ta yayyanka shi ta zuba a ruwa ta wanke sannan ta tsame ta ajiye, sai ta kuma dauko albasa ta bare ta yayyanka ta yanka mai kyau a kwance sannan ta wanke ta ajiye daban, sai ta kuma dauko tattasai kore da jan duk ta yanka su kanana suma ta ajiye daban_.
Sannan sai ta dauko kaskon suya ta dora a wuta ta soya nama amma naman bada yawa ake sakawa ba (kamar yanka goma kanana) idan kuma babu ma shikenan, bayan ta soya naman sai ta tsame shi ragowar wannan man dake kasko sai ta juye yankakkun albasa da tattasan nan ta soya su amma ba soyawa sosai ba_.
Sai ta dauko wannan wannan kabejin ta zuba akai sai ta dauko magi da gishiri da kayan dandano (seasonings) ta zuba akai sai ta dauko ruwa a kofi ta zuba sai taci gaba da soyawa sannan ta dauko wannan naman ta yayyanka shi kanana sai ta zuba akai, sannan taci gaba da jujjuyawa tana soyawa bayan mintuna zata ga kabejin yayi laushi sosai sauran kayan hadin ma suna hada jiki sun soyu gaba daya, sannan sai ta sauke ta dauko faranti (Plates) ta zubawa magida da iyali ta hada da lemon sha ko kunu mai dadi._
0 Response to "Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa (Koyi Da Kanki)"
Post a Comment