-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

KUNDIN TSATSUBA Hausa Novels

KUNDIN TSATSUBA Hausa Novels

KUNDIN TSATSUBA Hausa Novels



MARUBUCI: Abdulaziz sani madakin Gini

Posting by Abubakar Saleh Quyraemey

Admin @ Top Hausa Group WhatsApp 

Phone number : 08138873799


 Acikin sulusenin darene yayinda kwanakin wata suka cika goma sha biyu yafarka Duk dacewa tsakiyar darene amma gari yayi haske sakamakon hasken farin wata garin yayi tsit bakajin motsin  komai saii tsirarun  koke koken karnuka dana kananun kwari wata irin sassayan mai ratsa jiki tafara busawa adai dai wannan lokacin ne yayi juyi bisa gadonsa cikin yanayin jin dadin baccin babu komai ajikinsa saii wani gajeren wando iya guiwa wannan wando yafi shekara ashirin yana amfani dashi Dan tun yana Neman auren matarsa Zuhur kallo daya mutum xaiyi masa yasan cewa baccin yayi masa dadi sosaii saboda iskar dake shigowa dakin tacikin yar karamar tagar dake kallon gadonsa na karfen rabon da rizyal yasamu isasshen bacci irin nayau tunkafin hatsabibin dansa jafaru yasace kundin tsatsuba yagudu dashi tun bayan tafiyar jafaru din hankalin rizyal yadugunxuma yakasa xaune ko tsaye walau koda daddare koda rana musamman idan yatunada kalaman aljanunnan da yazo masa da batun kudin tsatsuba tun asannan barci yakwarace wa idanunsa abincima ya gagaresa. Abincima ya gagari shiga bakinsa har tsawon kwana arba,in amma shiru aljanin baidawo gareshiba abisa wannan daliline rizyal yashiga izuwa ga bokaye dan Neman kubuta saii da rizyal yaxiyarci bokaye hamsin da Biyar amma Duk Wanda yafadaawa bukatarsa saii yakoreshi yace kar yashafa masa kashin kaji domin al,amarin KUNDIN TSATSUBA yafi karfinsa yayinda rizyal yaje wajen bokan karshe wato na hamsin da biyar din wand yake a Birnin kisra wand ake kirada hajaral murul sai yabushe da dariya yace kwantar da hankalinka ya Abul hikima kakawo kuka inda xa.a share maka hawaye nixan baka maganinda indaiii kavar badashi atsakiyar gidanka babu wani aljanin daya isa yazo gidanka kodajin wannan maganan saii rizyal yayi farin ciki yakawo dukiya mai tarin yawa yabawa Boka shi kuma yadebo wani garin magani yavashi nan take sukayi sallama rizyal yakama hanya yabi fatake su kwana nan su tashi can har suka iso Birnin sin koda rizyal yashiga gidansa koshiga ciki baiyiba yafitoda garin maganin nan yafara barbadashi har saii da yazagaye gidan sa dashi dan kadama iska ta tarwatsashi saii yadinga tona kasa da hannunsa yanasawa aciki daga wannan rana rizyal yakwantar da hankalinsa kan batun KUNDIN TSATSUBA baxato ba tsammani saii gidan Yakama girgixa kamar zaibar doron kasa kaikace bishiya akeson jijjigewa anason zarato daga cikin kasa. Da sauran abubuwa yan mitsi mitsi saii yakwalla kara sa,adda aljani yaji wannan kara na rizyal saii yamaida masa da martanin dariya batare da yace dashi komai ba saii randakagu yasanya yan yatsunsa acikin kunnensa saii yazaro Boka hajarul mukurul yana wutsil wutsil da kafa yadorashi kusa da rizyal sannan yace masa shin ba  wannan ne abun dogaron nakaba  shin ba wannan ne yabaka maganinmu Ba to dakai dashi karyarku tasha karya tabbas kowa yatabamu zaisha mamaki ,idan baka manceba yakai abul hikima wancan lokacin munturo maka wani hadiminmu domin yashiryar dakai hanyanda xai kasance cikin kyakkayawan tsaro wannan hadimin sunansa karizul margus idan baka manceba wannan lokacin kanemi kasan sunansa dana maigidansa amma saii yace dakai baxaka sanshiba har saii ranan da danka jafaru yasamu Kubar muktahul zarbi yabude KUNDIN TSATSUBA tokasani cewa wannan rana taxo gashi yanxu kaji sunan nasa saura na maigidansa tabbas danka ya janyo maka masifan da saii Zarato daga cikin kasa tare da jijiyoyinta wata irin tswa mai ban tsoro tacika dakin da rizyal ke kwana cikin tsananin firgici rizyal ya farka da idanuwansa suka zazzaro sukayi kwala kwala gaba daya jikinsa Yakama kyarma aikuwa take yayi arva da wani mummumnan aljani wanda ko a labari bai tabajin irinsa ba aikuwa rizyal take yakoma kwance a sume koda mummum nan aljaninnan yaga abinda yafaru aiko take tabushe da wata mahaukaciyar dariya take yasuri rizyal cikin abinda baifi dakika daya ba ya luluka dashi acikin gajimare shidai wannan aljani dayasace rizyal sunansa randakal yanada fukafukai guda dubu dari hannayensa kuwa guda dari shidane hakama kafafunsa na iyayin tafiyan sa,a guda acikin dakika Dari yayinda randakal yadauki lokaci yana tafiya acikin gajimare saii asubahi ta riskeshi nanfa mugun sanyi yakada al,amarinda ya janyo farkawar rizyal kenan daga dogon suman dayayi koda ya farka yaga taurari sannan yaleko kasa yaga yana kallon duwatsu da da Cikakkun yan kauye banda kalle kalle babu abinda suke tayi wannan wajenne sukaga bishiyoyi dakuma duwatsu masu siffofin bil,adama kuma rayayyu suna harkokinsu kamar bil,adama adoron kasansu ta duniya ,randakaqu yadakawa su rizyal tsawa cikin rawan jiki suka karasa gareshi faruwan hakan keda wuya saii sukaga wani mulmulallan dutsen dake gabansu yabarbare kamar kwai kawaii saii gawani kerarren gida yabaiyana daga karkashin dutsen babban gida gaba dayan gidan anginashi da zallan dayamon ana cikin haka sai gawata kofa ta bayyana take kofan yafara budewa gama budewan kofan keda wuya saii wadansu aljanu masu kamada randakaqu suka dinga firfitowa atsatstsaye atsatstsaye suka jero har suka iso gabansu rizyal bambamcin wadannan aljanu da randakaqu shine sun nikashi sau goma kaida gani Kasan shine dan kautansu atsakiyar wadannan aljanu saii sukaga wani aljani siriri dogo xanqalele mai suffar bil,adama yaratso yana tafiyar taqama da kasaita yana taku daidaya fuskansa daukeda murmushi har iso garesu awannan lokacin aljanun sun qame qam saboda tsananin biyayya shima aljani randakaqu shima haka yakasance siririn aljanin yayi shiga irinta bil,adama kansa akwai wata farin rawani na zinare sannan jikinsa gaba daya lullube yake da akwai Jar alkyabba ta jauharhaqiqa shigar tayi masa kyau sosaii koda yaxo kusada dasu rizyal saii yace lale marhaban da babban baqo abul hikima tare da shararren Boka hajarul mukurul ina muku barka daxuwa kusani cewa daganan xuwa duniyanku tafiyace ta shekara dubu nine sarki SHAMHARU aljanin dayafi kowane aljani adoron kasa kusani cewa Duk wani Sirrin tsafi to abiyoni zuwa fadata zuwa fadata domin kuji dalilin dayasa nace kai tsaye aljani shamharu yajuya ixuwa fadarsa batare da wata fargababa rizyal da Boka hajarul mukurul sukabi bayansa suko aljanun nan basu motsaba saii bayan su shamharu sun qule cikin gidan nan ,

Sukuwa aljanunnan basu motsaba sanda su shamharu suka qule acikin gidan nan sannan sukabi bayansu randakaqu Ne yatake musu baya nan take gidan takulle kansa kofan nakullewa saii bararran dutsen nan yakoma yahade kansa ,ma,ana dutsen yakoma yanda yake kaikace tun fil azal wani gida baitaba wanxuwaba acikinsa sa,adda rizyal da Boka hajarul mukurul suka tsinkansu a fadar aljani shamharu gaba daya saii suka dimauce saboda ganin irin abubuwan qawanda keciki kuyangi da barori kuwa kaikace su sukayi Kansu saboda tsananin kyau sarki shamharu yayiwa su rizyal dawassu kujeru na alfarma kafin suyi yunkuri tunin wata irin iska ta zuqesu tazaunar dasu awajen take kuyangi sukaxo dauke da abinci irin Wanda su rizyal basu taba ganin irinsa ba ,batare da anyi musu tayiba suka yunkura da niyyan suci Kawai bisa mamaki sai sukaji cikinsu yakoshi fam ,ma,ana sunqoshi koda suka duba abincin da aka kawo musu saii sukaga sun ragu al,amarin dayayi matukar firgitasu kenan saii suka cika da mamaki yaushe mukaci abincin nan Boka hajarul mukurul Ne yayi wannan tambaya ga rizyal,rizyal yace wannan wace irin tambaya ne dani dakaifa duka abun yasamemu ,Abun yasamemu yanda kaji kuma kagani hakanima naji kuma nagani koda jin haka sai aljani shamharu yabushe dawata siririyar dariya kaikace wani tsuntsune yake rera waka mai dankaran dadin sauti lokaci guda kuma yayi shiru sannan yace yaku wadannan baki nawa inaso kusani cewa Duk irin wadannan abubuwa dakuka gani yafaru yanxu kadanne daga cikin sihiri na natsafi,yana gama fadin wannan batu saii yatafi ixuwa wata kasaitacciyar karagar mulki yaxauna take kuyanginnan da barorin nan suka tsaitsaya kikam kamar wassu gumaka ,aljani Shamharu yasake kyalkyalewa da dariya akaro na biyu sannan yadubesu yafara yiwa Kansa kirari kamar haka nine aljani shamharu sarkin taqaddaran duniya mutum da aljan basukainiba a sihiri duniya ta dabance dana mutune da aljanu babu Wanda yasan sirrina nikadai nasan sirrina nikadai nasan tsatsube - tsatsubena koda sarki shamharu yaxo nan akirarinsa saii kuma yafashe da kuka har da hawaye daki -daki lokaci guda yadago kai yanuna rizyal yace kai taqaddarin tsoho kai kadaine kabijiro da abinda xai bayyana sirrina ga duniya kasani cewa kasamu shekaru guda tamanin kana rubuta abubuwan al,ajabi tokasani dukka manyan abubuwan al,ajabi daka rubuta nine sanadinsu Duk aikin dakakeyi muna biya dakai bamuyi tsammanin zaka binciko sirrikammuba har saida mukaga karubuce sirrikammu guda dubu daya abisa wannan daliline mukaga yadace mutsayar da rubutun naka sannan mu adanashi yanda babu Wanda ya isa yakarantashi saboda haka ne muka wakilta aljani karutul bargus akan yaje gareka yayiwa littafinka lakabi da KUNDIN TSATSUBA kuma ya kulleshi da kubar nan na muktahul zarbi haka kuma muku umarceshi daya raba Kuban nan zuwa gida uku yakaisu bangunan karshen duniya uku duk dahakan kuma baka bashi ikon tabbatar da tsaro akan wannan kuba amma sabida sakaci irin nasa saii yashafa,a yakwanta bacci bisa gajiyan aikin dayayi mana har fitinannen danka da fitinanniyar yarinya yalisa suka je suka fito da markahul sabur daga cikin kurukukun sarki LUumanu suka turashi yaje yadauko sassan kubar nan ta muktahul zarbi yawo musu sukuwa suka hada kubar suka bude KUNDIN TSATSUBA ahalin yanxu sun karance shafuka hudu saura shafuka dari tara da chasa,in da shida zasu iya karance littafin nan da shekaru ashirin masu zuwa amma lallai inason kada katar dasu domin lallai idan nakuskura nabarsu suka kammalashi zasu samu irin sirrinkan tsafin danake taqama dashi niko banida burin dayafi ace nafi kowa nayiwa kowa nisa yazamana babu mai taka matsayi irin nawa har abada domin nacigaba da juya duniya kamar yanda ake juya waina acikin kasko ahalin yanxu duniyan kaf nike juyata amma Abu biyune yake Neman kawomin mishikila bakomai bane wadannan abubuwa face MUSULUNCI DA MUSULMAI na yadda cewa ubangijin musulunci yafi qarfina to amma baxanbishiba baxan bauta masaba nayi rantsuwa da ubangidana shugaban taqadararru da bijirarru wato shaidan cewa komai daren dadewa saii nazama sanadiyyan yakan musulunci da musulmai adoron kasa amma baxan samu nasarar yin hakanba har saii idan wani mahaluki bai karance KUNDIN TSATSUBA ba koda aljani shamharu yazo nan azancensa saii ya miki tsaye yadubi rizyal da boka hajarul mukurul yace kubiyoni abaya kai tsaye yawuce ixuwa wani dogon daki sukuwa suka bishi abaya da shigarsu saii suka iske wadansu dogayen akwatunan gilashi rufaffafu guda dari tara da casa,in da tara acikin kowane gilashi gangar jikin mutunce kamannin mutanen gaba daya iri dayane dukansu casa,in da tara din wannan gangan jiki a kafe take ko matsi batayi guda daya daga ciki daya kuma ta kone tayi baki kirin Wanda ke matsin abude take acikinta akwaii akwatin gilashi harma tana iyayin dukkan abunda rayayyun mutane sukeyi sarki shamharu yadubi su rizyal yace kunga wadannan gangunan jikin ba mutane bane ruhine guda Dari tara da casa,in da tara daga cikinsu guda dayane nagaskiya sauran tsafaffune wancan dake cikin wancan budadden gilashin shine na gaskiya kungani daii gaba dayansu siffa dayane kamanni daHuzairu to amma abinda baisaniba shine ba sarki lu.umanu yakashe ba daya daga cikin tsafaffun ruhinsane yakashe kuyi duba ixuwa wancan konannen jikin shine ruhin da aka kashe din cikin sauri rizyal da Boka hajarul mukurul suka waiga suka kalli konannen jikin ,cikin matukar al.ajabi sarki shamharu ya kyalkyale da dariya sannan yatafi ixuwa wannan ruhi mai motsin yatsaya daf dashi yafuskanci juna sannan yace yakai lu.umana kasani cewa ruhinkane anan amma gangar jikin kane acan Birnin taihar haka kuma kambun tsafi natare dakai ajikin hannunka yanxu zan sake aikawa dawani ruhin yakoma jikinka domin ka karbi kasanka sannan kuma ka kashe babban maqiyinka jarumi Huzairu ibn maz,ud kasani cewa yanxu gimbiya sima natare da aljani markahus sabur har yatafi da ita ixuwa garinsu Dan a daura musu aure yaxama wajibi gareka kaje katsayar da wannan daurin auren kuma kasake kamo markahus domin kasake tsareshi awannan kurku naka bamuda bukatan ka kashe domin akwaii aikin daxaiyi mana xuwa nan gaba yayinda shamharu yaxonan azancensa saii ruhi mai motsi ya numfasa yace yakai sarkin duniya mai zai hana kabani umarnin nakashe dukkanin musulmin duniya baki daya tunda sune masu kawo mana cikas a al.amurammu daganan nima sai natafi ixuwa gangan jikina nazauna nacigaba da jindadin rayuwata yayinda shamharu yaji wannan batu saii yabushe da dariya sannan yace yakai lu umanu aibazamu samu daman hallakar da musulmin duniya ba har saii idan an rufe KUNDIN TSATSUBA wato andaina karantashi wannan shine dalilin dayasa natura akazomin da wadannan mutanen biyu wato rizyal da Boka hajarul mukurul idan har munaso adaina karatun KUNDIN TSATSUBA to saii ankoma dabaya an,Ankoma da baya an tattaro labaran da rizyal ya rubutasu sannan asanyasu acikin wani sabon KUNDIN ma.ana dolene ayi KUNDIN TSATSUBA nabiyu sannan shima kuma ayi masa irin wannan ta muktahul zarbi ma.an akulleshi to daga wannan kuba tabiyune za,a iya a kulle wancan KUNDIN TSATSUBA ta hannunsu jafaru har akamosu azo dasunan mu yanke musu hukunci abisa laifin da sukayi mana kodajin haka sai rizyal yayi zunbur yamike yace haba haba yayama haka zata yiyu shin kamantanema saii da na shekara tamanin ina yawo kasa kasa wurin sarakai da tajirai da matsafa ina samo wadannan labarai tabbas yanxu dayawa daga cikin wadannan mutanen sun mutu babu daman samun wadannan labaran saadda rizyal yaxonan azancensa saii sarki shamharu ya tuntsire da dariya sannan yace kai karamin mai basira saurara kaji tarihi baya tsufa Kuma baya mutuwa saii daii masanansa su mutu saboda haka Duk jama,ar daka ziyarta koda sun mutu akwai yayansu idan babu akwai jikokinsu indai labarin yashafesu kobasu saniba to muzamu iya sanyawa su tuno dashi sufada kaikuma ka rubuta shamharu yasake juyowa izuwa ga ruhi mai motsi yadafa kafadarsa sannan yace yakai lu.umanu kayi sani cewa Kaine wakilinmu abangaren masu mulkin bil,adama nasan cewa bakaramar gwagwarmaya zakayiba shiyasama nabaka kariya da ruhi guda Dari Tara da casa,in da tara saboda haka yanxu kanada sauran ruhi dari tara da casa,in da takwas baxaka koma kasarkaba har sai munga bayan makiyanmu koda kuwa wadannan sauran ruhanan zasu kare yanxun nan xantura ruhi nabiyu yaje yashiga cikin gangar jikinka shamharu nagama fadin haka saii yaje yashafi akwatin gilashi na biyu kawai saii ruhin ciki yaratso ta cikin gilashin yafitoTa cikin gilashin ya fito sannan yazama haske saii yabace faruwan hakan keda wuya saii sarki shamharu yabushe da dariya shima ruhin sarki lu.umanu mai motsi shima yabushe da dariya bayan sunyi dariya sun more sai randakaqu yabayyana agabansa saii dubishi yace yakai randakaqu na umarceka daka dauki abul hikima tare da wannan boka nasa kutafi ixuwa ga mutanen nan daya ziyarta awannan lokacin inbasanan kunemi zuri,arsu susanar daku labarin ya rubuta kai kuma hajarul mukurul amfaninka awannan tafiya shine kayi amfani da al.alumanka natsafi wajen kareku daga sharrin masifun hanya kaikuwa randakaqu kakasance kagajarcemuku tafiyan shekara tamanin ixuwa kwana arba.in rizyal kaikuma katabbata karubuta dukkanin wani labari dakuka samu dai dai batare da kayi kari ko ragiba Duk Wanda yayi kuskure akan aikinsa sakamakonsa mutuwa nasallameku ko akwaii mai tambaya rizyal yayi gyaran murya yace yakai sarkin duniya meyasa kaceda Boka hajarul mukurul yabamu kariya ayayin tafiyanmu ahalin karfinku da sihirinku yafi nasa shamharu yayi murmushi yace wannan kuma wani sirrine daga cikin sirrikan aikinmu kudaii kawaii kubi umarni tambaya da bincike baxasu amfanekuba shamharu nagama wannan jawabi yashige cikin wani daki kafin rizyal ko Boka hajarul mukurul suyi wani yunkuri tunin randakaqu ya suresu ya azasu agadan bayansa kafin kibtawar ido yafice daga fadar ya lukuluka cikin gajimare wannan shine abinda yafaru tsananin sarki shamharu da rizyal ma.abocin hikima bayan ansaceshi daga Birnin sin ankaishi Birnin dahazur wajenda tsananinsa da duniya tafiyace ta shekara dubu ga jarumin aljani.


><><><>><<><><>


Al,amarin markahus sabur kuwa lokacin da yaga ya mallaki gimbiya sima sai zuciyarsa tacika makil da farin ciki saii yakara kaimi atafiyarsa dan ya Isa gida domin burisa yagama cika haka daii markahus sabur ya wanxu yanata sauri cikin tafiya amma sai daya shafe kwana goma sha uku sannan ya iso garinsu ,

Ya iso garinsu Samaratu na kwance acikin turakarta daniyan tayi bacci saii ga wata baiwarta mai suna lishiziya tashigo da gudu cikin dakin dazuwa tazube kasa gabanta tace yau kinada babban bako ga danki can markahus sabur yadawo tare da abinda yafita nema koda jin haka saii samaratu ta daka tsalle tadubi lishiziya tace lallai kinxomin da babban albishiri dan haka daga yau na yantaki nan take lishiziya tacika da tsananin farin ciki tayita godiya itako samaratu saii ta ruga da gudu tafita ixuwa waje inda ta iske markahus sabur tare daukeda gimbiya sima tamkar Wanda yadauko gawa cikin farin ciki samaratu ta ruga gareshi suka rungume juna sannan ta janye jikinsa tasake duban sima sannan tace yakai dana hakika kacika gwarzo kuma jarumi abun jarumai yaya akayi kayi arba da sarki lu .umanu da matarsa fatisa .markahus sabus ya numfasa sannan yadubeta yace yake ummina ai wannan ba fatisa bace tunin fatisa tamutu dan tare aka kullemu acikin kurkukun sarki lu.umanu dake karkashin kasa cikin mamaki samaratu tace kai dana dan mexakayimin karya ,Mexakayimin qarya a iya sanina babu wani mahaluki daya taba shiga kurkukun sarki lu.umanu yafito da raiii yaya akayi kafito araye itakuma wannan kyakykyawar daka dauko a ina kasamota markahus sabur yayi murmushi sannan yace ai labarine mai tsawo amma yanxu daii muje ciki muxauna kitaimakamin kitasheta daga barci narasa yanda xanyi tafarka samaratu ta dora hancinta a daii dai na gimbiya sima taje tana numfashi sai ta Dora hannuwanta akan kirjinta Kawai sai ta jijjiga kai tace ai wannan baccin bana kaida bane sihirtaccen barcine idan anaso tafarka saii anyi gagarumar aiki kodajin haka saiii hankalin markahus sabur ya dugunxuma sannan yace yake ummina inaso kisani komai wahalan aikin zanyishi domin ta farfado adaura mana aure yanxu daii muje ciki muxauna Dan nabaki labarin tafiya ta dakuma yanda akayi na mallaki wannan kyakykyawan budurwa samaratu tayi murmushi tace nayarda da hakan saii ta juya tashiga cikin turakar shikuma yatake mata baya dauke da gimbiya sima bayan sun zauna acikin turakarne ta mike takarbi gimbiya sima taje ta kwantar da ita akan gado sannan tadawo inda take zaune suka fuskanci juna batare da bata lokaci ba markahus sabur yabata duk kanin labarin abinda yafaru tsakaninsa dasu jafaru tun lokacin da suka dauko battar qarfe kawo ixuwa yanxu koda jin haka sai samaratu tace hakika nayarda damasu iya magana dasukace sai ansha wuya ake shan dadi kuma kowa kaga yazama wane babanza bane inba ba.asha dare ba ansha rana samaratu tadubi dan nata cikin tausayawa sannan tace kasha wahala dana nikuwa xantsaya tsayin daka domin kacika burinka kamar yanda kasani cewa mahaifinka yamutu shekaru masu yawa abaya Kai yakamata ace kagaji mulkinsa amma saboda Neman duniya bakasamu daman xamaba tabbas ko yau kasanar da sarki cewa kanason sarautarka xai Nada maka rawani ya tunbuke Wanda yake akai yanxu markahus yayi murmushi sannan yace yanxu daii mubar wannan maganan mukoma kan abar begena yaya za,ayine kitasheta daga wannan bacci mai nauyiKitasheta daga barci narasa yanda xanyi tafarka samaratu ta dora hancinta a daii dai na gimbiya sima taje tana numfashi sai ta Dora hannuwanta akan kirjinta Kawai sai ta jijjiga kai tace ai wannan baccin bana kaida bane sihirtaccen barcine idan anaso tafarka saii anyi gagarumar aiki kodajin haka saiii hankalin markahus sabur ya dugunxuma sannan yace yake ummina inaso kisani komai wahalan aikin zanyishi domin ta farfado adaura mana aure yanxu daii muje ciki muxauna Dan nabaki labarin tafiya ta dakuma yanda akayi na mallaki wannan kyakykyawan budurwa samaratu tayi murmushi tace nayarda da hakan saii ta juya tashiga cikin turakar shikuma yatake mata baya dauke da gimbiya sima bayan sun zauna acikin turakarne ta mike takarbi gimbiya sima taje ta kwantar da ita akan gado sannan tadawo inda take zaune suka fuskanci juna batare da bata lokaci ba markahus sabur yabata duk kanin labarin abinda yafaru tsakaninsa dasu jafaru tun lokacin da suka dauko battar qarfe kawo ixuwa yanxu koda jin haka sai samaratu tace hakika nayarda damasu iya magana dasukace sai ansha wuya ake shan dadi kuma kowa kaga yazama wane babanza bane inba ba.asha dare ba ansha rana samaratu tadubi dan nata cikin tausayawa sannan tace kasha wahala dana nikuwa xantsaya tsayin daka domin kacika burinka kamar yanda kasani cewa mahaifinka yamutu shekaru masu yawa abaya Kai yakamata ace kagaji mulkinsa amma saboda Neman duniya bakasamu daman xamaba tabbas ko yau kasanar da sarki cewa kanason sarautarka xai Nada maka rawani ya tunbuke Wanda yake akai yanxu markahus yayi murmushi sannan yace yanxu daii mubar wannan maganan mukoma kan abar begena yaya za,ayine kitasheta daga wannan bacci mai nauyin samaratu ta numfasa sannan tace baxan iya cewa komaiba har saii nayi bincike nan take ta bude wani akwatin karfe datayi budunbudun da kura harma yana tasoma lullubeta samaratu tafito dawani guntun madubi daga cikin akwatin shima saida ta hure qura daga jikinsa da iskar bakinta sannan tafar

Dalasimai na tsafi kafin ajima tajike sharkaf da gumi saii da tayi atishawa sau uku sannan ta ajiye madubin tsafin tadubi markahus sabur awannan lokacin idanunta sunyi jawur kamar anbada mata borkono yakai Dana abun soyuwana hakika banji dadin abunda Nagano ba domin wahalan dazakasha nan gaba ta ninka tabaya sau dari idan har kanaso ka auri wannan kyakykyawar yarinya to sai kasha wahala maimakon jikin markahus sabur yayi sanyi saii yayi murmushi yace yake ummina kiyi Sani cewa aikowane da namiji an haifeshine dan yayi wahala musamman akanku ku mata Duk irin abinda mutum yatara aduniya saii yakare wajen kyautata muku ni inaganin babu wani sabon labari dan na wahala akan auren gimbiya sima narokeki daki hanxarta sanar dani abinda yakamata nayi samaratu tayi gyaran murya sannan tace xanyi maka wata tambaya guda daya kafin nasanar dakai abubuwa guda uku wadanda zaka samo nahada maganinda za.a tashi gimbiya sima daga bacci kasani cewa dolene kasamo wadanda abubuwa acikin mako guda idan kawuce wannan lokacin sima xata mutu Dan kasance cewa ita bil,adama ce ba kamarmu aljanuba su bil,adama basa iyayin wata dogowar rayuwa muddin bacin abinci kafin nayi maka tambayan inaso nasanar dakai cewa akwai wani babban YAKI agabanka bayan ka auri gimbiya sima yakin ko bana komai bane saii na mallakar zuciyarta tasoka kamar yanda kake kaunarta kasani cewa tunin takamu da son waninka bawani bane face Huzairu ibn masud markahus sabur yayi dariya yace haba ummina kinsani cewa acikin al.ummanmu na aljanu babu wani kyakykyawan saurayi kamata balle acikin Bil,adama ninasan cewa gimbiya sima zata soni saii daii idan batayi arba daniba shin kinmantane cewa aganin farko fatisa takamu da qaunata samaratu tace ai ba.anan gizo yake saqaba abinda kakasa fahimta shine ita fatisa ruwa biyuce akwai jinin aljani ajikinta ita kuwa sima bil,adamace zalla lallai aure tsakanin mutum da aljani akwai wuyan sha,ani anayi amma baya qarko amma indai ka iya saye zuciyarta fiye da komai yanxu ga tambayata agareka ina battar nan debo tsumin dodo kiryanu kodajin wannan tambayan sai markahus sabur yayi shiru yashiga tunani daga can saii yanisa yace yake ummina kiyi Sani cewa lokacin dana gabata afadar sarki luumanu nafadi ladan aikina saii yaki amincewa da bukatata saii yakoreni daga fadarsa batare daya karbi tsuminba bayan nabaro Birnin taihar saii na yada zango awani waje saii natsinci kaina acikin mummunan bakin ciki nan take natuno da irin wahalan danasha  har natafi kogon zuhurim da irin wahalan danasha kafin nasamu nadebo tsumin dodo kiryanu amma gashi wahalar tazama ta banza tunda bukata bai biyaba kawaii saii naciro battar da tsumin yake ciki na fyadata da qasa nan take battar yafashe tsumin ya zube.




ramin sai naga wata kyakkyawar aljana tana ta shishshikar kuka nan ta dubeni tace dani mutum ko aljan nan nayi karfin hali nace mata ni mutum ne nace mata yake wannan aljana wanene ya daureki anan kuma ya sunanki koda jin wannan tambaya sai aljanar ta fashe da matsanancin kuka sai da tayi ta gaji sannan ta dago kai ta dubeni tace yakai wannan mutum kayimin tambayar labari mai tsawo amma bari na gajar ce maka shi ni sunana halsiya bin durhal ni yar babban attajiri ce a birnin hindu babana yanada matukar dukiya haka kuma shi dukiyar shi ba atare take a waje daya ba sai dai duk abinda ya shafa da hannunsa take zai zama dinare lokacin da mahaifina ya kwanta cutar ajali ya kadaita dani yace min yake yata ki sani cewa ni yanzu cuta taci karfina domin wannan cuta tawa bata tashi bace saboda haka na kiraki domin zan baki sirrin dukiya ta kuma ina gargadinki da kada ki auri kowa daga cikin zuri ar nan tamu ta aljanu haka kuma kada ki bawa kowa sirrin nan ga wani aljani face wani bil adama da ya baki taimako a sanda kike bukata haka mahaifina ya gama bani wasiyya sannan ya mutu nayi kuka mara tukewa to dama sarkin garinmu wani azzalumin sarkine ke mulki ana kiran sa da suna Durmusalu to a lokacin da durmusalu yaji labarin mutuwar mahaifina yazo ya sameni yace dani ya ke wannan yar attajiri mai sirrin dukiya ni ina gani mai zai hana ki aure ni in yaso kinga sai ki gani kin hada biyu ga mulki ga dukiya koda naji wannan batu sai na ce dashi ya kai wannan sarki kayi sani cewa mahaifina yabar min wasiyya da kada na sake ke na auri wani daga cikin zuri ar aljanu durmusalu yay yay nace nidai mqhaifina ya gargadeni da kada na sake na auri dan uwana aljani kuma kada na bada sirrin dukiyata sai ga wani bil adama da ya vani taimako kodajin haka sai durmusalu ya fusata yace ai ba a sarki biyu a gari daya ya sureni yayi sama dani izuwa wannan daji muna sauka durmusalu yayi tsafi kasa ta tsage muka shigo nan durmusalu yai daddaure ni da igiyar tsafi sannan ya dubeni ya bushe da dariya yace kinga wannan daurin da nayi miki hk zaki ta zama anan har izuwa lokacin da zaki sauya shawara Koda Halsiya tazo nan a labarinta sai ta sake fashewa da kuka sannan tace kuma duk da munyi haka durmusalu baya saurin tafiya sai ya kwana tare dani sannan ya tafi ni yanzu durmusalu ya ruguzamin rayuwa tunda ya sanni "ya mace yakai wannan mutum bil adama kayi sani cewa indai daurin da durmusalu yai min ne baya bata min rai face sani na da yayi "ya mace Ni kuma dana ji wannan labarin na tausa yawa halsiya sosai Inda nima na bata labarina daga farko har karshe sannan tace dani ya sunanka nace mata sunana kufuru bin aljar ya ke halsiya ni yanzu ya za ayi na fita daga wannan dakin karkashin kasa.

kodajin haka sai aljana halsiya ta bushe da dariya sannan tace ai baka da wata mafuta ta tsira yanzu in kaga ka fita daga nan sai ka tseratar da tawa rayuwar kaga duba ka gani ta inda ka biyo cikin hanzari na daga kaina na dubi wajennan da kafata burma sai naga ya shafe babu shi babu alamarsa sannan ajiyar zuciya anan na zauna da halsiya har tsawon wani lokaci cikin jin dadin rayuwa da walwala domin duk abin da nake nanema akwai shi a wajen ana nan sai halsiya ta dubeni tace to kai kufuru sai ka zauna cikin shiri domin saura sa a daya rak durmusalu ya iso nan sai na cewa halsiya,to yanzu ya zanyi sai tace ga wata akwatu nan wadda tsinken sakacen durmusalu ke ciki sai ka bude ka shiga ciki  nan na fara kokawa da wannan akwatin da nufin budeta amma ina abu ya faskara domin girman akwatin ya ninka girmana sau biyar nace wa halsiya na ksa bude akwatin kodajin haka sai halsiya ta bushe da dariya sannan tace gaskiya yan adam ku ragwagene yanzu bude,yar mitsitsiyar akwatinnan shi zai gagareka nan ta buso iskar bakinta akwatin ta bude na shiga ciki sai naji kamar na shiga rijiya gaba dari halsiya ta kara busa iskar bakinta akwatin ta rufe ruf naga ko tafin hannuna bana iya gani ina cikin wannan haline chan sai naji saukar wani abu jif ashe wannan sauka da naji ba ta komai bace face sarki durmusalu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sai da naji kamar dodan kunnena zai cire sannan yace yake wannan yar attari mai sirrin dukiya ki sani yau shekararki dari da hamshin anan shin kin sauya shawarane na tafi dake a daura mana aure ko kuwa tace ina haryanzu ban sauya ra ayi ba ina kan bakana ni yanzu dama kasheni kayi da yafi da takaicin da ka kunsanmun koda jin haka sai durmusalu yace bazan kashekiba nikam saidai nacigaba da more rayuwata dake nan ya bude abincinsa yaci sannan ya bude tulunan giyarsa guda Dari ya shanye akai sa a kuwa yau bai nemi tsinken sakacennasaba amma ko kadan bai sanwa halsiya ba yana gamawa ya farma ta ina daga cikin wannan akwatin na dinga jiyo kukan da ihun halsiya a wannan lokacine nace inda ache ni wani sadaukine daga cikin sadaukan duniya da saina,fito na halaka durmusalu

yana gama  wa ya kama aikin rago

nan fa ya fara munshari tamkar kakarin

Sa

 yayin daa ake yankashi


jim kadan halsiya tacee yakai kufuru sai ka hanzarta ka fito

 yanzu durmusalu yayi nisa cikin barcinsa

koda naji haka sai

nace haba halsiya

ya zaki ce dani haka

nifa yanzu ko tafin

hannuna bana iya gani

halsiya ta bushe da dariya sannan tace

au ashe fa na manta

cewa baza ka iya bude akwatinba

nan take halsiya  ta kara buso iskar bakinta

a karo na biyu

sai naga haske 

ya gauraye ko ina

nan take na kuma  

amfani da wannan igiyar

da shigo da ita na fita

A sannan ne nayi arba

da gangar jikin durmusalu

sai da  naja da baya

saboda tsabar tsoro

saboda girmansa

yakai  na katon dutse

fadin kirjinsa kuwa

yakai kamu tamanin 

kaurin digadigin kafarsa kuwa

yakai kamu sittin

da tsayin kamu dari da ashirin

nan take nayi amfani da

wannan igiyar da na fito  

daga akwatin nayi amfani

da ita na fara hawa

kan kafartasa

sai da na shafe sa,a sittin

kafin na wuce kan kafar tasa

na isa kirjinsa  nayi arba da 

makullin a sakale a jikin

silin gashin

nan take nasa takobina

na fara saran silin gashin

a kalla na sari silin gashin

sau saba,in sannan ya tsinke

na dauko mukullin da kyar

yana rinjaya ta muna faduwa

kasa tare na kawo shi

gaban halsiya

anan ne dabara ta ta kare

don bansan yadda zanyi

na zira makullin akafar

ya bude ba

na dubi halsiya nace

yake halsiya shin yanzu wace

dabara ce kike gani

zan iya yi makullin nan ya budu

Halsiya tace

oho nida bansan yadda zanyiba

tunda da na bada shawarar

yadda za ayi a ciri makullin

nan mukai ta wasa kwakwalwa

nida halsiya har tsawon sa,a guda

daga can sai halsiya taga

na dubeta nayi murmushi

ba tareda nace da ita komai ba

naje na dauko wannan igiyar

na daurata ajikin makullin

sannan na dauki igiyar

naje na ratayata ajikin

wani,karfe dake saman

kan halsiya sannan

nace da halsiya 

ta kama wannan igiyar

da bakinta ta rinka ja

 ahankali ni kuma zan hau kan makullin

idan yazo daidai da kofar kwadon

ni kuma sai na

saita makullin ya fada cikin

kwadon a haka zan juya shi

ya bude

Haka kuwa akayi aka dace

faruwar hakan keda wuya

halsiya ta girgiza sarkar

jikinta ta zube kasa

nan take halsiya ta dauki

takobi ta ta sarewa sarki

durmusalu hannu guda

da kafa guda nan take jini

ya kama bulbulowa daga 

cikin dungulmin

hannun nasa da kafar tasa

na dubi  halsiya

a fusace nace

damme baza ki kasheshi ba

a huta

halsiya tace

ai idan na kasheshi

ban huce takai cin

abinda yayin min ba

kaga idan ya farka

ya ganshi acikin wannan haline

zaiji irin bakin cikin

da nake ji a rayuwata

nan da nan halsiya

ta sureni ta aza agadon

bayanta tayi sama dani 

sai na ganni

a kololuwar sama

bayan tafiyar sa,a guda

aljana halsiya ta saukeni a

 tafiyar sa,a guda rak mukayi aljana halsiya ta sauke ni a baya birnin kisra

sannan ta dube tace muko min hannun ka

yakai wannan saurayi mai sa,a

koda naji ba gardama sai na mika mata hannun nawa

ta sumbata sau uku sannan tace daga yau duk abin da kaso ya zama dinare daka shafeshi

da wannan hannun naka

mai albarka komai yawan abu take zai koma dinare  ta yunkur zata tashi

sai nace dakata halsiya halsiya ta dakata ta dubeni tace

me yasa ka dakatar dani da naji haka sai nace

tambaya nakesan yi miki tabaya ta farko itace

meyasa naga kina kuka tambaya ta biyu itace

meyasa kika sumbaci hannuna sau uku tambaya ta uku itace

yanzu idan kin bar nan ina zaki kodajin haka sai halsiya ta goge hawayen ta tace

amsar tambaya ta farko shine nayi sabo dakai acikin kwana bakwan da mukai

gashi yanzu,ba zamu sake haduwa ba

amsar tambaya ta biyu shine na rabu da dukiya ta wadda na gada a wajen mahaifina na damkata gareka

tambaya ta karshe itace durmusalu ya keta min haddi ya sanni "ya mace

alhalin ba wanda ya taba sani na ‘’ya mace

yanzu da  na rabu dakai zuwa zanyi na kashe kaina

domin idan ban kashe kaina ba durmusalu ne zai halaka ni

don yanzu saura rabin sa,a ya farka tana gama fadin haka

sai ta bude fukafukanta ta tashi sama ta luluka

tun ina iya hango ta har ta bace acikin gajimare

ni kuma na ci gaba da tafiya ina ta mamakin ydd wannan abu ya faru

ina cikin tafiya sai na iso gaban wani katon dutse sai nace

Bari na gwada wannan sirrin da halsiya ta bani akan wannan dutsen mugani

kawai sai nakai hannuna da wannan niyyar na shafeshi

faruwar hakan ke da wuya kawai sai naga dutsen nan

Ya koma tarin tsubin dinare tsube Ban san sa,adda na bushe da dariya ba

Na tasamma birnin kisra da zuwa na iske sarki da fadawa ana fadan ci

na zube kasa na kwashi gaisuwa sannan nace wa sarki

Ni bafatakene nashi go wannan birnin naka da dukiya mai tarin yawa

tana don yin siyayya a kasarka nayi alkawari

zan biya duk harajin daka doramin nazo da ita tana bayan gari

jin wannan magana tawa tasa sarki da jama,arsa suka bushe da dariya

don su azatonsu ni mahaukacine koda na fuskanci haka sai raina ya baci

Nace kasa abini tare da fadawa guda dari in karya nake nayarda kasa a saremin kai

kodajin wannan magana tawa sai jikin sarki da jama,arsa yai sanyi

sarki yasa fadawa muka tafi da zuwa muka iske wannan

dutsen da ya koma tarin,dinare sai fadawa sukai ta mamaki 

Nace mutum hamsin su diba mutum hamsin kuma suyi gadi

dakaru suka dibi dukiya iya iYAwarsu muka tafi gaban sarkin kisra da

zuwan mu wani bawa ya shaida sarki yace ,,,,,,wannan ma bata kai

kashi guda ba daga cikin DUBU,:└(^o^)┘ kodajin haka saboda murna sai

sarki ya rungume ni daga wannan rana na zamo babban aminin sarkin kisra

Kawai Sai Nayi Zamana A Garin, na ci gaba da harkokin kasuwancina harna tumbatsa.

sa adda kufuru yazonan a labarinsa sai ni da sarkin farisa muka cika da natukar al'ajabi muka sallama lamarin kufuru  daga wannan rana kufuru ya jani a jikinsa sosai ya zamana na zamo babban hadiminsa. gaba daya yaransa sai da suka dawo karkashina yazamana nine mai raba musu kudi kuma nike jagorantar komai da komai na dukiyar kfr. haka al amarin ya kasance har tsawon shekara goma wata rana sai kufuru ya kaɗaita dani a turakarsa ya dubeni yace. "yakai abokina kayi sani cewa lokaci yayi da zan cika alƙawarin da na ɗaukar maka na cewar zan taimaka maka ka ɗau fansa akan ɗan uwanka zarusil falis. lallai sai ka kashe shi da hannunka kamar yadda suka kashe mahaifinku kuma sai ka karɓi karagar mulkin misra daga hannusa. yakai abokina kayi sani cewa tun daga lokacin da na hadu da kai nasa bokaye yin aiki bisa wann buƙata 

kuma yanzu sun tabbatar mini cewa yanzu lokaci yayi na aiwatar da komai kai sani cewa tuni yanzu sarkin farisa ya bani dakaru dubu dari wadanda zamu tafi dasu birnin misra muci sarki zarusil falis da yaki don haka ka kwana cikin shiri lallai gobe da safe zamu dau hanya tuni nasa an kera jiragen guda dubu masu inganci da girma don wannan tafiya lallai sa.a na tare damu ko kadan kada ka samu kokwanto a zuciyarka"

kashe gari da safe sojoji dubu dari suka taru a bakin tukun, kowannensu sanye cikin kayan yaki aka kawo isasshen guzuri da dawakai aka zuba ajiragen ruwa guda Dußu nida kufuru ne kadai tare da wadannan dakaru nan take muka shiga jiragen muka nausa cikin teku bayan tafiyar wata da watanni ne muka isa birnin misra koda da zuwan mu kofar gari sai attajiri kufuru yasa aka rubuta wasika kamar haka:-

Daga Hadiyas Bin Zalhik

zuwa ga sarki zarusil falis.

yakai dan uwana kayi sani cewa shekaru goma baya ka kashe mahaifinmu kai da "yan uwanka kuma a sanadinku mahaifiyata ta mutu ni kaina da kyar nasha da takuna. to yau gani na dawo da niyyar kasheka kuma na karbi kambun mulki. don haka sai kayi shirin kare kanka. ganinan isowa da dakaru Dußu dari. nan take aka baiwa wani soja wannan takarda ya hau doki ya sukwane shi har ya isa fadar zarusil falis. da takarda A DAKACE MU......

please wait a moment in shortly #mbr


KUNDIN TSATSUBA 3

Littafe na uku .

Na Abdul a ziz sani madakin gini

Typing. Suleiman' Zidane kd 

WhatsApp 09064179602.


Shiri kafin mako biyu nan take mayakan suka tabbatar masa da cewa zasu cigaba da shiri har nan da mako biyun batare da bata lokaci ba yayi sallama dasu yadawo gida domin yayi sallama dani awannan lokacin ina daukeda cikinka wata takwas jikina yayi nauyi bana iyayin komai saii daii kuyangi suyimin ina zaune aturaka yabayyana gareni cikin shirin yaki gaba dayan makamansa na yaki natare dashi koda naganshi cikin wannan halin saii hankalina yatashi namike zumbur natareshi ina mai cewa yakai mijina ina zaka yanxu cikin shirin yaki haka mahaifinka yayi murmushi mai taushi agareni yace kwantar da hankalinki ba yaki zantafi ba zankai ziyarane gawani boka wai shi zamarul hakma acan dajin ramlas domin neman taimako akan wani gagarumin yakin dake gabammu koda yazo nan azancensa saii nafashe da kuka al,amarin daya tayar masa da hankali kenan ainun yafara rarrashine yana cewa ina dalilin kukanki ya abar kaunata alhalin gani atare dake dolene nayi kuka domin nasan cewa abunda zan haifa zai zamo maraya yakai mijina kasani cewa duk abinda yafaru jiya afada nasamu labarinsa nasan cewa duk shirye shiryenka na yaki da azzalumi dauwamur huzubur tabbas yafi karfinmu lallai idan kukayi gaba da gaba dashi saii yayi nasara akanka narokeka narokeka dan darajar soyayyar dake tsakanina dakai kajanye batun yakin nan zaifi kyau murungumi kaddara mu kyale dauwamur huzubur yashigo kasarnan yayi abunda ransa yakeso nasan duk haqilo dakakeyi akan rai dayane wato ran Yar uwarka sarauniya shin yanxu zakaso arasa miliyoyin rayuka saboda Yar uwarka sarauniya kenan yayinda yaji wannan tambayan saii jikinsa yayi sanyi hankalin sa yakara dugunxuma baisan sa,adda idanunsa suka ciko da kwallaba Yakama kuka daga can kuma saii yakwala ihu mai firgitarwa har sanda barorin gidan da kuyangi gidan suka hallara agabansu koda sukaga babu komai saii suka koma mahaifinka yadago kai yadube ni yace yake abar kaunata  kiyi Sani cewa duk fadin duniyan nan babu abinda nakeso sama da Abu uku .

Zidane kd.

 Abu uku abu nafarko shine Yar uwata gimbiya hashlai nabiyu kuma shine mulkin kasan nan Wanda nagada tun iyaye da kakanni Abu na uku kuma shine ke na rantse da iyaye da kakanni baxan bari wani mahaluki yaxo yaketa al,adanmuba wajibine agareni na natsare sarauniya natsare mutuncinta natsare lafiyanta hakika nayi niyyan aiwatar da hakan babu gudu babu jada baya saboda haka ashirye nake nasalwantar da rayuwata dan ganin bayansu lokacin da mahaifinka yazo nan azancensa saii nasake fashewa da kuka har zuwa dan lokaci shi kuwa bai gusheba  yana lallashina har nadaina kukan sannan yace ni yanxu naxone nayi miki bankwana kuma baxan dawoba saii bayan mako biyu 

Kodajin haka saii na rungumeshi nace yakai mijina hakika Wanda yayi nisa bayajin kira babu wani kalma daxanyi amfani dashi dazaisa kajanye wannan maganan abunda nakeso dakai shine kayimin sallama irinta mai ciwon ajali ma,ana idan kanada wata wasiyya daxaka bari kafadeta domin inaji ajikina cewa wannan rabuwa daxamuyi dakai itace ta qarshe banyi tsammanin zamu sake haduwaba nan take tausayina yakama mahaifinka yasake rungumeni yana mai zubda hawaye yace Dan mexakice haka alhalin nagaya miki cewa zandawo bayan mako biyu yayinda naji wannan tambayan saii nadago kaina nace yakai mijina inasan kasani cewa ita tafiya kafin kayitane kake da ita amma dazaran kayita to kuwa itace take dakai saii abinda hali yayi nidaii inayi maka fatan alkhairi da samun nasara amma lallai kabarmin wasiyya sannan shima yace yake abar sona mafi soyuwa araina wasiyyata guda daya ce agareki inaso ki kasance mai matukar kaunar abinda xaki  haifa idan yakasance namiji kikyautata mishi komai yabukaci kiyi mishi kiyi mishi kar yabukaci wani abu yarasa sannan ki horar dashi bisa rashin tsoro da jarumtaka burina yagkdeni kuma ki rada masa suna MARKAHUS SABUR yayinda naji wannan sunan saii farin cikin wannan sunan domin kuwa ma,anar sunan shine magajin uba nadubeshi nace menene hikimarka akan wannan yadubeni yace ,

Zidane kd

>>Azzalumai domin naji irin Gwagwarmayar dayayi da Azzalumai dakuma azzalumi dauwamur huzubur shin yamutune a filin daga kokuwa cuta yayine tazamo ajalinsa ? Meyafarune da yar uwarsa gimbiya hashlai shin sarki dauwamur huzubur yabiya bukatarsa da ita kuwa ? Shin itama gimbiya hashlai bayan da sarki dauwamur huzubur yabiya bukatarsa da ita yakashetane kamar yanda yakeyiwa sauran yan uwanta mata ? Kokuwa cutace takasheta ? Yayinda samaratu taji wadannan tambayoyin daga bakin danta markahus sabur saii ta nisa tace yakai Dana kasani cewa wannan labari mai tsawone kaga tun safe muke zaune anan gashi har dare yaraba yanxu kayi hakuri kaje kakwanta kahuta kodan Saboda gajiyar doguwar tafiya dakasha zuwa gobe saii naci gaba dabaka labarin kuma kada kamance akwaii batun sauran abubuwa guda biyu Wanda zaka nemo yayin tafiyarka ixuwa kogon zuhurum saii goben zangaya makasu markahus sabur yamike tsaye sannan yace yake ummina menene amfanin sauran abubuwa biyun ai zatona tsumin dodo kiryanu yafisu muhimmanci samaratu tayi murmushi tace aa bai fisuba kaidai kayi hakuri zuwa goben zakaji komai nan daii sukayi sallama yatafi dakinsa ya kwanta wannan shine abinda yafaru tsakanin markahus sabur da mahaifiyarsa samaratu bayan ya Isa gida da gimbiya sima da nufin aurenta _______Acan birnin BAHAZUM  kuwa wata daulace Wanda al,ummar musulmi suka mamaye aqalla akwaii garuruwa zasu kai hamsin da biyar a karkashin wannan kasa dolene inda kaga rayuwar al.ummar dake wannan nahiya abun yabaka sha,awa domin kuwa ana zaman adalci babu wani bambamci tsakanin attajiri da talaka wadannan mutanen suna tafiyar da rayuwar sune bisa Shari,ar musulunci daga cikin wadannan garuruwa akwai wani dan karamin gari wanda ake kiransa da SAHARU shugaban al,ummar wajen sunansa ABUL UZAIRU ma,ana shine mahaifin jarumi uzairu amma ainihin sunansa shine MAS,UD ,mas,ud nada mace daya rak ana kiranta da suna Maryamu, maryamuce mahaifiyar jarumi uzairu kuma tun daga kansa basu sake samun.

Zidane kd

<b><fg=b00000ff>

}>>> samun haihuwa ba atakaicema daii rabonsu da ganin jarumi uzairu ya dauki lokaci mai tsawo kuma sunyi sallama dashine akan cewa yatafi yada addinin Allah zuwaga wata kasa Wanda ake kira SULBAYYA kuma zai dawo nan da wata guda indai yana raye kasar sulbayya daulace ta wassu manyan kafurai ma,abota bautan rana dayawa daga cikin mutanen bahazul sun rasa rayukansu akokarin shiga wannan gari don yada addinin musulunci mutanen sulbayya sun kasance masu matukar taurin kai da rashin imani kuma rikakkun matsafane ansha yin yaki tsakanin daular bahazul da daular sulbayya amma ragas akeyi ma,ana kare jini biri jini don haka kasashen biyu suna shakkan juna lokacin da maryamu taga danta uzairu taga  yashafe wata hudu bai dawo gidaba sai hankalinta ya dugunxuma takasa samun sukuni dare da rana wani lokacin saii daii tashiga daki tayita kuka batare da ansan halin da take cikiba bawani Abu bane yakesata kukanba saii dan irin tsananin sonda takeyiwa jarumi uzairu shiko mas,ud ko kadan baidamuba tundaga ranar da uzairu yabar gida ya cigaba dayin harkokinsa nayin hidima ga addinin musulunci daya saba bai sakeyin maganan uzairuba ,watarana yana barci cikin dare daya farka sai yaji maryamu nakuka mas,ud yamike tsaye yaje kanta batare data saniba kawai saii jin muryarsa tayi yana cewa yake matata ina dalilin kukanki awannan dare cikin firgici tadago kai tadubeshi gameda goge hawayenta sannan tace babu komai mas,ud yayi murmushi sannan yatsuguna dab da ita yadafa kafadarta yace kadaki boyemin damuwarki kiyi Sani cewa nine mijinki kuma iyayenki sun rasu bakida wani Wanda yafini yanxu aduniya nazamo tamkar uwa da uba yanxu agareki babu Wanda yasan halinki sama dani hakazalika nima babu Wanda yasan halina sama dake iya tsawon zamana dake yau shekara talatin kenan yaune ranata biyu Dana taba ganin kukanki rana nafarko itace ranan da mutanen kasar sulbayya suka kawo hari iyayenki suka rasu ranata biyu itace yau sanardani hakikanin abinda yafaru me

Zidan kd

KUNDIN TSATSUBA PART 3F}>>> Yafaru menene yafaru yayinda Maryamu taji Wannan batu saii tayi ajiyar zuciya sannan tace hakika abinda kafada dangane dani gaskiyane dan haka kuwa zanfada maka gaskiyar lamarina akan abunda ka bukata  kasani cewa dan mu UZAIRU yayi mana bankwana akan xanje kasar sulbayya dan yada kalmar Allah kuma yasanar damu cewa bazai wuce wata dayaba zaidawo gashi yau wata hudu kenan shiru babu labarin sa nasani cewa idan ya hallaka bisa wannan tafarki domin yayi shahada saii daii natayashi farin ciki to amma abinda yafi damuna shine kullum saii nayi mafarki dashi kuma acikin mafarkin ana nunamin cewa yana nan araye amma rayuwarsa nakokarin shiga cikin hadari wannan shine dalilin dayasa kaganni ina   kuka domin bansan yanda xanyi na taimaka mishiba sa,adda mas,ud yaji haka saii yayi shiru yana tunani bayan gushewar dan lokaci saii yadubi maryamu yace yake matata hakika mafarkinki abun dubawane domin nima nataba yin mafarki to babu abinda xamuyi face mushirya mutafi bahazul domin muje musamu shugaba musanar dashi abinda yake damunmu domin yakasance babban malami kuma masanin fassarar mafarki idan yayi istahara zaisanar damu hakikanin halinda uzairu yake ciki sai mushirya muje domin muji daga gareshi nan take Maryamu taji farin ciki ya lullubeta tunda asuban fari suka shirya suka kikkintsa suka kama hanyar birnin bahazul saii da suka shafe tsawon kwana uku sannan suka Isa birnin bahazul dashigansu cikin Birnin Birnin bahazul suka nemi gidan imam Khalid dayake sanannene nan danan akayi musu jagora zuwa gidansa dazuwa suka iskeshi a kofar gida yana bayarda fatawa ga almajiransa koda yaga baki saii yamike yataryesu cikin farin ciki sannan yadubesu yace da maryamu tashige ciki taje wajen matarsa ta huta shikuwa mas,ud saii aka bashi abun zama yazauna sannan aka kawo masa abinci da abin sha yaci yasha sannan yayi hamdala bayan imam Khalid ya sallami almajiransa yadubi mas,ud suka fuskanci juna sannan yace yakai wannan dan uwa hakika ina ganin kamar muntaba

Zidane kd


KUNDIN TSATSUBA PART 3G}>>> Kamar muntaba saduwa abaya daga ina kafito kuma meke tafe daku yayinda mas,ud yaji wannan tambaya saii yayi murmushi yace ya shugabana ni mutumin saharu ne hakika muntaba saduwa sa,adda akayi yakin karshe tsakanin kasar nan da kasar sulbayya nine wanda yakawo maka dauki sa,adda wani kafiri ya fincikoka daga kan doki kafado kasa yakawo maka mummunan Sara da tokobi nayi azama nakare saran nasokeshi da mashina yafadi kasa matacce koda jin wannan maganan saii imam Khalid ya rungume mas,ud cikin tsananin farin ciki sannan Yakama hannunsa suka shiga cikin gida gava daya da shigarsu suka iske Maryamu da matar imam Khalid zaune atsakar gida suna hira cikin nishadi su biyun suka dago kai suka dubesu saii suka cika da mamaki domin mas,ud da imam Khalid na rukunkume da juna tamkar yan uwanda suka dade basu haduba cikin mamaki hasiyatu matar imam Khalid tadubi mai gidan nata tace yakai mijina shin kunsan junane kodaii kun kasance yan uwa bamu saniba.

Zidane kd...

WhatsApp 09064179602

1 Response to "KUNDIN TSATSUBA Hausa Novels"