Farashi: Me yasa farashin albasa yayi tashin gwauron zabi a duk fadin Najeriya
Sunday, November 8, 2020
Comment
Farashi: Me yasa farashin albasa yayi tashin gwauron zabi a duk fadin Najeriya
Farashin buhun albasa ya tashi sama da kashi 200 cikin 100 a wurare da yawa musamman a kudancin kasar Najeriya
Saidu Baba, wanda ke sana’ar gwari a kasuwar Ose da ke Onitsha, Jihar Anambra, ya alakanta tsadar Albasa da ambaliyarda aka samu a arewacin kasar da kuma chanjin hamada, zanga-zangar Endsars.
Acewarsa, farashin ya tashi daga N22,000 zuwa N70,000 a yanzu haka, Bincike ya kuma nuna cewa a jihar Ondo buhun albasa wanda ada ake sayar da shi kan N20,000 yanzu yatashi zuwa N62,000.
A kasuwar Farin-Gada da ke Jos, Jihar Filato, buhun albasa wada ada ake sayarwa a kan N17,000 kafin zanga-zangar "Endsars" yanzu farashinsa yatashi zuwa N60,000.
0 Response to "Farashi: Me yasa farashin albasa yayi tashin gwauron zabi a duk fadin Najeriya"
Post a Comment