Dalilan Da Yasa Kotu Ta Bada Umarnin Kama Dauda Kahutu Rarara
Dalilan Da Yasa Kotu Ta Bada Umarnin Kama Dauda Kahutu Rarara
Wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta bada umarnin damko fitaccen mawakin shugaban kasa Buhari, Dauda Kahutu Rarara.
Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda yake shugabantar shari'ar, ya bayar da umarnin damko fitaccen mawakin sakamakon rashin bayyanarsa a gaban kuliya don kare kansa daga zargin da ake masa.
Tun dai daga farko, alkalin ya aika wa mawakin sammaci tare da bukatar ya bayyana a ranar 22 ga watan Disamban 2020 Ana tuhumarsa da boye wata matar aure ba bisa ka'ida ba. Wani mutum mai suna Abdulkadir Inuwa ne ya kai karar mawakin kotun domin neman hakkinsa.
Inuwa yana zargin Dauda Rarara da sanya matarsa ta aure a wani bidiyonsa na wakar siyasa mai taken 'Jihata Jihata ce.' Ya tabbatar wa da kotun cewa an kwashe tsawon wata daya ba a ga matarsa ba, kwatsam sai ga ta a bidiyon. A saboda haka yake rokon alkalin da ya bi masa hakkinsa.
Source: legit
0 Response to "Dalilan Da Yasa Kotu Ta Bada Umarnin Kama Dauda Kahutu Rarara"
Post a Comment